Tuesday, March 31, 2015

Shugaban Kasa Goodluck Jonathan Ya Cancanci Yabo


SHUGABAN KASA GOODLUCK JONATHAN YA CANCANCI YABO

Ba shakka mutum na biyu da za a yiwa godiya bayan an gode wa Allah a wannan zaben shi ne Shugaban Nigeria Dr. Goodluck Jonathan​ bisa irin yadda ya nuna dattako da kishin kasa ta hanyargirmama abinda 'yan Nigeria suka zaba, tarihi zai jima yana tuna Shugaba Jonathan bisa wannan namijin kokari da yayi na karbar sakamakon zaben da 'yan Nigeria suka yi, duk da cewa hukumar zabe bata kai ga bayyana sakamako na karshe ba, Shugaban kasa ya yiwa kowa yankan hanzari.  

Shugaban kasa, ya kawo karshen dukkan wani zullumin barkewar rikicin da aka dinga yi yayin fadin wannan sakamako. Manyan kasashen duniya da kungiyoyi da dama ciki da wajen Nigeria suka ta Kiran da a zauna lafiya a yin wannan zabe.

Shugaba Goodluck Jonathan ya cika alkawarin da yayi na cewa za'a yi zabe na gaskiya a wannan zabe. A sakon sa ga al'Umar Nigeria shi kansa GMB ya jinjinawa shugaban kasa Jonathan,  muna fatan wannan ya Bude sabon babi dan samar da sabuwar Nigeria. 

Wannan alamu ne da ke nuna al'amura zasu sauya a Nigeria In Sha Allah. Ina kara taya sabon Shugaban kasa Muhammadu Buhari​ murna da kuma fatan Allah ya shige masa gaba yayi masa jagora a wannan babban nauyi da yake kansa,  domin idan duniya baki daya na kan GMB wajen ganin yadda zai yi Gwamnatin da babu kamarta a tarihin Nigeria, wajen tsare gaskiya da adalci. Allah ka bamu lafiya da kwanciyar hankali da karuwar arziki a kasarmu. Fatan alheri ga Nigeria.

YASIR RAMADAN GWALE​
31-03-2015

Muhammadu Buhari Sabon Shugaban kasa


MUHAMMADU BUHARI SABON SHUGABAN KASA

Ban san lokacin da hawaye suka zubar min ba lokacin da Yusuf Muhammad Yandoma ya kira ni a waya yake sanar min cewa Muhammadu Buhari ya lashe zabe, duk da cewa ina bibiyar sakamakon a Channels TV. Wannan Nasara ce ga al'ummar Nigeria, Allah ya taya sabon Shugaban kasa murna.

Shugaban Kasa mai barin gado Goodluck Jonathan ba shakka ya nuna dattaku da kishin kasa ta hanyar karbar wannan sakamako nan take, Shugaban kasa Jonathan ya kafa tarihi na yin sahihin zaben da ba'a taba yin sa ba a Nigeria. Wannan ya nuna Demokaradiyya ta zauna sosai a Nigeria.

Allah ya tabbatar mana da alheri.

Yasir Ramadan Gwale 
31-03-2015

Wednesday, March 25, 2015

Tsakanin SAK Da CANCANTA


TSAKANIN KALMAR SAK DA CANCANTA

Ya zuwa 'yanzu babu wani dan Najeriya da yake bukatar ayi masa tallar wani dan takara dan ya zabe shi, kowa yasan wanda zai zaba a cikin zuciyarsa (illa kalilan da ana iya sauya musu ra'ayi a lokacin zabe, dan koni ma a zaben da ya gabata 'yan dakikoki kafin Zainab ta jefa kuri'ah na sauya mata ra'ayi, ko ba haka bane Zainab?), sai dai kawai ayi motsi dan karin samun tabbata akan manufa. Akwatu ce zata raba gardama tsakanin masu ra'ayin Sak da kuma cancanta.

Ina ganin idan har dan takara ya san cewa ya cancanta ba zai ji tsoron kalmar Cancanta ba, a ganina masu san bin inna rududu sune ke fatan gamayya. Amma ina ganin babu laifi ga wanda yace zai bi cancanta ko wanda yace Sak ko wanda yace daga sama har kasa, Demokaradiyya ta baiwa kowa damar bin son ra'ayinsa dan samar da Shugabanci karkashin tsarin zabe, dan siyasa dake da katin Jam'iyya idan ya zabi 'yan takarar jam'iyyarsa baiyi laifi ba (a dimokaradiyyance kenan fa), wanda baya jam'iyya yayi wake da shinkafa (ma'ana ya zabi cancanta) shima yana da 'yanci.

Amma ni abinda nayi Imani da shi, shi ne, Allah zai yi kowa tambaya akan yadda ya gudanar da rayuwarsa tudaga kuruciya har tsufa, dan haka zab'e yana daga cikin abinda muka aiwatar a rayuwarmu, kowannemu zai bada bayani akan abinda ya zab'a, wanda duk yayi Sak yana da hujja, wanda yayi daga sama har kasa shima yana da hujja, haka nan wad'an da suke cewa Cancanta zasu zab'a, kowannemu zai bada bayani, ranar da kudi da dangi da sanayya ba zasu amfani kowa ba (Bello Yabo yace, ranar da babu Ricky Tarfa ba Joel Kyari Gadzama), sai abinda kowa yaje da shi, Ya Allah kada ka kama mu akan abinda muka yi bisa jahilci da rashin sani.

Fatanmu Allah ya kaimu ranar zabe lafiya, kowa yasan makomarsa. Lokacin da muna firamare a Gwale, Malam Tahir yake ce mana, ranar Lahira za'a jima a tsaye, hankalin kowa ya tashi, kowa ya k'gauta, buri kawai yake ayi Hisabi yasan makomarsa, wani idan anyi wuta zashi bai sani ba, amma ya k'agu ayi Hisabi inji Malam Tahir a lokacin da yake bamu labarin tashin alkiyama shekaru 21 da suka shude a lokacin muna 'yan firamare a Gwale.

Wata rana aka tambayi Dakta Sani fatawa, shin b'arawon jarabawa me yake ci, Malam yace yaci Haram, tun daga lokacin na tsorata kwarai da gaske, idan barawon jarabawa yaci Haram, barawon zabe kuma me yake ci kenan? Ya Allah ka kare tsokar jikinmu daga bubbuga da Haram, Manzo yace duk tsokar naman da ta ginu da Haram wuta ce tafi cancanta ta babbake ta, Malamai Suka ce da Sayyadinu Umar Allah ya Yarda da shi yaji wannan magana, da yaci wani tsokar nama da bai amintu da halaccinsa ba, sai da ya sa hannu a mak'oshi ya dawo da naman, dan kar wannan yayi sanadiyar teba a jikinsa kuma ya kasance Haram ne.

Ni kam gaskiya kullam ina tsoron gamuwa da Allah, sai dai idan na tuna cewa Allah mai Rahama ne kuma mai jin kai, sai na kyautata masa zato cewa cikin kaddarawarSa da jin kansa zamu samu babban Rabo. Ya Allah kada ka sanya siyasar Demokaradiyya tayi silar halakarmu. Allah ka bamu Shugabanni masu jinkai da tausayi da hakuri da juriya. Fatan Alheri Ga NIGERIA!

Yasir Ramadan Gwale​
25-03-205

Wednesday, March 18, 2015

Wanda Ya Dogara Ga Allah Ya Rabauta

WANDA YA DOGARA GA ALLAH YA RABAUTA

Wata rana, a Masallaci aka daukewa Alhaji Isyaku Mota yaje Sallar Juma'a. Da ya dawo inda ya aje motar bai ganta ba, aka dudduba ko ina ba'a ganta ba, da ka kalli fuskar Alhaji Isyaku zaka ga alamun sauyi da ke nuna Alamun wani abu ya dan dameshi amma ba me tsanani ba, a lokacin aka fara yi masa adduar ALLAH YA MAIDA ALHERI, kana tunkararsa Murmushi zai yi maka har da dariya yana cewa ba komai tare da cewa Amin ga adduar da kayi masa. A lokacin har wasu suke cewa haba Alhaji Isyaku kamar ba wanda aka daukewa mota ba kai ta dariya, yace to ai a matsayina na Musulmi dole na yadda da kaddara! Kaji magana mai cike da tauhidi.

Daga nan wajen, yaje ya sanarwa da caji-ofis na 'yan sanda dake kusa, ko da za'a kama barawon Motar. Kana taka, Allah na tasa, Shi Allah buwayi ne gagara Misali, mai yin komai a lokacin da yaga dama. A wannan ranar Juma'ar da aka sacewa Alhaji Isyaku Mota, bayan ya koma gida da daddare sai ya tarar da wani abokinsa Dan Majalisa ya aiko masa da kyautar sabuwar Mota. Ya Salam, Al'amarin Ubangiji sai shi. Wallahi Allah maji rokon bawansa ne.

Duk wanda ya dogara ga Allah ya rabauta duniya da lahira. Duk halin da ka shiga na wuya da tsanani kada ka taba yankewa daga samun taimakon Ubangiji, ka shagaltu da kaskantar da kai ga Ubangiji kuma ka kyautatawa Allah zato.

Wannan hali da ake ciki na tsanani da rudani, mafita tana wajen Allah, mu kyautata masa zato, mu nemi taimakonsa da agajinsa, Allah ne yace shi mai ji ne, kuma mai gani ne, tare da haka yace, ku rokeni zan amsa muku. Ya Allah ka bamu mai kyau a duniya ka bamu mai kyau a lahira.

Yasir Ramadan Gwale
17-03-2015

Wednesday, March 11, 2015

Shin Za Ayi Zaben 2015 Kuwa?


SHIN ZA AYI ZABEN 2015 KUWA?

Sau da yawa lamura musamman na siyasa a Najeriya daga jita-jita suke zama gaskiya. Ina zaton batun d'aga zab'e daga Fabrairu zuwa Maris duk daga jita jita muka dinga ji har ya zama gaskiya, wannan abinda yake nunawa shi ne, a wannan babban zaben "interest" na masu mulki ne kawai ke aiwatuwa, ko al'umma sun yarda ko basu yarda ba.

Ya isa abin misali, ace anyi Babban Taron Manyan Masu Ruwa Da Tsaki Na kasa 'Council of State' aka ce babu batun d'age zabe daga Fabrairu, a wajen wannan taron duk wani 'who is who' a Najeriya ya halarta, aka tabbatar da cewa zab'e yana nan daram dam dam, har Shugaban hukumar zab'e Attahiru Jega ya tabbatarwa da taron cewar hukumarsa ta shirya tsaf domin gudanarda zabe a Fabrairu, 'yan Najeriya akai ta shewa.

Kwatsam kwanaki kad'an bayan wancan taro na copuncil of state, sai gashi hukumar zabe ta hannun Farfesa Jega da ya tabbatarwa da Council of State cewar zasu yi zabe a Fabrairu babu wata matsala, sai gashi ya bayar da sanarwar jingine zabe daga Fabrairu zuwa Maris da Afrilu! Ya akai haka ta faru? Ko da ba'a san da matsalolin da aka jingina da su bane? Wannan sanarwa haka tazo bagatatan, kuma ta zauna daram dam cewa an d'age zabe kuma ya d'agu. Amma a zahirin gaskiya, da yawan 'yan Najeriya sun kwana da sanin cewar dage zab'e ra'ayi ne na Gwamnatin Tarayya, domin maganar d'agawar ta fara samo asali ne daga Kanar Sambo Dasuki.

Bayan wannan sanarwa, Attahiru Jega ya shawa 'yan Najeriya alwashin cewar daga wannan d'agawar ba za'a kuma yin wata ba, zab'e sai anyi shi a Maris da Afrilu, kamar ba Jega ne yace sun shirya tsaf dan yin zabe a Fabrairu ba! A hakikanin gaskiya, dangane da wannan zab'en, ra'ayin gwamnati shi ne a sama, idan har da gaske Gwamnatin Najeriya na san ayi zabe to ba makawa za'a yi shi, idan kuma ya tabbata cewar bata son ayi zabe, to hakan Jega zai bayar da wata sabuwar sanarwa, idan yakai lokacin kenan.

A bayyane take cewar idan an sake d'age zab'e daga Maris, to za'a shiga rud'ani, sabida abubuwa zasu cakudewa tsarin Mulki, dan masu fashin ba'ki na cewa kundin tsarin mulki yace Tilar ayi zab'e kwanaki 30 kafin 29 ga watan Mayu, haka kuma, kundin mulkin Najeriya bai yi wani tanadi ba dangane da gwamnatin rikon kwarya ba a cewar masana. To idan aka d'age zab'en meye zai faru?

YASIR RAMADAN GWALE​
11-03-2015

Sunday, March 8, 2015

Ranar Addu'ah


RANAR ADDU'AH

Turawa sun ware ranar yau a matsayin ranar addu'ah, amma mu al'Umar Musulmi kullum cikin addu'ah muke da rokon Allah ya bamu daga cikin falalarsa Subhanahu Wata'ala. Ranar wata Juma'a naga tasiirin addu'ah wallahi. Ranar na tashi na tafi Masallaci da wari kuma a lokacin bani da kudi haka na tashi, bayan da na isa Masallaci nayi Nafila zan zauna kawai sai na hangi wani mutum ya daga hannu yana addu'ah, sai ya tunasar da ni, kawai nima na daga hannu zan yi addu'ah, abinda ya fara zuwa raina a lokacin shi ne wani mutum da nake bi kudi amma ya daina yi min waya. Kawai sai nayi addu'ah nace Ya Allah ka baiwa wane kaza ikon biyana kudina, nayi sauran addu'o'i na gama. Wallahi abin mamaki banyi minti biyar da yin addu'ar nan ba kawai sai wayata tayi kara, kamar ba zan dagaba, amma na make murya na daga wayar, kawai sai ji nayi yace Malam Yasir wane ne yake magana dan Allah ka gaya min inda zan tura maka kudin ka! Nan take nayi Sujjada na yiwa Allah godiya, nan fa na dinga zabga addu'ah ba kakkautawa. Ba shakka dukkan abinda bawa yake nema idan ya dirfafi addu'ah tare da kyauta tawaga Allah zato ba shakka zai sameshi ko meye. Shi yasa yanzu bana tsoran kudina su shiga hannun wani su makale, dan da adduah zan bishi. Allahumma Taqabbal Minna Du'a'ana .

Yasir Ramadan Gwale 
06-03-2015

Thursday, March 5, 2015

BOKO HARAM: Makaircin Kasar Tchadi karkashin Kulawar Faransa


BOKO HARAM: MAKIRCIN KASAR TCHADI KARKASHIN KULAWAR FARANSA

Manyan kasashen duniya da ke da kujerarar din-din-din a kwamatin tsaro na majalisar dinkin duniya, kusa sune kanwa uwar gami akan duk wani rikici da ke faruwa a galibin kasashen duniya. Suna amfani da wadannan yake yake da suke faruwa a kasashen duniya, tare da kirkirar kungiyoyi na ta'addanci da daure musu gindi da mara musu baya, sannan a gefe guda kuma su cika duniya da surutun yaki da ta'addnaci,ta hanyar samun cin kasuwar makamai. 

Abu mafi muhimmanci a wannan lokaci shi ne karfi ta fuskar kafafen watsa labarai. Domin da su ne ake yakar tunanin mutanan duniya, a sauya karya ta zama gaskiya, gaskiya kuma ta zama karya. Misalai akan haka shi ne, abinda ke faruwa a kasar Suriya! Har yau manyan kasashen duniya basu kira Bashar Assad da sunan dan ta'adda ba, domin yana yin abinda ake cin moriyarsa. Makamansu na kara samun kasuwa a kasashen da ke kewaye da Suriya, sabida tsoron kwararowar 'yan ta'addan Suriya zuwa kasashensu, sannan a gefe guda bashar Assad ba shida wata damuwa idan kasashen Yamma sun rushe Suriya gaba dayanta inda zai tabbata a matsayin Shugaba, tare da samun kariyar wadannan kasashe.

Da farko anyi wasa da hankulan mutane ainun a Suriya. Aka yi amfani da guguwar sauyi, aka kauda hankulan kasashe da dama daga abinda ya kamata su maida hankali kansa zuwa kare kai daga barazanar guguwar sauyi dake gauraye da 'yan ta'adda. Da farko akwai FREE SYRIAN ARMY suna yakin kwatar 'yancinsu bilhakki da gaskiya, da nufin kawo sauyi da kuma 'yanto Suriyawa daga bakin mulkin zalinci irin na Zurriyar Assad.

Lokacin da tafiya tayi Nisa FSA sun kama hanyar kifar da gwamnatin Assad sai aka yi kutsen kungiyar NUSRA da nufin taimakawa FSA dan yakar Assad, alhali kuwa Sharewa su Albaghadadi hanya akai dan shigowa Suriya su lalata batun yakin da ake yi da Assad, da kuam sanya tsoro a daukacin kasashen gabas ta tsakiya da kuma kasashen Arewaci da gabashin Afrika. Yanzu dai sunci nasarar kassarawa wannan gwagwarmaya a Suriya, ta yadda yanzu duk wasu masu yakar Assad sun narke sun zama ISIS, kuma kaikayi ya koma kan mashekiya, duk mai yakar Assad yanzu kai tsaye za'a kirashi dan ta'adda. 

ISIS kuma na cigaba da sanya tsoro da firgici a zukatan kasashe da yawa musamman wadan da suke da burbushin yake a tattare da su, yanzu dai LIBYA, SURIYA, YEMEN duk sun gama yawo. Wannan wani al'amari ne mai tsayi mai kuma rudani.

A Afrika kasar Faransa ita ce kasar da tayi fice wajen yakar 'yan Ta'addan kudu da Sahara. babu ko tantama cewa Duk wasu kungiyoyin ta'addaanci a Arewacin Afurka da yammaci akwai hannun Faransa a ciki, domin Faransa ita ta san, yadda ta tsuguna ta haifi 'yan ta'adda a MALI kuma ita ta murkushe su. Haka zalika duk wasu kungiyoyin hayaniya da karyar Addini da Shari'ah suna da alaka da Faransa ta kusa ko ta nesa, domin miliyoyin tantan da Allah ya huwacewa kasashen Arewacin Afurka sune ke haskaka fitulun Birnin Paris da gudanar da fadar Champs-Elyees.

Maganar da Shugaban Tchadi, Idriss Devi Ittono yayi na cewar ko dai Shekau ya fito daga inda yake a Boye ko kuma su bayyanawa duniya inda yake. Wannan kai tsaye ya nuna mana cewa duk wannan lokacin da aka dauka, ashe Tchadi na daurewa Boko Haram gindi. Domin shi dai wannan mutum Shekau, tuni Amerika ta bayar da sanarwar Ladar Dalar Amurka 50,000 ga duk wanda ya bayar da bayanan da suka kai ga kama Shekau. Har yau Amerika bata janye wannan sanarwa ba.

Ba shakka, kasar Tchadi ba tada karfi na iya daurewa Boko Haram gindi face ta samu cikakken goyon bayan kasar Faransa tare da samun tallafi da kuma dabaru. ya isa misaali yadda Faransa tayiwa Kasar Afurka Ta Tsakiya da Mali da Nijar da kuma Aljeriya, inda faransa take yiwa wadannan kasashe katsalandan a sha'anin tsaronsu.

Kasar Tchadi da faransa sunyi amfani da sakarci da tsoro irin na Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan​ sukai wakaci ka tashi a yankin Arewa maso gabashin Najeriya. Yanzu kuma a halin da ake ciki Faransa da Tchadi sun fahimci cewa matsin lamba ta sanya Shugaban Najeriya daukar tsauraran matakai dan yakar Boko Haram kuma Asiri na gab da tonuwa, shi ne Devi yayi farat da garajen cewar ko Shekau ya fito ko su tona masa Asiri. Daman Ashe sun san inda yake sukai Shakulatun Bangaro suna shigoNajeriya da sojojinsu da nufin yakar Boko Haram suna yiwa Najeriya leken asiri?

Koma ya ake ciki bama fatan gwamnatin najeriya ta ragawa kasar Tchadi akan duk wata maniksa da kutunguila da ta shirya dan daurewa ta'addancin Boko Haram gindi. Faransa kuwa daman taci dubu sai Allah . . . Mun san Allah Fa'alun Lima Yurid ne, zai maganta mana su ta inda basu zata ba. Allah ka taimaki musulunci da musulmi ka rusa kafurci da kafirai. makiyanamu na fili da na boye Allah ka sansu Allah kayi mana ganinsu. Allahumma Rudda Kaiduhum Alaiihim.

YASIR RAMADAN GWALE​
05-03-2015

Alhaji Shehu Shagari da Obasanjo


ALHAJI SHEHU SHAGARI

A cikin 'yan kwanakin nan Tsohon Shugaban Kasa, kuma shugaban farar hula na farko a Najeriya, Alhaji Shehu Shagari ya yi bikin yanka kyak din da ya nuna cewar cikarsa Shekaru 90 a wannan doron duniya. Wannan biki ya wakana ne a jihar Shagari ta haihuwa Sokoto, inda tsaffin Shugabannin kasa da suka hada da IBB, AbdulSalami, Shonekan da kuma Shugaban Kasa Goodluck Jonathan​ duk da ayyukan office ya halarci wannan kwaryakwaryar biki dan taya Shagari murna. 

Jaridun Najeriya da yawa, sun yi ta ruwaito sakwannin fatan alheri da manyan mutane a Najeriya suka dinga aikewa da Shagari dan taya shi murna da yi masa adduar samun nasara, wannan ya nuna irin yadda Shagari yake da tasiri a wajen manyan kasa. Shagari kusan an ce mutum ne da baya yin katsalandan a sha'anin tafiyar da harkokin gwamnati a Najeriya, yakan halarci taruka da suke na wajibi a gareshi.

CHIEF OLUSHEGUN OBASANJO

A wannan lokaci shima tsohon Shugaban kasa Aremu yake nasa bikin zagayowar ranar haihuwarsa. Ban san a ina Obasanjo ya gano wannan rana da aka haifeshi ba, domin kuwa a baya yasha fadin cewar shi baisan hakianin lokacin da aka haifeshi ba. obasajo ya rusa Najeriya daga 1999 zuwa 2007, ya tafka muguwar ta'asa da ta hada da cire Shugaban majalisar dattabai, da sanyawa a sace Gwamna, da kisan manyan mutane a Najeriya karkashin ikonsa da suka hada da Sheikh Jaafar Adama kano, Bola Ige, Funsho Williams, Henry Marshall da sauransu da dama.

Duk da irin ta'asar da Obasanjon ya shuka, yafi kowa yin katsalanda a wajen tafiyar da gwamnati a Najeriya tare da nuna cewa shi mai gaskiya ne, bayan kuwa duk wata barna da ake yi a yanzu shi ne ya kafa harsashin tabbatuwarta. Duk wani bakin mulki na shiririta da sakarci da ake zargin Shugaba Jonathan da yi Obasanjo ne silar wannan al'amari.

Yasir Ramadan Gwale 
05-03-2015

Monday, March 2, 2015

ALJAHI KABIRU SANI KWANGILA: Daya Tamkar Da Dubu


ALHAJI KABIRU SANI KWANGILA: Daya Tamakar Da Dubu

Duk mutumin da yake Kano ko makwabcin Kano, ba zai kasa sanin wannan dan tahaliki ba, Alhaji Kabiru Sani Kwangila a.k.a SKY, mutum ne mai arziki Attajiri mai taimakon bayin Allah da baya kyashin taimakawa a kowanne lokaci. Ya shahara da taimakawa addini a ciki da wajen jihar Kano, ya taimakawa da'awar addini fiye da yadda ake zato, kuma yana kan yin wannan taimako, mutum mai taimakon matasa galihu.

SKY wata rana an gayyace shi taron saukar Al-Qurani da kafa asusun gina wata makaranta. Bai sanni ba, bai taba gani na ba, labarina kawai aka bashi, ya aiko min da kudi wajen Kwata Miliyan, cewa naje wannan makaranta na kaddamar da wannan asusun gina makarantar a madadinsa, ya kuma bude asusun da wannan kudi da ya bayar, tare da alkawarin taimakawa makarantar a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

Hakika wannan al'amari yayi min dadi, sannan kuma naji matukar mamakin yadda wannan bawan Allah ya gasgatani ba tare da yasan ko waye ni ba. Naje makarantar na zauna a katuwar kujerar da aka warewa cif Lanca aka bani abin magana na kaddamar da wannan asusu.

Cikin ikon Allah a jiya na samu lokaci mai tsayi wajen tattaunawa da SKY akan batutuwa da yawa da suka shafi rayuwar Talaka da kuma cigaban Najeriya. SKY ya labarta min irin yadda ya dauki dawainiyar dalibai masu yawa zuwa kasashen duniya daban daban dan yin karatu. Ya tura mutum 60 zuwa Ingila dan yin karatu, mutum 40 zuwa Russia, 6 zuwa Amerika, 80 zuwa Indiya, mutum 200 zuwa Ghana, 38 zuwa Masar  sannan ya tura biyu uku zuwa Ukrain da Malaysia da Singapore da Uganda da da sauran kasashe da yawa.

Haka kuma, SKY ya shaida min cewar a shekarar da ta gabata yayi bajat na kudaden karatun yaran da yake daukar dawainiyarsu sama da Naira Biliyan daya, wannan kusan duk Shekara sai an kashe wannan kudi. Abin farin cikin duk wadannan mutane da yake daukar dawainiyarsu da dukiyarsa gaba dayansu 'ya 'yan Talakawa ne, wadan da bai san su ba. Allahu akbar! Wannan taimako SKY yana yinsa ne kawai fa ta fannin Ilimi banda sauran bangarori daban daban na rayuwar al'umma da ya taba da dukiyarsa. Banda wadan da ya taimakawa da ba wanda ya sani sai shi sai Allah, sai kuma wadan da ya taimakawa.

Ba shakka samun mutum irin wannan a cikin al'umma babbar Ni'ima ce. Domin shi daya ne tamkar da dubu. Allah ya saka masa da mafificin alherinsa, Allah ya yalwata masa dukiyarsa, Allah ya kiyaye shi ya kare shi daga sharrin makiya da mahassada na fili da na boye. Allah ka yawaita mana irinsa a cikin wannan Al'umma tamu. Ya Allah ka sakawa bawanka SKY da alheri, Allah ka sada shi da Manzonka Sallallahu Alaihi Wa Sallam. Allah ka taimaki masu taimako a duk inda suke.

Yasir Ramadan Gwale
02-03-2015