Thursday, August 28, 2014

Ta'aziyar Rasuwar Malam Magaji Danbatta

SAKON TA'AZIYAR RASUWAR MALAM MAGAJI DANBATTA

Yau na sami labarin rasuwar daya daga cikin Manyan dattawan da jihar Kano ta ke da su, kuma wanda rayuwarsa ta kare wajen hidimtawa al'ummar jihar Kano da Najeriya baki daya. Dattijo Malam Magaji Danbatta mutum ne wanda tsohuwar jihar Kano da ta hada da Jigawa ayanzu zasu jima suna tunawa da rayuwarsa kuma suna alfahari da irin gudunmawar da ya bayar a rayuwarsa dan bunkasa da cigaban wadannan jihohi.

Ba shakka, Malam Magaji Danbatta mutum ne da aka yi rashinsa sosai a tsohuwar Kano da kuma Kano ta yanzu. Malam Magaji Danbatta na daga cikin dattawa mutum shida da jhar Kano ke takama da su, kuma shime mutum na biyu cikin wadannan dattawa da ya kwanta dama. Ba jimawa muka wayi gari da rasuwar Sarkin Kano marigayi Alhaji Ado Bayero, wanda rasuwarsa ta girgiza Najeriya baki daya, kasancewarsa mutumin da ya yi tasiri matuka a rayuwar al'umma.

Malam Magaji Danbatta ya wakilci Kano a fannoni daban daban na rayuwa a Najeriya, ya kuma kasance mutumin da ake mutunawa kuma ake darajtawa a lokacin da yake raye. Akwai wani al'amari mai ban sha'awa a rayuwar Malam Magaji Danbatta, a wasu lokuta a baya ba zan iya tuna lokacin ba, amma 'ya 'yansa sun shirya wani biki da ya kayatar kwarai da gaske a Kano, inda suka taya mahaifinsu Magaji Danbatta murna cika Shekaru 50 da yin aure.

A yayin wannan biki da aka yi shi a gaban dubban jama'a Malam Magaji Danbatta ya bayyana cewar matarsa bata taba yi masa laifin da yayi Allah-wadai da ita ba, ya kara da cewar a tsawon wadannan shekaru 50 matarsa bata taba yin yaji ba, ya ce kuma kullum yana kara jin soyayyarta a cikin ransa, yayiwa 'ya 'yansa godiya a yayin wannan biki sannan kuma ya yi kira a garesu da sauran jama'a da suyi koyi da soyayya irin ta dattawa.

Muna addu'ar Allah ya jikan Malam Magaji Danbatta ya yafe masa kura-kuransa ya sa Al-jannah ce makomarsa Iyalansa kuma muna taya su al'hinin wannan rashi da suka yi. A madadina da dukkan dangi da 'yan uwa da abokai muke taya Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi Na Biyu da Gwamnan Kano Alhaji Rabiu Musa Kwankwaso da Gwamnan jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido ta'aziyar wannan rashi da muka yi Allah ya jikansa ya gafarta masa. 

Haka kuma muna mika ta'aziya ga Alhaji Dakta Aminu Alhassan Dantata da Khalifa Isyaka Rabiu da Yusufu Maitama Sule (Danmasanin Kano) da Alhaji Tanko Yakasai da suke zaman manyan dattawa a jihar Kano, Allah ya kara musu lafiya da jinkiri mai amfani.

Yasir Ramadan Gwale
28-08-2014

No comments:

Post a Comment