Wednesday, October 29, 2014

APC: Kwankwaso Yaci Zabe A Bashi Abinsa

Gwamna Rabiu Kwankwaso

APC: KWANKWASO YACI ZABE A BASHI ABINSA

Jiya talata 28 ga oktoban nan muka shaida yadda Miliyoyin 'yan jam'iyyar APC daga ko ina a fadin Najeriya suka hallara a Habuja babban birnin tarayya dan nuna goyan bayansu ga takarar Gwamna Kwankwasiya Amanaa matsayin shugaban kasa wanda zai yiwa jam'iyyar takara. Wadan da suka samu halartar taron sun shaida mana cewar Habuja tayi cikar kwari babu masaka tsinke, duk inda ka duba Jan Kai kawai ake kwalli da shi, mata da maza.

Ance duk wanda yake takara a APC jiya cikinsa ya duri ruwa. Saboda kaddamar da takarar mai girma gwamna a jiya ta yamutsa hazo, kuma ta nuna a fili inda mutane suka karkata. Dan kuwa masu abin (jama'a) sunce sun ji sun gani Kwankwasiyya Nigeria. A sabida haka muke yiwa Shugaban Kasa mai jiran gado murna da fatan alheri. Duk da yake ni ba dan wannan jam'iyyar bane, amma ya zama dole a matsayina na dan Kano nayi murna akan irin yadda Najeriya gaba daya kwata ta hadu tace sai mutumin Kano. Wannan karamci ne akai mana kuma mun gode.

Ina kuma isar da sakon taya murna ga Shugaban kasa mai jiran gado. Ina kuma fatan idan lokacin rantsuwa yayi a aiko min da goran gayyata dan mu hadu a Habuja mu shaida rantsar da Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso a matsayin Shugaban Najeriya na goma sha shida. Kwangwaratuleshan ga abokina Auwalu Lawan Aranposu akan wannan Nasara da suka samu. Ina kuma fatan źa'a dinga kulawa da hakkin makwabtaka da zumuncin da ke tsakaninmu idan an shiga Villa.

Ina kuma amfani da wannan dama wajen yin jaje ga 'yan Bahariyya suKwamared Baban Shareek Gumel da Ibrahim Sanyi-Sanyi da fatan zasu dauki dangana. Shima dan uwana Sunusi Musa ina masa jaje da Atiku Abubakar bai samu wannan nasara ba, shima dan uwa Bashir Ahmad ina tayaka alhini da Sam Nda bai samu wannan nasara ba. Ina kuma fatan zaku hadu dan dafawa mai girma Shugaban kasa mai jiran gado domin ciyar da Najeriya gaba.

29-10-2014

Tuesday, October 28, 2014

ATIKU ABUBAKAR: Kadangaren Bakin Tulu


ATIKU ABUBAKAR: KADANGAREN BAKIN TULU

Kasancewar Turakin Adamawa Atiku Abubakar daya daga cikin 'yan takarar Shugaban kasa a jam'iyyar hamayya ta APC ta sa ya zamo kadangaren bakin tulu a cikin jam'iyyar; ance kadangaren bakin tulu idan an jefeshi za'a fasa tulu, idan an kyale shi kuma dole ayi hakuri asha ruwan a haka.

Fitowar Atiku Abubakar takara tare da Gen. Buhari yana yiwa magoya bayan Janar din barazana. Domin duk wani yunkuri na samar da wanda zai yiwa jam'iyyar takara ta hanyar sasantawa ko kwansansus, Atiku ba zai yarda da shi, abinda yake nuna dole sai anyi zaben fitar da gwani wanda daliget ake sa ran zasu yi.

Zaben fitar da Gwani kusan shi ake kallo a matsayin wata dama da shi Atikun ya makalewa. Domin wannan zabe na fid da gwani shi ne zai bada damar amfani da kudi wajen sayan masu zabe. Abinda ake ganin tuni Atiku ya tanadi jakar kudi dan wannan zabe. Ba shakka masharhanta na ganin cewar kudi zasu taka muhimmiyar rawa a wannan zabe. Kuma zasu taimakawa Atiku wajen iya samun nasarar zama dantakara.

Haka kuma, alamu na nuna cewar duk wani yunkuri dan kaiwa zuwa ga wannan zabe tamkar shatale takarar Buahri ne da ke zaman wanda yafi sauran 'yan takarar jam'iyar yawan magoya baya. Daga gefe guda kuma tsohon Shugaban kasa Olushegun Obasanjo na gargadin Apc da kada su sake su sanya Atiku a matsayin dantakararsu, abinda ke kara bayyana jikakkiyar da ke tsakani Atikun da tsohon mai gidansa Obasanjo.

Koma dai ya abin zai kasance. Lokaci ne zai tabbatar da waye zai fuskanci Shugaban Kasa Dr. Goodluck Jonathan a zaben 2015 da ke tafe.

Yasir Ramadan Gwale
27-10-2015

Monday, October 20, 2014

Cire Hula A Coci


CIRE HULA A COCI: Kwanakin baya da naga manyan 'yan Siyasarmu su Gen. Buhari da Atiku Abubakar da Gwamna Kwankwaso a coci sun ciccire huluna a gaban pasto abin ya bani mamaki matuka, kuma ya sanya min tambayoyi a raina dangane da wannan al'amari. 

Yanzu saboda Allah ace arne kamar mai Malafa ya sanya mutane masu kima da daraja shiga coci suna cire hula dan kawai neman Mulki ba dan yin kira zuwa ga addini ba! Shin yanzu idan su basu iya yadda zasu jawo shi Masallaci ba har sa bari shi ya yi silar shigarsu coci su cire hula duniya na gani?

Watakila wani yace ai ba kafurci bane dan sun shiga coci. Nima bance hakan ba, amma dai saninmu ne cewar sun shiga ne ba dan yin kira zuwa ga addinin Allah ba. Sun je ne dan siyasa, watakila da shi Gwamna Okorocha ba a APC yake ba da ba wanda zaka gani a cikinsu.

A kwanakin baya da Gen. Buhari da Gwamna Kwankwaso da Atiku Abubakar duk sun aurar da 'ya 'yansu amma babu wani arne da aka gayyato yazo cikin Masallaci akai daurin auren da shi, kuma Okorocha na nan duk sauran arnan duk suna nan, amma sai mu 'yan ina da biki zamu dinga binsu coci muna tafawa muna dariya, ai idan ni banyi silar zuwanka Masallaci ba a dalilin kawancen siyasa to ba yadda zakai silar zuwana coci na cire hula tunda ba wa'azi na je ba.
Na kuma ga yadda akai ta kokarin bayar da kariya da bada uzuri ga wadan da suka shiga kanisar, amma tambayar da taita yawo a raina ita ce:

Yanzu tsakani da Allah idan Malam Ibrahim Shekarau ne ya shiga coci ya cire hula a gaban pasto shin za'a bashi uzuri kamar yadda aka baiwa su Buhari da Kwankwaso da Atiku?

Idan har Uzuri ne mutum ya shiga coci ya cire hula a gaban pasto dan siyasa, to ba shakka uzuri ne babba mutum ya shiga PDP dan yin siyasa. Allah ka nuna mana karya ka bamu ikon kauce mata ka nuna mana gaskiya ka bamu ikon binta.

Yasir Ramadan Gwale
19-10-2014

Saturday, October 18, 2014

Kudin Form Din Takarar Janar Muhammadu Buhari


KUDIN FORM DIN TAKARAR BUHARI

Naji cewar Buhari ya sayi takardun cikewa shiga zabe akan kudi wajen Miliyan 27.5! Hakika wannan kudin yayi yawa sosai. Hakan kuma na kara nunawa al'umma cewa al'amarin Mulki ko Shugabanci a Najeriya ba na Talaka ba ne. Duk kokarin da ake yi shi ne na tsame hannun talakawa daga sha'anin Mulki.

Yanzu idan a Apc nake kuma zanyi takarar Shugaban kasa sai na biya wadannan Miliyoyi bayan kudin da zan batar na harkar yakin neman zabe? Apc ce fa ake ganin jam'iyyar Talakawa da ta zo dan sharewa talaka hawaye! Wannan karara lasisi ne ake baiwa zababbu su yi sata san ransu. 

Na zata kudin Form a Apc ba zai wuce 'yan dubunnai ba dan kusanto da abin ga talakawa, amma dai zatona ba gaskiya ba ne. Kuma ni abinda ya fara zuwa raina shin yanzu idan Buhari bai samu nasara ba shi kenan yayi asarar wadan can miliyoyi? Dan naji ance bashin Banki ya ciyo dan sayan takardun.

Wannan ta sanya na tuna kwanaki da naji wasu na ikirarin zasu sayawa Buhari takardun shiga zaben, shin kudin ne yayi musu tsada ko kuwa! Allah masani. Shin idan Buhari bai ci zabe ba magoya bayansa zasu taimaka masa biyan wannan bashin?

Bana yiwa Buhari mummunan fata. Adduah ta ita ce duk wanda zai fi zama alheri a garemu a wannan zabe Allah ka bashi.

Yasir Ramadan Gwale
17-10-2014

Saturday, October 11, 2014

APC-Buhari/Atiku/Kwankwaso Da Zaben 2015: Hanya Daya Tak Da Ta Ragewa 'Yan Adawa Daga Arewa

APC/BUHARI-ATIKU-KWANKWASO DA ZABEN 2015: HANYA DAYA TAK DA TA RAGEWA ‘YAN ADAWA DAGA AREWA

* wannan rubutu yana da tsawo, ina fatan duk wanda zai yi ta'aliki ya kasance ya karanta har karshe.

Dukkan dangin yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah madaukakin sarki, tsira da amincinsa su kara tabbata ga shugaban Manzanni cikamakin Annabawa Muhammadu Dan Abdullahi; Allah yayi dadin tsira a gareshi da Alayansa da Sahabbansa da wadan da suka biyo bayansu da kyautatawa har ya zuwa ranar sakamako. Ina rokon Allah ya sa wannan abun da zan fada ya amfanemu baki daya, Allah kayi min jagoranci wajen fadin gaskiya.

Da farko yana da kyau mu mutanan Arewa Musulmi mu sani cewar dama ce muke da ita mukai sakaci ta kubuce mana, a dan haka ‘bari mukayi, masu magana kuma sun ce “ba’a yin ‘bari a kwashe duka”, ina fatan mai karatu zai kiyaye wannan magana da kyau! Idan muka duba Najeriya tun farkon kafuwarta har kawo yanzu, mu mutanan Arewa mun dad’e ana cin moriyar hakurinmu da kuma sakaci da sadaukarwarmu ba dan komai ba sai dan san zaman lafiya da zaman tare.

A baya anyi mana wawar Asarar Sa Abubakar Tafawa Balewa da su Sa Ahmadu Bello da sauransu wadanda ba dan komai aka kashe su ba sai dan Najeriya watakila kuma dan kasancearsu Musulmi daga Arewa. Mu ne mutanan Arewa saboda Alkawari da san zaman tare muka sadaukar da Shugabancin tarayya dake hannunmu muka dauka sukutum muka mikashi ga Obasanjo! Anyi hakan da kyakkyawar niyya ko akasin haka Allah shi ne mafi sani.

Tun bayan waccan dama da ta subuce mana, inda Obasanjo da aka bashi amana ya dinga gasa mana aya a hannu, har ta kai mun kai wani mataki da muke ta magagin yadda waccan dama da muka dauka da hannumu muka bayar muke fatan dawowarta hannunmu. Tun a shekarar 2003 da 2007 da kuma 2011 ake ta wannan fafutuka ta ganin cewar ikon tarayya ya koma hannunmu, domin da yawan mutanan Arewa munyi Imani cewar babu wani dan kudu da zai yi mana Adalci face idan har namu ya samu, shi yasa muka makance muke nema ido rufe.

A dan haka, kamar yadda na fada a baya cewar “ba’a yin bari a kwashe duka” inji ‘yan magana, to lallai ya kamata mu fahimci wannan magana da kyan gaske, mu kuma yi nazarin halin da muke ciki, mu kuma samarwa kanmu makoma ta gaskiya.

A dalilin neman waccan makoma, muka makance muka kasa tunanin meye abinda yafi kamata a garemu tunda mun kasance masu hamayya. Wannan ta sanya muke kiran “lallai mulki ya dawo Arewa” wanda wannan magana kuskure ce, da abinda yafi kamata shi ne mu ce lallai muna bukatar Musulmi ya zama Shugaban kasa na gaba, tunda yanzu wanda yake kai ba Musulmi ba ne.

Haka kuma, ba zai yuwu ba mu mika kukanmu ga Allah mahaliccinmu muna masu neman agaji da taimakonsa, sannan kuma mu sanya masa sharadi ba! Sharadin shi ne na cewar lallai sai dan Arewa (Buhari) ya zama Shugaban kasa! Tur kashi… ina fatan mai karatu yana biye da ni sosai kuma zai fahimci me nake nufi. Zanyi bayanin hakikanin abinda nake nufi nan gaba.

GEN. MUHAMMADU BUHARI: kamar yadda na fada a rubutun da na yi da yayi ishara zuwa ga wannan rubutun kuma nai alkawarin bayar da dalilai na. Anan yana da kyau mu mutanan Arewa Musulmi mu sani cewar ba wai Buhari ake ki ba, shi yasa aka ki bashi zabe a baya ba, a’a mu din ‘Yan Arewa Musulmi mu ne ake ki, mu ne ba’a so a zaman tarayya. Dan haka duk wanda yake zaton cewar a cire Buhari a kawo Gwamna Rabiu Kwankwaso ko Atiku Abubakar a matsayin dan takara shi ne ko ita ce mafita to bai fahimci al’amarin ba. Daman kuma masu magan sun ce "da dan gari akanci gari"

Ko an tsayar da Atiku ko Kwankwaso a wannan zaben da yake tafe, to abinda ya faru a baya shi ne dai zai sake faruwa, babu wani zani da zata canza, kamar yadda na fada mu dinne dai ba’a so. A dan haka ne duk wanda ya tsaya takara daga cikinmu yake shan mamaki.

ATIKU ABUBAKAR: Masu magana suka ce dama kwaya daya ce tal take zuwarwa wasu a rayuwa, idan sun yi azama sukanci amfaninta lokaci mai tsawo. Atiku Abubakar yana daga cikin wadan da suka samu dama mai kyau bayan zaben 1999, inda ya samu goyon bayan mafiya yawan gwamnonin Arewa na lokacin dan ayi wancakali da Obasanjo ya maye gurbinsa, amma Atiku ya barar da wannan damar.

Atiku ne fa saboda dadin Mulki ya dinga cinnawa gidansa (Arewa) wuta ya manta cewar idan sun gama Mulki zai baro Abuja ya dawo Arewa. Haka kuma, a baya ai Atiku Abubakar yayi takara a 2007 kuma anyi abinda akai, me ya iya yi? Don haka ko an sake tsayar da shi abinda akai masa a 2007 shi za a kuma yi masa, babu kuma abinda zai faru sai hanayi da hargowwa da ba zata iya canza komai ba.

GWAMNA RABIU KWANKWASO: Kwankwaso na daga cikin manyan na hannun damar Obasanjo a lokacin da Obj din yake sharafinsa. Ance har yanzu Gwamna Kwankwaso suna d'asawa da Obasanjo.

Gwamna Kwankwaso na daga cikin sabbin zubin da ake masa fatan tsayawa takarar Shugaban Kasa, da fatan zai yi abinda magabatansa suka kasa. Tauraruwar Kwankwaso ta fara haskawa ne tun lokacin da ta bayyana cewar akwai baraka tsakaninsa da Shugaban kasa, wanda wannan ta janyo masa farin jini da karbuwa a wajen mutane da yawa. Kamar Buhari da Atiku shima Kwankwaso babu wani abu da zai sauya idan ya zama dan takarar hamayya. Dan haka maganin kar ayi kar a fara.

Kamar yadda na fadi cewar Buhari zai fi zamarwa PDP karkatacciyar kuka mai dadin hawa idan ya zama dan takara, domin an san shi an kuma san logar kayar da shi zabe. Kuma PDP zasu fi kowa murnar kasancewarsa dan takara a wannan zaben, dan suna da lissafinsu a hannu. Haka kuma, yana da kyau mu sani cewar matsalar cin zabenmu mu ‘yan Arewa Musulmi a zaben tarayya a kudancin Najeriya take.

 Yana da kyau mu sani cewar PDP tana da girkakkiyar kuri’a a kudu, kuma tana da hanyoyin cin zabe sama da dubu na halal da na haram a kudancin Najeriya, a cikin jihohi goma sha bakwai (17) babu wata jiha da PDP ba zata samu sama da kashi 50 ba fiye da yadda hukumar zabe take bukatar kowane dan takara ya samu. Haka kuma, akwai jihohin da PDP tana cin zabe 100 bisa 100 ko mutum daya baya mutuwa kafin zabe. A Arewa kuwa babu wani dan takara dan Arewa da zai iya cin zabe a wata jiha 100 bisa 100!

Jam’iyyar PDP tana da tabbacin samun waccan kuri’ar ta kudancin Najeriya, zata sameta ta hanyar halal da haram. Wanda dan-takarar Arewa idan ya iya samun kashi ashirinda biyar a zabe na tsakani da Allah to shi ne ya iya samun jiha daya tak a kudu, itama sai anyi kamar ana yi.

A zaben daya gabata akwai jihar da Buhari kwata-kwata bai je yakin neman zabe ba. Sannan kuma, a bangaren PDP suna da masaniyar cewar Buhari na da karfi a Arewa, dan haka basu tayar da hankalin sai sun ci jihohin Arewa kamar yadda suka yiwa na kudu cin-dare daya, cin dari-bisa-dari ba, dan haka zasu dage ne wajen samun kashi 25, a lokacin da Buhari ko dan takarar Arewa yake murnar samun dubban kuri’u a Arewa, itama PDP ta baza komarta inda ta yakuto kashi 25 din da na Arewa ya kasa samu a kudu.

Zabe kuma ba zai taba cuwuwa a kudu ko Arewa kadai ba. Dole dan takara yana bukatar samun Nasara a jihohi 23 kafin ya samu Nasara, a yayin da mu a Arewa jiha 19 muke da ita muna bukatar jiha hudu kenan daga kudu. A hakanma da sauran rina a kaba! Domin a Arewa kana da jihar Plateau da Benue wanda ko ana ha-maza ana ha-mata dan takarar Arewa ba zai iya cin Plateau ba, har gwara Benue dan kiyayyarsu bata kai ta Berom ba.

A dan haka, duk wani yunkuri na tsayar da Buhari ko Atiku ko Kwankwaso takara a zabe mai zuwa tabbas karfafawa PDP guiwar cin nasarar wannan zabe ne. Watakila aji wannan magana bambarakwai, ba mamaki wani yayi fart da garaje yace karya ne… Amma dai abin da na sani shi ne lokaci ne kadai zai iya karyata wannan magana tawa ko da kuwa duk an taru an karyatani, dan haka indai da gaske muke kuma mun nufi Allah a wannan al’amari to dole Buhari da Kwankwaso da Atiku su hakura da duk wani batu ko yunkuri na yin takara a 2015 indai da gaske dan al’umma suke! Watakila mai karatu yace sam ba zata sabu ba, domin waye zai yi takarar kenan, ina nan dauke da amsar tambayarka mai karatu, kai dai biyoni kaji inda zan sauka.

KALMAR “IDAN” TAKWARA CE GA “DA”: Sau da dama in maganar wannan zaben ta taso, mu mutanan Arewa mukance “IDAN” har Yarabawa suka zabi dan takararmu to munci zabe! Wannan kalma ta “idan” tana nuna cewar bamu da wani tabbas kenan akan Yarabawa dangane da wannan zabe, duk kuwa da cewa tsakanin mu da su ‘yan Uba muke. Shi yasa idan abinda ya saba faruwa ya faru sai muyi amfani da kalmar “DA” ma’ana da anyi kaza da kaza ya faru.

Ina fatan mai karatu yana biye da ni, domin yanzu ne zamu yi bayanin mafitar wannan halin da muke ciki na tsahin Bamabami da kaskanci da karyewar tattalin arziki da koma baya ta fuskar ilimi da noma da kiwo da harkar lafiya da wutar lantarki da sauransu. Ga mafita nan tafe.

MECECE MAFITA A GAREMU? Wannan tambaya muhimmiya ce, da kowa zai so jin amsarta, ba shakka amsar wannan tambaya tana da sauki, kuma ita ce zata nuna makomarmu a wannan zabe da yake tafe. Watakila Allaah ne ya karbi adduarmu abinda ya faru na hadaka ya faru tsakanin ‘yan siyasa a Arewa da yankin Yarabawa suka hada kai dan samun mafita guda daya. Bari na sake tuna mana abinda na fada dazu a baya, amaganar da na ce “ba’a yin bari a kwashe duka” to lallai mu sani mu mutanan Arewa munyi bari dan haka ba dole ba ne mu kwashe duka, sai dai wanda zai kwasu wanda ba zamu iya kwashewa ba kuma mu barwa Allah.

Abinda nake nufi anan shi ne duk ‘yan Arewa dake san yin takarar Shugaban kasa a APC su hakura a dauko dan kudu Beyerabe Musulmi wanda ba Bola Tinuba ba, kuma ba Gwamna Fashola ba. Yana da kyau mu sani cewar a halin da muke ciki a yanzu mu ‘yan Arewa muna bukatar wanda zai yi mana Adalci ne a zaman tarayya, wanda ba zai zalince mu ba, wanda zai bamu hakkokinmu a matsayinmu na ‘yan Arewa Musulmi, kuma mutum wanda mu ‘yan Arewa ba zamu ji shakka akansa ba.

A dan haka mutumin da nake ganin zaifi karbuwa a wajenu fiye da duk wani Beyerabe shi ne Gwamnan jihar OSUN Abddul-Rauf Aregbesola! Eh tabbas shi nake nufi, gwamna Aregbesola a ganina shi ne mutumin da ‘yan Arewa ba zasu ji shakkar mara masa baya ba, kuma mutane da yawa zamu nutsu cewar zai yi mana Adalci idan ya zama Shugaban kasa.

Dalili akan haka shi ne, kamar yadda na fada a  baya, matsalar cin zaben dan Arewa a kudu take, na tabbata kuma nayi Imani idan ka kawo gwamna Aregbesola daga yankin Yarabawa kana da tabbacin samun kuri’ar yankin Kudu-maso-yamma gaba dayanta. Dan haka idan muka yi hakuri da damarmu muka barwa ‘dan kudu Bayerabe Musulmi to ba shakka Shugaban Kasa Goodluck Jonathan babu inda zashi, domin bayan ka rikita masa lissafi, to ka kassara shi duniya da lahira. Mu kuma tuan cewar a baya mun sadaukar da su Tafawa Balewa da Ahamadu Bello munyi hakuri da rashinsu, balle kuma hakuri da tsayawa zabe!

Idan akayi haka, mutane daga kudu irinsu Femi Fani-Kayode hankalinsu zai yi matukar tashi domin zasu yi ta yin ihun Muslim-Muslmin Tiket, wanda ihunsu da maganganunsu babu abinda zai karawa wannan tafiya sai karfi da kara samun yakini, domin Yarabawa zasu jajirce wajen ganin sun zabi Rauf tunda Yarbawa Musulmi su ne suke da rinjaye a yankin kudu maso yamma, tunda dan uwansu aka kawo. Daman tun asali ai su Awolowo ne suke nuna cewar Yarabawa ba ruwansu da addini dan kawai su danne yarabawa, amma wannan Magana ko kusa ba gaskiya bace, domin duk wanda yasan yarabawa ya san mutane ne masu san addini da san Musulunci. Mu kuma dole mu dawo daga rakiyar tuninmu na cewar Beyerabe ba musulmin kwarai ba ne, yana fifita Yare akan addini, wannan zato ne wanda shima kirkirarsa akai dan nesanta Musulmin Arewa da Musulmin Yarbawa.

A dan haka, anan Arewa mu kuma zamu hadu gaba daya mu zurarawa Rauf Aregbesola kuri’ah kan kace kwabo an fara lissafin Rauf a matsan shugaban kasa na gaba. Ina fatan ya zuwa yanzu mai karatu ya samu nutsuwa akan wannan batu, dan haka sai a samu mutum daga yankin Arewa-maso-yamma a bashi mukamin mataimakin shugaban kasa ko dai Gwamna Kwankwaso ko kuma wani zakakuri wanda zai iya tsolewa mutanan kudu-maso-kudu da kudu-maso-gabas ido.

A ganina wannan ita ce kadai hanyar da mulkin Najeriya zai dawo hannun dan Arewa a shekarar 2024, kaga daga nan sai muyi ta yi har illa masha Allah, inyamurai da mutanan kudu-maso-kudu sai dai suga ana yi. Kuma wannan ita ce mafitarmu a wannan zaben, tunda mufa mutanan Arewa bari muka yi, kuma ba zai taba yuwuwa ba ace sai mun kwashe duka, waton hannun karba hannun mayarwa. Dole ko mun so ko munki mulki ba zai dawo hannun dan Arewa ba sai da ‘yan dabaru.

Haka kuma, akwai wani kuskure da mu mutanan Arewa muke tafkawa amma ko a jikinmu, domin a 2011 a yankin Arewa maso yamma kadai akwai mutane kusan miliyan tara (9m) da suka yanki katin jefa kur’ah amma basu yi zabe ba, shin ina suka shiga? Mutuwa sukai ko me? Wannan kuri’ar fa tafi ta yankin Inyamurai baki daya, dan haka dole sai munyi abinda ake kira da turanci Mobilization na kuri’un jama’a har daren da za’a kada kuri’ah a samu wasu jajirtattun matasa su dinga bin mutane gida-gida suna jaddada musu cewar lallai asubar fari ta yiwa mutane a layin zabe, abi kauye-kauye, gari-gar, unguwa-unguwa, ina tabbatar maka mai karatu 2015 sai Musulmi ya zama shugaban kasa indai anyi haka da gaske kuma da kyakkyawar niyya.

Dan haka kamar yadda na fada wannan ita ce kadai hanyar da nake ganin zamu iya samun zabe a 2015, kauce mata kuwa ko mun yarda ko bamu yarda ba karawa PDP kwarin guiwar cin zaben Shugaban kasa ne. Buhari, Atiku, Kwankwaso kuwa sai mu yi musu addua tare da nuna godiya amma su yi hakuri da takara dama ce kuma ta wuce su. Yarabawa kuwa tuni ka sayesu ka biya kudin, domin muddin muka basu wannan damar dole su tsaya kai da fata wajen ganin dan-takara daga yankinsu yaci zabe. Ina fatan Allah ya nuna mana zaben 2015 rai da lafiya, ni da ku zamu zo nan facebook muna baiwa juna wannan labarin ko akasinsa.

Wanda zai karyata yana da iko, wanda zai gasgata shima yana da iko, amma ni dai nasan lokaci shi ne alkali, shi zai gasgatani ko ya karyatani. Dan haka mai hankali yi tunani.

Yasir Ramadan Gwale
11-10-2014

Tuesday, October 7, 2014

Jihad


JIHADI: Zai zama abin da daure kai ace anje ana dasawa mutane kayan fashewa kuma wasu su dinga ikirarin wai Jihadi suke yi idan sun mutu Allah zai tashe su a sahun su Hamza Ibn Abdulmuddalib saboda suna zaton sun mutu shahidai! Ko kusa wannan gurbataccen tunani ne, da gurguwar fahimta da zafin kan addini cikin matsanancin jahilcin addini, wanda irinsu Osama Bin Laden suka shuka shi yayi tsiro a zukatan wasu daga cikin fusatattun matasan Musulmi da basu gama fahimtar meye Addinin Islama ba. Shin meye Jihadi a Musulunci?
Yasir Ramadan Gwale
07-10-2014

Friday, October 3, 2014

Godiya Ta Musamman



GODIYA TA MUSAMMAN: Kusan tun kwana uku kafin jiya Malamina a CAS Alasan Sule ya rubuta sakon fatan alheri akan Timeline dina yake tuna min ranar da aka haifeni. Tun daga lokacin kuma na fara samun sakon taya murna da fatan alheri.

Hakika nayi murna da farin ciki a jiya yadda mutane suka dinga lekowa turakata suna barin sakonnin fatan alheri da addu'o'i a gareni, kuma fatan alherin bai tsaya gareni ba ni kadai har Zainab jama'a da dama sunyi mata addu'ah da fatan alheri a dalilin wannan rana. Ba shakka naji dad'in wannan al'amari, da ni da Zainab muka kasance cikin adduoinku a jiya.

Muna matu'kar godiya a gareku baki daya. Da so samu ne nabi dukkan wadan da duka aiko da sako nai musu godiya a jikin sakon, amma kasancewar abin da yawa ban samu dama ba, amma duk wanda ya aiko da sakon na gani kuma naji dadi.

Ba shakka hakan na nufin ina kara kusa ga ajalina ne, na shirya ko ban shirya. A shekarun da aka diba min naci wani adadi daga ciki. Ina rokon Allah ya amsa dukkan adduoinku na alkhairi da kuka yi mana. Ina kuma fatan hakan ya zama tuni a gareni cewar ako da yaushe ina iya riskar ajali. Allah ya sa yadda muka zo muna masu Imani da Allah mu koma muna masu Imani a gareshi Subhanahu wata'ala.

Nima zan d'an koma baya na tunawa kaina baya dan na fahimci yadda rayuwa ta sauya a gareni. Wannan hoto da kuke gani an dauke shi a shekarar 1988. Wannan yaron da kuke gani ni ne. Yau gashi gabbai sunyi tsawo gashi ya baibaye fuska. Akwana a tashi ance jariri ango ne.

Amadadina da Zainab da dukkan 'yan uwa d danginmu muna muku godiya da fatan alheri. Allah ya saka da alheri ya bar zumunci.

Yasir Ramadan Gwale
03-10-2014

Nasiru Sufi



NASIR SUFI: A madadin ni da Zainab muna taya abokinmu Malam Nasiru Sufi Junior murnar kammala karatu da samu daraja ta farko First Class a jami'ar Ming Chuan University dake a Taiwan. Muna fatan alheri da fatan samun nasara a rayuwarka Malam Sufi. Allah ya yi maka jagora.

Yasir Ramadan Gwale
01-10-2014

Dakta Habibu Sani Babura



DAKTA HABIBU SANI BABURA (Talban Babura): Ina amfani da wannan dama nayi murna na kuma nuna farin ciki da godiya ga Gwamnatin Jimhuriyyar Nijar karkashin Jagirancin Shugaba Mouhammadou Issoufou bisa ga lambar girma ta kasa da ya baiwa Dakta Habibu Sani Babura.

Ba shakka munyi farin ciki da wannan karramawa da aka yi mana. Wannan ya kara nuna mana irin zumunci da 'Yan uwatanka ta makwabtaka tsakanin Nijar da Najeriya. Muna godiya ga Gwamnati da al'ummar kasar Nijar baki daya.

Dakta kuma muna kara taya shi murna. Muna kuma yi mada addu'ar Allah ya kara masa lafiya da nisan kwana. A madadin ni da Zainab muna taya shi murnar wannan lambar girma da ya samu.

Yasir Ramadan Gwale
01-10-2014

Ta'aziyar Galadiman Kano



GALADIMAN KANO: Alhaji Tijjani Hashim Galadiman Kano kamar yadda 'yan uwa da dama suka sani a yau da safe muka wayi gari da labarin rasuwarsa a babbsn birnin tarayya Abuja wanda ake shirin yin jana'izarsa yanzu. Muna adduar Allah ya jikansa ya gafarta masa, ba shakka rashin Galadima babban rashi ne, domin shi uba ne na al'umma wanda kullum kofarsa a bude take dan taimakawa Talakawa da masu karamin karfi, Galadima ya samu shaida a wajen mutane da yawa wajen taimakawa wadan da aka zalunta ko aka dannewa hakkinsu.

A baya bayan nan Galadima ya taimakawa Addini sosai kuma ya taimaki masu addini sosai. Rashinsa bai tsaya ga Masarautar Kano kadai ba, wannan rashi ne da ya shafi al'umma gaba daya. Allah ya jikansa ya gafarta masa, kurakuransa Allah ya kankare su.

A madadina da Zainab muna mika sakon ta'aziyarmu ga Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II da Gwamnatin Kano da kuma al'ummar Kano baki daya. Allah ya kyauta namu karshen.

29-09-2014

Sheikh Jaafar Mahmoud Adam Kano



Wata rana Sheikh Jaafar Mahmoud Adam RAHIMAHULLAH yana karatun Tafseer a Masallacin Beirut Road a Kano sai wani baturen kasar Ingila ya zo zai Musulunta. Baturen yace ya zo ne daga Yankari wajen shakatawa da ke Bauchi, baturen yayi bayanin cewar shi ba wa'azi akai masa da ya musulunta ba, yace a dalilin karance karance da bincikensa ya fahimci Addinin Musulunci gaskiya ne. Baturen ance har Aure yayi a Bauchi daga bisani ya koma Ingila shi da matarsa a can yacigaba da binciken addinin Musulunci. Kwatsam rannan muna kallon Tashar Huda sai ga wannan Baturen yana wa'azi yana karanto ayoyin al-qurani yana fassarawa. Wanda muke zaune muke kallo tare da shi Alhaji Mustapha Dan Chanji shi ne ya gane baturen lokacin da ya ganshi kuma yaga sunansa yaga sunan da Malam Jaafar ya rada masa na Abubakar shi ya cigaba da amsawa. Alhaji mustapha yace min kaga su turawa idan sun musulunta da gaske suke yin Musulunci. Allah ya tabbatar da mu akan shiriya ta gaskiya. Allah kuma ya jikan Malam Jaafar Mahmoud Adam.

28-09-2014