Tuesday, April 30, 2013

BARAWON JARABAWA MA BARAWO NE


BARAWON JARABAWA MA BARAWO NE

A karshen makon da ya gabata, dalibai da dama ne suka rubuta Jarabawar UTME ko JAMB. Kusan bayanai sunce dalibai sama da miliyan da rabi ne suka rubuta jarabawar, Amma abinda ya bani mamaki irin yadda naga wasu da hankalinsu suka dinga bayar da satar amsa firi palo ko kunya basa ji, wani har kuri yake yi, wai shi ya taimakawa masu jarabawa! Shin yanzu da satar jarabawa za'a shiga jami'ah sannan kuma ayi abin kirki? Lallai abin akwai daure kai da tashin hankali, musamman idan muka yi hasashen makomarmu a nan gaba. Wadannan barayin jarabawa sune fa nan gaba zasu zama shugabanni, idan har zasu yi satar jarabawa akwai tabbacin idan suka ga dukiyar al'umma baza su sata ba?

Ilimi shine gishirin rayuwa, duk al'ummar da bata da masu "Ingantaccen Ilimi" tana cikin babbar matsala. Domin duk shekara makarantun gaba da sakandare zasu yi ta yaye jahilan dalibai a matsayin wadan da suka kammala karatu. Alabashshi daga baya su shiga siyasa duk su rikata al'amura su hana kasar tafiya yadda ta kamata. Naji wani daga cikin masu bayar da satar jarabawar yana ikirarin cewa "Ai kawai a sata idan an shiga Jam'iah komai zai ware" Haka naga wani ya fada! Tayaya komai zai ware tare da kayan sata? Da idona wani lokaci a baya naga wani Malamin Jami'ah yana sayar da Takardar Jarabar "post UME" abin ya dauremin kai matuqa, yadda malamin Jami'ah zai daurewa satar Jarabawa Gindi.

Lallai 'yan uwana dalibai da matasa sai an zage dantse anyi karatu. Idan ba haka ba kuwa za'ayi da nasani mara amfani, da yawanmu muna ta bata lokaci a facebook da sauran shafuka bayan ga abubuwa masu muhimmanci a gaba amma ba'a kula su ba. Lallai ne duk dalibin da yake son ganin ya fito da kyakykyawan sakamako sai ya dage yayi karatu da gaske ba da wasa ba, kuma ba da dogaro da satar jarabawa ba.

Yanzu ba dole nan gaba gine-gine suyi ta ruftawa da mutane ba, saboda Injiniyoyin da sukayi aikin mafiya yawancinsu barayin jarabawa ne ba kwararru bane. Likitoci suyi ta yanka mutane suna kashesu. Abin akwai ban tsoro matuka idan muka tuna makomar masu zuwa nan gaba. Domin al'amarin kullum kara tabarbarewa yake yi, Ingancin Ilimi yana kara yin kasa. Ana ta samar da dubgaggun malaman Firamare da sakandare da sauransu.

Allah ya kyauta.

Yasir Ramadan Gwale
30-04-2013

Saturday, April 27, 2013

SHUGABA JONATHAN KO TANTAL BATAITE




SHUGABA JONATHAN KO TANTAL BATAITE
Tunda aka samar da wannan kasar mai suna Najeriya a kusan shekaru dari (100) da suka gabata ba'a taba samun kidahumin shugaba mara mutunci kamar shugaba Jonathan ba. Hakika, wannan shugaban ya nuna rashin iyawa da kasawarsa karara ta cewa ba zai iya jagoranci wannan kasa bisa gaskiya da Adalci ba. Shugaban kasar da yayiwa kansa dabaibayi da cin-hanci da rashawa da kuma muguwar satar da ta zarce hankali. Shugaban wanda kullum yake ta kokarin ya nunawa duniya cewa gwamnatinsa tana iyakar yinta wajen sauke nauyin da al'ummar Najeriya me mabambantan kabilu suka dora masa, wanda a hakikanin gaskiya, dukkanninmu 'yan Najeriya muna san shi (shugaban kasa) katafaren makaryaci ne mara kan-gado, mugun mutum ne mara tsoron Allah.

A dukkan lokacin da Shugaban zai tattauna da 'yan jaridu musamman na ketare yana ta kokarin ya nuna musu cewa yana yin iyakar kokarinsa illa kawai abin nanne da ake cewa, idan dambu yayi yawa baya jin mai! Wanda a kashin gaskiya su 'yan Najeriya sun san da cewa wannan hasararriyar gwamnatin bata yin komai wajen sauke wannan nauyi na jagorancin da yake kanta, face wadaka da warisa da dukiyar kasa. Dukkan wasu surutai da shugaban kasa yake yi, mun san cewa karya ce tsagwaronta kawai yake shararata a duk lokacin da sanyin dakin watsa labarai ya doke shi.

Da gangan shugaban da gwamnatinsa suka ki samar da cikakken tsaro a yankin Arewacin Najeriya ba wai dan abin ya gagaresu bane. Yau idan gwamnati ta so duk wasu masu tayar da kayar baya da hannu za'a kamasu ba tare da amfani da muggan makamai ba. Amma da yakke akwai wata boyayyar manufa wadda ba ta alheri bace da suke son cimmawa, kullum suna nuna cewa abin yana neman ya gagari kundila (sha'anin tsaro). Kullum suna kira cewa wai talakawa su taimaka da bayanan da zasu kai ga bin sawun masu aikata laifuka dan samo bakin zaren, bayan sun manta cewa shi talakan da suke neman agajinsa shine suke kashewa baiji ba, kuma bai gani ba. Kuma ma idan banda tsabar rainin wayo da wulakanci, ina amfanin dukkan irin kudaden da ake warewa dan sha'anin tsaro suke tafiya? Saboda an mayar da mu kamar gidadawa bamu san abinda muke ba, suna can suna watanda da dukiyar kasa, sannan su dinga bulayin iska bayan sun kwankwadi barasa wai a taimaka musu da bayanai. Kaji Iskanci! Shugaban da kusan a kullum sai kara zama wata kwarkwantacciyar 'kura' yake yi ga mutanan Arewacin kasarnan ta hanyar karya tare da lalata yankin. Daman gari banza ya aka iya da 'kura' balle ta kwarkwance, kaga kuwa lallai sai wanda Allah ya tsallakar.

Shugaban kasa ya kidime inda yake ta bagauniya, kamar wanda ya sha giyar Agogoro, hankalinsa ya tashi, kullum tunaninsa ya za'ayi ya tsawaita wa'adin mulkinsa bayan 2015. Tabbas, shugaban kasa da masu bashi shawara da makusantansa musamman irinsu Tony Aneni da Doyin Akupe da irinsu Ahmed Gulak da su Aku-kuturu (Labaran Maku) da sauransu, duk suna yi masa ingiza wawa-kwari ne, ta inda zasu kaishi su baro, koma sun riga sun kaishi sun baro; domin su din bukatar kansu ce kawai a gabansu, ba wai al'ummar kasarnan ba. Shugaban ya zama rakumi da akala, suna dorashi akan mummunar turba wadda babu inda zata saukeshi sai dandalin Nadama da kuma da-nasani a lokacin da bazata amfaneshi ba, domin kuwa, duk cikinsu babu wanda zai yarda ya tayashi zama a kiri-kiri ko Kurmawa bayan zaben 2015. Kowannensu ta kansa zaiyi ya kyaleshi, tunda shine Direba sitiyari yana hannunsa lokacin da motar ta fara neman kakarewa duk fasinjojin ciki arcewa zasu yi su bar direban da jangwam, alhali shi Direban ko gidan mai be sani ba a jikin motar, haka nan za'a cimmasa, mugun Arne!

Haka kuma, a rahotannin da muke ji, daga bakin Aku-kuturu cewa, bazasu lamunci aibanta shugaban kasa da 'yan Najeriya suke yi ba a kafafen sadarwa na Internet, har wata majiya ta ce shugaban ya bayar da kwangilar kusan dalar Amurka Miliyan 40 dan a dinga leka masa akwatunan Email da Status Update na facebook da Twitting din 'yan Najeriya, dan a tunaninsu zasu fara daukar mataki. Lallai kuwa shugaban kasa ya dauko dala babu gammo. Amma ni shawarar da zan baiwa su Aku-kuturu shine su fara da kara yawan dakuna a gidajen yarin kasarnan, domin saboda bacin rana.

Shukka babu, mu mutanan da wannan shugaban ya zalunta, ya karkashe mana al'ummarmu babu gaira babu dalili, ya karya mana tattalin arziki dan-mugunta da keta da tsabar bakin ciki. Insha Allah, zamu yi dukkan mai yuwuwa wajen ganin munkai keyar wannan shugaban kasa a 2015. Zamuyi addu'ah domin itace matakin farko, kuma malamai sun gaya mana cewa ita addu'ah takwabin mumini ce; sannan kuma, zamu yi amfani da dukkan wasu hanyoyi da suka halatta a garemu wajen ganin mun cimma nufinmu, na kakkabe wannan shugaban ko yaso ko yaki Bi'iznillahi.

Daman mu da muka yi Imani, Allah ya gaya mana yana taimakon wadan da aka zalunta idan sun yi hakuri kuma sun tashi da gaske. Hakika munyi hakuri, kuma zamu tashi mu zage dantse a matsayin wadan da wannan mutumin da 'yan tawagarsa suka zalunta dan-ganin mun taka musu burki ko da tsiya ko da arziki, kuma Insha Allah muna kyautata zato cewa a wannan karon Allah zai taimekmu.
Yasir Ramadan Gwale
27-04-2013

A KAI-KAICE SHUGABA JONATHAN YANA AIWATAR DA MUGUWAR MANUFAR OBASANJO TA RAGE YAWAN MUSULMI A AREWA!!!




A KAI-KAICE SHUGABA JONATHAN YANA AIWATAR DA MUGUWAR MANUFAR OBASANJO TA RAGE YAWAN MUSULMI A AREWA!!!
Duk da irin tsanani da mawuyacin hali da Musulmi muke ciki a Arewa ko Najeriya, baza mu taba mancewa da muguwar manufar Obasanjo ba. Shakka babu gwamnatin tsohon shugaba Olushegun Obasanjo mu mutanan Arewa ba zamu taba mancewa da ita a tarihi ba, bisa irin yadda ta gallaza mana ta saka al'ummar Arewa Musulmi cikin wani irin mawuyaci kuma matsanancin hali. Halin k'a'ka nika yi, da ni 'yasu, banda fatara da mugun talaucin da aka kakaba mana ta karfi da yaji, aka kashe mana dubban mutane a Shagamu da sauran sassan kudancin kasararnan ba, aka kashe mana masana'antu ta karfi da yaji dan a gurgunta tattalin arzikinmu a nakastamu ta yadda za'a kwantar da tattalin arzikinmu kasa ya kasa motsi, aka talauta manyan 'yan kasuwarmu, masu shigo da kaya daga waje da kuma masu sana'anta kayansu anan cikin gida ta hanyar kashe masana'antun da rashin samar musu da wutar lantarki da sauran abubuwan bukata nay au da kullum.

Obasanjo a wancan lokacin, yayi amfani da hukumar kwastam, domin nakasta kasuwancinmu. Bahaushe zai shigo da kaya na dubban miliyoyi kasarnan zuwa Arewa tundaga saukarsu akan ruwa, ya biya kudin futo da dukkan haraji da ake biyawa haja, sai ya kawo kayansa ya kasa a kasuwa a Kano ko a Kaduna, sannan jami'an kwastam zasu biyoshi har kantinsa su kwashe masa kaya su kone su kurmus, da sunan kayan da gwamnati ta hana shigo da su! Duk wannan yana nan rubuce cikin kundin tarihinmu, bazamu taba mancewa da shi ba. Allah ne kadai yasan irin adadin mutanan da aka talauta ta wannan hanyar a Arewa; daman ba'a maganar kankanan masana'antumu da kuma manyan da suke a tsakanin Kano da Kaduna wadannan duk sun zama tarihi sai dai tsaffin gine-gine da suka zama sansanin batagari da sauran kwari da suke washshagare walle a cikin wadannan gine-gine.

Sannan kuma, a lokacin gwamnatin Obasanjo da ta gabata aka kone mana manya manyan kasuwannin da suke Arewa Misali kasuwar Galadima Road da take Kano, da kasuwar 'yan magani da take a Kaduna da babbar kasuwar dake birnin Jos wadda kaso 90 ciki 100 Musulmi ne suke juya dubban miliyoyin Nairori a ciki, duk wadannan manyan manyan kasuwanni ne da kudi suke kewayawa a ciki a kullum ranar Allah, wadda ankonesu tun zamanin tsohuwar gwamnatin Obasanjo, Yanzu Alhamdulillah wasu sun tashi wasu kuwa har yanzu suna nan a kwance. Banda mutananmu da aka dinga dorasu a jirgin sama ana rikito da jirgin mutanan su mutu, duk wannan muna sane.

Yanzu idan ka dauki babbar kasuwar Jos, Allah ne kadai yasan adadin miliyoyin da aka yi hasara a wannan kasuwa, 'yan kasuwar da aka karya aka durkusar dasu, Allah ne kadai yasan adadinsu, bayan an durkusar da kasuwancinsu aka dinga binsu har gida ana kashewa, Obasanjo ya kasha, sannan Dariye da magoya bayansa suma su kasha, sannan a kashe matansu bayan anyi musu fyade ana ribace 'ya 'yansu kanana ana mayar dasu bayi a kasarsu ta haihuwa.

Idan bamu manta ba, tun bayan da Obasanjo ya zo a matsayin shugaban kasa na goma sha uku (13) ya fito da kiyayyarsa a fili balo-balo ga Musulmin Arewacin kasar nan. Tun bayan zuwansa ne, ya fara aiwatar da mummunan nufinsa na rage adadin musulmi da suke cikin soja da 'yan sanda, ta hanyar kashe wasu daga cikinsu a jirgin sama, ko kuwa a yi musu ritayar karfi da yaji, sannan dukkan wani babban soja ko dansanda da aka sauke ana maye gurbinsa ne da kirista ko na Arewa ko na Kudu, sannan a wasu jihohi da suke da kiristoci kamar Bauchi da Gombe da Borno da Adamawa da Taraba da Kaduna ake raba daidai tsakanin Musulmi da kirista wajen daukan sabbin sojoji da 'yansanda, wannan abun ko shakka babu haka gwamnatin Obasanjo ta aiwatar tun a wancan lokacin! Kai hatta jihohin da suke da Musulmi 99.9 sai da aka dauki Kiristoti a aikin soja da dansanda irin Zamfara da Jigawa.

Ma'aikatan gwamnatin tarayya kuwa kusan sai da (arna kiristoci) suka kusan mamaye dukkan ma'aikatan gwamnatin tarayya. Kaje Babbar sakatariyar gwamnatin tarayya dake Abuja kai zaka dauka a Idiyaraba kake ko a Onica arnan sun mamaye ta gabaki daya, kwata-kwata ba'abi tsarin daukar ma'aikata da ake kira "quota system" ba. Anyi masa fyade a nan wajen. Idan ka shiga wata ma'aikatar a Abuja sai kaga Hausawa 'yan Arewa Musulmi basu fi cikin 'yan yatsunka ba, kuma wai sunan Babban birnin tarayya yana yankin Arewa inda Mulsulmi suke da rinjaye kenan, dukkan wadan da suka isa suyi Magana suna kallo babu wanda yace uffan! Wadan da suka iya rashin kunya daga cikin shugabbani marasa kishi sune zasu ce wai mu 'yan Arewa ne bamu da 'Qualification' kamar yadda aka ruwaito kakakin rundunar sojojin Najeriya yana fada.

Haka kuma, muguwar gwamnatin ta Obasanjo ta kirkiri wani shiri wanda shine kashin bayan mayar da Musulmin kasarnan saniyar ware, ta kira wani abu waishi Babban taron makomar kasa ko 'Supreme National Conference' wanda aka yi mana rainin wayo iyakar rainin wayo, amma daga cikin 'yan bokonmu da wadan da suke kiran kansu sune manya da yaku bayin da masu rike da mukaman babu wanda ya iya kalubalantar abin. Domin a cikin mutum 382 da aka ce zasu halarci wannan taro mutum 150 ne kacal Musulmi sauran 217 gabaki dayansu kiristocine, kuma masu ilimin gaske, wadan da suka san kan-tsiya da makirci. Mu kuma a namu bangaren siyasa ta damamala abin inda gwamnoni suka yi ta bada sunayan wasu rafkanannun mutanen da sun gaji suna bukatar hutu wai sune zasu wakilcemu a wajen wannan taro. Allah ya isa!

Sannan aka zo aka shirya WAI kidayar jama'a 'census' inda akayi mana wakaci ka tashi, aka kwashe mana kafafu. A wannan kidaya akace za'a kirga yawan gidaje da mutane, aka kaskantar da wasu jihohin irinsu kano da Kaduna da Katsina da Sokoto da Borno aka rage musu yawan jama'a. Sannan daga bangaren kudu aka daukaka darajar wasu jihohin ta fuskar yawan jama'a irinsu Bayelsa da Delta da Ekiti da Akwa Ibom da sauransu, wadan da a zahiri basu kai yawan mutanan cikin irnin kano ba. Duk fa, wadannan Obasanjo yayi wannan ne damin share fagen kakkabe Musulmi daga rike wasu dukkan manya manyan mukamai na gwamnati irin yadda Shugaba "Poul Biya" na kamaru yayi na zare hannun Musulmi daga cikin dukkan wasu al'amura na hukuma. Wannan shine irin abinda Obsanjo yaso aiwatarwa Allah ya watsa aniyarsa. Shakka babu wadannan kadan ne daga cikin irin mugayan manufofin Gwamnatin Obasanjo akan Musulmin kasaranan, musamman na Arewa.

Kamar yadda dukkanmu muka sani, Obasanjo shine kashin bayan wannan shugaba na yanzu Goodluck Jonathan wanda shine shugaba na goma shabiyar (15). Kafin wannan shugaban da yawan 'yan Arewa sun san da cewa bayan da Allah ya kashe tazarcen Obasanjo! Domin babu wasu 'yan Arewa da zasu yi mana burga cewa sune suka kashe tazarcen Obasanjo, wallahi mun sani Allah ne ya hana Obasanjo tazarce, domin acikin duk masu cewa su suka kashe tazarce babu wanda yake yiwa Obasanjo baranza, ya riga yaga wallensu, yasan 'yan iska ne mazinata 'yan luwadi mashaya giya! Idan banda 'yan kadan da sukayi dan Allah, dan al'ummar kasa. Dan haka kar yake kallonsu shi(Obasanjo).

Dan haka ne shi Obasanjon ya dauko Marigayi Malam Umaru Musa YarAdua a matsayin wanda zai gajeshi. Da yawan 'yan Arewa sun sani cewar Obasanjon ya dauko Umaru ba da kyakykyawar niyya ba ne, Allah masani! Amma dai yanzu mai aukuwa ta auku, ko da niyya ko babu niyya ya zuwa yanzu Obasanjo ya ci nasarar aiwatar da mummunan nufinsa ta wata kaikaitacciyar hanya. Duk kuwa da ana ta ruwaitowa a Jaridu cewa akwai tsamin dangantaka ko alaka tsakanin tsohon shugaba Obasanjo da wannan shugaba maici, mun san cewa duk wannan wasan kwaikwayo ne ake yi da hankulan wasu daga cikinmu, Obasanjo yana kawar da hankulan mutane daga kan irin muguwar barnar da ya aikata, ta hanyar nuna mana shi yana kalubalantar wannan gwamnati, amma kuma a cikin sirri sai a ruwaitoshi yaje ya gana da wannan shugaban sun tattauna a kebe ba tare da bayyanawa 'yan jarida abubuwan da suka tattauna ba.

Shakka babu, wannan shugaban, Goodluck Jonathan, shine wanda yake biyewa Obasanjo wajen tabarbarewa da lalacewa. Haka kuma, muna da masaniyar cewar dukkan abinda yake yi muguwar manufar Obasanjo ce da bai samu dama ba, yake aiwatarwa a halin yanzu, inda yake ta kakkabe hannun musulmi daga manya manyan madafun iko da lalata tattalin arzikin Arewa da tabarbara harkar ilimi da dangoginta; daman kuwa tsaro yanzu ba'a Magana, Allah ne kawai yake kare rayukan bayinsa muminai, domin anci nasarar kakaba mana wasu kungiyoyi da sunan Musulmi ko Musulunci da bayar da mummunan hotanmu a duniya da nuna cewa mu din ba masu san zaman lafiya bane. 

Sannan kuma, akayi amfani da dakarun tsaron da mafiya yawancinsu kiristane suke dinga kahsemu babu ji babu gani da sunan farautar masu aikata laifi. A duk duniya babu wata doka da tace a kashe mai laifi, shi mutumin da ya aikata laifi, duk abinda yayi zargi ne har sai ankaishi kotu ta tabbatar masa da laifinsa sannan ya zama mai laifi, a bisa tsarin doka cewa aka yi idan har ta kama za'a harbi mai laifi to a harbeshi d harsashin ROBA ba kashe shi za'a yi ba,  Idan kuma har ta kama za'a yi amfani da harsashi mai RAI to za a harbeshi ne a kafafuwansa, amma mu kam babu ko daya da ake aiwatarwa, soja arne mashayin giya zai harbi Musulmi a kai ko a kirji ya kashe Musulmi bisa hujjar mai laifine, kuma ya kashe banza a wajensu, dan babu wani abin da za'a yi. Yawanmu ya zama na tsintsiya babu shara, masu iliminmu da dattabanmu basu iya amfanar da mu da komai ba, illa kara jefa mu cikin kaskanci da wahala da wulakanci.

Yana daga cikin mugun gadon da Obasanjo ya barwa wannan shuguban haddasa manya manyan rigingimu guda biyar (5) a Arewa, wadan da idan aka ci nasarar aiwatar dasu to shugaban zai samu damar cigaba da mulkinsa har illa masha Allah. A'azanallah! Idan bamu manta ba shugaban sojojin Najeriya Burgediya Ihejirika yayi wata ritaya ta babu gaira babu dalili ga manya manyan sojoji musulmi inda aka maye gurbinsu gabaki daya da kiristoci 'yan kudu, kuma duk surutunmu ya tashi a maho, dan bai hanasu aiwatar da nufinsu ba. Daga cikin rikice-rikicen da aka barwa wannan shugaban dan yayi dukkan maiyuyuwa wajen ganin ya ruruatsu sune:

1- Abu na farko, shine kokarin haddasa fada ko rikici tsakanin Musulmi da Kirsta a Arewa. Wanda wannan abu ne sananne kuma bayyananne cewa anci nasarar haddasa wannan fadan, da kuma sanya muguwar gaba tsakanin Musulmi da kirista a Arewa. Kusan kullum kiristoci takalar musulmi suke yi da fitina a kasarnan, eh! Tabbas takalar fada suke yi, ina nufin kiristan Arewa, wannan abu ne da baya bukatar buga wani misali domin duk wanda ya kwana ya tashi a Arewa yasan da haka.

2- Abu na biyu, shine haddasa fada ko rikici tsakanin 'yan Arewa da mutanan kudu maso gabas (yankin Inyamurai)  Shakka babu suna nan suna yin aiki dare da rana wajen ganin an hadamu fada. Domin duk mutanan kudancin kasarnan babu wadan da suka kai Inyamurai sakewa a Arewa suyi kasuwanci babu tsangwama. Wannan ce ta sanya a kwanakin baya suka kai harin Bom a tashar Mota a sabon garin kano inda galibin Inyamurai ne ke safarar fasinja daga kudu zuwa Arewacin kasarnan, anyi wannan mummunan aiki da gayya ne da nufin hadamu fada dasu, saboda alakar dake tsakaninmu ta kasuwanci ta wargaje.

3- Abu na uku, shine kokarin assasa wata muguwar kiyayya da gaba tsakanin mutanan Arewa da mutanan yankin kudu maso kudu. Wanda tarihin siyasar kasarnan ya nuna cewa akwai kyakykyawar dangantakar siyasa da mutanan kuryar kudancin kasarnan da 'yan Arewa. Haka ta sa a kullum ake ruwaito 'tsagerun yankin suna takalar mutanan Arewa da fitina da tashin hankali da munanan kalamai, masu barazana ga tsaro, amma babu ko mutum guda da aka taba kamawa da sunan tuhuma dan tayar da tarzoma. Edwin Clack da tsagerun kungiyar MEND wadanne irin barazana ce basa yi a kullum? Wadanne irin kalaman takala ne basa yi a kullum? Idan banda lalacewa ta 'yan Arewa 'yan iska 'yan daba da ko suturar kirki basuda, 'yan fatsa masu kamun kifi, wai sune suke takalarmu da fitina da tashin hankali, mu kuma kullum muna ta kokarin kare kanmu da nuna cewa ba haka abin yake ba. Allah ya sawwake.

4- Abu na hudu, shine kokarin assasa muguwar fitina tsakanin Talakawa 'yan Arewa da shugabannin Arewa. Tabbas, akwai shirin da suke yi na ganin an hada talakawa fada da shugabanninsu, misali, kullum ana ruwaito jaridun kudancin kasarnan suna cewa 'yan Arewa ne suka mallaki kaso 80 ko wani abu makamancin haka na rijiyoyin manfetur a yankin kudancin kasarnan! Kamar hannunka mai sanda ake yi mana mu farmusu. Da kuma nuna cewa 'Yan Arewa sune suke da Mataimakin Shugaban kasa, da Shugaban majalisar Dattawa, da Kakakin Majalisar wakilai da sauran manyan masu rike da mukamai barkatai, dan hadamu fada dasu! Amma kuma sun mance da cewa dukkan wadannan mutanan da ake fada gabaki daya shugaban kasa shi kadai ya rinjayesu, basu isa su hana komai aiwatuwa ba. Sai dai abinda shugaban baiyi Nufi ba. Bil Hasalima majalisar kasarnan ta gayyaci shugaban kasa yaje yayi mata bayanin akan halin da ake ciki na tsaro a daidai lokacin ya sa kafa ya fice yabar kasarnan, har yau kuma bai amsa wannan gayyatar ba, kuma babu wani abu da ya biyo baya.

5- Abu na biyar kuma na karshe, shine aiwatar da kisan kare dangi akan talakawan Arewa musulmi ne ko kirista. Wanda wannan shima yana daya daga cikin abin da aka fara aiwatarwa a garin BAGA na jihar Borno a 'yan kwanakin da suka gabata. Banda mutanan da ake kashewa a kullum ta Allah a jihar Plateau. Haka kuma, su Arnan kudu su Obasanjo da tawagarsu ta su wannan munafukin shugaban Jonathan hatta kiristocin Arewa ba burgesu suke yi ba, suna tare da sune kawai a lokacin da Kiristan Arewa yake kashe Musulmin Arewa, amma banda wannan wallahi basa kaunar wani kiristan Arewa, a wajensu duk Hausawa ne 'yan Arewa.

A ganina wadannan kudurori guda biyar sune mummunan kayan gadon da Obasanjo ya barwa wannan munafikin shugaban, shi kuma yake aiwatarwa. Kuma ana amfani da rubabbun cikinmu wajen dannemu da nuna cewa mu Musulmi mune bamu da gaskiya bama son zaman lafiya, ga mari kuma ga tsinka jaka! Wato a dokemu a hanamu kuka. Lallai Ina kira garemu mu Musulmi 'yan Arewa mu tashi tsaye mu fahimci irin muggan kulle-kullen da aka yi mana danganin mun warwaresu mun fitar da kanmu daga cikin halin kangi da bauta da fatara da wahala da tsoro da firgicin da muke ciki.

Idan har wannan shugaban yaci nasarar aiwatar da wadancan munanan kudurori guda biyar, to ya samu damar cigaba da mulkin kasarar nan a bagas ko 'yan Arewa sun so ko basu so ba. Kamar yadda yanzu bayanai suke nunawa cewa a karon farko 'yan Arewa zasu dunkule dan su yaki wannan gwamnati maici kuma su hana mata wucewa ko ta halin kaka! Idan shugaban yaga babu mafita to idan ba Allah ne ya kiyaye ba, zai yi ta haddasa rikice-rikice ne a nan Arewa babu kakkautawa daga karshe shugaban kasa yace ya kafa dokar ta-baci a Najeriya gabaki daya, ya rushe majalisar kasa ya rushe gwamnonin Jihohi da shugabannin kananan hukumomi, ya kakkafa wadan da yake so, har tsawon wata shida kamar yadda doka ta tanada, shi kuma yayi amfani da karfin ikonsa ya hana kasar zama lafiya dan cigaba da bakin mulkinsa na zalunci da danniya da shan-jinin al'umma. Allah ya kiyaye! Ko mu yarda ko kar mu yarda wannan itace mummunar niyyarsu akan Musulmin wannan kasar. Ya rage namu kodai mu tashi haikan wajen yakar wannan al'amari da dukkan karfinmu da kuma dagewa da addu'o'I a masallatai da cikin sallolin farilla da na nafila ko kuma mu ci gaba da zama cikin kaskanci da wahala har tamu ta zo ta same mu.

Har yanzu, duk da mun san da cewa wadannan shugabanni namu na Arewa sune suka kaimu suka baro, su sani, suna da kima a idanunmu suna da sauran burbushin mutunci a idanunmu mu talakawa. Dan haka suji tsoron Allah su yi mana kyakykyawan jagoranci, mun yarda cewa babu wata al'umma da zata ci gaba ba tare da jagoranci ba. Dan haka wajibinsu ne su tsaya tsayin daka wajen kare mana martabarmu da martabar Addininmu da al'ummominmu. Idan kuma ba haka ba, wallahi duk wata guguwa da zata taso a nan gaba su zata fara yin awon gaba dasu. Dan kuwa sune zasu yi asara! Allah ya kiyaye.

Dan haka a matsayinsu na shugabanni kuma jagorori wajibine su kula da bukatun wannan al'umma tamu wajen ganin ansamar mana da cikakke kuma ingantaccen tsaro na rayuka da dukiyoyinmu. Kuma, lallai ne, wajibinsu ne, su matsawa wannan gwamnati idan har da gaske suke cewa yanzu ruhin kishin al'ummar Arewa ya dawo jikinsu wajen samar mana da abubuwa guda bakwa(7) wadannan abubuwan sune:

1-   Samar mana da ingantaccen Ilimi ga dukkan al'ummarmu. Ilimi tundaga matakin firamare har zuwa karama da babbar sakandare da kuma jami'ah, ya kasance kyauta ga dukkan al'ummarmu kuma wajibi ga kowanne Yaro.

2-   Samar mana da cikakken tsaro na rayuka da dukiyoyinmu da dukkan guraran sana'o'inmu, da matattarar mutane da makarantu da gidajenmu da guraran Ibadarmu da guraran tarurrukanmu, ba tare da tsanantawa ko muzgunawa mutane ba.

3-   Samar mana da tsaftatacce kuma ingantaccen ruwan sha, ga dukkan al'ummarmu birni da kauye, da kuma samar mana da ruwan da zamu yi noman rani dashi da wadataccen taki da kuma samar mana da ruwan da dabbobinmu zasu sha.

4-   Samar mana da kyawawan hanyoyin zurga zurga na motoci da na mutane, tundaga Jaba har zuwa kwangwalam da dukkan sauran yankunanmu. Hanyoyi Masu inganci da karko a dukkan biranenmu da kauyukanmu.

5-   Samar mana da tsayayyar wutar lantarki wadda bata yankewa. Wutar lantarki mai karfi ba manja ba, wadda zata dauki dukkan wani nau'I na kayan latironi.

6-   Samar mana da ingantaccen tsarin kiwon lafiya. Tsarin da zai inganta asibitocinmu da muke da su, tare da samar mana sababbi da suka kunshi dukkan wasu na'urori na zamani da manyan injina. Sannan kuma da samar mana ingatatttun dakunan shan magani, da kankanan dakunan shan magani a kauyuka.

7-   Samar mana da ingantaccen tsarin habakar tattalin arzikin kasa. Tsarin da zai kula da harkokin noma da kiwo a dukkan yankunanmu, tare da tayar da komadar dukkan masana'antunmu da suka durkushe wanda zai baiwa jama'armu damar samaun aikin yi bayan sun kamala karatu.
Wadannan sune abubuwan da muke son ganin sun yi tsayin daka da su da Gwamnoni da 'yan majalisun dattawa da na wakilai da shugabannin kananan hukumomin wajen tursasawa wannan azzalumar gwamnati ta samar mana da su. Tunda Ai shugaban kasa ba shugaban 'Yan kudu maso kudu bane, shugaban Najeriya ne, kuma muma 'yan Najeriya ne.
Idan kuwa ba haka ba, Ina kara tabbatarwa da wadannan shugabanni namu cewa wallahi a nan gaba guguwar da zata taso, su zata fara lakumewa a karon farko. Allah ya kiyaye. Daga karshe, ina rokon Allah ya bamu zaman lafiya mai dorewa a Arewa da Najeriya baki daya, Ya Allah wannan shugaban kasa kada ka bashi ikon aiwatar da wadannan munanan kudurori akan al'ummar Musulmin wannan kasa. Ya Allah ka hada kan musulmi bisa kan tutar gaskiya da Adalci, Ya Allah ka cecemu, kajikan yara da mata da tsofaffi da gajiyayyu da matasa.

Yasir Ramadan Gwale
26-04-2013  

Tuesday, April 23, 2013

MASU KASHE MUTANE BAZA SU DAINA BA, HAR SAI . . .


MASU KASHE MUTANE BAZA SU DAINA BA, HAR SAI . . .

Wadansu musulmi su kan dauki wani tsarin rayuwa na daban marar dadi wanda ya sha bamban da irin rayuwar da Alkur’ani ya nuna. Daya daga cikin kusakuran da irin wadannan mutane masu raunin imani da alfahari, wadanda ba su damu da aikin yada sakon musulunci ta hanyar dabi’u masu kyau ba, shi ne yadda suka dauki rayuwar wannan duniya kawai ba ta wuce mutum ya yi aure ya tara da iyalinsa, ya haifi ‘ya’ya ya rene su sannan ya tara abin duniya ba. Tabbas wadannan abubuwa ne da ba su sabawa koyarwar musulunci ba. Amma inda kuskuren yake shine musulmi ya mance da babban dalilin zuwansa wannan duniya, wanda shine bauta da bin dokokin Allah, ya ta’allaka kawai kan aure da haifar ‘ya’ya, da kin tafiyar da ni’imomin da Allah ya yi masa akan tafarkin addini inda ya kan tafiyar da daukacin rayuwarsa cikin hanyar gulma da cin naman sauran musulmi alhalin ya watsar da kyawawan dabi’u na addini.

Sannan wasu sun dauki hanyar zubar da jinin mutanan da basu jiba, basu gani ba, muslumi ne ko kirista, wai ita ce hanyar jin dadi da morewa a wajensu. Shin wanne irin dadi masu kashe mutane suke ji idan sun aikata kisan nasu? Shin wanda ya kashe wani shi zai iya hana kansa mutuwa ne? Idan da ace zai iya hana kansa mutuwa TABBAS da yaci riba akan wanda ya kashe, amma tunda ba zai iya hana kansa zuwa barzahu/lahira ba, to ya sani ya sake laftawa kansa nauyi ne da ba zai iya dauka ba ranar alkyama. Allah ta'ala yana fada cewa:

Ranar da Alkiyama za ta tsaya, masu laifi za su yi rantsuwa cewa ba su zauna a duniya daidai da awa guda ba. Kamar haka suka kasance ana rudar da su.- Sura ta 30, aya ta 55

Yana da kyau mu sani cewar su wadannan miyagu azzalumai masu aikata kisan kai da alfasha, har duniya ta zo karshe baza su daina aikata irin wannan danyan aiki nasu ba, har sai lokacin da mutumin da za'a kashe ya tashi domin kare kansa! Dan haka ya zama dole a garemu mu tashi tsaye a cikin lungunanmu da unguwanninmu dan baiwa rayukanmu da na iyalanmu kariya. Shakka babu, abinda ya faru a Baga (Borno) da Gujba(Yobe) kisan kare dangi ne, amma abin takaici sai bayan awanni 48 sannan shugaban kasa ya bayyana cewa WAI a gudanar da bincike, wanda muna da masaniyar duk irin wadannan kashe-kashe da akeyi cewa ake a gudanar da bincike, bamu taba jin inda binciken ya tsaya ba, wannan shima haka abin zai wuce kamar yadda saura suka wuce, bama fata. Abinda ya faru karara ya tabbatar mana da cewa hukumomi ba zasu iya samar mana da tabbatacce kuma Ingataccen tsaron rayuka da dukiyoyinmu ba, bil hasali ma sune suke kara taimakawa 'yan ta'adda miyagu Azzalumai wajen cigaba da karkashe al'umma.

Kuma karya ne wallahi shugabanni su ce wai mu koma mu dinga ADDU'A! Shin su sun yarda da addu'ar ne? Ai Manzon Allah ba addu'ah yayi ya kwanta ba. Kowa yasan mutanan da suke aikata wannan ta'addanci ba MALA'IKU bane kuma ba AL'JANU bane, Bil-adama ne, dole hukumomi su tashi wajen baiwa al'ummarsu kariya ta dukiyoyinsu da rayukansu, ba wai kawai ace mu koma gida muyi addu'ah ba, idan haka ne, ina amfanin hukuma idan har addu'ah kawai za'ayi Allah ya bada zaman lafiya. Amerika ai ba addu'ah suke yi ba, aiki suke yi da gaske na kare al'ummarsu. Dan haka hukumominmu basu da wani dalilin da zasu kalli al'umma su ce wai su koma masallatai su yi addu'ah ba. Ina amfanin mas'uliyyar da take kansu? Ba ina inkarin addu'ah bane, tabbas akwai bukatar muma mu dage da addu'ah. Amma mu kwan da sanin baka yin addu'ah ka kwanta sai ka tashi kayi aiki da gaske sannan Allah zai taimake ka.

Dan haka, Kada ka taba zaton abinda yake faruwa ba zai zo kanka ba. Ya zama dole mu tashi muce YA ISA HAKA NAN, idan kuma ba haka ba zamu cigaba da zama cikin kaskanci da wulakanci a cikin gidajenmu. Allah ya kiyaye.

Yasir Ramadan Gwale
23-04-2013

Monday, April 22, 2013

GAME DA BATUN MUSULUNTAR RABARAN PETER JATAU!!!


GAME DA BATUN MUSULUNTAR RABARAN PETER JATAU!!!

Kusan a jiya shafukan facebook da yawa da kuma wall na mutane ya cika da bayanin albishir ga 'yan uwa Musulmi cewa wani kasurgumin fasto da yake a ZARIA jihar Kaduna ya karbi musulunci. Mutane da dama sunyi ta nuna murna da farin ciki game da wannan batu na musuluntarsa. Harma naga wani dan uwa ina zaton sunansa Comrade Yusuf Lawal Amaru ya rubuta wani labari cewa yanzu haka suna wani masallaci suna sauraron karatun Malam Jatau wanda aka ce an sauya masa suna zuwa Muhammad Al'ameen. Anan yana da kyau mu Musulmi mu zama wayayyu ba gidadawa ba, Muna murna tare da maraba lale da duk wani wanda zaiyi Imani da Allah da manzonsa, amma labari irin wannan yana da matukar kyau idan an kawowa mutane shi su yi bincike kafin dorar da shi, ban sani ba watakila mutumin da su Comrade Amaru saka saurari wa'azinsa ko shima sunansa PETER JATAU, amma yana da kyau mu sani Shin waye Rev. Peter Jatau kuma guda nawa ne? Dalili kuwa shine a can shekarun baya a Kano a zamanin Gwamnatin Malam Ibrahim Shekaru wani mutum me wannan suna ya kunno kai da cewa shi me wa'azin addinin kirista ne a kasar Zazzau kuma ya kai matsayin Rabaran amma yanzu ya musulunta, an kaishi wajen manyan mutane a kano sosai harda sarakuna inda suka yi masa goma sha-tara ta arziki, sannan kuma, Freedom Radio suma sunyi wani shiri da shi na kusan sa'a guda. Wannan abun duk ya faru ne a wancan lokacin.

Haka kuma, a lokacin da Kungiyar Izala ta shirya wani wa'azi a Gombe a kwanakin baya an gabatar da wani mutum da aka ce sunansa Rev. Peter Jatau ya karbi Addinin Musulunci, kuma yana son ya gaisa da mutane, a wajen wannan wa'azi aka hawar da Mutumin da aka ce sunansa Peter Jatau kan Mumbari ya yi Magana, mutum ne fari amma ba fari tas ba, a wannan lokacin an hada shi wannan mutum Peter Jatau da daya daga cikin Malamanmu a Kano akan cewa Shi Malamin ya sanya a koyar das hi Peter Jatau Ilimin Addinin Musulunci, sunyi Musayar lambar waya da malamin namu da kuma shi Peter Jatau akan cewa idan suka dawo Kano Jatau zai nemi Malam, da yake shi Jatau din ya bayyana cewa yana zaune ne a Kano, shiru-shiru bayan komawa kano daga Gombe Jatau bai kira Malam ba, balle ayi maganar koyar da ilimin addinin Islama, da malam yaga haka sai ya shiga yin bincike akan shin waye Peter Jatau, a sakamakon Bincikensa ya gano cewar shi wannan mutum indai sunansa Rev. Peter Jatau to ya jima da karbar Musulunci ba wai sabon Musulunta bane, har kuma yanzu da nake wannan rubutu shi Peter Jatau bai nemi Malam akan amanar da aka dankawa Malamin akan cewa zai sanya a koya masa Ilimin Addinin Islama ba.

Kwatsam, kuma, a Zaria ina zaton a jiya sai wannan labari na Musuluntar Peter Jatau ya bulla, sai muka shiga cikin rudani akan shin Peter Jatau nawa ne? Lallai jama'a yana da kyau ayi taka tsantsan akan wannan Mutum Rev. Peter Jatau. Sannan kuma muna kira a gareshi idan zai yi Musulunci to ya tsaya ya yi Musulunci tsakaninsa da Allah. Akwai bayanai masu yawa akansa Idan hali yayi zamu bayyana. Wassalamu Alaikum.

Yasir Ramadan Gwale
23-04-2913

Saturday, April 20, 2013

BUDADDIYAR WASIKA ZUWA GA USTAZ ABUBAKAR SHEKAU


BUDADDIYAR WASIKA ZUWA GA USTAZ ABUBAKAR SHEKAU

Dukkan irin dangin yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah madaukakin sarki, tsiranSa da AmincinSa su kara tabbata ga fiyayyan halitta Manzon tsira Annabi Muhammad Salallahu Alaihi Wasallam da alayansa da sahabbansa da kuma wadan da suka bi tafarkinsu har ya zuwa ranar sakamako. Ina shaidawa babu abin bautawa bisa cancanta sai Allah kuma Annabi Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne. Ina bude wannan wasika da mafificin kalami, shine, Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh.

Ustaz Abubakar Shekau, na zabi rubuta maka wannan wasika ne, domin isar da wani sako a gareka, dan tunasar da kai abubuwan da ka sani, Manzon Allah yace Ku tunasar domin tunasarwa tana amfanar Munumai (Hadith). Ina fatan wannan sako na wa zai isa zuwa gareka cikin Aminci. Muna rokon Allah ya Amintar da mu a dukkan inda muke.

Uztaz Shekau, da farko ina mai yin kira a gareka da kaji tsoron Allah! Ka sani cewa dukkaninmu a wannan duniya, ba komai muke ba face bayi masu bauta ga Ubangijinmu mahalicci, kamar yadda ya fada a cikin littafinSa mai tsarki a cikin sura ta 51 aya ta 56 cewa ban halicci dan-Adam da al-jani ba face dan su kasance masu bauta a gareni, Subhanahu wata'ala, tsarki ya tabbata a gareshi! Allah Subhanahu Wata'ala ya aiko mana da Manzo wanda shine cikamakin Annabawa dan ya zo ya sanar da mu Addini, kamar yadda ya fada, lallai addini a wajen Allah shine Muslunci/Islama. Alhamdulil Lah, muna yiwa Allah godiya bisa wannan ni'ima ta kasancewarmu Musulmi ba dan zabinmu ba, sai dan haka ya hukunta. Alhamdulillah!

Haka kuma, Allah madaukakin sarki ya fada a cikin sura ta 76 aya ta 2 cewa Hakika mun halicci mutum daga digon maniyyi gaurayayye don mu jarraba shi. Kuma muka sanya shi mai ji da gani. Wannan aya ta nuna mana cewa shi mutum dan adam ba komai yake ba a wajen Allah, domin Asalinsa wani ruwa ne gaurayayye kamar yadda Allah ya fada, wato dukkan wani mahaluki a bankasa Maniyyi ne me wari. Dan haka babu abin da ya dace dan Adam ya shagalta da shi face neman dacewa a wajen ubangijinSa mahalicci. Ya Allah muna rokonka tare da tawassuli da kyawawan sunayanka madaukaka ka sa mu dace da rahamarka kuma ka tseratar da mu daga Azabarka.

Uztaz Shekau, ina zaton kana sane da irin halin da al'ummar kasar Arewa suke ciki a Najeriya na zullumi da tsoro da firgici da tashin hankali da razana da rashin kwanciyar hankali. Uwa uba kuma ga tsananin talauci da fatara da ya yi mana katutu, kuma yake karuwa a wannan lokaci, da yawan mutane suna cikin wannan firgici ne akan abinda basu san hawa ba kuma basu san sauka ba. Hakika Allah madaukakin Sarki ya fada a cikin Al-qur'ani, sura ta 29 aya ta 2 cewa, Shin mutane suna zaton za a kyale su haka nan don sun ce “Mun yi imani” ba tare da an jarrabe su ba. Hakika sai an jarrabi mutane da tsanani da tashin hankali! Ya Allah muna rokonka kada ka jarrabemu da abinda bazamu iya jurewa ba. Ustaz Shekau, ina kira a gareka cewa kaji tsoron Allah ka yi kira ga mutananka akan ku ajjiye makamai ku kyale al'umma su samu walwala, a bisa wannan tsanani da muke ciki, musamman irin yadda al'umma suke ta kiraye-kirayen neman zaman lafiya da yin addu'o'i.

Haka kuma, Kamar yadda muka samu labari cewa asalin abin da ya fusata ku, ya sanya kuka dauki (doka a hannu) makamai shine kashe muku mutane da aka yi a yayin da kuke hanzarin zuwa jana'izarsu a garin Maiduguri a shekarar 2009. A bisa yadda muka ji ana ruwaito ku kuna fada cewa wannan yana daga cikin dalilin da ya sanya kuka dauki doka a hannunku! Uztaz Shekau shin yanzu baza ku yi duba ya zuwa wannan ayar da ke cikin suratu ankabutu ba, ku maida lamuranku ga Allah, domin Allah yace sai an jarrabemu? Shin abinda ya sameku ba jarawabawr Ubangiji bace? Shin bazaku kasance masu da'a a gareshi ba Subhanahu wata'ala? Shin ko kun manta fadin Allah madaukakin sarki a cikin Sura ta 3 aya ta 142 cewa, Shin ko kuna zaton za ku shiga Aljanna ba tare da Allah ya san wadanda suka yi kokari daga cikinku da kuma wadanda suka yi hakuri (juriya) ba? Shin kun manta da wannan ayar ne, Shin bazaku kasance daya daga cikin mutanan da Allah yake buga misali da su ba cikin masu hakuri da juriya ba?

Haba jama'a! ku sani biyayya ga shugabanni wajibi ne a cikin addinin Musulunci. Daukar doka a hannu wannan ya sabawa koyarwar addinin Musulunci. Lallai kuji tsoron Allah ku ajjiye makamai ku karbi wannan ahuwa da manyan mutane suke ta kira ga hukuma akan tayi muku. Sahabin Manzon Allah mai daraja Khalid Ibnu Waleed Allah ya kara yarda da shi, a lokacin da aka je yaki dan yin jihadi, ya daga takobi zai sare kan wani Mushriki sai ya furta kalmar shahada amma duk da haka Khaled ya fille kan sa, daga baya ya baiwa Manzon Allah labarin abinda ya aikata, nan take Manzon Allah yace "Allumma inni abra'u ilayya min ma san'a kahiludn" Manzan Allah ya barranta daga abinda khalid ya aikata na kashe mutumin da ko sallah bai taba yi ba, kawai furta kalmar Shahada ya yi! Shin tsakaninku da Allah zaku iya kididdige adadin yawan mutanan da suka rasa rayukansu ta sanadiyar abubuwan da hannayanku suka aikata, a jihohin Borno da Yobe da Bauchi da Kano da sauran jihohi? Shin bakwa jin tsoron Azabar Allah ne? Lallai dukkanmu Musulmi munyi Imani da cewar Allah mai tsananin Ukuba/Azaba ne! Kuma ku sani tun daga farkon duniya har karshenta Allah bai halicci wata RAI da zata iya jurewa azabarSa ba, Hasbinallahu wani'imal wakeel! Shin kuna tunanin azabar Allah kuwa? Lallai idan kun manta ku fadaku cewa Allah mai tsananin azaba ne ga wadan da suka aikata laifuka.

Mutane newa ne suka tagayyara a wadannan jihohi ta sanadiyarku? Mutum nawa kuke zaton kun halaka da basu san hawa ba, kuma basu san sauka ba? Ku kun kashe sannan jami'an tsaro suma sun kashe. Tsammaninku ko da anyi muku ahuwa kun karba shike nan shima Allah ya yi muku ahuwa? Bakwa tunanin makomarku? Bakwa tunanin irin mutanan da suka rasu ta sanadiyarku? Wallahi ku sani rayuwar duniya ba komai bace sai wargi kamar yadda Allah ya fada a cikin sura ta 29 aya ta 64 cewa Rayuwar duniya ba komai ba ce sai wasa da wargi. Lahira – wannan ita ce rayuwa ta hakika, in da sun san haka. Lallai ku kasance masu tuna lahira da tunanin makomarku idan an koma lahira! Lallai ku sani Lahira gaskiya ce, Wuta gaskiya ce, Al-jannahma gaskiya ce. Tabbas, wadan da suka cancanci shiga wuta babu makawa sai sun shigeta komai dadewar da suka yi a duniya. Haka kuma Allah yana fada a cikin sura ta 35 aya ta 5 cewa Ya ku mutane! Alkawarin Allah gaskiya ne. Kada rayuwar duniya ta rude ku kuma kar mai rudi ya rude ku a cikin al’amarin (bin) Allah, lallai kuyi duba na hankali zuwa ga wadannan ayoyi idan kun kasance Musulmi na gari masu Imani.

Dan haka, ku sani tunda Allah ya halicci duniya babu wanda ya taba kaucewa mutuwa, babu kuma mai iya kauce mata. Allah ne ya fada a acikin littafinsa mai tsarki cewa kowacce RAI sai ta dandana mutuwa. Dan haka Lallai ne, Uztaz Shekau ka tunasar da mutananka cewa Alkawarin Allah gaskiya ne, kuma baya tashi. Mutane da yawa sun shiga cikin firgici da damuwa da tashin hankali duk a sanadiyarku, lallai kuji tsoron Allah ku bar mutane su sakata su wala a cikin garuruwansu, kamar yadda sauran al'ummatai na gurare daban daban suke watayawa a cikin kasashe da garuruwansu.

Shin bazaku yi kokari ku zama daga cikin mutanan da Allah yake buga Misali da su a cikin Suratul Bakara ba inda yace suna neman Sabati a duniya da lahira, kamar yadda ya ce a aya ta 201 "Daga cikinsu kuma akwai masu cewa ‘Ya Ubangijinmu, ka ba mu kyakkyawa a duniya da kuma kyakkyawa a lahira, kuma ka tsare mu daga azabar wuta." Shin bazaku kasance cikin wadannan mutane da Allah ya bada labarinsu ba? Haka kuma, Allah yana fada a cikin sura ta 70 aya ta 60 cewa Masu kyautatawa basu da wani sakamako a wajen Allah face kyautatawa, kamar misalin haka ne ga duk wadan da suka munana ko suka tsanantawa Al'ummar Manzon Allah, Allah zai tsananta musu ya munana musu, Allah ya kiyashemu.

Lallai ku sani Manzon Allah yace dukkan mutumin da wani ya dauki wani nau'i daga cikin nau'ukan makamin da zai iya yin kisa ya kashe mutumin da bai jiba ba kuma gani ba, lallai ranar lahira wanda aka kashe din zai kamo wuyan wanda ya kashe shi zuwa gaban Allah, yace ya ubangiji tambayi wane me nayi masa ya kasheni! Shin mutum nawa kuke zaton zasu kamo wuyanku a ranar Alkiyama dan neman fansar jininsu da kuka yi sanadiyar kwararsa ba tare da hakki ba? Lallai kuji tsoron firgici da razani da yake tattare da ranar tashin alkiyama, ranar da kudi da mulki da zurriyya da sanayya baza ta amfanawa da kowa komai ba, sai kawai wanda ya zowa da Ubangiji da tsarkakkiyar zuciya.

Daga Karshe, Uztaz Abubakar Shekau, Ina kara jadda magana ta a gareka da kaji tsoron Allah kaida jama'arka! Kuma ku sani a tare da dukkaninmu akwai mala'iku masu kididdige aikin kowannemu. Duk wanda yayi alkhairi komai kankantarsa zai gani, haka duk wanda yayi kishiyarsa komai kankantarsa shima zai gani. Wasu zasu zo suna cewa wannan wanne irin littafi ne da bai bar komai ba. Wasu kuwa suna cewa "Ha'u muqra'u kitabiya" Ku sani ku kara sakankancewa Babu wani mahaluki da zai iya jure azabar Allah, kuma Allah da kansa ya kore zalunci akan kansa, sannan ya ce sai ya sakawa duk wanda aka zalunta yayi Allah ya isa ko bai yiba. Sai dai fa idan wanda aka zalunta din ne yace ya yafe, shin mutanan da kuka zalunta a ina zaku gansu ku iya neman gafararsu? Idan wadan da suke raye sun yafe, wadan da suka rigamu gidan gaskiya kuma fa? Allah shine shaheed!

Ya Allah muna rokonka ka Amintar da mu a cikin garuruwanmu, Ya Allah ka bamu zaman lafiya mai dorewa, Ya Allah duk mai neman shiriya daga cikinmu Allah ka shiryeshi kayi masa jagora, wanda kuma baya nemanta ya kangare mata, Ya Allah ka tozarta shi ka wulakanta shi, ka nesanta al'ummar Manzon Allah daga kaidi da makircinsa. Ya Allah mun tuba ka karbi tubanmu.