Saturday, February 25, 2012

Su Wa Ke Da Alhakin Lalacewar Ilimi A Yankin Arewa?

Ilimi garkuwar dan Adam, kamar yadda wani mawaki yake cewa “can hakika bada tangarda ba, an lura mai ilimi shike morewa kwalkoliyar daraja shi hau shi dare dam, shi ko marar ilimifa ko hangawa, kalbi marar ilimi abin rainawa, himma da kwazo garkuwar mashiyinku . . . hakika kamar yadda wannan mawaki ya gwarzanta ilimi ya cancanci wannan yabo, haka kuma ya nuna cewa mai llimi kamar wani kare ne abin a wulakanta domin dai kowa yasan kare wata dabbace da bata da wata kima tsakanin mutanan kwarai, haka kuma mai ilimi shi ne fitilar al’umma shi yake bayyanar da haske daga duhun jahilci.

Ilimi shi ne yake maida karami ya zama babba mai kima da daraja, haka kuma rashinsa yakan sanya kaskanci da wulakanci, ka kwatanta dukkan wata irin kasaita da karramawa da kasani da ilimi, ka kuma kamanta dukkan kaskanci da wulakanci da koma baya ga rashin ilimi. Hakika tazarar ilimi da jahilci tazara ce mai yawan gaske da kana iya kamanta ta da sama da kasa, domin ko da wasa biyun bazsu taba haduwaba. Na tuwa ranar da aka sanyani makarantar firamare, ina dokin shiga makaranta, bayan da muka shiga ofishin hedimasta, ya daga kansa ya nunamin wata kalanda da hoton wani gida na bukka yace dani yaro kaga wannan gidan, na daga kaina na kalleshi yace ilimi na iya bunkasashi ya kasaita, haka kuma duk girman gida ilimi na rusashi; hakika wannan magana tayi tasiri a iya tsawon rayuwata kuma sau da yawa nakan tuna wannan magana. Don kuwa wata rana muna hira da marigayi Arc. Musa Tanko Waziri yake shaidamin cewa shi ya taso mahaifinsa talaka ne, amma yanzu gashi ya mallaki gida da mota kuma ba gadone na mahaifinsa ba, yace to haka ilimi ke daukaka mutum daga rayuwa ta kaskanci zuwa rayuwa ta daukaka.

Idan kuma muka dawo batun ilimi a yankin Arewa abin a zubar da hawaye ne a ciza yatsa. Domin bincike da alkaluman kididdiga na kara nuna cewa kullum harkar ilimi tana kara samun koma baya a wannan yankin da akajima ana daukin ganin ya dore. Hakika yankin Arewa shi ne yankin da yafi kowane yanki yawan mutane a Najeriya, bayaga haka kuma ga fadin kasar noma da albarkar kasa, amma sai dai wannan yanki namu cike yake da tarin jahilai da marasa aikinyi, halin da wannan yanki yake ciki hakika wani irin mawuyacin hali ko yanayi ne da ya shallake hankali da tunani ganin cewar magabatanmu da sukayi kokarin yimana tsuwurwurin samun ingatacciyar rayuwa da samun nagartacce kuma ingataccen ilimi sun kafa harsashi mai kyau. Saninmu ne cewar da yawan magabatanmu na yanzu sunyi karatu kyauta a lokacin da kasafin kudin wannan kasa bai kai kaso daya cikin dari na kasafin kudi na yanzu ba, sunyi karatu kyauta aka basu aiki da motocin hawa da gidajen kwana su da iyalansu da kuma albashi mai inganci, amma har kawo yanzu sun kasa biyan wannan kasa bashin da ta basu na moriyar ilimi da suke ci a yanzu.

A shekarar da ta gabata ta 2011 hukumar kula da kidayar jama’a ta kasa National Population Commission karkashin jagorancin shugabanta Cif Samoila Danko Makama ta fitar da wata kididdiga da take nuna cewa a Najeriya yankin Arewa maso gabas shi ne yankin da yafi kowane yanki yawan mutane jahilai, inda yankin Arewa maso Yamma yake binsa a baya da kuma yankin Arewa ta tsakiya; sannan wannan kididdiga ta nuna cewa yankin kudu maso yamma shi ne yanki da yafi kowane yanki karancin mutanan da basu yaki jahilci ba, haka kuma wannan kididdiga ta nuna cewa jihar Ekiti kusan itace jihar da tafi kowace jiha adadi mafi karanci na wadanda basu je makarantar boko ba; a yayinda jihohin Jigawa da Zamfara da Yobe da Gombe da kuma Kebbi sukafi adadi mafi yawa na wadan da basu halarci makarantun Firamare da sakandare ba.

Haka kuma, wannan kididdiga ta nuna cewa mafiya yawan mutane a Jihar Legas suna kashe kusan kashi 63 na kudadensu wajen yin hidima ga karatun ‘ya ‘yansu, inda sukace mafi karancin kudin da iyaye kan kashewa ‘ya ‘yansu yakan kama daga 20,000 zuwa abin da ya yi sama a duk zangon karatu; sannan kuma ya nuna cewa a yankin Arewa mafiya yawan mutane masu dan abin hannu sukan kashe kusan kashi 17 na kudinsu domin karatun ‘ya ‘yansu abin da ya kama daga 5,000 zuwa abin da ya yi sama kadan akan karatun ‘ya ‘yansu, kuma yankin da yafi kula da harkar kartun yara kanana a Arewa shi ne yankin Arewa ta tsakiya. Muna tsaka da wannan komabaya ne kuma kwatsam sai ga wasu da suke da’awar shi kansa karatun Bokon Haramunne!

Hakika wannan rahoto abin duba ne kwarai da gaske. Ya rage na mutanan Arewa su gasgata wannan rahoto ko su karyatashi amma dai ko babu komai gaskiyar al’amura tana kara bayyana, domin a yayinda dalibai 2,300 suka samu damar rubuta jarabawar JAMB a shekaru biyu da suka gabata a Jihar Jigawa takwarorinsu na jihar Imo kusan 90,000 suka sami nasarar cin wannan jarabawar. Haka nan kuma a shekarar da ta gabata kamar yadda sabon gwamnan jihar Zamfara ya fada a wata hira da ya yi da jaridar Daliy Trust ya ce yara 60 ne kacal suka sami nasarar cin darasi biyar na shiga jami’a wato 5credit a jarabawarsu ta WAEC da NECO acikin kusan yara 30,000; sanna kuma a dai wannan shekara da ta gabata a cikin yara 18,000 da suka zauna wannan jarabawar ta NECO guda 18 ne kawai suka iya samun darasi guda biyar a jihar Gombe kaga kenan ana da kwantan yara 17,982 a wannan jihar da bazasu sami damar shiga jami’a ba. Sannan kuma idan zamu iya tunawa a shekarar 2003 matasa 45,000 suka samu nasarar kammala jami’a a jihar Imo a daidai lokacin da matasa 5,000 ne kacal suka sami nasarar kammala jami’a a jihar Kano, jihar da akace tafi kowace jiha yawan jama’a a Najeriya da kusan mutane sama da miliyan 10 a kididdiga ta baya-bayannan.

Shakka babu wannan alkaluma suna kara tabbatar da cewar yankin Arewa shi ne yafi kowane yanki adadi na wadanda basu yaki jahilci ba a Najeriya. Hakika wannan ba karamin kalubale bane ga daukacin gwamnatocin Arewa da sarakunan Arewa da manya masu fada aji a wannan yanki, domin wannan ba karamin abin tashin hankali bane ace irin wadan nan alkaluma ba wai raguwa suke ba kullum karuwa suke, nasan Allah ne kadai yasan adadin daliban da ake bari kwantai a kowace shekara a Arewa da basu sami damar shiga jami’a ko makarantar gaba da sakan dare ba. Nasan a jihar Kano akwai wata makaranta da gabaki daya dalibanta kaf babu dalibi ko daya wanda ya iya samun nasarar cin darasi biyar na 5credit. Duk wannan na faruwa ne a lokacin da gwamnatocin Arewar suke ikirarin kashe makudan kudade a harkar ilimi.

Duk da irin wannan komabaya da ake samu a harkar ilimi a Arewa, kuma ga wata matsala ta karancin dakunan daukar darussa da kuma cunkoso a wadanda ake da su, ka kai ziyara duk wata makaranta ta firamare ko ta sakandare da ke kusa da kai kaga yadda ake cunkusa yara sama da dari a aji daya. Sanna kuma ga matsalar karancin malamai domin zakaga malamin lissafi guda daya shi ne yake koyar da ‘yan aji 1 da aji 2 da 3 na babba ko karamar sakandare, sannan kuma ga rashin kwarewa da ta dabaibaye malaman musamman na firamare da karamar sakandare, domin a wani bincike da na gudanar na kai ziyara wata makaranta inda na sami wani malami dalibai sun kewayeshi yana ta yi musu feleke inda na bukaci yin magana da shi da turanci abin mamaki sai yayi tsuru-tsuru yana kame-kame ya nemi da mu koma gefe na fuskanci kwata-kwata baima san abinda yake ba, kuma wai a haka ake koyar da karatu, ka rasa wai me ake koya musu ne! Sannan kuma mun sani cewa yara manyan gobe wadanda sune ake fatan zasu rike kasarnan idan hali ya yi amma anbata musu lokaci da rayuwa, kaga yaro ya kammala sakandare bazai iya baka cikakkiyar jumla da turanci ba a haka ake son yaje yayi ko ‘yar difiloma ko wani karatun yazo a bashi koyarwa a firamare! kuma wadan nan yara acikinsu ne akesa ran Arewa ta fitar da likitoci da injiniyoyi da manyan malamai a fannoni daban daban da suka shafi al’umma.

Bayan haka kuma, jami’o’in da muke da su a Arewa bazasu iya daukar kaso 25 na daliban da suke kammala sakandare ba a kowacce shekara, a bara kawai a dalibai 45,000 ne suka nemi guraban karo karatu a jami’ar Bayero da ke kano amma dalibai 3,000 ko sama da haka ne jami’ar zata iya dauka, haka idan kaje jami’a Ahmadu Bello dake zariya da Usmanu Danfodiyo dake Sokoto da Maiduguri abin yake. Idan kuma ka dauki jihar Ogun a yankin kudu maso yamma tana da adadin jami’o’i da zasu iya bayarda takardar shaidar kammala digin farko kusan guda 8 daman kar ka tambayi jihar Legas da ta ke da jami’o’i barkatai da suke bayar da wannan shaida. Mu kalli yadda gwamnan jihar Rivers mista Rotimi Amechie inda ya dauki nauyin dalibai ‘yan asalin jiharsa kusan 45,000 zuwa karo karatu a fannoni daban-daban a kasashen turai da Amerika abinda ko gwamnatin tarayya bata taba yin irin wannan muhimmin kokari ba inda ya ware kudi wajen Naira Biliyan 14 domin wannan aiki.

Sannan kuma, idan muka kalli wadannan alkaluma babu wani shiri da gwamnatocinmu suke da shi mai karfi na koyar da matasanmu sana’o’in hannu domin su dogara da kansu, da kuma fuskantar rayuwarsu ta nan gaba, kullum ana kara samun ‘yan zaman banza da kashe wando da ‘yan maula da tumasanci da ‘yan jagaliya, ka kalli kowane irin babban titi ko mahada a yankin Arewa kaga tarin mabarata masu karfi da jini a jika wadanda zasu iyayin sana’o’i amma anaji ana kallo sun zama mabarata kuma ana kara kashe musu guiwa mai makon karfafasu, a gefe guda kuma gashi kullum rayuwa tana karayin tsada kudi suna karayin karanci a hannun mutane, wallahi idan ba hankali mukayi ba wataran kanaji kana kallo al’majirai zasuyi yi maka taron dangi su turmusheka su wafci kudi daga gareka, mu kalli irin yadda kana tsayawa akan danja/titi zakaga al’majirai sun baibaye maka mota kamar saci babu, shin yanzu bazamu kalli wannan a matsayin wani kalubale ko barazana ba?

Sau da yawa sai kaji mutanen Arewa suna cewa sana’o’in hannunma sunyi karanci a yankin Arewa. Wanda kuma idan kabi wannan magana sai kaga ba gaskiya bace, domin mu kalli irin dimbin inyamurai da yarabawa ‘yan kudu da suke yankin Arewa shin zaman banza sukeyi? Mu kalli irin yadda ‘yan Nijar da Kamaru da cadi suke tudadowa yankunanmu musamman idan aka ce maka rani ya yi shin zaman banza suke yi? Wani zai iya cewa ai suma ‘yan Arewa suna zuwa yankin kudu, sai mu tambaya shin idan ‘yan Arewa sunje kudu me sukeyi? Da yawan ‘yan Arewa dake kudu sunayin kaskantattun sana’o’ine misali shushana(me wankin takalimi) da makamantansu, kuma wani abinda zai baka mamaki da haushi shi ne sai kaga mutumin Arewa yana sana’ar sayar da zaren zura carbi a kudu ko kuma sayar da allura da zare, shin ka taba ganin inyamuri ko beyerabe yana sana’ar sayar da goro da taba a Arewa?

Ga rashin ilimi ga jahilci ga matsanancin talauci shin me ka ke jin zai faru? Mukallai yadda rikicin bayan zabe ya auku a yankin Arewa, domin wannan ba rikicin kabilanci bane ko na addini da Najeriya tayi kaurin suna akansa ba, duk wadan da sukayi wannan kone-kone da fashe-fashe ‘yan Arewa ne kuma dukiyar ‘yan Arewa suka kone! Shin wannan ba zai zama izina ga shugabanninmu ba? Bahaushe yace a lokacin da ka kure mage taje bango to ka sanifa kanka zata juyo, Lallai da tarin jahilai marasa aikinyi gara tarin masu ilimi marasa aikinyi domin shakka babu mai ilimi ba zai shiga hanayi da hargitsi irin wannan da zai kai ga hasarar dukiya ba, kuma alal a kalla mai ilimi yana da wani tunani na daban da ya sha bamban da jahili duk da shima yana da nasa tarin matsalolin na kaucewa dukkan wasu sana’o’in hannu.

Sannan kuma shi talaka bayan irin wannan mugun koma baya da yake aciki, babu wani yunkuri da yake yi na kwatar kansa daga wannan hali da ya yi kama da kangin bauta ko mulkin mallakar bakaken fata ‘yan uwansa, iyaye basayin wata hobbasa domin ganin ‘ya ‘yansu sun sami kyautatuwar rayuwa anan gaba, ankyale yaro shi ne malamin kansa shi ne zaiyiwa kansa tunani kuma ya yankewa kansa hukunci! Kaga iyaye na gadarwa da ‘ya ‘yansu talauci da gangan, bayan wanda hukuma ta jefasu ciki.

Ya kamata hukumominmu su tsaya su duba wannan koma baya da wannan yanki namu yake ciki da kuma nemo hanyoyin da za’abi wajen warware wadan nan matsaloli. Kuma yana daga cikin al’adarmu a wannan kasa shi ne duk wata matsala da take damun al’umma sai kaji hukumomi sunce a kafa kwamitin bincike bayan ga abu nan a zahiri babu bukatar kafa wani kwamiti, kaji anwarewa kwamiti dimbin kudi kuma a karshe ba’a aiki da rahoton kwamitin, yanzu kwamitoci nawa ne aka kafa tundaga 1999 zuwa yanzu wane kwamiti aka taba yin aiki da rahoton da ya kawo? Shin nawane aka kashe wajen aikin kwamitoci daga wannan lokaci zuwa yanzu zaka samu dimbin kudadene suka tafi a iska ba tare da biyan bukata ta ko sisi ba.

Hakika duk wanda ya bibiyi wadan nan alkaluma, sai ya yi tambayar shin su wane suke da alhakin duk wadan nan abubuwa da suka dabai-baye wannan yanki mai tarin albarkar kasar noma, musamman ta fuskar ilimi, ina gani wannan ba laifi bane da za’a dorawa hukuma ita kadai ba kusan bangarori hudu sunyi tarayya a ciki. Na farko su ne yaran domin da yawan yaranmu yanzu basason karatu domin suna kallon kawai wahalar da su ake yi, yara sun gwammace su bata lokaci mai yawa wajen kallon kwallo da tattaunawa a kan dakali da guraran hira marar amfani, da kuma bata lokaci mai tsada wajen tattaunawa ko musayar ra’ayi a zaurukan sada zumunta a 2go da sauransu.

Sannan bangare na biyu, su ne iyaye, hakika iyaye suna da gudunmawa mai yawan gaske da zasu baiwa ‘ya ‘yansu wajen samun ingatacciyar rayuwa. Da yawan iyaye a Arewa basu damu da abin da ya shafi karatun ‘ya ‘yansu ba, mu kalli abokan zamanmu Yarabawa zakaga beyerabiya tana gasa masara ko tallar gugguru da gyada kawai domin ta sami kudin da zata biyawa ‘ya ‘yanta kudin makaranta. Iyaye maza sun gwammace su canza sabuwar talabijin ko sabon babur da su biyawa ‘ya ‘yansu kudin makaranta, ita kuma uwa ta gwammace tayi zubin adashi ta dinka atamfar ankon bikin kawarta da ta taimakawa danta ko ‘yarta da kudin sayan litattafan karatu.

Bangare na uku kuma, sune al’umma, hakika al’umma suna da gudunmawa mai yawan gaske wajen ganin yaransu sunsami ingataccen ilimi, ta hanyar daukan nauyin yara marasa galihu da kuma shiryawa yara darussa na musamman da kuma fadakar da yaran illalar da ke tattare da jahilci da rashin aikin yi. Abin mamaki sai kaga kowa bai damu ba, yaransa kawai ya sani, akwai wani yaro da ya rasa dukkan iyayansa ya kasance babu wanda yake kula da rayuwarsa kasancewar a gidan haya ya taso sai wata tsohuwa take bashi abincin dare, wannan yaro maganar wannan mata kawai yakeji duk abinda tace ya bari ya bari, kaga da haka al’umma suke taimakawa rayuwar irin wadan nan yara da ansamu kyautatuwar lamura da samun ingantacciyar al’umma, sannan ya kamata mu fadaku mu sani ba komai ne hukuma zatayi mana ba, akwai abubuwanda dole sai mun hada dari da kwabo wajen taimakawa rayuwarmu da ta yaranmu.

Kashi na karshe kuma, su ne gwamnati ko hukuma, hakika duk gwamnatin da ta san metakeyi tasan dukkan abubuwan da ya damu al’ummarta kuma sun san hanyoyin da za’abi wajen magance dukkan matsalolin da suke barazana ne ga dorewar al’umma. Ko dai gwamnati a mataki na karamar hukuma ko jiha ko gwamnatin tarayya. Daga karshe ina mai addu’ar Allah ya shiryi shugabanninmu, kuma Allah ya basu ikon sauke nauyin da yake kansu na al’umma.

Yasir Ramadan Gwale

yasirramadangwale@hotmail.com

http://yasirramadangwale.blogspot.com

Saturday, February 18, 2012

Sani Hashim Hotoro: Matsalar ANPP a Kano

Yanzu dai sanin kowa ne cewa ta faru ta kare dangane da dukkan wasu abubuwa da suka shafi babban zaben 2011, inda tuni ya zama tarihi kuma ya shiga kundin tarihin kasarnan, haka itama shekarar 2011 mukayi bankwana da ita sai dai wani jikon, haka kuma ‘yan siyasa da dama sun gwada kwarinsu a wannan zabe wasu ta kai musu inda suke ta murna da sowwa, wasu kuma sun rasa inda akayi aka haihu a ragaya jugun jugun. Hakika lokaci ya yi da yaka mata a zauna a kalli wasu dalilai ne ko matsalolin da suka janyowa jam’iyyar ANPP matsala a wannan zabe duk da muhimmiyar damar da ake da ita, ta cewa gwamna mai tafiya dan wannan jam’iyyar ne.

Zance na gaskiya akwai tarin matsaloli da suka janyowa wannan jam’iyya samun nakasu, kuma sannan ‘yan hamayya sunyi amfanii da propaganda domin kawo wa jam’iyyar matsala kuma sukayii sa’a suka cimma nufinsu. Misali fitacce masanin nan Gerhard Lensky a shekarar 1991 yace duk mutumin da yake son wani muhimmin abu yakanyi amfani da dukkan wasu hanyoyi da yake ganin idan ya bi su zai kai ga samun wannan abu, ta hanyar kama zukatan mutane da wasu abubuwa sabbi kuma masu sauki akan al’umma wadanda sukayi dai-dai da hankali da tunani. Haka kuma idan zamu iya tunawa shugaban kasar Amerika Barack Obama a lokacin da yake yakin neman zabe ya yi amfani da wasu kalamai da suka janyo masa karin farin jini da karbuwa a tsakanin Amurkawa, domin ya yi amfani da kalamar “Yes we can” ma’ana tabbas zamu iya. Kusan duk sadda ya fita yakin neman zabe zaiyi ta maimaita wannan kalma, haka har ta samu karbuwa a tsakanin Amurkawa kuma akaci sa’a wannan kalami ya kara masa karbuwa sosai.

Idan kuma muka dawo Kano, babban dan hamayya Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi amfani da wani take kamar yadda Obama ya yi wajen kama zukatan musamman matasa, wannan take shi ne kwankwasiyya amana, hakika kamar yadda Lensky ya fada dole mutum ya yi amfani da wani abu sabo kuma wanda zai dace da hankali da tunanin mutane domin kama zukatansu a lokacin da yake neman wani abu muhimmi. Idan muka dauki dan takarar gwamnan na PDP a jihar kwara Abdulfattah Ahmed shima ya yi amfani da wani take mai suna Legasy continues shima wannan ya yi tasiri kwarai da gaske wajen samun karbuwarsa. Inason a yimin kyakkyawar fahimta ba ina nufin dantakararmu baiyi amfani da irin wannan salo ba, a’a ko kadan bana nufin haka hasalima Mallam Salihu Sagir Takai ya yi amfani da wani salo na babu makami sai addu’a wanda a karshen lokaci aka zo da wannan take, wanda a hakikanin gaskiya taken da wahala ya sami karbuwa idan anbi bayanan manazarta sanin dabi’a da tunanin dan Adam, domin yadda Ibn Khaldun ya fada acikin littafinsa mai suna ‘mukaddima’ baka amfani da sunan wani adu da kasan hadari ne ga al’umma domin samin amincewarsu, komai kyan abinda zaka fada kuwa, tana iya yiwuwa Ibn Khaldun shima ya yi kuskure a wannan ra’ayin nasa, domin ba fadar Allah bace.

Haka kuma, muna kallon yadda aka rinka yakar Mallam salihu ta kowanne bangare. Domin daga cikin irin propagandar da akayi amfani da ita kuma tayi tasiri a zukatan mutane ita ce cewa jama’ar kano basa son Takai, sukayi ta kururuta wannan magana wanda duk munsan karya ne, daga karshe har mutane suka fara gamsuwa cewa Takanannanfa ba’a sonsa ya kamata mai girma gwamna ya sauyashi daga cikin wadan da suka rudu kuwa harda da yawa daga cikin ‘yan ANPP, kaga wannan anyi amfani da wani abu da ba gaskiya bane domin a kullum shi abokin adawarka neman wata hanya yake da zai sare maka guiwa a wajen jama’a, don mai-makon kayi tallar manufofinka sai ya canza maka akala inda zaka koma kare kanka da nuna cewa abinda yake fada akanka ba gaskiya bane, shi kuma a gefe guda yana ci-gaba da yada nasa manufofin.

Sannan kuma, aka sami wani bangare acikin jam’iyyar ANPP wadan da ake kira ‘yan tabare wanda abinda da sukeyi kamar kara gishiri ne a cikin garin ‘yan adawa, amma uwar jam’iyya tana kallo batayiwa wannan tufkar hanci ba duk da ‘yan boko da dumbin masana da muke da su a cikin wannan tafiya, inda suma sukaci nasarar kama zukatan al’umma da wadan nan kalamai. Baya ga haka akazo ana cewa Mallam Salihu mai hannun jarirai ne haka shima akayi amfani da dama aka dauke hankalinmu daga bayyana hakikanin manufarmu ga al’umma zuwa nuna cewa abin ba haka bane.

Sannan idan muka kalli wani salo da PDP suka yi amfani da shi wajen kama zukatan matasa a wannan zabe shi ne, duk kankantar masoyin PDP da kwankwasiyya basa wasa da shi, domin nasan wani da yana da ra’ayin wannan tafiya ta su, duk da baima gama fahimtar kansa ba, amma suka daukeshi da muhimmanci, haka zakaga suna gayyatarsa zuwa dukkan irin tarukan da suke yi, anan sai na lura da cewa gaskiya su basa wasa da magoyin bayansu komai kankantarsa, domin shi wannan yaro ya shirya wani taro na motsa ‘yan jam’iyya amma idan kaga manyan mutanen da suka halarci wannan taro abin zai baka mamaki, kaga ko babu komai wannan kara kaimi ne ga matasa masu goyon bayansu, kamar yadda Max Weber ya ce duk dan adam yana son ka bashi kima da girmansa, wannan zata sanya kaci nasara akansa.

Idan kuma muka kalli bangaren ANPP ta wannan janibi, zance na gaskiya basuyi komai akansa ba, don basu cika baiwa kana nan magoya baya muhimmanci ba, wadan da kuma sune abokan tafiya sune sarakan yaki, domin wasu manyan mutanan idan da zasu zo taro ko bazasu ce komai ba wani karin karfin guiwa ne ga magoya baya. Wallahi Allah ya albarkaci wannan tafiya da mutane masu akida ta gaskiya wadan da ba wani abu suke son a basu ba illa kawai kwarin guiwa da karfafasu, domin nasan matasan da suka taimakawa wannan tafiya da kudinsu da lokacinsu da tunaninsu, ba su da niyyar su sami wani abu idan ankai ga gaci, amma jam’iyya batayi wani abu na kuzo mu ganiba wajen binkitosu tare da karfafamusu guiwa.

Manyan shugabannin wannan jam’iyya suna maida hankali ne ga manyan ‘yan jam’iyya. Mutanan da wallahi wasu ko zaben basa fita suyi, suna gida a kwance suna tsegumi, kuma yana daga cikin nasarar ‘yan PDP da suka kama zukatan matasa da mata shi ne duk abin da aka basu domin su rabawa al’umma sukanyi iyakar kokarinsu wajen hakan, amma wallahi nasan ‘yan ANPP da dama wadan da za’a basu wani abu su raba amman zasu jibge agida suda iyalansu, ina fatar za’a yimin afuwa akan wannan magana, domin wallahi kishin Mallam Salihu Sagir Takai ya sanyani rubuta wannan koke, amma dai ina ganin lokaci ya yi da zamu fadi gaskiyar al’amura domin samin mafita a lokaci na nan gaba.

Wata rana na tattauna da wani abokina akan wannan tafiya ta Mallam Salihu, ya shaidamin cewa matsalar shugabannin jam’iyyar ANPP shi ne suna da raina magoya baya, nace masa hakika ka fadi gaskiya domin a irin yadda nake kallon shugabannin jam’iyya na jiha da kananan hukumomi basu dauki magoyin baya a bakin komai ba, domin zakaga wannan unguwar akwai daya daga cikin shugabannin jam’iyya ko dai a mataki na jiha ko na karamar hukuma kuma ga masoya na hakika sai kaga babu ruwansa da su; wanda irin wadan nan mutane ‘yan PDP suke saurin ribata a karon farko.

Kamar yadda wannan sakamakon zabe ya nuna idan har kotu ta tabbatar da shi cewa ba mune mukayi nasara ba wanda bana fatan hakan, to ya nuna cewa lallai Mallam Salihu Sagir Takai da Dr. Bashir Shehu Galadanci suna da dumbin magoya baya domin samun adadi irin wannan mai yawa da yakai sama da Miliyan daya to kuwa bai kamata a yi sakaci har ya zogaye ba, ya kamata a tsaya a kalli hanyoyin da suke na hakika wadan da za’a bi wajen tufke barakar da ake da ita da kuma dinke dukkan wata matsala da ake da ita. Hakika akwai ‘yan jam’iyyar da sunyi kokari wajen ganin wannan tafiya ta sami nasara, bai kamata a kyale su ba, ya kamata a cigaba da karfafa musu guiwa tare da tabbatar da su, anan nima nake son yin amfani da wannan damar wajen yin jinjina ga Hon. Dr. Musa Iliyasu Kwankwaso domin hakika yana daga cikin mutanan da suka bayar da gudunmawa babu dare babu rana wajen samun nasarar wannan tafiya, haka shima Alhajin Baba (taimako) ya cancanci yabo domin yayi iyakar yinsa wajen samun nasarar wannan tafiya da sauran duk wadan da suka baiwa wannan tafiya gudunmawa a zahiri ko a badini.

Sannan bazan mance da mutane irina wadan da muka baiwa wannan tafiya dukkan irin gudunmawar da ta halatta a garemu ba tare da fatan samun wani abu ba a matsayin return, ina jinjina ta musamman ga kananan kungiyoyi na tafiyar Mallam Salihu, Hakika ayyukanmu da addu’armu bazasu tafi a banza ba insha Allah.

Daga kashe, ina mika wannan koke nawa ga mai girma shugaban jam’iyyar ANPP Alh. Sani Hashim Hotoro da cewa lallai ya kamata a tsaya a kalli irin matsalolin da muka fuskanta a wannan tafiyar da kuma hanyoyin da za’a bi wajen kawo gyara, kuma muna tabbatar muku cewa wallahi muna nan tare da wannan tafiya ta Mallam Salihu Sagir Takai da Dr. Bashir Shehu Galadanci. Zan rufe da baitin wata waka da wani mawaki ya yiwa wannan tafiya cewa “takai da galadanci ayari na alkhairi ya zowa kanawa” Allah ya tabbatar mana da wannan ayari da kuma alkhairin da ke cikinsa. Muna tawassali da sunayen Allah tsarkaka, madaukaka, Allah ya karbi addu’o’inmu ya tabbatar mana da alheri ko a yanzu ko a nan gaba.

Yasir Ramadan Gwale

yasirramadangwale@gmail.com

http://yasirramadangwale.blogspot.com

Sunday, February 12, 2012

General Murtala Muhammad: Tafiya da Gwani Mai dadi!

Najeriya kasa mai yawan al’umma, da tarin kabilu daban-daban. Wannan kasar tamu kusan zamu ce ta raini muhimman mutane da suka rayu a wannan bigire wadan da duniya ta shaida kwazonsu da jajircewarsu da karfin halinsu da kuma nuna kishin al’ummarsu. Kusan tun lokacin da aka samar da wasu yankuna mabanbanta yanki mai fadin kasar noma da tarin jigawa daga Arewa da kuma yanki mai cike da kurmi da bishiyun kwakwa daga kudu a matsayin kasar Najeriya a shakarar 1914, kamar yadda tarihi ya bayyana matar Gwamna Lugga ita ta samar da wannan suna daga Niger Area ya koma Najeriya.

Tun a wancan lokaci aketa fafutukar tabbatar da kafuwar kasa daya al’umma daya kamar yadda ake cewa, wanda a zahiri al’umma biyu ce, da mabambantan kabilu. Anyi ta kokarin samarwa da mutanan wannan yanki abubuwan more rayuwa da suka hada da wutar lantarki da sufuri da inganta noma da kiwo da ilimi da lafiya ga wannan al’umma. Amma har kawo wannan lokaci wannan kasar bata shaida irin wadan can alkawura da akasha yi mata a lokuta masu tsawo ba. Kusan wannan lokaci da muke ciki shi ne wani mawuyacin lokacin da kasarnan bata taba ganinsa ba tun shekarun 1914, abinda ya hada da rashin tsaro, cire tallafin albarkatun man fetur, hare-haren bama-bamai, garkuwa da mutane, satar mutane tare da yankasu, mugun talauci da bakin jahilci, kwankwadar barasa, rikicin addini da na kabilanci, rikicin manoma da makiyaya, Allah ya kawo wadan da zasu kubutar damu daga wannan mawuyacin hali.

Yau litini 13 ga watan fabrairu, tayi dai dai da ranar da marigayi General Murtala Ramat Muhammad ya cika shekaru 36 da rasuwa, a irin wannan ranace akayiwa wannan dan tahaliki kisan gilla, awani yunkuri na juyin mulki wanda baici nasaraba. Da ace Gen. Murtala yana raye har wannan shekarar, da ya cika shekaru 74 a wannan sararin duniyar mai fadi, an haifeshi a shekarar 1938 a tsakiyar birnin kano, kaico, Gen. Murtala ya rasu yana matashi domin bai cika shekaru 40 a duniya ba, an kasheshi a lokacin da yake da shekaru 38 da haihuwa, ya rasu yana begen ganin wannan kasar ta sami ingataccen shugabanci, nan da wasu shekaru biyu masu zuwa wato 2014 Gen. Murtala zai shafe shekaru 38 acikin kabarinsa kwatankwacin shekarun da Allah ya rubuta masa a rayuwarsa ta wannan duniyar, Allahu akbar, Allah ya riskar da rahamarsa gareshi a dai-dai wannan lokaci.

Zaiyi kyau a ce gwamnati ta sauya darussan Social Studies domin karantar da yara manyan gobe irin gudunmawa da nagartar mutane irinsu Gen. Murtala Muhammad, hakika gwarzo ne abin koyi da tarihin kasarnan bazai cika ba idan babu tarihin irin gudunmawar da ya baiwa cigaba da wanzuwar wannan kasa da kuma wannan nahiya tamu ta Afrika, abin kaico shi ne yara da dama kawai suna ganin hotonsa ne ajikin takardar kudi ta Naira 20 ba tare da sun san hakikanin waye shi ba. Ka kamanta dukkan wani shugaba mai kishin al’umma da son cigabansu da kaunar kasarsa da irin so da kaunar da wannan dan tahaliki ya nunawa wannan kasa, shin ko Asibitin Murtala dake birnin kano da filin sauka da tashin jiragen sama na Murtala Muhammad da ke Legas da titunan Murtala Muhammad dake galibin jihohin kasarnan sun isa su biya abinda wannan bawan Allah ya yi wa kasarnan a kwanaki 199?

Gen. Murtala kusan ya shafe kwanaki 199 a kan kujerar shugabancin kasar nan a matsayin Head of state, ya hau mulki daga 29 ga watan yuli 1975, zuwa 13 ga watan fabrairu 1976. Murtala shi ne mutum na biyar a jerin shugabannin kasar nan goma sha biyar, a iya tsawon kwanakin da ya shafe yana shugabanci bai kama ko kadangare ya daureba da sunan tuhumarsa da cin amanar kasa kusa tarihi ya nuna cewa shi ne shugaban da bai taba daure kowaba a mulkin wannan kasar, haka kuma shi ne mutumin da ya fara assasa cewa mulki zai koma hannun farar hula, wanda mataimakinsa da ya dora daga inda ya tsaya Gen. Olushegun Obasanjo ya cika wannan alkawari a shekarar 1977 inda Shehu Aliyu Shagari ya zama zababben shugaban kasa, haka kuma shi ne ya kirkiro jihohi da dama da kuma inganta al’amarin kananan hukumomi, haka nan kuma shi ne mutumin da ya kafa harsashin maida cibiyar mulki daga Legas zuwa tsakiyar Najeriya inda ake kira Abuja, yanzu mutumin da ya yi wadan nan muhimman ayyukan ya dace tarihi ya mance da shi? Ko shakka babu amsar zata zama a’a, don haka ya zama dole gwamnati ta yi wani tsari domin koyar da yara halayyar mutanan kirki irinsa.

Ance kusan shi ne mutumin da ya fara daidaitawa ma’aikatan gwamnati sahu musamman ta wajen zuwa aiki akan lokaci da hukunta dukkan wanda ya karya doka, a wani littafi da fitaccen marubucin nan Mista Chinue Achebe ya rubuta mai suna The Troble with Nigeria, ya yi bayanin kwanakin Murtala na farko-farko a mulkin wannan kasa, yace ko wane ma’aikaci na dari-dari da aikinsa da kuma tsoron kairya doka musamman a birnin Legas inda nanne fadar gwamnati a wancan lokaci ta ke. Yace sau da yawa Gen. Murtala ya kanyi bazata ya fito kan titi da safe ya tsallaka ba tare da danja ta bashi hannun ba domin ganin matakin da ‘yan sanda zasu dauka, ance wata rana ya tuka mota danja ta tsaidashi amma ya wuce abinsa da yalo fifa ya kamashi yace sai sunje caji ofis, ya nemi ya bashi dan na goro amma dansandan nan yace ina, ai yanzu gwamnati tayi doka, domin laifine akama ka kuma ka bada kudi domin fansa, suna zuwa ofishin ‘yansanda kawai sai ya ware nadin da ke fuskarsa nan da nan DPO ya gane shugaban kasa ne inda take ya sara masa, yalo fifa kuma yace kafa me naci ban baki ba domin yana tunanin ya gamu da gamonsa. Haka dai marubuta da dama suka ringa bayyana Gen. Murtala wajen yin shigar burtu da bad da kama domin gano ko ana karbar cin-hanci ko a’a.

Gen. Murtala wadan da suka sanshi sunce mutumne mai kwarjini da babu alamun wasa a tattare da shi, ance da zarar ya kalleka da ido idan baka da gaskiya sai kaga mutum ya hau tsima da kyarma, haka kuma Murtala mutumne da yake son yin abu da gaggawa ba tare da bata lokaci ko jin kiri ba, don haka ne akoda yaushe yake yawan mai maita kalmar da gaggawa da gaggawa, Allahu akbar irin mutanan da Arewa ta fitar a wancan loakcin kenan, Bahaushe mutumin kano a birnin ikko ikon Allah. Ance lokacin da yake Head of state gidansa da yake aciki a lokacin da yake rike da mukamin Director of army signal corps kafin zamansa shugaba bai fita daga ciki ba domin haka kullum yake fita daga shi sai direba zuwa dodan Barrack a legas, shi mutumne da bai cika son wasa ba don haka ko jerin gwanon motoci baya yi haka kuma baya kunna jiniya a lokacin da yake fita ko dawowa. Haka kuma shi kadai daga shi sai direbansa suke zuwa kano tun daga Legas a motarsa ba ta gwamnati ba, tafiyar sama da kilomita dubu 1000.

Wani marubuci, Aliyu Ammani ya bayyana Murtala a zaman wani gwarzo a lokacinsa wanda aiki kawai ya sanya a gaba, mutum mai saukin kai kuma maras girman kai. Yace wani tsohon Lauya kuma tsohon malamin jama’ar Legas mai suna Dr. Obarogie Ohanbamu ya rubuta a Mujallarsa mai suna African Spark cewa Gen. Murtala ya azurta kansa kafin ya zama shugaban kasa da mallakar dimbin dukiya da gidaje, amma duk da haka Gen. Murtala baiyi amfani da ikon da yake da shi ba wajen ci masa mutunci ko sanyawa a kameshi tare da gana masa gwale-gwale kamar yadda aka san sojoji da yi a Najeriya kawai sai ya kai shi kara zuwa Igbosere magistrate Court domin ayi musa shari’a da mutumin da ya bata masa suna a cikin jarida ance kotu ta zauna ta saurari wannan kara, kuma ta dage zaman zuwa 17 ga watan maris 1976, Allah mai yadda yaso Gen. Murtala bai riski wannan lokacin ba Allah ya cika masa ajalinsa, sai dai a wata hira da abokin Gen. Murtala na kusa ya yi da jaridar The Punch ta ranar 4 ga watan mayu 1982, marigayi Cif MKO Abiola ya ce Gen. Murtala ya rasu ya bar Naira bakwai da kwabo ashirn da biyu(N7.22) a cikin asusunsa na ajiya, tabdi jan kaji fa shugaban kasa kenan! Allahu Akbar! Haka kuma ya bar duniya bashida gida ko katuwar gona ko gandun daji da gandun dabbobi.

Ammani, ya cigaba da cewa a ranar 11 ga watan Janairun 1976, Gen. Murtala ya kada hantar kasashen yamma da wata kasida da ya gabatar a taron kasashen Afrika na OAU da akayi a birnin Adis Ababa na kasar Eithiopia akan ‘yancin kasar Angola mai taken Afirka ta kawo karfi wanda da turanci ake kira Africa has come of age.

Gen. Murtala ya yi jawabi kamar haka, ya ce “ ya mai girma shugaba, idan ina tuna irin yadda fararen fata suka bautar tare da nuna wariya ga bakaken fata a kasar Afurka ta kudu, zuciyata tana kara bugawa ne, wannan al’amari yana dugunzumani matuka kamar yadda dukkan wani mai kishi yake jin ciwo idan ya tuna wani abu irin wannan” haka Gen. Murtala ya ci gaba da jawabi yana cewa “ yanzu fa kasar Afurka ta kawo karfi, babu wata kasa da zata cigaba da bamu umarni muna bi, kowacece kuma duk karfinta, dole mu hada karfi da karfe wajen yakar wannancin-kashi da akeyi mana domin kwatowa ‘yan uwanmu ‘yanci ko da kuwa hakan zai kai ga salwantar rayuwarmu” Allahu akbar haka ikon Allah yake Gen. Murtala yana wannan jawabi ne a lokacin da tuni Allah ya rubuta cewa kwanaki 34 ne kacal suka rage masa a duniya, haka dai ya cigaba da jawabi mai cike da armashi da kwarin guiwa da nuna rashin tsoro ko gazawa.

Haka Gen. Murtala yake da karfin hali da rashin nuna tsoro ga kuma kwarjin. Kamar yadda marigayi Sunday Awoniyi yace shi mutumne da ko da yake a makaranta a Barewa College Zariya baya fada da sa’anninsa sau da dama zaka samu yana fada da na gaba da shi akan anzalinci na kasa. Kamar yadda masana sukayi bayani ana son shugaba jarumi mai kwarjini maras tsoro da kuma karfin hali, hakika Gen. Murtala ya cika dukkan wadan nan abubuwa da suka sanya zai iya zama kowane irin shugaba.

Haka dai mutanan kirki suke cigaba da gushewa a wannan rayuwa, a dai-dai lokacin da ake bukatar juriyarsu da jajircewarsu. Hakika Najeriya ta yi rashin gwarzo abin koyi, daya tamkar da dubu, muna addu’ar Allah ya jikan Gen. Murtala ya kai rahama kabarinsa ya sanya mutuwa ta zamo hutu a gareshi, Ya Allah ka arzurta wannan al’umma da mutane masu karfin hali da kwazo irin nasa koma wadan da suka fishi. Allah ya jikan General Murtala Ramat Muhammad . . . ranka ya dade zan karkare da wata magana mai cike da azanci kamar haka, da nasan zamu rabu da bamu saba ba, sabo mai dadi ga rabuwar tazo, kamar yadda ka nuna kishi ga kasarmu muma muna yimaka addu’ar fatan alheri, duk da nasan bakajina a halin yanzu, amma inada yakinin insha Allah addu’ata zata riskeka. Allah ya hadamu a darussalam da alheri. Bahaushe yana cewa kada Allah ya kawo ranar yabo! Amma nikam ina fatar Allah ya cigaba da nunamin ranar da zan yabi mutanan kwarai irinka, lallai Hausawa suna cewa tafiya da gwani mai dadi, idan gwanin bai lalace. Tabbas mun shaida cewa kai gwani ne.

Yasir Ramadan Gwale

yasirramadangwale@gmail.com

http://yasirramadangwale.blogspot.com

Friday, February 10, 2012

Siriya: Bashar Al-Assad, Karshen Alewa kasa!

Kusan yanzu idan akwai wani abu da yafi kisan kare dangi a duniya to za’a iya kiran abinda Bashar Al-assad ya ke yi a kasar da yake mulki tsawon lokaci da jam’iyyarsa ta Ba’ath ta shafe shekaru kusan 43 tana yi, musamman kisan kiyashin da ya ke yi a Birnin Homs da Dar’a. Hakika abin da ya ke faruwa a wadan nan birane ya yi muni kwarai da gaske kamar yadda Saleh Al-Dabbakeh da yake aiki karkashin International Human Right Groups a kasar Siriya ya shaidawa gidan talabijin na BBC cewar munin abin da yake faruwa a wannan birni na Homs ya yi yawa ainun.

Haka shima wani matashi Ez-Al-deen Al-halabi daga tsakiyar birnin Homs ya shaidawa gidan talabijin na Al-Jazeera ta wayar tarho cewar hakika mutanan wannan birni suna cikin wani irin mawuyacin hali na harbe-harbe babu kakkautawa daga dakarun da gwamnatin Bashar Assad da ta jibge a wannan birni, da gidan talabijin din na Al-jazeera suka tuntubi Salam el-Homsy ta hanyar amfani da Skpe yace mutanan wannan gari suna fuskantar karancin abinci da ruwan-sha da magunguna ga shi kuma babu wutar lantarki a wannan gari, ya kara da cewar akwai matsananciyar yinwa tsakanin al’ummar sannan kuma yace wani likita ya shaida masa cewa kananan yara da yawa suna mutuwa.

A rahotan da yake aikawa da gidan talabijin na BBC daga birnin Bierut mai makotaka da kasar Siriya Jim Miur ya ce rahotannin da suke fitowa daga wannan birni, yace hakika mutane suna cikin tsanani kamar yadda ya yi hira da wani magidanci da ya fusata yace ina dukkan kungiyoyin kare hakkin bil-Adama suna gani Assad zai karar da al’ummarsa domin ci gaba da mulkinsa na danniya da cin zali.

Ita ma a nata bangaren Majalisar dinkin Duniya ta ce kusan tundaga fara wannan bore ankashe fiye da mutane 5,000 a kasar ta Siriya wanda dakarun gwamnatin Assad sukayi, tace a makon da ya wuce kawai an kashe fiye da mutane 400 a wannan birni na Homs inda ‘yan Adawa suke da karfi, kididdiga dai ta nuna cewa muslumi sunni sune suke da rinjaye a wannan kasa.

Haka kuma, rahotanni suna cewa manyan sojojin kasar suna ballewa daga bangaren gwamnati suna komawa gurin ‘yan adawa kamar yadda wani gidan talabijin mai goyon bayan ‘yan adawar ya ke fada a shirye-shiryensa da yake watsawa da harshen larabci, inda kuma sukace dukkan alkaluman da ake bayarwa akan kisan da dakarun gwamnati sukayi ya ninka ninkim ba ninkim.

Bashar Al-Assad: kusan za’a iya cewa duk abinda ya keyi gadone da mahaifinsa ya barmasa, don shima Hafiz Al-Assad ya aikata irin wannan danyen aikin a shekarun 1980s ya halaka dumbin magoya bayan ‘yan jam’iyyar nan ta Islama wadda ake kira Muslim Britherhood bayan boren da sukayi na Allah wadai da mulkinsa a wancan lokaci. Shi dai Assad yana bin tsarin kama karyar da jam’iyyarsa ta Ba’ath ta ke aiwatarwa kusan tun a shekarun 1963, ita dai wannan jam’iyya wani mutumne da ake kira Micheal Aflaq ya kafa ta kuma tun wannan lokaci har kawo yanzu itace ta ke mulki, kuma banda mulkin danniya da kama karya babu abinda suka sanya a gaba. Shi dai Assad ya fito ne daga wata karamar kabila da ake kira Al-awites marar farain jini tsakanin ‘yan kasar.

A cikin ‘yan kwanakin da suka gabata majalisar Dinkin Duniya, karkashin kwamitin sulhu suka kada kuri’a akan wani kuduri da kasashen yamma irinsu Amerika da Birtaniya da Faransa suka kawo da yake cewa lallai Assad ya yi murabus, amma kasashen Rasha da Chana suka hau kujerar naki akan wannan kuduri inda suka ce wai yakin basasa na iya barkewa a wannan kasa. Kusan duk wannan abin da yake faruwa shi shugaba Bashar Al-assad yana rawa ne da bazar wadan nan kasashe domin yana da masaniyar cewa duk irin wannan babatu da kasashen yamma sukeyi akan kasarsa gara musu shi akan wani sabon shugaban Siriya da zaizo da basu sanshi ba, domin suna tsoron kada su kori Assad kuma su sami wani shuagaba da zai sukurkuta alakar kasar Syria da Israela, domin ko babu komai Assad ya yi shiru akan tuddan Golan da Isreala ta mamaye.

Wannan cema ta sanya ake ganin Shugaba Assad yana yin duk abin da yake yi ba tare da wani tsoro ko shayi ba. Amma duk da kungiyar kasashen larabawa basa tabuka wani abin kuzo mu gani su ne suka fara gabatar da wannan kuduri a gaban kwamitin sulhun majalisar dinkin duniya na fatattar shi Assad, inda Firaministan kasar Qatar Hammad Bin Jassim Althani ya wuce gaba wajen gabatar da wannan kuduri, kuma sukaci nasara Amerika ta goyi bayansu akan lallai Assad ya sanna yi, ita dai wannan kungiya ta kasashen Larabawa daman shi Assad baya kallonta da wata kima ko daraja da zata iya zama barazana a gareshi domin yasan cewa kusan suna zaman ‘yan amshin shatan kasashen yamma ne, domin a ganinsa da suna da tasiri da ya gani akan kasar Iraqi da Libiya da Tunisiya.

Kungiyar ta kasashen Larabawa ta tura wakilai da suke je Birnin Damascus don tattaunawa tsakanin Assad da ‘yan Adawa, da kuma ziyartar inda tashin hankalin ya yi tsamari kamar birnin Homs domin suga yadda za’a iya sasantawa tsakanin gwamnatin Assad da ‘yan Adawa karkashin Muslim Brotherhood, inda suka je suka dawo ba tare da samun wani mataki na kuzo mu gani ba. Haka shima sarki Abdallah na kasar Saudiyya yaga baiken kasashen Rasha da Chana bisa matakin da suka dauka na hawa kujerar naki akan Siriya inda ya zargesu da abin kunya, yace bai kamata a tsaya a zura ido ga Assada yana cigaba da kisan talakawa bayain Allah ba.

Idan zamu iya tunawa wannan juyin juya hali ya samo asali ne daga kasar Tunisiya inda wani mutum mai saida kayan marmari da ake kira Bouzizi ya bankawa kansa wuta a gaban ginin majalisar dokokin kasar sakamakon matsananciyar rayuwa da yace yana fuskanta, wannan ta haifar da zanga-zanagar da tayi sanadiyar awon gaba da shugaba Zainul Abedeen Ben Ali, inda daga nan ta harbu zuwa kasar Masar inda aka jiyo Shugaba Husni Mubarack yana kira ga kasashen yamma cewa muddin suka bari akayi awon gaba da shi to su kwan da sanin cewa dukkan shugaban da zai biyo bayansa mai tsananin kishin addinin Islama ne kamar yadda ya ce, amma wannan barazana bata hana kasashen yamma su juya masa baya ba wajen marawa ra’ayin jama’a baya, babu girma babu arziki Mubarack duk da irin daular da ya shiryawa kansa ya sauka daga kujerar mulki yana ji yana gani ya koma sham el-Sheikh da zama.

Haka abin yake ga shugaba Ghaddafi, inda ya yiwa al’ummarsa barazana akan yin bore, haka ya debo mutane sojojin haya daga kasashen Afirka da ake kira Sub-Saharan Africa suka dinga kashe jama’arsa musamman a biranen Misirata da wasu garuruwa da suka hada harda Benghazi da Bani-walid da wani shashi na Birnin Tripoli babu ji babu gani kawai domin sun juyawa shugabancinsa na shekaru 42 baya, nan yaja kunnen NATO cewa muddin suka kuskura suka sanya baki akan abinda ya shafi Libiya to zai haifar da yakin basasa, kuma idan har suka bari ya kubuce a zaman shugaban Libiya to al-qa’ida ce zata karbi ragamar mulkin kasar Libiya, shi ma dai wannan barazana a banza domin NATO ta shiga inda ta mara baya ga ‘yan adawa kuma suka ci nasarar kifar da azzalumar gwamnatinsa da batasan kimar jinin al’ummarta ba, haka kungiyar ‘yan adawa karkashin jagorancin NTC suka ci nasara.

Shararren malamin nan na Musulunci Sayyid Qutub ya ce neman ‘yanci wata bishiyace da bata tsiro bata tofo har sai masu nemansa sun shayar da wannan bishiya da jinin jikinsu, haka kuwa ya faru domin al’ummar kasar Masar sun kwanda sanin cewar matukar za’a nemi ‘yanci sai anrasa rayukan mutane da dama, duk da barazanar Mubarack haka suka fita dandalin ‘yanci na Tahrir domin rera sananniyar wakar nan ta neman ‘yanci ta al-shab yurid, isqat al-Nazim. Haka shi ma babban MUFTI na kasashe Larabawa Shekh Dr. Yusuf Al-Qardawi ya yi wata fatawa a khudubar juma’a da ya yi daga kasar Qatar inda yace ya halatta duk wani shugaba da ya juya baya yana yakar al’ummarsa a kashe shi idan anganshi, wannan ya yi tasiri kwarai da gaske wajen kawar da shugaba Gaddafi, domin yaci amanar mutanan da ya shafe sama da shekaru 40 yana shugabanta.

Shima a kwanakin baya da yake hira da jaridar Daily Telegraph ta Birtaniya Shugaba Bashar Al-Assad yace matukar kasashen yamma suka bari ‘yan adawa karkashin Muslim Brotherhood sukaci nasarar kifar da gwamnatinsa to kuwa wata mummunar girgizar kasacce zata faru a kasashen Larabawa, lallai duk wanda yaji wadan nan kalamai na Assad yasan cewa ya kidime; domin ya manta da irin kisan kiyashin da mahaifinsa Hafiz Al-assa ya yi alokacin da yake mulki kuma ya manta da dubban mutanan da suka halaka a biranen Aleppo da Constantinople da Jerusalem da Baghadad da Damascus duk wannan bai haifar da girgizar kasa ba sai mulkin wani mutum kwaya daya Assad shi ne zai haifar da girgizar kasa!

Hausawa dai suna cewa abin da yaci Doma baya barin Awe duk, da irin wannan barazana da Mubarack da Gaddafi sukayi bai hana guguwar sauyi tayi awon gaba da su ba, don haka Assad ya kwana da sanin karshen alewa dai kasa haka shima zai bi sahun wadan nan shugabanni, watakila irin kisan da za’ayi masa ya fi na Gaddafi muni, duk da yana ikirarin yana da magoya baya a birnin Damascus, a gefe guda kuma yana tunanin cewa Hezbollah da kasar Iran zasu bashi goyon baya wanda a hakikanin gaskiya duk wanda yake bibiyar siyasar kasashen gabas ta tsakiya yasan da cewa Assad yana yaudarar kansa ne kawai da tunanin samun goyon baya daga Iran da Hezbollah.

Kamar yadda Mutanan Benghazi da Tunis suka shaki iskar ‘yanci muna fatar nan bada jimawa ba ‘yan uwanmu da suke biranen Homs da Dar’a dama wadan da suke a birnin Damascus suma zasu shaki irin wannan iskar, kamar yadda juyin juya halin kasar Faransa ya ce dole a baiwa kowa ‘yanci batare da la’akari da launin fata ko kabila ko addini ba, tunda ‘yancin dan Adam din da kasashen yamma suke ta kwarmato Assad na takawa, amma kuma muna da yakinin cewa duk da irin dasawar da suke yi a yanzu lokaci kankani zasu juya masa baya.

Haka shima Shugaba Ali Abdallah Saleh na Yemen ba’a barshi a baya ba wajen aikata ta’addaci ga a’ummarsa ta hanyar yin amfani da jami’an tsaro suna muzgunawa masu bore da mulkin danniya nasa, wanda a karshe yakeson gadar da dancikinsa. Bayan da yake ta kokarin fararutar ‘yan alka’ida domin ya farantawa Amerika da sauran kasashen yamma, shima muna nan muna jiran lokacin da kasashen yamma zasu juya masa baya kamar yadda hakan ta faru da takwaransa Mubarack inda al’ummarsa sukayi ta rera wakar neman ‘yanci ta al-sh’ab yurid isqat al Nizam da sannu suma mutanan Yaman zasu sami irin wannan ‘yanci.

Yasir Ramadan Gwale

yasirramadangwale@hotmail.com

http://yasirramadangwale.blogspot.com

Mallam Nuhu Ribadu: Juma’ar da za ta yi kyau . . .!

Mallan Nuhu Ribadu


A wata magana mai cike da armashi ta Bahaushe yana cewa, sai an shiga cikin rijiya sannan ake iya yashe ta, babu wanda zai iya yashe rijiya daga waje face ya shiga cikin ta, idan ta kama ma har ya bata kayansa. . . Mallam Nuhu Ribadu kamar yadda kowa ya sani shi ne dan takarar Shugaban kasa a karkashin jam’iyyar ACN a zaben 2011 da ya gabata. Kafin zamansa dan siyasa Ribadu tsohon ma’aikacin hukumar ‘yan sanda ta kasa ne, wato ya kai har mukamin mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, inda bayanai suka nuna har tsallaken mukami akayi masa daga mataimakin kwamishina zuwa mataimakin sifeto janar na rundunar ‘yansada na kasa saboda kwazonsa da kwarewa wajen iya aikinsa.

Sunan Mallam Nuhu Ribadu ya fara bayyana ne a lokacin da ya jagoranci hukumar yaki da yiwa tattalin arzikinsa zagon kasa da kuma yakar cin-hanci da rashawa, wadda akafi sani da EFCC, hakika ya nuna kwazo sosai lokacin da ya shugabanci wannan hukuma, domin ya kama tare da gurfanar da mutanan da ake ganin baza su iya tabuwa ba a kasarnan, bisa zarginsu da yin almundahana da dukiyar kasa. Misali bayan da sashi na 308 na kundin tsarin mulkin kasar nan ya baiwa masu rike da mukamin shugaban kasa da mataimakinsa da gwamnoni kariya daga gurfana gaban kowane irin kwamitin bincike, Ribadun yace kusan daukacin gwamnonin kasarnan barayi ne, da kuma shugabannin kananan hukumomi domin sunyi rubdaciki da dukiyar al’umma tunda yake bashida ikon kamasu ya gurfanar da su, shakka babu wannan ba karamin aiki ya yi ba, ko iya nan ya tsaya.

Sai dai ya kama tare da garkame wasu daga cikin gwamnonin da kuma tonawa wasu asiri, haka kuma da yawa daga cikin manyan attajiran kasarnan da suke ci-da gumin talakawa ya tona musu asiri, kuma da yawa sun shiga taitayinsu don ya diga ayar tambaya ga wasu daga cikin hamshakan attajiran nan irinsu Femi Otedola da Mike Adenuga da Muhammad Babangida da ya mallaki hannun jari mai yawa a wasu kamfanoni a kasar Ingila wanda mujallar Times Magazine ta wallafa.

Bayaga damke tsohon gwamnan jihar Bayelsa DSP Aliemieghsigha, ya kuma kama takwaransa na Jihar Delta Mista Jame Ibori wanda ake ganin babu wanda ya tallafawa takarar marigayi YarAdua da kudi irinsa, Ribadun karkashin hukumarsa ya zargesu da zambar kudi kusan dubban miliyoyin daloli, rahotanni sun nuwa cewa Mista Ibori ya yi kokarin baiwa Ribadu toshiyar baki ta wasu makudan kudi amma Ribadun yaki karba. Sannan kuma ya fallasa irin adadin kudaden da gwamnoni sukayi rubdaciki da su a yayin da suke kan mukamansu, misali inda ya bayyana tsohon gwamnan Jihar Jigawa Ibrahim Saminu Turaki ya yi almundahana da kusan Naira Biliyan 36, da sauran gwamnoni da daman gaske ya yinda wasu kuma suka arce suka bar kasarnan wanda suka hada da tsohon gwamnan Jihar Edo Mista Locky Igbinideon da Adamu Mu’azu na jihar Bauchi da sauransu da dama a wancan lokacin.

Haka kuma, aikin da hukumar EFCC da Mallam Nuhu Ribadun ya jagoranta ya sanya sunan Najeriya da yayi kaurin suna wajen cin hanci da rashawa ya dan samu sararawa sakamakon hukumar dake kididdige adadin kasashen da sukafi cin hanci da rashawa ta duniya suka sassauto da sunan Najeriya daga matakin koli zuwa na kasa-kasa. Hakika Mallam Nuhu Ribadu ya yi kokari wajen yakar cin hanci da rashawa a lokacin da ya rike wannan hukuma, sai dai da dama sunga laifinsa akan cewa kamar ana amfani da shi ne wajen muzgunawa masu adawa da gwamnatin Obasanjo ta wancan lokacin.

Amma dai ko me jama’a zasu ce akan wannan aiki Mallam Ribadu ya yi rawar gani, domin ita barna ko da kashi daya cikin dari aka rage ta anyi aiki, sanin kowane a yadda sunan Najeriya ya baci da cin hanci da rashawa babu yadda za’a iya yakarsa cikin lokaci kankani, hakika dole a yaba masa. Idan ba’a mantaba har ‘yar shugaban kasa Obasanjo a wannan lokacin Ribadun ya zarga da cin hanci da rashawa, wanda, idan da babu alamun gaskiya a tattare da shi da dawahala ya yi hakan.

Wannan ce ma ta sanya majalisar Dinkin Duniya ta zabi Ribadun a matsayin wanda zai jagoranci wata tawaga da zata tafi ya zuwa Afghanistan domin aikin sanya ido da kuma bankado cin hanci da rashawa a wannan kasar, hakika idan da bashida kwazon aiki ko kuma yanada alamu na rashin gaskiya da wahala ya samu wannan muhimmin aikin aikin.

A lokacin da gwamnati ta bayar da sanarwar sunasa a matsayin mutumin da aka nada wanda zai jagoranci mutane 21 domin sanya ido da kuma bayarda bayanai akan rarar kudin mai, jama’a da dama sukayi ta tofa albarkacin bakainsu akan wannan batu. A cewar Mallam Nuhu Ribadu ya samu dimbin sakonnin waya da na imel da kira akan wannan sabon mukami da gwamnati ta bashi, wasu su karfafa masa guiwa ya karba wasu kuma su ce kada ya karba, har dai ya yanke hukuncin zai karbi wannan muhimmin aikin bayan da ya yi shawara da makusantansa da kuma mutanan da yake ganin zasu bashi shawar ta gari, sannan ya kira wannan aikin da sunan wata sabuwar dama ta bankado cin-hanci da rashawa a harkar manfetur da aka dade ana zargin hukumar NNPC da aikatawa.

Bayan da aka bayyana sunansa a matsayin sabon shugaban wannan hukama ta Petropleum Revenue Special Task Force, jama’a da dama suka shiga maida martani akan wannan batu, wasu na cewa daman aiki ya yiwa PDP a sakamakon fitowarsa takarar Shugaban kasa domin ya raba kan kuri’ar Arewa ko kuma ya kawowa Buhari cikas, dama wasu zarge-zarge da dama wadan da basu da tushe. Hakika Mallam Nuhu Ribadu ya cancanci ya karbi irin wannan muhimmin aiki domin tarihinsa ya nuna zai iya, kamar yadda yace kusan duk rayuwarsa ya taso yana hidimane ga kasarsa kamar yadda ya buga misali yace ya gada ne daga mahaifinsa; domin mahaifinsa daga Danmajaisar tarayya daga Legas a jamhuriya ta farko ya dawo Yola domin rike wani dan karamin kwamitin da zai tallafawa rayuwar al’umma.

Da yawanmu muna fatar samun gyaruwar al’amuran kasarnan, amma kuma da yawan mutanan kwarai sukan kame hannayensu daga yunkurin kawo gyara. Idan har mutanan kirki zasu nade hannu suce su baza su shiga gwamnati a kawo gyara tare da su ba, ko shakka babu za’a jima gyara bai zoba domin babu yadda gyara yake zuwa lokaci guda. Misali sanin kowane da Abacha da Babangida suka hada baki aka kifar da gwamnatin Buhari a 1981 amma wannan bata hana Buharin ya karbi aikin da gwamnatin Abacha ta bashi na hukumar tara kudin rarar man fetur ta PTF ba wanda kowa yasan wannan hukuma tayi aiki na azo a gani, abin tambaya da Buhari ya kame hannunsa yaki karbar wannan aiki za’a samu gyara ta wannan bangare? Shakka babu amsar itace a’a, don haka ba laifi bane idan har Nuhu Ribadu da ya yi takara tare da Jonathan kuma ya karbi aiki a gwamnatinsa domin tallafawa rayuwar ‘yan Najeriya da kuma hidima ga kasarsa ta haihuwa.

Idan zamu iya tunawa a lokacin da akayi zabe tsakanin Tsohon Shugaban kasar Amerika George W. Bush daga jam’iyya Refublican da kuma John F. Kerry daga jam’iyyar Democrat, a shekarar 2004, da John Kerry bai sami nasara ba ya yi aiki a kwamitoci da dama a gwamnatin ta Bush bayan kasancewarsa dan majalisar dattijai, haka shima John McCain ya yi ayyuka a kwamitoci daban-daban a wannan gwamnatin ta Barack Obama wannan ya nuna cewa lallai idan ana batu na ginin kasa da kuma ci gabanta babu siyasa a ciki kowa ajiye jam’iyya yake yi a hadu a gina kasa tare, a gudu tare a kuma tsira tare.

Sabida haka ina ganin kuskure ne mutane su zargi Nuhu Ribadu akan wannan aiki da aka bashi, adaidai lokacin da kasarnan ta ke da bukatar mutane masu gaskiya wajen alkinta dukiyar al’umma, ko babu komai jama’a sun shaida irin aikin da yayi a lokacin da ya rike EFCC abinda zai tabbatar da hakan mu kalli wadan da suka biyo bayansa a wannan hukuma, kowa cewa yake gwara Ribadun akan musamman ita Farida waziri da ta biyo bayansa da kuma shi Mallam Ibrahim Lamode duk da cewa sabone bai dade ba.

Don haka, muna taya dan uwanmu Mallam Nuhu Ribadu murna tare da fatan alheri a wannan sabon aiki da ya samu mai cike da kalubale. Muna fatar zai yi aiki fiye da wanda ya yi a EFCC wanda duniya ta yaba masa kwarai da gaske, kuma muna masa addu’ar Allah ya kareshi daga dukkan wani sharri ya kuma bashi kwarin guiwar yin aiki bisa gaskiya da adalci. Allah ya taimaki kasarmu Najeriya ya bamu lafiya da zaman lafiya, ya kuma shiryi shugabanninmu ya sanya musu tsoronsa da kuma basu ikon sauke nauyin da yake kansu na al’umma.

Yasir Ramadan Gwale

yasirramadangwale@hotmail.com

http://yasirramadangwale.blogspot.com

Wednesday, February 8, 2012

Siyasar Kano Tsakanin Shekarau da Kwankwaso!!!



Siyasar kano sai kano, wannan take ko shakka babu ya yi daidai da siyasar kano. Hakika idan ana maganar siyasa a Najeriya akayi maganar Kano to ko shakka babu anzo muntaha wato magaryar tukewa, ba zai zama abin mamaki ba idan akace mutumin kano ya kware wajen iya siyasa, domin sanin kowa ne cewa jihar kano itace mahaifar Uban ‘yan siyasa marigayi Mallam Aminu Kano. Hakika Mallam Aminu Kano ya raini mutane da dama a siyasa, mutane masu akida ta cigaba da kuma kishin al’umma.

Yanzu siyasar kano ta dauki wani sabon salo, domin yanzu idan ana maganar siyasa a kano to babu kamar Mallam Ibrahim Shekarau da Engnr. Rabiu Musa Kwankwaso, don yanzu sun zama alkibla a siyasar kano kasancewar yadda sukayi tasiri matuka a siyasar, ta hanyar dumbin magoya bayansu, da kuma fada aji a tsakanin magoya bayansu, bari muyi bayaninsu daya bayan daya.

Mallam Ibrahim Shekarau: kusan shi ne mutum na farko da ya kafa tarihi a siyasar kano, domin ana cewa ba’a maimaita mulki a jihar kano sau biyu a jere, kamar yadda da daman ‘yan siyasa suke fada cikinsu harda marigayi tsohon gwamnan Kano Muhammad Abubakar Rimi. Cikin wani lokaci mai cike da sabatta juyatta Mallam Shekarau ya zama gwamnan kano a karo na biyu, inda ya karya maganar nan da aka dade ana yinta tsakanin al’ummar Kano. Mallam Ibrahim shekarau ya yi tasiri ainun a zukatan ‘ya ‘yan jam’iyyarsa ta ANPP da kuma da yawa daga cikin matasa da dattawa da kuma mutane masu kishin addini, kai ba su kadai ba ma kusan kowanne bangare na al’ummar kano zaka samu masoya na hakika na Mallam Ibrahim Shekarau.

Sanin kowa ne mallam mutumne wanda yake kokarin sanya addini acikin dukkan al’amuransa na siyasa, wannan ta sanya da yawan wadan da suke hammay da mallam suke ganinsa a matsayin mai ci-da addini, wanda wannan kalma kusan duk wanda ya fadeta ko dai bai san addinin ba ko kuma kawai yana fadar kalmar ba tare da yasan hakikanin ma’anarta ba; atakaice ma’anar ci-da addini a Musulunci “shi ne mutum ya san wani abu na addini wanda al’umma suke matukar bukatarsa amma yace bazai sanar da su ba sai anbiyashi wani adadi na kudi ko dukiya” wannan abinda aka bashi idan yaci to shi ne al’akalu biddini wannan atakaice ita ce ma’anar ci-da addini a musulunce, idan kuwa haka ne to inaganin duk wanda ya alakanta Mallam Ibrahim Shekarau da cewa yana ci-da addini shakka babu ya zalunceshi, kuma ya jahilci addini.

Baza kayi maganar siyasar Mallam Shekarau bakayi batun hakuri da yake dashi ba. Kusan yana daga cikin abin mamaki dangane da Mallam shi ne hakurinsa ya bayyana karara, domin a cikin wani yanayi da yana iya daukar dukkan matakin da yaga dama ga duk wanda ya taba mutuntakarsa, misali an sami wani shakiyyin dan siyasa ya buga hoton malamin da iyalinsa da wasu kalamai na batanci aka kuma kama wannan dan siyasa amma duk da yana da ikon daukar mataki yace ya yafe, sannan mutumne da ake shiga radiyo a fadi magana akansa babu linzami, duk da haka ya yi hakuri, wannan na daya daga abinda ya karawa mallam soyayya a zukatan jama’a da dama.

Mallam Ibrahim Shekarau, kusan a dukkan jawabansa akan jiyoshi yana farawa da karanta suratul fatiha da kuma yin addu’a bayan kammala dukkan wasu jawabai da ya yi, haka kuma mallam mutumne da ya shiga lungu da sako na jihar kano ya zabo mutane masu addini domin sanyasu a mukamai daban-daban da suka shafi al’umma, da dama wasu sunyi kokarin kiyaye nauyin da aka dora musu, wasu kuma sun yaudari malamin domin ayyukansu ya nuna basuda alaka da addini a aikace, sai dai kawai a sifa.

Sannan bayan da mallam yazo karshen zangonsa ya mara baya ga takarar Mallam Salihu Sagir Takai wanda ya yi shugaban karamar hukumar Takai, kuma ya yi kwamishinan Ruwa da kuma kananan hukumomi a jihar kano, sun fuskanci adawa mai tsanani sosai daga ‘yan hamayya, anjefesu da kalamai na bace ainun, haka kuma sun fuskanci adawa mai yawa daga cikin jam’iyyarsu ta ANPP musamman wadan da suke goyon bayan Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo suna ganin kamar juya baya ne ga biyayyar da akecewa Gwarzon na nunawa Mallam Shekarau din.

Bari kuma mu kalli ban garen Engnr. Rabiu Musa kwankwaso. Hakika siyasar kwankwaso tanada abin mamaki kwarai da gaske a jihar kano. Domin siyasarsa ta nuna cewa shi mutum ne mai juriya da karfin hali sosai. Kwankwaso mutum ne da yake da goyon bayan matasa da yawa daga cikin al’ummar kano da kuma ‘yan bangarensa na kwankwasiyya a cikin jam’iyyarsu PDP.

Hakika duk yadda ka kai da adawa da kwankwaso dole ka yarda cewa yanada matukar kishin jihar kano, sai dai mutumne da yake amfani da kausasan bayanai a mafi yawancin magan-ganunsa haka kuma kwankwaso mutumne mai yawan barkwanci, domin da wuya ka saurari kalamansa batareda ya sanyaka dariya ba.

Haka kuma bayanai sun nuna cewa kwankwaso mutumne mai son abubuwa da gaggawa, sabanin mallam shekarau da yake son abi al’amura sannu-sannu, haka kuma kwankwaso mutumne mai matukar son girma kamar yadda wadan da suka sanshi suke cewa domin mutumne da kokadan baya yarda da raini.

Shakka babu kwankwaso ma ya kafa tarihi a siyasar kano domin bayan da bayanai suka nuna cewa ya rabu da al’ummar kano dutse hannun riga a zangon mulkinsa karo na biyu, inda har rahotanni suka nuna cewa ya koma Kaduna da zama shi da iyalansa, daga baya a hankali farin jininsa ya fara dawowa, inda ya komo kano kuma ya yita zagayen kananan hukumomi domin motsa magoya bayansa. Sai dai bayan da ya dawo ya zo da wani slo daban na jan hankalin matasa wannan kuwa shi ne wani take da ake yi masa na kwankwasiyya amana hakika wannan ba karamin abu bane da zaiyi saurin janye hankalin matasa ba, domin ko da shugaban kasa yazo kano sai da yayi wannan take kuma jama’a suka amsa, wanda wannan ta nuna cewa kwankwason ya yi tasiri ainun.

Kwankwaso ya sake dawowa gwamnan kano a karo na biyu bayan tsaiko da ya samu daga gurin Mallam Ibrahim Shekarau na shekaru takwas, wannan kuma ya nuna jajircewar kwankwason da kuma nuna kwazonsa a siyasa duk da bayanai sun nuna cewa uwar jam’iyyarsa ta kasa ta so ta tadeshi a zaben gwamnan da ya gabata, amma da yake abin da Allah ya kaddara shi ne yake faruwa, basu ci nasarar shataleshi ba.

Wannan ta nuna kwarewa matuka a siyasa ta wadan nan mutane guda biyu Mallam Ibrahim Shekarau da Rabiu Musa Kwankwaso, idan har gwamna kwankwason yaci nasarar kammala zangonsa na biyu to sun zama kusan kafada-da-kafada da Shekarau a siyasance, kuma za’a dade ana tunawa da su a siyasar kano.

A bayyane ta ke cewa farin jinin mallam Shekarau na kara samun tagomashi bayan barinsa gidan gwamnati; haka shima kwankwason sai bayan ya gama munga irin yadda yake a tsakanin al’umma zamu tabbatar da kaiwarsa makura. Haka kuma a zaben 2015 kowane bangare zai tsayar da gwaninsa domin gadon kujerar gwamnan kano tsakanin Kwankwason da Shekarau, da alamun cewa daga bangaren Shekarau bazata sauya zani ba wato Mallam Salihu Sagir Takai shi ne zai zamo dan takara a 2015, yayinda a nasa bangaren shi ma ake ganin kamar zaiyi nune, alamu dai sun fara nuna cewa kwankwaso na son gadarda Rabiu Suleman Bichi a bayansa wanda a yanzu shi ne sakataren gwamnatin Kano, kafin zamansa kusan ana masa kallon na kusa da kwankwason sosai domin shi ne ma ya rike shugaban darikar kwankwasiyya a jam’iyyar PDP.

Duk wannan lokaci ne zai tabbatar mana da kwarewar siyasar Mallam Ibrahim Shekarau Sardaunan kano da kuma Engnr. Dr. Rabiu Musa Kwankwaso a siyasar kano a zaben 2015 mai zuwa idan Allah ya kaimu.

Yasir Ramadan Gwale

yasirramadangwale@yahoo.com

http://yasirramadangwale.blogspot.com

Tuesday, February 7, 2012

Dr. Rabiu Musa Kwankwaso: Albasa Tayi Halin Ruwa!

Dr. Rabiu Musa Kwankwaso: Albasa Tayi Halin Ruwa!

Kusan akwai wani abin mamaki dangane da sake zaben Muhammad Rabiu Musa Kwankwaso a matsayin gwamnan kano a karo na biyu. Hakika ya zowa da dama da abin mamaki kwarai da gaske cewa kwankwaso shi ne mutumin da kanawa suka sake zaba a 2011, domin sanin kowane mutumin kano ne cewa gwamnan bai kwashe da dadi da al’ummar kano ba a shekarar 2003 lokacin da ya nemi sake komawa a karo na biyu. Kamar yadda muka shaida an rabu dutse hannun riga tsakanin kwankwaso da al’ummar jihar kano, don gwamnan ya so komawa a wani lokaci mai cike da jumurda dangane da al’amuran da suke da alaka da aiwatar da aiki da shari’ar musulunci.

Kamar yadda muka sani ne cewa gwamnan da ya fara kaddamar da aiki da shari’a shi ne tsohon gwamnan jihar zamfara Sanata Ahmad Sani Yariman Bakura a shekarata 2000, wannan ya tsuma al’umma da dama a Arewacin Najeriya musamman al’ummar kano, inda akayi ta shirya laccoci da wa’azi dangane da burin da al’umma suke da shi na aiwatar da aiki da shari’a a kano kamar yadda akayi a zampara, wannan ta sanya gwamnan kano na wannan lokaci kwankwaso ya shiga wata sabuwar tsaka mai wuya dangane da kiran da jama’a suke masa da ya kaddamar da aiwatar da aiki da shari’ar musulunci bayan matsin lamba da ya sha daga kusan kowane bangare na al’ummar kano musamman wadan da suke da ruhi na addini, rahotanni sun nuna cewa a wannan lokacin gwamnan ya kaddamar da shari’ar ne ba don yana so ba, sai don babu yadda zaiyi.

Wannan soyayya ta shari’ar musulunci da al’ummar kano suka nuna ta haifar da samuwar takarar tsohon gwamna Mallam Ibrahim Shekarau, wanda akace ya fuskanci matsananciyar rayuwa a lokacin da yake ma’aikacin gwamnati, a lokacin Rabiu Kwankwaso, don ance yana halartar kusan wa’azozin da akeyi na motsa zukatan jama’a dan gane da shari’ar Musulunci, a saboda yana halartar tarukan da suke da alaka da shari’ar Musuluncin ne hakan ta janyo akace an maidashi malamin makaranta daga sakataren dun-dun, Allah masani.

Bayan da gwamna Mallam Ibarhim Shekaru ya shafe shekaru takwas a kan kujerar gwamnan jihar kano ya mara baya ga takarar Mallam Salihu Sagir Takai kasan cewarsa mai ruhin addini, wannan ta sanya duka bangarorin biyu suka fuskanci bakar adawa daga ‘yan hamayya cewa an dauko masu hannun jarirai dama wasu kalamai marasa dadin ji aka rika alakantasu da Sardaunan da dan takararsa.

Sai dai kuma, kwankwaso ya nuna aniyarsa ta sake zama gwamna a karo na biyu. Bayan ya tsallake turaku da daman gaske da jam’iyyarsa ta sanya masa, Gwamnan wanda ya yi ta amfani da kausasan kalamai a lokacin da yake yakin neman zabe, kalamai masu tsoratarwa kwarai da gaske. Domin a wata maganarsa da kusan ta zama zaurance tsakanin al’ummar kano wacce akajiyoshi yana cewa “Ja janjaros danja” da kuma wata magana da itama ta zama kamar zaurance wacce da yawa daga cikin ‘yan jam’iyyarsa baka rasasu da ita a waya inda yake cewa “wannan Ja shi ne maganin mayu, maganin MAHAHAA” aciki har yake cewa batun zabe anyi angama Rabiu kwankwaso yaci zabe a bashi abinsa” wanda duk wanda yaji wadan nan maganganu yasan ba’a taki zaman lafiya ba.

Tabbas da ace tsohon gwamna Mallam Ibarhim Shekaru yana son fitina a wancan lokaci da ya gurfanar da tsohon gwamnan a bisa wadan nan kalamai da suke barazana ga tsaro. Bayan haka kuma akwai wasu kalamai suma da suke barazana ne ga tsaro da zaman lafiya inda yake cewa “ko asa kaci GORO dan UJULE, ko asa maka JANBAKI, ko kuma yaro kaji WUJU-WUJU kazaga ka rasa ina gabas ta ke”, shakka babu duk wanda yaji wadan nan kalamai yasan barazana ne ga zaman lafiya a dai-dai wannan lokaci da jihar kano take da bukatar kyakkyawar al’kibla, amma da yake tsohon gwamnan ba mai son tashin hankali bane sai bai yi komai akan wadan nan kalamai na Rabiu kwankwaso ba.

Jama’a da dama musamman ma’aikatan gwamnati suna fargabar dawowar tsohon gwamnan a matsayin sabon gwamna domin anjiyoshi a lokacin yakin neman zabe yana cewa duk wani ma’aikaci da gwamantin Mallam Ibrahim Shekarau ta dauka idan ya dawo to sunansa korarre, da kuma ‘yan famsho wadan da suna masa ganin ya hanasu hakkinsu a lokacin da yake gwamna, wadan nan dama wasu da dama sun sanya jama’a tsoron dawowar kwankwaso a matsayin gwamnan kano, domin anringa ganin makamai tsirara a hannun magoya bayansa a dik sanda ya fita yakin neman zabe.

Baya ga haka kuma ana ganin lokacin da kwankwason yake kokarin dawowa lokaci ne da jam’iyyarsa ta PDP ta dage sai anzabi shugaba Jonathan wanda sukayi masa lakabi da MAINASARA JONATHAN, a daya bangaren sauran al’umma kuma suna ganin wannan dama ce ta ‘yan Arewa, wannan ta sanya da yawan mutanan Arewa suke kyamar PDP domin a tsahon lokacin da suka shafe suna mulki a kasarnan sun kasa samarwa da al’umma ingatacciyar wutar lantarki duk da irin biliyoyin da aka kashe malala, da yawan mu ‘yan Arewa muna Allah wadai da manufofin jam’iyyar PDP domin babu abin da suka sanya a gaba face shan jinin ‘yan Najeriya ina nufin matsanan ciyar rayuwa domin tun daga 1999 zuwa yau babu wata matsala da zaka iya cewa yau gashi sun dauka kuma suna kai karshenta, kullum sai karairai iri daban-dabn.

A lokacin da kwankwason yake yakin neman zabe ya yi alkawari ga jama’ar jihar kano da daman gaske, inda a karamar hukumar Kibiya mukaji yana rantsuwa cewa waallahi dukkan alkawuran da ya dauka sai ya cika su, muna nan muna jira kuma muna fatar su zama hujja a gareshi ba hujja akansa ba. Bayan ya dare kan kujerar gwamna, kwankwason ya fara ne da kididdigar ma’aikatan gwamnatin domin fitar da ma’aikatan jabu kamar yadda suka yi ikirari cewa suna nan da yawa suna cin bulus, wannan ta sanya hantar ma’aikata da yawa ta kada domin ba kowane ke son bincike ba, a cewar wani dan siyasa ko danka ne akace zai yi maka bincike dole hankalinka ya tashi ballantana hukuma, amma ta wannan bangaren kam munyabawa mai girma gwamna domin bai kamata a kyale wasu haka kurum su rika karbar abin da ba hakkinsu ba.

Bayan haka kuma, gwamnan ya kirkiro da sabuwar jami’a a kano wadda aka sanyawa sunan North West University (jami’ar Arewa maso Yamma) hakika wannan ma wani muhimmin ci gaba ne da gwamnan ya kawo jihar kano kasan cewa kididdiga ta nuna cewa akalla akwai yara kusan Miliyan daya da suke makarantun sakandare daban-daban a fadin jihar kano, duk wanda ya kalli wannan alkaluma kuma yaga abinda gwamna ya yi dole ya yaba masa ta wannan gefen, dama wasu ayyuka da aka bijiro da su wanda sun cancanci a yaba akansu.

Amma a irin yadda gwamnan yake bita da kulli akan tsohon gwamna Sardauna wannan ya nuna kamar da gaske ne yazo ne domin ramuwar gayya. Domin sau da yawa akanji gwamnan na magana akan sabon gidan da gwamnati ta ginawa Sardaunan, dama mayarda hannun agogo baya akan wasu muhimman ayyuka da gwamnatin sardauna ta bari, musamman kasurgumin aikin nan na samar da babbar cibiyar harkar sadarwa da babu irinta a kasarnan wadda ake kira Kano ICT Park, bayan kashe dubban kudade akan wannan aiki amma da sabon gwamna ya zo ya yi buris da wannan aiki.

Hakama aikin da mai girma Sardauna ya kirkiro na ADAIDAITA SAHU wanda mai martaba sarkin kano ne jagoran wannan shiri, shi ma anyi burus dashi, hakan bazai bada mamaki ba domin Hausawa sunce barewa bazatayi gudu ba danta ya yi rarrafe, daman PDP ba kishin ‘yan Najeriya suke ba na kawar da matsala sai dai kawo sabuwar matsala, kaga sai muce anan albasa tayi halin ruwa, dama manufarsu ce wannan.

Bayan haka kuma, akwanakin baya aka kaiwa ofishin shiyya na kamfanin Media Trust da ke kano hari inda ake zargin daya daga cikin jami’an gwamnatin kwankwason da hannu cikin wannan aika-aika, kamar yadda itama gwamnatin tarayya ta PDP taje gidan tsohon Ministan Abuja Mallam Nasiru el-Rufai tayi masa aika-aika saboda ya shiga zanga-zangar nuna adawa da cire tallafin manfetur da gwamnatin tayi, duk wannan na kara nuna mana cewa lallaai albasa tayi halin ruwa idan dan PDP na kasa ya muzgunawa jama’a, domin a can saman ma haka abin yake.

Sannan ga maganar tashin bama-bamai a kano. Rahotannin sun tabbatar da cewa ‘yan kungiyar Boko Haram sune suka kai wadan nan muna nan hare-hare inda sukayi ikirarin kai wannan harin, a cewarsu har wasika sun aikewa da gwamnatin amma batayi komai akai ba. Kuma anan ne zamu zargi shi mai girma gwamna da sakaci babba ta fuskar tsaro domin tunda wannan kungiya suka bayarda wannan sanarwa babu wasu alamu da suka nuna andauki mataki na kare al’umma daga wannan barazana. Hakika dole gwamna ya dauki al’hakin sakaci da ya yi tabbas da andauki mataki da abin yazo da sauki, zakayi mamaki ace ajihar kano an daddasa bama-bamai har kusan guda hamsin a cikin birni kuma duk sun tarwatse amma a kasa gano lokacin da ake dasa wadan nan bama-bamai wannan abin akwai daure kai kwarai da gaske, muna fatar Allah ya kare aukuwar hakan anan gaba.

Sannan bayan wannan al’amari ankawo sojoji da ‘yan sanda masu yawan gaske da suke tsanantawa al’umma akan hanyoyin da aka sanya rodubulo, jama’a na gaggawar komawa gida domin gudun kada su karya dokar da aka sanya, amma ko ya ya mutum ya taka wannan doka sai ya sha wulakanci mai yawan gaske, wanda wannan dole gwamnati ta takawa abin birki. Allah ya taimaki jihar kano ya bamu lafiya da zaman lafiya, kuma muna addu’ar Allah ya shiryi shugabanninmu ya basu ikon cika mana alkawuran da suka dauka mana, ya kade mana fitina da tashin hankali.

Yasir Ramadan Gwale

yasirramadangwale@hotmail.com

http://yasirramadangwale.blogspot.com