Saturday, December 5, 2015

Godiya Da Fatan Alheri Ga Sojan Nigeria


GODIYA DA FATAN ALHERI GA SOJAN NAJERIYA

Daga Ranar Juma'a 4 ga watan Disamba zuwa 10 ga wata,  lokaci ne da Rundunar Sojan Najeriya ta ware a matsayin makon da za a godewa sojojin Nigeria dake fagen daga #ThankASoldier. A dan haka, a wannan rana ta Juma'a kuma a wannan sa'a ta karshe ta wannan rana muke tawassuli da sunayan Allah tsarkaka madaukaka, Ya Allah ka Jikan sojojin mu musamman wadan da suka rasu a fagen daga domin kare kasarmu daga farmakin 'yan ta'adda masu tada zaune tsaye, Allah ya jikan su ya gafarta musu, masu raunuka daga cikinsu Allah ya basu lafiya.

Anan nake amfani da wannan dama, nayi kira ga sauran 'yan Najeriya da su cigaba da yiwa Najeriya da sojojin mu adduar fatan alheri da samun nasara a fagen daga. Allah ya tabbatar mana da samun zaman lafiya dawwamamme mai dorewa, Allah ya kade mana dukkan fita. Haka kuma, ina kira ga mai girma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya daure ya kaiwa sojojin mu dake fagen daga ziyara, a musamman jihar Borno, ba shakka wannan zai kara musu kwarin guiwa da karsashin yin aiki tare da nuna kishin kasa, Bugu da kari, hakan zai basu kwarin guiwar cewar ana gamsuwa da aikinsu.

Kamar yadda Shugaban kasa ya ambata cewar zai shige gaba domin fafarar 'yan ta'addar da suka hana wannan kasa zaman lafiya, muna rokon Shugaban kasa da ya daure ya kai musu ziyara dan yaba musu. Sannan kuma, muna fatan Gwamnati zata inganta jin dadi da walwalarsu tare da biyansu dukkan hakkokinsu akan kari, wadan da suka yi Shahada kuma muna fatan Gwamnati ta dinga biyan iyalansu akan lokaci. ALLAH ya taimaki Sojan Najeriya ya basu kwarin guiwa. Allah ya bamu Lafiya da zaman lafiya. #ThankASoldier 

Yasir Ramadan Gwale 
05-012-2015

No comments:

Post a Comment