Monday, September 24, 2012

Tarihin Kasar Zazzau



Tarihin Kasar Zazzau

Alhamdulillah, kamar yadda Hausawa suke cewa rana bata karya . . . jiya na ce zan bada tarihin kasar zazzau, to yau gashi Allah ya nufa, dan haka sai ku biyo ni daga dan abinda na tsakuro.

A salin kasar zazzau angano ta ne a karni na goma sha daya 11, inda wani mutum da ake kira da suna GUNGUMAU ya fara kafa garin a matsayin gari. Inda aka maida wajen wata kasuwa ko mahada ta hada-hadar bayi zuwa sauran kasashen da ke kudu da hamada sahara, ‘yan kasuwa daga kano da katsina sune suke kawo gishiri inda ake basu bayi a matsayin fansar wannan gishiri da suka kawo. Su kuma su daukesu su tafi da su domin su sayar.

Sai dai, kasar Zazzau tana daga cikin kasashen Hausa guda bakwai, wanda Bayajidda ya kafa. Asalin kasashen Hausa wadan da Bayajidda ya kafa kuma ake kiransu da sunan Hausa Bakwai, sune, Kano, Katsina, Daura, Gobir, Rano, Garun Gabas da kuma Zazzau a cikon ta bakwai wadannan sune kasashen Hausa.

Amma kuma a wani kaulin ance Sarki Bakwa Turunku shi ya kafa kasar zazzau, kuma ya baiwa garin sunan karamar ‘yarsa wato zaria. Shi  wannan sarki kamar yadda na fada, Bakwa Turunku daga cikin ‘ya ‘ya guda biyu da yake da su, kuma suka shahara, kuma aka sansu, sune Zariya da Amina wadda aka fi sani da sarauniyar zazzau, da yake kasar zazzau ta fi shahara da sunan Amina dan haka zan maida hankali kacokan kan ita sarauniya Amina.

Sarauniyar  Zazzau Amina, tarihi ya nuna ta rayu daga shekarar 1533 zuwa 1610, ɗaya ce daga cikin ‘ya'ya biyu da sarkin Zazzau Bakwa Turunku ya haifa. Wato ita Amina ɗin da kuma ƙanwarta mai suna Zariya, wadda daga sunanta ne aka samu sunan Zazzau. Amina ta yi sarautar Zazzau bayan rasuwar mahaifinta, daga shekara ta 1509 zuwa 1522, wato shekarunta 13 ke nan akan karagar mulki. Kuma ita ce mace ta farko da ta mulki masarautar Zazzau, kuma ta shida a cikin sarakunan haɓe ko Hausa waɗanda sukai mulki bayan Addinin Musulunci ya fara bayyana a ƙasar Zazzau.

Haka kuma, tarihi ya nuna cewa addinin Musulunci ya fara bayyana a kasar zazzau tun kusan karni na sha biyar amma bai bayyana sosai ba sai bayan Jihadin fulani a shekarar 1808. A wannan shekara ne Fulani suka kaddamar da jihadi kuma suka kwace kasar zazzau daga hannun Maguzawa, sarkin zazzau na wancan lokacin da fulani suka kora sai ya koma kasar Abuja, inda ya kafa masarauta a Suleja kuma ake kiransa da sunan Sarkin Zazzau, watakila wannan shi ne dalilin da ya sa haryanzu ake da “sarkin zazzau suleja”.

Sarauniya Amina ta shahara matuƙa a ƙasar Hausa da ma yankunan da daular Usmaniyya ta mulka. Ta yi yaƙe-yaƙe a wurare da dama a fadin kasar Hausa. Idan aka ɗauka tun daga Zariya har zuwa ƙasar Abuja akwai ƙananan garuwa da dama da sarauniya Amina ta kafa, sai dai ba masu girma ba ne, saboda kamar dai wurare ne da ta ci zango a wajen.

Dangane da batun waje ko kuma garin da Sarauniya Amina ta rasu, a gaskiya babu tabbas, to amma masana tahiri suna kyautata zaton cewa ta rasu ne a can ƙasar Gara, wato ƙasar Igala kenan wadda yanzu ta ke cikin jihar Kogi, a halin yanzu. Wannan dalili ne ma ya sa ba a san takamaiman inda kabarinta ya ke ba har a yanzu.

Sannan kuma asali ita Amina ba Sarauniya bace ana kiranta ne da sunan MAGAJIYA, domin tun tana shekara 16 mahaifinta Bakwa Turunku ya bata sarautar Magajiya, ko da ta zama sarauniya tana yaki ta cigaba da amsa sunan Magajiya, ance sarkin Nupe shi ne mutumin da ya fara bata sunan Sarauniya ko Gimbiya.

Idan aka koma ga maganar zuriyar sarauniya Amina, a gaskiya abu ne mai wuya ace ga waɗansu da suke zuriyarta ne, tun da agaskiya yadda tarihi ya nuna, sarauniya Amina har ta mutu ba ta yi aure ba. Don haka babu wata shaida dake nuna cewa a ciki ko wajen zazzau, akwai wasu da za a iya cewa zuriyarta ne.

Sannan bayanai sun tabbatar da cewar Sarauniyar zazzau Amina ita ce ta fara shata ganuwar kasar zazzau kamar yadda yake a al’adar kasar Hausa kusan ko wane gari yana da ganuwar da ta kewaye birni wato Badala..

To sai dai duk da cewa, akwai bayanai masu sarƙaƙiya da kuma saɓani na masana tarihi a game da ainahin rayuwar sarauniya Amina, to amma dai magana mafi rinjaye ita ce, Sarauniya Amina ta taɓa wanzuwa a doron ƙasa, a matsayin sarauniya a Zazzau. Duk da wasu suna ganin tarihin sarauniya Amina zuki ta malle ce.

Akwai sarakunan Hausa ko Haɓe guda goma sha takwas (18) da kuma sarakunan Fulani goma sha uku 13. Da kuma sarakunan da suka riski lokacin turawan mulkin mallaka wadan da suka hada da Sulayman wanda ya yi mulki daga watan maris zuwa Afrilu na shekarar 1903 wato wata biyu kacal ya yi a gadan sarauta, daga nan kuma sai Ali ibn Abdulkadir daga 1904 zuwa 1920, daga shi kuma sai Dallatu ibn Uthman Yero wanda ya yi mulki daga 1920 zuwa 1924, sai kuma Ibrahim ibn Muhammad Lawal Kwassau wanda ya yi mulki daga 1924 zuwa 1936, sai Malam Jafar ibn Ishaq daga 1936 zuwa 1959, daga shi sai Muhammadu Al-Amin ibn Uthman 1959 zuwa 1975 daga shi kuma sai sarki mai ci a yanzu wato Alh. Shehu Idirisu daga 1975 zuwa yanzu.

Zazzagawa dai mutane ne manoma sunfi shahara da noman suna noma kayayyakin amfanin gona da suka hada da Doya da Makani da Auduga da sauransu, kuma dai mafiya yawancinsu Gajeru ne ba dogaye ba.

Kasancewar kanawa sunsha basu ruwa a kusan dukkan wata karawa da ake yi a can baya, dan haka ne suke daukar Kanawa a matsayin iyayan gidansu tare da basu girma na musamman, su kuma kanawa saboda karamci suka daukesu a matsayin abokan wasa.

Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale



Friday, September 21, 2012

Allah Ya Halicci Tururuwai Da Mu'ujizozi


Allah Ya Halicci Tururuwai Da Mu'ujizozi 


 Tururuwa! Wata halitta ce daga nau’ukan kwari da Allah madaukakin Sarki ya halitta bisa hikima da ikonSa. Shi ‘Al-Khaliku’ ya fi kowa sanin dalilinsa na tsara dabi’un Tururuwa a yadda suke, to amma ba shakka akwai ayoyi da hikimomi masu yawa tattare da irin tsari na musamman da wasu mu’ujizozi da Allah ya kebanci tururuwa da su, wanda dole hankali ya yarda cewa Allah ya yi su ne don su zamo ayoyi, kuma abin lura da tunani ga mutane.

Tururuwa ta sha bamban da duk wasu halittu na kwari da dabbobin da Allah Ta’ala ya halitta, domin salonta, hikimominta, tsarin gudanarwarta, zubin siyasa da tafiyar da al’umarta, ayyuka tukuru da sadaukarwarta, suna bayyana zunzurutun iko da iyawar Allah ne, a gefe guda kuma suna fassara Mu’ujizozi da fifikonta bisa sauran kwari da dabbobi da Allah Buwayi gagara misali ya halitta. Da yawa daga cikin dabbobi suna da wata baiwa ta hali ko dabi’a ta musamman, wanda bisa nazari dan Adam zai iya daukar darasin rayuwa a cikinta. Misalin hakan shi ne zuma, malam-buda-man-littafi, kurciya, gara, kiyashi, zaki, kyanwa da sauransu. A cikin yin hakan kuwa babu wani kaskanci ko fifikon wadannan dabbobi a kan dan Adam din. “Hikima kayan muminini ce, duk inda ya gan ta sai ya dauki abinsa,” in ji hadisi.

Kowane janibi na rayuwar tururuwa akwai darasi abin koyi a cikinsa, to amma bari mu dauki darasin sadaukarwa mu yi magana a kai, mafi yawan tururuwai sukan kai dubu 500 zuwa miliyan guda a duk inda suka mamaye a matsayin yankinsu, suna da tsari na kowa da aikinsa ‘Division of Labour’, suna da ‘Supervisors’ wadanda za su binciko inda ya dace a kafa gida don yin sansanin zama. Akwai wadanda za su rungumi aikin gina gidan da tsara shi sashi-sashi. Sukan samar da dakuna da bangarori sama da 500 a gidan nasu. Akwai masu yanko ganyayyaki da dauko su don kawo wa masu gini, wato ‘Leaps Scatters’, a tare da su akwai kananan tururuwai masu ba su kariya daga duk wani farmaki da ka iya zuwa ta sama ko kasa (musamman na zuma). Wadannan dakaru ’yan-ta-kife ne, a kodayaushe suna cikin shirin yin ko ta kwana ko shahada.

Babu wanda zai iya hana kansa yin mamaki saboda ganin shurin tururuwa a gine a kasa, wanda tururuwai suka gina. Dalili kuwa shine shurin tururuwa gini ne mai ban al’ajabi wanda tsawonsa ya kai mita 5-6. a tsakanin shurin akwai nagartaccen tsarin dake kula da dukkan bukatunsu wanda ba zai taba sanyawa su fito cikin hasken rana ba, saboda yanayin jikinsu. A cikin shurin, akwai tagogi na shan iska, dakunan haihuwa, gidaje, farfajiyoyi, wurin samar da makarai na musamman, kofofi, dakunan zama lokacin zafi dana hunturu ; a takaice dai, akwai komai a ciki. Abin mamaki da wadannan tururuwan da suke gina wadannan shurika shine kasancewar su  makafi, domin duk tururuwar da ka sani ko ka ke gani to bata gani da ido. Abu na biyu na mamaki game da tururuwa shine, idan muka kwatanta girman tururuwa da shurinta zamu ga cewa, tururuwan sunyi nasarar gina wani gini wanda ya nunka su girma sama da sau 500.

Haka kuma, a cikin al-qur’ani mai tsarki Allah ya saukar da suru sukutum da sunan Tururuwa, wato Suratul Naml wadda ita ce sura ta ashirin da bakwai (27) a cikin jerin surorin al-qur’ani; kuma Allah ya bamu labarin cewa Tururuwa ta yi magana da ‘yan uwanta lokacin da Annabi Sulaimanu ya zo wucewa, inda ta bukaci al’ummar tururuwai su shiga gidajensu . . . Shakka babu banda ikon Allah babu mai iya haka, domin ka duba kankantar tururuwa amma ta yi magana. Har ila yau, suna da wata kasaitacciyar sifa: idan da zamu raba shurin gida biyu, gidan farko shine na ginin, daga sama hanyoyin, dakunan da titunan sunyi kama da juna. Kuma da za’a mayar da wannan rabin to zuwa wani dan lokaci hanyoyin da gidajen zasu koma su hade dai-dai kamar ba’a taba rabasu ba, kuma tururuwan Zasu cigaba da harkokinsu kamar basu taba rabuwa da juna ba.

Tafiyar saka na tarihin tururuwa a irin wannan hali, tsari, dabi’a da salo nata, bisa binciken ‘Shatter’ na tsawon shekaru sama da miliyan dari takwas da suka shude, wanda mahaka tarihin dan Adam suka yi, ya zamo daya daga cikin hujjjoji masu karfi na karyata akidar ‘Theory of Evolution’ wato Ka’ida juyin halitta da wasu masanan falsafa ke da shi, kuma da wannan tarihi na tururuwa ne aka samar da wani babi mai kanu ‘The Evolution misconception’. Wato Jahilcin masana Ka’idar Juyin Halitta.

Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale



Wednesday, September 19, 2012

Ngozi Okwonjo-Iweala Ta Kasa Fahimtar Ma’anar Rashawa Da Cin-Hanci



Ngozi Okwonjo-Iweala Ta Kasa Fahimtar Ma’anar Rashawa Da Cin-Hanci

An shaida ma na cewa Dr Ngozi Okonjo-Iweala, ministar kudi kuma ministar da a ka dorawa alhakin habaka tattalin arzikin kasa, an horar da ita ne a Bankin Duniya domin yin jagoranci, inda har ta kai mukamin daya daga cikin manyan daraktocin bankin. Saboda haka za mu iya cewa ta fahimci ka’idojin da ke samar da jagoranci nagari. Abin kunya ne a ce ta na cikin gwamnatin da a ka sace Naira tiriliyan 2.6 ba tare da ta nuna kwarewarta wajen hana afkuwar hakan ba. Abin mamaki matuka ganin yadda Okonjo-Oweala ta amince ta jagoranci ma’aikatar da za a tafka irin gagarumar sata duk da irin tarbiya da horon da a ka ce ma na ta samu a bankin duniya. Amma wannan da alamu wannan shi ne dan-ba ga abinda Okonjo-Oweala ta sa gaba.

A ‘yan makonnin da suka gaba ta ne, ta fito ta shaidawa duniya cewa za ta iya jingina da kamfanonin man da rahoto ya kama da laifin wawure dukiyar kasar da ta kai tiriliyoyin Naira. A ta bakinta “mu na da burin cewa wadanda a ke kallo a matsayin sun aikata babban laifi za mu yi jinga da su, idan har su na son yin aiki tare da mu ta yadda za mu ba su dama su warware matsalar ta hanyar shigowa da shi.” Matsalar wannan gwamnatin ita ce irin ta Obasanjo, wato masu gudanar da ita sun mance da ma’anar kalmar almundahana. Kuma duk da cewa Okonjo-Oweala ta sami kwarewar mataki na duniya a bankin duniya, amma ta na karbar mukami a gwamnatin Jonathan sai ta koma ta zama tamkar kidahumar ’yar kauye.

A wajen ministar kudin, wasu daga cikin barayin ‘ba su tafka babban laifi ba’. Ba ta shaida ma na wacce sata ce ba babban laifi ba. Watakila satar Naira biliyan daya daga cikin Naira tiriliyan 2.6 ita ce ‘ba babban laifi ba’. Ko ma ta zama Naira miliyan 100? Ina iya tuna wani jami’in gwamnati da a ka yi zargin ya sace Naira biliyan uku, ya amsa a fusace ya na mai cewa, “Naira biliyan 2.5 ne kawai.” Shin irin wannan shawarar ta ke bai wa iyayen gidanta a bankin duniya? Abin mamaki ne ganin yadda ita ce wacce ta yi ritaya daga gwamnatin Obasanjo kan abinda bai kai wannan zama badakala ba, amma a yau ita ta nutsu da abinda ke faruwa. Abu ne wanda hankali ba zai dauka ba a ce ita ce har yanzu a cikin gwamnatin da a ke tafka badakala irin ta gwamnatin Jonathan.

Ba wannan kadai ba. Okonjo-Oweala, wacce ta ke kallon bashin Dala biliyan 32 a matsayin abu mai tsananin hatsarin da ba za a jure ba kuma ta jagoranci gwamnatin Obasanjo a 2006 a ka biya Dala biliyan 18, inda a ka yafe Dala biliyan 32 don ceto kasar daga kangin bashi, a yau kuma ita ce ta ke cewa bashin Dala biliyan 45 ba komai ba ne na damuwa (bayan fa shekara shida kacal da yafe Dala biliyan 32). Shin akwai abinda na kasa ganewa ne a nan? Babu fa abinda a ka san Jonathan na aikatawa da kudin nan bayan biyan albashi. Kada a manta fa a wannan lokaci ne a ke sayar da kowacce gangar danyen mai a kan Dala 80. Bugu da kari, lokaci ne wanda a ka sace tiriliyan 2.6 a shekarar zabe, inda kuma mu ke ranto bashi domin mu biya albashi. Wadanne irin mutane ne wadannan haka? Shin keta ce ko sun tsani kasar ne ko kuma mu da ke zaune cikinta?

Karbar bashi ba laifi ba ne ga kasa. Muhimmin abu shi ne abinda ka yi da kudin da yadda ka tafiyar da shi. Na yi imani da cewa mu na da bukatar karbo bashi domin mu zamanantar da kayayyakinmu da su ka lalace a gaggauce. Za mu iya biyan bashin cikin sauki idan har za mu hana tafka almundahanar da a ke yi a halin yanzu cikin kasar tamu. Nijeriya ta na bukatar tashi tsaye wajen cigaban zamani, amma mu na bukatar akalla Dala biliyan 100 wajen zamanantar da ita. Dala biliyan 100 ba tare da aikata cin hanci da rashawa ba ya ishe mu. Duba fa ka gani, bashin da a ke bin mu na Dala biliyan 45 a yanzu ya bace a cikin sabunta abubuwanmu, ka kuma auna Dala biliyan 12 din da a ka ce Obasanjo ya batar a ‘samar da wutar lantarki’ ita ma ta yi batan dabo. Mu tuna irin ayyukan da za a samar da kuma yaye talauci da za a yi da kudin. Amma wasu mutane sun sace hatta kudin da za a biya albashi, sannan kuma su ka koma su ka karbo bashin Dala biliyan 45, domin sake biyan wannan albashin dai ta hanyar kudin tallafin mai na karya. Ba wai kawai ayyuka a kasa za a rasa saboda tafka rashawa ba, a’a, har mu da ’ya’yanmu ma an gadar ma na da bashin dala biliyan 45. Ba za mu iya cigaba da tafiyar da Nijeriya a haka ba.

Babu wata kasa a duniya wacce ta binkasa ba tare da yakar cin hanci da rashawa ba. Rashawa ta na kashe kasa ne; tuni ta ragargaza Nijeriya. A Malesiya da Singafur a na yin hukunci mai tsauri ne ga masu tafka rashawa. Idan kuwa haka ne ba abin mamaki ba ne don ’yar kankanuwar kasa kamar Singafur ta shiga sahun kasashe mafi cigaba a duniya. A lokaci guda kuma ginin Malaysian Petronas Twin Towers da ke Kuala Lumpur ya zama gini mafi tsororuwar tsawo a bayan kasa, wanda hakan ke alamta karfin tattalin arziki. Kada a manta, Malesiya ta na fitar da gangar danyen mai kasa da 600,000 ne kawai a kullum, yayin da mu kuma mu ke iya fitar da ganga miliyan 2.5 a rana guda. A hakikanin gaskiya ma dai, ba don almundahana ba, Nijeriya za ta iya fitar da ganga miliyan hudu a kullum. Ban da fa arzikin gas, wanda shi ma wani bangare ne mai zaman kansa a sha’anin danyen mai.

Jamus ce kasa mai karfin arziki a Turai, amma fa ta na cikin kasashen da a ke hukunta rashawa da tsaurin gaske. Kasar Sin, wacce ta zo daga bayan-baya ta zama ta biyu a duniya ta bangaren tattalin arzikin kasa, ta na cikin kalilan din kasashen da a ke zartar da hukuncin kisa a kan sace kudin al’umma. A Amurka, ba komai ba ne a sanyawa duk wani ‘mai ji da kansa’ ankwa a hannu, idan a ka same shi da laifin rashawa. Tambayi shugabannin Enron ko na Ponzi, Bernard Madoff ka sha labari. A yanzu haka da na ke yin wannan rubutu, wani babban janar a rundunar sojan Amurka, William Ward, a na kan tuhumar sa bisa aringizon kashe kudi.

Hakika mu san cewa, Jonathan ba ya damuwa kuma ba ya ji a jikinsa kan batun rashawa. Ya ce ba zai bayyana wa duniya abinda ya mallaka ba; ya kamata hakan ya sa mu fahimci yadda ya dauki batun rashawa.

Amma kasancewar Okonjo-Oweala a cikin gwamnati tabbas ba ya taimakawa kasar da komai. Ta na taimakon kanta ne kawai ta hanyar cigaba da kasancewa a cikin gwamnati. Har sai ta janye fassarar ma’anar da ta bai wa rashawa kumata fice daga cikin gwamnati, sannan ne ’yan Nijeriya za su fara kallon ta da sauran mutunci.

Wannan bayani Malam Sam Nda Isiah babban edita na Jaridar Lweadership ne ya rubuta a shafinsa na Monday Column.
Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com

Saturday, September 15, 2012

Sunana Al-Majiri Dalibin Tsangaya



Sunana Al-Majiri Dalibin Tsangaya

Ni al-majiri ne dalibin tsangaya, Tsangaya nan ne makarantarmu inda muke karatun al-qur’ani mai tsarki, waje ne da muke kwana mu tashi, babu rufin kwano, wani zubin idan lokacin damina ya zo bama iya barci musamman idan ana ruwa da daddare haka muke fakewa a labe a jikin garu kamar kadangaru har sai ruwa ya dauke, sannan mu sharce inda zamu kwanta. Tsagaya dai makarantar mu ce ba kamar irin makarantar boko ba ce, da ake karatu a zaune akan kujeru da litattafai da biruka. Mu a tsangaya muna amfani ne da allon katako wanda muke yin rubutu da alkalami da tawada, kowa yana da allonsa, kuma karatun kowa daban da na kowa.

Zan gaya muku kadan daga cikin tarihin rayuwata a matsayina na Al-majiri, da irin yadda muke rayuwa a tsangaya, da yanayin karatunmu, da kuma dalilin da ya sanya muke fita bara domin neman dan abin kalaci. Sannan zan gaya muku shakku na dan gane da hukumomi akan shirinsu na mayar da makarantun Allo irin na tsangaya wajen su yi dai-dai da na boko, sannan zan sanar da ku wasu hanyoyi da nake ganin idan anbi za’a taimakawa rayuwar al-majirai.

Bari na fara da gaya muku hakikanin ma’anar sunana wato AL-MAJIRI. Wannan suna na al-majiri, kusan zance suna ne wanda ake gayawa duk wani dalibi da yabar garinsu zuwa wani gari domin neman karatun al-qur’ani, inda zai hadu da sauran yara da suka zo daga garuruwa mabambanta. A mafi yawancin lokaci idan za’a kai yaro al-majiranci, yakan tafi ne da ‘yan tsummokaransa na sawa da tabarmar kwanciya da kwanan abinci da kuma Allo na katako, kusan wadan nan sune abinda aka san al-majiri yana zuwa da su daga gidansu, ‘yan gata daga cikinmu sune wadan da ake hadosu da sabulun wanka da na wanki, wadan da kalilan ne kwarai da gaske a cikin al-majirai, kasancewar galibinmu Al-majirai ‘ya ‘yan talakawa ne, iyayanmu basu da wani karfi da zasu iya yi mana dawainiya.

Al-majiri ba shi ne yake zaben makarantar da za’a kaishi ba, sau da yawa wasu daga cikin iyayanmu ma basu san makarantun da muke karatu ba, domin wani zubin amanarmu ake dankawa a hannun wasu daga cikin wadan da suka tumbatsa a harkar al-majiranci, inda suke kaimu makarantun allo mu hadu da sauran dalibai, wani lokacin sai dai kawai a sanar da malamin tsangaya cewar ankawo sabon dalibi wani zubin ko kauyensa ma wani al-majirin ba’a fada, kasancewar Tsangaya makaranta ce da ba’a cike form idan za’a shiga, ba’a bukatar takardar haihuwa ballantana ace za’a bada admission ko maganar biyan kudin makaranta.

Lokacin da babana ya kawoni tsangaya, bayan da ya hannantani ga Alaramma, ko kudin kashewa bai bani ba, ban kuma tambaya ba, haka kuma malaminma bai tambaya ba, kuma bana ganin kowa daga cikin dangi na, har sai shekarar ta zagayo sannan ne zamu ci sa’a mu tafi gida inda zamu yi sallah karama ko babba tare da iyayenmu da ‘yan uwanmu, ba kowa ne daga cikin al-majirai yake katari da irin wannan damar ta zuwa gida sallah ba, akwai wadan da idan suka fito daga gida wata kila su da komawa har gaban abada, wasu wadan da basu yi sa’a ba, saisu yi shekarar da shekaru babu ko mutum daya daga cikin danginsu da ya taba waiwayarsu, kar ka so kaji yadda irin wadan nan ‘yan uwannawa al-majirai suke cikin damuwa.

Lokacin da aka kawoni makaranta a rana ta farko, rannan na zama mai cin gashin kaina, domin zan shiga sahun ‘yan uwana da na tarar wato kolawa wadan da gaba daya shekarunmu daga 7 zuwa 15, bamu kai matsayin Garada ba; gardi shi ne al-majirin da ya balaga, kuma ya dan nu-na a karatun al-qur’ani, garada yayyanmu ne, domin suna aikenmu muna zuwa idan muka yi musu laifi wani zubin har horo suke yi mana, sai dai ba me yawa bane.

A wajen ‘yan uwana kolawa zan sami gamba na koyi yadda ake fike al-kalami da yadda ake rubutu, sai dai lokacin da aka kawomu Alaramma ne yake yi mana rubutu domin ba mu kai waladaina ba, za dai mu ringa yin rubutu a cikin allon-sha dan hannunmu ya fada, kafin mu koma yi da kanmu. Wannan shi ne kadan daga cikin rayuwar da muke a tsakaninmu kolawa da yayyenmu garada.

Bari kuma yanzu na yi muku bayani dangane da bara. BARA dai kolawa ne suke yin ta domin fita waje su samo dan abinda aka ci aka rage, kolawa saboda su yara ne shi yasa suke yin bara, amma duk mutumin da ya kai matsayin gardi baya yin bara. Kolawa sune wadan da ko mai gida ya shigo ya gansu a gidansa suna bara ba zai ji wata damuwa ba, sabanin idan gardi ne, domin ya balaga, mutane bazasu bari ya shigar musu gida yana bara ba.

Muna shiga gida gida ne, muna cewa ko dan kanzo iya, ko dan dago dago iya, iya nine danki muhammadu. Wannan dai su ne kalaman da kolawa suka fiya yi a duk gidan da suka shiga yin bara, sai dai yanayin wasu garuruwan yakan sha bamban da na wasu haka kuma, irin kalaman da ake fada suma akan samu sauyi daga wani wajen zuwa wani wajen. Akan kirawo mu da ALMAJIRI KAWO KWANON KA, mukan samu ragowar tuwan da aka ci aka rage wato tuwo miyar kuka ko kubewa wani zubinma muka sami shinkafa da wake ko dai wani abincin da aka ci aka rage. Wannan abincin da muka samu shi muke ci, sannan mu yo guzurin wani zuwa makaranta, kolawa idan sun dawo daga bara sukan zo da abinci kala-kala, anan ne wasu daga cikin garada da suke tsangaya zasu zabi wanda suke so su ci suma, haka kuma idan aka yi dace da samun wani abinci mai dadi akan kaiwa Alaramma ya sanya albarka.

Sau da yawa abin da muka barato da daddare shi ne muke ci da safe, wato Karin kumallo. Domin almajirai basa yin bara da safe, duk almajirin da ka gani yana bara da safe to ba al-majirin tsangaya bane, domin na tsangaya suna da lokuta kayyadaddu da suke fita yin bara. Mukan fita bara ne daga karfe 11 na safe zuwa karfe 2 na rana domin mu sami abincin da zamu ci na rana (lunch) sannan mu sake komawa bara daga karfe 8 na dare zuwa karfe 9 na dare, wadan nan sune lokatan bara. Duk al-majirin tsangaya baya bara da yamma kamar yadda na ce baya yi da safe ko bayan sallar magaruba, duk wani al-majiri da kuka gani yana bara a wadan can lokuta da nace ba’a bara to shakka babu ba al-majirin tsangaya ba ne, ma’ana ba mai neman karatun al-qur’ani bane.

Kolawa basa yin bara dan a basu kudi, ko ka gansu akan titi suna wanke gilashin motoci, al-majirai muna bara ne kawai domin samun abin da zamu ci. Muna yin uwar daki wato gidan da muke zuwa muna yi musu aiki kama daga debo ruwa da zubar da shara shima ladanmu shi ne a bamu abinci ba kudi ba. Haka kuma, idan kuka ga al-majiri a kasuwa ko tasha ko kan danja wato mahadar tituna to ku tabbaci hakika ba al-majirin tsangaya bane, ba mai neman karatun al-qur’ani bane. Wannan shi ne bayani dangane da bara.

Abu na gaba kuma, zan yi muku bayani dangane da yadda muke karatu. Kamar yadda na fada tsangaya dai makaranta ce da ba’a bukatar ka cike wata takarda domin samun izinin shiga, haka kuma, babu wata takardar shaida da ake bayarwa ga duk wanda ya kamala karatunsa na tsangaya. Muna rubuta al-qur’ani ne da hannu sannan mu hardace shi, wannan zata bamu damar mu wanke allo sannan mu kuma yin wani rubutun haka za ayi ta yi har sai an sauke al-qur’ani, idan kuwa aka sauke to har da haddarsa gaba ki daya aka sauke.

Wasu suna karatu hade da yin darasu, wasu kuma sai sun gama sannan zasu ringa rubuta al-qur’ani da ka, sannan su je wajen malami ya yi musu darasu, malam baya yarda ko kadan ka leka takardar al-qur’ani a lokacin da ake yi maka darasu, za’a yi maka gyara ne ka haddace shi da ka! Daga lokacin da mutum ya kamala darasu to ya zama alaramma shima, idan yaso sai ya koma ya tuso tilawa, daga nan kuma ya rubuta al-qur’ani idan kuma aka ci sa’a ya rubuta kuma ya haddace ba tare da anci gyaransa ko da na fataha bane to wannan ya zama GWANI kenan. Allah ya bamu albarkacin Al-qur’ani.

Daga nan kuma sai mu matsa zuwa zauruka domin daukar karatun litattafai a wajen malamai na soro ko zaure. Anan ne zamu koyi kaw’idi da ahalari da litattafan fiquhu domin mu san hukunce-hukuncen addini. Daga wannan lokacin kuma sai Alaramma ya shiga duniyar neman ilimin addini, yana bin zauruka da masallatai yana daukar karatu na ilimi.

Idan zamu iya tunawa mai girma shugaban kasa Goodluck Jonathan ya taba cewa tsarin karatun tsangaya shine silar sukurkucewar al’amuran tsaro, kuma shi ne kashin bayan kungiyar Boko Haram. A wannan gabar nake gayawa shugaban kasa cewa ya yi babban kuskure akan wancan ikirari nasa. Ni al-majiri dalibin tsangaya ina tabbatarwa da shugaban kasa cewa ni ba dan Boko Haram bane, haka kuma tsangaya bata koyar da kowa Boko Haram. Sai dai kamar yadda ake iya samun bata gari a cikin al’umma da Dukkan bangarori na rayuwa, to ana iya samun bata gari a cikin ‘yan uwana al-majirai daliban tsangaya.

Me Tsngaya ta ke bukata? Abinda Tsangaya take bukata shine cikakken tsarin koyo da koyarwa wanda ya dace da addinin musulunci da kuma al’adar Hausawa, komai kyan tsari indai bai dace da irin al’adarmu ba, shakka babu ba zai samu karbuwa ba. Muna bukatar a inganta mana tsangayu da samarwa alarammominmu cikakkiyar kulawa da samun walwala. Muna bukatar samun makewayi, domin daga cikin irin hantarar da jama’a suke yi mana shi ne cewar muna bata musu gurare da kasha da fitsari, wannan kuwa ba laifinmu bane, domin kowa yasan kasha da fitsari larura ce da ta ke kan kowa, kuma hukumomi basu yi mana tanadin makewayi ba, sannan kuma, muna bukatar samun famfuna inda zamu ringa samun ruwan sha da na wanka da kuma wanke ‘yan tufafinmu, wannan dangane da muhalli kenan.

Idan kuma muka juyo ta bangaren walwala da jin dadi. Al-majirai muma ‘ya ‘ya ne, muna da bukatar mu ringa cin abinci kamar yadda dan kowa yake ci ba ragowa ba, anan ina nufin a samar mana da masu dafa abinci da kuma shi kansa abincin da za’a dafa mana, da bamu tufafin da zamu ringa sauyawa, da sabulun wanka da na wanki.

Makarantun tsangaya bamu da bukatar tsarin karatu na tantebur (time table). Domin wannan tsari ne da ya ci karo da irin yanayin da muka taso da karatun al’qur’ani tun tale-tale, haka kuma, bamu da bukatar sai ansamar mana da litattafai da kujerun zama a tsangaya, mun fi bukatar tabarmi akan kujerun da ake so a samar mana.

Ya mai girma shugaban kasa, ta ya ya za’a ce mu biyo wadan nan hanyoyi na karatu a tsangaya, rana a tsaka za’a dauko ‘yan boko wadanda wani ma bai taba yin karatun allo ba tun da uwarsa ta haifeshi ace sune zasu tsara mana yadda karatun tsangaya ya kamata ya kasance, muna da tsari, muna da alarammomi, sun san Dukkan abubuwan da makarantun tsangaya suke da bukata, indai taimako za’a yi mana na fisabilillahi, sai a tuntubemu a ji ra’ayinmu. Sannan mu kanmu al-majirai a ji tabakinmu domin muna da abin fada da yawa.

Kamar yadda na fada tsangaya bata da bukatar cike wani form idan za’a shiga! To me ya sa aka ce wannan tsari na makarantun tsangaya na zamani da gwamnati ta kuduri aniyar samarwa a daukacin jihohin Arewa sai Al-majirai ne kadai zasu ci gajiyarsu? Anya kuwa babu wani lauje cikin nadi? Indai  gaskiya ne abar abin kofa bude mana duk mai sha’awa ya kawo dansa shima ya zo ya zama kolo, kuma mu da muke karatun al-qur’ani bamu da bukatar sai an koya mana turanci a tsangaya.

A kyale mu mana muje makarantar boko kamar yadda ‘ya ‘yan kowa suke zuwa makarantar boko, muma ‘ya ‘ya ne muna son karatun zamani. Amma danme aka waremu aka ce sai mu kadai, a barmu mu shiga makarantun da muka ga dama mana, mu zauna tare da sauran yaran al’umma, muma mu ci gajiyar ilimin zamani. Indai har da gaske hukuma ta ke, to daga yau ta ce Dukkan wani al-majiri ya je Dukkan makarantar da yake son karatun boko gwamnati zata dauki nauyinsa, Alabashshi abar mana tsangayunmu yadda muke karatunmu.

Daga karshe, ina son na tambayi shugaban kasa da mukarrabansa shin menene hakikanin gaskiyar wannan al’amari na gina makarantun tsangaya guda 100 a Arewacin Najeriya? Shin anyi ne domin taimakon tsangaya da daukaka darajar tsangaya ko kuwa anyi ne domin dakushe tsangaya da karatun al’qur’ani? Kamar yadda muka ji ance gwamnatin tarayya ta ware kudi har Naira Biliyan Biyar (5B) domin giggina wadan nan makarantu. Lokacin da mai girma shugaban kasa ya je Sakkwato bude makarantar tsangaya ta farko da gwamnatin tarayya ta gina, munji ance sauran ragowar suna dab da kammaluwa, domin anci kasha 75 na aikinsu, shin me ya sa har yanzu bamu sake jin mai girma shugaban kasa ya kuma bude wata makarantar tsangaya ba?

Sannan wane tabbaci muke da shi cewar wadan nan kudade da aka ware domin wannan aikin ba za’a sace su ba, kamar yadda aka sace kudin samarwa ‘yan Najeriya wutar lantarki zamanin Obsanjo har kusan Naira Tiriliyan daya da Biliyan uku, haka kuma, muna da masaniyar yadda aka sace kudin fanshon ‘yan sanda har kusan naira Biliyan talatin da shida (36B) duk wadan nan sunfi al-majirai kima da daraja a idon gwamnati amma aka sace dukiyarsu ko kuma hakkinsu, inaga namu mu al-majirai da bamu da wani gata sai mahaliccinmu.

Kuma ni a matsayina na al-majiri ina ta jin mutane suna korafi cewar harkar ilimi ta tabarbare gabaki daya ta yadda ‘yan makarantar boko basa iya cin jarabawa, malaman kuma basu da wani ingancin da zasu koyar, amma duk da wannan surutu da balokoko da al’ummar kasar nan suke yi, gwamnati bata ware wasu makudan kudade ba, wajen ingantasu sai makarantar Tsangaya, zance na gaskiya ina cike da shakku mai yawa akan wannan al’amari na inganta makarantun tsangaya, ban sani ba watakila saboda ni al-majiri ne shi ya sa nake irin wannan tunani.

Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale 

Friday, September 14, 2012

Akwai Bukatar Sake Fasalta Aikin Dan Sanda A Najeriya



Akwai Bukatar  Sake Fasalta Aikin Dan Sanda A Najeriya

Da farko zan fara da yabawa sifeto janar na rundunar ‘yan sanda Muhamma D Abubakar. Hakika ga duk wanda ya saurari kalaman shugaban ‘yan sanda na kasa tun bayan kama aikinsa zai yaba masa tare kuma da kyautata masa zato cewa lallai da gaske yake, domin shugaban ya fito ya fadi gaskiyar irin munanan halayen ‘yan sandan Najeriya da kuma rashin iya aikinsu, wannan kusan abu ne da duk dan Najeriya yake da masaniya akansa ga ‘yan sanda. A wata zantawa da ya yi da shuwagabannin ‘yan sanda na kasa, ya fito fili ya farke musu laya inda ya zargi ‘yan sanda da cin hanci da rashawa da kuma rashin iya aiki da munanan halaye da sauran dabi’un da basu dace da aikin dan sanda ba, ya kara da cewa ana tura ‘yan sanda ga daidaikun masu kudi da kamfanoni wanda hakan ya sa hukumar ‘yansanda suke rasa jami’an da za su gudanar da aikin samar da tsaro  ga talaka; sannan yace sassan binciken rundunar ‘yan sanda ba za su iya gudanar da ayyuka cikin adalci ba, sai dai in wadanda lamarin ya shafa suna da kudi. Ofisoshin ’yan sandan da sassan binciken miyagun ayyuka (CIDs) da jami’an gudanar da ayyuka sun zamo cibiyoyin hada-hadar kasuwanci da wuraren amsar kudade daga ayyukan da bataliyoyi da rukunnan ’yan sanda da na sama suke kafa su domin amfanin kansu.

Hakika duk wanda ya duba wadan nan maganganu da sabon sifeto ya yi zai sa ran samun gyara a tsawon wa’adinsa. Shakka babu aiki a kasa shi ne zai tabbatar da wannan batu, domin akacewa kare ana biki a gidansu yace mu gani a kasa, don haka muna kyautata zato akansa cewa zai kawo sauye sauye masu ma’ana a rundunar ‘yan sandan Najeriya, ganin cewa kusan adadin yawan ‘yan sanda Najeriya bai wuce 400,000 ba, haka kuma rundunar yansanda tanada akalla babban caji ofis da ake kira Police Division guda 1,115 a duk fadin Najeriya, haka kuma, akwai matsakaitan caji ofis da ake kira police Station guda 5,515 da kuma kananan ofisoshin ‘yan sanda na cikin unguwa da ake kira out post kusan 5,000. Lallai duk wanda ya kalli wannan adadi yasan akwai bukatar akawo sabbin sauye sauye a harkar ‘yansanda na kasa, tare da kara adadin yawan ‘yan sanda da kuma ofisoshinsu, yanzu a Najeriya ana maganar mutum miliyan 167 ta ina wadan nan ‘yan sanda zasu iya lura da wadan nan dumbin al’umma mai wuyar sha’ani.

Sannan duk da haka akwai kusan ‘yan sanda 120,000 da suke a gidanjen masu kudi da kamfanoni da kuma rakiya ga manyan jami’an gwamnati. Wanda wannan wani abin takaici ne a lokacin da ake fuskantar matsalar tsaro amma dagangan aka tura irin wannan adadi suke aikin tumasanci da maula da sunan bada kariya, domin duk dansanda da ka gani kofar gidan wani babban jami’in gwamnati dan jagaliya ne, hakama wadan da suke a manyan kamfanoni da suka hada da bankuna zaka samu kawai kasuwancinsu sukeyi, duk da cewa kudin da aka ware a harkar tsaro a kasafin kudi na wannan shekarar sunada dan karen yawa, wanda idan tsaron ake da gaske, wannan kudi zai isa dan najeriya ya kwanta a kofar gidansa ya yi barci harda minshari batare da yana fargabar ko da cinnaka ba.

Misali a kasafin kudi na wannan shekarar ta 2012, abin da aka warewa hukumar ‘yan sanda shi ne Naira Biliyan 331.2. wanda wannan adadi ya kunshi ofishin babban ministan ‘yan sanda da kuma rundunar ‘yan sanda da kuma sauran sassan ‘yan sanda. A cikin wannan adadi an ware Naira Biliyan 5.8 domin aikin ofishin ministan ‘yan sanda na kasa, sannan an warewa rundunar ‘yan sanda da manyan bangarorinta kusan Naira Biliyan 307.9, har ila yau kuma an warewa hukumar gudanar da  aikin ‘yan sanda Police Service Commission Naira Biliyan 2.5. idan har za’a rabawa kowane caji ofis na ‘yan sanda a kalla kowanne zai tashi da Naira 696,000, haka kuma, bisa la’akari da wadan nan alkaluma kowane caji ofis zai kashe abinda bai kai naira 2000 a kowace rana domin tsaron ‘yan Najeriya. Wanda wannan abin kaico ne, idan ka dauki mashawarcin kasa na fuskar tsaro wanda ake kira National Security Adviser shi kansa yana da masu bashi shawara kusan mutun 100 wadan da suke lashe kusan Naira Miliyan 950, anya kuwa da gaske ake a harkar tsaro? Musamman dukiya da rayukan talakawa?

Shakka babu aikin dan sanda muhimmin aiki ne da bai kamata a yi wasa ko sako-sako da shi ba. Dan sanda shi ne kusan al’umma suke cikin bukatarsa a koda yaushe, don haka suna da bukatar kayan gudanarwa masu inganci kwarai da gaske. Kamar yadda sabon sifeto ya zargi ‘yan sanda da rashin iya aiki, sai kayi mamaki a Najeriya dan sanda yana cewa mu bamu saba da irin wannan hari na sunkuru ba, ko kuma bamu saba da harin ‘yan ta’addaba, duk wanda yaji wannan yasan da cewa akwai wauta da rashin iya aiki da tsoro, domin a har kullum shi mai laifi ai kokari yake ya yi amfani da hanyar da jami’an tsaro basu santa ba wajen aikata laifinsa, don haka wannan wajibin ‘yan sanda ne su sake dabaru na tunkarar abokan gaba, da kuma iya kwance muggan makai ko abubuwa masu iya fashewa. Misali lokacin da wani Bom ya tashi da wani Dan sanda a jihar kaduna akwanakin baya a kusa da masallacin sarki musulmi Bello, kusan lokacin da akaga wata jaka ake kyautata zaton Bom ne an nuno wani dan sanda hannu rabbana ya tunkari wannan jaka zai bude, kaga ko shakka babu wannan akwai wauta aciki, tayaya hukuma zatabar danta ya sayar  da rayuwarsa a arha ta irin wannan hali, domin ina amfanin ‘yan sanda masu kayan aikin kwance boma bomai da ake kira Anti-Bomb Squard?

Sannan lallai akwai bukatar baiwa ‘yan sanda horo na musamman akan kama mai laifi batare da anhalakashi ba. Abin mamaki sai kaga ‘yan sanda kamar a tsorace suke idan anje inda masu laifi suke maimakon a shirya dabarun kamasu kawai sai dai kaji ruwan harsasai sun bude wuta, wanda bisa ga dokar ‘yan sanda haram ne dan sanda ya harbi mai laifi sai dai fa idan yaga babu yadda zaiyi da shi, kuma shima harbin akwai mataki da ake bi, domin kodai ayi amfani da hayaki maisa kwalla ko harsashin roba, idan kuma ta kama za’ayi amfani da harsashi mai rai to a harbi kafafu; amma abin mamaki shine duk ‘yan sandanmu basa bin wannan mataki, kusan wanda ba’ace suyiba shi sukeyi na harbin mailaifi a kirji ko a kai. Misali, ‘yan kwanakin da suka gabata wasu ‘yansanda a unguwar rijiyar zaki a kano suka budewa wasu mata wuta. Wai da sunan farautar ‘yan Boko Haram, haka kuma, wani dan sanda ya harbe wani yaro har lahira a unguwar Gwale daura da caji ofis na Gwale, wannan ko shakka babu shi ne yake kara nuna rashin kwarewar ‘yansanda tare da rashin ilimi da ya yi musu katutu, rayukan al’ummar kasa yafi komai daraja, domin da babu al’umma da shi kansa dansandan bashi da amfani, shi ya kamata ya salwantar da rayuwarsa domin kare al’umma kamar yadda yake a kundin dokar ‘yan sanda.

Sannan batun samar da ‘yan sandan jihohi wanda yake ta tayar da kura, shima wani muhimmin batu ne da bai kamata siyasa ta dabaibaye al’amarin ba. Domin babu yadda zaka dauki dansanda daga Abakalaki ka kaishi kauran Namoda kace ya baiwa al’ummar wajen tsaro da kariya, domin na farko yarensu ya sha bamban, addininsu ya saba, abinci, sutura da al’adu duk sun bambanta sannan kuma uwa uba baisan takan yadda garin yake ba, taya kake sa ran cewa wannan dansanda zai iya farutar mailaifi a wannan yanki? lallai idan aka sami ‘yan asalin waje to shakka babu su sukafi sanin yadda za’aci lagon masu laifi, kamar yadda babu yadda zaka dauki dansanda daga Malunfashi ka kaishi Otu-oke ko Ikorodu kayi tsammanin zakaga daidai, wannan yasa da yawa daga ‘yan sandan Najeriya matsorata ne na gaske.

Duk wanda ya kalli irin yadda ‘yansanda ke jibge buhunan yashi jibge a kofar kowace haraba ta ‘yansada ta jihohi ya san da cewa a tsorace suke. Dan sanda aikinsa shi ne ya baiwa al’umma kariya ba kansa ba, za kaga sunyi kuri da ido sun zuro kan bindiga waje suna muzurai, wanda kuma wannan yake nuna duk mutumin da ya koma kare kansa a gida, shakka babu ancishi da yaki, aikamata ya yi suyi kokari wajen amfani da kwarewa da fasaha wajen hana miyagu sakat, ta yadda bazasu iya shigowa cikin al’umma su aikata miyagun laifuka da mugun alkaba’i ba.

Sannan lallai a tanadi hora mai tsanani ga duk dansandan da aka samu da sakaci ko sabawa dokar aiki. A kwanakin baya ansami wasu ‘yansanda da sukayi garkuwa da wata budurwa suka dinga aikata zina da ita, wanda wannan mummunan aiki ne, kuma yana bukatar horo mai tsanani, da kuma hukunta dukkan wanda aka kama da laifin harbin kan mai uwa da wabi, irin haka yayi sanadiyar mutuwar matashin nan wanda ya shiga zanga zangar Allawadai da janye tallafin manfetur a legas, inda dansanda ya bude wuta akan ‘yan zanga-zanga.

Haka kuma, harkar jindadin ‘yan sanda wani muhimmin abune da ko kadan bai kamata ayi sakaci da shi ba. Tayaya za’a baiwa mutane bindigogi da harsasai masu rai sannan kuma a hanasu samun kyakykyawar walwala ayi zaton samun abinda akeso, lallai ya zama dole a inganta albashi da alawus-alawus na ‘yansanda, tare da basu horo akai-akai, da kuma, samar da sabbin kayan aiki na zamani da suka hada da kayan sadarwa, da motoci masu silke da marasa sulke, da rigar kariya da ake kira bullet proof da sauransu, duk da mun san akwai su, amma basu wadatar ba.

Sannan yana da kyau a sake duba tsaffin rahotannin kwamitin binciken yadda za’a fasalta aikin dan sanda a Najeriya wanda Alhaji MD Yusuf tsohon shugaban ‘yan sanda na kasa ya yi a shekarar 1994; da kuma wani rahoto da Tamuno ya yi mai suna National Security, da kuma wanda Danmadami da MD Yusuf da Osayande suka jagoranat a shekarun 2001 da 2008 da kuma 2012. Muna fatan  Shugaban ‘yan Sanda zaiyi amfani da kwarewa wajen kawo sabbin sauye-sauye wadanda magabatansa basuyi ba. Akwai tsaffin ‘yan sanda da sun nuna kwarewa kwarai da gaske kuma sun cancanci a yaba musu irinsu Ibrahim Kommasi da MD Yusuf da Nuhu Ribadu da Muhammadu Gambo Jimeta da sauransu. Haka kuma, anyi wadan da suka tafi nan bada jimawa ba irinsu Sunday Ehindaro da Mike Okiro da Obonnaya  Onovo da kuma Hafiz Ringin duk wadan nan ya kamat su zama darasi ga  shugaban ‘yansanda MD Abubakar, yasan wadan da suka kammala aikinsu lafiya kuma suke da kima har yanzu, sannan kuma yasan wadan da suka gama babu yabo babu fallasa da kuma masu abin kunya da Allah wadai irinsu Tafa Balogun.
Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@hotmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale


Thursday, September 13, 2012

Musulmi Allah Ya Bamu Hakuri



Musulmi Allah Ya Bamu Hakuri

Ya ‘yan Musulmi a cikin alkur’ani mai tsarki a sura ta 29 aya ta 2, Allah maigirma da daukaka yana cewa “shin tsammaninku dan kunyi Imani bazamu jarrabeku ba” hakika Allah ya jarrabi wadan da suka gaba cemu da tsanani da musiba da tashin hankali, har sai da sahabbai suka ringa tambayar Manzon Allah shin yaushe ne nasarar Allah zata zo? Manzon Allah ya ce ku sani Nasarar Allah a kusa take.

Ya ‘yan uwa wannan abin da ya faru ba sabo bane, sannan kuma ba abin mamaki bane. Idan zamu iya tunawa a shekarar 1988 wani marubuci dan Asalin kasar Indiya mazaunin kasar Burtaniya mai suna Ahmed Salman Rushdie ya taba rubuta wani littafi mai suna THE SATANIC VERSES wai shaidanun ayoyi a cikin al’qur’ani. Wannan littafi da wannan la’anannan mutum ya yi ya tayar da kura a daukacin kasashen Musulmi a wannan lokaci, inda da yawa daga cikin manyan malaman musulunci suka fitar da fatawar da take halasta jinin Salman Rushdie.

Wannan littafi karara karyata manzon Allah ne cin-fuska ne wa Musulmi baki daya. Amma saboda turawa makiya Allah ne makiya gaskiya wai ta dalilin wannan aka karrama Salman Rushdie da lamabar yabo mafi girma a duniya ta SIR, inda kuma aka bashi cikakkiyar kulawa a kasar Burtaniya, Allah ya la’anci Rushdie da ire irensa.

Daga cikin abubuwa na tashin hankali da suka samu Musulmi a wannan makon shi ne wayar gari da akayi da samun wani fim da yake nuna surar Manzon Allah Salallahu Alaihi wasallam, wanda wasu shedanu makiya Allah makiya zaman lafiya suka shirya, wanda kuma suka samu goyon baya daga muguwa annamimiya kasar Amerika. Ya Allah ka La’anci Dukkan masu cin-zarafin Musulunci da Musulmi. Haka nan tarihi ke maimaita kansa dangane da irin yadda wadan nan makiya Allah suke cin zarafin Musulunci.

Ya ‘yan uwa mu tuna Sahabin Manzon Allah mai daraja AMMAR BIN YASSIR. Shifa Ammar ba wai zagin manzon Allah akayi dan ya ji haushi ba, a’a kama shi aka yi aka ce shi da kansa ake son ya zagi manzon Allah! Ya ‘yan uwa shin akwai abinda ya kai wannan tashin hankali da firgici! Shin idan da kaine Ammar a wannan lokacin ya zaka ji a ranka? Haka nan Ammar ya aikata zuciyarsa tana cike da damuwa da bacin Rai da tashin hankali, ya zo ya Baiwa manzon Allah labara, manzon Allah ya tambayeshi shin ya kaji a Ranka? Ya shaidawa manzon Allah cewar yaji tashin hankali da damuwar da bait aba ji ba a rayuwarsa.

Shakkak babu wannan abinda ya faru abin bakin ciki ne da damuwa da tashin hankali. Ya ‘yan uwa wannan ba zai zama sanadiyar da zamu afkawa mutunan da basu jiba basu gani ba, mu sani cewa Allah ya riga ya bamu hakuri, Manzon Allah ma ya bamu hakuri. Mu nuna fushi da damuwarmu ta hanyoyin da suka dace da shari’ah.
Allah ya huci zuciyarmu

Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale

Tuesday, September 11, 2012

Mallam Mudi Sipikin: Anya Najeriya Tayi Maka Halacci Kuwa?



Mallam Mudi Sipikin: Anya Najeriya Tayi Maka Halacci Kuwa?

Duk wanda ya san tarihin gwagwarmayar siyasa da akayi a najeriya ya san da cewa mudi sipikin yana daga sahun gaba na masu wannan fafutuka. Su mallam Mudi kusan su ne wadan da sukayi gwagwarmaya tun zamanin turawa, lokacin da Bature yake sawa a daukeshi aka yana karanta jarida, hakika wadan nan bayin Allah sunyi gwagwarmaya da turawa musamman ta nemawa Talakawan wannan kasa ‘yancin kai da ‘yancin walwala. Su mallam mudi sipikin sunyi gwagwarmaya tare da su Marigayi Mallam Aminu Kano Allah ya jikansa da irinsu mallam Lawan Dambazau da marigayi Sa’adu Zungur da sauransu.

Mallam Mudi sipikin yana daya daga cikin mutum 56 da akaje London comperence da su domin tattauna yadda za’a bada ‘yancin wannan kasa. Ta sanadiyar wannan taro na Landan Najeriya ta samu Mulkin kai daga hannun Turawan Burtaniya. A duk cikin wadan nan mutane da suka je wannan taro na Landan Mallam Mudi Spikin shi ne kadai mutumin da yake a raye yanzu haka. Amma haka aka yi bikin cikar Najriya shekaru hamsin da Samun mulkin kai, aka raba kyaututtuka ga Mutanan da suka nuna hazaka wajen dorewar wannan kasa, amma babu ko daya daga cikin ‘yan Siyasarmu da ya tuna da wannan bawan Allah, abin da zai iya zama abin kunya ga ‘yan siyasarmu musamman na Arewa. Bayan ita kanta gwamnati su kansu Talakawa basu kyautawa wannan dan tahaliki ba, domin duk gwagwarmayar da suka yi, ba sunyi ne dan kashin kansu ba, a’a sunyi ne domin amfanin Talakawa, andoke su an dauresu, duk dan saboda nemawa talakawa ‘yanci amma yanzu talakawa basa bukatar shawarwarin irinsu.

Duk wanda ya je Fagge gidan Mallam Mudi Spikin dole ya tausayawa wannan dan tahaliki dattijo mai halin dattako. Kaga gidan da yake a zaune, ba wani gida ne na kuzo mu gani ba, bayan kuma ga ‘yan siyasa can da basu tsinanawa kasar nan da komai ba, suna kwana a tafka tafkan Gidaje a Legas da Abuja da Kaduna. Bari mu kalli irin gwagwarmayar Siyasar da su Mudi Spikin suka yi tundaga kafa Jam’iyyar NEPU da sauran gwagwarmayar Siyasa.

Bari mu fara da tarihin kafuwar Jam’iyyar  NEPU,  kamar yadda tarihi ya bayyana an kafa NEPU ne a ranar 8-8-1950. Haka kuma, mutum takwas ne suka kafa ita wannan jamiyya wadanda suka hada da Bello Ijumu da Abba Maikwaru  da Mudi Sipikin, da Magaji danbatta da Baballiya Manaja  da Musa Kaula  da Abdulkadir danjaji  da kuma Garba Bida. Wadannan sune mutum takwas da suka kafa wannan jam’iyya gwagwarmayar ‘yanto talaka daga kangin bautar sarakuna da Turawa,  bari mu sake  komawa baya kadan domin mu kalli tarihi.
Asalain wannan guguwar sauyi ta fara ne tun lokacin da aka kafa jam’iyyar NCNC (National Council of Nigeria and the Camerroun) a ranar 26 ga watan Augusta a shekarar 1944.  Ita ce jam’iyyar siyasa  ta farko da za a iya kiranta ta kasa baki daya, domin kuwa ta watsu ko ina a Najeriya. Kuma itace jam’iyyar siyasa da ta fara kokarta wa wajen wayar da kan talakan Najeriya domin ya san ‘yancinsa da kuma kokarin samar musu da muryar gabatar da koke-koken da suke da su ga Turawan mulkin mallaka.
A zaben da jam’iyyar NCNC ta yi wa malam Sa’adu Zungur a cikin shekarar 1948 a matsayin sakatarenta na kasa da kuma kokarin da ta yi kokarin ganin cewa kowane bangare na kasar nan ya samu wakilci acikinta, wannan kuma wani gagarumin sauyi ne na siyasar kasar nan. Wannan wayon ‘yan mulkin mallaka ya mayar da hankali wajen jaddada bambance-bambance marasa masalaha da suke tsakanin ‘yan Kudu da ‘yan Arewa a siyasar Najeriya.
Bayan kafa NCNC acikin shekarar 1944 sai aka yi  yajin aiki na kasa baki daya, wanda kuma wannan yajin aiki shi ne na farko a tarihin  Najeriya wanda aka share  kwanaki 44 ana yi. Wannan yajin aiki bayan girgiza   tattalin arziki karkashin ‘yan mulkin mallaka da ‘yan barandansu wato sarakuna, ya kuma nuna afili inda mulkin mallaka yake da rauni da kuma nakasa.
Cif Makel  Imoudu dan majalisar gudanarwa na NCNC ne ya jagoranci wannan yajin aikin da ya gurgunta tattalin arzikin kasa  karkashin Turawan mulkin mallaka. A karkashin wannan fafutuka da NCNC ta yi ne aka dinga ganin jama’a a birane daban- daban suna shirya gangami da aka ringa Allawadai da Bature a fili balo-balo babu tsoro.
Bayan gama wannan gwagwarmaya ne kuma aka samu bullar Northern Elements Prograssibe Association wato NEPA a Kano wadda aka kafa a ranar 1 ga watan Disamba a shekarar 1946, wannan kusan ita ce jam’iyyar siyasar farko daga Arewacin Najeriya. Kafa wannan jam’iyya keda wuya ya bayyana cewa tsatstsauran ra’ayi shi ne mafarinta, wanda kuma shugabannin ta sune irinsu Habib Raji Abdalah da Abubakar Zukogi wadanda kuma alakarsu da Zik ba boyayya ba ce.
Ana cikin irin wannan hali ne kwatsam sai aka wayi gari da bullar sabuwar jam’iyyar Northern elements Prograssibe Union NEPU, kamar yadda muka fada a baya ita wannan jam’iyya ta kafu ne da mutum 8 kuma ranar 8 ga watan 8 a shekarar 1950.
Marigayi Alhaji Abba Maikwaru shi ne ya zama shugaban NEPU na farko  kuma Bello Ijoumu shi ne sakatare. Don haka NEPU ta fara ne amatsayin Jam’yyar siyasar Arewa mai sigar kishin kasa. Kasancewar NEPU ruhinta yana cikin talakawa da manoma da ma’aikata da sauran al’umma da ake dannewa kuma ake zalunta, don haka ne wannan jam’iyya ta sadaukar da manufofinta wajen gwagwarmaya domin ceto al’ummomi da aka danne da kuma kokarin tabbatar da ‘yancin dan Adam da dimokuradiyya.
A shekarar 1976 ne lokacin da aka samu zababbun shugabannin kananan hukumomi wanda aka raba su da sarautar gargajiya. Amma ba’a rabu da bukar ba  domin galibi ‘yan mulkin mallaka sun gadar da mulkin ne zuwa ga ‘yan barandansu na wannan lokaci wato ‘yan boko da sojoji marasa imani da kishin kasa, wadda a yanzu sun shirya komai sai su suke iya zama komai domin daga cikin shegantakar da suka fara yi shi ne cewa babu wanda zai iya tsayawa zabe a zabe shi sai mai takardar shedar gama makarantar sakandare wanda wannan lokaci kaso 90 duk talakawane da ba su yaki jahilci ba, ta hakane bayan mulkin mallakar Turawa kuma aka fuskanci mulkin mallaka karkashin bakake  wadanda su kadai ne ke iya zama gwamna ko ciyaman ko kansila, har ila yau kuma sun mai da karatun boko sai mai kudi ne zai iya yinsa, kuma sai tajirine zai iya biyan kudin shiga zabe.
Bayan wannan hali ne da ake ciki sai aka samu yakin basasar da ya kusan wargaza kasar nan wannan shi ne ya kawo cikas ga cimma nasarorin da NEPU ta sa a gaba ana cikin wannan hali ne sai aka samu bullar jam’iyyar ceton Al’umma wato PRP karkashin jagorancin Malam Aminu Kano wadda kuma aka kaddamar a ranar 28 ga watan Oktoba 1978, a Kaduna. Wannan ta baiwa malam  Aminu Kano damar gwagwarmayar ceto talakwa.
To ko me yabiyo bayan wannan gwagwarmaya? Kusan idan zamu amsa wannan tambayar sai mu ce babu abinda ya biyo bayan wannan gwagwarmaya face Butulci da cin-amana daga shugabanni Na siyasa wanda da gudunmawar talakawa mai yawa aka yi wannan wa-kaci-ka tashi.
Duk da kokarin da jam’iyyar Nepu da PRP suka yi na fitar da talaka daga halin talauci da kangin bauta, amma abin haushi da takaici shi ne haryanzu muna nan a gidan jiya. Talaka ya zama dan maula da tumasanci, baya kishin kansa sannan shugabanni basa kishin kasa, sun sace dukiyar kasa tare da Jahiltar da talakawa.
Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale