Monday, December 28, 2015

Hattara Jama'ah



HATTARA JAMA'A MUSAMMAN  MASU ABABEN HAWA!

Dazu dan uwa Tijjani Ahmad yake bamu labarin wata fitina da ta kunno kai a cikin wasu unguwannin cikin Birnin Kano. An wayi gari wasu mutane marasa tsoron Allah masu fama da cutar bakar Hassada da mugunta da Kyashi da munanawa Allah zato suna bi unguwanni suna Bankawa motocin mutane wuta babu gaira babu dalili a lokacin da Sahu ya dauke, abin ya faru a unguwar Gwammaja da Tal'udu da kuma Titin Aminu Kano. Dan haka, jama’a musamman wadan da suke da motoci kuma ba suda garejin aje mota suke barin su a waje suna kwana, ya zama dole a sanya ido. 

Mutanen da suke aje motocin su a makarantu ko wani filin unguwa da su lura kuma su sanya ido sosai, a samu masu gadi san kare dukiya. Ba shakka duk wanda zai sanya motar mutane wuta ta kone kurmus dan kawai Hassada da Kyashi to wannan ya kai matukar mutum mara tsoron Allah. Ana bi ana kashe mutane babu ji babu gani, ba tare da wani hakki ba. Yanzu kuma abin ya koma kan dukiyoyin mutane lallai lokaci yayi da mutane zasu tashi dan baiwa unguwannin su da dukiyoyinsu kariya. Ya Allah ka kare mu da karuwar ka, masu wannan mugun nufi Allah ka tona asirinsu. Ya Allah ka tsare mu ka tsare mana dukiyoyinmu. 

Yasir Ramadan Gwale 
28-12-2015

Thursday, December 17, 2015

Taya Murna Ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari Ya Cika Shekaru 73


Abokina Attahiru Muhammad Marnona a lokacin da na taya Malam Nuhu Ribadu murna ya cika Shekaru 55 yayi ta min Wa'azi cewa Ahlussunnah basa yin Happy birthday. Yau kuma kwatsam sai na ci karo da sakon sa a Whatsapp yana tunasar da ni cewar a yau ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya cika Shekaru 73 a duniya, dan haka yana fatan yaga na taya Shugaban kasa murna indai ba kiyayya nake ba. Nai musrmushi 😊. Albashirin Marnona? Ina fatan zai ce Dabino, a madadin ni kaina da dukkan ahalin mu muna yiwa Shugaban kasa fatan alheri a cikin wadannan Shekaru 73 da yayi a duniya, ina fatan kuma wannan ya zama tuni a gare shi cewar kaso mai yawa na daga kwanakinsa a duniya sun wuce, ba ko Shakka abin da ya rage masa ba mai yawa bane, Ina rokon Allah ya bashi ikon Aikata alkhairi mai yawa a kwanakin da suka rage masa. Har yanzu mutanan Nigeria suna kyautata zato a gare ka Shugaban kasa, muna fatan Allah ya baka lokacin da zaka cika dukkan alkawarin da ka dauka, ina maka fatan alheri da fatan duk alkawarin da kayi ya zama hujja a wajenka ba hujja a kanka ba.

Haka kuma, ina amfani da wannan dama wajen yin kira ga Shugaban kasa, akan ya gargadi kasashen duniya masu yiwa Nigeria shisshigi a cikin abinda ya shafe mu na cikin gida. Yana da kyau Shugaban kasa ya nuna irin wadannan masu katsalandan cewar Nigeria kasa ce mai cikakken iko da take cin gashin kanta, bama karkashin ikon ko wace kasa, duk abin da ya shafe mu na cikin gida bai kamata wata kasa tai mana shisshigi a ciki ba, matukar bamu nemi taimako ko agaji ba. Allah ya taimaki kasarmu Nigeria ya sada mu da dukkan alkhairai wadan da zasu amfane mu. Masu yi mana katsalandan kuma muna daga musu dan yatsan gargadin karshe. ☝☝☝☝

Yasir Ramadan Gwale 
17-12-2015 

SHIAH: Nasiha Daga Bakin Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi Na Biyu


SHIAH: NASIHA DAGA BAKIN MAI MARTABA SARKIN KANO MUHAMMADU SUNUSI NA BIYU

A dangane da abinda ya faru a Zaria, Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi Na Biyu yayi Nasiha mai ratsa zukata akan wannan batu. Ya kuma yi kira mai matukar muhimmanci.  Na san da yawan mutanan Kano sun saurara jiya a Freedom Radio. Tun lokacin da akai wannan batarna'ka tsakanin yaran Sayyid Zakzaky da Sojoji na zabi kame baki na kan wannan lamari, domin abu ne da nake gani tsakanin sojoji da masu kunnen k'ashi. Cikin ikon Allah, daya daga cikin abinda yake damuna a Rai sosai game da Shiah da Zakzaky, mai martaba Sarkin Kano ya wanke mun shi.

Ta bakin Sarkin Kano,  Kasar Najeriya an gina Musulunci ne a bisa doron Ahlussunnah Wal Jama'ah. Dan haka duk wanda ya zo da batun darikun sufaye da sauran su, to daga baya ya zo da shi. Haka kuma, kamar yadda Sarkin ya fada, tun farko anyi sakaci, domin, an san Da'awar Zakzaky karya ce ba Musulunci bane, akai shiru aka barshi ya shiga kauyuka ya tara jahilai a matsayin mabiya, har yake neman zamarwa al'umma barazana shi da mabiyansa na kin mutunta dan Adam da kuma dokokinsa hukuma. 

Tabbas akwai laifin Sarakuna wajen yaduwar Shiah a Najeriya, domin sun san tushen Musulunci babu aqidar Zagin sahabbai ko Matan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam, amma sabida ana ganin Ahlussunnah ne ke adawa da abin da kuma kausasa harshe akan koyarwar Shiah, sai ake ganin kamar matsala ce da ta shafi Ahlusunnah ko 'yan Izala Sarakuna sukai kurum Zakzaky na halaka musu al'umma, alhali an san karya yake yi ba Musulunci yake ba.

Alhamdulillah, ya zuwa yanzu Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi ya farga, kuma ya ankarar da 'yan uwansa Sarakuna da Sauran al'umma cewar,  Musulunci a Najeriya an gina shi ne akan koyarwar Ahlussunnah Wal Jama'ah, dan haka an gina mu akan mutunta dangi da iyalan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam da suka hada da Ahlulbaity da Sahabbai da Matansa Sallallahu Alaihi Wa Sallam. Allah ya sakawa Mai Martaba sarki da wannan nasiha mai matukar muhimmanci. 

Kuma wani abin Albashir ga al'ummar Musulmi a Najeriya, shi ne, Wannan Waki'a ta Zaria da ta auku tsakanin Soji da Yaran Zakzaky, tayi Sanadiyar Kawo karshen yadawar  Shiah a Najeriya In sha Allah. Domin filin Husainiya da ake yin kafurci da zagin Sahabbai a cikinsa, asalin sa filin Deport ne na NA wato Chidit Barrack, shi ne Sardauna Sokoto Firimiyan Jihar Arewa Sir Ahamadu Bello ya nemi Turawa su bashi filin dan yana gina filin Polo, kuma a yarjejeniyar da akai da Soji wannan fili ba na sayarwa bane, amma aka samu wata Gwamnati a Kaduna ta maida filin Mallakarta kuma ta baiwa Zakzaky. To Alhamdulillah yanzu haka Buratai ya ce filin Husainiya ya dawo gayaunar sojoji.

Bayan haka kuma, gidan Zakzaky da ke Gyallesu asalinsa shima Gwamnatin Abdussalam Abubakar ce ta gina masa, ta bashi kyauta a matsayin Diyyar abinda Marigayi Gen. Sani Abacha yayi masa, to al'umma dake zaune a Gyallesu sun rubuta dubban sakonnin koke koke akan irin cuzguna musu da Zakzaky da yaransa suke yi, dan haka shima wannan gida Zakzaky ya karya dokar bashi gidan, dan haka sojoji sun kwace shi. A yanzu dai zamu iya cewa Buratai yayi Jana'izar Shiah a duk fadin Najeriya.

Saura da me? Ya kamata al'umma su sani, kuma su fadaka, babu wata akida ta zagin Sahabbai da Iyalan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam a cikin addinin Musulunci. Dan haka kamar yadda mai martaba Sarkin Kano yayi kira dole Sarakuna su tashi tsaye wajen Yaki da duk wanda ya zo dan gurbata addinin Musulunci da aka gina shi akan koyarwar Ahlussunnah Wal Jama'ah a wannan kasa tamu mai Albarka. Ya Allah kasa  wannan shi ne karshen Shiah a Nijeriya. Allah ka taimaki Musulunci da Musulmi ka kaskantar  da Shiah da duk masu goya musu baya na saurari da na b'oye munafukai masu takiyya. 

Yasir Ramadan Gwale 
17-12-2015

Saturday, December 5, 2015

Godiya Da Fatan Alheri Ga Sojan Nigeria


GODIYA DA FATAN ALHERI GA SOJAN NAJERIYA

Daga Ranar Juma'a 4 ga watan Disamba zuwa 10 ga wata,  lokaci ne da Rundunar Sojan Najeriya ta ware a matsayin makon da za a godewa sojojin Nigeria dake fagen daga #ThankASoldier. A dan haka, a wannan rana ta Juma'a kuma a wannan sa'a ta karshe ta wannan rana muke tawassuli da sunayan Allah tsarkaka madaukaka, Ya Allah ka Jikan sojojin mu musamman wadan da suka rasu a fagen daga domin kare kasarmu daga farmakin 'yan ta'adda masu tada zaune tsaye, Allah ya jikan su ya gafarta musu, masu raunuka daga cikinsu Allah ya basu lafiya.

Anan nake amfani da wannan dama, nayi kira ga sauran 'yan Najeriya da su cigaba da yiwa Najeriya da sojojin mu adduar fatan alheri da samun nasara a fagen daga. Allah ya tabbatar mana da samun zaman lafiya dawwamamme mai dorewa, Allah ya kade mana dukkan fita. Haka kuma, ina kira ga mai girma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya daure ya kaiwa sojojin mu dake fagen daga ziyara, a musamman jihar Borno, ba shakka wannan zai kara musu kwarin guiwa da karsashin yin aiki tare da nuna kishin kasa, Bugu da kari, hakan zai basu kwarin guiwar cewar ana gamsuwa da aikinsu.

Kamar yadda Shugaban kasa ya ambata cewar zai shige gaba domin fafarar 'yan ta'addar da suka hana wannan kasa zaman lafiya, muna rokon Shugaban kasa da ya daure ya kai musu ziyara dan yaba musu. Sannan kuma, muna fatan Gwamnati zata inganta jin dadi da walwalarsu tare da biyansu dukkan hakkokinsu akan kari, wadan da suka yi Shahada kuma muna fatan Gwamnati ta dinga biyan iyalansu akan lokaci. ALLAH ya taimaki Sojan Najeriya ya basu kwarin guiwa. Allah ya bamu Lafiya da zaman lafiya. #ThankASoldier 

Yasir Ramadan Gwale 
05-012-2015

Jaafar Jaafar Ne Ya Tunzura Bala Ibn Na'Allah


JAAFAR JAAFAR NE YA TUNZURA IBN NA' ALLAH

Sen. Bala Ibn Na'Allah ya gabatar da wani kuduri gaban majalisar Dattawa da ya samu karatu na daya domin yin doka akan takaita ko iyakance abinda masu Kwarmato a Social media irinsu Jaafar Jaafar zasu yi, wanda yanzu batun ke cigaba da jan doguwar muhawara. Ina ganin wannan kuduri da Sen. Na'Allah ya gabatar baya rasa Nasaba da yamadidin da Jaafar ya fara yi akan shigar (kasaita)da Sanatan yayi lokacin wata liyafa da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiryawa Shugabannin Majalisar Dattawa da su Jaafar suka ga rashin dacewa a tare da tsukiyar da Sanata Na'Allah yayi, wanda hakan yasa Jaridu da dama musamman na Internet suka cigaba da yayata Bala Ibn Na'Allah da kuma shigar tasa.