Wednesday, July 30, 2014

Abokanka Makasanka

ABOKANKA MAKASANKA


Wani abokina ya bani labari mai daure kai, yace ya gayyaci wasu abokansa su je gidansu dan su ci abincin Sallah, su goma ya gayyata, dukkansu abokansa ne babu wanda ba shi ya gayyata ba. Da suka zo gidan ya kawo abinci kala-kala aka ci akai warisa aka kunna Talabijin aka kalla, kawai Bawan Allah da ya shiga dakinsa sai yaga babu wayarsa kuma babu kudinsa Naira 20000. Ya kira daya daga cikinsu ya sanar masa abinda ya faru, yace tabbas shigowarku na shiga daki na aje wayar da kudin kuma idan banda ku babu wanda ya shigo, kuma gashi ku duka kuna nan. Ya tambayeshi yanzu ya zamu yi, kawai abokin ya fusata yace Wallahi sai anyi caje na rashin mutunci har under wear sai an duba. Anyi cajen kuwa an duba ko ina ajikin kowa amma ba'a ga kudin ba kuma ba'aga waya ba. Sai daga baya aka ga Sim din wayar a cikin Ban-daki, wanda ya dauka da yaga ba zasu satu ba sai ya zuba kudin da wayar cikin Shadda, amma da yake bandaki ne mai ruwa an tsamo wayar kudin kuwa ruwa ya tafi da wasu. Da aka bincika su goma kowa ya shiga ban-dakin.

Wadannan fa wai sune mutanan da ka kyautatawa. Allah ka karemu da mutuwar zuciya.

Yasir Ramadan Gwale 
30-07-2014

Tuesday, July 29, 2014

Hare-Haren Da Aka Kai Kano

HARE-HAREN DA AKA KAI A KANO

"Allah ya sa ba 'yan matan Chibok ba ne aka yi amfani da su wajen kai harin kunar bakin wake a Kano"

Wannan maganar naga mutane da dama suna fadinta tun bayan da aka kai hare-hare a Kano. Wannan maganar sai ta sanya na fara tunin ko jama'a sun fara gamsuwa cewa BH ne ke kai wadannan hare-haren? Allah masani.

Indai tunani na gaskiya ne, to mun kama hanyar magance matsalar da ta addabemu. Babu yadda mutum zai zauna idonsa na ciwo amma yana cewa laifin kafa ne, ya zama dole a sha maganin ciwon ido dan ido ya samu lafiya, idan kuwa za'a bige da neman maganin ciwon kafa to a sannu idon zai mamaye fuska. Allah ya jikan wadan da suka rasu a wadannan hare-haren da 'yan Ta'adda suka kawo Kano, masu raunukan cikinsu Allah ya basu lafiya. Dole mu cigaba da yin addu'o'in Alkunuti da muka saba yi a Ramadan kuma mu yi riko da sababi na neman Allah ya fitar da mu daga wannan halin da muke ciki.

Amma lallai mu sani ba kawai addu'ah zamu yi a wayi gari komai ya lafa ba, harkoki sun koma kamar yadda aka saba, dole ta inda aka hau tanan ake sauka. Zamu zama gidadawa idan har wanda ba Dan Arewa ba watakila ma ba Musulmi ba ya fimu fahimatar yadda za'a shawo kan wannan Bala'i da muke ciki. Tilas a duba hanyoyi na gaskiya dan kawo karshen wannan al'amari. Batun siyasa dole a ajiye shi gefe a yi magana ta gaskiya, rayukan al'umma ne suke salwanta babu ji babu gani.

Matar da ta je saro kalanzir dan ta kasa ta sayar, meye laifinta? Yara kanana da basu balaga ba, meye laifinsu? Wasu da dama Allah yana yi musu talala mai kamar sake a cewar Bahaushe, suna tsammanin akan dai-dai suke saboda suna samun Nasara akan ayyukan barna da suke yi, da sannu irin wadannan mutane ajali zai riskesu sun shirya ko basu shirya, a tashe suna masu nadamar da bazata amfanesu ba, suna kaskantattu wulakantattu.

YASIR RAMADAN GWALE
29-07-2014

Baki Biyu

BAKI BIYU: Abinda yake faruwa Ghazza na aikin Ta'addanci da zalinci da tauye 'yancin Bil-Adama da Israela ta ke yi, Amerika ta goyi bayansa tare da cewa Israela na da ikon kare kanta daga 'yan "ta'adda" a cewarsu. Amma kuma Amerikar da kanta na cewa Russia na taka 'yancin Bil-Adama yayin da ta ke nuna goyan baya ga 'yan ta 'bare a Crimea na kasar Ukrain. Indai abinda Russia ta yi ba daidai bane ko sunansa tauye 'yanci,to na tabbata abinda Israela ke yi a Ghazza shi yafi zama rashin daidai da tauye 'yanci.

YASIR RAMADAN GWALE
29-07-2014

Sunday, July 27, 2014

Sakon Barka Da Sallah Cikin Alhini

SAKON BARKA DA SALLAH CIKIN ALHINI

Amadadin ni YASIR RAMADAN GWALE da Zainab da su Utman, da dukkan 'yan uwa da dangi da abokan arziki muna mika sakon taya murnar Barka Da Sallah na wannan Shekara ga dumbin al'ummar Musulmi musamman a Najeriya da suka Sallahci wannan rana ta yau a matsayin Ranar idin karamar Sallah wanda hakan yake tabbatar da karewar kwanaki 29 masu albarka na watan Ramadan, Allah ya sa ibadun da muka gabatar a wannan wata karbabbu ne, laifukan da muka yi a wannan wata wadan da muke sane da wadan da bama sane Ya Allah kai mai afuwa ne kana son Afuwa, Allah ka yi mana afuwar laifukanmu.

Babu shakka lokacin Sallah lokaci ne na murna da farinciki da kuma ambaton Allah. Ina amfani da wannan damar wajen yiwa kaina Nasiha da jin tsoron Allah da kiyaye dokokin Shari'ah a yayin gudanar da Shagulgulan Sallah. Allah ya maimaita mana ta badin badada lafiya.

Babu shakka dole mu yi alhinin halin da kasarmu ta ke a ciki na zaman zullumi da razani da wadansu makiya Allah makiya zaman lafiya makiya addinin Allah suka sanyamu a ciki, Ya Allah kasansu kasan duk inda suke a labe, kasan irin makircin da suke kulla mana Allumma rudda kaiduhum Alaihim! Al'ummar Musulmi da yawa a yankin Ghazza na Palastine zasu yi Sallah a gobe cikin tashin hankali da fargaba da razanai sakamakon hare-haren zalinci da Israela ke kai musu, Allah ka amintar da su ka sanya wadan da suka rasu su tashi a matsayin Shahidai, yan uwanmu da aka karkashe a Borno da Yobe da Adamawa da Kano da Kaduna da sauran jihohinmu Allah ka jikansu ka gafarta musu.

Allah ka bamu lafiya da zaman lafiya a duk inda muke. Yana da kyau idan mun hadu da juna mu yiwa juna addu'ah tare da fatan karbuwar ibadunmu. Wata Shekara a BUK Sheikh Abubakar Jibrin ya ce a Rungume juna a yi murna. Barka Da Sallah.

Yasir Ramadan Gwale
27-07-2014

Saturday, July 26, 2014

Abin Al-Ajabi Mai Ban Tausayi

ABIN AL'AJABI MAI BAN TAUSAYI

Da yawa daga cikin jaridun kasashen larabawa na yau Asabar sun ruwaito labarin wata jaririya mai cike da ban tausayi da kuma ban al'ajabi. Ita dai wannan jarirya an haifeta ne bayan da mahaifiyar ta da ke dauke da cikinta ta rasu. Mahaifiyar wannan jaririya mai suna Sheima tana kwance kan gadonta a dakinta a birnin Ghazza a daidai lokacin da sojojin Israela suka harbo wani makamin roka da ya sauka akan gidansu, nan take gidan ya rushe gaba daya, mahaifiyar wannan jaririya ta yi kokarin kubutar da ranta da na d'an cikinta, amma ina! Sheima ta rasu a sakamakon munanan raunuka da ta samu sakamakon manyan duwatsun da suka rufto akanta, cikin gaggawa matasan Palasdinawa masu taimako suka tono Sheima daga cikin barguzan ginin da ya rushe akanta aka garzaya da ita Mustashfa.

Bayan da aka garzaya asibiti da wannan baiwar Allah ne aka tarar tuni Allah ya yi mata cikawa. Ba tare da wani bata lokaci ba likitoci suka shiga kokarin ceton abinda ke cikin matar, cikin taimakon Allah aka yi sa'ar farka cikin matar aka ciro jaririya da ranta. Ita dai wannan jaririya yanzu haka tana asibiti ana kula da ita, likitan da ya yi aikin ceton wannan jaririya Dr. Fadi ya yiwa Allah godiya da ya basu ikon ceton ran wannan jaririya, sannan ya kuma yi bayanin cewa hakika ya tausayawa wannan jaririya domin ta zo duniya a wani irin yanayi na tashin hankali da ya mamaye yankin Ghazza, gashi an kashe mahaifiyarta an kuma kashe mahaifinta.

Yanzu dai tuni dangin wannan jaririya suka bayyanawa duniya cewar sun mayarwa da jaririyar sunan Mahaifiyarta. Allah ya jikan mahaifiyar wannan jaririya ya gafarta mata. Allah ya taimakin Musulunci da Musulmi ya kaskantar da kafurci da kafurai. Mutanan Ghazza Allah ya taimake su akan abokan gaba.

Yasir Ramadan Gwale
26-07-2014

Thursday, July 24, 2014

Gaskiya Daya Ce

GASKIYA DAYA CE

Mu 'yan Arewa muna addu'ar Allah ya yi mana maganin abubuwan da suke faruwa na tashe-tashen Bama-bamai, amma a gefe guda kuma mun kauda kai daga ainihin masu laifi muna jingina laifi ga Goodluck Jonathan da cewa shi ne yake kashe 'yan Arewa, su kuma 'yan Kudu suna ganin duk dan Arewa dan BH ne, a gefe guda kuma su 'yan Boko Haram da na yi Imani sune suke aikata wannan ta'addancin mun kauda kai daga garesu suna ta cin karensu babu babbaka.

Wallahi matukar muka cigaba da juya baya ga gaskiya haka zamu wayi gari sun mamaye ko ina da hare-harensu, tunda muna kauda kai a garesu. Indai da gaske muke fatan karbuwar addu'armu akan abubuwan da suke faruwa dole mu nemi inda gaskiya ta ke dan ayi amaganin wannan al'amari. Ta yaya ido yana ciwo ana cewa laifin kafa ce sannan a yi zaton samun waraka? Ya zama dole mu gayawa kanmu gaskiya, ga inda laifi yake, ga inda matsala ta ke muna ji muna gani amma muna yin buris da cewa ba hakan bane.

Yakamata mu ajiye duk wani batu na Siyasa mu fuskanci gaskiyar abubuwan da suke faruwa, rayukan al'ummarmu suke salwanta dare da rana. Duk wanda ya kalli Video da Sahara Reporters suka sanya na sojan Air Force mai suna Umar Abubakar da su 'yan BH suka kama suka yanka, zai tabbatar da cewa abinda ke faruwa sune suke aikatawa, domin su basu yarda cewa Muluncin da muke yi gaskiya ba ne, a wajensu duk wanda ya saba da aqidarsu dagutu ne jininsa ya halatta. Tayaya mutanan da suke da irin wannan ra'ayi da tunani da suka yi imani su mutu akansa, zasu tausayawa al'umma?

Indai gaskiya muke nema dole mu nemi inda ta ke, idan kuma zamu cigaba da kauda kai ga masu laifi, to babu shakka har jikokinmu zasu bamu labari ko bayan ranmu na irin abinda ke faruwa. Wasu da yawa kanyi tambayar wai a ina su 'yan BH suke samun makamai da kudade. Wannan tambaya ce mai kyau, amma kuma an manta cewa duk kumgiyoyin 'yan Ta'adda irinsu Al-Qaida da Alshabab da Hizbola da sauransu duk jirgi daya ya kwaso su da BH inda suke hanyarsu duk iri daya ce. Shi Shedan ai danginsa yawa garesu kuma sashinsu na taimakon sashi.

Yasir Ramadan Gwale
24-07-2014

Kano

KANO: Jiya muka yi alhinin abinda ya faru a Kaduna na tashin bom da ya yi sanadiyar halakar mutane da dama, kwatsam kuma yau muma sai gashi an gaishemu da shi a Kano. Babu shakka Allah Buwayi Gagara Misali Assami'u Ne kuma Albasiru! Idan wadannan masu tayar da hankali sun faku a garemu babu shakka ba zasu iya kaucewa ganin Ubangiji ba. Muna tunawa wadannan miyagu azzalumai cewa tunda Allah ya halicci duniya ya halicci lokaci, da sannu suma lokacinsu zai riskesu, zasu su mutu suna wulakantattu abin wualakntawa. In Sha Allahu azzalaumai ba zaku ci nasara ba, ku koma ku karanta tarihi babu wani wanda ya shuka zalinci kuma rayuwarsa ta dore, duk wani dan iska da yace muku wannan hanya ce ta shiga Al-jannah ya cuceku, da ku da shi zaku dandana kudarku a wajen Allah ba zamu gushe ba muna yi muka fatan Narko na azabar Allah. Miyagu azzalumai 'yan ta'adda marasa tsoron Allah munafukai.

Ya Allah ba dan halinmu ba, Ya Allah ba dan laifukan da muka aikata ba, Ya Allah mun tuba ka yafe mana laifukanmu. Allah ka bamu lafiya da zaman lafiya, Ya Allah kada ka baiwa mmiyagu azzalumai 'yan Ta'adda Nasara akan al'ummarmu. Allah duk wadan da suke shirya wannan mummnan tashin hankali Allah ka sansu kasan a duk inda suke Allah ka wargaza sha'aninsu, Allah ka rusa su, Allah ka dammara su, Allah karka basu alherin duniya da lahira. Allah ka azabtarda su azaba mai radadi.

Allah ka amintar da mu. Allah ka bamu lafiya da zaman lafiya. Wadan da suka rasa rayukansu a tsakanin jiya a Kaduna da yau a Kano Allah ya jikansu ya gafarta musu, wadan da suka jikkata kuma Allah ka basu lafiya, Allah ka sanya abinda ya samesu ya zama kaffara a garesu. Allahumma Taqabbal Minna Du'a'ana Ya Rabbal Alameen.

YASIR RAMADAN GWALE
24-07-2014

Kaduna


KADUNA: Gwamnatin jihar Kaduna karkashin jagorancin Gwamna Mukhtar Ramalan YERO ta dage dokar hana fita da aka sanya a jiya ta tsawon awa 24 a cikin garin Kaduna. Wannan sanarwa ta fito ne ta bakin mai taimakawa Gwamna na musamman akan harkokin yada labarai Ahmed Maiyaki. Dan haka, Gwamnati na kiran jama'a da su fita harkokinsu na yau da kullum. Allah ya bamu lafiya da zaman lafiya mai dorewa.

YASIR RAMADAN GWALE
24-07-2014

Wednesday, July 23, 2014

Karshen Magana

KARSHEN MAGANA: Dazu kenan a fadar Shugaban Kasa yayin da Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II ya je fadar dan yin buda baki tare da Shugaban Kasa Dr. Goodluck Jonathan. Wannan gaisawa ta rufe kofar dukkan wata gutsiri tsoma da turka turka tsakanin fadar Shugaban Kasa Da Sarkin Kano. Allah ya taimaki Shugabanninmu ya hada kansu wajen yiwa al'ummar Kasa aiki. Babu shakka naji dadin wannan ziyara da Sarkin Kano ya kai fadar Shugaban kasa, dan sabanin ba zai taba zama alheri ba.

YASIR RAMADAN GWALE
23-07-2014

Zaman Lafiya


ZAMAN LAFIYA

Yana da kyau a;'ummar Najeriya mu maida hankali wajen duban hanyoyi sahihai na yadda za'a dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a dukkan sassan kasarnan. Duba da irin abubuwan da suke faruwa suna nuna cewa kasarmu Najeriya tana da wasu mugayen makiya da basa yi mata wani fata face na rugujewa, suna aiki babu dare babu rana wajen ganin sun firhita al'umma an koresu daga garuruwansu. Da dama al'ummar kudancin jihar Borno sun tsere daga gidajensu wasu sun koma Kamaru wasu Cadi wasu nijar, mwannan babban abin takaici ne mutane su bar mahaifarsu akan laifin da basu aikata ba. Lallai sai mun tashi tsaye wajen ganin wadannan miyagu azzalumai basu ci nasarar wagaza mana kasa ba. Mu sani ba muda wata kasa da zamu je mu yi tinkaho da ita face wannan kasar tamu, babu inda muke da kima da mutunci face a cikin kasarmu. Ya zama dole muyi duk abinda zamu iya wajen ganin kasarmu bata wargaje ba, dole mu koyti yadda zamu zauna da juna lafiya da sauran al'ummat kasarnan.

Yasir Ramadan Gwale
20-07-2014

Jaje Na Ga Gwamnaton Kaduna Da General Muhammadu Bugari

Ramalan Yero
KADUNA: Ba babu shakka labarin da ya fito daga garin Kaduna a almurun yau labari ne mai kada zukata. In Sha Allahu 'yan Ta'adda Miyagu Azzalumai ba za su ci nasara ba, da sannu suma ajalinsu zai riske su, su mutu suna wulakantattu kaskantattu batattu. Allah ka rusa su Allah ka darkakesu ka wargaza duk wani mummunan nufinsu akan al'ummar Musulmi, Ya Allah albarkar wadannan kwanaki da suka rage ba dan halinmu ba Ya Allah ka kawo mana dauki, Allah ka dawo mana da dawwamammen zaman lafiya a kasarmu. Allah ka jikan wadan da suka rasa rayukansu a wannan mummunan tashin hankali.

Lallai wajibin hukumomi ne su dauki dukkan wasu matakai na samar da nutsuwa a cikin zukatan al'ummar da suke Shugabanta, Allah ka baiwa shugabanninmu ikon daukar matakan da suka dace domin dakile wannan Ta'addanci. A madadina da 'yan uwa da abokaina muna mika ta'aziyarmu ga gwamnatin Kaduna da al'ummar jihar Kaduna Allah ya jikan wadan da suka rasu, masu raunuka Allah ka basu lafiya. Muna kuma mika sakon jaje ga Babanmu General Muhammadu Buhari a bisa wannan abu da ya faru da shi, Allah ya kara kiyayewa Allahumma Ameen. Haka kuma muna mika jajenmu ga Sheikh Dahiru Usman Bauchi da shima wannan ibtila'i ya kusa rutsawa da shi, Allah ya kare su da karewarsa. Allah ya bamu lafiya da zaman lafiya.

YASIR RAMADAN GWALE
23-07-2014

PALASTINE: Tun Ina Yaro Karami

PALASTINE: TUN INA YARO KARAMI

Tunda na tashi na fara wayo nake jin sunaye irinsu Madeline Olbright, Ahmed Yassin, Yassir Arafat, George H.W Bush, Bill Clinton, Shimon Firez, Yitzhak Rabbil, Ariel Sharron, Hosny Mubarack da sunayan gurare irinsu Camp David, Geneva, Oslo, New York, Whitehouse, Pentagon, Sham-el-Sheikh . . . Daga nan na fara fahimtar batun tattaunawa tsakanin Israela da Palastine, ina iya tunawa tun Gemun Malam Yassir Arafat bai yi fari fat nake ganinsa a kusa da Bill Clinton da Shimon Firez ana daukarsu hotuna a Camp David ana ta turanci, ina iya tuna lokacin da idan an nuno wata dattijuwa tana sanye da jan baki gashinta ruwan zuma a gaban lasifikoki da yawa tana turanci naji a gida ana cewa wannan dai shedaniyar mata ce, har na saba da ganin hotonta a TV na fahimci sunanta Madeline Olbright, har na fahimci ita ce sakatariyar harkokin wajen Amerika.

Tafi tafi na saba da jin labarin irin tattaunawar da ake yi a gidan shakatawar Shugaban kasar Amerika na Camp David, da Sham-el-Sheikh a Masar, idona ya saba da ganin wani dattijo da ake turawa a kan kujera yana zaune da farin hirami akansa da dogon gemunsa, mutane suna ta zuwa suna sumbatar hannunsa da kumatunsa ashe shi ne Shugaban Hamas Sheikh Ahmad Yassin Allah ya jikansa.

Tun a wancan lokaci idan na tashi da safe nakan ga mahaifina yana jin BBC ko VOA ana labarin tattaunawa a Geneva ko a Sham-el-Sheikh a lokacin nake sauraron su Sale Halliru su Isa Jikamshi suna bada labarin fadace-fadace da ake yi a kasashen Larabawa musamman Palastine,

A lokacin da gidan talabijin na Al-Jazeera na larabci ya fara watsa shirye shiryensa na fara jin kalmomi irinsu INTIFADA ina ganin wani mutum da lasifika a hannu yana larabci idan ya gama yace Akram Khuzam Al-Jazeerah Moscow nake jin irinsu Tayseer Alluni suna ta bayani yadda ake ta yin gaganiya a duniya.

Tun a wancan lokacin da na saba da jin labarin abinda ke faruwa a Palasdinu na san sunan Ghazza da Ramallah da Hizbullah da Fatah da Hamas da Jihadil Islami. Har yanzu haka ina jin wannan labari kuma akan matsala kwaya daya da na tashi naji ana ta batunta a ko da yaushe ita ce dai har yanzu ake tattaunawa, wanda a ganina duk wasu maganganu da ya kamata a fada tuntuni anyisu a baya.

Har ta kawo gashi yanzu da na kakkaranta tarihi da dama akan abinda ya faffaru a baya ba ni da wayo, har na zama ina da masaniyar irin wainar da ake toyawa a gabas ta tsakiya kuma zan bibiyi abinda yake faruwa a Ghazza na yi sharhinsa. Duniya Makaranta ce mai cike da dumbin ilimi! Lallai al'ummar Palastine sun jima suna cikin ukubar Israela. Allah ka yaye musu wannan masifa da bala'i.

YASIR RAMADAN GWALE
23-07-2014


Makaryata-Mayaudara-Munafukai

MAKARYATA: Wato babu wani abu a cikin harkokin Diplomasiyya kamar karya da yaudara da sauyawa gaskiya wurin zama. Dukkan maganganun da Kerry ya yi a Cairo da wadan da Ban ki-Moon ya yi a Tel Aviv da wadan da Netanyahu da Mahmoud Abbas suke yi sai ka rasa ina hankalin mutnan duniya yake irin yadda suke juya gaskiya kiri-kiri akan abinda ke faruwa a Ghazza. Ta yaya Isareal ta kashe mutanan Ghazza sama da mutum 600 daga 8 ga wannan watan zuwa yau, su kuma 'yan Hamas ana cewa sun kashe 'yan Israela 28 amma duk da haka a UN da Whitehouse da Cairo a dinga ce mana wai Israela na da 'yancin kare kanta! Ta yaya za a iya fahimtar da ni wannan dodoridon?

Israela ta kashe mata da yara da tsoffi ta rusa masallatai ta doki asibitoci da makaranta tana kai hare-hare ta sama da ta kasa da ta cikin teku ace amma wai kare kanta ta ke yi. Amma kuma wai ace Israela ba Palasdinawa ta ke yaka ba, ita da 'yan Hamas take fada. Wannan wacce irin yaudara ce haka, mutane da hankalinmu a maida mu kamar bama fahimtar rayuwa!

Su kansu Shugabannin kungiyar Hamas din da galibinsu sun tare a kasar Qatar suna kwance cikin Ni'ima ana can ana kashe talakawa sai dai kawai surutai da suke ta faman yi marasa kan gado. Itama Gwamnatin Abbas dake Ramallah daman ita da hannun Israeli a kafuwarta babu wani katabus da zasu iya yi. Illa shirme da shirita, domin shekaru nawa ana tattaunawa a Camp David wace irin matsaya ce ba'a cimma ba, babu wani abu da aka cimma da Israela bata sa kafa ta shure ba, amma kuma su Abbas suna cewa wai a tattuna. Ina amfanin Shan ruwa idan baya maganin kishruwa?

Amma kuma duk wannan cin kare babu babbaka da Israela ta ke yi su Abbas da 'yan kanzaginsu sai su nunawa duniya cewai wai abinda yake faruwa ba na addini ba ne, tsakanin Laabawa ne da Yahudawa 'yan share wuri zauna. Allah ka kiyashe mu tabewa.

Hanya guda daya ce da kasashen Larabawa (Musulmi) zasu iya ladabtar da Isarela akan Ghazza. Wannan hanyar kuwa ita ce, su ce sun daina hako Man Fetur har sai Israela ta kwashe tarin jami'an tsaronta daga yankunan Palasdinawa da ta mamaye, sannan su dawo da sayar da man fetur, Na yi Imani irin wannan yaren ne kadai zai shiga kunnuwan Amerika da ita Israelar. Wanda wannan wata hanya ce mai wuyar bi da irinsu marigayi Sarki Faisal na Sa'udiyya ne kadai zasu iya bi babu wata fargaba, Allah ya jikansa da gafara.

Babu shakka abubuwan da suke faruwa a Ghazza kullum kara kazancewa suke yi, asarar rayuka karuwa ta ke yi cikin sauri. Allah ka agazawa wadannan mutane.

YASIR RAMADAN GWALE
23-07-2014

Tuesday, July 22, 2014

Shin Akwai Wadan Da Za Su Iya Tunkarar Israela?

Obama Da Netanyahu
SHIN AKWAI WADAN DA ZA SU IYA TUNKARAR ISRAELA?

IIsraela tafi karfin kowa a kasashen Musulmi ta fuskar karfin Makamai da karfin fasaha. Hatta kasashe irin su Pakistan da suka mallaki Nukiliya babu yadda zasu iya da Israela ballantana kuma kasashen larabawa da galibi Israelawa ke kera musu makaman da suke saya a Amurka. Dan haka dole kowa ya yi Shakkar Israela. Abu mafi muhimmanci shi ne mutane da shugabannin kasashen Musulmi su komawa Alkur'ani su karanta Me Allah ya fada akan Yahudawa. Sannan a koma zuwa ga Allah, a yi riko da dukkan sabubba na karbar addu'ah da kuma cin Nasara a rayuwa.

Amma zance na gaskiya Israela tafi karfin kowa. Duk wasu da ake zaton za su iya yin wani abu akan Isarela suma sun san babu abinda zasu iya illai kawai surutai a gidajen Radiyo da Talabijin. Majalisar dinkin duniya a aljihun Amerika ta ke babu wani abu da take aiwatarwa face ra'ayin Amerika. Haka kuma, ita Amerikan kanta a cikin tafin hannun Israela ta ke, dan haka duk wani surutu da za'ai a majalisar dinkin duniya akan Israela duk zancen banza ne.

Sanin kowa ne babu wani hakki na bil Adama da Israela bata taka shi ta murje a Ghazza ba, amma wa ya isa yace Uwar Sarki Mayya ce? Shi ya sa sai ayi ta kewaye kewayen cewa ai Israela na da damar kare kanta daga hare-haren rokokin 'yan Hamas, mutanan da galibin makaman da suke harbawa a sararin iska suke watsewa.

Wasu da dama kuma kan zargi shugabannin kasashen Larabawa da cewa sun kasa yin wani abu a Ghazza. NA farko dai ya kamata mu sani duk wani abu da larabawa zasu yi akan Ghazza ko Israela to bai wuce SURUTU na fatar baki ba, domin sunfi kowa sanin wace Israela da irin karfin da ta ke da shi ta fuskar karfin Makamai. Israela kadai tafi dukkan kasashen gabas ta tsakiya karfin Makamai. Sai dai kawai idan za ai siyasar yarjejeniya kaji Hizbola na cika baki alhali babu abinda zasu iya, su kuma Iran da yake munafukai ne sai su ce ai sune suke taimakawa Palasdinawa da makamai, indai gaskiya ne muji karajin makaman da Tehran ke da su a biranen Ashdod da Tel Aviv.

Abinda na yi Imani kadai zai iya rusa Israela shi ne karfin ikon Allah, da kuma karfin Imani na wadan da ake zalunta. Israela idan tafi karfin kowa bata fi karfin Allah ba, fatan kawai shi ne mu dage da addu'ah mu kuma yi riko da sabubban karbar addu'ah, sannan a gefe daya surutan da ake yi a cigaba duk da babu wani tasiri da yake yi, dan in duk duniya zata cika da zangar-zangar kyamar Israela to su ko a jikinsu wai an tsikari kausasa.

Muna rokon Allah ya kaiwa Palasdinawa masu rauni dauki, Allah ya amintar da su. Su kuma Yahudawa Allah ya fimu sanin abinda yafi cancanta da su, Allah ya yi musu ninkin ba-ninkn abinda suka yiwa Musulmi na cin zali.

YASIR RAMADAN GWALE
22-07-2014

Monday, July 21, 2014

RA'AYINA: Ziyarar Wasu Malamai Zuwa Fadar Shugaban Kasa Dan Yin Karin Kumallo

RA'AYI NA: ZIYARAR WASU MALAMAI ZUWA FADAR SHUGABAN KASA DAN YIN KARIN KUMALLO 
 
Ni kam banga wani abin cece kuce ba dan wasu Malamai sun je fadar Shugaban Kasa sun karya kumallo tare da shi a yayin da suka kai Azumi. Wannan ai ba wani abin bata lokaci bane, a matsayinsu na 'yan Najeriya suna da ikon amsa gayyatar karin kumallo idan Shugaban kasa ya gayyace su. Addinin Musulunci ai ba Addini ba ne da yake kyamar wanda ba Musulmi ba, Manzon Allah SAW ya karrama Abu Sufyan Sarkin Makkah a lokacin kuma shi ba Musulmi ba ne.

Ni fatan da nake yi ma ace sun yiwa Shugaban Wa'azi sun gaya masa Me Allah Yace, sun gaya masa irin nauyin hakkin Shugabanci da irin nauyin da yake kan Shugaban kasa na yiwa 'yan Najeriya Adalci a matsayinsa na Shugaban kasa. Allah ya sa sun karanta masa Al-Qur'ani ya saurara, na yi Imani Shugaban ba'a taba zama kusa da shi an karanta masa ayoyin Al-Qur;ani ba. Ai a Africa an taba yin wani Shugaban Kasa da Ya Musulunta yana kan Mulki, idan aka yi sa'a ai sai Shugaban ya tuba yabi Allah.

Shugaban kasar Ghana John Dramani Mohamma har masallacin Idi yake zuwa dan taya Musulmi murnar Sallah, duk da shi a Zaune yake baya yin Sallar sannan kuma idan ya koma gida ya yanka rago. Ko babu komai ai ya nunawa Musulmin kasar cewa shi Shugaban Kasar ne baki daya ba na wasu mutane kawai ba.

Yanzu idan Malamai basa kusantar masu Mulki suna gaya musu gaskiya suna yi musu wa'azi, shin su Doyin Okupe ko Ruben Abati muke tunanin zasu dinga yiwa Shugaban kasar Wa'azi? Ai ni babban Buri na ma shi ne Kungiyar Izala ta shirya gagarumin Wa'azin Kasa a sake gayyatar Shugaban Kasa Dr. Goodluck Jonathan a samu Alaramma Yahuza Bauchi ko Alaramma Ahmad Sulaiman sun dinga rera karatun Al-qur'ani Shugaban yana ji da kunnensa.

Dan haka ina kira ga duk wani Malami ko Alaramma da ya samu gayyata zuwa fadar shugaban kasa dan su karya kumallo to ya amsa wannan gayyata, kuma ya yi kokari ya yiwa Shugaban kasa wa'azi ya karanta masa alkur'ani ya saurara. Jama'a kuma ya kamata a daina aibata Malamai dan sun amsa gayyatar Shugaban kasa. Ai mu 'yan Najeriya ne, Goodlock kuma shi ne shugaban kasa ko muna so ko bama so, ko mun ki ko mun so babu yadda muka iya shi ne dai Shugaban kasa.

Yanzu jama'a shi kenan sai mu hadu mu duka mu nade hannu, mu ce ba za'a yi gwamnati da mu ba sai lokacin da namu ya samu? To idan namu bai samu ba shi kenan sai mu yi ta zama a haka? Ku su mutanan kudu kame hannu sukai lokacin da namu suna Mulki suka ce babu ruwansu sai lokacin da nasu ya samu? Allah ka shiryi Shugaban kasar Najeriya Alfarmar wadannan kwanaki, Allah ka sanya Imani da tsoronka a cikin zuciyarsa, Allah ka sa ya fahimci irin girman hakkin da yake kansa na jagoranci. Allah kai ne mai juya zukata Allah ka juyo da zukatansa zuwa ga aikata daidai. Mu kuma mabiya Allah ka kara mana juriya da hakuri kuma ka bamu ladan hakuri. Allah ka nuna mana gaskiya a duk inda take ka bamu ikon aiki da ita, ka nuna mana karya ka bamu ikon kauce mata.

YASIR RAMADAN GWALE
21-07-2014


Magidanci Ya Yiwa Wani Matshi Dukan Kawo Wuka

WAL MAKALUFATU 'Da Sassabawar Kamanni' WANI MATASHI YASHA DUKAN TSIYA

Jaridar Independent ta kasar Burtaniya ta ruwaito labarin wani matashi mai suna Raymond Frolander dan shekara 18 da aka yiwa dukan kawo wuka. Magidancin dai ya bugawa 'yan Sanda waya ne ta lambar 911 yana sanar da su su hanzarta kaiwa matashin da ya yiwa dukan kawo wuka dauki, sakamakon kama matashin da yayi yana lalat da 'dansa mai shekaru 11.

'Yan sanda basu yi wata wata ba suka hanrta zuwa inda Raymond Frolander ke yashe ikin jini male-male, inda nan da na suka garzaya da shi dan neman ceton ransa, daga bisani kuma aka zargi matashin da laifin cin zarafin kananan yara ta hanyar yin lalata da su. Da yake bada bahasi bayan da abin ya fito yaron da aka yi lalata da shi yace, kusan tun yana dan shekaru 8 Raymond ke yin lalata da shi dubunsa bata cika ba sai a wannan lokacin da da mahaifin yaron ya kamasu. Yaron ya cigaba da cewa, a duk lokacin da yaje wajen wasa Raymond kam biyoshi ta haka ne har ya saba da shi kuma har yake zuwa gidansu, rahotanni sun tabbatar da cewa iyayan yaron sun saba sosai da matashin Raymond sakamakon zuwa gidan da yake yi akai-akai.

Sai dai a nasu bangaren 'yan Sanda sun ce ba zasu zargi mahaifin yaron da aikata wani laifi ba, domin a cewarsu mahaifin ya aikata abinda ya aikata ne dan kare dansa, haka kuma dan sanda mai gabatar da kara Daytona Police lallai mahaifin yaron ya cika uba na gari. Allah ya shirya su mu kuma ya karemu ya kare mana zuriyarmu.

YASIR RAMADAN GWALE
21-07-2014

Thursday, July 17, 2014

Azumin Obama

AZUMIN OBAMA:

A yau jaridar The Citizen ta kasar Sudan ta ruwaito cewar shugaban kasar Amurka Barack Obama yana Azumi kuma yana gayyatar dukkan al'ummar Musulmi zuwa fadar White House domin yin buda baki da shi. Obama na yin azumi ne dan taya al'ummar Musulmi murnar shigowar watan Ramadan mai alfarma. Obaman yace ba wannan ne karon farko da ya taba yin azumi ba, kuma zai buda baki da Dabino ne da bakin ruwa kamar yadda Musulunci ya koyar.

Sai dai a wata sanarwa da kungiyar al'ummar Larabawa ta kasar Amurka mai suna American-Arab-Anti Discreminiation Committee fitar ta yi kira akan dukkan Larabawa da sauran Musulmi da su kauracewa wannan shan ruwa da Obama ya kira, a cewarsu sunyi hakan ne dan nuna fushinsu akan irin goyon bayan da Obama ya ke baiwa Israela na gallazawa al'ummar Ghazza da ta ke yi a 'yan kwanakin nan.


Shekaru 20 Bayan Da Aka Yiwa Musulmi Kisan Kiyashi A Srebrenica: Kotun Duniya Ta Yi Adalci

SHEKARU 20 BAYAN DA AKA YIWA MUSULMI KISAN KIYASHI A SREBRENICA: Kotun Duniya Ta Yi Adalci

Munira Subasic take cewa da misalin lokacin zawali muna zaune a sansanin 'yan gudun hijira a Srebrenica tun bayan barkewar yaki a Bosnia inda aka farwa Musulmi da kisa babu ji babu gani, tun cikin shekarar 1992, da gumu ta yi gumu yaki yayi yaki ne can wajen shekarar 1995 aka kwaso ragowar Musulmin da suka yi saura aka tattaremu a Srebrenica karkashin kulawar sojojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar dinkin duniya, a cewa Munira muna zaune da zawalin wannan ranar sai ga rundunar mayakan turawa karkashin jagorancin General Ratko Mladić suka kewayemu, suka ware mata daga cikinmu da tsofaffi sai ya rage saura zaratan samari da kuma mazajenmu.

Munira ta kara da cewa da idona naga an hallaka mijina da kuma d'ana, a wannan ranar sai da aka kashe sama da mazaje 8000 a gaban idan sojojin Majalisar dinkin duniya ba tare da sun daga ko icce ba, duk kuwa da irin kururwa da neman taimako da muka dinga yi, muna a taimakawa mazajenmu, amma ihunmu ya kare a kunnen kurame.

Tsohon sakatare Janar na Majalisar dinkin duniya Mista Kofi Aan ya bayyana abin da ya faru a Srebrenica da cewa kisan kiyashi ne da aka yiwa wata al'umma; ya kuma kara da cewa abin da ya faru wani bakin shafi ne a cikin kundin tarihin majalisar dinkin duniya, yaci gaba da cewa, wannan kisan kiyashi da aka yi a Srebrenica shi ne irinsa na biyu a tun bayan yakin duniya na biyu da aka yiwa a Turai, ya kuma bayyana shi da wani abin Allah wadai da dan Adan ya aikawa dan Adam.

Sai dai tun bayan wannan ta'addanci da sojojin turawa suka aikata a watan yulin 1995 a Srebrenica, wadan da abin ya shafa sun shigar da kara kotun hukunta manyan laifukan yaki ta duniya dake Hague a kasar Holland. A jiya dai masu gudanar da wannan Shari'ah sun yanke hukunci na karshe tun bayan shekaru 20 da aikata wannan kisan kiyashi, inda suka zargi kasar ta Holland da alhakin abinda ya faru, domin suna da masaniayr hakan zata faru amma suka sanya aka kawo musulmin Bosnia zuwa Srebrenica, haka kuma kotun ta bukaci a biya iyalai 300 diyyar raykan da aka kashe musu.

YASIR RAMADAN GWALE
17-07-2014

Wednesday, July 9, 2014

Al-amura Sun Ta'azzara a Yankin Zirin Ghazza



AL'AMURA SUN TA'AZZARA A YANKIN ZIRIN GHAZZA

Babu shakka a cikin wannan makon al'amura sun ta'azzara a yankin zirin Ghazza ta Palastinu tun bayan kisan matashin nan Muhammad Abu Kheidr dan shekaru 16 da wasu Yahudawa suka halaka shi a Jerusalem. Wannan kisa na Muhammad Abu Kheidr ya ja hankalin kasashen duniya sosai, kasancewar matashin da aka kashe yaro karami, wannan ta sanya Piraministan Israela Benyamin Netanyahu ya fito ya yi Allah wadai da kisan da Yahudawa Barbarar yanyawa sukaiwa bapalasdine, inda ya bayyana kisan da cewa wani abin takaici ne mai muni da ya zubar da mutuncin Yahudawa, ya kuma sha alwashin kamo wadan da suka yi wannan kisa tare da hukunta su. Sai dai kungiyar Hamas da ke da iko da Birnin Ghazza da kuma Gwamnatin Mahmoud Abbas Abu-Mazein ta soki lamirin wannan kisa da aka yiwa Muhammad Abu Kheidr.

A nasu bangaren, kungiyar Hamas ta sha alwashin kai hare-haren ramuwar gayya da makaman roka, inda rahotannin daga kafafen yada labarai na kasashen Turai suka bayyana cewar an harba Makaman Roka sama da 200 zuwa cikin yankin kasar Israela daga zirin Ghazza. Tun bayan wannan hare-hare ne aka jiyo Netanyahu na magana da kakkausar suka akan wadannan hare-hare na ramuwar gayya, duk kuwa da gagarumin sabanin da aka samu a gwamnatin natenyahu tsakaninsa da Ministan harkokin wajen Israela Agvidol Liberman.

Al'ummar kasar Palastinu da ke yankin zirin Ghazza sun ga tashin hankali mummunan daga irin hare-haren da Israela ta ke kaiwa babu kakkautawa zuwa yankin, duk kuwa da cewar suna dauke da Azumi. Babu shakka Israela ta yi muguwar barna a yankin Ghazza tare da kashe mutane da dama da jikkata wasu da rusa gidaje da makarantu a yankin na Ghazza. A nasu bangaren mai magana da yawon fadar White House dake Amurka ta nuna cewar Israela na da ikon kare kanta daga hare-haren Roka. shima a nasa bangaren Sakatare Janar na majalisar dinkin duniya Banki-Moon ya yi kira da cewa akai zuciya nesa, dan wannan ba lokaci bane na ramuwar gayya a cewarsa.

Hakika Palastinawa dake yankin Ghazza suna cikin ukuba da Israela ta ke yi musu. Ya Allah ka kai musu dauki, ka wargaza dukkan wani shiri na Azzalaumar haramtacciyar kasar Israela, ka rusa gwamnatin Netanyahu da 'yan kanzaginsa da masu goya masa baya. Allah ya baiwa Palasdinawa nasara akan abokan gabarsu, Allah ka daukaki Musulunci da Musulmi ka kaskantar da kafirci da kafirai.

Yasir Ramadan Gwale
10-07-2014

Godiya Ta Musamman Daga Mundubawa Kano

Sabon Ministan Ilimi Malam Ibrahim Shekarau
GODIYA TA MUSAMMAN DAGA MUNDUBAWA KANO

Muna amfani da wannan damar wajen nuna godiya da jinjina ga dumbin al'ummar da sukai ta aiko da sakwannin fatan alheri ga Sabon Ministan Ilimi na tarayyar Najeriya Malam Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano, hakika jama'a da dama a ciki da wajen Najeriya sun nuna mana soyayya a bisa wannan cigaba da al'ummar Jihar kano da Arewacin Najeriya suka samu na sabon Minista a majalisar zartarwa ta Najeriya. Allah ya sakawa kowa da alheri ya baiwa sabon Ministan Ilimi ikon aiwatar da ayyukan da suke tattare da ofishinsa, Allah ya bashi ikon kawo sauye-sauye masu ma'ana a iya tsawon wa'adin mulkinsa.

Haka kuma, Fadar Mundubawa na maraba da dukkan shawarwari ga sabon Ministan Ilimi daga kowanne Dan Najeriya, kofa a bude ta ke ga duk wanda yake da wata fikra wadda zata ciyar da harkar ilimi gaba a Najeriya. Allah ya taimaki Najeriya, ya azurtamu da shugabanni na gari Adalai.

YASIR RAMADAN GWALE
10-07-2014

Monday, July 7, 2014

Kira Na Musamman Daga Mata

KIRA NA MUSAMMAN DAGA MATA

Na samu sakwannin inbox daga 'yan uwanmu mata suna ta rokon da ku sanya su cikin addu'o'inku a yayin buda baki da lokacin add'o'i a Ramadan akan Allah ya basu mazajen aure. Wallahi kusan sai da abin ya ban tsoro naga sakwanni masu bukata iri daya kamar hadin baki, lallai da yawa daga cikin mata suna cikin matsananci halin bukatar adduah akan Allah ya basu mazajen aure salihai. Muna addah tare da tawassuli da kyawawan ayyukan da muka gudanar a kwanakin Ramadan, Allah ka biyawa wadannan bayin Allah bukatunsu na alheri, Allah ya basu mazajen aure na gari masu tarbiyya.

kuma ina kira ga 'yan uwa Maza da suji tsoron Allah su yi aure, masu biyu ma su kara me uku ma ya kara. Allah ya bada yadda za'ayi. Akwai wasu 'yan uwanmu guda biyu da kullum muna tare da su a facebook suna da larura da ta shafi Ji suna matukar bukatar addu'ah, Allah ya inganta musu jinsu da ganinsu, Allah ya baiwa marasa lafiyarmu lafiya masu lafiya Allah ya kara mana lafiya. Mamatanmu Allah ya jikansu. Allah ya bamu lafiya da zama lafiya da abinda lafiya zata bukata.

YASIR RAMADAN GWALE
07-07-2014

Labarin Da Ya Tayar Min Da Hankali A Cikin Azumin Nan

LABARIN DA YA TAYAR MIN DA HANKALI A CIKIN AZUMIN NAN

Furera Bagel ta bayar da wannan labari akan Timeline dinta kamar haka: Tana cewa, ina cikin matukar damuwa da tashin hankalin abinda ya faru, inda har na dinga ganin abin a mafarki. Tace, wani lokaci na ziyarci gidan yayata dan sada zumunci, sai na sameta cikin wani irin yanayi marar dad'I kwarai da gaske. Da na tambayeta dalilin halin da ta ke ciki, ta bani labarin kamar haka:

Wannan abin ya faru da wata 'yar uwarmu ne, wannan matar tana cikin wani irin matsananci halin rayuwa, daga baya kuma wani mummunan al'amari ya kuma bijiro musu. Ita dai wannan matar sunyi aure da mijinta Shekaru 25 da suka gabata, wanda tun bayan aurenta da mijinta aka kama mata dakin haya guda daya tana cikinsa tsawon kusan shekaru 20; kwatsam bayan wani lokaci sai mijin matar ya kara yin wani sabon aure, anan ne mijin ya kara karbar wani dakin haya guda daya a gidan da yake zaune, inda kowaccensu take zaune a daki daya.

Amma wannan mutumin bai kama daki ko guda daya ba, domin 'ya 'yansa da suka tasa su zauna a ciki ba! Matar takan kwana da 'ya 'yanta budurwoyi a daki daya idan mijinta na dakin daya matar, amma yaranta maza sai su tafi makwabta su kwana tare da sauran 'yan uwansu maza. Can bayan wani lokaci, dan wannan mata mai kimanin shekaru 12 ya kamu da rashin lafiya, inda aka kaishi asibiti dan yi masa magani. Amma bayan wani lokaci rashin lafiyar wannan yaro ta sake tasowa, anan ne suka yanke shawarar daukar yaron dan kaishi a yi masa gwaje-gwaje dan gane cutar da take damunsa.

Bayan da aka dauki jinin yaron dan skekaru 12 aka auna ne, aka tabbatar musu da cewa yaron yana dauke da cutar HIV mai karyar garkuwar jiki. Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un! Uwar yaron ta shiga cikin damuwa da tashin hankalin yadda yaro kankani ya kamu da cutar kanjamau irin wannan!

Tun farko, matar bata taba samun nutsuwar danta yaje gidan makwabta ya kwana da wadan da suka grime shi a shekaru ba, amma kasancewar mijinta yaki kamawa yaransa dakin haya a gidan, babu wani abu da zata iya yi illa ta kyale yaron yaje makwabta ya kwana duk dare, amma daga wannan lokacin matar ta kudiri aniyar dole al'amura su sauya daga yadda suke faruwa. Nan ne fa matar ta kuduri aniyar samarwa kanta da 'ya 'yanta mafita, ta fara yin sana'ar toye-toye a bakin titi duk safiya, ta sanyawa ranta burin mallakar gida dan tsugunar da 'ya 'yanta.

Allah buwayi gagara misali, ya baiwa wannan mata ikon mallakar fili, cikin hukuntawarsa Subhanahu Wata'Ala, ta gina gida mai daki biyu da falo da kicin da ban-daki da tsakar gida. Amma a lokacin da ta mallaki wannan gidan tuni 'ya 'yanta mata guda biyu sunyi aure, kun san abinda mijinta yayi kuwa? Kawai sai ya saki waccan matar da ya kara aurowa daga baya, sannan yabi matarsa sabon gidan da ta gina ya tare tare da ita.

Dan wannan matar da yake yaro ne mai shekaru 12, yana nan yana cigaba da karbar shawarwari da magunguna akan cutar da yake dauke da ita mai karya gaekiuwar jiki, adaidai wannan lokaci ne kuma, ciwon yaron ya sake tsananta, dukkan karfin jikinsa ya kare, garkuwar jikinsa tayi matukar rauni. A lokacin da yayar Furare Bagel ta ziyarci mahaifiyar yaron ne ya yi musu bayanin yadda aka yi ya kamu da cutar HIV! Yaron yace, "lokacin da nake zuwa gidan makwabta na kwana ina karami sosai, idan ina kwance sai wani mutum ya zo ya tilasta min kwanciya tare da shi dan biyan bukatar sha'awarsa tare dani, yakan yi min ta karfi ba dan ina so ba, mutumin ya ciga da zuwa wajena duk dare yana tursasamin kwanciya da shi lokaci mai tsawo da ya wuce. Mutumin da yake yi min wannan abu kuwa shi ne makwabcinmu da nake kwana a gidansa, yaron yace mutumin kamar mahaifi yake a wajensa"! Wannan shi ne labarin da yaron ya basu, inda ya nuna cewar wannan mutumin da yake zuwa wajensa da daddare yana kwana da shi ne ya sanya masa wannan cuta ta HIV.

Hakika wannan labari ya tayar min da hankali a cikin wannan azumi matuka. Furare Bagel a cikin jawabinta ta ce, shin me yasa ba zamu taimakawa wannan mata ba wajen kama wannan makwabcin nasu dan gurfanar da shi a kotu a tuhumeshi da laifin yin lalata da kananan yara ba? Ina lauyoyi daga cikinmu masu san taimakon masu karamin karfi? Lallai ya kamata mu taimakawa wannan mata da aka riga aka kashe mata yaro.

YASIR RAMADAN GWALE
07-07-2014

Wednesday, July 2, 2014

Mallam Ibrahim Haruna Ismail Shekarau (Sardaunan Kano)

MALAM IBRAHIM HARUNA ISMAIL SHEKARAU (Sardaunan Kano)

Ina mai amfani da wannan damar wajen mika sakon taya murna da fatan alheri ga Mai Girma Sardaunan Kano Malam (Dr.) Ibrahim Shekarau bisa damar da ya samu bayan tantance shi da majalisar kasa ta yi a yau don zama daya daga cikin 'yan Majalisar Zaratarwa na tarayyar Najeriya. Muna fatan Allah ya yi masa jagoranci a wannan sabon aiki da ya samu Allah ya amfanar da al'ummar Najeriya da irin baiwar da Allah ya huwace masa. Muna rokon Allah da sunayansa tsarkaka ya bashi ikon sauke nauyin aikin da yake kansa. Allah ya azurtamu da shugabanni na gari Adalai.

Yasir Ramadan Gwale
02-07-2014

Tuesday, July 1, 2014

Abinda Ya Faru Da Ni A 2010

ABINDA YA FARU DA NI A 2010

Ranar wata juma'a na yi wanka na tafi masallacin Al-Furqan misalin karfe goma na safe, bayan da na isa masallaci na yi alwala zan shiga Masallaci ina goge ruwa a fuskata, sai ga waya ta na ruri, ko da na duba sai naga wani abokina ne ya kirani, na d'aga muka gaisa, yace Yasir kana ina? Na ce masa ina masallaci yanzu haka, sai yace, to Dan Allah kayi maza-maza ka hau mota ka zo Abuja yanzu-yanzu. Sai naji garam! Yace karka damu ka hau mota yanzu dan ka iso da wuri.

Banyi wata-wata ba na koma gida na shirya jakata na dauki katin ATM na yi Sallama da gida na tafi. Na kama hanya sai Dangi randabawul nan na samu mota na hau, muka dan bata lokaci kafin mu tashi, zoooo muka kama hanya, mun sami Sallah Juma'a a hanya ina zatan kusa da Zariya. Bayan nan muka kama hanya muna tafiya zummm muna tafiya, mun isa Abuja bayan Sallar Isha, na bugawa Abokina waya nace masa gani na zo Abuja.

Daga nan yace naje Area 11 wajen masallacin Juma'a na jirashi, na dauki mota kuwa sai Ministers gate. Ina tsaye sai ga shi an tukoshi a 406 mai launin koriya, yace na hau, na bude kofa na shiga, daga nan Muka shiga cikin unguwar Maitama wajen Masallacin Juma'a na Maitama. Muka je gidan wani Alhaji dan kano ne mutumin kirki kwarai da gaske, muna shiga muka sameshi yana kallon NTA a wani katafaren falo, yana kishingide a jikin wani tuntu na fata, ya nuna mana kan tebur, abokina yace Yasir bisimillah kaci abinci, na duba teburinnan cike yake makil da kayan dadi, ga kaji ga kifi ga apple ga soyayyar doya ga abubuwa kala-kala har da alale irin mai kwai a cikinnan.

Bayan da naci na gyatse, na sha ruwa da lemuka iri-iri har da Shuwefs. Sai naga duk mutanan dake falon a zaune suke a kan kafet nima na zauna a kasa, maigidan sanye da farar jallabiya da bakar hula ya mikomin hannu muka gaisa, daga nan ya nuna min wani fulas dogo yace ga kofi can dauko, da na dauko na zuba sai naga kunun tsamiya ne mai rai da lafiya, na tsiyaya na kukkurba. Haka dai na cika cikina taf har da kyar nake nishi, abinku da wanda yaga banza! Lol

Muna zaune sai abokin nawa sukai waya yace gashi nan zuwa. Muka hau mota muka tafi wani gida anan dai unguwar maitama ne, muna isa naga gidan dan'karere mai gadi ya fito ya bude mana kofa, muka shiga sai na duba ashe akwai jar miya a jikin farar shadda ta, muka tarar da wasu mutum hudu, daya daga cikinsu dan kano ne wani dan siyasa ne, na shanshi shima ya sanni, yana zaune akan kujera yana daddanna waya muka gaisa da shi sunansa Musa Gwadabe, gefe kuma wasu manyan mutane ne su biyu suke hira, daga jikin bango kuma ga wani mutum ba tsoho bane sosai sanye da fararan kaya da hularsa a karkace irin yadda muke ganin hotunan Alh. Isah Kaita ke karkata hula mutumin yana karatun al-qur'ani.

Muka samu waje muka zauna, da mutumin ya gama karatun Qurani sai naga mutum biyun nan dake gefe sun juyo wajensa sai na fahimci shi ne mai gidan. Bayan da suka gaisa ya kira wani daga cikin masu gadi nan da nan aka kawo wani katon daron abinci, akwai tuwon semo da teba a ciki sannan ga miyar bushashshiyar kubewa da kaji zukul-zukul a ciki ga kuma wata irin miyar ganye ina jin ko Edikong Ekong ce, nace ni kam na koshi amma dai zan danci kazar, suka bushe da dariya. Nace ai mu a Kano bama yin miyar yauki da Kaza.
Bayan da aka gama cin abinci sai ruwa ya sakko shaaa, muna zaune, sai abokina ya matsa kusa da mutumi yace masa Ranka Ya dade wannan shi ne Yasir Ramadan Gwale, mutumin ya miko min hannu muka gaisa na sanya hannu biyu muka gaisa.

Da muka gama gaisawa sai yace kasanni? Nace Ranka ya dade ban sanka ba, amma tunda na zo nan dole zan sanka. Yace sunana Sani Zangon Daura, sai Musa Gwadabe yace bakasan Danmasanin Daura ba? Nayi masa mujamala nace kwarai kuwa, daga nan mukai Sallama abinda zai gudana ya gudana aka kaini masauki . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . .!

ABINDA YA FARU DA NI RANAR ASABAR A FACEBOOK [2]

Sai kuma mu dawo labarin abinda ya wakana tsakanina da Hala Ebrahem. Ina zaune ina ta tararrabin yadda zan fita daga dakinnan sai naga an had'a projector an kunna, aka kuma kunna wasu fitulu ba masu haske sosai ba, can sai ga wani mutum ya zo da kyamara ya yana daukar hotuna, sai naji tsoron kar yazo kaina ya dauki hotona ban san ina hoton za shi ba, da naga ya kusa zuwa kaina sai nayi dabara na kara wayata a kunnena na sunkuyar da kai kamar ina waya, har sai da na fahimci ya wuce sannan na d'ago.

Baifi minti goma ba, sai naga wani mutum yazo ya dauki abin Magana ya gaishemu ya yi mana barka da zuwa sannan yace RAMADAN KAREEM daga nan na dan samu nutsuwa nace watakila ba mugwaye bane. Ya ajiye abin Magana ya tafi, can sai ga wata budurwa sanye da bakaken kaya da jan kallabi itama ta dauki abin Magana ta danyi surutanta, amma ni hankalina duk ba kanta yake ba, ina ta sakar yadda zan gudu.

Ilai kuwa sai naga wata ta tashi tayi bakin kofa inda gabza-gabzan mutanan suke, ta yi musu Magana suka bata hanya. Nima na tashi a tsure na nufi kofa, sai nace musu zanje waje na dawo, suka bude kofa kuwa, nan naji wata iska ta shigeni me sanyi. Na sauko daga kan bene, na tarar da ragowar shidannan na bakin kofa suma nace zanje na dawo suka bani hanya na wuce.

Da yake lokacin da na fito magriba tayi sai naje wani masallaci dake kusa da wajen nayi Sallah, na ja gefe na tsaya ina tunanin irin yadda nayi kasada haka kurum ban san mutumba ya kirani kuma na zo, nan dai na hakkake cewa koma dai me ya faru kaddara ce da babu wanda zai iya tsallake mata. Ina zaune ina tunanin abinda ya faru, sai ga Hala ta kirani tace ina nake, nace mata na zo wani Masallaci zanyi Sallah, tace idan nayi Sallah na kirata, na zauna na huta, da na koma kusa da wajen sai naga mutane suna fitowa, sai na kira Hala tace min naje wajen da ake shiga kofa zan ganta da Koren Gyale da Bakar riga.

Sai na koma can baya dan in hangota naga wacece, inda tace na duba banga alamar da ta nunamin ba. Sai na kuma dauko waya zan kira, ina kira sai batirina ya mutu, nan na sake kunna wayar na dauki lambarta ko zan samu wani ya kirata, ina tsaye sai naga wannan da nace muku Naga yayi kama da Kiriminal yazo wajena yace na biyoshi, na bishi banyi fargaba ba, sai ya hadani da wata siririyar yarinya, ta miko min hannu mu gaisa, sai na saka hannuna a al-jihu na gyada mata kai, ta dauki wayarta naji ta kira Hala tace mata gani ga Yasir, sai ta nunamin wasu mutane a tsaye bakin wasu fulawoyi tace naje wajensu, daga wajen ina hango bakin titi nasan ko ihu na yi zan samu agaji.

Ina zuwa sai naga samari ne guda uku da wani mutum ya dan manyanta, da kuma wata mata sai wasu 'yan mata su biyu sun kewaye wata a tsakiya, kuma budurwar nance mai bakaken kaya da jan dankwali take yi musu jawabi. Ina tsaye ina duban hanya ko da zanga dugu-dugu zan iya arcewa, ahaka matarnan ta dinga Magana da su daya bayan daya suna tafiya har sai da kowa ya waste daga ni sai ita sai kuma siririyar yarinyar da ta rakoni.

Matar tace min ina da tambaya? Nace babu, tace me ya sa, nace haka kurum, tace to ni zan iya tambayarka? Nace mata a'a, sai tayi dariya tace ai ba tambayar jarabawa zan yi maka ba, nace eh duk da haka ba sai kin tambayeni ba, tace to ita tana da tambaya, sai nace to da sharadin idan zaki yi tambayar da turanci. Tace ba komai, daga nan ta fara yimin wasu surutai wai suna da kamfani da zan iya saka kudi naci riba cikin kankanin lokaci, tace idan na saka Dala dubu biyu a cikin kwana 8 zanci ribar Dala Dubu Goma, tace min akwai wanda yaci ribar Dala Dubu Talatin a cikin sati uku, nan dai na fahimci ashe abin Damfara ce.

Da ta gama jawabi sai nace bani business card dinki sai ta fara inda-inda, nace a ina kamfanin naku yake, sai tace zan karbi lambarka duk lokacin da ka shirya sanya kudinka kayi min Magana, ni kuma zan zo na sameka! A raina nace yanzu ke kinga nayi kama da wanda za'aiwa irin wannan zancen banzan, ai san banza na baikai haka ba.

Haka dai muka rabu ina ta ta'ajibin abinda ya faru. Amma kuma har na baro wajen banga Hala Ebrahem ba. Kunji karhsen abinda ya faru. Babu bukatar na rantse dan wasu su yarda da ni Amma Wallahi yadda na gaya muku haka abin ya faru. 'Yan damfarar da suke aiko mana da sakwanni ta Inbox na hadu da su ido da ido. Amma abinda na fahimta masu aiko da sakwannin nan mutane watakila da suka sanka.

YASIR RAMADAN GWALE
01-07-2014

Abinda Ya Faru Da Ni Ranar Asabar A Facebook

ABINDA YA FARU DA NI RANAR ASABAR A FACEBOOK

Kamar mako guda da ya wuce na ina goge irin sakwannin da ake turomin a Inbox na babu gaira babu dalili da wasu mata ke turowa, wanda sun addabi mutane da yawa da irin wadannan sakwanni nasu. Ina cikin haka sai ga wata Hala Eberahem ta aiko min da sako, nan da nan na aika mata da martini nace da ita "Very Stupid" na goge sakonta, bayan wasu 'yan dakikoki sai ta sake aiko sako tana cewa "thank you" can sai ta kuma aikowa tace "sorry", a raina nace daman ana iya samun wadannan shedanun a yi Magana dasu.

Bayan wani lokaci a ranar ta sake aiko min da sakon ban-hakuri. Sai na yi mata Magana, ta gaishe ni, na sake yi mata Magana, da alama bata iya turanci sosai ba, sai naga ta fara yin Magana da larabci, haka muka yi Magana muka rabu. Bayan kwana biyu sai ta sake aiko min da sako a dai-dai lokacin da na sake bude shafin Inbox dina, ina ganin tace "Hi" ban-yi wata wata ba nace "very stupid" saboda ina zaton irin su ne suka aiko da sako, sai bayan da sakon ya tafi sai naga alamar munyi "conversation" ban lura da sunanta ba, abinda na fara cewa a raina, shi ne, yau dai na yi kwakyariya.

Bata damu ba sai ta aiko min da skon cewa tana da wata muhimmiyar Magana da ni, amma ga lambar wayarta na kirata. Sai na yi mamaki, na yi kasadar kiran wayar da layina, sai naji mace ta dauka, bayan munyi Magana mun gaisa sai tace, dan Allah akwai wani "event" muhimmi lallai tana son na halarta, a raina nace to wannan ta sanni ne daman kuma tasan inda nake har take gayyata ta. Ta yi min kwatancen wajen, sai naga nasan kusa da inda ta kwatanta min, amma kuma bangane ainihin inda za ai event din ba, bayan da muka gama waya sai na share.
 
Ranar Asabar tace min za'ai abin da karfe hudu na yamma. A lokacin da muka yi Magana, ta gayamin cewa idan naje wajen za'a tambayi sunana na gaya musu, sannan kuma za'a tambayi a dalilin wa na zo na fadi sunanta. Ranar Asabar ina zaune a daki tare da abokaina mu uku, sai ga wayarta da karfe hudu daidai, bayan na daga sai nace mata ai na manta yauce ranar, amma gani nan zuwa nan da minti 45, na baiwa abokaina labarin abinda ya gudana tsakani na da ita, suka ce "Lallai Yasir a gaisheka da kokari, haka kurum zaka dauki kafa kaje wajen da baka san dalilin kiranka ba . . ." Nace musu kudai idan kunji ni shiru to ga kwatancen da ta yi min kubi bahasina.

Nayi wanka na dauko wani tsohon Jeans da na jima ban sashi ba, na dauko wata riga mai dogon hannu na saka, na kawo hulata (tashi-kafiya-nace) na saka na kawo gilashina nasa saka, abokina ya kalleni yace, yau wacce rana Yasir ya sanya kananan kaya. Nace kudai ku yi adduah Allah ya sa alheri ne. Na hau mota tiryen-tiryen sai kusa da inda akaimin kwatance, da naje daidai wajen sai na samu wani mutum a zaune yana karanta jarida na tambayeshi ko nan ne waje kaza, sai yace eh, nace to kasan inda ake wani dan al'amari? Yace bai sani ba, muna haka sai ga Hala ta kirani, sai nace ga wani masanin wajen yi masa kwatance.

Bayan da na bashi waya suka yi Magana sai ta yi masa kwatance, yace ya gane, yace min ka hango wani dogon gini gashi can daga gabas, to hannun hagu da shi akwai wata karamar hanya, ka shiga nan ne wajen. Na kama hanya, ina 'yan kula-uzai . . . na isa daidai wajen kuwa, sai na d'an lab'e ina hango me ke faruwa a wajen, sai na hangi wasu mutane gabza-gabza su shida sanye da bakaken kaya sun tsuke sun sanya jan lakatayen, na dubesu nace ai kuwa duk cikinsu babu wanda ba zai iya makureni ba, har zan koma, sai nayi karfin hali.

Na dauki waya na bugawa Hala nace gani a wajen, tace na shiga wajen zasu tambayi sunana, za kuma su tambayeni a dalilin wa na zo na fadi sunanta. Na yi Shahada ina zuwa sai naga gabza-gabzan nan sun jeru a bakin kofa, bance musu komai ba na tsaya, sai wani ya yi min ishara zuwa ga wani mutum da yake zaune da takardu a gabanshi, ina zuwa wajensa yayi min fara'ah da alama mutumin ba yaro bane, ya tambayi sunana na gaya masa ya duba takarda sai gashi, yace a dalilin wa na zo, na fada masa ya duba sai ga sunanta, to a lokacin da nake tsaye ashe akwai wasu mutum biyu mce da namiji da suka zo bayana suka tsaya.

Kawai sai gani na yi ya musu ishara su tafi da ni, macen ta shiga gabana namijin ya tsaya a bayana suka ce muje, na bisu zugui-zugui muka hau wani bene, muna hawa amma ina hango mutanan waje ta cikin gilashi, suka kaini cikin wani daki, ina shiga sai naga an kunna fitulu marasa haske, ga kujeru anjera a dakin ga kuma wasu mutum 6 a bakin kofa ta cikin dakin ba ta waje bag a kuma wasu mutane zasu kai goma a zaune a wajen, suka nunamin wata kujera na zauna ina 'yan addu'o'in da suka zo min, can sai naji an saki disko mai karar gaske, nace To fah! Na dauko wayata na kira abokina, nace nifa gani an kawo wajen shedanci, abokina yace Allah ya kiyaye, nace Amin.

Ina zaune sai naga an kashe fitila, dakin yayi duhu amma kana ganin mutane wanda ka sani zaka iya shaida shi, ina 'yan addu'o'ina, sai na dauko wayata na kira wannan Hala din, sai tace min kar na damu kawai na zauna zamu hadu zuwa jimawa, ina zaune ina kallon mutanan da ke wajen, can sai naga an shigo da wani sai aka ce ya zauna kusa da ni, ai da na kalli gayen sai naga gaskiya wannan ya yi kama da Kiriminal, nan dai na fara tsoro amma dai na dake.

Ina zaune ina tunanin yadda zan gudu amma ina duba kofa naga kartinnan 6 suna tsaye jingine bakin kofa, sai nayi tsoron kar naje suce ba zan fita ba, ga dakin da duhu sai kawai hasken waya kake hangowa, can sai naga wani ya zo da projector zai hada. Naga gashi ana shigo da mata da maza wajen. . . . . . . . . . Zan katse labarin anan na baku labarin abinda ya faru shigen irin wannan a 2010, daga nan kuma sai na jona kuji yadda muka karke da su Hala Ebrahem. Sai mun hadu gobe idan Allah ya kaimu. Mu sha Ruwa lafiya.

YASIR RAMADAN GWALE
30-06-2014