Monday, December 28, 2015

Hattara Jama'ah



HATTARA JAMA'A MUSAMMAN  MASU ABABEN HAWA!

Dazu dan uwa Tijjani Ahmad yake bamu labarin wata fitina da ta kunno kai a cikin wasu unguwannin cikin Birnin Kano. An wayi gari wasu mutane marasa tsoron Allah masu fama da cutar bakar Hassada da mugunta da Kyashi da munanawa Allah zato suna bi unguwanni suna Bankawa motocin mutane wuta babu gaira babu dalili a lokacin da Sahu ya dauke, abin ya faru a unguwar Gwammaja da Tal'udu da kuma Titin Aminu Kano. Dan haka, jama’a musamman wadan da suke da motoci kuma ba suda garejin aje mota suke barin su a waje suna kwana, ya zama dole a sanya ido. 

Mutanen da suke aje motocin su a makarantu ko wani filin unguwa da su lura kuma su sanya ido sosai, a samu masu gadi san kare dukiya. Ba shakka duk wanda zai sanya motar mutane wuta ta kone kurmus dan kawai Hassada da Kyashi to wannan ya kai matukar mutum mara tsoron Allah. Ana bi ana kashe mutane babu ji babu gani, ba tare da wani hakki ba. Yanzu kuma abin ya koma kan dukiyoyin mutane lallai lokaci yayi da mutane zasu tashi dan baiwa unguwannin su da dukiyoyinsu kariya. Ya Allah ka kare mu da karuwar ka, masu wannan mugun nufi Allah ka tona asirinsu. Ya Allah ka tsare mu ka tsare mana dukiyoyinmu. 

Yasir Ramadan Gwale 
28-12-2015

No comments:

Post a Comment