Saturday, February 28, 2015

Sakwannin Whatsapp Dubu Talatin


SAKWANNIN WHATSAPP DUBU TALATIN 

Yau sakwannin wayata na Whatsapp sun kai fiye da 30,000. Kusan kullum ina samun sako a Whatsapp sama da 500 da yawansu ban san daga ina suke zuwa ba. Kusan idan zan zauna a kullum sai na share lokaci mai tsayi ina karanta sakwannin Whatsapp, abinda yake bani mamaki shi ne yadda nake samun kaina a cikin wasu groups da ban san dalilin sakani a ciki ba, ba shakka akwai groups din da nake ciki wadan da ina jin dadin su fiye da kima, wasu ina yin matukar farin ciki tare da godiya ga wanda yayi adding dina, amma wasu kam har mamaki nake idan naga an sakani a ciki.

Zan ce na gaskiya bana samun damar duba dukkan sakwannin da nake samu a kullum, nakan karanta wadan da ido na ya kai garesu ne kawai ko kuma wasu mutane da nasan tattaunawa tsakanin a da su tana da muhimmancI. Yana da kyau ga wanda yake da lambata yake san yayi adding dina a wani group ya sanar da ni. Wadannan sakwannin ba su ne suke bani mamaki ba illa idan na duba file dina naita ganin hotuna har da na tashin hankali, shi yasa kullum cikin goge hotuna nake yi. Ya kamata dai Turawan nan su kyalemu mu amfani lokacinmu haka, yanzu dan Allah da wanne zamu ji da E-Mail ko Facebook ko Twitter ko Google Plus ko LinkedIn ko Whatsapp? Gashi kuma shi dan Adam mai buri ne so yake ya zama all round alhali lokaci ba a tsaya yake ba.

Na laura da cewar an fi saurin yada Alkhairi da Sharri a Whatsapp kuma yafi da dama sirri. Wallahi idan naga wani sakon ana yadawa sai nace to wai ina hankali da tunani da Allah ya bambanta Bil-Adama da dabbobi da shi! Wani abin baka bukatar sai an kawo maka aya ko Hadisi ko fatawar magabata zaka san karya ne, yana da kyau mutane su dinga tantance duk wani sako da aka turo musu kafin su yada shi. Akwai mutane kebantattu da nake sanya su a addu'ah sabida kaunarsu da yada Alkhairi a Whatsapp Malam Umar S Zaria da  Ibrahim Nasidi Abu-Ilham​ Mustapha Alfurqan da Ismail Lamido da Mohammed Jungudo​ da sauransu da dama da basa gajiyawa wajen yada Alkhairi, Allah ya saka musu da alheri.

Haka kuma, na laura wasu kan kwaso wasu bayanai a Facebook suyi ta yadawa a Whatsapp ba tare da jingina abin zuwa ga asalin mai shi ba, wanda  wannan tozarta Amana ne, da yawa wasu sukan  dauka haka ba laifi bane, suyi dandatsa ko Plagiarism a social media. Yana da kyau mu kiyaye wa mutane amanarsu, Allah ka sa mu kasance sahun gaba wajen yada Alkhairi tare da kawar da Sharri. Allah ka shiryemu shirin addini ka bamu lafiya da zaman lafiya.

Yasir Ramadan Gwale 
28-02-2015

Sunday, February 22, 2015

Tsakanin Obasanjo Da Jonathan Waye Ba Mabarnaci Ba?

TSAKANIN OBASANJO DA JONATHAN WAYE BA MA'BARNACI BA?

Tsohon Shugaban Kasa ya zama Gwarzo a wajen Mutane da yawa masu saurin manta baya musamman a Arewa. Tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo mugun dan fashi ne kuma dan damfara, ya yiwa Miliyoyin al'ummar Najeriya fashin zabe a 2003 da 2007 da kuma hannunsa akaiwa al'umma fashi da damfara a 2011. Obasajo duk shi ne silar gurguincewar Demokaradiyyar Najeriya shi ya fara ginin tubalin lalacewar al'amura da yawa da suke cigaba da balbalcewa a yanzu.

Obasanjo shi ne yaci dunduniyar Arewa ta hanyar amfani da wasu rubabbun Gwamnoni na lokacinsa ya murgudewa cigaban Arewa kafa. Ya karya Babban Bankin Arewa da duk wani Dan Arewa ke alfahari da shi, sai da ya tabbatar yakai Bankin kasa ta yadda ba zai kara shurawa ba; Sannan Obasanjo ya yi amfani da karnukan farautarsa daga cikin Gwamnonin lokacinsa ya karya gidan Jaridar Arewa na NNN. Obasanjo ya lalata harkar Noma da kiwa a Arewa ya yiwa mutanan Arewa asara mai dumbin yawa da sunan wata cuta H1N1 da ake kira Murar Tsuntsaye, aka kashewa manyan Manoma dabbobi da tsuntsaye da sunan yaki da wannan cuta.

Bugu da kari Obasanjo ya karyar harkar Noma ta hanyar lalata Hadejia/Jama'are River Basin Development Authority. Ya shigo da wata irin ciyawa daga kasashen Turai wadda take tsotse ruwa tare da mayar da gulabe kufai, aka bi garuruwan da wannan kogi ya ratsa aka fesa wannan muguwar ciyawa duk da nufin karya manoma a Arewa ta yadda za ai shekara da shekaru mutanan Arewa basu farfado ba, wannan ya faru akan idan wadan da suka san abin. Ya lalata aikin Tafkin-Chadi yai amfani da sinadaran da suke busar da Tafkin duk domin karya tattalin arzikin Arewa. Obasanjo gawurtaccen Mabarnaci ne da ya yiwa Arewa zalinci na fitar hankali.

Sannan kuma, Obasajo ya shiraya wata kidayar jama'a ta bogi, duk domin gurgunata Arewa, aka i amfani da wannan kidaya ta karya aka rage mana yawan jama'a a Arewa, sannan aka karawa mutanan kudu yawa, Obasanjo yayi amfani da wannan kidaye wajen dankwafe Arewa, wasu jihohi a kudu da basu kai yawan jama'ar Gwale ba aka kambasu aka kara musu lamba duk dan a karyamu a nuna rashin yawanmu ko a kamantamu da mutanan kudu ta fuskar yawa. Bayan a bayyane take cewar yawanmu ya ninka ninkin ba-ninkim, domin a tsakanin mutanan Arewa ne kadai masu mata hudu da 'ya 'ya talatin ko arba'in suke da yawa bila'adadun.

A 2007 Obasanjo ne ya shirya zabe mai cike da kazanta wanda hatta turawa masu sanya Ido a zabe sai da suka yi Allah-wadai da wannan zabe. YarAdua da kansa da Obasanjo ya kawo shi sai da ya bayyanawa duniya cewar lallai zaben da ya kawo shi karagar mulki "kazantaccen zabe ne mai muni" ya kuma yi alkawarin gyara a harkar zabe a Najeriya, har ya kafa kwamatin Mai Shari'ah Uwai. Duk irin wannan fashi da Obasanjo ya yiwa 'Yan Najeriya bai taba yin Nadamarsa ba, bai taba neman gafarar 'yan Najeriya akan wannan mummnan ta'adi da ya tafka ba, bal ma bai taba ganin abinda yayi kuskure bane. Bayan kuwa a Arewa kowa yasan cewa Obasanjo ya zalinci mutane yayi mana fashi da damfara ta zabe.

Haka kurum rana tsaka, Obasanjo ya zama Gwarzo a idanun Mutane Arewa bayan bai taba nadamar dukka irin bala'i da musifa da ya tafkawa mutanan Arewa ba! ba shakka dukkan irin wata dangin barna da sakaci da shakulatun bangaro da Shugaban kasa mai ci Goodluck Jonathan ya tafka Obasanjo ne silar hakan, bai kuma taba shaidawa duniya nadamarsa ba akan haka, dan haka babu yadda Obasanjo zai zama gwarzon rana tsaka.

A ganina da Shugaban kasa Goodluck Jonathan da Obasanjo duk mabarnata ne, maha'inta da suka cuci Al'ummar Naijeriya sukai badakala mai yawan gaske, suka kasa sauke nauyin da ke kansu na shugabanci duk da irin ruwan-kudin da Allah ya yiwa gwamnatocinsa. Kudaden da Obasanjo da Jonathan suka samu sun isa a rushe Naijeriya a sake ginawa. Har yau Obasanjo bai bayyanawa duniya ina yakai kudin wutar Lantarki Dalar Amurka Biliyan Goma Sha-Shida ba, babu wutar kuma babu kudin. Haba, duk wannan almundahana da Obasanjo ya tafka akwai abinda zai aikata na rana tsaka da zai mantar da mu irin kitififin da ya shirya mana. Allah ka cece Najeriya daga hannun duk wasu miyagu azzalumai.

Yasir Ramadan Gwale
22-02-2015

Monday, February 16, 2015

ZABEN 2015: Tsakanin GMB Da GEJ Ido Ba Mudu Ba . . .


ZABEN 2015: TSAKANIN GMB DA GEJ, IDO BA MUDU BA . . .

Da an gudanar da wannan zabe kamar yadda aka tsara a ranar 14 ga wannan wata da ya gabata, da yanzu haka watakila sakamako ya gama fitowa, al'umma ciki da wajen Najeriya sun san inda alkiblar kasarnan ta dosa. Allah bai nufa za'a gabatar a ranar da 'yan Najeriya suka hakkake ita ce ranar zabe ba, amma duk da haka al'umma suka sake mika wuya ga sabuwar ranar da aka tsara dan aiwatar da wannan muhimmin zabe da zai tabbatar da Najeriya a matsayin jim'huriya ta shida.

Shugaban Kasa Dr. Goodluck Jonathan shi ne mutumin da Najeriya bata tab'a samun shugaba kamarsa ba, nayi tsammanin Gwamnatin Mr. Jonathan tafi kowacce Gwamnati a Najeriya kafa tarihi wajen ciyar da Najeriya gaba da kaso mai yawa, kasancewar shi ne mutum kwaya daya tak da kafin ya zama Shugaban kasa sai da ya zama Mataimakin Gwamna, ya zama Gwamna, ya zama Mataimakin Shugaban Kasa, sannan ya zama Shugaban Kasa. A tarihi ba'a taba samun Shugaban Najeriya da ya ratso wannan rintsi ba. Bisa la'akari da irin wadannan matakai da Mista Jonathan ya ratso ya kamata ace yafi kowanne Shugaba da aka taba yi a Najeriya gogewa da sanin makamar aiki, amma sai dai kash!

Tun bayan da ya kama aiki a matsayin cikakken Shugaban kasa a ranar 5 ga watan Yunin 2010, Mr. Jonathan yayi ta yin tufka da warwara a sha'anin tafiyar da gwamnati, Mr. Jonathan ya aikata sakaci mai yawa a Gwamnatinsa ta yadda ya dabaibaye kansa da mutanan da duniya ta shaida cewa marasa gaskiya ne. Bashakka a Shekarun da Mr. Jontahan ya shafe a matsayin Shugaban Najeriya tun daga 2010 har zuwa yau, ya tabbatarwa da 'yan Najeriya gazawarsa ta fannoni da yawa a al'amuran da suka shafi sha'anin tafiyar da Gwamnati.

Mr. Jonathan bai yi sa'ar samun mutane nagari wadan da zasu bashi shawarar tafiyar da Mulki cikin gaskiya da adalci ba, har ya zamo mutumin da za'a dinga buga misali da shi kamar yadda ake kiran sunan Jerry Rolins a Ghana da Sam Nyioma a Namibia da irinsu Julius Nyarere a Tanzaniya. Shugaban kasa yayi bankaura da hauragiya mai yawa, wadda a matsayin kasa irin Najeriya da take da karfin fada aji a duniya kuma take da buwaya a tsakanin kasashen Afurka ace Shugabanta ya kasance haka ba.

Naji matukar takaici lokacin da naji mutum d'an daba irin Julius Malema tsohon shugaban Matasan jam'iyyar ANC a Afrika ta kudu ya kalli Najeriya ya dinga zagin shugabanta! Amma kuma a gefe guda, Shugabanmu na Najeriya da laifinsa a dukkan irin cin-kashi da wasu daga waje sukaiwa Najeriya, domin ya nuna rashin kwarewa da iya tafiyar da mulki. Zaka yi mamaki a ce General Gowon a Shekaru 31-2 ya iya saita Najeriya tare da kawo karshen yakin basasa.

Duk da wannan kasawa da gazawa ta Shugaban kasa da ta bayyana, ba ga 'yan Najeriya kadai ba; har da sauran kasashen duniya, wannan ba dalili bane da zai sanya al'umma su tozarta Shugaban Najeriya ta hanyar jifansa da yi masa ihu ko kona motocinsa a lokacin da yake yawan kamfe. ko kusa wannan ba daidai bane, a matsayinsa na dan Najeriya doka ta bashi damar ya nemi 'yan Najeriya su zabe shi idan sunga dacewar hakan dan yacigaba da shugabanci. 

Abu mafi muhimmanci da zamu yi amfani da shi dan nunawa Shugaban kasa rashin gamsuwarmu da shi shi ne mu kauracewa zabarsa a wannan zabe, amma tozartashi dan kawai muna adawa da ko dan kasancewarsa ba Musulmi ba, wannan ba daidai bane a matsayinsa na Shugaban kasa.

Haka kuma, GMB da yake zaman dan takarar jam'iyyar hamayya, ba shakka duk mai lafiyayyan hankali da yasan me yake, yasan abin nan da Bahaushe ke cewa ido ba mudu ba amma yasan k'ima. Ko shakka babu idan ka hada GMB da GEJ to shakka babu GMB yafi GEJ cancantar ya zama Shugaban Najeriya nesa ba kusa ba, domin  'yan Najeriya kudu da Arewa sun kyautatawa GMB zaton cewa zai yi fiye da abinda babu wani Shugaba da bai yi ba a baya, al'ummar Najeriya sun gamsu da cewa GMB yana da kishin Najeriya matukar kishi dan haka suke masa fatan zai iya fito da Najeriya daga halin ni 'yasu da take ciki.

A duk da haka wasu na tafka babban kuskure cikin tsukakken tunanin da tsukakkiyar fahimtar cewar GMB ne kadai zai iya ceto Najeriya daga halin da take ciki, duk wanda tunaninsa ya kasance irin wannan to ba shakka ya munanawa Allah zato, sannan ya takaice ni'imar Allah. Akwai dumbin mutane da suke da kishin kasa da watakila zasu iya yin abubuwan da ba'a taba zato ba idan an basu dama.

'Yan Siyasa da suke dauke da katin wata jam'iyya ko sun fada ko basu fada ba, suna fatan jam'iyyarsu ta kafa Shugabanci a kowane irin mataki, abinda ake cewa daga sama har kasa. Sauran al'umma da basa dauke da katin kowacce jam'iyya sune ke bakacewa su fitar da mutanan kirki a kowacce jam'iyya suke domin zabarsu. Abu mafi muhimmanci anan shi ne, shin mun yarda cewar SIYASAR DEMOKARADIYYA HALAL CE? Idan har mun yarda da cewar Demokaradiyya Halal ce a Musulunci, kuma Shiga jam'iyyar Siyasa Halal ne, to babu wani dalili da wasu sabida zafin kai zasu kafirta wani dan ya goyi bayan jam'iyyarsa a kowane irin mataki.

A ganina a siyasance idan d'an siyasa yace yana goyan bayan jam'iyyarsa to yana goyan bayan dukkan 'yan takararta ko da kuwa bai furta hakan ba, indai ya d'auki kansa a matsayin halastaccen d'an wannan jam'iyya. Kuma ko da ya goyi bayan wani dan takarar na jam'iyyarsa da ba Musulmi ba, bana zaton yayi hakan da nufin tarayya da shi a cikin abinda ya shafi Imani na Aqidah ta addini illaiyaka batu na siyasa. Domin kuwa siyasa gaba dayanta Maslaha ce, kowanne d'an siyasa yana duba a ina ne maslaharsa da ta mutanansa zata iya biya cikin sauki sai ya shiga.

Misali akan haka, a baya GMB ya fahimci ba lallai ayi masa adalcin da yake so ba, kuma ya fahimci maslaharsa ba zata iya biya a ANPP ba dan haka ya fice ya koma CPC, haka tsohon Gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau da aka haifi APC da shi, da ya fahimci ba za ai masa adalci ba kuma maslaharsa da ta mutanansa ba zasu biya ba a APC dan haka ya fita ya koma PDP, haka Gwamnonin PDP biyar da suka fice, suma sunga cewar Maslaharsu ba zata iya biya a jam'iyyar ba dan haka suka fice suka koma APC! To wannan yake bamu hotan cewa ita siyasar Demokaradiyya gaba dayanta Maslaha ce, inda mutum yaga zai samu maslaha kuma za ai musu adalci shi da mutanansa, nan zasu share wuri su zauna.

Dan haka duk wanda yayi amfani da addini ya halattawa wasu siyasa, sannan kuma ya haramtawa wasu siyasa to wannan babban Azzalumi ne. Bana zaton kirista da yake goyon bayan APC dan yayi tarayya da Musulmi a aqidah ta Musulunci bane ya sanya shi yin jam'iyyar, haka nan shima Musulmi wanda yake yin PDP bana zaton dan ya yarda da Aqida ta kafurci zai bi abinda ya zaba.

A tunani na duk wani Malami da zai yi maganar halaccin a zabi wata jam'iyya shi ne ya dace da addini, to abinda ya kamata ya fara duba halaccinsa shi ne tushe ko ginshiki wato DEMOKARADIYYA, babu yadda wani zai gamsu cewar tsarin Demokaradiyya ya halatta amma kuma wasu jam'iyyu su Haramta ga wasu mutane, wannan kam ko waye ya fadi haka bai yi Adalci ba.

Nakan yi mamaki matuka, idan naga yadda mutane ke mayar da martani a fusace, kaga sabida siyasa Musulmi na yiwa Musulmi mummunar adduah. Wani Allah ya tashi wane tare da wane, ai na zata a lahira za aiwa kowannemu Hisabi ne gwargwadon aikin da ya aikata ko da kuwa kusa da wa ya tashi, Manzon Allah SAW ya gaya mana cewar babu wani daga cikinmu da ayyukansa zasu iya tsallakar da shi face Rahamar Allah. Ba Shakka Allah Mai Gamammiyar Rahama ne kuma mai jin kai, Rahamar Allah bata takaitu ga wasu kebantattun mutane ba, rahamar Allah ta yalwaci kowa. Ya Allah ka lullubemu da rahamarka, ka siturtamu, ka yafe mana kura kuranmu.

Fatana shi ne Allah ya dubemu ya dubi halin da muke ciki na kaskanci da wulakancci ta yadda a kasarmu wasu suka zama 'yan gudun hijira. Allah ya fitar da mu daga cikin wannan hali, Allah ka azurtamu da samun Shugabanni na gari Adalai wadan da zasu tausaya mana su ji kanmu. Allah kasa ayi wannan zabe lafiya a gama lafiya.

Yasir Ramadan Gwale
16-02-2015

Monday, February 9, 2015

Adalcin Da Buhari Ya Yiwa Mr Jonathan


ADALCIN DA BUHARI YA YIWA MR JONATHAN

A cikin tattaunawa da aka yi da dan takarar Shugaban kasa karkashin jam'iyyar Adawa ta APC. An tambayi Muhammadu Buhari​ ko yana zargin Gwamnatin Najeriya karkashin Mr. Jonathan da daurewa Boko Haram Gindi. GMB ya bada amsa da cewar, baya zargin Gwamnatin Najeriya da hannu wajen balahirar Boko Haram domin babu wasu shaidu da suka tabbatar masa da hannun gwamnati a ciki, yace sai dai yana zargin gwamnati da gazawa da sakaci na wajibin da yake kanta. GMB ya kara da cewar da ana yin abinda ya kamata da ba'a kawo har yanzu wannan rikici na cigaba da wanzuwa ba.

Tambayar da na yiwa kaina ita ce, shin yanzu idan da GMB ne Shugaban kasa wannan balahira ke faruwa karkashn gwamnatinsa, idan AlJAZEERA suka tambayi Femi Fani-Kayode ko Dr. Doyin Okupe cewar shin suna zargin da Hannun Gwamnatin Muhammadu Buhari​ ko babu! Watakila Amsar da zasu bayar ta bada mamaki.

Adalci shi ne sanya komai a Muhallinsa. Addinin Musulunci ya hori Musulmi da yin Adalci ko da kuwa akan abokan gabarsu ne. Shi yasa ma Bahaushe ke cewa gaskiya ko ta karece a bashi kayarsa. Da Adalci ne ake samun dorewar rayuwa cikin aminci. Rashin Adalci da bashi muhimmanci shi yakai Najeriya halin da take ciki. Mutanan kudu basa yiwa Na Arewa Adalci, Na Arewa basa yiwa na udu Adalci kirista basa yiwa Musulmi Adalci. Kowa kokarin kore kasawa da gazawa yake daga kansa ya maida ita zuwa ga abokin zaman tarayya.

Bamu ce a dauki hakkin wani a bamu ba, ko abinda yake hakkin wani ne a hanashi. Kullum kiranmu shi ne ayi Adalci a zaman tarayya, a baiwa kowanne mai hakki hakkinsa. Mai gaskiya a bashi gaskiyarsa ko da ba'a sansa, Mara gaskiya a bashi rashin gaskiyarsa sannan ayi masa nasiha.

Ina da yakinin Adalci zai zaunar da al'ummar Musulmi da Kirista Bahaushe da bayerabe da Inyamuri lafiya, cikin aminci ba tare da fargabar yankan baya, kyashi, hassada, kiyayya, gaba ko danne hakki ba. Idan kowa ya samu Nutsuwar cewar za'ayi masa adalci a zaman tarayya ba Shakka za'a zauna lafiya. 

Amma a cikin irin halin da muke ciki, an raba tsakanin al'ummar Najeriya, ta yadda kowa yana jin nasa ne kadai zai iya yi masa adalci, indai ba nasa bane, to ba shida cikakkiyar nutsuwar cewa za'a biya masa bukatunsa na wajibi. Fatana Allah ya azurta wannan kasa tamu da Shugabanni masu Adalci da tsoron Allah. 

YASIR RAMADAN GWALE​
09-02-2015

Sunday, February 8, 2015

ZABEN 2015: Ido Ba Mudu Ba . . .


NAJERIYA DA ZABEN 2015: IDO BA MUDU BA . . .

Mutane da yawa na ruduwa da yawan Jama'a a wajen kamfe su dauka wanda yafi tara Jama'a shi zai ci zabe. Amma ba nan gizo yake sakar ba a zance na gaskiya, domin a zaben 2011 a yankin Arewa Maso Yamma da yafi kowane yanki yawan masu dauke da katin zabe, akwai sama da mutum miliyan tara da basu yi zaben Shugaban kasa ba, kuma sun karbi katin zabe. Sannan wasu dubbai sunyi zaben amma sun lalata kuri'unsu da su da wanda bai yi zabe ba duk daya. Tambayar ita ce shin ina wadannan mutane suka shiga? Ba irinsu bane suke zuwa su cika wajen taro a lokacin kamfe, amma idan zabe yazo su lafke a gida ba? Wane shiri muke da shi wajen ganin duk wanda yake da katin zabe yayi zabe? 

Muna da yakinin wadancan Miliyan taran ba zasu kuma kwantawa suki fitowa zabe ba? Dubban mutanan da suke lalata kuri'u a lokacin zabe wane shiri muke  da shi wajen ganin cewa a bana basuyi asarar zabe ba? Jihar Katsina a zaben da ya wuce itace tafi kowacce jiha yawan kuri'un da aka lalata (invalid) Wadannan dama wasu na daga cikin batutuwan da ya kamata mu kalla kafin zabe. Misali a zaben da ya gabata sai da na tabbatar Zainab tayi zabe sannan na tura mata katin waya nace tai ta bugawa kawayanta waya tana gaya musu muhimmancin su fito suyi zabe. To bana ma haka zanyi.

Yasir Ramadan Gwale 
08-02-2015

ZABEN 2015: Duniya Ta Sanyawa Najeriya Ido


ZABEN 2015: DUNIYA TA SAWA NAJERIYA IDO

A safiyar yau Sakataren harkokin wajen Amerika Sen. John Kerry​ ya fitar da wata sanarwa da take nuna rashin amincewar Washington akan dage babban zaben kasa da hukumar zabe karkashin jagorancin Attahiru Jega tayi. Sanarwar tayi Allah-wadai da wannan yanayi da ya bayar da damar tura wannan zabe zuwa wani lokaci na gaba. Da farko dai, muna Allah-wadai da tsoma bakin Amerika a cikin harkokin cikin gida da suka shafi Najeriya. Najeriya kasa mai 'yanci da bata karkashin mulkin kowacce kasa a duniya. Bai kamata Amerika ta dinga yin katsa-landan a harkokin cikin gidan Najeriya da basu shafeta ba.

Dan gane da batun dage zabe kuwa, ba shakka ina daya daga cikin mutanan da suke ta fatan ganin wannan zaben yazo ya wuce dan mu san wace irin makoma ke garemu, hakika wannan zabe yana cikin zukatan duk wani dan najeriya a ko ina yake, wannan ta sanya yanzu 'yan najeriya ba suda wata hira da ta wuce batun zabe. Cikin kaddarawarsa, Subhanahu Wata'ala, rade-radin da ya kunno kai cewa za'a dage wannan zabe daga ainihin lokacin da aka tsara zuwa wani lokacin na daban ya tabbata.

Shugaban hukumar zabe ya bayar da sanarwar dage Zabe zuwa wani sabon lokaci a watan maris mai zuwa. Ba shakka, kuma nayi Imani da cewa Attahiru Jega mutumin kirki ne da ba za'a hada kai da shi a cuci al'ummah ba, na kyautata masa wannan zaton. Dan haka wannan dage zabe ba zai zama wani abin tashin hankali ko fusata ba, tunda Jega ya tabbatarwa da duniya cewar kamar yadda kundin tsarin Mulki ya tanada 29 ga watan mayu dole a samu sauyin Gwamnati.

Wannan sauyi da yazo mana afujajan mun karbeshi cikin kaddararawar Allah. Manzon Allah yace, Madallah da al'amarin mumini, idan abinda yake so ya samu sai yayiwa Allah godiya, tare da haka sai Allah ya sanyawa abin alkhairi a gareshi, idan kuma akasinsa aka samu sai ya maida komai zuwa ga Allah yayi hakuri, sai Allah ya sanya masa alkhairi kuma ya bashi ladan hakuri.

Muna fatan Allah ya sa wannan abin da ya faru ya kasance alkhairi ne, kuma adduaata ita ce, Allah yasa ayi zabe lafiya a gama lafiya. Domin yanzu haka duniya ta sanyawa Najeriya ido wajen ganin anyi zabe mai tsabta. Jega kuma muna yi masa adduar fatan alheri Allah ya bashi ikon gudanar da wannan zabe cikin Nasara, Allah kayi masa jagoranci wajen tabbatar da gaskiya da aiki da ita a wannan zaben.

YASIR RAMADAN GWALE​ 
08-02-2015