Wednesday, October 31, 2012

Kabarin Shugaban Kasa!



Kabarin Shugaban Kasa!

A lokacin da marigayi shugaban kasa malam Umaru Musa ‘YarAdua yake da rai, yana yawan kai ziyara makabartar wali dan marina a jihar katsina. Yana zuwa wannan makwantai domin ziyara ga kushewar mahaifinsa da kuma dan uwansa; marigayi ‘YarAdua ya taba tambayar mai gadin makabartar cewa, “kana da da tabbacin idan na mutu zan samu waje a wannan makabartar, musamman kusa da mahaifina da kuma dan uwana? Sai mai gadin ya mayar da tambaya zuwa ga marigayi ‘YarAdua, ranka ya dade me kake nufi? Sai ‘YarAdua ya ce masa na lura da sabbin mutanen da ake biznewa suna yawa, sannan mai gadin makabartar ya amsa masa da cewar Insha ALLAH bazaka rasa waje ba a wannan makabarta. ALLAH cikin ikonsa mai aukuwa ta auku ga ‘YarAdua, kuma burin da yayi na samu makwanci a cikin wannan makabarta ALLAH ya cika masa, muna addu’ar ALLAh ya jikansa da rahama.

Dukkaninmu munyi imani da cewa akwai rata mai yawa tsakanin fadar shugaban kasa da kuma gidan talaka. Wannan kusan zaka iya cewa rata ce da tsakanin yana da yawan gaske, domin fadar shugaban kasa wajene da aka tsarashi na musamman, ba dan komai ba, sai domin amfanin rayuwar duniya da jin dadi da morewa. Amma kuma babu wanda yake shakkar cewa da kabarin shugaban kasa da kabarin almajirin da ya mutu a hanya da bashi da ko damar shiga gidan haya daya suke, yadda aka sanya shugaban kasa a cikin rami, aka nade gawarsa da farin kyalle haka za’ayiwa wannan talaka, wannan ya nuna dangantakarmu daya ce da masu mulki. Alhamdulillah! kamar yadda addinin musulunci ya tanada idan musulmi ya rasu gaggawa akeyi a binneshi ba sai an bata wani lokaci ba. Wannan ya tunamin da wani baiti da MARAYA Jos yake cewa:

Kai mai akwai ka gane, In baka ɗan misali, Ranar komuwa ga Allah
Yadi biyar fari ɗai, A ciki za a nannaɗe ka, Rami guda a kan tona
Ka tuna ba a tona goma, Don wai kana da hali, Ciki za a turbuɗa ka
Haka nan wanda bai da kome, Ran komuwa ga Allah, Yadi biyar fari ɗai
Ciki za a nannaɗe shi, Rami guda a kan tona, Ka tuna ba a tona goma
Don wai fa bai da kome, To malam idan ka duba, Tanan haka dangantakar ku daidai”.

Marigayi tsohon Shugaban kasa mallam Umaru ‘YarAdua, ya sha fama da jinya kafin ALLAH ya karbi rayuwarsa.  A cikin hadisin da Bukhari ya fitar da shi manzon ALLAH sallalahu Alaihi wasallam yana cewa ALLAH yana kankare zunuban bawan da aka jarrabeshi da cuta kafin rasuwarsa, Shuagab YarAdua yayi sa’a, domin ya shiga cikin sahun mutanan da za’a kankaremusu zunubansu sakamakon tsananin rashin lafiya da aka jarrabeshi da ita. Allah mai girma da dauka ya fada a cikin littafinsa mai tsarki Al-kur’ani a cikin sura ta 3 aya ta 185 cewa ‘Lallaine tabbas kowace RAI zata dandani mutuwa’ shugaban kasa dai ya riga ya dandana tasa.
 Fadar shugaban kasa nanne wajen da yafi ko ina samun tsaro da kariya a duk fadin Najeriya, amma wannan tsaro bai iya hana mala’ikan mutuwa shiga wannan fadar ba wajan dauko ran shugaban kasa ya fito salin’alin. Allah Akbar! Haka nan, mala’ikan mutuwa ya shiga wannan fada ya dauko ran magabacin YarAdua, marigayi Gen Sani Abacha, ba tare da ya fuskanci wata barazana ko tirjiya daga dukkan jami’an tsaron da ke wannan fadar ba, ALLAH kenan mai yadda ya so, duk kauna da soyayya da kariya da ake baiwa masu mulki ashe bata da wani amfani tunda bazata iya hana mala’ikan mutuwa shiga duk inda yaga dama ba, lallai ne kowace RAI bazata mutu ba sai ta cika ajalinta.

Dan haka, duk wanda ya fahimci manufar wannan rayuwa kuma ya kalli karshenmu gabaki daya, sai ya samu natsuwa a cikin zuciyarsa, ya san cewar ALLAH baya barci yana nan yana kallon kowa. Kuma, kowa zai tafi da ayyukan da ya aikata ne, idan Alheri ka aikata wallahi babu abinda zaka gani sai alheri, hakama idan sharri ka aikata babu abinda zaka gani sai shi, ALLAH shi da kansa ya haramta zalinci akansa, ballanatana danAdam. Munyi imani da cewa dukkan wani tsanani akwai rahama a karshensa, fatanmu shine ALLAH ka sanya karshenmu yayi kyau, halin da muke ciki ALLAH ka sayaya mana, ALLAH ka sa can tafi nan.

Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale



Monday, October 29, 2012

ABINDA YA SHAFI ABBAS FAGGO YA SHAFEMU




ABINDA YA SHAFI ABBAS FAGGO YA SHAFEMU

A gobe ne idan ALLAH ya kaimu Abbas Ahmed faggo zai bayyana a gaban kotu. Idan bamu manta ba, Gwamnan Bauchi Malam Isa Yuguda da kwamishinan shari’ah na Bauchi suka sanya aka kame tare da garkame Abbas saboda ya bayyana ra’ayinsa a shafinsa na facebook akan facaka da almundahana da yace antafka da dukiyar al’ummar jihar Bauchi a dalilin bikin dan gidan gwamna isa Yuguda. Lauyan dake kare Abbas ya bayyana cewar a gobe ne za’a  gurfanar da wanda yake karewa a gaban kotu ta uku dake cikin garin Bauchi, kotun tana nan kusa da gidan Muda Lawal a sabuwar GRA dake cikin garin Bauchi. Dan haka ana kira ga duk masu rajin kare hakki ko ‘yancin Bil’adama cewa ga ranarsu, lokacin da zasu nuna kauna da soyayya ga Adalci da daidaito da kuma ALLAH wadai da mulki na danniya da karya tsarin mulki da dannewa mutane ‘yancin fadin albarkacin bakinsu. Dan haka ina al’ummar Jihar Bauchi masu son ci gaba, ina kungiyoyin dalibai masu neman kawo sauyi, ina kungiyoyin sa-kai ana kiranku gobe kuyi tururuwa zuwa wannan kotu domin yin ALAH wadai da mulki irin na ‘yan kama-karya, mulkin da yayi kama da na mallaka.

Wannan shari’ah ta Abbas ba tashi bace shi kadai, abu ne da ya shafi dukkaninmu masu amfani da kafar sadarwa ta Internet. Dole ayiwa Abbas adalci, domin adalci gareshi adalci ne ga dukkaninmu. Lokaci yayi da zamu yi tir tare da tofin Alla-tsine ga tsarin mulkin kama karya irin na su gwamna Isa Yuguda. karni na 21 ba lokacin kama karya bane, kan mage ya waye. Shugaban kungiyar lauyoyi reshen jihar Bauchi ya shaidawa Dr Aliyu Tilde cewar zaije wannan kotu tare da wata kakkarfar tawaga ta lauyoyi domin ganin yadda wannan shar’ah zata gudana.

Manzon ALLAH Salallahu Alaihi wasallam ya cewa sahabbai ku taimakawa dan uwanku da aka zalunta, sannan ku taimakawa dan uwanku da yayi zalunci. Sai  Sahabbai suka tambayi manzon ALLAH tayaya zamu taimakawa dan uwanmu da yayi zalunci? Manzon ALLAH ya ce a duk lokacin da wani dan uwanku yayi laifi idan kuka la’ance shi to kun taimakawa shaidan akansa, idan kuwa kuka yi kokarin hanashi aikata wannan abinda da yayi to kun taimaka masa akan shaidan. Dan haka, muna kira ga Gwamna Isa Yuguda yaji tsoron ALLAH ya sauraremu tun kafin lokaci ya kure masa, tun kafin lokacin da zaiyi da ya sanin da bazata amfaneshi ba. Kada Isa Yuguda ya manta cewa wani ne ya sauka daga kan kujerar gwamna sannan ya hau, to haka shima nan gaba zai sauka wani ya hau. Idan kuwa kaki ji to tabbas bazaka ki gani ba, domin akwai EFCC tana nan tana jiranka, ka tuna magabatanka irinsu makwabcinka Danjuma Goje da Aliyu Akwe Doma kaima wannan ranar tana jiranka! Lokacin da zaka ringa cewa inama dai na saurari koke-koken al’umma da kiraye-kirayensu, zaka yi dana sani nan gaba kadan kuma nadama ce karshenka Yuguda.

Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale

   


ZABEN AMERIKA: Abinda Mutane Da Yawa Basu Fahimta Ba (6)



ZABEN AMERIKA: Abinda Mutane Da Yawa Basu Fahimta Ba(6)

Wednesday, October 10, 2012

ZABEN AMERIKA: Abinda Mutane Da Yawa Basu Fahimta Ba (5)



ZABEN AMERIKA: Abinda Mutane Da Yawa Basu Fahimta Ba (5)

Harin 11 ga watan satumba na 2001 da aka kai tagwayen gine-gine cibiyar kasuwanci ta duniya a New York cike yake da abin mamaki da kuma tuhumce-tuhumce. Lokacin da abin zai faru annunawa duniya cewa ga wani jirgi nan da ba na yaki ba, ya taho ya tunkuyi wannan gini, a zahiri wannan shine abinda aka ringa bayyanawa mutane a kafafan watsa labai, to amma wani abu mai cike da sarkakiya shine, bayan da aka doki wannan gini babu ko alamar wannan jirgi, wanda abin mamaki ne kwarai da gaske, ace jirgi ya doki gini amma kuma babu baraguzan jirgin, wannan ya sanya shakku sosai dangane da ainihin abinda ya doki wannan gini, shin jirginne da gaske? Ko kuwa wani abune daga cikin ginin ya tarwatsa shi? Bugu da kari, bayan da aka ce jirgi ya doki ginin a hawa na can sama, sai gashi ginin dake hawa na daya da na biyu duk sun kama da wuta, zai zama abin mamaki kwarai da gaske ace irin haka ta faru, sannan kuma da abin ya faru ginin ya kama zagwanyewa yana yin kasa, duka wadannan abubuwan mamaki ne, domin ya akayi baraguzan jirgin suka bace bat sama ko kasa? Sannan ta yaya gine-ginen kasa suka kama da wuta? Sannan tayaya akayi daga dukan gini sai ya zagwanye gabaki daya? Yana da kyau mai karatu ya sani duk wannan anyi ne domin a rudi duniya da sanya shakku a tattare da mutane.

Yana da kyau mu fahimta duk wannan abin da ya faru fitina ce wadda CIA suka shirya ta, tare da manyan kiristoci domin su tayar da hankali duniya, kuma akayi amfani da rubabbun musulmi masu son abin duniya domin cimma wannan mugun nufi na matsafa ‘yan mafiya. Kuma duk sunyi karatunsu a Amerika aka yi amfani da su domin cimma wannan boyayyar manufa, daga cikin mutanan da Amerika tayi amfani da su akwai Shugaban Afghanistan na yanzu Hameed Karzai wanda Ba-Amerike ne dan Aghaninstan yana aiki a kamfanin mai a Amerika aka dauko shi domin a yi amfani da shi wajen rusa musulunci da Afghanistan, lokacin da ya zo ko birnin kabul bai gama sani, sannan kuma Amerika sunyi amfani da wani mutum Zalmey Khalil Zadeh a matsayin jakadansu a Afghanistan; a can kuma munga yadda aka yi amfani da su Nuri Al-maliki da Iyad Alawi a Iraqi.

Da aka tambayesu (Amerika) cewa ina buraguzan jirgin da ya doki wannan gini? sai suka ce ya narke ya shiga cikin karikitan ginin. Wanda kamar yadda muka sani mafi yawan hatsarin jirgi idan ya faru yakan bar sassan jikinsa, amma wannan da ya faru babu ko da kusa daga cikin sashin jirgin, kuma suka yi amfani da kafafen watsa labaransu suka sanya mutane suka yarda cewar sassan jirgin sun narke a cikin baraguzan ginin.

Kamar yadda bayanai suka nuna, shi wannan gini ba dai-dai yake da sauran gine-gine ba, domin babu kasa kokadan a cikin ginin, karafane da gilasai da alminiyo a cikin gini gabaki daya. Wanda bayan wannan abu ya faru munga kura da hayaki sun turnuke, ta ina aka samu kura da hayaki a cikin ginin da akayi da karafa da gilasai? Mazon ALLAH Salallahu Alaihi Wasallam ya ja hankalin al’umma akan yadda a karshen zamani fitina zata kasance kamar kura da hayaki, kuma Alamu ne na zuwan mahadi yadda kura da hayaki zasu turnuke, daga nan kuma sai wasu fituntunu su biyo baya (Al-muttaki al-hindi, Al-burhan fi alamat al-mahdi Akhiriz zaman) Dan haka wannan hayaki da ya biyo bayan rubzawar wadannan gine-gine alama ce da take nuna zuwan fitina, wadda ya zuwa yanzu ta bayyana kowa ya ganta.

Daga cikin hikima ta injiniyoyi, ta nuna cewa wannan ginin ya tsufa yana iya faduwa, ginin yana bukatar a rushe shi a sake gina sabo. A gurare da dama a duniya akwai irin wannan hikimar ta rushe tsohon gini, sukan yi amfani da na’ura mai rushe gini, kamar yadda wannan na Pentagon ya faru, sannan a kama mutane da laifi, bayannan a sake su rana a tsaka, bayan ankama wanda ake son kamawa tun can usuli, wannan shine kusan abin da ya faru. A saboda ana zargin musulmi ne da kai wannan hari wannan shi ne zai bayar da damar mamaye Afghanistan da Iraqi da sauransu?

Domin mai karatu ya sake tabbatar da cewar wannan abu da ya faru duk shiri ne, na mafiyawan Amerika, ita wannan cibiya bayanai sun tabbatar da cewa wadannan Yahudawa barbarar yanyawa sune kusan suke mamayeta a kullum da harkoki na hada-hada, amma ranar da abin zai faru babu ko daya daga cikinsu da yaje wajen, sannan kuma anga wasu mutane daga nesa da suke ta dauko hotunan ginin ‘yan mintoci kadan kafin faruwar wannan al’amarin, abinda ya sake tabbatar min da cewa Amurkawa ne da kansu suka rusa wannan gini. Akwai wani fim mai suna THE SWORD FISH, ina fatan mai karatu ya samu dama ya kalli wannan fim din shakka babu zai tabbatar da cewar wannan abin da ya faru na rushewar wannan ginin daman can shiryayye ne. Kawai suna amfani da kafafan watsa labarai ne sun cin duniya da buguzum.

Bayan da wannan abin na 11 ga satumba ya faru, sai majalisar dokokin Amerika suka yi wata fargar jaji, inda suka kafa wata hukuma mai suna The National Commission On Terrorist Attack Upon The Us wadda aka fi sani da  (9-11 Commission) inda nan da nan Shugaba Bush ya sanya hannu dan tabbatar da wannan hukuma domin ta bayyana hakikanin abinda ya faru a wannan rana ta 11 ga satumba, inda suka dauke hankalin duniya daga ainihin inda gaskiya take zuwa sai abinda suka fadawa mutane, wannan hukuma sun saki wani rahoto na kanzon kurege akan abinda ya faru, kana iya duba wannan rariya domin ganin abinda suka ce http://www.9-11commission.gov/report/index.htm duk wannan ba komai yake nunawa ba illa kaiwa makura na makircin Amrika ga kasashen musulmi da kuma mamaye arzikinsu.

Haka kuma, marubucin littafin The Ghost Wars, mista Steve Call ya yi wasu bayanai masu sarkikiya a cikin wannan littafi da ya wallafa a shakarar 2004, inda ya yi bayanin cikakke akan kungiyar leken asiri ta CIA da kuma bayanin yadda gwamnatin Bush ta shiga Afghanistan da kuma abinda ya shafi Bin Laden. A wani fim Documentary wanda gidan talabajin na Al-jazeera suka haska acikin watan Yuli mai suna I KNEW BIN LADEN wanda suka yi isharori masu sarkakiya akan abinda ya faru, domin anyi hira da mutane na kusa da Bin Laden.

Kungiyar leken asirin Amurka ta CIA kusan ta fara aikin leken asiri a kasashen duniya kusan tun zamanin shugaban Amurka na farko wato George Warshington, amma bata zama cikakkiyar hukuma ta gwamnati ba sai zamanin da akayi yakin duniya na biyu inda ta rika bada rahotannin asiri, a lokacin ne shugaban Amurka na wancan lokacin Franklin D Rooservelt ya nada babban lauyan binrnin New York Williams J Danovan  a matsayin shugabanta na farko, wanda tsohon masanin yaki ne, kuma tsohon masanine a harkar da ta shafi binciken kwakwaf.

CIA kusan babu wata kungiya mai hadari a duniya sama da ita. Wannan kungiya kusan dukkan kasashen duniya babu inda bata aiki, sannan babbar hanyarsu ta samun bayanai sune ta hanyar amfani da jakadunsu dake kasashen duniya domin aiko musu da rahotannin yadda al’amura ke kasancewa, suna amfani da mutane da yawa a cikin kasashen su domin su ringa basu bayanai na asiri, ba tare da wadan da ake aikin da su sun san me ke faruwa ba. A shekarar 2004 shugaba Bush ya sake inganta aikin CIA inda ya sanya hannu a ranar 14 ga watan Disamba akan gyaran fuska da akayiwa dokokin CIA da suka kira Terrorism Prevension Act.

Tambayar da wata kila wasu ‘yan uwa zasu iya yi ita ce wannan abinda ya faru na 11 ga satumba shine silar mamaye Afghanistan da Iraqi ko kuwa akwai wata manufar daban? Kuma ina matsayar yunkurin kamfanin Unocal na shimfida bututun iskar gaz a Afghanistan ya tsaya? Insha ALLAH zamu zo da bayani akan haka, anan gaba.

Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale

   

Sunday, October 7, 2012

ZABEN AMERIKA: Abinda Mutane Da Yawa Basu Fahimta Ba (4)



ZABEN AMERIKA: Abinda Mutane Da Yawa Basu Fahimta Ba (4)

Kasashen yammacin turai karkashin jagorancin Amerika basu damu da duk wani jini da zai zuba ba indai bukata zata biya, matukar jinin ba na Amerikawa bane ko na turawa ja-ja-yen fata ba. Babbar manufar ‘yan jari hujja ita ce shigar da kwadayi da hadama da babakere akan kimar haja tun kafin lokacin amfaninta ya zo, dan haka tsarin jari hujja ya ginu ne akan cin gwagwgwabar riba a harkar kasuwanci, ‘yan jari hujja zasu iya baiwa ko wace haja irin kimar da bata da ita, kuma jama’a su raja’a akanta abinda Karl Max ya korawo da sunan ‘Tsatsube’ bisa wannan ka’idar ‘yan jari hujja zasu iya maida kimar Ruwa ta fi ta Zinariya ko Tagulla.

Idan muka koma yankin tafkin caspean zamu ga cewar bayanai sun tabbatar da cewar akwai gangar danyan mai a kwance a wannan tafki da ta kai kusan ganga sama da biliyan 49, wannan antabbatar da samuwarta, sannan kuma ana hasashen samun karin wasu ganguna da suka tasamma biliyan 500 zuwa sama. Dan gane kuma da bayanin Iskar gaz da ke wannan yanki, har yazuwa yanzu babu wasu al-kaluma da suka tabbatar da adadinta amma sai dai babu wanda yake shakkar cewar yankin yana tattare da iskar gaz mai dankaren yawan tsiya, sai dai daga lokaci zuwa lokaci kasashen da suke kewaye da wannan yanki sukan fitar da alkaluman da suke ganowa na dimbin makamashin da yake yankin, kasashen sun hada da Rasha da Iran da Azarbaijan da Turkministan da kuma Kazakstan.

A shekarar 2011 ma’aikatar mai ta Iran ta bayyana gano makamashin iskar gas dake bangarenta da ya kai cubec mitre tiriliyan daya a gabar ruwanta. A cikin watan oktoban shekarar 2011 kamfanin mai na TOTAL ya bayyana gano iskar gaz a gabar ruwan kasar Azarbaijan da ta kai cubec mitre biliyan 350, sannan kuma a cikin filin Talotan na kasar Turkumistan an bayyana gano makamashin Iskar gaz da ya kai Tiriliyan 21.1 a ma’aunin cubec mita, kasashe guda biyu kawai Kazakstan da Turkministan suna da dimbin makamashin iskar gaz a gabar ruwansu da ya kai kimar dalar Amurka Tiriliyan 12.

A zamanin rusashshiyar tarayyar sobiya ita da Iran ne kadai suke raba arzikin wannan yanki na caspean dai-dai-wa-dai-da bisa yarjejeniyar da suka kulla tun cikin shekarar 1921 domin sauran kasashen da suke kewaye da wannan yanki na caspean duk suna karkashin tarayyar Sobiya ne a matsayiin jamhuriyoyi. Rushewar da tarayyar sobiya ta yi a 1991 shine abinda ya karfafawa manyan kamfanonin ‘yan jari hujjar Amerika guiwa inda suka fara nuna kulafucinsu a fili akan arzikin da yake wannan yanki. Kamar yadda muka fada a baya cewa sanannen abu ne cewa akwai aure irin na katolika tsakanin gungun kamfanonin ‘yan jari hujjar Amerika da kuma duk wani shugaban Amerika da aka zaba da kuma dukkan manyan jami’an gwamnati masu fada aji.

Babbar matsalar da ba’a warwareta ba shine ta yaya za’a debo arzikin da yake dankare a wannan tafki na caspean zuwa inda ake da tsananin bukatarsa. Dan haka wadannan gungu na Corporate Capitalism na Amerika suka tabbatarwa da kansu cewar mafitar wannan arziki da yake wannan yanki shine a gina hanyar al-hariri wato Silk Road wadda za’a debo wannan arziki zuwa inda ake so, sai dai yin hakan ba abu bane mai sauki domin akwai matukar wahala da hadari tattare da yin hakan, amma kuma romon da yake cikinsa shine yake rinjayarsu.

Ta hanyoyi guda uku ne kadai za’a iya fito da wannan arziki na makamashi zuwa Amerika. Wato kasar Chana tayi iyaka da tafkin caspean ta gabas, sannan kasar Rasha da Iran da Turkiyya sunyi iyaka da shi ta yamma, sai kuma Afghanistan da Pakistan suka yi iyaka da shi ta kudu. Tsarin farko da kamfanin UNOCOL (Wanda Iyalan Bush da Bin laden suke da hannu jari acikinsa) ya fito da shi akan yadda za’a shimfida bututun da zai dauko makamashin kasar Turkuministan, shine za’a shimfida bututun dai zai ratsa ta kasar Afghanistan ya bi ta birnin karachi na Pakistan daga nan kuma ya tuke zuwa ga tekun indiya wato Indian Ocean. Wannan shine kalubale na farko da wannan kamfanin ya zai fuskanta, duba da cewar kasar Afghanistan tana fama da yakin basasa tun bayan ficewar Rasha tsakanin ‘yan Taliban da kuma gamayyar kungiyoyin Norhern Alliance karkashin jagorancin Sha Ahmed mas’ud.

Dan haka wannan kamfani ya yi amfani da wannan damar wajen kutsa kansa cikin yakin basasar Afghanistan dan share hanya ga bututunsa da zai ratsa Afghanistan ba tare da ya fuskanci wata tirjiya ba. Dan haka, a bisa shawarar da jakadan Amerika a Pakistan Robert Oakley ya baiwa wannan kamfani dan haka, kamfanin ya kulla kawance da kungiyar Taliban wadda a wannan lokaci ikon da suke da shi bai wuce birnin Kandahar ba kawai, bisa cikakken hadinkai daga gwamnatin Bill Clinton ta wannan lokaci da kuma taimakon kungiyar leken asiri ta Amurka CIA aka kulla wannan alaqa tsakanin kamfanin da Taliban ta wancan lokacin. A wannan lokacin Osama  Bin Laden yana Afghanistan, dan haka ina mai cike da shakkun sahihanci ko gaskiyar Osama Bin laden cewa ba Amurka ne suka yi amfani da shi domin cimma wannan nufi na su ba, idan mai karatu bai mantaba a baya mun fada cewa shi wannan kamfani Iyalan Bush da Bin Laden suna da hannun jari a cikinsa.

Hikimar kulla wannan kawance tsakanin ‘yan mafiya na makamshi daga Amurka da kungiyar Taliban ta ‘yan takife ya bayyana kamar wata daran goma sha biyar a lokacin da Ted Roll ya rubuta wata kasida a cikin San Francisco Chronicle ta ranar 2 ga watan Nuwamban 2001, wato wata guda kenan bayan harin 11 ga watan satumba a tagwayan cibiyar kasuwancin Amurka, ina fatan mai karatun da yake bina ya alakanta wannan bayanai da suka gabata da kuma harin 11 ga watan satumba, ya gani akwai alaka ko babu! Ga abinda Ted Roll yake cewa “idan ka sami danyan man fetur din da ba’a fara taba shiba, sannan kuma kana da bukatar dibarsa, sai ka kulla yarjejeniya da gwamnatoci masu karfi wadanda suke da kusanci da kamfanonin mai na Amerika. Dan haka tsari mafi dacewa shine a shimfida bututun da zai ratsa Afghanistan ya bi ta karachi har ya bulle bakin gabar ruwan Arebiya, sai dai mutanan Afghanistan sun kasa kafa gwamnati saboda yakin basasar da yake a tsakaninsu. A saboda haka abinda ya kamata ayi shine abinda CIA ta ringa yi na kafa gwamnati mai kawo zaman lafiya ‘a fadarsu’ Gwamnati wacce zata kawo karshen yakin basasa sannan ta bada kariya ga bututan da kamfanin UNOCAL zai shimfida da zai ratsa ta Afghanistan”.

Wani marubuci Stave Coll ya fada a cikin wani littafi da ya rubuta mai suna Ghost War cewa kamfanin mai na Unocal ya taimakawa da kungiyar Taliban da kudaden da makaman da ta yi amfani da su wajen kame birnin kabul daga hannun ‘yan Northern Alliance a cikin shekarar 1996. Shi kuwa Ted Ross ya fada cewa kungiyar taliban ta samu bayanan sirri akan Northen Alliance a hannun CIA tare da kugiyar leken asirin Pakistan. Allah ne kadai yasan adadin mutanan da suka hallaka daga Kandahar zuwa kabul domin baiwa Taliban ikon kafa gwamnati a Afghanistan, a mastayin share fage ga kamfanin Unicol domin safarar arizkin Iskar gaz daga yankin gabas mai nisa zuwa Amerika da sauran kasuwannin duniya.

Bayan da taliban ta samu shekaru biyu da samun gindin zama a Kabul, gwamnatin Amurka ta wancan lokacin ta gayyaci ministocin Afghanistan har Warshington domin tattaunawa. Anyi wata ganawa ta musamman da karamin ministan harkokin wajen Amerika mai kula da kudancin Asiya Karl Inderforth da wadannan ministoci daga Afghanistan, daga cikinsu akwai ministan ma’adanai da masana’antu Ahmed Jan da ministan Al’adu Amr Muttaqi da kuma ministan tsara dabarun ayyukan taliban Deen Muhammad, ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar da sanarwar wannan ganawar a matsayin wani muhimmin ci-gaba.

Kamar yadda masu iya magana suke cewa yaki dan zamba ne, babban makamin da Amurka ke amfani da shi a karon farko a duk harkar yaki shine kafafan watsa labarai inda take cin mutane da buguzum. Tambaya anan ita ce shin suwaye hakikanin wadanda suka shirya harin 11 ga watan Satumba? Suwa ke da alhakin kai harin? Me ye ya sa Amerika ta shiga Afghanistan da karfin tuwo tun bayan wannan hari?

Mu hadu a muqala ta gaba domin jin wasu bayanai masu sarkakiya dangane da wannan batu.

Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale






Saturday, October 6, 2012

ZABEN AMERIKA: Abinda Mutane Da Yawa Basu Fahimta Ba (3)



ZABEN AMERIKA: Abinda Mutane Da Yawa Basu Fahimta Ba (3)

Ina fata masu bina basu manta inda muka tsaya ba, a mukalar da ta gabata, wato mun tsaya da bayani, inda Amerika ta kitsa yakin Iraqi domin ta mamaye danyan man fetur, yanzu kuma zamu dan sauka daga kan wannan batu domin mu duba wani batun da yake da alaka da siyasar ta Amerika.

A shekarar 2009 da ta gabata Shugaban kasar Rasha Dmitry Medvedev ya kawo ziyarar aiki zuwa Najeriya, inda ya gana da tsohon shugaban kasa marigayi Umaru Musa YarAdua. Wannan ziyara da shugaban Rasha Medvedev ya kawo zuwa Najeriya ba wata ziyara ce ta Allah da Annabi ba illa ta kokarin da kasar Rasha take yi na fadada ikonta akan makamshi, domin akarkashin wannan ziyara kamfanin Gazprom na Rasha ya rattaba hannu akan wata yarjejeniyar zuba jari a Najeriya da takai kusan dala Biliyan biyu da rabi ($2.5b) a Najeriya. Kuma sannan kamfanin ya sanya hannu akan wata kwangila da kamfanin NNPC na Najeriya ta shimfida bututun iskar gaz wanda zai tashi tun daga garin Warri a Najeriya domin ya isa kasar Rasha, wannan aiki na shimfida bututun iskar gaz zai tashi tundaga wannan gari na Warri ya ratsa ta Jamhuriyyar Nijar sanna ya bi ta garin Hassi Ramel dake kasar Al-jeriya, daga nan kuma ya hade da cibiyar da take baiwa nahiyar Turai iskar gaz dake gabar Tekun Meditareniya.

Duk wannan bayani bai wuce batun da ya shafi tattalin arziki ba tsakanin kasar Najeriya da kuma Rasha, ba komai wannan yake nunawa ba illa irin yadda kasar Rasha take son nuna karfinta ga abokiyar burminta Amerika akan harkar da ta shafi makamshi a duk inda yake a fadin duniya. Najeriya dai bata wuce wani dan karamin filin yaki ba a tsakanin kasar Rasha da kuma kasashen yammacin turai bisa jagoranci Amerika ba, domin babban filin daga ga wadannan kasashe shi ne yanki gabas mai nisa na tsakiya da kuma yankin gabas ta tsakiya, domin yankin gabas ta tsakiya nanne inda Allah ya huwacewa dimbin arzikin makamashin gurbataccan manfetur da dangoginsa, shi kuma, yankin gabas mai nisa na tsakiya wato Far East ko Asiya ta tsakiya wani yanki ne da Allah ya hore masa dimbin arzikin makamashin isakar gaz.

Wani marubuci Naomi Chvosky ya ce “a zahirin gaskiya Amerika tana son ta mallaki duk wani makamshi da ke fadin duniyar nan domin shimfida iko wanda zai taimakawa manyan masana’antunta” duba da wannan magana, zamu ga cewa mafi yawancin man fetur din da Najeriya take fitarwa yana zuwa Amerika ne kai tsaye, dan haka kuwa babu yadda Amerika zata bari kasar Rasha ta mamayi duk wata harka ta makamashi da ta shafi Najeriya.

Yanzu haka a wannan karnin da muke ciki na 21 gabaki daya hankalin kasar Amerika ya karkata ne zuwa ga abinda ya shafi makamashi musamman na iskar Gaz, wanda Rasha ta dade da yin fice akansa. Wannan ce ta sanya tsohon shugaban kasar Rasha da ya sauka Vladmire Putin ya karkato da hankalin Rasha zuwa ga abinda ya shafi harkar siyasar kasa da kasa da kuma sauran siyasar duniya da kuma tattalin arziki; domin a cikin ilimin kasa da kasa da ake kira da suna International Relations akwai wani muhimmin batu da ya ke magana akan siyasa da tattalin arziki, wannan ce ta sanya kasar Rasha taga babu yadda zata yi face ta kulla kawancen siyasa da kuma tattalin arziki da kasar Chana da Iran akan yankin Gabas mai nisa ta tsakiya ko kuma Asiya ta tsakiya, domin yanki ne mai sarkakiyar gaske, kuma mai dimbin arzikin makamashi.

Wani muhimmin darasi da kasar Rasha ta dauka daga yakin cacar baki tsakaninta da yammacin Turai a karkashin jagorancin kasar Amerika shine gasar kera makamai, domin wannan shine abinda ya yi saurin karya Rasha a hannun abokan gabarta, domin shugaban Amerika Ronald Regan ya ringa kiran rusashshiyar tarayyar Sobiya karkashin Rasha da cewa wata muguwar daula ce mai tsotse bargo da laka gabaki daya. Dan haka tun a shekarar 2000 da Putin ya zo a sabon shugaban Rasha ya yi kokari wajen mayar da Rasha wata muhimmiyar kasa a fagen kera makamai da kuma iskar gaz, domin har yanzu Rasha ita ce ke bin bayan Amerika a fage kera makamai, Rasha ta karfafa ikonta sosai akan kamfanin Gazprom wajen yawaita hannun jarinta a wannan kamfani.

Tsohon shugaban kasar Rasha Boris Yeltsin bai haifarwa da Rasha da komai ba a fagen siyasar tattalin arziki face samar da ‘yan mafiya masu son mamaye makashi ta ko wace fuska, wadanda mafiya yawancin wadannan ‘yan mafiya Yahudawa ne masu biyayya ga kasar Israela, irin wadannan gungu na ‘yan mafiya ne, Shugaba  Putin yayi ta kokarin ganin ya kakkabesu dan ganin ya shimfida nasa ikon, har kuma hakarsa ta cimma ruwa, inda yaci nasarar kafa na hannun damarsa wato shugaban Rasha na yanzu Dimitry Medvedev a matsayin shugaban kamfanin Gazprom, wannan mutum Medvedev shine suka yi musayar shugabanci da Putin bayan da wa’adin Putin ya kare a matsayin Prime Minista da kuma shugaban kasa, wanda wannan shine yake kara tabbatar da auren din-din-din tsakanin siyasa da kuma makamshi a wajen fadar gwamnatin Kremlins da ke Moscow.

Ita kanta kasar Rasha kasa ce da Allah ya huwacewa dimbin arzikin iskar gaz da ke kwance a karkashin dusar kankarar Saberia. Domin a manya manyan filayan da Rasha take da su a wannan yanki a kwai wani fili da ake kira da suna Urengoy wanda daya ne daga cikin wadannan filaye akwai dimbin makamshin iskar gaz da ya kai kimamin cubic metre Tiriliyan goma (10tr). A rahoton kungiyar Tranferency Internatinal akan kasar Rasha, ya nuna cewa ita ce wacce tafi kowace kasa arzikin iskar gaz a duniya domin ita kadai nata yakai kimanin kashi 24% na adadin dukkan Gaz din da ke wannan duniyar, a yayinda kasar Iran ke biye da Rasha da kaso 16%, sannan kuma, kasar Qatar ke biye da Iran da kaso 10%.

Watakila mai karatu ya ce daga maganar siyasar kasar Amerika kuma mun bige da bayani akan kasar Rasha. Shakka babu kamar yadda na fada kusan tun a farkon mukalarmu cewa siyasar Amerika tana cike da sarkakiya da kutunguila acikinta. Domin siyasar kasar Amerika bazata taba cika ba idan ba’a kawo wadannan bayanai da suka shafi Rasha ba, domin suna da alaka da abinda ya shafi makamashi. Sannan kuma idan mai karatu ya lura munyi batun biyayyar mafiyan kasar Rasha ga Yahudawan Israela, wanda wannan shi kansa wani batu ne mai zaman kansa dangane da abinda ya shafi siyasar Amerika, domin su wadannan mutane na Corporate Capitalism kusan suma Yahudawa ne, sai dai daga su har na Rasha din bawai ainihin yahudawan da Allah ya bamu labarinsu a al’qur’ani bane, domin galibin wadannan Yahudawan na yanzu su Netanyaho da Yizhaq Rabil da su Ariel Sharon da Olmet da su Bill Clinton da Bush da sauransu duk barbarar yanyawa ne, ba Yahudawa ne zuryan ba. Haka kuma, baza ka taba yin bayanin siyasar Amerika ba tare da anyi batun kungiyar leken asiri ta CIA ba da kuma harkar kafafen watsa labarai, wadannan wasu muhimman al’amura ne a siyasar Amerika, wanda zamu yi bayaninsu nan gaba insha ALLAH.

Idan muka duba kuma, zamu ga cewa alakar kasar Rasha da kamfanonin makamashi na yankin Asiya mai nisa, ya fara ne kusan tun kafin rugujewar tarayyar Sobiya, domin har yanzu wannan dadaddiyar alaka tana nan. A shekarar 2007 da ta gabata kamfanin makamashi na Rasha Gazprom ya karbi kusan kashi 75% na dukkan makamashin da kasar Turkministan ta fitar, wanda ya kai kimanin ma’aunin cubec metre biliyan 42.6. sannan kuma, daga kasar Kazakstan ya kai kimanin biliyan 8.5, haka kuma, itama kasar kazakhstan ya kai biliyan 9.4; anan dole mai karatu ya lura sosai domin akwai bambanci tsakanin kasar KAZAKSTAN da kuma KAZAKHSTAN. Wadannan kasashe sune kasashen da suka fi kowace kasa  arzikin iskar gaz a yankin Asiya mai nisa ta tsakiya, dan haka, adadin iskar gaz dinda kamfanin Gazprom ya karba daga wadannan kasashe ta kai kimanin tiriliyan 60.7 a ma’aunin cubec mitre acikin shekara guda daya kacal.

Muhimmancin da wannan yanki yake da shi, a wajen kasar Rasha ya dara wanda yankin gabas ta tsakiya yake da shi a wajen kasar Amerika, a saboda haka irin muhimmancin da yankin gabas ta tsakiya yake da shi a wajen Amerika kamar tankin mota ne a wajen mai tuka mota, dan haka duk irin sansanonin sojin da Amerika take da su a wannan yanki bai wuce na ganin duk arzikin manfetur din yankin bai subuce mata ba, hatta irin kariyar da Israela take samu daga Amerika duk yana ta’allake da wannan arziki na makamashin manfetur ne, domin yanzu da za’a wayi gari ace babu wannan arziki a yankin gabas ta tsakiya, ita kanta kasar Israela sai dai ta san inda dare ya yi mata.

A saboda kasar Rasha ta samu gindin zama wajen gaje moriyar arzikin wadannan kasashe na gabas mai nisa sai ta yi kokarin kafa wani kawancen da aka ce ba’a so a sami sabani, tsakaninta da kasashen wannan yanki wadan da suka hada da kasar Chana wadda ita ke zaman a matsayi na biyu bayan Rasha wajen cin-moriyar makamashin iskar gaz da yake fita daga wannan yanki, wannan kawance shi aka kira Shanghai Corporation Organization wanda ya kunshi kasashen Asiya ta tsakiya guda hudu da suka hada da Kazakhstan da Kyrgistan da Uzbakistan da kuma Tajkistan, tun bayan kafa wannan kungiya a shekarar 2001 sai ga kasar Amerika a 2006 ta kawo kokon bararta cewa wadannan kasashe su yiwa Allah su sanyata a matsayin ‘yar kallo a cikin wannan kawance, wanda karkashin jagoranci Rasha suka yi fatali da wannan roko na kasar Amerika.

Idan mai karatu bai manta ba,  a baya can  munyi maganar tekun caspean sea wanda muka ce yana da dumbin arzikin makamashi wanda har mafiyoyin Amerika suka fara nuna kulafucinsu akansa, da tunanin yadda za’a hako shi zuwa kasar Amerika. Insha Allah a mukala ta gaba zamu maida hankali ne akan wannan yanki, da bayanin yadda Amerika da Rasha  suka haifar da yakin kasar Afghanistan domin samun hanyar da zasu shirya bututun da zai dauko wannan arziki zuwa kasashensu, wannan batu na arzikin da yake a tekun Caspean sea shima wani batu ne mai sarkakiyar gaske dangane da siyasar kasar Amerika, amma da sannu insha Allah zamu warwareshi domin jama’a su fahimci yadda al’amarin yake.

Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale



Thursday, October 4, 2012

ZABEN AMERIKA: Abinda Mutane Da Yawa Basu Fahimta Ba (2)



ZABEN AMERIKA: Abinda Mutane Da Yawa Basu Fahimta Ba (2)

Siyasar Amerika tana da fusaka biyu, wato akwai wadda ake yi ta zahiri wadda Amerikawa suka sani kuma suke bibiyarta, wato siyasar Amerika ta cikin gida wadda ta shafi Amerikawa. Da yawan Amerikawa gidadawa ne, ta yadda basu san galibi yadda al’amura ke gudana tsakanin Amerika da sauran kasashen duniya ba. Kamar yadda a kasar Meseddoniya a kullum tarbiyyar da ake yiwa ‘yan kasar shine daga Allah sai mesedoniya, haka itama Amerika, kullum tarbiyyar da ake baiwa Amerikawa shine daga Allah sai Amerika, dan haka ne aka jahiltar da mafiya yawansu akan abinda ya shafi hakikanin alakar Amerika da sauran kasashen duniya, sannan aka dauke musu hankali ta hanyar shagaltar da su da abubuwa na more rayuwa da jin dadi.

Wannan ta sanya kullum Amerikawa basu da wani tunani sai abinda ya shafi aikin yi, jima’i wanda ya hada da morewa da jin dadi da shakatawa da kuma hutun karshen wata ko na karshen shekara. Wannan kusan sune suka damu da yawa daga Amerikawa na zahiri da muke gani, dan haka nema, duk wasu abubuwa na banza da wofi da bata lokaci sai kaga Amerikawa sun basu muhimmanci, kamar kallon karrama taurarin fina-finai na Hollywood, kallon namun daji, linkayawa a bakin kogi (beach) da sauran sharholiya, haka kuma, su Amerikawa wannan shine ya damesu. Dan haka sukeyiwa sauran kasashe musamman na musulmi wani irin kallo a matsayin na Abokan gabar Amerika, saboda abinda ake watsa musu a kafafa watsa labarai kenan.

Kamar yadda dubban mutane suka kalla a ranar larabar nan da ta gabata 3 ga watan oktoba, anyi muhawara ta fako tsakanin Obama da Romney. Wadda a wannan muhawara aka tabo abinda ya shafi siyasar Amerika ta cikin gida. Mista Jim Lehrere na kafar watsa labarai ta PBS Newshour shine ya jagoranci wannan muhawara da ta hada Obama da Romney a karon farko a bainar jama’a, wadda abinda aka tabo a wannan muhawara kusan abubuwa ne da duk wanda yake bibiyar siyasar Amerika ta zahiri ya sansu, wato batun nan mai cike da kalubale na Tsarin kiwon lafiya na Obama (health care), da batun makomar tattalin arzikin kasar Amerika anan gaba (The future of the Economy), da kasafin kudin gwamantin tarayyar Amerika (The federal Budget), da kuma batun bashin da ya dabaibaye Amerika, wanda Amerika ita ce kasar da tafi kowace kasa yawan bashi a duniya (The National Debt) domin yanzu batun da ake suna da bashin da ya kai Dala Tiriliyan goma sha shida ($16t) wanda idan ka kwatatanta da na Najeriya da Gej ya ciwo ($45b) bai wuce kudin shan-shayi ba akan na Amerika.

Haka kuma, batun da Amerikawa suka fi damu da shi shine abinda ake kira da turanci DEFICIT wato abinda Amerikawa suke kashewa yana dara abinda suke samu na albashi, da kuma batun samar da aikin yi yake taka muhimmiyar rawa, yanzu rashin aikin yi a Ameriaka yakai kashi takawas (Unemployment rate 8%), wanda kusan shine agaba wajen abinda ya damu Amerikawa. Sannan da wani batu da aka jima ana yin takaddama da shi tsakanin Obama da Romney shine na batun haraji akan hamshakan mutane da kuma talakawa (Tax cut). Kusan wadannan a takaice sune suka mamaye wannan muhawara da akayi a jihar DENVER, sannan za’a cigaba da wannan muharawa tsakanin ‘yan takarar biyu ranar 16 ga watan Oktoba a jihar New York wadda zata dora akan abubuwan da aka faro tattaunawa akansu ne, sannan kuma da muhawara ta karshe wadda za’a yi a ranar 22 ga watan nan na oktoba za’a karkare wannan muhawara a jihar Florida wadda zata maida hankali akan siyasar Amerika ta daya bangaren mai cike da sarkakiya wato siyasar Amerika da kasashen duniya da suke cewa Foriegn Plocy.

Tun bayan faduwar tsohuwar hadaddiyar tarayyar sobiya (USSR) a shekarar 1991, kasar Amerika ta samu damar shuka irin abinda ta ga dama da kuma shigewa gaba wajen yin yadda taga dama da kasashen duniya wanda ake kira UNILATERALISM, a wannan lokacin Amerika ta yi ta shimfida hanyar da zata mamaye duniya musamman a goman karshe na karni na 20 wato daga 1991 zuwa 1999. Ta shirya tsaf tare da kammala shirinta akan mamaye dimbin albarkatun manfetur da ALLAH ya huwacewa yankin GABAS TA TSAKIYA, domin bayanai sun tabbatar da cewar da akwai gangar danyan man fetur fiye da ganga Biliyan 350 a kwance a kasar IRAQI wanda ya dara man da kasar SAUDIYYA take da shi a yankin gabas ta tsakiya, domin bayanai sun tabbatar da cewar Saudiyya tana da gangar danyan mai da ta kai ganga Biliyan 267. Wannan batu na mamaye albarkatun danyan man da ke yankin gabas ta tsakiya shine ya sanya Gwamnatin Amerika karkashin George Wolter Bush ta shiga Iraqi da karfin tuwo a shekarar 2003, inda suka yaudari duniya da cewar marigayi Saddam Hussain ya mallaki makaman kare dangi. Duk kuwa da cewar hukumar dake kula da makamashin Nukiliya ta duniya IAEA karkashin Mohammed el-Baradai ta tura tawaga mai karfi karkashin Hans Blicks wanda suka je sukayi iya kar bincike basu ga komai ba.

Wannan yunkuri da Amerika take yi na mamaye dumbin arzikin gurbataccen mai da yake kwance a yankin gabas ta tsakiya shine ya sanya da yawa daga cikin kasashen gabas ta tsakiya suke cikin halin yaki kusan tun cikin karni na 20 har kawo yanzu. Kada ka bini bashin rantsuwa domin dukkan wadannan fadace-fadace da akeyi a yankin gabas ta tsakiya shirayyene daga kasar Amerika domin mamaye arzikinsu. Tun bayan da Amerika ta shiga Iraqi kuma ta hambarar da marigayi Saddam Hussein Allah ya jikansa, suka shiga watandar dan yan manfetur din da yake a kasar domin a karon farko anbaiwa katafaran kamfanin mai na Amerika Halliburtun ta hanyar reshensa mai suna KELLOG BROWN AND ROOTS kwangilar yashe tare da tsabtace rijiyoyin manfetur na Iraqi wadanda aka kona, sannan kuma aka sake baiwa kamfanin kwangilar sake samar da wasu sabbin cibiyoyin kula da danyan manfetur a Iraqi wanda ya kai kudi wajen dala biliyan 900.

Babbar alkiblar gwamnatin Bush da ta gabata shine, tana tare da ‘yan Mafiya masu mamaye duk wata harka da ta shafi makamashi da manfetur. Manuniya akan haka shine, daya daga cikin manyan kamfanonin mai na ARBUSO wanda shima Iyalan Bush wato Bush kakan George Bush suke da hannun jari mai karfi a cikinsa, haka kuma suma Iyalan Bin Laden suna da hannun jari mai gwabi a cikin wannan kamfani, wadannan hannun jari da wadannan hamshakan Iyalai suka mallaka ita ce ta haifar da wata alaka tsakaninsu mai cike da rudani, kuma mai cike da sarkakiya da dabaibayi, domin daga baya anrinka samun rashin jituwa wadda tana harsashe zuwa ga abinda ya faru na harin 11 ga watan satumba a 2001, domin jaridar The Los Angels Times ta ranar 8 ga watan fabrairun 2004 ta buga wani labari mai taken “Abubuwan da iyalan Bush suke dauka da daraja sune, yaki da dukiya da man fetur”.

Dick Cheny wanda idan bamu manta ba shine ya yiwa George Bush mataimakin shugaban kasa, shine kusan shugaban wani sashe na katafaren kamfanin nan na Halliburtun kamar yadda muka fada shahararre ne a Najeriya a harkar manfetur da dangoginsa, da kuma wasu kasashe da suka hada da na gabas ta tsakiya gaba daya da kuma kasashen Indonesia da Burma, haka kuma, tsohuwar shugaban hukumar leken asiri ta kasar Amerika kuma tsohuwar mashawarciya ta fuskar tsaro, har ila yau tsohuwar sakatariyar harkokin wajen kasar Amerika lokacin gwamnatin Bush, Dr Condolizzer Rice ta taba zama shugabar katafaren kamfanin mai na Chevron a shekarun 1999 zuwa 2000, wanda shima kamfanine na daya daga cikin wadancan shaidanu na Amerika wadanda sune suke juya duk wani shugaban kasar Amerika ya so ko bai so ba.

Dan haka domin wadancan gungu na Corporate Amercan Capitalism su cigaba da mamaye arzikin manfetur dake yankin gabas ta tsakiya sunyi ta yin amfani da wasu mutane a matsayin dodorido domin su sami damar yin yadda suke so, domin gwamnatin Bush ta yi amfani da wasu mutane domin cimma waccan boyayyar manufa irinsu Iyad Alawi a mastayin sabon shugaban Iraqi tun bayan hambare marigayi Saddam Hussein Allah ya jikansa, haka harka zo kan mutane irinsu Nuri A-Maliki da Ibrahim Al-Ja’afari duk wadannan mutane daga Amerika aka daukosu aka basu mukamai domin su sharewa wadancan shaidanu hanyar mamaye danyan man da yake kwance a Iraqi.

Mu hadu a kasida ta gaba.

Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale



Wednesday, October 3, 2012

ZABEN AMERIKA: Abinda Mutane Da yawa basu Fahimta Ba!



ZABEN AMERIKA: Abinda Mutane Da Yawa Basu Fahimta Ba!

Yanzu a wannan karni na ashirin da daya (21) kasar Amerika it ace kasar da take jagorantar tsarin jari hujja a duniya. Amerika it ace kasar da kusan tafi kowace kasa karfin tattalain arziki, da kuma, karfin makamashi, wanda yanzu kusan shi ne yake juya wainar siyasar duniya. Wato tsarin siyasa da karfin tattalin arziki, a wannan karnin baka samun karfin tattalin arziki sai ka mallaki karfin makamashi kamar yadda Henry Kissinger ya fada a hirar da ya yi da jaridar Daily Squab a ranar 27 ga watan Nuwamban 2011, inda yake cewa “wanda yake da iko akan makamshi, to ya sami iko akan kasashe” wannan iko da kasar Amerika take da shi kusan shi ne ya bata ikon juya kasashen duniya yadda taga dama.

Siyasar kasar Amerika ta sha bamban da siyasar sauran kasashen duniya musamman kasashen masu tasowa. Siyasar kasar Amerika tana cike da sarkakiya da kutunguila da makirci na kin karawa, sannan uwa uba kuma abinda yake jan linzamin siyasar kasar Amerika shine ‘tattalin arziki’. Wato baka iya zama mai fada aji sai kana da karfin tattalin arziki kamar yadda da yawa suke da masaniyar cewar kasar Amerika kusan it ace ke kan gaba wajen jagorancin kasashen duniya mafiya karfin tattalin arziki da ake kira da suna G20 da kuma kasashen masu karfin arzikin masana’antu na G8 dama ko ‘G’ wacece, duk zaka samu Amerika it ace take da karfin fada a ji a tsakanin Dukkan kasashen da suka kulla kawance.

Kusan tun bayan faduwar kakkarfar tarayyar Soviet wadda Rasha ta yiwa jagoranci Amerika ta samu damar cin karanta babu babbaka wajen yin yadda taga dama da kasashen duniya a mastayin jagorarsu. Duka da rusashshiyar tarayyar Sobiya karkashin jagorancin Rasha da kasar Amurka ba wani abu suke yiwa ba, illa irin dumbin arzikin makamshi da Allah ya huwacewa wannan duniyar, sai dai sun dan sha bamban ta wata fuska, domin ita kasar Rasha tafi mayar da hankalinta ne akan abinda ya shafi makamashin iskar Gaz, wanda nasan da yawa jama’a suna sane da katafaren kamfanin isakar gas dinnan na kasar Rasha da ake kira Gazprom. Dalilin da ya sanya kasar Rasha tafi mayar da hankali akan abinda ya shafi makamshin isakar gaz yana da alaka da yanayinsu na dusar kankara a Rasha da kuma gabashin Turai, wanda wannan kamfani na Gazprom kusan shine babban kamfani mallakar Rasha da yake samar da makamashin isakar gas ga ita kasar rashan da kuma kasashen da ke gabashin Turai harma da na yammacin turai; sanna kuma ita a nata bangaren kasar Amerika tafi mayar da hankali ne akan abinda ya shafi gurbataccan man fetur da dangoginsa, saboda manayn masana’antun da take da shi.

Dan haka siyasar kasar Amerika kusan tana tafiya ne kacokaan akan abinda ya shafi cigaba da mamayar tattalin arzikin kasashen duniya. Ina jin jama’a bazasu manta da kamfanin kasar Amerika mai suna Halliburton ba, wanda aka zarga da badakar cin hanci ta dubban miliyoyin daloli akwanakin baya a Najeriya, shi wannan kamfani mallakar wasu manyan attajiran kasar Amerika ne wandanda kuma sune suke juya akalar siyasar kasar Amerika, shi wannan kamfani wanda cibiyarsa take a Texas, Iyalan Bush da Iyalan Bin Laden suna da hannun jari mai girma acikinsa. A kashin gaskiya siyasar Amerika kusan tafi ta kowace kasa makirci da mafiyanci da kutunguila da kuma sarkakiya, sanannen abu ne cewar akwai alaka mai karfi tsakanin manyan kamfanonin jari hujja na Amerika da ake kira Corporate Capitalism da gwamnatin Amerika, domin wadannan gungu na mafiyawa sune suka shigar da duk wani shugaban kasar Amerika fadar white House da kuma wakilan majalisar dokoki da ta dattabai, dan haka sune suke samar da shugabannin Amerika da wakilai wadan da zasu kare manufofinsu na kasuwanci.

Tsohon shugaban kasar Amerika Franklin D Roosevelt  ya taba fada a gaban majalisar dokokin Amerika a ranar 29 ga watan Afrilun shekarar 1938 cewa “cin gashin kai na tsarin demokaradiyya ba zai taba zama cikin aminci ba, idan har akwai wasu tsirarun mutane da suka kafa wasu cibiyoyi da karfinsu ya fi na gwamnatin demokaradiyyar da jama’a suka zaba. Wannan yana nufin cewa gwamnati ta zama ta wasu dai-dai kun mutane da wasu cibiyoyi da zasu ringa sarrafa ta daga nesa kenan”. A hakikanin gaskiya wannan shine abinda yake faruwa dangane da siyasar kasar Amerika, duk ihun da wani shugaban kasar yake yi ko daga Democrat yake ko daga Republican yana yi ne karkashin kulawar wadannan shaidanun mafiyoyi.

Wani muhimmin misali akan haka shine, daya daga cikin manyan kamfanonin mai na kasar Amerika mai suna UNOCAL ya taba nuna maitarsa a bainar jama’a dangane da dumbin albarkatun makamashin da suke kwance a tafkin Caspian sea, daya daga cikin manyan shugaban kamfanin mai kula da alaka tsakanin kasa da kasa Mista John J Merosca ya taba gabatarwa da kwamatin dake kula da alaka tsakanin kasashen na majalisar dokokin Amerika a ranar 12 ga watan fabrairu na shekarar 1998 cewa “ akwai dumbin albarkatun makamashi da Allah ya huwacewa yankin tekun Caspian”  daga nanne kuma ya yi wata ishara mai cike da kitumurura waddaa zata kai ga shimfida bututan da zasu kai ga hako wadannan albarkatu da ke kwance a wannan tafki.

Yana da kyau mu fahimta cewa babu wani bambanci na kuzo mugani dangane da siyasar cikin gida da waje tsakanin manyan jam’iyyun kasar Amerika guda biyu wato Democrat da Republican. Kasar Amerika kusan sha-kundum ce, siyasar kasar Amerika ta wuce ayi kamfe da suna wutar lantarki ko ruwan famfo ko harkar lafiya ko harkar ilimi, fiye da shekaru dari kasar Amerika ta fitar da kanta daga wannan mastalar, dan haka wadannan sunyi kadan su mamaye siyasar kasar Amerika.

Bugu da kari, ga duk wanda yake bibiyar yakin neman zaben da ake yi tsakanin Barack Obama da Mitt Romney kusan batu ne guda uku da suke jayayya akansa! Abu na farko shi ne, Shin kasar Rasha abokiyar gabar Amerika ce ko kuwa kawarta ce da akewa juna kallon hadarin kaji, sannan kuma da batun Shin akaiwa Iran hari a yanzu ko kuwa sai wani lokaci na nan gaba, duk kuwa da cewa shi kansa wannan batu na kasar Iran wani batu ne mai cike da sarkakiyar gaske, haka kuma, da batun shin Amerika zata jibge dakarunta a kasar Syria ko kuwa. Wanda wannan batu na Syria yake kara nuna cewa ba mai karewa da wuri bane domin shima yana cike da makirci da kutunguila irin ta shaidanun ifuritan Amerika masu juya tsarin jari hujja, sannan da ibilisan kasashen irinsu Rasha da chana da Iran. Kada ka dada kada ka raga wadannan sune manyan batutuwan da suka mamaye yakin neman zabe tsakanin Obama da Romney.

Abinda zai kara tabbatar da cewar duka wadannan jami’iyyu na Amerika bakisnsu daya, inda suka saba shine wajen aiwatarwa, misali jami’iyyar Democrat ta Bill Clinton ta shiga kasar Afghanistan ta hanayr tattaunawar Diplomasiyya, yayin da jam’iyyar Republican ta George Bush ta shiga Afghanisatan ta hanayr amfani da karfin soji, idan akwai bambanci to wannan shine bambancin dake tsakanin wadannan jam’iyyu amma duk manufarsu day ace, kawai a aiwatarwa suka bambanta. Shugaban Obama ya taba fada cewa gwamnatin kasar Amurka kamar wani jirgin kasa ne da ya yake tafiya duk shugaban kasar Amerika sai dai ko ya kara gudunsa ko kuma ya rage gudunsa, amma ba zai iya tsaida shi ba, ballantana kuma ya canza masa akala daga yamma zuwa gabas, wannan shine kusan hakikanin makirci da kutunguilar siyasar Amerika.

Haka kuma, shata iyakokin manufar kasar Amerika dangane da kasashen duniya aiki ne na kwararrun cibiyoyi, ba na jam’iyyar siyasa ba. Wato wannan yake kara tabbatar mana da cewa su wadancan shaidanu karkashin Corporate capitalism sune suke yin uwa suyi makarbiya a harkar siyasar kasar Amerika bayan anyi zabe an gama. Wannan yake nuna Amerika ba kamar kasashene masu tasowa ba, ta yadda duk shugaban da yazo yana iya rusa Dukkan ayyukan da magabacinsa ya yi, sannan ya dora nasa sabo, Amerika tasha gaban haka, duk kwarewarka da wayo da dabara dole ka tafi akan wannan tsari da kazo ka tarar.
Dan haka duk wasu ihu da hayaniya da jam’iyyun Democrat da Republican zasu yi, bai wuce share hanyar da za’a cimma wadannan manufofi na kasarba.

Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale