Friday, March 30, 2012

Bara, Roko, Tumasanci, Al-majiranci da kuma karatun al-qur’ani a Arewa!!!


Bara, Roko, Tumasanci, Al-majiranci da kuma karatun al-qur’ani a Arewa!!!

A kasar hausa idan akace almajiri ana nufin wani dalibi da yafito domin neman ilimin alqurani; wannan shi ne almajiri. Kuma galibi almajirai ana tura su gurin wani malamin alqurani ko kuma malamin da akafi sani da alaramma. Shi wannan alaramma shi ne wanda wadan nan iyaye da suka aiko dansu wajen sa domin ya nemi ilimin alqurani rayuwarsa ta ke a hannunsa. Alhaliknsa ne koyawa wannan almajiri karatun alqurani da kuma lura da yadda wannan almajiri yake gudanar da rayuwarsa tare da sauran abokan zamansa almajirai. Wanda wadan nan almajirai suna karatu a hannun malaminsu a wasu lokuta sanannu. Misali yawancin makaran tun Allo suna fara karatu daga bayan sallar Asuba zuwa lokacin da rana ta hudo daga nan za’a salami kowane yaro don ya fita domin neman abin da zaici har zuwa kimanin karfe takwas na safe daga nan za’a koma karatu baza a tashi daga karatu ba sai karfe goma na safe zuwa sha daya a wannan lokacin akansamu wasu almajiran da suke fita neman tuwan da aka ci jiya da daddare aka rage wanda akafi sani da dumame. Sannan wadan nan almajiran suna da lokacin shakatawa kusan tundaga wannan lokacin da suka tashi harzuwa lokacin sallar Azahar sannan wasu su koma makaranta suyi rubutu ko wankin Allo kodai wani dan aiki da zasuyi amakaranta wanda wannan lokacin shi zai daukesu zuwa la’asar daga nan ne fa karatu yake kankama harzuwa dab da magaruba daga nan za’a tashi zuwa sallar magriba baza a dawo karatu ba sai bayan sallar isha to daga nan ne za’ayi karatu harzuwa lokacin day a sawwaka. Wannan shi ne karatun makarantar Allo wanda ake turo yara daga garuruwa zuwa gurin alarammomi domin neman karatun Alqurani.

Sannan su wadan nan malamai da akafi sani da alarammomi ba dukansu ne malaman da za’a kira malaman Addini ba domin Addinin musulunci bai takaitu zuwa ga karatun alkurani ba kawai; akwai sauran karatu na litattafan hadisi da fiquhu wanda wadan nan malaman da suke wannan karatu su akafi sani da malaman zaure; to a musulunce wadan nan sune ake kira malaman Addini domin sunhada ilimin duka na Alqurani da na hadisai. Sannan su kuma alarammomi galibin su sunfi shahara da karatun alkurani wato ba tare da sanin fassararsa ba a wani lokacin ana kiransu dasunan Gardawa. To a gaskiya baduk wadan nan gardawa ko alarammomi bane malaman Addini. Ba ina muzanta karatun kur’ani bane ko alarammomi.

Sannan idan muka duba Bara ko roko wanda galibin wadan nan Almajirai suke yi da sunan karatun alqurani. Agaskiya bara bata da alaka da karatun alkurani yanzu misalin idan kadauki kano da Maiduguri zaka iske yara suna bara da sunan sunzo karatun Alkurani tundaga karfe bakwai nasafe harzuwa karfe takwas na dare. Sai kayi mamaki ina karatun da suke yi ko kuma ina malaman da aka damka amanar wadannan yara a hannunsu suke. Zaka gansu babu tsafta babu takalma akafafunsu gashi kuma kayan su duk sun yage kai kace tonosu akayi daga bola kuma da sunan su makaranta alkurani ne shin anan me suke nunawa? Ga wanda baisan karatun alkurani ba idan ya gansu mai zaidauka? Wanda kuma a zahirin gaskiya wannan hali da suke ciki na kazanta Alqurani yayi turda ita. Kuma zaka samu su wadan nan yara da ake kira Almajirai wanda galibi shekarunsu daga biyarne zuwa shekara goma sha biyar suna bin kwararo lungu da kuma manyan tituna musamman na cikin birni kai zaka samu Almajiari sunazuwa har ma’aikatun gwamnati misali Audu bako sakateriya a kano zaka iske almajiarai maza da mata yara da manya da ‘yan jagaliya duk suna roko da tumasanci. Wanda a halinyanzu a kano alkalumma suna nuna cewa akwai almajirai sama da miliyan biyu duk da gwamnatin da ta gabata taya iyakar kokarinta wajen taga ta tallafawa abin wanda maimakon wannan ya zama ansamu raguwar abin a a kullum sai kara samun karuwar almajirai akeyi. Kaduba kasuwanni ko ina kaje kaga almajiri kuma waishi dalibin alqurani ne.

Baya ga wadan nan yara da suke bara da sunan neman abin da zasu ci akwai kuma wani kashin na mabarata wanda sukuma ba makaranta alqurani bane wasu tsofaffi ne mata da maza da yawan wadan nan tsoffi suna bin manyan tituna da unguwannin masu hannu da shuni da kofar gidajen attajirai dan sunan bara wani lokacin zaka gansu tare da kana nan yara kodai sunayi musu jagora ko kuma suna binsu rabe-rabe, sannan idan ka dubi wadan nan tsofaffin da kyau zaka ga ba ‘yancikin birni bane domin akan tituna suke kwana, misali kaje titin miyangu road dake kano da Abbas Road da Tukur Road da Audu Bako Way duk zaka rika ganinsu da tsummokaransu jibge mata da maza, watakila idan ka bibiya a kauye da suke zaune suna da mahalli da ‘yan kaji da agwagi da suke kiwo duk da munsan cewa akwai matsananciyar rayuwa acikin kauyuka amma zaka samu mutuwar zuciya ce ta fito da wadan nan tsaffi daga kauyukansu, a gefe guda kuma gwamnati babu wani yunkuri da take yi na taimaka musu, munsan da cewa akwai gidan tsofaffi kusan a kowace jiha a Arewacin Najeriya misali a kano akwai wanda Audu Bako ya gina a Mariri yana nan haryanzu inbanda kadangaru da gafiyoyi da kunami sune kawai ke budurinsu a wannan gida.

Sannan wani kason kuma na almajirai su ne kutare da makafi da guragu wadanda akafi sani da nakasassu ko masu bukata ta musamman, suma suna nan suna bin tituna da ma’aikatu da guraran zaman jama’a da masallatai da majami’u, kai yanzu abin harma yakai kawai da mutum yaji ciwo a hannu ko a kafa kawai saya nannade hannu ko kafa da bandeji da sunan shi almajiri ne ataimaka masa kai abin ma ya wuce nan zaka ga kato lafiyarsa kalau yan cewa wa jama’a sutai makamasa. Wanda anan jama’a da dama sun taimaka wajen karfafawa wadan nan masu mutuwar zuciya gwiwa domin da mutum yace a taimaka masa sai kaga jama’a kowa na yunkurin zura hannu a aljihu yana lalubo ragowar canji, bayan ga makwabtansa sune a hakku da ya taimakawa akan wani mutum da hanyace ta hadasu, da dama wasu suna sane da cewa makwabtansu suna cikin mawuyacin hali na bukata mai makon su taimaka sun gwammace su je bakin titi su cigaba da kashewa wadannan mutane zuciya.

Bayaga wadan nan akwai masu bara yar tafida gidanka wato mobile begging sukuma suna bin masallatai ne da an idar da sallah sai kaga kato lafiyayye ya tashi tsaye kodai yace jama’a ni matafiyi ne ina neman ataimakamin guzurina ya yanke ko kuma yace jama’a nabaro iyalina babu abin da zasuci a taimakamin. Wasu kuma zaka ga nasu salon daban ne domin su kuwa rataya gatari suke a kafada suna bin guraren zaman jama’a suna cewa wallahi munnemi aiki bamu samu ba ku taimaka mana dana abinci hakadai bara salo-salo idan kaga wani salon barar ma abin sai ya baka kunya da mamaki. Wata rana wani magidanci yana zaune a kofar gidansa sai ga irin wadan nan mutane da gatura biyu a kafadunsu suka rokeshi, da ya kallesu sai yace tunda baku sami aikiba ga aiki yace ku sare wannan bishiyar ku daddatsata nawa zan biyaku sukayi ciniki kafin ya shiga gida ya fito sun tsere, kaga wannan karara ya nuna karya sukeyi daman mabarata ne.

Shin wai mu muka fi kowa talauci ne akasar nan ko kuwa mu muka fi kowa mutuwar zuciya? Shin ina alakar bara da alkurani? Wai yanzu abin haryakai ga almajirai zasu hada kudi sutafi lagas ko Ibadan ko Abuja ko wasu garuruwan ba wadan nan ba dasunan bara.Ga misali za a kwaso almajirai daga legas azo kano a zubar dasu kuma kaji babu wani mataki da gwamnati ke dauka na magance aukuwar hakan anan gaba. Ga kuma manyan Almajirai wadan da suke barar kasa da kasa wato international bagging wato irin masu zuwa saudiyya da Sudan kusan nayi maka jam’i duk almajirin da ka gani a Sudan insha Allahu Bahaushe ne wai yana tara kudin tafiya maka ta barauniyar hanya wanda da yawa suna mutuwa a teku a cikin wannan tafiya mai hadari a cikin kwale-kwale.

Anan yaka mata gwamnati tatsaya tayiwa abin duban tsanaki bawai ataimakawa almajirai ba kawai a’a yaya za’a yi a rage kwararsu zuwa cikin birane, wannan shi ne babban abin da gwamnati yaka mata tayi domin idan katai makawa goma to insha Allahu zaka samu sabbabin almajirai wanda sun nunka wadan nan da aka taimakawa. Sannan sukansu malamai yaka mata sufadakar da mutane dan gane da cewa bara bata da alaka da karatun alkurani.

Abin Tambaya me ya sa kawai Hausawa ake gani suna bara da a Najeriya? Me gwamnatocinmu suke na yakar talauci da fatara? Me ya sanya ‘yan kudu basa yin bara kamar yadda akeyi a Arewa? Misali idan ka kalli kasafin kudi na bana na jihohin Arewa ya ninka na jihohin kudu amma kuma tsananin rayuwa yana Arewa jihar Ekiti tanada kasafin kudi na Naira Biliyan 88, Kuros Riba Naira Biliyan 144, Ananbara Naira Biliyan 82, Enugu Naira Biliyan 74. Amma idan ka kalli na jihohin Arewa sai kaga ya fi nasu nesa ba kusa ba misali a bana Jihar Kano tanada kasafin kudin da yakai Naira Biliyan 210, Borno Naira Biliyan 150, Gombe Naira Biliyan 92 duk da irin wadan nan makudan kudi da ake warewa amma baka ganin wani canji duk shekara, ga rubutun kasafin kudi akan takarda abin gwanin sha’awa amma kuma yana tsayawa iyakar takardar ne kawai domin babu wani abu da yake nuna cewa ana aiwatar da wannan kasafin kudi dake kan takarda tundaga gwamnatin tarayya har ta jihohi.

Lallai akwai babban aiki na kokarin yakar bara da almajiranci a jihohin Arewa. Misali idanda da gaske shugabannin Arewa suke me zai hana su kai koke zuwaga majalisar kasa da gwamnatin tarayya akan a kirkiro da sabuwar wata ministiri ta al-majirai kamar yadda aka kirkiraro ma’aikatar Neja dalta inda ake taimakawa da zauna gari banza tsageru da dimbin kudade kuma ana kaisu kasashe dabam-dabam suna zuwa suna karatu. Idan har tsagerun Neja Dalta zasu zama barazana a kudu don haka aka samar masu da Ministry to shakka babu muma a yankin Arewa al’majirai babbar barazana ne domin da irin wadan nan Al-majirai Mai Tatsine yaci karensa, haka kuma irinsu suke saurin shiga kungiyoyi irin na Boko Haram wanda tuni bayanai suka nuna tun asali sune ‘yan gani kashenin Muhammad Yusuf ire-irensu ya rika ribata da kalamansa, shakka babu muna bukatar a kirkiro da sabuwar ma’aikatar al-majirai ta gwamnatin tarayya domin idan har za’a sami al-majirai sama da miliyan 2 wanda sunkai ko sun ninka yawan mutanan jihar Bayelsa da delta da Ekiti da Ebonyi.

Yasir Ramadan Gwale

yasirramadangwale@hotmail.com

http://yasirramadangwale.blogspot.com

Wednesday, March 7, 2012

Matsalar Dan Arewa!!!

Matsalar Dan Arewa!!!

Naka yanzu sai naka, ‘yan Arewa ga naku . . .! Wannan wani baiti ne na wata waka da akayiwa wani dan siyasa da ya fito neman takara daga Arewa. Hakika wannan baiti yana nuna abubuwa da yawa; kusan a bayyane ta ke cewar duk lokacin da kaji ana maganar Arewa to ko shakka babu ana batun wata matsala da ta faru ne, da wahala kaji ankira sunan Arewa ana maganar samar da wata sabuwar jami’a ko wani muhimmin abu na cigaba, da yawan manya ‘yan Arewa basu cika tunawa da wannan yanki namu ba sai idan sun shiga cikin wani mawuyacin hali, sannan zakaji suna maganar Arewa, Ko kuma idan suna cikin wani hali na bukata sai kaji suna cewa to jama’a ga namu kada mu kishi domin naka naka ne; tabbas maganar haka take cewa “naka fa sai naka”, amma abin tambaya anan lokacin da namun ya samu dama me ya yi mana da ya nuna cewa shi dinfa namu ne? Akwai ‘yan Arewa da yawa da suka samu dama da zasu kawowa Arewa cigaba mai yawan gaske a lokacin da suka sami dama amma da yawa haka damar ta bare basu amfana mana komai ba, sai bakin ciki da takaici.

Yanzu idan zamuyi magana ta gaskiya, mukalli duk irin matsalolin da yankin Arewa ke ciki, me shugabanninmu sukayi na fitar damu daga cikin mawuyacin halin da muke ciki? Sanin kowa ne cewa yankinmu shi ne yankin da yafi kowane yanki komabaya ta kowanne fanni a kasarnan, gashi kuma Arewa shi ne yankin da ya fitar da galibiln ‘yan siyasar da sukayi tasiri a al’amuran siyasar kasarnan. Yanzu idan zamu dauka daga shekarar 1999 zuwa yanzu da mulki ya ke a hannun farar hula, wace irin matsala ce da ta ke damun Arewa shugabanninmu suka sanyata agaba akaga bayanta? Amsar itace babu, sai dai kawai dogon turanci da iya lankwasa harshe da karya hula agaban goshi da nuna ‘yan bokwanci da bajekolin manyan riguna da dirka-dirkan motoci a lokacin taruka. Yanzu mu dauki matsalar wutar lantarki da rashin aikin yi, kusan babu matsalar da tafi gallabar yankin Arewa kamar wannan matsala, ‘yan Arewa sune suka kawo Olushegun Obasanjo a 1999 suka tallata shi domin a zabe shi, amma me sukayi na ganin cewa Obasanjon ya kawo karshen matsalar wutar lantarki da magance zaman banza a Arewa? Kullum kuma kara fadawa cikin matsala mukeyi daga wannan zuwa waccan. Bayaga rashin aikin yi da ya addabi matasanmu da rashin ingancin ilimi da kiwon lafiya da matsalar tsaro da rikicin manoma da makiyaya, da kuma mafi muni a iya tsawon tarihin Arewa shi ne al’amarin Boko Haram, don ko sha’anin rikicin mai tatsine da ya faru a kano da maiduguri a shekarun 1978-80 bai kai kaso daya cikin goma na abin da ke faruwa a yanzu ba.

Idan muka duba matslar ilimi kusan mune mukafi kowa yawan jahilai (illiteracy) a kasarnan, jahilai ina nufin ta bangaren ilimin boko tunda yake da shi ne gwamnati ke la’akari wajen aiwatar da dukkan ayyuka na hukuma, domin baza a dauke ka aiki kowane iri ba sai kana da takardun makaranta; yaranmu sune wadan da basa iya cin jarabawa, malaman makarantunmu sune suke fama da rashin kwarewa da rashin ingataccen yanayin koyo da koyarwa; kusan shugabannin da suke ikirarin yanzu sune shugabannin Arewa idan ka bincika zaka samu sunyi karatune kyauta ba da kudin iyayansu ba kai hasalima galibi ‘ya ‘yan talakawa ne, amma da al’amura suka dawo hannunsu duk suka maida hannun agogo baya. Domin a lokacin da kasar nan batada kudi kamar yanzu aka dauki dawainiyarsu ta karatu da bukatunsu, a gefe guda kuma ana ta kokarin samar da kamfanoni da masana’antu domin samar da guraban aikin yi ga wadan da suka gama makaranta, irin manyan kamfanonin da muke da su irinsu Arewa Textile da manyan masakun Kano da Kaduna da UTC da PZ da Liventise da kamfanin mulmula karafa na ajakuata da kamfanonin siminti da muke da su da manyan kantunan kamfani irinsu John Holt duk wadan nan sun zama tarihi gine ginen kawai suka rage duk da suma suna fuskantar barazanar yanayi, sannan ragowar wadan da suka rage irinsu kamfanin buga jaridu na Arewa wato NNN da Gaskiya Tafi Kwabo suna cikin mummunan yanayi na Rai kwa-kwai mutu kwa-kwai duk wannan yana faruwa ne a lokacin da samun kudin da kasarnan ya ninka ninkin ba ninkim kaji ana maganar kudi malala gashin tinkiya, a lokacin da kasafin kudin kowace jiha a Arewa bai gaza Naira Miliyan dari ba (M100).

Yanzu ina amfanin kungiyar tuntuba ta dattawan Arewa ta ACF da kungiyar Gwamnonin Arewa da duk kungiyoyin da muke da su masu ikirarin Arewa? Sai kayi mamaki shin wai duk irin kungiyoyin da muke da su da sunan Arewa waccece ta gaskiya domin bayaga ga ACF akwai kananan kungiyoyi da daman gaske tundaga na dalibai da na ‘yan boko da na Matasa da na ‘yan kasuwa da tsofaffin sojoji da sababbi duk wacece ta ke yi da gaske akan wannan yanki? Abin da zai baka mamaki mu kalli takwarorinmu ‘yan kudancin kasarnan, idan muka dauki Yarabawa mutum daya ya iya hada kan dukkan yarabawan kasarnan suka zabi jam’iyya daya a zabubbukan da suka gabata sai kace shin wannan wane irin mutumne kuma jama’arsa wasu irin mutane ne? Bola Ahmed Tinubu ya tsaya kai da fata akan al’ummar yarabawa ya shiga lungu da sako domin ya tabbatar sun zabi jam’iyyar ACN kuma sukai hakan, kuma idan ka duba bashida mukami na komai a cikin jam’iyyar, kaga wannan shi ne kyakkyawan jagoranci; ina ‘yan Arewa da muke ikirarin mungaji siyasa daga mutane irinsu Mallam Aminu kano da Sa’adu Zungur da sauransu shin wannan ba zai zamar mana abin isharaba; haka kuma, idan ka dauki al’ummar gabas ta inyamirai suna karkashin jagorancin mutum daya, yanzu a ‘yan kwanakinnan da Ojukku ya mutu duk wani inyamiri dake kasarnan sai da ya rufe kantinsa domin nuna alhinin wannan mutum da suka kira jagoransu kai inyamirai har a kasar Amerika basu bude kantunansu ba lokacin da ake jana’izarsa duk domin nuna girmamawa gareshi. Yaznu idan ka dawo nan gida Arewa shin waye zai iya magana da murya daya a saurareshi? Shin akwai wanda zai iya cewa a zabi mutum guda kuma ayi hakan? Shin akwai wani da zai mutu mu nuna alhinai kamar yadda inyamurai suka nunawa Ojukku? Waye zai iya bada umarni kowa yabi, shi kenan mun zama mu bamu da kan-gado!

Sannan uwa uba kuma akazo akayi amfani da addini aka raba kan Arewa. Sanin kowa ne cewa a yankin Arewa babu wata magana ta kabilanci sai ta addini domin kiristan Arewa yana matukar kin Musulmin Arewa haka musulmi ma, duk ilimin da muke da shi ya tashi a maho tunda bamu iya amfani da shi ba wajen dai-daita tsakaninmu, akazo aka haifar da kiyayya da gaba babu gaira babu dalili kullum mune akejiyowa a shafukan jaridu da kafafen yada labarai muna kashe junanmu muna barnata dukiyar ‘yan uwanmu da suka jima suna tsuwurwurinta. Yanzu irin dimbin rayukan daka rasa da dukiyar da akayi hasara madudu ta sanadiyar rikicin jihar Pilatu da Kaduna Allah ne kadai yasan adadinsu, haryanzu an rasa wanda zaiyi magana a saurarashi dangane da wannan batu, sai dai kawai ayi taron nuna isa da shan shayi a tashi . Haka kuma, akazo ta karfi da yaji aka haifar da wata kungiya da suke ta bata sunan Arewa da musulunci inda suke ta dasawa tare da tayar da Boma-bamai babu kakkautawa ta ko ina a Arewa anrasa yadda za a iya shawo kan wannan al’amari.

Matsalar dan Arewa kamar yadda na lura ita ce, kowannenmu so yake ace shi ne shugaba, shi yake bayar da umarni ana karba, ina ganin wannan ce ta haifar da kungiyoyi masu yawa da basa iya amfanawa da wannan yanki da komai ba, kuma, ga zatona wannan bazai rasa nasaba da kasawar kungiyar dattawan Arewa ta ACF da kungiyar Gwamnonin Arewa ba. A shekarar da ta gabata ta 2011 manyan ‘yan Arewa da suka tsaya takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP wato Alh Atiku Abubakar da Gen. Ibrahim Badamasi Babangida da Alh Aliyu Gusau da Bukola Saraki wani kwamiti karkashin jagorancin Mallam Adamu Ciroma ya yi kokarin hada kansu domin fitar da mutum guda wanda zai tsayawa jam’iyyar takara daga yankin Arewa wanda sukaci nasarar fitar da Atiku Abubakar, ko shakka babu wannan babban abin a yaba ne domin abin da bamu taba zato bane ya faru, har ga Allah da yawanmu bamuyi zaton za’a zabi mutun guda sauran su hakura ba, wanda wannan shi ne babban abin da muka rasa tun da farko, da ace tun farko haka muke akwai jagoranci karkashin mutum guda da tuni bama cikin halin da muke ciki. Don haka da alama zamu dade cikin halin da muke ciki na fatara da komabaya da jahilci matukar bamu dinke mun ajjiye dukkan bambance bambance ba mun tafi karkashin jagoranci guda daya ba. Domin wadan nan kungiyoyi da muke dasu babu abinda za su yi face kara raba kan Arewa. Yanzu mu duba yadda kullum ‘yan yankin da ake kira tsakiyar Arewa ko middle belt suke ta kokarin nuna kamar su ba ‘yan Arewa ba ne; yanzu Arewa daga guda daya ta zama uku wato Arewa maso yamma, Arewa maso Gabas da kuma tsakiya ko idan son samu ne yaci gashin kansa, to haka zamu ci gaba da rarrabuwa matukar bamu hade munyiwa Arewa aiki bai daya ba.

Bazamu gushe ba muna tunawa da wadan da suka nuna kishinmu da gaske ba irinsu Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto da su Mallam Aminu Kano da Sa’adu Zungur da kuma irinsu Sunday Awoniyi duk sun nuna kishin Arewa da gaske, babu bambancin kabila ko na addini. Allah ya kawo mana zaman lafiya a yankin Arewa, kuma Allah ya sa shugabanninmu su fadaku su maida hankali wajen cigaban wannan yanki namu. Allah ya taimaki kasarmu Najeriya gaba daya.

Yasir Ramadan Gwale

Yasirramadangwale@hotmail.com

http://yasirramadangwale.blogspot.com

Monday, March 5, 2012

Yunkurin Rage Yawan Musulmi a Najeriya ta Arewa!!!

A shekarar dubu biyu da shida (2006) da ta gabata tsohuwar gwamnatin shugaba cif Olushegun Obasanjo da ta shude ta gudanar da kidayar jama’a a Najeriya. A wannan kidaya da akayi kamar yadda aka bayar da rahoto ankirge ko kididdige adadin gidaje da kuma al’ummar Najeriya, inda aka samu alkaluma da suke nuna cewa Najeriya tana da yawan mutane da adadinsu yakai kusan sama da miliyan dari da sittin da biyar (M165) wanda wannan kidaya ta nuna cewa Arewacin Najeria inda galibin mazauna wannan yanki musulmi ne, shi ne yakin da yake da kaso mafi yawa na al’ummar Najeriya, inda jihar kano tayi fice da kusan dadain da ya haura sama da mutum miliyan tara (M9) a cewar wannan rahoto; wanda kuma jihar legas da ke zaman jiha mafi girma akudancin Najeriya tazo ta biyu da kwatankwacin wannan adadi na kano, sai dai hukumomin jihar sunyi farat inda sukace basu yarda da wannan kidayar ba domin suna ganin babu yadda za’ayi ace wata jiha tafisu yawa a duk fadin Najeriya, haka nan suma hukumomin wannan jihar suka fito da nasu alkaluman kidayar masu cin karo da juna da na gwamnatin tarayya.

Abin mamaki, kuma abin daure kai, har wayau kuma abintambaya, dangane da wannan kidaya shi ne me ya sa ba’a kirga adadi ko yawan al’ummar Musulmi da kirista ba a wannan kidaya. Lallai ya kamata duk mai hange ya yi wannan tambaya shin meyasa aka tsallake batun addini a wannan kidaya? Kasan cewar Najeriya kasa ce da addini yake da tasiri ainun tsakani Musulmi da kirista, kuma zai zama abu mai muhimmanci ta wajen sanin adadin Musulmi da kuma Kirista, domin ganin yadda ya kamata a rika rabon mukaman gwamnati tsakanin musulmi da kirista, amma gwamnatin Obasanjo ta wancan lokaci ta ki yarda da a kirga yawan Musulmi da Kirista; sai dai a bayyane ta ke cewar ko a kirga yawan musilmi ko kada ayi hakan, a bayyane take cewar musulmi sune suke da kaso mafi yawa acikin al’ummar Najeriya, wanda ya sani, ya sani wanda kuma bai sani ba ya sani; don ansan cewa mafiya yawan musulmi suna da matan aure fiye da daya kuma sunada yawan ‘ya ‘ya wannan ta sanya adadin al’ummar musulmi ke karuwa cikin sauri.

Kamar yadda bayanai suka nuna cewar Musulmai sune ke da kusan kason da ya haura sama da kashi 74.8 a cikin al’ummar yanki Arewa. Kamar yadda wannan kididdiga ta nuna yankin Arewa maso yamma(North West) shi ne yankin da yafi daukar kaso mafi yawa na al’ummar Arewa, kuma wannan yanki shi ne yake da kaso mafi karanci na al’ummar kirista, domin idan ka cire kudancin kaduna babu wani guri kuma da yake da kiristoci masu dan dama a wannan yanki. Sannan kuma idan ka dauki yankin Arewa maso gabas(North East) shi ne yankin da yafi na yamma yawan kiristoci, sanin kowa ne akwai kiristoci a jihoin Adamawa da Taraba da Bauchi da Gombe da kuma jihar Borno, kusan idan ka dauki wadan nan jihohi jihar Taraba itace jihar da ta fisu yawan kirista sannan Adamawa da Gombe da Bauchi da kuma Borno ke binta a baya. Daga nan sai yankin Arewa ta tsakiya(North Central) inda kididdiga ta nuna kamar ana kan-kan-kan tsakanin Musulmi da kirista; amma sai dai a zahirin gaskiya ba haka bane domin idan ka dauke jihohin Benuwai da Pilato sune kadai jihohin da kiristoci suke da rinjaye, idan kuma ka kalli jihohin Kwara da Kogi da Nassarawa da Niger kusan musulmi suke da rinjaye a wadan nan jihohi.

Tun lokaci mai tsawo kiristocin Arewa suke ta kokarin kara yawan al’ummar kirista a wannan yanki na Arewa ta hanyar shiga lungu da sako na yankunan wannan yanki domin su maida mutanan da basuyi imani ba wato maguzawa kiristoci, wannan kuma ya faru ne da gudunmawar Turawa ‘yan Mishan, tun kusan zamanin ‘yan mulkin mallaka; domin a lokacin da yarima mai jiran gadon sarautar Birtaniya Prince of wales yarima charles ya kawo ziyara jihar kano, yaje gurare daban-daban daga cikin guraran da ya ziyarta harda wani kauye da ake kira kadawa a yankin karamar hukumar Kura inda bayanai suka tabbatar da cewar wannan kauye a kusan shekaru 80 ko sama da haka da suka gabata wata baturiyar ingila ta taba gina coci a kauyen wannan ta sanya ya kai ziyara cikin baraguzan cocin domin ya tuna da aikin da tayi, inda aka daukeshi hotuna aciki, domin garin da yake a wancan lokacin yanzu ya tashi. Haka kuma, kiristoci sunayin dukkan mai yuwuwa wajen kama kudancin jihar Kano domin a wata ziyarar wa’azin maguzawa da na kai zuwa wasu yankunan kananan hukumomi dake kano kamarsu Sumaila da Rogo da Bebeji da Kiru da sauransu tuni kiristoci sukayi nisa wajen maida yan uwanmu masu magana da yare irin namu da kuma al’adu da dabi’u irin namu, sunyi kokarin ribace musamman matasa da dama a wasu kauyuka inda aka maidasu kiristoci, misali a wani kauye da ake kira Gidan kota dake karamar hukumar Sumaila kiristoci sun mamaye kauyen inda suka giggina musu coci-coci da dakunan shan magani(Dispenseries) da basu taimakon takin zamani da garman Noma da basu suturu sababbi masu dauke da kodai hoton da ake cewa Yesu(Isa almasihu) ne ko kuma hoton paparoma john poul na biyu, haka abin yake idan ka shiga wani kauye da ake kira Bari a karamar hukumar Roggo da Talatar Jiddo a Bebeji, duk wannan anayi ne akan idanun Sarakunanmu na gargajiya wadan da ke ikirarin musulnci. Yanzu kuma wani shiri da kiristoci suke yi shi ne na mallake wasu yankuna namu misali, sunyi ta kokarin kama tare da mallake kudancin kowace jiha a yankin Arewa, idan ka dauki kudancin Kaduna sunriga sun mamayeshi tare kuma da kokarin kakkabe musulmi daga wannan yanki, duk wanda ya kalli rikicin zangon kataf da zankowa tundaga 1980 har zuwa yau zai tabbatar da haka, haka kuma suna ikirarin mallakar Kudancin jihohin Adamawa da Bauchi da Borno da Gombe da Niger da Nassarawa da Kogi da Kwara da wani sashe na kudancin jihar kebbi.

Wata dabara da kiristocin Arewa suke yi ita ce, suna daukar matasa masu jini a jika na wadan can kauyuka da muka ambata suna kaisu kasashen kudu ana horar da su yadda zasu kirawo ‘yan uwansu zuwa addinin kirista da basu ‘yan kudaden da zasu baiwa wanda yayi taurin kai da kuma yiwa masu unguwanninsu hidima da baiwa matansu sarkokin gicciye, domin zaka ga da yawa daga cikin mata da yara kanana da sarkokin gicciye(kuros) amma zasu cemaka su ba kiristoci bane, sannan kamar yadda na fada a sama suna yin amfani da garmar noma da sayan injin nika su baiwa duk wanda ya zama kirista; domin zaka ga limamin musulmi bashi da ko keke hawa ga rigarsa duk ta yage amma ga wani daga zamansa kirista ya fara sanya sutura mai dan kyau da sabulan wanka mai kanshi da sauransu. Wanda kamar yadda na fada duk wannan yana faruwa ne akan idanunmu, munyi sake wasu sukazo har cikinmu suka dauki al’ummarmu suka mayar da su kiristoci munaji muna kallo, ba’anan gizo yake sakarba domin wadannan matasa da ake mayarwa kiristoci ana ta kokarin cusa musu akidar kin duk wani musulmi Bahaushe tare da nuna musu cewar mudin makiyansu ne, domin munyi watsi da su bama kulawa da su.

Tabbas, shirye shirye sun kankama na kokarin rage adadin yawan al’ummar musulmi a Arewa, domin idan muka kalli rikicin Jos da yaki ci yaki cinyewa, kullum Musulmi ake kaiwa hari a kashesu a lalata dukiyoyinsu duk wannan da manufa; da kuma rikicin kudancin Kaduna ka bincika yanzu mafiya yawan mazauna garin zankowa wadanda Hausawa ne musulmi yanzu sun bar garin inda suke samun mafaka a sansanin ‘yan gudun hijira dake mando a cikin garin Kaduna, kaga ke nan anacin nasarar kakkabe musulmi daga kudanci kaduna, duk wannan ‘yan bokonmu da sarakunanmu da tsofaffin sojoji da sababbin sojoji da ‘yan sandanmu da ‘yan siyasarmu duk suna kallo ana karar damu babu wanda zai iya magana, kwanakin baya mai martaba sarkin Katsina Abdulmumin Kabir yakai ziyara sansanin ‘yan gudun hijira a kaduna shakka babu wannan abin karfafa guiwa ne, ya kamata da majalisar sarakuna Arewa da kungiyar Jama’atu Nasrul Islam suyi wata hobbasa wajen ganin anmaida Hausawa mazauna garin zonkowa garinsu kuma anbiyasu diyyar rayukan da aka kashe musu tare kuma da biyansu diyyar dukiyoyinsu da suka yi hasara. Kamar yadda kungiyar CAN take ruwa tayi tsaki akn dukkan wani abu da ya shafi wani kirista.

Sannan hanya ta biyu ta kokarin rage al’ummar Musulmi shi ne amfani da akayi da kungiyar Boko Haram da kuma sunan musulmi. Shakka babu biri ya yi kama da mutum, domin wannan al’amari na Boko Haram yana kara bayyana cewa kwata-kwata ba Musulmi ne suke kai wadan nan hareharen ba; domin idan muka lura su wadan da suke kai harin nan da sunan wannan kungiya suna kaiwa jami’an tsaro ne, wannan wani hoto ne da ake nunawa na tsorata al’ummar musulmi daga shiga aikin dan sanda, sannan kuma a gefe guda ana yin amfani da ‘yansandan bogi da sojojin bogi suna kara kashe al’ummar musulmi da sunan farautar ‘yan Boko Haram, domin duk wanda ya kalli abinda rundunar hadin guiwa ta tsaro a jihar Borno ta JTF sukeyi ya kara tabbatar mana da haka, domin suna shiga gida-gida suna kashe mutanan da basu jiba basu gani ba, da sunan bankado ‘yan kungiyar Boko Haram; kaga kenan duka biyu ga hare-haren Boko Haram ga kuma kisan ‘yansanda da suke kashe fararen hula.

Tabbas yanzu ta bayyana cewa kiristoci musamman na Arewa sune suka assasa kungiyar Boko Haram tare da amfani da ita akan nuna cewa musulmi ne. Yanzu idan zamu iya tunawa ankama wata mata mai suna Lucy Dangana akwanakin baya a iyakar Najeriya da kasar chadi ta shigo da makami wadda wannan mata kirista ce ba musulma ba kuma ta nuna cewa wadan nan makamai na Boko Haramne, amma shiru ka ji batun, sannan ga shi Allah yana tonawa wasu da dama asiri inda ake kama kiristoci cikin kama irinta musulmi suna yunkurin dana ko tayar da Bom a coci da nufin cewa Musulmi ne kamar yadda ya faru a Yenagoa a jihar Bayelsa da kauyen miya barkate a jihar Bauchi, domin kafin Bom ya tashi a harabar coci saunawa ya tashi a tsakanin musulmi, musulmi nawa ne suka rasa rayukansu ta sanadiyar wannan rikici da ake ta dangan tashi da addini da Boko Haram, idan banda wadan nan ‘yan kwanaki da bayanai suke nuna cewa ana kai hari a harabar coci, ai kusan dukkan harin da aka kai musamman na baya-bayan nan na boma bomai a johohin Yobe da kano da Gombe duk musulmi ne da daman gaske suka rasa rayukansu.

Sannan daga karshe bayan duk wadan nan abubuwa da akeyiwa musulmi, sannan akoma ana bankawa dukiyoyinmu wuta tare da sanyawa mafiya yawancin kasuwanninmu wuta da nufin karya tattalin arzikinmu ta yadda za’a hanamu katabus, daman kuma ta ban garen karatun Boko anriga anyi mana fintinkau, abin da ake kira Quota system a gwamnatin tarayya duk gurin da ya kamata a sanya dan Arewa sai a sanya kirista daga Arewa, wanda kuma idan mukabi kididdiga ta ‘yan sanda da muke da su a Arewa zamu sha mamaki domin idan bamu zo kan-kan-kan da kiristoci ba ta kuwa bazamu tsere musu ba musamman a kana nan ‘yansanda da ake kira kurata, daman kuma su ake turawa kwantar da tarzoma, duk bayan wannan kitumurmura da kutungwila da makirci da aka shirya na murkushe al’ummar musulmin Arewa, gwamnatin tarayya ta gayyato sojojin kasar Amurka da sunan kokarin shawokan al’amuran tsaro, kamar yadda mukaji Sabon jakadan Amerika a Najeriya MacCulay yana fada bayan harin bom da aka kai akano cewa kasar Amerika tana tunanin bude karamin ofishin jakadancinta a Kano da kuma yadda zataga yadda zata taimakawa Najeriya wajen magance matsalolin tsaro, inda yace a shirye suke su horar da jami’an tsaronmu yadda ake iya kwance bama baman da aka dana kafin su tashi. Kaga duk wannan abubuwa ne da suke nuna biri yayi kama da mutum.

Lallai idan barci muke to yanzu lokaci yayi da al’ummar musulmi ya kamata su farka. Domin yanzu makircin da ake shirayamana yana ta kara bayyana, a yayin da duk wadan nan kutunguila da ake shirya mana take cin Nasara mu kuma muna can mun maida hankalinmu akan batun izala da darika ko batun maulidi bidi’ah ne ko ba bidi’ah bane, bayan ga babbar musibar da take tunkaromu da babu ruwanta da darika ko izala ko me maulidi ko marar maulidi, sannan wasu da suke ikirarin su musulmi ne har suna jawo wadan nan arnan a jiki suna nuna aiduk daya ake, wanda kowa yasan karya ne biyu muke, idan har munyarda mauludi musulunci ne ina kirista ina maulidi, me ya hada kifi da kaska, Bahaushe yace duk wanda baiyi sharar masallaci ba to tabbasa bazai kasa yin ta kasuwa ba.

Daga karshe ina addu’ar Allah ya tona asirin dukkan wadan da suke shiryawa mana wannan kullu kurciyar, kuma Allah ya maida kaidnsu garesu, Allah kaci gaba da yimana kariya da kariyar nan taka, kayi mana garkuwa da garkuwar nan taka, ka tsaremu ka taremana dukiyoyinmu, shugabanninmu na Musulmi kuma Allah ka shiryesu ka yi musu jagoranci, mu kuma Allah ka sanya mu kasance masu da’a da biyayya ga shugabanninmu.

Yasir Ramadan Gwale

Yasirramadangwale@hotmail.com

http://yasirramadangwale.blogspot.com

Thursday, March 1, 2012

Addinin Musulunci Ba Addinin ‘Yan Ta’adda ba ne!!!

Addinin musulunci shi ne addinin gaskiya wanda Allah ya aiko Annabi Muhammad Sallalahu Alaihi wasallam dashi kuma ya kasance shi ne cikamakin annabawa, kuma addininsa ya kasance cikamakin addinai, don haka babu wani abu da manzon Allah yatafi yabari face ya yiwa musulmi bayaninsa, don haka ne ya cewa sahabbansa da sauran al’ummar musulmi idan kunyi sabani a tsakaninku sai ku koma ga al’qurani da Hadisi, wato sunnarsa. A sabida haka nema a khudubar bankwana da manzon Allah yayi aikin hajjinsa na karshe yace yau ne nake shaida muku cewa Allah yacika addininsa. Don haka babu wani kari ko ragi da zai zo acikinsa nan gaba.

Don haka addinin musulunci addini ne da yake damfare da rayuwar musulmi gaba daya, kuma musulmi na hakika shi ne wanda yake bibiyar me addini yace kafin ya aikata wani aiki, ba sai ya aikataba sannan ya nemi me addaini yace game da wannan abu daya aikata, don haka, rayuwar musulmi rayuwa ce da take tattare da hikima da amana da basira da sanin yakamata, musulmi shi ne aka sani da Hakuri da juriya da tausayi ga taimakawa marayu da nakasassu da mabukata, musulmi baya tayarda hankalin mutanen da basuji basu gani ba. Musulunci addini ne da bai takaicewa kowa komai ba kuma shi ne addinin daya baiwa kowane mai hakki hakkinsa don haka bai takewa wani ko wata hakki ba, kamar yadda wasu la’annanu suke ta kururuwar iblis cewa musulmi suna danne hakkin musamman na mata.

Misali a makon da ya gaba mukaji, wani dan majalisa daga jihar Kuros Riba(Cross River) ya mika wani kuduri gaban majalisar dokokin jihar inda yake neman majalisa tayi dokar da zata baiwa mata ‘yancin gadon iyayansu, abin mamaki banda wannan dan majalisa ya kawo wannan kuduri baka taba jin wannan batu ba, kaga yanzu da misali a wata kasar musulmi dake Arewa ne aka samu irin wannan da sai kaji kungiyoyin da aka kyankyashesu daga kasar Turai da Amerika suna ikirarin ana dannewa mata hakkinsu na cin gadon iyayansu. Haka suma kasashen turai duk da wannan tsugudidi da suke yiwa kasashen musulmi babu wanda ya kaisu danne hakkin mata, yanzu suna ta kumfar bakin cewa Saudiyya ta dannewa mata ‘yancin tuka mota, kuma suna ta kokari su zuga matasa mata musamman wadan da sukayi karatun boko da su fito suyi bore akan basu wannan ‘yancin.

Idan kuma muka dawo batun da ake alakanta musulmi da shi domin bakanta musu, da kuma bata sunan musulunci musamman a gurin wadan da suke kokarin fahimtarsa shi ne kalmar Ta’addanci. Kalmar Ta’addanci ba sabuwar kalma bace a gurin musulmi kuma dukkan musulmi na hakika yana alla wadi da aikata ta’addanci koda kuwa akan dabbobine ba mutane ba, kamar yadda yanzu aduniya ana tsaka da yaki da ta’addanci, kullum ana alakatanta Kalmar ta’addanci ga musulmi ko kuma musulunci, bayan anki yi mana fassarar hakikanin ma’anar wannan kalma, kuma menene mutum zai yi a kirashi da sunan dan ta’adda, ba adalici bane don musulmi ya aikata wani laifi ka alakanta wannan laifin da addininsa ba, don haka bazai zama halal ba don wani musulmi ya aikata wani laifi ya nemi kariya da addini, manzon Allah yace “da Fatima ‘yar Muhammad Allah ya yarda da ita, zatayi sata wallahi da na yanke mata hannu” don haka wannan yake nuna a musulunci babu sani babu sabo duk wanda yayi za’ayi masa gwargwadon abunda ya aikata.

Yanzu kusan duk wani abunda musulmi ya aikata sai akirashi da sunan dan tada zaune tsaye, ko mai tsattsauran ra’ayin kishin addini, dama wasu kalamai na batanci da ake ta kokarin aibata musulmi, ciki kuwa harda jaridun kudancin Najeriya; ko kuma da musulmi ya yi wani kuskure sai kaji anacewa yana neman aikata ta’addanci. kuma, turai da Amurka basuyiwa musulmi adalci ba domin kullum sukan kira musulmin daya aikata wani laifi dan ta’adda ko kuma wasu kungiyoyi na musulunci. Yanzu misali akwai kungiyar ‘yan ta’adda da ke Arewacin Ireland a kasar Birtaniya kowa yasan abin da sukeyi ta’addanci ne akan fararen hula, amma babu wata kafar watsa labarai ta kasashen turai ko gida Najeriya da suka taba kiransu da sunan ‘yan ta’adda. Sannan kuma, mu kalli kungiyar Tamil Tigas a kasar Sri Lanka babu wanda ya kira abinda da sukeyi da sunan ta’addanci duk da dimbin jama’ar da suka halaka; idan kuma muka dawo gida Najeriya mu kalli kungiyar da ake kira ta tsagerun yarabawa ta OPC karkashin jagorancin cif Ganiyu Adams, da kungiyar da suke fafutukar samar da kasar Biafara wadda Ojukku ya jagoranta duk sun kashe dumbin al’umma, amma wa mukaji ya taba kiransu da sunan ‘yan ta’adda!

Akwai manya manyan mutane wadan da ba musulmi ba sun aikata laifukan da idan akwai wani abu da ya zarta ta’addanci to da za’a iya kiransu da wannan suna amma bakaji ana kiransu da ‘yan Ta’adda ba, misali Adolph Hitler karkashin Nazi ya halaka dubban yahudawa amma ba’a taba alakanta wannan abu da yayi da sunan aikata ta’addanci ba, hasalima turawan Jamus ko son tada wannan magana basa son ayi, haka kuma missolouni ya kashe dubban mutane a Italiya ba’a taba kiran abin da yayi da sunan ta’addanci ba, haka kuma a shekarar da ta gabata aka samu wani matshi ya yi harbin kan mai uwa da wabi a kasar Nezalad ko Holand inda ya halllaka mutane sama da 30 amma duk wannan ba ta’addanci bane!

kawai musulmi da kungiyoyinu su ne ‘yan ta’adda misalai kungiyar Jama’a Islamiyya ta Abubakar Bashir dake kasar Indonusiya ankirata da kungiyar ‘yan ta’adda kuma shima jagoran kungiyar ance Dan ta’adda ne, ko masu matsanancin kishin addini, haka kuma ka dauki kungiyoyi irinsu Hamas da Jihadul Islami a Palastinu duk ankirasu da suna kungiyoyin ‘yan tada zaune tsaye dama kar ka tambayi kungiyoyi irinsu Taliban dake Afghanistan, da kuma kokarin da ake tayi na nuna cewa akwai kungiyar al-qa’ida a Arewacin Afirka.

Haka kuma ka dauki daidaikun mutane, musulmi ne amma duk ankirasu ‘yan Ta’adda misali Ayman Alzawahiri da su Baitullah Mehsud da Abu Mus’ab Alzarqawi da su Mullah Dadullah kai harda dama irinsu Abdulbasit Ali Almagarahi wanda ake zargi da kai harin Lokobi. Idan kuma muka dawo gida Najeriya akwai kungiyoyi da daman gaske awannan kasa ankira wasu ‘yan ta’adda wasu kuma ankauda kai daga garesu misali duk irin abinda MEND take aikatawa a yankin Neja Dalta ba’a taba ganin wannan abun a matsayin Ta’addanci ba, itama kungiyar tsagerun yarabawa wadda ake kira OPC ta aikata shegantaka da tsiya iri-iri amma ba’a taba kiranata da kungiyar ‘yan ta’adda ba sannan kuma mukallai mutane irinsu Zamani Lekot da Zamani kaza sun aikata kisan kiyashi ga musulmin zangon kataf amma duk wannan ba ta’addanci bane haka kuma mukalli irin yadda karfi da yaji aka kakaba kungiyar Boko Haram da musulunci da musulmi, duk da ayyukansu sun nuna sunyi hannun riga da musulunci, domin ko a hareharensu kusan gabaki daya musulmi suke kashewa.

Sannan kuma, gashi yanzu tana sake bayyana cewa kiristoci sune ‘yan Boko Haram, abinda ya faru a harim Bom din da aka kai COCIN church da ke birnin Jos, da kuma wasu matasa da aka kama da yunkurin dasa Bom a takwarar wannan coci a Bauchi duk wannan yana kara nuna cewa wannan makarkashiyace ake shiryawa Musulmi, abin mamaki sai gashi jaridun kudu da kiristoci duk sun ja bakinsu sun tsuke akan wannan batu, sai ma wani kokari da akeyi na nuna cewa Musulmi ne suka kai wannan Hari bayan, bayanai sun nuna cewa shi wanda ya kai wannan harin na Jos kirista ne. Abin haushi shi ne lokacin da aka kai harin Bom din madallah sai ga Sarakunan Arewa da Malaman addini da suhgabanni har rige-rige sukeyi zuwa Abuja domin su jajantawa kiristoci da kungiyar CAN, a ranar da abin ya faru sarkin Musulmi ya sabi takalmansa ya yi Abuja domin ya baiwa shugaban kasa hakuri akan wannan batu, amma sai ga shi duk hare-haren da ake kaiwa musulmi babu wani kirista da kake jin yana magana akai; duk wannan abin bazai bamu mamaki ba, domin Allah yace kada ku taba daukar mushirikai a matsayin masoya ko majibinta!

Rahotanni da dama sun nuna cewa, kiristoci ne suke batar da kama ta hanyar sanya doguwar riga da nada rawani, kamar yadda aka kama wani kirista a jihar Bayelsa yana shirin kona coci, haka itama wata mata da aka kama a Bauchi tana shirin sanyawa wata coci wuta duk domin a dorawa musulmi wannan laifi. Wani abin da zai baka mamaki shi ne irin yadda gwamnati ta doge akan sai anbankado tare da hukunta wadan da suka kai harin ranar kirsimatin shekarar da ta gabata a wata coci a garin Madalla, inda aka zargi wani Kabiru Sokoto kuma aka alakantashi da wannan kungiya ta Boko Haram; abin tambaya me ya sa ba’a binciko wadan da suka kaiwa musulmi hari a garin Jos ba, a ranar idi? Sannan me ya sanya ba’a hukunta wadan nan mutanan da aka kama da yunkurin kona coci ba? Kamar yadda da yawan Jaridun kudu suke ta kururuwar me ya sanya ba’a yanke hukuncin kisa ga dan Najeriyar nan da ake zargi da yunkurin tayar da Bom a cikin jirgi a kasar Amerika ba.

Sanna kuma, yanzu kusan ana ta kokarin a nuna cewa duk dan Arewa ko musulmi kamar dan kungiyar Boko Haramne, wanda mu kanmu musulmi munyi allawadai da wannan kungiya ta Boko Haram da ayyukanta, kuma mun tabbatar da cewa ba musulmi bane na hakika. Alhamdulillahi munyi imani da Allah, acikin al-qur’ani, acikin surata 29 aya ta 2 Allah mai girma da daukaka yana cewa “tsammaninku kawai don kunyi imani, haka kawai sasakai ku shiga aljanna batare da irin misalin bala’i da tashin hankali da tsanini da wadan da suka gabaci wadan da suka gaceku basu sameku ba” ya Allah munji kuma munyi da’a. Muna kallon dukkan wadan nan abubuwa da suke faruwa a matsayin wata jarabawa da Allah ya ke yiwa Musulmin wannan kasar, kuma muna rokon Allah ya bamu ikon samun kyakkyawan sakamako. Hakika munyi hakuri, kuma muna kanyin hakuri, amma wannan bazai hana mu tashi tsaye wajen bincike tare da kokarin kare kanmu da dukiyoyinmu daga wadan nan miyagu azzalumanba. A kwanakin baya munjiyo shugaban kungiyar CAN Pasto Ayo Oritsejafor yana kira ga kiristocin wannan kasa da kowannensu ya tashi tsaye domin kare kansa daga dukkan wata barazana ta musulmi ko kungiyar Boko Haram.

Sai ka rasa su waye jagororin Muslumi a wannan kasa, duk irin wadan nan abubuwan da suke faruwa kowa ya kame bakinsa ya yi shiru tundaga malamai da sarakuna da ‘yan siyasa, kowa tsoron magana yake musamman akan abinda ya shafi wannan kungiya ta Boko Haram alhali kuma munsan suna kara bata sunan musulmi ne, wannan kuma bai hana magautanmu amfani da wannan dama suyi ta kururwa da wanna batu ba, da nuna cewar kusan dukkanmu ‘yan wannan kungiya ne. Har yanzu ankasa samun wadan da zasu tashi tsaye suyi kira ga gwamnatin Jihar Pilato da ta biya Musulmi diyyar irin dukkan abin da akayi musu a wannan jihar, kowa ya ja baki ya tsuke, amma ko ya akaji wani abu ya fashe a coci sai ace gwamnati ta biya diyya!

ko shakka babu musulmi ana iya samunsa da kuskure tunda ba ma’asumi bane zai iya aikata ba daidaiba kuma kamata yayi idan musulmi ya aikata wani laifi kada ajingina wannan laifi zuwa ga addininsa, kamar yadda idan kirista yayi laifi musulmi ba zai jingina wannan laifi zuwa ga kiristanci ba, tabbas musulmi na hakika ba dan ta’adda bane kuma addinin musulunci baya koyar da ta’addanci kuma shine ma addinin daya fara allawadi da aikata ta’addanci. domin mace ta shiga wuta saboda mage haka kuma musulmi ya shiga aljanna saboda kare.

Daga karshe ina amfani domin jajantawa al’ummar Arewacin kasar nan bisa wadan nan abubuwa da suke faruwa musamman tashin bama bamai a Borno da Yobe da kano da Gombe dukkan musulmin da suka rasa rayukansu Allah ya jikansu ya gafartamusu, kuma wadanda sukayi hasarar dukiya sanadiyar wannan al’amari Allah ya mayarmusu ninkin abin da suka rasa, kuma wadan da suke aikata wannan ta’addaci muna rokon Allah ya tona musu asiri ya wargaza nufinsu. Allah ya tabbatar da mu akan hanya ta gaskiya, ya bamu lafiya da zama lafiya a kasarmu.

Yasir Ramadan Gwale

yasirramadangwale@hotmail.com

http://yasirramadangwale.blogspot.com