Tuesday, August 5, 2014

Gaskiyar Malam Nuhu Ribadu Ta Bayyana


GASKIYAR MALAM NUHU RIBADU TA BAYYANA

JAridar Premium Times ta ranar Lahadi ta ruwaito labarin cewar Jam'iyyun APC da PDP na matukar zabarin Malam Nuhu Ribadu dan ya yi musu takarar Gwamna a zaben cike gurbi da za ayi a Adamawa a watan Oktoba mai zuwa. Dukkan jam'iyyun biyun sun nuna cewar babu wani mutum da yafi cancanta da wannan takarar a wannan lokacin Kamar Malam Ribadu. Jaridar ta ruwaito fadar Shugaban kasa na rokon makusantan Ribadu kamar tsohon Amininsa kuma Shugaban Jam'iyyar PDP Alhaji Adamu Muazu da su yiwa Allah su roki Nuhu Ribadu ya shigo PDP dan ya yi musu takara a cikin jam'iyyar, tuni dai fadar Shugaban kasa ta kafa wani kwamiti da zai zauna da Malam Nuhu Ribadu dan ya lallabe shi ya shigo PDP, kwamitin dai an kafa shi karkashin jagorancin Ministar kudi Dakta Ungozi Okwanjo Iwela.

A nasu bangaren jam'iyyar APC sun nuna matukar kaguwa akan Malam Nuhu Ribadu ya amsa cewar zai yi musu takarar gwamnan a arkashin jam'iyyar. Sai dai masharhanta da dama na ganin da wuya Malam Nuhu Ribadu ya samu cikakken goyon bayan tsohon mataimakin Shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar wanda ake yiwa kallon shi ne uban jam'iyyar a jihar Adamawa, a cewarsu akwai tsohuwar jikakkiya tsakanin Ribadu da Atiku Abubakar. Haka kuma wasu na ganin APC zata yiwa Malam Nuhu Ribadu turin jeka-ka-mutu ne idan suka bashi wannan takara, ta hanyar zuba masa ido shi kadai ba tare da nuna masa wani cikakken goyon baya ba. A yayin wasu ke ganin idan Ribadu ya amsawa PDP to zai samu cikakken goyon baya ba kuma tare da ya kwashe kwabonsa ba.

Sai dai wasu da dama na ganin tuntuni Malam Nuhu Ribadu na da korafi akan jam'iyyar tasa ta APC domin, an jiyo Ribadu na korafin yadda jam'iyyar ta dauke kanta daga halin da tsohon Gwamnan jihar Murtala Nyako ya fada, Premium Times ta ce Malam Ribadu yayi korafi sosai akan yadda aka zubawa Nyako ido a cikin jam'iyyar aka asa yin wani katabus dan sasanta tsakaninsa da 'yan majalisar. Haka kuma, jaridar ta ce, daman kuma APC bata zabi duk wanda Malam Nuhu Ribadu ya marawa baya ba a zaben jam'iyyar da ya gudana a kwanakin baya.

Da wannan ne wasu masharhanta ke ganin PDP na iya samun galabar janyo ra'ayin Malam Nuhu Ribadu duba da cewar jam'iyyar ta APC bata cika nuna damuwa da irin kokarin Nuhu Ribadu ba. Sai dai a nasa bangaren har yanzu Malam Nuhu Ribadu bai ce komai ba akan batun, da Premium Times ta tuntubi mai magana da yawun Nuhu Rubadu Abdulaziz Abdulaziz ya ce, Nuhu Ribadu yana tattaunawa tare da tuntubar mashawartansa akan wannan al'amari.

Babu shakka gaskiya da rikon Amana da Malam Nuhu Ribadu ya nuna a dukkan ayyukan da ya rike sune suka janyo masa wannan daukakar da manyan jam'iyyu ke rokonsa Allah ya yi musu takara, duk kuwa da cewa Ribadun bai nema ba kuma bai nuna sha'awarsa ta yin takarar ba.

Yasir Ramadan Gwale
05-08-2014

No comments:

Post a Comment