Wednesday, March 27, 2013

SU WA KE DA HAKKIN SAMAR DA ZAMAN LAFIYA A KASAR SIRIYA?

SU WA KE DA HAKKIN SAMAR DA ZAMAN LAFIYA A KASAR SIRIYA?

Kusan yanzu a bayyane take cewar babu inda aka mayar da zubar da jini ba wani abin labari ba a duniya kamar kasar Siriya. Gwamnatin kasar Siriya karkashin Jagorancin Jam'iyyar Ba'ath wadda iyalan Assad suka yiwa kaka-gida kusan tun shekarun 1971 suke aikata wannan ta'annati karkashin al-ummar da suke ikirarin suna shugabanta. Shugaba Bashar Assad da mahaifinsa Hafiz Assad dai dukkanninsu 'yan Shi'ah ne kuma sun fito ne daga wasu tsirarun kabilun da ake kira Shi'ah Alawiyyin, masu nuna goyon baya ga kasar Iran.

Wannan satoka-sa-katse na kasar Siriya ya samo asali ne a ranar 15 ga watan Maris na shekarar 2011, sakamakon Yekuwar da masu adawa da mulkin zalunci da danniya karkashin Baath da Assad Dan shi'ah suke yi tsawon lokaci. Tun a wannan rana ne aka ga dumbin jama'a a babban birnin Damaskas sun fito suna kira ga Shugaba Assad da ya san inda dare yayi masa, domin a cewarsu sun gaji da zama cikin zalunci da kaskanci. Wannan gangami ya samu karbuwa a tsakanin al-ummar Siriya inda a watan Afrilu birni na biyu mafi girma a Siriya Aleppo shima ya dauki harami daga nan sai sauran garuruwa da suka hada da Homs da Hama da Idlib harda yankunan kan iyaka duk suka dauka. Wannan bore kuwa ya biyo bayan wata guguwar sauyi da ta kada a kasashen larabawa tun a wannan lokaci kamar yadda masharhanta a yankin suke cewa, domin wannan guguwar sauyi ita ce tayi awon gaba da shugabanni na wannan yanki da suka hada da Shugaba Mubarack na Masar wanda ya shafe kusan shekaru 30 yana kan karagar mulki da Shugaba Ben-Ali na Tunisiya da Ali Saleh na Yemen da kuma shugaba mafi jimawa akan karagar mulki a yankin kasashen larabawa wato Mu'ammar Ghaddafi wanda shi guguwar aikawa da shi lahira tayi ba da wata-wata ba.

Haka kuma, a watan Afrilun ne shugaba Assad ya baiwa sojojin gwamnati umarnin su bude wuta akan masu bore. Wannan umarni ya haifar da mummunan sakamako inda ya haifar da kisan gilla ga mutanan da galibinsu Sunni ne da basu san hawaba balle sauka, wannan ne ya yi saanadiyar samar da Katafariyar kungiyar kawancen Masu Adawa da gwamnatin Assad da kuma wasu sojoji da suka balle daga jikin gwamnati suke ganin babu yadda za a sanyasu su ringa kashe 'yan uwansu babu ji babu gani. Daga nan sai kungiyar hadakar jam'iyyun Siriya ta Gauraya da Sojoji masu biyayya garesu, sojojin da suka balle suna da makamai a hannunsu kuma suna da dabarun yaki, dan haka sai aka samu kungiyar matasa 'yan sa-kai wadan da zasu taimakawa wadannan sojoji dan mayar da fansa ga dakarun gwamnati, wannan ne yayi sanadiyar rikidewar gamayyar 'yan adawa suka dauki makamai suna fuskantar gwamnati.

Daga nan aka samarwa da gamayyar 'yan adawa masu dauke da makamai dan-kare kansu cikakken tsarin gudanarwa da tafiyarwa karkashin tsarin soji sirki da tsarin demokaradiyya. An kafsa kazamin fada tsakanin Dakarun gwamnati masu biyayya ga Assad wadan da galibinsu Shi'ah ne da kuma dakarun sa-kai masu biyayya ga gamayyar kungiyoyin 'yan Adawa inda jini ya dinga kwarara a daya daga cikin birane mafiya tarihi a duniya Damaskas. Munin abin bai tsaya iyaka Damaskas ba ya sake kazancewa ainun a birnin Aleppo da Dar'a da Homs da Hama.

Bayan da wannan al'amari ya dauki wani irin salo ne, sai kungiyar kasashen larabawa da aka fi sanai da Arab League a turance da majalisar dinkin duniya da kasashen turai da Amerika suka tsoma baki.

Zamu cigaba insha Allah.