Saturday, August 30, 2014

Nuhu Ribadu Ne Yafi Dacewa Ya Zama Gwamnan Adamawa - Abdullahi Dahiru


NUHU RIBADU NE YAFI DACEWA YA ZAMA GWAMNAN ADAMAWA - Abdullahi Dahiru

Anyi kira ga al'ummar jihar Adamawa da su kada kuri'arsu ga Malam Nuhu Ribadu a zaben da za ayi nan gaba a wata mai kamawa idan har Ribadu ya samu sahalewar jam'iyyarsa ta PDP. Wannan kiran ya fito ne daga bakin wani Likita kuma mai fashin baki da sharhi akan al'amuran siyasa da zamantakewa da rayuwar al'umma a Najeriya.

Dakta Abdullahi Dahiru ya bayyana Malam Nuhu Ribadu a zaman mutumin kirki mai gaskiya da tsoron Allah. Da yake karin bayani a shafinsa na facebook Dakta Dahiru ya kara da cewa Malam Nuhu Ribadu ya tsrewa sa'a wajen zama gwamnan jihar Adamawa a tsakanin abokan takararsa.

YASIR RAMADAN GWALE 
30-08-2014

Nuhu Ribadu Ya Kama Hanyar Zama Gwamnan Jihar Adamawa


NUHU RIBADU YA KAMA HANYAR ZAMA GWAMNAN ADAMAWA

Dukkan alamu sun nuna cewa takarar Malam Nuhu Ribadu ta Gwamnan jihar Adamawa na kasnshin turare d'an-goma. Masu magana sun ce juma'ar da zata yi kyau ana ganeta tun daga almurun Laraba, amma bisa abinda muke gani Juma'ar Malam Nuhu Ribadu tun kusan Asubahin laraba muka hango haskenta. Abinda suke nuna cewar Malam Ribadu na gab da zama sabon Gwamnan jihar Adamawa.

Allah muke roko ya dafawa Malam Nuhu Ribadu a wannan takara, Allah ka sa ya fidda suhe daga wuta idan ya zama Gwamna. Allah ka yi masa jagora kada ka barshi da iyawarsa.

Thursday, August 28, 2014

JIGAWA TARIN ALLAH: Fatan ALheri Ga Jigawa A Shekaru 23


JIGAWA TARIN ALLAH: FATAN ALHERI GA JIGAWA A SHEKARU 23

Zanyi amfani da wannan damar wajen taya 'yan uwanmu al'ummar jihar Jigawa murnar cika shekaru 23 da samun jiha. Ba shakka duk wani abin farin ciki da ya samu Jigawa to ya samu Kano, a shekaru 23 da Jigawa ta shafe a matsayin jiha mai cin-gashin kanta, anyi abubuwa masu yawa dan inganta rayuwar al'ummar wannan jihar, haka kuma Gwamnoni da dama sun gabata tun daga na soja har zuwa na farar Hula da suka Shugabanci al'ummar Jihar Jigawa.

Amma a bisa bayanai da abubuwa na zahiri da muka gani, jihar Jigawa bata samu cigaba ba kamar wannan lokacin da Gwamna Sule Lamido ke jan ragamar al'ummar jihar. An samu sauye-sauye masu yawa a Biranen jihar Jigawa da kauyukanta kamar yadda bayanai suke nunawa. 

Kusan tun shekarar 2009 rabona da Dutse babban birnin jihar Jigawa. Ban san yadda Dutse ta zama ba a yanzu, amma a irin bayanan da nake samu shi ne cewar an samu sauye-sauye masu yawa kwarai da gaske a ciki da wajen Dutse, anyi gine-gine na kece raini da gina manya da kananan hanyoyi da kuma gina katafaren filin sauka da tashin Jiragen Sama da sauran ayyukan cigaba.

Bayanai musamman wadan da muke samu daga wajen Malam Mansur Ahmed da kuma irin hotunan da muke gani sun nuna cewar Gwamna Sule Lamido ya ciri tuta wajen sanya Jigawa ta amsa sunanta na sabuwar Duniya. Muna taya al'ummar Jigawa murnar samun wannan cigaba mai ma'ana. 

Haka kuma, a wasu bayanai da muka karanta a kwanakin baya sun nuna cewar Jigawa na daya daga cikin jihar da ta ke da dumbin mutanen da ba su da aikin yi a Arewacin Najeriya, kuma talauci na karuwa sosai a jihar. Anan ne nake son yin Amfani da wannan damar wajen yin kira ga Gwamna Sule Lamido wanda mun san hadimin Talawa ne, ya kara zage dantse wajen taimakawa rayuwar talakawa da kuma inganta ayyukan Noma da kiwo a Jigawa da sauran fannonin da suka shafi rayuwar al'umma kai-tsaye.

Ina kuma kira da babbar Murya ga al'ummar Jihar Jigawa musamman Talakawa su sani cewar Gwamnati ba tada aikin da zata iya baiwa kowa, kuma Gwamnati ba zata iya biyan bukatun kowa ba, a dan haka dole al'umma su tashi tsaye haikan wajen ciyar da kansu gaba da kuma jiharsu. Muna musu fatan alheri, Allah ya taimaki Jihar Jigawa Ameen.

Wani abokina Malam Abdul Ahmad Burra ya fada a cikin rubutunsa cewar babban rashin da mutanan Jigawa zasu yi a 2015 shi ne na Gwamna Sule Lamido Hadimin Talakawa, muna yiwa Gwamna Lamido fatan Allah ya sa ya gama mulkinsa lafiya, kuma Allah ya baiwa 'yan Jigawa wanda yafi Gwamna Sule Lamido a 2015.

Yasir Ramadan Gwale
28-08-2014

Ta'aziyar Rasuwar Malam Magaji Danbatta

SAKON TA'AZIYAR RASUWAR MALAM MAGAJI DANBATTA

Yau na sami labarin rasuwar daya daga cikin Manyan dattawan da jihar Kano ta ke da su, kuma wanda rayuwarsa ta kare wajen hidimtawa al'ummar jihar Kano da Najeriya baki daya. Dattijo Malam Magaji Danbatta mutum ne wanda tsohuwar jihar Kano da ta hada da Jigawa ayanzu zasu jima suna tunawa da rayuwarsa kuma suna alfahari da irin gudunmawar da ya bayar a rayuwarsa dan bunkasa da cigaban wadannan jihohi.

Ba shakka, Malam Magaji Danbatta mutum ne da aka yi rashinsa sosai a tsohuwar Kano da kuma Kano ta yanzu. Malam Magaji Danbatta na daga cikin dattawa mutum shida da jhar Kano ke takama da su, kuma shime mutum na biyu cikin wadannan dattawa da ya kwanta dama. Ba jimawa muka wayi gari da rasuwar Sarkin Kano marigayi Alhaji Ado Bayero, wanda rasuwarsa ta girgiza Najeriya baki daya, kasancewarsa mutumin da ya yi tasiri matuka a rayuwar al'umma.

Malam Magaji Danbatta ya wakilci Kano a fannoni daban daban na rayuwa a Najeriya, ya kuma kasance mutumin da ake mutunawa kuma ake darajtawa a lokacin da yake raye. Akwai wani al'amari mai ban sha'awa a rayuwar Malam Magaji Danbatta, a wasu lokuta a baya ba zan iya tuna lokacin ba, amma 'ya 'yansa sun shirya wani biki da ya kayatar kwarai da gaske a Kano, inda suka taya mahaifinsu Magaji Danbatta murna cika Shekaru 50 da yin aure.

A yayin wannan biki da aka yi shi a gaban dubban jama'a Malam Magaji Danbatta ya bayyana cewar matarsa bata taba yi masa laifin da yayi Allah-wadai da ita ba, ya kara da cewar a tsawon wadannan shekaru 50 matarsa bata taba yin yaji ba, ya ce kuma kullum yana kara jin soyayyarta a cikin ransa, yayiwa 'ya 'yansa godiya a yayin wannan biki sannan kuma ya yi kira a garesu da sauran jama'a da suyi koyi da soyayya irin ta dattawa.

Muna addu'ar Allah ya jikan Malam Magaji Danbatta ya yafe masa kura-kuransa ya sa Al-jannah ce makomarsa Iyalansa kuma muna taya su al'hinin wannan rashi da suka yi. A madadina da dukkan dangi da 'yan uwa da abokai muke taya Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi Na Biyu da Gwamnan Kano Alhaji Rabiu Musa Kwankwaso da Gwamnan jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido ta'aziyar wannan rashi da muka yi Allah ya jikansa ya gafarta masa. 

Haka kuma muna mika ta'aziya ga Alhaji Dakta Aminu Alhassan Dantata da Khalifa Isyaka Rabiu da Yusufu Maitama Sule (Danmasanin Kano) da Alhaji Tanko Yakasai da suke zaman manyan dattawa a jihar Kano, Allah ya kara musu lafiya da jinkiri mai amfani.

Yasir Ramadan Gwale
28-08-2014

Wednesday, August 27, 2014

PDP da APC


PDP DA APC

Ina fatan duk wanda zai yi magana akan wannan rubutu to ya tabbata ya kai karshensa. Ina farawa da sunan Allah mai kowa mai komai. Kamar yadda na bude da harafan PDP da APC to zanyi batuna ne kacokam akansu da kuma halayenmu. Kasancewar yanzu siyasar Najeriya na tafiya ne tsakanin APC da PDP, haka kuma al'ummar Najeriya sun kasu gida biyu ko dai masu nuna goyon baya ga PDP ko kuma APC.

Ya 'yan uwa yana da kyau mu fahimci cewa ita Jam'iyyar siyasa wani dandamali ne da ake takawa a hau dan kaiwa ga dare madafun iko, dan shugabantar al'umma. A bisa tanadin kundin tsarin mulkin Najeriya, babu wani mutum da zai iya zama shugaba a kowanne mataki na wakilci ko zartarwa sai ya biyo ta kwararon jam'iyya PDP ce ko APC ko wata daban.

Sau da dama ni da kai da sauran al'umma mukan yi kuskuren fahimtar ma'anar siysar jam'iyya, da kuma kuskurewa fahimtar ma'anar ita kanta siyasa. Da dama sukan dauka tilas ne siyasa ta zama gaba tsakanin mutnan da suke jam'iyyu mabanbanta. Watakila yau da Buhari zai gayyaci Shugaban kasa su ci abincin rana tare su biyu, sai dukansu su zama abin zargi a wajen magoya bayansu.

Ya isa abin misali a ce maka Atiku Abubakar wanda jigo ne a APC, kuma yake taimaka mata ta kowanne fanni dan samun nasararta amma ace dansa na cikinsa yana auren diyar Ahmed Adamu Mu'azu wanda shi ne Shugaban jam'iyyar PDP na kasa baki daya! Jam'iyya ta bambanta su amma kuma su din sirikan juna ne, Shin wannan ba zai zama darasi na kurkusa da zamu dauka ba?

Gwamnan Bauchi Isa Yuguda yana ANPP ya auri diyar shugaban kasa marigayi Malam Umaru Musa YarAdua. Shin idan siyasar jam'iyya gaba ce Shugaban Kasa zai aurawa dan ANPP 'yarsa ta cikinsa? Haka fa Tsohon Gwamnan Zamfara Mahmuda Aliyu Shinkafi yana ANPP ya auri diyar tsohon Shugaban kasa Ibrahim Badamasi Babangida wanda jigo ne, kai kusan shi ne babban Fulogi a PDP suka zama surikan juna.

Ka koma baya kaga yadda AVM Mukhtar Mohammed yana ANPP kuma dan-gani kashenin General Buhari amma kuma matarsa da yake Aure tana PDP tana takarar Sanata, wannan kuma bai kawo komai a cikin auratayyarsu ba sai karuwar dankon zumunci da soyayya da kaunar juna. A kwara yanzu Bukola Saraki na APC kanwarsa uwa daya uba daya ita kuma tana PDP, hakan kuma bai haifar da komai a alakar dangantaka tsakaninsu ba, sai zumunci da kaunar juna.

Amma sai mu da muke na can kasa, da muka fi su iya fahimtar siyasa muke zaton cewar dolenmu mu zama abokan gabar juma matukar jam'iyyunmu sun bambanta, mu dinga jifan juna da miyagun kalmomi da munana kalamai? Ya kamata mu nutsu muyi hankali musan inda yake mana ciwo. Da PDP da APC dukkan su jam'iyyu ne da babu wadda aka gina manufofinta dan fita wa'azin maguzawa, babu wacce aka gina dan kare Addinin Musulunci ko kare muradun Musulmi.

Yana da kyau mu fahimci cewar mu da muke nunawa juna Adawa maras kyau mara kan gado saboda bambancin jam'iyya sai mu zama abin dariya a wajen wadan da muke gani su ne shugabanni idan mun gansu tare da juna a wajen taruka suna taya juna murna. Sau nawa muke ganin hotunan Buhari da Obasanjo a taruka suna musabiha suna yiwa juna dariya? Bayan kuma dukkanmu mun san cewar anyi takara tsakanin Obj da Buhari a 2003 da 2007 har aka je kotu dan kwatar hakki? Shin Obasanjo da Buhari basa kishinmu ne suke musabiha da juna a gaban kyamara?

A zaben 2011 da akayi takara tsakanin Goodluck Jonathan da Muhammadu Buhari, babu wani abu na nau'in rashin jin dadi da bai faru ba, anyiwa mutane da dama ta'adi da sunan goyon bayan wadannan mutane. Amma a bikin cikar Najeriya shekaru 100 aka nuna Shugaban kasa Jonathan yana ratayawa Buhari lambar girma a wuya dukkansu suna yiwa juna dariya, karshe kuma suka yi musabiha.

Dukkan wadannan abubuwa da suka faruwa kuma suke cigaba da faruwa ba zasu zamar mana darasi ba, sai mun dauki layin raba tsakanin junanmu? Duk wata baragada da hayagaga da mutum zai yi dan nuna goyon baya ko Adawa da sunan jam'iyya mutanan cikin jam'iyyar kuma abokan juna ne, sai yaya?!

Meye Kwankwaso bai yiwa Buhari ba a lokacin zaben 2003? Amma yau da Buhari da Kwankwaso suna cikin jam'iyya daya. Wane irin abu ne bai faru ba tsakanin Bafarawa da Wamako ba, amma sai da suka hada jam'iyya daya, kuma suka yi magana da juna. Duk wadannan jagororin siyasar muna jin mu da muke mabiya mun fisu fahimtar siyasa ne?

Yau ina Najatu Mohammed ina Buhari? Wace irin magana ce Najatu bata gayawa mutane akan Buhari ba, amma yau sun raba gari da Buhari jam'iyyarta daban jam'iyyar Buhari daban, ya kamata mu fahimci maganar da ake cewa Siyasa ba tada tabbataccen masoyi kuma bata da tabbataccen makiyi.

Ya kamata mu sani cewa idan hankali ya bata, to, hankali ne yake nemo shi. Dukkanmu fatan Allah ya bamu Shugabanni nagari muke yi, kuma kowa yasan ba Mala'iku za'a turo mana ba, kuma ba wani mutum za'a sauko mana da shi daga sama ba ya zama shugabanmu, daga cikinmu Shugaban zai fito. Tayaya muke fatan samun kyautatuwar rayuwa alhali mu bamu mutunta kanmu ba kuma bamu mutunta wadan da muke fatan nan gaba su zama Shugabanni ba?

Ya zama dole mu fahimci tsantsar gaskiya dangane da siyasar Najeriya da kuma siyasar Jam'iyyar PDP da APC. Babu wata jam'iyya da aka bude kundinta da Bisimillah. Babu kuma wata jam'iyya da ake aiwatar da manufofinta a duk jihar da take Mulki. Da gwamnatin Akwa Ibom da Gwamnatin Yobe ba suda wani bambanci wajen tafiyar da jagoranci, duk abinda Gwamna yake so shi ake aiwatarwa ko ya dace da jam'iyya ko bai dace ba, haka abin yake a ko ina a Najeriya.

Dan haka, mune zamu cigaba da kasancewa a wahale wasu na can a kwance suna amfanuwa da jahilcinmu gidadancinmu na kin fahimtar ma'anar ita kanta rayuwarmu da kuma siyasa da hamayyar siyasa.

Zamu zama Azzalumai na gaske idan jam'iyyar Siyasa ta zama ita ce ma'aunin mutanan kirki da na banza a wajenmu. Mutum yayi duk abinda yaga dama a PDP amma daga randa ya shiga APC sai a yi masa kallon shi tsarkakakke ne. Shi kenan mun zama gidadawa na karfi da yaji?

Masu mulki sai su handame, su tara, su kuntata ga son kai da wawura. Sai ma kaga wata tsana ko kiyayya ta shiga tsakanin su da al'umma. Ba tausayi ba hange ba tuna makoma ba waiwaye da daukan izina daga darassin rayuwar su ta baya ko rayuwar wani da suka sani.

Ta kowanne fanni ka dubamu babu gaskiya a lamuranmu! Kalli yadda malamai suke a yanzu, tarbiyyar su, kalmomin su, alakar su da juna. Mu dubi yadda kowa yake neman ya shahara ko a san shi, duba tsakanin su da mahukumta da masu dukiya.

Ga karanci ibada, ana wa'azi ba ikhlasi. Kowa na tsoron fadin gaskiya a zarge shi, mabiya sun zama sai abinda suke so shi Malamin zai fada, shi kuma ba zai taba fadin abinda zai saba musu ba dan kar su watse masa. Wannan ita ce ta jawo akai shiru akan matsalar Boko Haram har ta zamo ala kakai, shi'a ke ta yaduwa, ana tsoron bayyana ra'ayin siyasa don mabiya! Ila aina tazahabun?

Yan bokon mu sukayi watsi da ilimin Allah, suka kasa ciyar mana kasa gaba da nasu ilimin, suka kawo dabarun son duniya, ga annobar cin rashawa ga dukkan nau'i na cin bulus ana karya hula ana dogon turanci na gaza gani da yawan suka da iya kalubale a rubuce da kuma baki amma ba kere kere ko wani ci gaban zamani daga masanan mu. Suka jawo mana tasirin jita jita ta hanyar radio da jaridu, suka koyawa mutane zama cima zaune duk akayi watsi da sana'oin gado, kowa ya nade hannu yana san cin na banza.

Sarakuna suka manta gadon iyayen su, suka ki karatun addini, suka fi damuwa da masha'a da kade kade da bushe bushe da nadin sarautu, ana ta hawa dawakai ana bushasha, har ta kai kusan kullum Kimar su raguwa ta ke yi. Duk sarkin daya mutu na bayansa zai zo ya gazashi karbuwa, ba kwarjini, ba wani girma na darajar mulki.

Al'umma kuma ta zabi zaman kara zube da gadi da son kai da kan-jiki. Maula da kwadayi da tumasanci ya zama babba da yaro, roko ya zamo maza da mata ba sai wadanda suka gada ba. Rashin ilimi ya jawo ana addini da rayuwa da ka. Kowa yana da ta cewa a addini, wanda ya san addini da wanda bai sani ba.

Gamu da rashin bin doka da sabawa ka'ida ta addini da ta hukuma. Rashin tarbiyyar addini tasa kowa ba wanda yake rusunawa sai mai bashi. Rayuwa ta koma kowa a fusace kamar ana filin daga, bamu dana gaba don malunta ko mulki wadda keda tasirin yasa ko ya hana mu. Aka daina yiwa juna zaton alheri, kowa sai ka bi nasa ya gode maka. Wallahi duk wannan jahilncin addini ne ya samu ciki. Dubi yadda ake sanar da ganin wata dubbai suyi tawaye amma ji yadda aka yada labarin wanka da gishiri don maganin ebola gida kadan ne ba suyi ba.

Duk wadannan abubuwa da ke faruwa ba zasu zama izna a garemu ba? Sai mu koma jifan juna da miyagun kalmomi da kazafi da karairayi kawai saboda bambancin ra'ayin siyasar jam'iyya! Wace irin al'umma ce mu? Allah ka nuna mana gaskiya mu fahimci gaskiya ce ka bamu ikon binta ka nuna mana karya mu fahimceta ka bamu ikon kauce mata.

YASIR RAMADAN GWALE
25-08-2014

Sunday, August 24, 2014

Shugaba Goodluck Jonathan


SHUGABAN KASA GOODLUCK JONATHAN

Shugaban Kasa Dr. Goodluck Jonathan shugaba ne da wata rana zamu tuna shi ta fuskar hakuri da juriya da kuma rauninsa da muke cin moriya a Arewa da Najeriya baki daya. Idan muka yi nazarin yadda karfin mulki na zamani yake tafiya ba'a taba samun shugaba a Najeriya mai juriyar hakuri da sallamawa bangarorin kasa irin Jonathan ba.

Babbar matsalar sa itace Najeriya ta yiwa kwakwalwarsa yawa, kuma bashi da kwarewar tafiyar da mulki sosai, sannan yana da sakaci kan tsaro, da bada damar a hukunta masu laifi. Haka kuma,  wadan da ke kewaye dashi sun fishi wayewa da sanin Shugabanci dan haka suka karkata mulkin kasar zuwa ga bukatar su.

Da zan baiwa Shugaban kasa Shawara da sai nace kada ya tsaya zabe a 2015, ya marawa dan Arewa baya a zaben da yake tafe, amman ya tabbatar Mulki bai kufcewa PDP ba.

YASIR RAMADAN GWALE
24-08-2014

ADAMAWA: Takarar Nuhu Ribadu Na Kara Samun Tagomashi


ADAMAWA: TAKARAR NUHU RIBADU NA KARA SAMUN TAGOMASHI

A jiya asabar ne a Yola babban birnin jihar Adamawa aka busa kusumburwar yakin neman zaben Malam Nuhu Ribadu a matsayin dan takarar gwamnan jihar karkashin jam'iyyar PDP mai alamar lema. Tun da sanyi safiyar asabar din ne dubun-dubatar matasa suka yi fitar farin dango zuwa tashar jirgin saman jihar Adamawa domin marabtar bakon da ake tsumai. Bayan da matasa suka sarraha aka yi wokokin tsuma zukata da nuna biyayya da goyon bayan takarar Malam Nuhu Ribadu ne, can bayan zawali bakon ya sauka.

Gurin ya barke da sowwa da murna yayin da matasa suka yi adabo da Malam Nuhu Ribadu. Ribadu ya fito daga cikin jirgi sanye da fararen kaya, dinkin babbar riga da jamfa da hula zanna mai launin fari da ruwan omo da ratsin ja da baki. Cikin farin ciki da annashuwa Malam Nuhu Ribadu ya kasa rufe bakinsa dan nuna gamsuwa da abinda ya gani na soyayya da kauna da dubban mutane suka nuna masa, nan ya dinga daga hannu yana gaishesu yana musu addu'ar Allah ya muku albarka, tare da maimaita Alhamdulillah, yana mai cike da sakankancewa da al'amarin ubangiji.

Daga nan ne tawagar Malam Nuhu Ribadu tayi jerin gwano zuwa wajen da aka shirya shi musamman dan zuwan Bakon Alkhairi, kuma Gwamna Mai Jiran Gado ISA. Bayan isar tawagar ne kuma shi mai gayya mai aiki Malam Nuhu Ribadu ya jagoranci bude katafariyar sakatariyar yakin neman zabensa da aka samar.

Malam Nuhu Ribadu yayi kalamai masu ratsa zukata da mika lamuransa ga Allah a yayin wannan taro, ya kuma yi kira ga al'ummar jiharsa da ya jima yana nuna musu kauna da cewa su kasance masu da'a da biyayya da kuma sanya Allah a cikin dukkan al'amuransu, ya kuma yi addu'ar Allah ya dafawa wannan takara da al'umma suka nuna sha'awarsu akai.

Yasir Ramadan Gwale
24-08-2014

Thursday, August 21, 2014

Malam Nuhu Ribadu 2014


NUHU RIBADU 2014: Ofishin yakin neman zaben Malam Nuhu Ribadu a matsayin dan takarar Gwamnan jihar Adamawa ya dauki harami da tutoci masu launin Ja da Fari da Kore, inda suke kadawa hagu da dama cikin sassanyar iskar damina. Ga Allah muka dogara, shi ne mai bayar da mulki ga wanda yaso. Malam Nuhu Ribadu For Adamawa State Governor Allah ya amince.

YASIR RAMADAN GWALE
21-08-2014

Wednesday, August 20, 2014

ADAMAWA: Malam Nuhu Ribadu Ya Shiga Takara Gadan-Gadan


ADAMAWA: MALAM NUHU RIBADU YA SHIGA TAKARA GADAN-GDAN

Malam Nuhu Ribadu ya fanshi tarkadun tsayawa takarar Gwamnan jihar Adamawa a karkashin jam'iyyar PDP mai alamar lema. Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah madaukakin sarki da ya albarlaci Malam Nuhu Ribadu da tsayawa wannan takara, domin bayar da tasa gudunmawar dan cigaban al'ummarsa, dan samar musu da ingantacciyar rayuwa, dan inganta ilimi da kiwon lafiya da sufuri, dan taimakon addinin Allah. Wannan takara ga Allah Malam Nuhu Ribadu yake nema, yabiyo hanya kamar yadda ta halatta ga duk mai neman takara ya gabatar da bukatarsa a karon farko ga jam'iyya, idan Allah ya kaddara cewa shi ne dan takara a bazama wajen jama'a dan neman goyon bayansu.

Malam Nuhu Ribadu ba attajiri bane, bai tara abin duniya dan baiwa mutane dan abin hasafi su zabe shi ba, yana fatan jama'a su tsarkake zukatansu, su duba cancantarsa wajen wannan aiki. Ba shakka mun shaida cewa Ribadu ya cancanci rike duk wani mukami a fadin tarayyar Najeriya.

Gaskiya da rikon amana irin ta Malam Nuhu Ribadu ta bayyana tun bayan da ya zama mataimakin kwamashinan 'yansanda, inda daga nan yaci gaba zuwa Shugaban hukumar EFCC da al'ummar Najeriya da sauran duniya suka shaida kwazonta. A saboda kwazo da aiki da gaskiya ta sanya har aka yiwa Ribadu tsallaken mukami a aikin dan sanda. Allah ya tabbatar da alheri a wannan takara. Zabin Allah shi ne zabi, muna yiwa mutanan Adamawa fatan samun Malam Nuhu Ribadu For Adamawa State Governor 2014.

Ya Allah kayi riko da hannun Malam Nuhu Ribadu idan ya zama Gwamna, Allah kada ka barshi da iyawarsa, Allah ka zama gatansa. Gareka muke nema Lam Yalid Wa Lam Yu Lad.

YASIR RAMADAN GWALE
20-08-2014

Sunday, August 17, 2014

Malam Nuhu Ribadu!

Nuhu Ribadu yana gaisawa da Atiku Abubakar
MALAM NUHU RIBADU: Sunan Malam Nuhu Ribadu ya fara bayyana ne ga mafiya yawancin al'ummar Najeriya a lokacin da ya jagoranci hukumar EFCC mai yaki da zamba da almundahana ga dukiyar kasa. Malam Nuhu Ribadu yayi aiki bil-hakki da gaskiya wajen dawo da martabar sunan Najeriya da ya zube a idon duniya, wajen ganin ba'a cigaba da kwasar dukiyar talakawa ba. Ribadu yayi aikin da babu wani mahaluki da yayi a lokacinsa, ya kama tare da tuhumar mutanan da ake zarginsu da azurta kansu da dukiyar Haram, ya dawowa da gwamnati da dumbin dukiyar da aka diba ba bisa ka'ida ba.

A saboda aiki tsakani da Allah babu sani babu sabo da Malam Nuhu Ribadu yayi a lokacin da yake shugabantar EFCC ya sanya Transparency International suka fara mutunta sunan Najeriya a fannin yaki da cin-hanci da rashawa. Mutane a ciki da wajen Najeriya sun yabawa Malam Nuhu Ribadu a bisa irin yadda ya rike gaskiya a aikinsa duk da barazanar da aka dinga yi masa da bashi toshiyar baki amma ya kekasa kasa.

A dalilin kwazonsa da jajircewarsa ta sanya Majalisar dinkin duniya ta daukeshi aikin binciken badakalar rubda-ciki da dukiyar al'umma dake zargi a kasar Afghanistan, ya kuma nuna hazaka a lokacin da yayi aikin. Daga nan likkafar Malam Riabdu ta dinga cigaba, har ta kai ga rusashshiyar jam'iyyar ACN ta Yarabawa suka nemeshi da ya zo yayi takarar Shugaban kasa a karkashin jam'iyyar dan samar da sabuwar Najeriya.
Duba da kwarewa da gogewa irin ta Malam Nuhu Ribadu ya sanya gwamnatin Shugaban kasa Goodluck Jonathan ta nada shi a matsayin wanda zai shugabanci kwamitin Petroleum Revenue Special Task Force dan sanya ido da bayar da shaida akan kudin rarar Man-fetur, ya kuma kammala aikinsa cikin nasara, yayin da al'ummar kasarnan suka yabawa Rahaton Kwamitinsa.

A 'yan makwannin da suka wuce, Malam Nuhu Ribadu ya samu kansa a cikin wani yanayi da za'a iya cewa Allah ne ya nunawa al'umma gaskiyarsa, inda jam'iyyun APC da PDP suka dinga zawarcinsa akan yayiwa Allah ya yi musu takarar Gwamnan jihar Adamawa a zaben cike gurbin da za'ayi nan gaba a Oktoba mai zuwa. Kungiyoyin matasa da yawa daga jihar Adamawa suka dinga kira ga Malam Nuhu Ribadu da ya yi musu takarar Gwamnan jihar karkashin jam'iyyar PDP duk kuwa da cewar shi yana jam'iyyar APC mai hamayya.

A dalilin wannan kiraye-kiraye ne Malam Nuhu Ribadu a jiya ya yanke hukunci na karshe, inda ya amince da shiga jam'iyyar PDP domin bayar da tasa gudunmawar kamar yadda ya saba dan samar da sabuwar Najeriya mai mutunci da kima. Ana sa ran cewa Malam Nuhu Ribadu zai zama dan-takarar Gwamna na PDP a Adamawa. Na yi imanin cewar Malam Nuhu Ribadu zai iya yin dukkan aikin da aka bashi dan hidimtawa al'umma tsakaninsa da Allah. Kamar yadda ya sha nanatawa cewar a shirye yake ya taimakawa kasarsa a kowanne irin mataki idan ambukace shi.

Muna yi masa fatan alheri. Ina kuma amfani da wannan damar na yi kira a gareshi da ya kasance mutum mai gaskiya da rikon Amana kamar yadda aka sanshi, kuma yaji tsoron Allah wajen alkinta dukiyar al'umma a duk inda ya samu aikin hidimtawa al'umma. Allah ya taimaki Najeriya ya bamu Shugabanni na gari Adalai masu rikon Amana. 

Yasir Ramadan Gwale
17-08-2014

PDP Ta Samu K'aruwar Malam Nuhu Ribadu

PDP TA SAMU KARUWAR MALAM NUHU RIBADU

A yau Allah ya kaddari tsohon shugaban hukumar da take yaki da yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati, kuma tsohon dan takarar Shugaban kasa a rusashshiyar jam'iyyar ACN Malam Nuhu Ribadu ya tsallaka jam'iyyar PDP daga APC. Wannan shigar ta Malam Ribadu dai ta biyo bayan zawarcinsa da tsohon abokinsa kuma Shugaban jam'iyyar PDP na kasa Alhaji Ahmed Adamu Muazu yayi, da kuma kokarin da fadar shugaban kasa ta yi na ganin Ribadu din ya tsallako PDP dan ya yi takarar Gwamna a zaben cike gurbi da za ai. Shigar Malam Ribadu dai zata kawo sauye-sauye da yawa a cikin PDP ta jihar Adamawa a cewar masharhanta.

Ya zuwa yanzu dai jiga-jigai daga cikin APC da suka hada da tsohon gwamnan Kano kuma Sardaunan Kano Malam Ibrahim Shekarau da tsohon gwamnan Sokoto Alhaji Attahiru Bafarawa da tsohon madugun APC a yankin Arewa maso gabas Alhaji Ali Modu Sheriff duk sun shiga PDP daga APC abin da yake nuna kara karfin PDP tare da zahwanyar da APC da ke zaman babbar jam'iyyar hamayya.

YASIR RAMADAN GWALE
17-08-2014

Saturday, August 16, 2014

Shari'ar Musulunci A Hannun 'Yan Daba

SHARI'AR MUSULUNCI A HANNUN 'YAN DABA (K'AURAYE)!

Kusan yanzu Allah ya kawo mu wani lokaci da 'yan daba (Kauraye) 'yan ta'adda suke daukan makamai suna Allahu Akbar wai su zasu kafa Shari'ar Musulunci. Wannan al'amari haka yake faruwa a Iraqi da Nigeria da Mali da Somaliya da Yaman da sauran kasashe da dama, wasu tunzurarrun matasa suna dauke da muggan makamai akan motoci wani zubin suna busa taba sigari wai su ne zasu kafa kasar Musulunci su yi Shari'ah.

Sai kayi ta mamaki idan kaga fuskokin mutanen da ke ikirarin su ne zasu kafa Shari'ah a Iraqi ko Najeriya ko Mali, ba su da wata kamala da ta ke nuna su din suna da ilimin addinin da zasu jagoranci al'ummah har su tsaida musu da Shari'ah. Ta inda zaka fahimci dukkan wadannan masu wannan ikirari tantagaryar makaryata ne, shi ne wane Musulunci suke bi da ya yi umarni da kisan mutanan da basusan hawa ba balle sauka? mutane suna zaman zamansu azo a tayar musu da abubuwan fashewa wasu su mutu wasu namansu yai daidai, wasu su karairaye haka kurum, kuma wadannan tsagerun su dinga ikirarin wai Shari'ar Musulunci suke son tabbatarwa!

Ya zama wajibi jama'a su fadaka su san cewar, wadannan mutane da suke dauke da bakaken tutoci da rubutun La Ila Ha Ilallah, karya suke yi ba Musulunci suke ba, kuma babu abinda ya hada su da kafa Shari'ar Islama. Sau da dama ana yaudarar mutane musamman masu kishin addini har su dinga kallon irin wadannan matasa amatsayin masu kishin addini ko Jihadi, wanda a zahiri manufofinsu sunci karo da na Musulunci.

Tayaya mutanan da basu da wani Ilimin Addini basu ma san addinin ba, basu da wani iko na shugabanci, ba malamai ba, tantagaryar jahilai su dauki makamai suna Allahu Akbar wai zasu yi Shari'ah har mutane su dinga ganinsu a matsayin masu kare addini, a fahimtata dukkansu ba gaskiya ba ne a cikin al'amarinsu, kungiyoyi irinsu Al-Qa'ida da Al-Shabab da Tuareg da ISIS da Boko Haram da sauran irinsu, dukkansu babu wani alkhairi da sukajawowa Musulunci illa bakin suna a wajen wadan da ba Musulmi ba. Hanyarsu daban, ta Musulunci daban, domin dukkansu sunfi kama da 'yan daba ko kauraye akan ka kirasu da masu Jihadi ko kishin Musulunci, siffofinsu da ayyukansu sunfi kama da na Khawarij. 

Babu shakka batattu ne, suna kan bata da tabewa mai girma, idan har da gaske Musulunci suke kishi dole su koma makaranta su koyi ilimin addinin su sanshi a wajen Malamai na gari masu tsoron Allah. Addinin Musulunci ba addini ba ne na tashin hankali ko jefa rayuwar mutane cikin garari. Kuma ta ina mutumin da ba shugaba ba zai tsayar da Shari'ah akan mutane?

Inda zaka fahimci wadannan 'yan daba bakinsu daya duk inda suke, shi ne ka duba irin Tutar Al-Qa'ida ita Boko Haram a Najeriya da ISIS a Iraqi da Alshabab a Somaliya da mutanen Mali suke amfani da ita. Ko kusa wadannan mutane ba suda alaka da Musulunci ko ta kusa ko ta nesa da irin abinda suke yi na kisan gilla ga al'umma. Ta yaya zasu dinga kashe mutanan da suke son tabbatarwa da Shari'ah, misalia Najeriya Boko Haram na ikirarin aiwatar da Shari'ar Musulunci amma kuma zasu dinga kashe Musulmai? Shin haka Musulunci ya fada daman ko kuwa nasu addinin ne ya yiumarni da zubarda jinin bayin Allah? 

Wadannan mutane Allah ya sansu kuma yasan nufinsu ba na alheri ba ne, Ya Allah ka tsaremu daga sharrin wadannan 'yan daba 'yan ta'adda marasa tsoron azabarka. Allah ka taimaki Musulmi na hakika ba masu batasunan Musulunci ba.

YASIR RAMADAN GWALE
15-08-2014

Thursday, August 14, 2014

Malam Nuhu Ribadu Na Gab Da Subucewa APC


MALAM NUHU RIBADU NA GAB DA SUBUCEWA APC

* APC na matsa lamba ga Ribadu kada ya fita.
* PDP ta tabbatarwa da Ribadu takarar Gwamna
* Fadar Shugaban kasa tayi alkawarin bashi goyon baya

Jaridar The Nation Newspaper ta ruwaito cewar, shugabancin jam'iyyar Hamayya ta APC na yin dukkan mai yuwuwa wajen ganin tsohon dantakarar Shugaban kasa a rusashshiyar jam'iyyar ACN, kuma jigo a cikin jam'iyyar APC, tsohon shugaban hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati Malam Nuhu Ribadu bai sauya sheka zuwa PDP ba.

Wata majiya mai tushe ta tabbatar da cewar tuni Malam Nuhu Ribadu ya gama dukkan shirye-shiryen tsallakawa PDP daga APC, wasu masharhanta na cewar daman can zaman doya da manja ake yi tsakanin Ribadu da shugabancin jam'iyyar APC. 

Haka kuma, akwai alamun da suke nuna cewa daga yau Alhamis zuwa gobe juma'a ake sa ran Malam Nuhu Ribadu zai bayyana sauya shekarsa daga APC zuwa PDP inda ake sa ran zai yi takarar Gwamna a zaben da za'ai na cike gurbin Murtala Nyako a Oktoban nan mai zuwa.

Bayan wannan sanarwa ne kuma ake sa ran Malam Nuhu Ribadu da tawagar yakin neman zabensa da masu yi masa fatan alheri zasu gudanar da wani kwarya-kwaryar gangami a Yola babban birnin jihar Adamawa.
Sannan kuma, a nasu bangaren shugabannin jam'iyyar APC sunyi wani zama na gaggawa da shi Malama Nuhu Ribadu domin rarrashinsa akan ya yiwa Allah ya ajiye batun komawa PDP da yake shirin yi acewarsu hakan wani komabaya ne ga jam'iyar.

Wata majiyar kuma ta tabbatarwa da The Nation cewar shugabancin jam'iyyar PDP reshen jihar Adamawa ya nuna cikakken goyon bayansa ga takarar Malam Nuhu Ribadu a PDP din duk kuwa da wasu rahotanni da ke nuna cewa masu hankoron yin takarar a PDP na kokarin yiwa Malam Nuhu Ribadu fancale a yunkurinsa na shigowa PDP din, a yayin da Manyan masu ruwa da tsaki karkashin jagorancin tsohon Gwamna Boni Haruna suka nuna amincewa da Ridabu a matsayin sabon dan PDP kuma dantakarar Gwamna.

Itama a nata bangaren fadar shugaban kasa tuni ta nuna farinciki da amsa kiraye-kirayen da aka yiwa Malam Nuhu Ribadu na yin takarar karkashin PDP, sun kuma nuna baiwa Ribadu dukkan goyon bayan da ya dace wajen ganin ya samu nasarar zama Gwamnan Adamawa a zaben da za'a yi nan gaba.

Yasir Ramadan Gwale
14-08-2014

Tuesday, August 12, 2014

Azumin Sitta Shawwal


AZUMIN SITTA SHAWWAL

Manzon Allah SAW yace ku tunasar domin tunasarwa tana amfanar Muminai. Ina amfani da wannan damar wajen tunasar da kaina da sauran 'yan uwa cewa yau Talata 17 ga watan Shawwal. Kamar yadda Malamai suka sha yin bayanin Azumin Sitta Shawwal da irin falalarsa, lallai wadan da basu samu damar yn wannan azumi ba su daure su azumici kwanaki shidda kafin shudewar wannan wata nan da makwanni biyu masu zuwa. Allah ya sa mu dace da babban rabo, ya kuma sanya ibadun da muka gabatar a Ramadan karbabbu ne, ya inganta cewa Sahabbai sukan yawaita maimaita addu'ar Allahumma Taqabbal Minna (Allah ya karbi Ibadunmu) bayan shudewar kwanakin Ramadan. Allah ya yaye mana dukkan masifu da bala'o'in da suke damun mu.

A 'yan kwanakin nan rahotanni sunce 'yan Ta'adda sun shiga garin Gwoza a Borno inda suke yunkurin kafa iko a wajen, muna addu'ar Allah ya kawo mana dauki a cikin wannan al'amari. Ba shakka an aikata dukkan dangin ta'addanci da rashin Imani a jihar Borno da kewayenta, muna add'ar wadan da suka rasu Allah ya jikansu ya gafarta musu, marasa lafiya kuma Allah ya jikansu.

Muna rokon Allah ya arzurtamu da alkhairan duniya da lahira. Shugabanninmu Allah ya sanya tausayin al'umma a zukatansu. Allah ya shiryemu shiriya ta gaskiya.

YASIR RAMADAN GWALE
12-08-2014

RECEF TAYYIB ERDOGAN: Tafiya Da Gwani Mai Dadi

Recef Tayyib Erdogan

RECEF TAYYIB ERDOGAN TAFIYA DA GWANI MAI DADI

Priaminstan kasar Turkiyya Malam Recef Tayyib Erdogan ya zama abin misali a idan shugabannin kasashen duniya. Kusan yanzu alamu na nuna cewa babu wani Shugaba da yakai Erdogan tasiri da samun karuwar farin jini a tsakanin al'ummarsa, tun bayan da ya zama Firaminista shekaru 10 da suka gabata kullum farin jininsa da haibarsa karuwa ta ke yi a idon jama'ar kasar, inda a koda yaushe yake baiwa 'yan Adawa ruwa.

Erdogan dai mutum ne mai ra'ayin addini da sauyawa al'umma tunani daga duniyanci zuwa rayuwar da ta dace da koyarwar addini da kuma zamananci. Misali na kurkusa zaka iya cewa Gwamnatin Erdogan irin ta ce kungiyar Muslimbrotherhood a Masar ta yi kokarin samarwa, koma ka ce dungurungum Gwamnatin Erdogan ita ce irin gwamnatin da MB suke da tsarin aiwatarwa, ba shakka Shugaba Mursi ya so aiwatar da gwamnati irin wadda ake yi a kasar Turkiyya, sai dai al'amarin Mursi ya gamu da garaje da gaggawa inda aka tunzura al'umma dan yiwa yunkurin Mursi kafar ungulu, wanda hakan ya yi sanadiyar tuntsurwar gwamnatin Mursi din harma ta kai shi zuwa gidan kaso.

A gwamnatin da Erdogan ya aiwatar a Turkiyya ya cimma nasarori da daman gaske, da suka shafi harkar ilimi da kiwon lafiya da sufuri da kimiyya da kere-kere da kuma kyautatawa al'umma da inganta alaka tsakaninsa da kasashen Musulmi da kuma kasashen Larabawa da na turawa, kasancewar Turkiyya ita ce kasar da ta hada Gabashi da Yammacin duniya. Erdogan Ya cimma dumbin Nasarori wajen inganta rayuwar al'ummarsa a shekaru goma (10) da ya shafe a matsayin Piraminista, haka kuma, dubban mutane ne suka samu aikin yi a fadin kasar.

Tattalin arzikin kasar Turkiyya ya bunkasa sosai a wadannan shekaru goma sama da na kasashen da suke da arzikin mai a gabas ta tsakiya. Haka kuma, turka-turkar karyewar tattalin arziki da manyan kasashen duniya suka fuskanta (Meltdown) a 'yan shekarun da suka gabata, Allah ya tsallakar da kasar Turkiyya bata fada cikin matsalar tattalin arziki ba.

Bayan da Tayyib Erdogan ya gama wa'adin mulki na Shekaru goma, yanzu al'ummar kasar sun sake zabensa a matsayin sabon Shugaban kasa a wannan karon, wato kamar abinda ya faru a Rasha kenan, inda Vladimir Putin ya gama wa'adin Shekaru 10 a matsayin Piraminista, aka kuma zabarsa a matsayin Shugaban kasa, sai dai a Russia Putin ya sanya Piraministansa Medvedev a aljihu sai yadda yaga dama ake tafiyar da kasar inda ya karawa kansa iko fiye da na Piraminsta.

A Turkiyya muna fatan Allah ya yiwa sabon Shugaban kasa Erdogan jagoranci ya cigaba da baiwa mara da kunya, ya fidda suhe daga wuta. Ba shakka Erdogan ya zama wata katuwar fitila da zata haskawa Shugabanni da masu san darewa Shugabanci hanyar da zasu cimma muradunsu ba tare da zubewar haiba da yakanarsu ba. Allah ya azurtamu da Shugabanni na gari Adalai irinsu Erdogan.

Yasir Ramadan Gwale
11-08-2014

Sunday, August 10, 2014

OSUN: PDP Ta Yi Nasara, RAUF Kuma Ya Ci Zabe


OSUN: PDP TA YI NASARA, ROUF KUMA YACI ZABE

Dazu Abubakar Aminu Ibrahim yake gayamin cewar sakamakon zaben jihar Osun ya fito inda PDP ta samu Nasara fiye da wadda ta samu a baya, yayin da Gwamna mai ci ya sake komawa. Ina amfani da wannan damar na taya Malama Zainab (Yazain) murnar Nasarar da jam'iyyarsu ta samu a jihar Osun, ina kuma taya USTAZ RAUF AREGBESOLA murnar samun wannan nasara da yayi.

Babu shakka nauyi ya kuma hawa kansa (Aregbesola) bayan wanda ya d'auka shekaru hudu da suka gabata, yanzu ma an sake bashi amanar al'ummar jiharsa ta Osun. Muna kira a gareshi da yaji tsoron Allah wajen alkinta dukiyar al'ummar da yake shugabanta, ya kuma sani cewar zai zama abin tambaya ranar Alkiyama akan Amanar da aka danka masa ta Mulkin Jama'a.

Muna fatan Allah ya yi riko da hannunsa wajen aikata daidai, haka kuma muna kira a gareshi ya yi kokari wajen yaki da cin-hanci da rashawa, ya kuma yi iyakar iyawarsa wajen inganta rayuwar al'umma. Ina masa fatan alheri da fatan gamawa lafiya. Shi kuma dan takarar PDP da bai samu zabe ba Allah ya bashi dangana, ya kuma tsananta masa rabo a nan gaba. Wassalamu Alaikum Warahmatullah.

YASIR RAMADAN GWALE
10-08-2014

Saturday, August 9, 2014

Ebola


EBOLA: Ance sunan Ebola asali ya samo wannan sunan ne daga wani kududdufi mai dauda cike da dagwalo a kasar kwango. Wannan cuta da bincike ya tabbatar da cewa mutanen farko da suka kamu da ita, sun sameta ne sakamakon cin naman dajin da akayi farautarsa irin su Beran dinka da Damo da gafiyoyi da jemage da sauran dangin haiwanat irin wadannan. Haka kuma likitoci sun tabbatar da cewa wanna cuta na da saurin yaduwa da kuma halaka jama'a nan take.

Wannan cuta ta bulla ne a karon farko a shekarar 1976 a kasar Sudan ta kaudu ta yanzu, a wancan lokacin kusan mutum 284 suka rasu sakamakon kamuwa da wannan cuta. Sannan a karo na biyu wannan cuta ta kuma bulla a kauyen Yambuku a Zaire kasar Kwango inda mutane kusan 318 suka harbu da ita, da damansu suka margaya sakamakon wanan cuta.

Karona hudu da wannan cuta ta bulla, ita ce a jihar Virginia ta kasar Amurka, wanda bayanai suka nuna cewa ta bulla ne a sakamakon cin namu wasu birre da aka shiga da su garin daga yankin nan mai fama da yamutsi na Mindanao a kasar Filifins a cikin shekarar 1989. Wanda mutane kalilan ne suka harbu da wannan cuta.

Haka kuma, karo na karshe da aka ji labarin bullar wannan cuta shi ne lokacin da wata Likitiya a kasar Kwadebuwa take duba lafiyar wani biri, bayanai sun tabbatar da cewar birin da Likitiyar ta duba yana dauke da cutar, nan ta ke kuma matar ta harbu da cutar a cikin shekarar 1994.

Daga nan kuma sai a ranar 6 ga watan Augutan wannan shekarar aka samu labarin bullar wannan cuta a kasashen Gini da Laberiya da Saliyo, ance cutar ta sake bulla ne sakamakon cin naman dabbobin da aka yi farautarsu a wadannan kasashe. Tuni dai wannan cuta ta aika da sama da mutu 700 lahira a dalilin harbuwa da suka yi da ita.

Bayanai na likitoci sun tabbatar da cewa wannan cuta na da saurin yaduwa da kuma saurin halaka mutane kamar yadda kullum ake bayani a Talabijin da Radiyo da jaridu. Haka kuma, wasu bayanai sun nuna cewar bayaga cin naman dabbobin da aka ambata ko yin cudanya da mai cutar, ana kuma iya harbuwa da ita ta sanadiyar cin 'ya 'yan itatuwan da Birbiri ya fara gatsa su a bishiyarsu.

Kamar yadda dukkanmu muka sani, tuni wannan cuta ta bulla a Najeriya, kuma ana ta daukan matakan kariya tare da kira ga jama'a da su tabbatar da tsaftar abincinsu da abin shansu da kuma gurin kwanansu. Haka kuma bin ka'idojin da hukumomin lafiya suka gindaya zasu zama garkuwa ga wannan annoba. Wadan da suka kamu da wannan cuta Allah ya basu lafiya, wadan da kuma suka mutu Allah ya jikansu, mu kuma Allah ya karemu da karewarsa.

DISCLAIMER: A cikin hadisi na 625 a cikin Sahihul Bukhari, Manzon Allah SAW ya ce idan annoba ta barke, kada wani da yake dauke da wannan cuta ya fita zuwa garin da basu da ita, kada kuma wanda yake zaune a inda annobar ta barke ya fita daga inda yake dan gudun kamuwa da ita. Riko tare dayin amfani da bayanan kariya da likitoci suka bayar zasu tairigakafin wannan cuta. Kuma jama'a su yawaita rokon Allah akan neman tsari daga wannan annoba.

YASIR RAMADAN GWALE
09-08-2014

Al-jana A Kano

ALJANA A KANO: A can wani shudadden lokaci a Kano anyi wata Aljana da ta addabi mutane a Kano ta razana al'umma sosai amma kuma babu wanda ya taba ganin wannan aljanar, ita dai wannan aljana ina zaton sunanta 'yar Madabo, amma ance zuwa gidan mutane ta ke yi ta ce musu su bata ruwa ta sha, indai aka bata ruwan to da ta sha zata watsar da ragowar a gidan shi kenan mutan gidan zasu mutu, a yadda labarin ya yadu a lokacin kenan, a wannan lokacin rigakafin wannan aljana shi ne a barbade kofar gida da toka, ance indai Aljanar ta zo kofar gidan taga Toka ba shakka ba zata shiga ba. Ina iya tuna lokacin da su Ali Aliyyu Gwale suka dinga fito da murhu daga cikin gidansu suna barbade kofar gidan da toka, mu kuma muna zaune a makarantar Allo a lokacin. Sau da dama tarihi kan maimaita kansa a wasu siffofi ko kamanni mabanbanta. Nima naga alamun zamu yi maza-maza ni da Zainab mu saro gishiri dan muci zamar Ebola. Allah ya karemu daga Aljana Ibola.

YASIR RAMADAN GWALE
08-08-2014

Wednesday, August 6, 2014

NETANYAHU: Yaki Ya Kare A Yankin Zirin Ghazza

Netanyahu

NETANYAHU: YAKI YA KARE A YANKIN ZIRIN GHAZZA

Shugaban haramtacciyar kasar Israela Benjamin Netanyahu - בנימין נתניהו a ganawar da yayi da manema labarai dazu-dazun nan, ya shaidawa duniya cewar yakin zalinci da suka shafe kwanaki 29 suna aiwatarwa akan al'ummar Ghazza ya zo karshe, hakan dai na zuwa ne tun bayan amincewar da Bangaren Palasinawa na Hamas da kuma ita Israelan suka yi na tsagaita wuta na awanni 72. A yayin da yake wannan ganawa da Manema labarai, Netanyahun ya nuna musu wani hoton Video dake nuna WAI irin hare-haren roka da hamas suka kai Israelar wanda hakan yayi sanadiyar mutuwar Yahudawa 64.

Sai dai a cikin jawaban nasa, Netanyahu ya nuna cewar sun tafka kusakurai da dama wajen wannan yaki inda yace sun kai hare-haren da suka yi sanadiyar mutuwar fareren hula da yawa, ya kara da cewar babu yadda zasu yi dole ce ta sanyasu kai wannan hare-haren a cewarsa suna yi ne dan kare al'ummar kasarsu ta Yahudawa, ya kara da cewa Hamas sun fake da farerenn hula ne dan samun kariya. Haka kuma Netanyahu ya kwatanta kungiyar Hamas da kungiyoyi irinsu Boko Haram da Hizbola da kuma ISIS.

A wannan yaki da aka yi kimanin mutane 2000 ne Israela ta kashe a yankunan zirin Ghazza wadan da galibinsu yara ne da mata da tsaffi, sanna kuma hare-haren da Israelar ta kai sun raunata sama da mutum 10000, haka kuma sama da 100,000 sun tsere daga gidajensu da samun mafaka, bayaga dubban gidaje da aka rurrusa a unguwanni da dama na yankunan Palasdinawa a yankin zirin Ghazza, hari mafi muni shi ne wanda aka kai a unguwar Shejaiyah wanda dubban kananan yara suka rasa rayukansu, haka kuma mata da dama sun rasu a wannan unguwa, haka abin yake a unguwannin Bait-Hanun da Khan-Yunis inda dubban gidaje da Masallatai da makarantu suka kasance a rurrushe.

Sai dai a nasu bagnaren kasar Amerika bayan goyon baya da suka bawa kasar Israela a wannan yakin tare da nuna cewa Israela na da ikon kare kanta da kuma nuna cewar Hamas kungiya ceta yan ta'adda, Amerika din ta bayar da sanarwar tallafin Dala Miliyan 49 dan sake gina yankunan Palsdinawa da yaki ya daidaita a yankunan zirin Ghazza.

Tuni dai daman aka soma wata tattaunawa a birnin Alkahiran kasar masar ranar Asabar tsakanin bangarorin Palasdinawa da Isrela karkashin sa-idon Majalisar dinkin duniya da kuma gwamnatin Masar. Fatanmu shi ne Allah ya taimaki Palasdinawa mazauna Ghazza ya kara musu karfin Imani, ya dora su akan abokan gabarsu Yahudawa a koda yaushe. Ya Allah kada ka kuma maimaita musu irin wannan mummunan zubar da jini. Allah ka taimaki kasashen Musulmi.

YASIR RAMADAN GWALE
06-08-2014

Tuesday, August 5, 2014

GHAZZA: Abin Boye Yana Fitowa Fili A Burtaniya

Lady Warsi tare da David Cameron

GHAZZA: ABIN BOYE YANA FITOWA FILI A BURTANIYA

Babbar Ma'aikaciya a ofishin da ke kula da harkokin wajen kasar Burtaniya Malama Lady Warsi ta ajiye mukaminta na Minista a sakamakon yadda taga Gwamnatin da Praminista David Cameron ke jagoranta na nuna goyon bayanta ga irin zalincin da Israela ta ke yi a Ghazza. Lady Warsi wadda ita ce Musulma kwaya daya tal da take aiki tare da Piraminista Cameron a gwamnatin, ta rubuta a shafinta na Twitter kamar yadda BBC suka ruwaito tana cewa, "cikin matukar Nadama a wannan safiya nake bayyanawa Shugaba Cameron tare da gabatar masa da takardar barin aiki da na yi, ba zan taba goyon bayan duk wani tsari na zalinci ba akan Ghazza" a cewar Lady Warsi.

A nasa bangaren Piraminista David Cameron ya yabawa Lady Warsi a iya tsawon lokacin da ta yi aiki da shi, ya kuma yi mata godiya. Sai dai Cameron din yayi wasu kalamai da suke nuna borin kunya, inda yace "Ina bukatar ganin an tsagaita wuta a Ghazza ba tare da gindaya wasu sharudda ba". Wannan murabus na Lady Warsi ya samu goyon bayan jam'iyyar Adawa ta Labour tare da yaba mata bisa yadda ta nuna kishi da jajircewa.

A wani labarin mai kama da wannan itama BBC ta kori Ma'aikacinta Mai dauko mata Rahoto daga yankin na Zirin Ghazza Mista Jeremy Bowen a sakamakon rahoton da ya aiko cewa shi baiga ta inda 'yan Hamas suke amfani da fararen hula dan samun mafaka da su ba, zargin da Israela ta jima tana yi. Sai dai ita Israela ta nuna rashin jin dadinta a wadannan kalamai na Jeremy Bowen inda ta bukaci BBC da ta dauke Mista Bowen daga Ghazza nan take kuma BBc suka cika wannan umarni na Israela. Allah yana tare da mai gaskiya.

YASIR RAMADAN GWALE
05-08-2014

Gaskiyar Malam Nuhu Ribadu Ta Bayyana


GASKIYAR MALAM NUHU RIBADU TA BAYYANA

JAridar Premium Times ta ranar Lahadi ta ruwaito labarin cewar Jam'iyyun APC da PDP na matukar zabarin Malam Nuhu Ribadu dan ya yi musu takarar Gwamna a zaben cike gurbi da za ayi a Adamawa a watan Oktoba mai zuwa. Dukkan jam'iyyun biyun sun nuna cewar babu wani mutum da yafi cancanta da wannan takarar a wannan lokacin Kamar Malam Ribadu. Jaridar ta ruwaito fadar Shugaban kasa na rokon makusantan Ribadu kamar tsohon Amininsa kuma Shugaban Jam'iyyar PDP Alhaji Adamu Muazu da su yiwa Allah su roki Nuhu Ribadu ya shigo PDP dan ya yi musu takara a cikin jam'iyyar, tuni dai fadar Shugaban kasa ta kafa wani kwamiti da zai zauna da Malam Nuhu Ribadu dan ya lallabe shi ya shigo PDP, kwamitin dai an kafa shi karkashin jagorancin Ministar kudi Dakta Ungozi Okwanjo Iwela.

A nasu bangaren jam'iyyar APC sun nuna matukar kaguwa akan Malam Nuhu Ribadu ya amsa cewar zai yi musu takarar gwamnan a arkashin jam'iyyar. Sai dai masharhanta da dama na ganin da wuya Malam Nuhu Ribadu ya samu cikakken goyon bayan tsohon mataimakin Shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar wanda ake yiwa kallon shi ne uban jam'iyyar a jihar Adamawa, a cewarsu akwai tsohuwar jikakkiya tsakanin Ribadu da Atiku Abubakar. Haka kuma wasu na ganin APC zata yiwa Malam Nuhu Ribadu turin jeka-ka-mutu ne idan suka bashi wannan takara, ta hanyar zuba masa ido shi kadai ba tare da nuna masa wani cikakken goyon baya ba. A yayin wasu ke ganin idan Ribadu ya amsawa PDP to zai samu cikakken goyon baya ba kuma tare da ya kwashe kwabonsa ba.

Sai dai wasu da dama na ganin tuntuni Malam Nuhu Ribadu na da korafi akan jam'iyyar tasa ta APC domin, an jiyo Ribadu na korafin yadda jam'iyyar ta dauke kanta daga halin da tsohon Gwamnan jihar Murtala Nyako ya fada, Premium Times ta ce Malam Ribadu yayi korafi sosai akan yadda aka zubawa Nyako ido a cikin jam'iyyar aka asa yin wani katabus dan sasanta tsakaninsa da 'yan majalisar. Haka kuma, jaridar ta ce, daman kuma APC bata zabi duk wanda Malam Nuhu Ribadu ya marawa baya ba a zaben jam'iyyar da ya gudana a kwanakin baya.

Da wannan ne wasu masharhanta ke ganin PDP na iya samun galabar janyo ra'ayin Malam Nuhu Ribadu duba da cewar jam'iyyar ta APC bata cika nuna damuwa da irin kokarin Nuhu Ribadu ba. Sai dai a nasa bangaren har yanzu Malam Nuhu Ribadu bai ce komai ba akan batun, da Premium Times ta tuntubi mai magana da yawun Nuhu Rubadu Abdulaziz Abdulaziz ya ce, Nuhu Ribadu yana tattaunawa tare da tuntubar mashawartansa akan wannan al'amari.

Babu shakka gaskiya da rikon Amana da Malam Nuhu Ribadu ya nuna a dukkan ayyukan da ya rike sune suka janyo masa wannan daukakar da manyan jam'iyyu ke rokonsa Allah ya yi musu takara, duk kuwa da cewa Ribadun bai nema ba kuma bai nuna sha'awarsa ta yin takarar ba.

Yasir Ramadan Gwale
05-08-2014

ADAMAWA: Mallam Nuhu Ribadu Ne Zai Zama Dan Takarar Gwamnan PDP


ADAMAWA: MALAM NUHU RIBADU ZAI ZAMA DAN TAKARAR GWAMNAN PDP

Jaridar TheCable ta jiya Asabar ta ruwaito wani labari da yake cewa tsohon shugaban hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa Mallam Nuhu Ribadu na samun matsin lamba akan ya tsaya takarar zaben Gwamnan jihar Adamawa da za'a yi mai zuwa. Majiyar jaridar ta ce, Ribadun na samun kiraye-kirayen tsayawa takarar, tuni kuma jam'iyar PDP ta kuduri aniyar baiwa Malam Nuhu Ribadu tikitin tsayawa takara a doran jam'iyyar.

Haka kuma, wata majiya a cikin jam'iyyar PDP ta tabbatar da cewar, tana da kwarin guiwar cewa Malam Nuhu Ribadu zai amsa wannan kira na tsallakawa PDP daga APC dan ya cike gurbin kujerar Gwamnan jihar da aka tsige Murtala Nyako, zaben dai ana sa ran guddanar da shi a watan Oktoba mai zuwa nan gaba a wannan shekarar. Haka suma a nasu bangaren wata kungiya da ake kira Adamawa Concerned Youths for Good Governance suna ta jaddada kira ga Malam Nuhu Ribadu da ya amsa wannan kiran.

Wasu masharhanta na ganin idan Malam Nuhu Ribadu ya tsallaka zuwa PDP kuma ya zama dan takarar Gwamna a jihar Adamawa babu shakka zai doke dukkan wanda APC zata tsayar duba da gaskiya da rikon Amana ina na Ribadun. Haka kuma, da dama na ganin fitar Malam Nuhu Ribadu daga APC zai zama wani babban koma baya ga jam'iyyar.

Sai dai a nasa bangaren Malam Nuhu Ribadu har ya zuwa yanzu bai ce komai ba dangane da wadannan kiraye-kirayen da ake yi masa na tsayawa takara, da kuma damar da PDP zata bashi idan ya shigo Jam'iyyar.

Yasir Ramadan Gwale
03-08-2014

Saturday, August 2, 2014

SHI'ANCI: Mai Hankali Yi Tunani


SHI'ANCI: Mai Hankali Yi Tunani!

Sau da dama akan jiyo mabiya addinin Shia'ah karkashin jagorancin Zakzaky suna kira a garemu MU al'ummar Musulmi Ahlussunnah da mu zo a hada kai dan a yiwa addinin Allah aiki a kuma fuskanci abokan gaba tare, wannan kira ba bako bane a kusan kunnan kowa. Wannan magana tana nuna cewar su 'yan SHI'AH sun yarda da cewar MU al'ummar Musulmi Ahlussunnah Musulmi ne, kuma sun yarda da Musuluncinmu dan haka ne suke fatan mu hadu tare da su dan baiwa addinin Allah kariya, ya dan uwana mai karatu, Tayaya 'yan Shia'ar da basu yarda da Musuluncin Abubakar RA da Umar RA da Utham RA da Nana-Aisha RA da Nana-Hafsa RA ba amma kuma mu suka yarda da Musuluncinmu? Shin lafiyayyan hankalin zai karbi wannan magana, ace mu ka yarda da Musuluncinmu dan haka kake kiranmu da mu hada kai da kai, amma kuma kana tuhumar Manyan Sahabban Manzon Allah SAW cewar ba Musulmin kwarai bane. Mai Hankali yi tunani!

Ai bana jin akwai zalincin da ya kai mutum ya kore Abubakar RA da Umar RA da Utham RA da Nana-Aisha RA da Nana-Hafsa RA daga Musulunci ya kafirtasu sannan kuma shi ya kira kansa Musulmi Masoyin Manzon Allah SAW shin lafiyayyan hankali zai karbi wannan maganar? 'Yan Shi'ah mugayen azzalumai ne fasikai mujirimai, tsammaninsu muma tunaninmu irin nasu ne, suna tsammanin munyi kama da wadan da za'a yaudara da kalmar HADIN-KAI? Ai tun ran gini tun lokacin zana shi, babu wata magana mai dadi da 'yan Shi'ah zasu iya janyo hankalinmu da ita dan mu hada kai da su muddin suna kudire cewar wadannan sahabban da na ambata ba Musulmi ba ne.

Mu Ahlussunnah da kuke gani munyi imani cewar duk duniya babu wani dan Adam da ya kai Abubakar RA bayan Manzon Allah SAW girma da matsayi a Musulunci. Dan haka duk wani wanda yake zaton wai zamu tausayawa dan Shi'ah dan yana ikirarin an zalunce shi to ya sauya tunani, ai asalima mu a wajenmu duk abinda aka yiwa dan Shi'ah ba'a zalince shi ba, domin shi ne Azzalumi na tun farko, dan babu Azzalumi face wanda ya kore Abubakar RA da Umar RA da Utkam RA da Matan Manzon Allah SAW daga Musulunci sannan shi kuma ya tabbatar da kansa a matsayin Musulmi har yake tunanin baiwa addini kariya.

Ya dan uwa gabarmu da Shi'anci fa da gaske muke, muna tsananin kyamar shi'anci. Amma kuma mu din ba makiya ne na 'yan Shi'ah ba, sai dai akidar da suka kudurce ita muke kyama, yau idan da Zakzaky zai tuba ya Musulunta ya daina Shi'anci wallahi zai samemu masoya na hakika a gareshi fiye da jahilan da suka kewaye shi suke masa bauta, dan mu Muna yin soyayya ne dan Allah ba dan wani abin daban ba. Kuma muddin mutum ya mutu ko aka kashe shi yana SHI'ANCI wallahi summa tallahi ba zamu taba yi masa addu'ar Allah ya jikansa ba ko ta wacce irin hanya ya mutu matukar da waccan mugunyar Aqidah a tare da shi.

Mu bamu taba yin murna dan wani ya mutu ba, dan munyi Imani mutuwa tana kan kowa, kasancewarmu a raye shi ne yake tabbatar mana da cewar watan wata rana ajali zai riskemu mun shirya ko bamu shirya ba, dan haka duk wanda ya yi murna dan wani ya mutu, to shima tana nan zuwa kansa indai mutuwa ce.

Dan haka babu ruwanmu da batun wai an zalinci 'yan shi'ah mu tausaya musu, ai mu bamu ga inda aka zalince su ba, domin babu yadda mutane zasu tare hanya su hana Gwamna wucewa su hana Sarki wucewa su hana jami'an tsaro wucewa sannan a ce wai wadannan ba Azzalumai ba ne, ta ina! Ai idan har aka cigaba da kyale wannan Zalincin to ya nuna cewa wasu Shaidanun mutane sunfi karfin doka, ai dole a tauna tsakuwa dan aya ta ji tsoro, duk wanda ya keta doka to doka ta yi aiki akansa ko waye shi, ko mune muka saba ka'idar hukuma a zartar mana da hukuncin da doka ta tanada. Dan haka muna kira ga hukuma lallai duk wanda ya karya doka to hukunci ya hau kansa. Ai dan tuwon gobe ake wanke tukunya. 

02-07-2014

Friday, August 1, 2014

Ghazza

GHAZZA: Gidan Talabijin na ABC News dake Amerika ya ruwaito labarin wata mata dake a Unguwar Rafah a yankin Kudancin zirin Ghazza ta haifi Tagwaigwai wato 'yan hudu. Matar dai ta haifi yara hudu uku daga cikinsu Maza yayin da dayar ta kasance mace, jariran dai an bayar da labarin cewar suna nan cikin koshin lafiya.

Wata mata da ta yada wannan hoton a shafinta na Twitter ta bayyana cewar duk da yadda Israela ke kai hare-hare babu kakkautawa a yankin Zirin Ghazza inda a safiyar nan ta kashe sama da mutu 1,500 amma Allah bai hana al'ummar Palasdinawa mazaunan Ghazza yaduwa cikin sauri ba. Muna taya Mai Jego barka, wadannan yara kuma Allah ya raya su.

YASIR RAMADAN GWALE
01-08-2014