Monday, December 28, 2015

Hattara Jama'ah



HATTARA JAMA'A MUSAMMAN  MASU ABABEN HAWA!

Dazu dan uwa Tijjani Ahmad yake bamu labarin wata fitina da ta kunno kai a cikin wasu unguwannin cikin Birnin Kano. An wayi gari wasu mutane marasa tsoron Allah masu fama da cutar bakar Hassada da mugunta da Kyashi da munanawa Allah zato suna bi unguwanni suna Bankawa motocin mutane wuta babu gaira babu dalili a lokacin da Sahu ya dauke, abin ya faru a unguwar Gwammaja da Tal'udu da kuma Titin Aminu Kano. Dan haka, jama’a musamman wadan da suke da motoci kuma ba suda garejin aje mota suke barin su a waje suna kwana, ya zama dole a sanya ido. 

Mutanen da suke aje motocin su a makarantu ko wani filin unguwa da su lura kuma su sanya ido sosai, a samu masu gadi san kare dukiya. Ba shakka duk wanda zai sanya motar mutane wuta ta kone kurmus dan kawai Hassada da Kyashi to wannan ya kai matukar mutum mara tsoron Allah. Ana bi ana kashe mutane babu ji babu gani, ba tare da wani hakki ba. Yanzu kuma abin ya koma kan dukiyoyin mutane lallai lokaci yayi da mutane zasu tashi dan baiwa unguwannin su da dukiyoyinsu kariya. Ya Allah ka kare mu da karuwar ka, masu wannan mugun nufi Allah ka tona asirinsu. Ya Allah ka tsare mu ka tsare mana dukiyoyinmu. 

Yasir Ramadan Gwale 
28-12-2015

Thursday, December 17, 2015

Taya Murna Ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari Ya Cika Shekaru 73


Abokina Attahiru Muhammad Marnona a lokacin da na taya Malam Nuhu Ribadu murna ya cika Shekaru 55 yayi ta min Wa'azi cewa Ahlussunnah basa yin Happy birthday. Yau kuma kwatsam sai na ci karo da sakon sa a Whatsapp yana tunasar da ni cewar a yau ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya cika Shekaru 73 a duniya, dan haka yana fatan yaga na taya Shugaban kasa murna indai ba kiyayya nake ba. Nai musrmushi 😊. Albashirin Marnona? Ina fatan zai ce Dabino, a madadin ni kaina da dukkan ahalin mu muna yiwa Shugaban kasa fatan alheri a cikin wadannan Shekaru 73 da yayi a duniya, ina fatan kuma wannan ya zama tuni a gare shi cewar kaso mai yawa na daga kwanakinsa a duniya sun wuce, ba ko Shakka abin da ya rage masa ba mai yawa bane, Ina rokon Allah ya bashi ikon Aikata alkhairi mai yawa a kwanakin da suka rage masa. Har yanzu mutanan Nigeria suna kyautata zato a gare ka Shugaban kasa, muna fatan Allah ya baka lokacin da zaka cika dukkan alkawarin da ka dauka, ina maka fatan alheri da fatan duk alkawarin da kayi ya zama hujja a wajenka ba hujja a kanka ba.

Haka kuma, ina amfani da wannan dama wajen yin kira ga Shugaban kasa, akan ya gargadi kasashen duniya masu yiwa Nigeria shisshigi a cikin abinda ya shafe mu na cikin gida. Yana da kyau Shugaban kasa ya nuna irin wadannan masu katsalandan cewar Nigeria kasa ce mai cikakken iko da take cin gashin kanta, bama karkashin ikon ko wace kasa, duk abin da ya shafe mu na cikin gida bai kamata wata kasa tai mana shisshigi a ciki ba, matukar bamu nemi taimako ko agaji ba. Allah ya taimaki kasarmu Nigeria ya sada mu da dukkan alkhairai wadan da zasu amfane mu. Masu yi mana katsalandan kuma muna daga musu dan yatsan gargadin karshe. ☝☝☝☝

Yasir Ramadan Gwale 
17-12-2015 

SHIAH: Nasiha Daga Bakin Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi Na Biyu


SHIAH: NASIHA DAGA BAKIN MAI MARTABA SARKIN KANO MUHAMMADU SUNUSI NA BIYU

A dangane da abinda ya faru a Zaria, Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi Na Biyu yayi Nasiha mai ratsa zukata akan wannan batu. Ya kuma yi kira mai matukar muhimmanci.  Na san da yawan mutanan Kano sun saurara jiya a Freedom Radio. Tun lokacin da akai wannan batarna'ka tsakanin yaran Sayyid Zakzaky da Sojoji na zabi kame baki na kan wannan lamari, domin abu ne da nake gani tsakanin sojoji da masu kunnen k'ashi. Cikin ikon Allah, daya daga cikin abinda yake damuna a Rai sosai game da Shiah da Zakzaky, mai martaba Sarkin Kano ya wanke mun shi.

Ta bakin Sarkin Kano,  Kasar Najeriya an gina Musulunci ne a bisa doron Ahlussunnah Wal Jama'ah. Dan haka duk wanda ya zo da batun darikun sufaye da sauran su, to daga baya ya zo da shi. Haka kuma, kamar yadda Sarkin ya fada, tun farko anyi sakaci, domin, an san Da'awar Zakzaky karya ce ba Musulunci bane, akai shiru aka barshi ya shiga kauyuka ya tara jahilai a matsayin mabiya, har yake neman zamarwa al'umma barazana shi da mabiyansa na kin mutunta dan Adam da kuma dokokinsa hukuma. 

Tabbas akwai laifin Sarakuna wajen yaduwar Shiah a Najeriya, domin sun san tushen Musulunci babu aqidar Zagin sahabbai ko Matan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam, amma sabida ana ganin Ahlussunnah ne ke adawa da abin da kuma kausasa harshe akan koyarwar Shiah, sai ake ganin kamar matsala ce da ta shafi Ahlusunnah ko 'yan Izala Sarakuna sukai kurum Zakzaky na halaka musu al'umma, alhali an san karya yake yi ba Musulunci yake ba.

Alhamdulillah, ya zuwa yanzu Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi ya farga, kuma ya ankarar da 'yan uwansa Sarakuna da Sauran al'umma cewar,  Musulunci a Najeriya an gina shi ne akan koyarwar Ahlussunnah Wal Jama'ah, dan haka an gina mu akan mutunta dangi da iyalan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam da suka hada da Ahlulbaity da Sahabbai da Matansa Sallallahu Alaihi Wa Sallam. Allah ya sakawa Mai Martaba sarki da wannan nasiha mai matukar muhimmanci. 

Kuma wani abin Albashir ga al'ummar Musulmi a Najeriya, shi ne, Wannan Waki'a ta Zaria da ta auku tsakanin Soji da Yaran Zakzaky, tayi Sanadiyar Kawo karshen yadawar  Shiah a Najeriya In sha Allah. Domin filin Husainiya da ake yin kafurci da zagin Sahabbai a cikinsa, asalin sa filin Deport ne na NA wato Chidit Barrack, shi ne Sardauna Sokoto Firimiyan Jihar Arewa Sir Ahamadu Bello ya nemi Turawa su bashi filin dan yana gina filin Polo, kuma a yarjejeniyar da akai da Soji wannan fili ba na sayarwa bane, amma aka samu wata Gwamnati a Kaduna ta maida filin Mallakarta kuma ta baiwa Zakzaky. To Alhamdulillah yanzu haka Buratai ya ce filin Husainiya ya dawo gayaunar sojoji.

Bayan haka kuma, gidan Zakzaky da ke Gyallesu asalinsa shima Gwamnatin Abdussalam Abubakar ce ta gina masa, ta bashi kyauta a matsayin Diyyar abinda Marigayi Gen. Sani Abacha yayi masa, to al'umma dake zaune a Gyallesu sun rubuta dubban sakonnin koke koke akan irin cuzguna musu da Zakzaky da yaransa suke yi, dan haka shima wannan gida Zakzaky ya karya dokar bashi gidan, dan haka sojoji sun kwace shi. A yanzu dai zamu iya cewa Buratai yayi Jana'izar Shiah a duk fadin Najeriya.

Saura da me? Ya kamata al'umma su sani, kuma su fadaka, babu wata akida ta zagin Sahabbai da Iyalan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam a cikin addinin Musulunci. Dan haka kamar yadda mai martaba Sarkin Kano yayi kira dole Sarakuna su tashi tsaye wajen Yaki da duk wanda ya zo dan gurbata addinin Musulunci da aka gina shi akan koyarwar Ahlussunnah Wal Jama'ah a wannan kasa tamu mai Albarka. Ya Allah kasa  wannan shi ne karshen Shiah a Nijeriya. Allah ka taimaki Musulunci da Musulmi ka kaskantar  da Shiah da duk masu goya musu baya na saurari da na b'oye munafukai masu takiyya. 

Yasir Ramadan Gwale 
17-12-2015

Saturday, December 5, 2015

Godiya Da Fatan Alheri Ga Sojan Nigeria


GODIYA DA FATAN ALHERI GA SOJAN NAJERIYA

Daga Ranar Juma'a 4 ga watan Disamba zuwa 10 ga wata,  lokaci ne da Rundunar Sojan Najeriya ta ware a matsayin makon da za a godewa sojojin Nigeria dake fagen daga #ThankASoldier. A dan haka, a wannan rana ta Juma'a kuma a wannan sa'a ta karshe ta wannan rana muke tawassuli da sunayan Allah tsarkaka madaukaka, Ya Allah ka Jikan sojojin mu musamman wadan da suka rasu a fagen daga domin kare kasarmu daga farmakin 'yan ta'adda masu tada zaune tsaye, Allah ya jikan su ya gafarta musu, masu raunuka daga cikinsu Allah ya basu lafiya.

Anan nake amfani da wannan dama, nayi kira ga sauran 'yan Najeriya da su cigaba da yiwa Najeriya da sojojin mu adduar fatan alheri da samun nasara a fagen daga. Allah ya tabbatar mana da samun zaman lafiya dawwamamme mai dorewa, Allah ya kade mana dukkan fita. Haka kuma, ina kira ga mai girma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya daure ya kaiwa sojojin mu dake fagen daga ziyara, a musamman jihar Borno, ba shakka wannan zai kara musu kwarin guiwa da karsashin yin aiki tare da nuna kishin kasa, Bugu da kari, hakan zai basu kwarin guiwar cewar ana gamsuwa da aikinsu.

Kamar yadda Shugaban kasa ya ambata cewar zai shige gaba domin fafarar 'yan ta'addar da suka hana wannan kasa zaman lafiya, muna rokon Shugaban kasa da ya daure ya kai musu ziyara dan yaba musu. Sannan kuma, muna fatan Gwamnati zata inganta jin dadi da walwalarsu tare da biyansu dukkan hakkokinsu akan kari, wadan da suka yi Shahada kuma muna fatan Gwamnati ta dinga biyan iyalansu akan lokaci. ALLAH ya taimaki Sojan Najeriya ya basu kwarin guiwa. Allah ya bamu Lafiya da zaman lafiya. #ThankASoldier 

Yasir Ramadan Gwale 
05-012-2015

Jaafar Jaafar Ne Ya Tunzura Bala Ibn Na'Allah


JAAFAR JAAFAR NE YA TUNZURA IBN NA' ALLAH

Sen. Bala Ibn Na'Allah ya gabatar da wani kuduri gaban majalisar Dattawa da ya samu karatu na daya domin yin doka akan takaita ko iyakance abinda masu Kwarmato a Social media irinsu Jaafar Jaafar zasu yi, wanda yanzu batun ke cigaba da jan doguwar muhawara. Ina ganin wannan kuduri da Sen. Na'Allah ya gabatar baya rasa Nasaba da yamadidin da Jaafar ya fara yi akan shigar (kasaita)da Sanatan yayi lokacin wata liyafa da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiryawa Shugabannin Majalisar Dattawa da su Jaafar suka ga rashin dacewa a tare da tsukiyar da Sanata Na'Allah yayi, wanda hakan yasa Jaridu da dama musamman na Internet suka cigaba da yayata Bala Ibn Na'Allah da kuma shigar tasa.

Monday, November 30, 2015

Harin Bom Din Da Aka Kaiwa 'Yan Shiah Masu Tattaki


HARIN BOM DIN DA AKA KAIWA 'YAN SHIAH MASU TATTAKI 

Da yawan mutane wanda suke cewa su ba Shiah bane, kuma su ba Wahabiya ko 'yan Izala bane, suka cika facebook da surutu wai an kaiwa 'Yan Shiah hari, amma 'yan Izala sunyi shiru sun ki Jajantawa. Abin ya bani mamaki kwarai, idan banda san Jan magana ina ruwanka, da zaka sa dole sai wani yayi magana akan abinda bai shafe shi ba? Hakkin Gwamnati ne kula tare da tsare rayuka da dukiyoyin al'ummar da ta ke shugabanta,  da ya kamata masu wancan zargi su fara yiwa Gwamnati magana akan me yasa bata jajanta musu ba a matsayin su na 'yan Najeriya da alhakin su yake kanta.

Ai sanin kowa ne, kuma a bayyane yake a cikin Karantarwa Malaman Sunnah anyi dukkan dangi Allah wadai da tashin hankali da kisan al'ummar da basu san hawa ba basu san sauka ba, wannan ce ta sanya sam baya daga cikin manufofin Ahlussunnah fita zanga zanga domin baiwa rayuwa kariya. Malamanmu sun cika duniya da karatuttuka da bayanai da Jan hankali akan masu kisan kai babu ji babu gani, kowane malamin Sunnah indai yana da'awa sai ka ji ya fadakar akan illa da nauyin hukuncin kisan al'ummar da ba su da laifi ba.

Amma sabida abin san Jan magana, sai wani dan taratsi, ya zakalkale wai shi 'activist' ko 'liberal' yana fadin har yanzu banji 'yan Sunnah sun Jajantawa 'yan Shiah ba. Kuma fa karya yake, sau nawa Malaman Sunnah suke zuwa asibiti domin Jajantawa wanda harin Bom ya shafa dan kawai nuna tausayawa da jin kai, amma ba hakkin su bane sai sunyi hakan, wasu lokutan ma har tallafi suke bayar wa. Kuma akan wannan hari Shugaban Majalisar malamai na kungiyar Izala ta kasa Sheikh Dr. Ibrahim Jalo Jalingo ya fitar da sanarwar ja je ga wanda abin ya shafa, ya nuna musu jin k'ai irin na DanAdamtaka, amma duk wannan bai wadatar ba. Haka kuma, ni tunda nake ban taba ji ko ganin inda El Zakzaky ya Jajantawa al'ummar da harin Bom ya shafa ba, balle kuma duba su, sai akan TATTAKIN da ko a shi'ah ma baida Asali, wai akansa ne mutane ke da bakin magana. 

Kuma idan akwai wanda za a zarga a wannan lamari bai wuce Zakzaky ba, domin duk sanda zasu yi taro sai yace za a kawo musu hari, amma duk da haka ya kafe ya kirawo mutane su fito, ai da yana da tausayi da jin k'ai, idan ya samu rahotannin da yace yana samu na kai musu hari, da kamata yayi ya dinga tausayawa mata da yara, a dinga dauke musu zuwa a duk lokacin da yake jin za a iya kai musu farmaki, amma a haka sabida zalinci zai kirasu, mata da d'anyan goyo wasu da katon ciki, ga yara kanana suna ja a hannu, amma haka zai tilasta musu fitowa. Tsakanin mu da shi waye mugu mara tausayi? 

A baya har aka biyo Malaminmu Dr. Ahmad Gumi aka sa masa Bom Allah ya tsare shi, amma bamu 'yan Shiah ko Zakzaky dayansu ya jajanta masa ba, haka aka je har masallacin 'yan taya a Jos wajen karatun Malam Sani Yahaya Jingir aka jefa masa Bom, tare da bude wuta akan bayin Allah dake halarce a wajen karatun, bamu ji Zakzaky ko wani dan Shiah ya jajanta masa ba, sannan kuma ka zarge mu wai dan me bamu jajanta musu ba? Me kake so kace? Idan kace Ahlussunnah ne suke yi, sai muce ka dai fake ne kana so ka soki Musulunci ne, saboda su masu yin wancan d'anyan aikin, Domin kuwa Ayoyi da hadisai suke jawowa suce su ne dalilinsu akan ta'addancin da suke wa al'umma, kenan kana son ka soki ayoyi da Hadisan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam cewa su ne suke kunshe da waccan mugunyar koyarwar? 

Haka kuma, wani abu da zai sake barrantar da Ahlussunnah daga Tafarkin 'yan ta'adda, shi ne babu wani cikinsu da ke cikin Iftila'i da yake kiran YA MUHAMMAD SAW a matsayin maceci a cikin irin wancan hali, sai dai kaji suna kiran YA HUSSEIN suna neman cetonsa.  Dan haka, ko dan gaba, ba alhakin mu ba ne Jajantawa duk wanda harin Bom ya shafa? Wannan hakkin hukumomi ne, su ya kamata ka fara yiwa zargi ba wanda kake gaba da su ko kinsu ba. Baya daga cikin manufofin Ahlussunnah zubar da jini, ko waye yayi haka, ba koyarwar Sunnah bace, kuma ya sabawa Karantarwa sunnah ko da ya jingina kansa da Sunnah. Allah ya bamu lafiya da zaman lafiya.

Yasir Ramadan Gwale 
30-11-2015

Sunday, November 29, 2015

Zancen Zuci . . . 2015


ZANCEN ZUCI . . . 2015

BEFORE:

* Ai yana hawa komai zai canza . . .

* Shi kad'ai ne zai iya Gyara kasarnan!

* Shi ne kad'ai mai gaskiya!

* Shi ne mutumin da ya san maganin matsalolin kasarnan.

* Idan ba shi ba waye zai iya gyara Nijeriya?

* Daga ranar da aka rantsar da shi Nijeriya zata hau saiti.

* . . . Ai yana hawa duk matsaloli sun kare.

* Matsalar Boko Haram ta zo karshe, yana hawa.

* 'yan matan Chibok, ai kamar an sako su, an gama...

* Kayan abinci da na masarufi duk zasu yi arha...

* Duk barayin kasar nan sai ya kamo su...

* Su Ngozi da su Diezani sai sun dawo da abinda suka sata!

* Man fetur zai yi arha, yana hawa zai dawo N40.

* Zai daidaita farashin Nera da Dala.

* Ku dai kawai ku zabi canji.

* (waka) Sai Baba Buhari . . . Sai mun yiwa . . . Zigidir

AFTER:

* Bari kuga ya fara nad'e nad'e.

* Yanzu wad'annan Ministocin har sai an b'ata wannan lokacin dan zabosu, kayya!?

* Haba! Nijeriyar da aka rusa a shekaru 16... sai adduah

* . . . ta yiwa Nijeriya illa ba karama ba!

* A dai yi hakuri, komai a sannu ake binsa.

* Baba ka cika tafiyar hawainiya (Baba Go-Slow).

* Ai fa sai munyi hakuri gyaran Nijeriya sai a hankali.

* ... Wallai mutane sun cika gajen hakuri!

* Daga hawansa har mutane sun fara korafi?

*Bam nan bam can... anya canji ko sanji?

* Watansa shida fa, Haba!

* Ai dan ba shi yayi bajat din bane.

* Ku jira zuwa Janware ku gani idan anyi bajat.

NOW:

* Wannan wane irin Canji ne?

* Babu Manfetur gashi yayi tsada ga masifar layi.

* (waka) Baba Buhari yaci zabe, Abinci yayi tsada...

* Wai Gwamnanoni ba zasu iya biyan albashi ba?

* An kai hari kasuwar Farm Centre a Kano, Kaiyya!

* Baba ya cika yawo fa...

* Wai Iran zashi?

* Sarkin yawo yau kuma an tafi Malta da Faransa.

* Har fa yanzu Bamabami basu dena tashi ba fa!

* Anya kuwa Buharin nan...?

* A ce komai yayi tsada haka?

* Tab! Farashin Dalar Amurka fa ya kai 242.

* Rayuwa fa tayiwa masu karamin karfi tsanani...!

*Bla bla bla

Wad'nnan su ne wasu daga cikin irin kalaman da naji mutane da yawa na fad'a,  kafin da bayan zab'e da kuma yanzu. Har ya zuwa yanzu mutane na cigaba da bayyana ra'ayinsu akan salon tafiyar Gwamnatin Baba Buhari.

Yasir Ramadan Gwale
29-11-2015

Domin Magance Matsalolin Tsaro Gwamnonin Arewa Su Yi Koyi Da Jihar Gombe


DOMIN MAGANCE MATSALOLIN TSARO GWAMNONIN AREWA SU YI KOYI DA JIHAR GOMBE 

Jihar Gombe na daga cikin jihohin da suka sha fama da matsalolin tsaro, kama daga na tashin bama ba ai musamman a tashoshi mota da kasuwanni da kuma hare hare kuna bakin wake. Gwamnatin Gombe karkashin jagorancin Gwamna Ibrahim Hassan Dankwambo, ta yi himmatu wajen ganin ta shawo kan tare da kawo karshen matsalolin tsaro a jihar. Bayan tattaunawa da kuma yin Nazari mai zurfi na bin hanyoyin da za a shawo kan matsalolin tsaron a jihar. Gwamnatin ta yi wani tsari na dauko hanyar mutanan da ake kira Civilian JTF da suke Maiduguri domin taimaka musu a sha'anin tsaro.




 A dan haka ne Gwamnatin Gombe, tayi musu tsari na kula da walwalarsu da basu alawus mai kauri domin wannan aiki. Gwamnatin ta zabe mutane masu Amana, da fatan ganin zaman lafiya ya dawwama a Najeriya ta zuba su a cikin gari a matsayin masu talla ko masu goge takalma, amma suna lura da motsin kowa dan haka da zarar sunga mutumin Borno ko wani Kanuri da suke da shakka akansa zasu cunawa Jami'an tsaro, haka kuma, suna nan a unguwannin da yawa suna yawo a matsayin masu talla. Da farko Gwamnati ta so ta basu motoci da babura, suka shaida mata aikin nasu baya bukatar wannan.


A ranar farko da wadannan mutane suka fara aiki a Gombe, sai da suka gano gidaje kusan biyar a cikin garin Gombe da ake kera Bom, kuma sun kama Bamabaman da aka kera sama da guda dari, bayan an cafke mutanan da suke wannan danyan aiki. Wannan tasa, Gwamnati tayi Nazarin irin hadarin aikin, kuma gashi ba ma'aikata bane na din-din-din da suke da fansho da garatuti, dan haka ne, Gwamna yayi umarnin baiwa wadannan CJTF alawus na Naira dubu goma a kowacce rana, dan haka Gwamna yace duk sati za'a dinga biyansu wannan alawus.

Cikin taimakon Allah, tunda Gwamnatin Gombe tayi wannan tsari har yau Bom bai kuma tashi a Gombe ba. Ba shakka wani tsari abin yabawa ne, duk da cewa rayuwa da mutuwa duk a hannun Allah suke, amma yana daga cikin wajibin hukumomi tsare jini da dukiyar al'umma. Kuma wannan tsari yana da kyau sauran Gwamnatocin Arewa su kwaikwaya, domin tsare rayuka da dukiyar al'umma. Girma da daraja ta Ran dan Adam tafi dukkan abinda za a baiwa mutanan a matsayin alawus. Dan haka, nake kara jinjinawa Gwamnatin Gombe karkashin Gwamna Dankwambo akan wannan hobbasa da tayi domin kula da tsaron rayukan al'umma. Anan nake kira da Babbar murya ga sauran Gwamnatocin jihohin Arewa musamman wadan da suke fama da wannan matsala ta tsaro da su yi koyi da gwamnatin jihar Gombe. 

Domin ko da Gwamnatin tarayya tayi nasarar fatattakarsu daga dajin Sambisa, to wannan ba shi ne yake nuna kawo karshen 'yan ta'adda masu tayar da Bamabamai ba, tilas ayyukan tsaro karkashin jihohi ya cigaba domin amintar da al'umma a gidajensu da masallatai da guraren kasuwancinsu. Haka nan sauran Jami'an tsaro masu kaki, tilas a kula da walwalarsu da basu hakkokinsu akan kari domin samun karsashi da kuzarin yin aiki dan kula da ayyukansu na wajibi da kuma basu kwarin guiwa ta hanyar ziyarar su da karfafa musu guiwa. Allah ya tabbatar mana da zaman lafiya mai dorewa a jihohinmu da kasarmu baki daya. 

Yasir Ramadan Gwale
28-11-2015

Wednesday, November 25, 2015

Magajin Garin Kano Tsohon Mukaddashin Firaminista Ya Kwanta Dama


MAGAJIN GARIN KANO MALAM INUWA WADA YA KWANTA DAMA 

Tsohon Minista, tshon Dan takarar Shugaban kasa, tsohon dan siyasar Jamhuriya ta farko da ta biyu da ta uku kuma Magajin Garin Kano Malam Inuwa Wada ya kwanta dama. Daya ne daga cikin ministocin da suka rage tun Jamhuriyar farko a Nigeria, Malam Inuwa  Wada (Magajin Garin Kano) ya riga mu gidan gaskiya a yau dinnan. Ya rasu yana da shekaru 103 a mafi rinjayen zance. Marigayi Magajin Garin Kano, shi ne mutum na farko da ya fara assasa siyasar Jam'iyya a Arewacin Najeriya. Tun cikin shekarunsa na kuruciya Magajin Gari ya kafa Skawut  (Boy scout) a Arewacin Najeriya baki daya, kafin daga bisani ya zama Babban Jam'in Skawut na yankin Arewa baki daya. 

Magajin Garin Kano da a ne daga cikin mambobin majalisar kasa ta farko kuma tsohon Ministan ayyuka da ma'aikatar sha'anin tsaro. Yana daga cikin kalilan din mutanan da sukai tasiri kuma masu hazaka  a siyasar Jamhuriya ta farko da ta biyu. Ya taba tsayawa takarar shugabancin Najeriya a Jamhuriya ta uku. Ya yi aiki da gaskiya da nuna jarumataka da kwazo sosai a dukkan mukaman da ya rike.

Magajin Garin Kano Malam Inuwa Wada ya taba rike ragamar Najeriya baki daya a lokacin da Marigayi Sir Abubakar Tafawa Balewa ya bashi rikon ragamar,  dan ya zama mukaddashin Prime Minister a lokacin Balewa yayi wasu tafiye tafiye. Yana daga cikin mutanan da ska tsallake juyin mulkin 1966 da yayi sanadiyar rasuwar Sir Abubakar Tafawa Balewa a Lagos da Sir Ahamadu Bello Sardaunan Sokoto Firimiyan Jihar Arewa a Kaduna, ya tsallake 30 jiya da baya lokacin da aka kai harin yana kasar Geneva dan duba lafiyar idonsa.

Marigayi Magajin Garin Kano Malam Inuwa Wada yana da dangantaka ta jini da tsohon Shugaban kasa Marigayi Murtala Mohammed, shi ne mutumin da ya saka shi a makaranta kuma ya rabba shi har zuwa shigarsa aikin sojan da yayi silar zamansa Shugaban Najeriya. Ance Magajin Garin Kano MalamInuwa Wada duk da tsufa da yawan shekaru Sallar Jam'i bata cika wuce shi ba. Allah ya jikansa ya gafarta masa ya yafe masa kurakuransa. 

Yasir Ramadan Gwale 
25-11-2015


Tuesday, November 24, 2015

Mutuwa Daya Ce Idan An Tafi Babu Dawowa


MUTUWA DAYA CE IDAN AN TAFI BABU DAWOWA

Sau da yawa wasu mutane kan rud'a kansu, ta hanyar gaggawar bayar da labarin da hankali ba zai kama ba. Ga duk mutumin da yake da lafiyayyane hankali, ai ba yadda za a tabbatar da mutum ya mutu, sannan wani Wustaz yace wai zai masa addu'ah ya tashi, kuma wasu su yarda, har ana gaggawar yadawa cewar wane bai mutu ba. Hankali ba zai kama wannan ba, banga dalilin da mutane zasu dinga gaggawar yada irin wannan magana da ba gaskiya ba. Da ana Mutuwa a dawo ko a yiwa Gawa addu'ah ta tashi, da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam har yanzu yana raye. Wanda duk ya mutu kwanan sa ya kare, kuma ya tafi kenan.

Audu dai ya mutu, kuma an binne shi. Ya rage namu, shi kam zai riski abinda ya aikata, muna masa fatan Allah ya yafe masa. Dan haka koda yaushe mutuwa take zama wa'azi ga wanda yake raye, a talaka da mai mulki duk mutuwarsu wa'azi ce, domin tabbaci ne, kowa zai riski lokacinsa, ya sani ko bai sani ba. Mai hankali shi ne yake daukar izna, duk lokacin da yaji anyi mutuwa, dan ya kara jin tsoron Allah ta hanyar kiyaye dokokinsa, da neman Rahama da GafararSa Subhanahu Wata'ala. Allah ka jikan mamatanmu, Allah ka kyauta karshen, ka yafe mana kurakuranmu da laifukanmu.

Yasir Ramadan Gwale 
23-11-2015

Saturday, November 21, 2015

Yadda Aka Kashe Sir Ahamadu Bello Sardaunan Sokoto Firimiyan Jihar Arewa Akan Idona - Direban Sardauna


YADDA AKA KASHE  SIR AHAMADU BELLO SARDAUNA SOKOTO A KAN IDO NA - Direban Sardauna 

Alhaji Ali Sarkin Mota shi ne ya zan ta da Wakili Jaridar Leadership yadda aka kashe Sir Ahamadu Bello Sardaunan Sokoto Firimiyan Jihar Arewa akan idonsa. Ya shaidawa Midat Joseph dan Jaridar cewar zan iya mantawa da komai, amma banda yadda sojoji suka kashe Sardaun da iyalin sa  a gaban ido na a 15 ga watan Janairun 1966.

Leadership: Kana gidan Firimiya a ranar 15 ga watan Janairun 1966. Me zaka iya tunawa da ya faru a wannan ranar?

Sarkin-Mota: Ga wadan da suke zaune a Kaduna zasu shaida yadda sojoji suke yin atisaye a makarantar Kafital dake unguwar Malali a garin Kaduna, duk lokacin da za ayi wani biki a hukumance. Amma a lokacin da ake shirin yiwa Sir Abubakar Tafawa Balewa Prime minister da Firimiya juyin mulki a 15 ga Janairun 1966 mun ga sojoji suna yin atisaye ba tare da wani biki ya gabata ba na hukuma. 

A ranar Juma'a 14 ga watan Janairun 1966, wani abokin aikina ya sanar da ni cewar, muna sa ran yin bakin alfarma a wannan rana daga Yammacin Najeriya zasu kawowa Firimiya ziyarar bangirma. Sai daga baya aka tabbatar min da cewar Cif Samuel Akintola, shi ne zai kawo ziyara Kaduna, a wannan rana, an shaida mana cewar zai sauka a filin jirgin sama na Kaduna da Misalin 11:30 na safe, dan haka ne muka shirya na tuka Sardauna zuwa filin jirgi shi da 'yan tawagarsa da Ministocinsa domin taryen Samuel Akintola. 

Mun isa filin jirgi muna zaune a zauren manyan baki muna jiran saukar jirgin da ke dauke da su Akintola sai Firimiya ya duba agogonsa yaga lokaci ya nuna 12:00 na rana, daga nan ne Firimiyan ya aiki daya daga cikin Ministocinsa akan,  yaje ya samu masu lura da sauka da tashin jirage ya tambaye su, me ya faru aka samu jinkirin saukar jirgin su Akintola, dan aiken yana zuwa suka shaida masa cewar, rashin kyawun yanayi ne ya hana jirgin sauka a kan lokaci, amma zai iso nan da 12:30. Muka cigaba da zama muna jira har 12:30 tayi babu alamun saukar wani jirgi, Firimiya ya kuma aikawa a tambayi ma'aikatan, shin ya akai har yanzu jirgin bai sauka ba, suka sake shaida masa cewar rashin kyawun yanayi ne ya janyo tsaiko, amma jirgin zai iso nan da 1:00, muna zaune har agogo ya nuna, karfe daya babu alamun saukar wani jirgi, aka kuma cewa, muyi hakuri Jirgin zai sauka karfe 1: 30.

Daga nan ne, Firimiya ya tashi zai fita tunda yake Juma'a ce ranar dan zuwa Masallaci, sai ya gayawa mataimakinsa, Aliyu Makaman Bidda, cewar ya tsaya a filin jirgi ya taryi Akintola idan ya karaso,  domin shi zai wuce Masallaci. Cikin raha da kakaci, sai Makaman Bidda yace masa, ranka ya dade, shin ka maida ni arne kenan ni ba zan je Sallah ba? Firimiya ya mayar masa da amsa, cewar bana nufin haka ko kadan,  illa kawai ina nuna maka matsayin ka na mataimaki, a lokacin da bana nan ka tsaya ka wakilce ni. Nan dai Makaman Bidda ya nunawa Firimiya muhimmancin ya tsaya da kansa ya taryi Akintola din, idan ya so yayi Sallar azahar a filin jirgin, nan dai Firimiya ya gamsu, suna cikin yin Sallar Azahar ne sai jirgin su Akintola ya sauka. 

Bayan su Firimiya sun idar da Sallah ne, aka ďanyi kade kade da bushe bushe na taryen manyan baki kamar yadda aka saba ana taren baki na alfarma. Daga nan Firimiya ya gabatar da Ministocinsa ga Samuel Akintola, a lokacin da muke kokarin fita daga zauren karbar baki, sai muka hangi Gilmawar Mejo Chukwuma Nzeagwu a cikin kakin soja, sai Firimiya ya tambaya me Nzeogwu yake yi a cikin filin jirgin sama sanye da kaki? Sai Akintola ya tambayi Firimiya ko da matsala ne? Sai Firimiya yace, abun mamaki ne naga Soja da kaki yanzu yana zirga zirga, daga nan su duka biyu sukai dariya suka wuce muka fita dan hawa mota. 

Na wuce gaba na tuka su zuwa gidan saukar baki na Gwamnati inda Firimiya ya shirya wa bakin liyafar cin abincin rana shi da 'yan tawagarsa, sannan kuma su yi tattaunawa a kebe. Akintola ya dan yi min hasafi  (inji Direban sardauna) Har ma dogarinsa yake cewa nai masa wani abu shima. A lokacin naji mutane suna fadin cewar, Akintola ya gayawa Sardauna cewar, a yanayin yadda abubuwa suke faruwa, Gara su nemi mafaka a wata kasar su bar Najeriya, amma dai ni banji wannan magana daga bakin su ba, a wajen jama’a naji. Bayan sun gama tattaunawa, bakin sun gama cin abinci, muka dauko su dan raka su filin jirgi, domin komawa. Anan ne, muka sake ganin Mejo Chukwuma Nzeagwu, wannan karon yana sauri yana bin Kwambar motocin mu,  kamar akwai wani abu da yake son fadawa shugabannin guda biyu.

Bayan da Akintola ya hau jirginsa ya koma, suka yi Sallama da Firimiya. Muka kama hanya dan komawa gidan Gwamnati, sai Firimiya ya lura Nzeogwu yana biye da shi a baya. Da yaga haka, sai yace, maza yi kwana ka kaini cikin gari na dan motsa jik a otal din Hamdala, anan ne galibi Firimiya kan tsaya ya shakata a lokacin da yake hutu baya aikin komai, kafun mu isa wajen, sai Firimiya yace, na kaishi gidan kwamashinan 'yan sanda na lokacin, MD Yusufu, muna isa gidan sai muka tarar Kwamashina baya nan, mun iske wani dan sanda yana gadi a bakin Kofa, dan sandan  dake gadi ya tambayi Firimiya,  idan ya dawo wa za a ce masa ya zo? Sai Firimiya yace masa, ka gayawa oganka,  wani dogon mutum me gashin baki yazo bai same shi ba. Sannan Firimiya ya zaro Fan daya ko biyu a aljihunsa ya baiwa dan sandan. 

Da muka fito daga gidan MD Yusufu, sai na tambaye shi, ina kuma zamu je? Sai yace na kai shi unguwar Kakuri, muna zuwa Kakuri sai ya shaida min cewar yana son zai kai ziyara DIC  (Defence Industry Cooperation), muna gab da isa bakin kofar shiga sai muka ga an rubuta baro baro, 'No Enter By Order' ma'ana ba wanda zai shiga sai wanda aka yiwa izni. Sai na gayawa Firimiya cikin raha cewar, Mubi fa a hankali sojojin nan zasu iya harbi, ba hankali gare su ba, Firimiya bai ce komai ba, da yake da Azumi a bakinsa, sai na kalle shi ta madubi muka hada ido, sai yace mun, kana zaton ko bacci nake? Sai nace masa, ranka ya dade naga kayi tagumi ko akwai wani abu da yake faruwa ne? Sai yace, kawai ina tunanin wannan rayuwar ne, sai na sake tambayarsa, ko da akwai wata matsala ne? Sai yace mun, bai san me zai faru da shi ba idan ya mutu, sa ya kara da cewar  "bana fatan na kara shekaru biyar nan gaba" yace gaskiya shi ya gaji da wannan rayuwar. Sai nace masa, haba ranka ya dade ya zaka dinga irin wannan tunani, ai kullum addu'ar mu Allah ya baka lafiya da yawan rai. Nace masa, Yallabai, idan ka mutu yanzu, akan idon mu komai zai jagwalgwale a kasarnan, sai ya kara cewa, ni dai wannan rayuwa ta ishe ni. Daga nan sai yace, na maida shi gidan Gwamnati. A lokacin biyar na Yamma ta kusa, an kusa Shan Ruwa, muna isa gida har ya bude Kofa zai shiga sai ya kira daya daga cikin hadimansa, Mamman Bakura, ya shaida masa cewar, idan an kira Sallah kusha ruwa Kada ku jirani, shi kansa Bakura yayi mamaki domin mun saba da Firimiya muke buda baki tun farkonsa Azumi.

Leadership: ka bayyana mana abubuwa na karshe da suka faru da Sardauna a gaban idonka? 

Sarkin-Mota: Bayan da aka yi Sallar Asham, sai Firimiya ya sauko daga sama ya shaida mana cewar kowa yana iya tafiya ya kwana cikin iyalansa, sai daya daga cikin hadimansa da ake kira Jarumi, yace shi yana nan ko bukatar gaggawa zata taso. Ni kuma ina tare da a iyalina a gidan Gwamnati a bangare na, da Misalin karfe daya na dare, ina wanke mota a lokacin, sai Firimiya ya sauko yana kwalawa me askinsa kira, yazo da sauri, da yazo sai ya gaya masa yana son yayi masa asiki a daren. Sai ya tambayeni da su wa yaga in magana dazu? Sai nace masa da 'yan sandan da suke gadin gidan Gwamnati muke magana.

Ashe ban sani ba, nayi kuskure, mutanan da na zata masu gadi ne, ashe sojoji ne, tuni sun shigo gidan a sace, sun rarraba kansu kusfa kusfa. Daga nan Firimiya ya aiki Bakura ya sayo masa kilishi da balangu, daga nan Firimiya yace na zo, na hau sama na daukowa masu gadin Lemo su sha, na shiga na dauko musu 'Tango'. A wannan lokacin bamu sani ba ashe, tuni wadannan sojojin sun kashe masu gadin gidan Gwamnati, suna gani na, suka kirani suka ce nai maza maza na bar gidan, kafun na tafi sai daya daga cikinsu yace mun 'ina Sardauna yake' Sai na nuna masa ban san wa yake tambaya ba, a lokacin wajen karfe daya da rabi na dare, sai ya sake tambaya ta, ina Sardauna yake, nace musu, tun da yamma da muka dawo daga Hamdala ban mu sake haduwa ba.

Su uku ne, sojojin, sai daya daga cikinsu yace, sun bani dakika biyar na fada musu inda Sardauna yake ko su kashe ni. Sai nayi karfin hali, nace musu, kuna iya kashe ni idan kun so, sai suka kyale ni suka shiga cikin gidan suna neman dakin da yake, a lokacin nan sun duba ko ina basu ganshi ba, daga nan suka shiga sashin da iyalansa suke, suka fito da su waje, suna tambayarsu ina Sardauna yake, ana haka, sai iyalan Firimiya suka garzayo inda nake suka hadu da iyalina. Sai kawai muka fara jin sojojin suna harbi ratata, na kirga harbi yakai sau goma, daga nan suka budewa dakina wuta a zaton su Firimiya yana ciki, suka karya Kofa suka shiga, suka farfasa gilasai, suka birkita dakin amma basu ga Firimiya ba. Daga nan sojojin suka shiga harbin kan mai uwa da wabi, anan ne fa, iyalin Firimiya suka shiga kururuwa, Inno matarsa, tana ta cewa, Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un, daga nan, sai daya matar tasa Hafsatu ta hango Firimiya sanye da doguwar Jallabiya kansa babu hula yana tsaye, sai tayi sauri ta mika masa mayafinta, ta ce ya lulluba yayi basaja ya gudu. Sai Firimiya yace mata, ba zai saka ba, ai shi suke nema kuma gashi. Nima na tashi da sauri na karasa inda Firimiya yake, na kamo hannunsa, amma ina ya dage.

A lokacin nufi na shi ne, na kamo shi, na jashi zuwa dakina na b'oye shi, tunda sun tabbatar baya ciki, amma ina da wani yayo harbi sai na wuntsula na bar Firimiya a tsaye. A lokacin sojojin suka kashe wutar gidan gaba daya, sai Inno ta taso a guje dan ta zo inda Firimiya yake, ashe wani soja ya hango ta, kawai sai ya biyo ta a baya, yana fadin, Ina Sardauna yake, jin haka sai Firimiya yayi magana yace gani nan, Allahu akbar! Anan wajen Ajalinsa ya sauka, Firimiya yana tsaye kusa da wani makewayi, matarsa Hafsatu ta rukunkumeshi, sojan kuwa, fadi yake ta sake shi ko ya bude musu wuta gaba daya, amma ina Ajali yayi kira, bata ko saurare shi ba. Ta gayawa sojan ka kashe ni tare da shi, daga na kuwa bai yi wata wata ba ya bude musu wuta su biyun, akan idona, Ahamadu Bello Sardaunan Sokoto aka kashe shi tare da matarsa Hafsatu a lokacin. Karfe 4 na asubahi tayi, na suma da ganin gawar Firimiya tare da matarsa a gabana. Kun ji yadda sojoji suka kashe Sir Ahamadu Bello Sardaunan Sokoto Firimiyan Jihar Arewa a Kaduna ranar 15 ga watan Janairun 1966. Allah ya jikansa yaji gafarta masa. Wannan bayani na fassara shi ne daga Jaridar Leadership ta yau.

Yasir Ramadan Gwale 
21-11-2015

Friday, November 20, 2015

Gwamnoni Na Wadaka Da Kudin Al'umma Suna Kiran Ba Kudi

GWAMNONI NA WADAKA DA KUDIN AL'UMMA SUNA KIRAN BA KUDI 

Abin mamaki ne Gwamnonin Nigeria da suke wadaka su ci su sha a kudin Al'umma, wai ba zasu iya biyan mafi karantar Albashi ba. A cikinsu fa babu wani Gwamna da ya rage irin wadakar da yake da dukiyar al'umma, kowa wane Gwamna idan kaga yadda yake dibar 'yan rakiya a yawace yawacensa bai rage ba, ga shatar jirgi da suke dauka ba kan gado, tafiya Kano zuwa Abuja Gwamna zai dau shatar jirgi ya kwashi mutane  cikin dukiyar al'umma. Ko a satin da ya gabata Gwamnatin Kano Shatar Jirgi sukai aka kwashi mutane zuwa Adamawa daurin auren wani Kwamashina cikin dukiyar al'umma.

Ga wani yawon karya da Gwamnonin suke fita kasashen waje wai kiran masu zuba jari jihohinsu, cikinsu kuwa har da Gwamnan Yobe wai yaje Japan da China yana kiran 'yan Kasuwa su zo Yobe su zuba jari, shin wannan ba wauta bace da barna da dukiyar al'umma, ko tsammanin Gwamna su 'yan kasuwar basu san me ke faruwa a Yobe ba? Shugaban Gwamnonin Najeriya Abdulaziz Yari kullum a tafiye yake yana yawace yawace a jirgin shata, Yaki zama ya yiwa al'ummar sa aiki. Tun daga hawansu mulki babu wani Gwamna da bai je kasar waje ba da sunan ziyarar Bogi wai ta Kiran masu zuba jari? 

Gwamnan Bauchi har wata ziyarar bige yaje Jamhuriyar Czech wai kiran yan Kasuwa,  shin 'yan Kasuwa nawa ne suka zo Bauchi daga Czech? Haka nan fa, Gwamnan Katsina da yake ta korafin ba a yiwa Jihar komai ba, ya kwashi kudi zai gina Hotel a inda baida amfani, shin wannan Hotel din ita ce Bukatar talakawa a Katsina?  Ya kamata Gwamna ya sani yanzu lokacin aiki ne domin amfanin al'umma ba amfanin wasu tsirarun ba.

Gwamnan Kaduna da ya kaddamar da wasu dankara dankaran motocin haya a Kaduna wannan ba barna ce da kudin al'umma ba? Shin wannan motocin al'umma suka fi bukata? Kaduna din da suka ce tayi shekaru 16 babu tituna masu kyau a cikin gari, kuma shi ne za a kawo tsala tsala motocin da aka saya da kudin al'umma dan kawai su lalace a cikin shekara guda? Wadannan Gwamnonin ba su da tausayi idan har suka tabbatar da wannan batu na kin biyan mafi karancin Albashi,  a lokacin da rayuwa take kara tsada.

Farashin komai ya daga, kud'in buhun shinkafa ya haura dubu goma, kayan masarufi duk sunyi tsada, mai yayi karanci kuma yayi tsada, rayuwa ta tsananta ga al'umma, basa neman mafita dan ce to al'umma daga halin kangi da mawuyacin hali sai wadakarsu suke yi? Bama yi musu Hassada su ci kaji su hau zunduma zunduma motoci daga cikin dukiyar al'umma, amma ya dace suji tsoron Allah su tausayawa al'umma, ana rayuwa hannu baka hannu kwarya, komai ya tsananta ga al'umma, ace dan Albashin da bai taka kara ya karya ba, ace wai ba zasu iya biya ba. Haba Nigeria har tayi tsiyacewar haka dan Allah.  Da ace ana yin Mid-term election a Nigeria da Gwamnonin sun sha mamaki.

Ya kamata kowanne Gwamna ya dakatar da duk wasu yawace yawace da suke a Abuja na ba gaira babu dalili suna kwana a Hotel da katuwar tawaga su tsaya su duba abinda ya dace da zai kawowa jihohinsu cigaba da zai amfani rayuwar al'umma da suka fito suka zabe su, haka nan tafiye tafiyen da suke zuwa kasashen waje na rashin lissafi dole su dakatar, a tsara gudanar da rayuwar al'umma cikin ingataccen yanayi da kwanciyar hankali da karuwar arziki. Allah ka fid da mu daga wannan mawuyacin hali.

Yasir Ramadan Gwale 
20-11-2015

Thursday, November 19, 2015

Jan Hankali Ga Masu Yada Munanan Hotunan Tashin Hankali


JAN HANKALI GA MASU YADA MUNANAN HOTUNAN TASHIN HANKALI 

Naga mutane da yawa da suke ta yin kira ga Jama'a akan su dena yada hotuna masu tayar da hankali, musamman wadan da aka dauka a yayin tashin Bom.  A ganina yana daga cikin rashin ladabi mutum Musulmi ya tsaya daukan hoton gawa a lokacin da aka zare mata Rai!  Musulmi yana da Alfarma ta tsare masa mutunci da tsiraici a yayin da yake raye ko yake mace, sam bai dace ba mutane a lokacin in da gawa ta Musulmi tafi bukatar addu'ah sama da komai, amma mutane su manta da cewar wanda ya mutu addu'ah yake bukata,  su shagaltu da daukan hotuna suna yadawa, abin mamakin wasu da aka dauki hotunan gawarwakinsu ba wai addu'ah ake musu ba, illa addu'ah ga wanda suka kashe su, to ina amfanin ka dauki hoton mutane kana yiwa wasu addu'ah?  Abin bakinciki wata gawar cikin tsiraici ake daukar hoton ta ba tare da nuna martabar ta ba ake yadawa. Kayi tunani shin gawar da aka dauki hoton  tsiraicinta a Bude, idan da yana raye zai bari a dauki hoton? To haka zalika idan ya mutu yana da hakkin a tsare masa mutuncinsa.

Ya 'yan uwa a hakikanin gaskiya babu wani abun burgewa mu dinga yada hotunan Hannu ko kafa ko rabin jikin mutum ko wani abu mai tayar da hankali musamman gawar da tayi daga-daga dan kawai muna son nuna irin girman tashin hankalin da ya auku. Wanda duk ya mutu kwanan sa ya kare, kowa da hanyar da Allah yake Kaddara masa hanyar mutuwa,  muyi kokarin suturta gawarwakin wadan da suka rasu a tashin Bam tare da nema musu gafara, shi ne abin yafi dacewa ba tozarta tsiraicin su ba. Allah yasa mu cika da Imani mu tashi da Imani,  Allah ka yaye mana wannan masifa da bala'i.

Yasir Ramadan Gwale 
18-11-2015

Wednesday, November 18, 2015

Sa'udiyya: Babu Wanda Yafi Karfin Doka Hatta Sarki Salman


SA'UDIYYA: BABU WANDA YAFI KARFIN DOKA HATTA SARKI SALMAN 

Gidan Talabajin na Al-Arabiyya ya ruwaito Sarkin Sa'udiyya Salman Bin Abdulaziz yana shaidawa manyan jami'an Gwamnatinsa cewar kaf fadin Kasar Sa'udiyya babu wanda yafi karfin doka hatta shi kansa (Sarki Salman) bai fi karfin doka ba. Sarkin ya kara da cewar duk wani dan kasar ta Sa'udiyya na da 'yanci ya kalubalanci kowa a Kotu matukar anci zarafin sa ko an take masa Hakki ko da shi da kansa ne za a iya gurfanar da shi a kotu.

Sarkin ya fadi haka ne, a ranar Laraba a yayin da yake gabatar da jawabi ga manyan jami'an Gwamnati dake Yaki da cin hanci da rashawa. Sarki Salman ya shaidawa al'ummar Sa'udiyya cewar kofar sa da kunnen sa a Bude suke dan sauraron korafin duk wanda aka takawa Hakki, yace za a biyawa kowa hakki ba tare da nuna bambanci tsakanin dan Sarauta da wanda ba shi ba. Sarkin yace, yafi damuwa da hakkin al'ummar kasar sama da hakkin sa a matsayinsa na Salman Bin Abdulaziz. 

Haka kuma, Sarkin ya gargadi jami'an hukumar Yaki da cin hanci da karbar rashawa cewar su sani Allah da ManzonSa sune suka fara Yaki da cin hanci da rashawa, dan haka su yi aiki da gaskiya da amana. Jama'a  Wannan fa shi ne, Sarkin Sa'udiyya Salmanu Dan Abdulaziz wanda Iran da Shiah da 'yan kanzaginsu a Nigeria  kullum suke yiwa jafa'i da fatan masifa da bala'i su auka musu, kullum bakin cikinsu Alsaud. Ya Allah ka yiwa bawanka Sarki Salman jagoranci, Allah ka taimake shi ka kunyata makiyansa na sarari da na b'oye. Allah ka taimaki adalan Shugabanni a duk inda suke, Allah ka taimaki kasarmu Nigeria. 

Yasir Ramadan Gwale 
19-11-2015

Saturday, November 14, 2015

SUWA ZA A ZARGA DA KAI HARIN BIRNIN PARIS NA FARANSA?



SUWA ZA A ZARGA DA KAI HARIN BIRNIN PARIS NA FARANSA? 

A tsakar daren jiya wayewar garin yau Asabar kafafen yada labarai na kasar Faransa suka bayar da labarin wasu hare hare da aka kai birnin Paris shalkwatar Gwamnatin kasar Faransa, inda mutane fiye da 100 rahotanni suka nuna cewar sun mutu. Bayanai sun tabbatar da cewar gurare biyar aka nufa da wannan hari,  inda hare hare ya rutsa da su sun hada da:

1- Harin Bom a Harabar wani filin wasa mai suna Stade De France, inda aka ce Shugaban kasar Faransa, Farnciou Hollande yana wajen inda yake kallon kwallo tsakanin Faransa da kasar Jamus. Bayanai sunce a gigice a aka fice da Shugaban kasar daga filin wasan, inda hankalin mutane ya tashi, kowa ke gudun yada-kanin-wani.

2- Anyi Garkuwa da mutane kusan 100 dari a wani gidan disco da ake kira Bataclan concert hall, inda daga bisa ni aka ce an kashe gaba dayan mutanan da ke cikin gidan disco din.

3- Waje na uku da aka kai wannan hari shi ne wani katafaren gidan cin abinci da ake kira  Le Carillon, inda aka dinga harbin kan-me-uwa-da-wabi. Rahotanni sun ce kimanin mutane 11 suka hallaka a yayin wannan bude wutar.

4 - Waje na hudu da aka kai wannan hari ita ce wata karamar mashaya da ake kira LA Belle Equipe inda aka budewa mashaya wuta bayan sunyi mankas, bayanai sunce ba a samu asarar rayuwaka da yawa a mashaya ba, amma dai an samu jikkata da yawa.

5- Waje na biyar kuma na karshe da aka kai wannan hari shi ne wani gidan cin abinci da ke sayar da kayan kwalama da ake kira Le Petit Cambodge, anan ma maharan sun bude wuta kan masu ciye ciye da lashe lashe babu ji babu gani.

A Jumlace bayanai sun ce an kashe mutane sama da 120 a daren jiya a Birnin Paris. Wannan harin yayi matukar girgiza  Faranasawa ma zauna birnin Paris, tuni bayanai suka ce Shugaban kasar Hollande ya soke halartar taron kasashe masu karfin Tattalin arziki da ake kira G-20 da zai fara gudana yau Asabar a kasar Turkiyya. 

Idan ba a manta ba, Jaridar nan ta Charlie Hebdo mai zanen hotunan batanci, tayi wani zanen batanci akan wani jirgin kasar Russia da yayi hatsari a Birnin Sinai na kasar Masar ya kashe duk mutanen da ke cikinsa, zanen dai ance yayi matukar bakantawa Gwamnatin Kasar Russia rai, inda aka ce Shugaban kasar VV Putin ya nuna rashin jin dadinsa kan wannan cin mutunci da Charlie Hebdo ta yiwa kasar, ba tare da girmama rayukan wadan da suka rasu ba.

Tuni dai kasashen duniya ciki har da kasar ta Russia suka taya Faransa jimamin ab inda ya faru. A ganina wannan harin ba shida wata alaka da Musulunci balle a dora laifin ga Musulunci. Amma dai al'adar kasashen Turai ce na dora laifin irin wannan hari akan kungiyoyin 'yan tayar da kayar baya da ke jingina kansu da Musulunci, tun ba a kai ga yin binciken gano hakikanin su waye suka kai harin ba. Allah masani.

Yasir Ramadan Gwale 
14-11-2015

Sunday, November 8, 2015

Raddi Akan Fatawar Aminu Gamawa Kan Zaben Mace


RADDI AKAN FATAWAR MALAM AMINU GAMAWA KAN ZABEN MACE

Addinin Musulunci shi ne addini a wajen Allah, duk wani addinin da ba shi ba b'ata ne kuma tab'ewa ce. Babu wani abu da Musulunci ya bari bai yi bayani ba. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam kafin yabar duniya yayi bayanin komai da ya shafi al'amarin Musulmi, musamman Al'amari na shugabanci da Amanw da adalci da zamantakewa da kasuwancin da sauransu. Haka zalika Manzon Allah ya fada cewar "Halal a bayyane take haka ma Haram a bayyane take", Allahumma sai dai abinda Shari'ah tayi shiru akansa kuma malamai sukai sabani akai. Amma duk lokacin da sabani mai girma ya bayyana game da hukuncin wani lamari, abinda Musulunci yayi umurni da shi shine a koma ga Alqur’ani da Hadisin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa sallam don samun mafita.

Jiya naga wata sabuwar fatawa da Malam Aminu Gamawa ya fitar, inda ya bayyana cewar "Munafuki shi ne wanda ya taya Matar Taraba murna ta samu zabe, sannan idan mace ta tsaya zabe a jihar sa ba zai zab'eta ba" Haka Aminu Gamawa ya bada wannan fatawa mai cike da hatsari, domin fatawa ce da kai tsaye ta ke kunshe da kafirta musulmi. A hakikanin gaskiya wannan ba karamin kuskure bane sauyawa abu fassara domin ta dace da son ran mutum akan abinda yake son ya zargi wasu. Haka kuma, irin wannan fatawa ta 'yan boko, tana daga cikin manya manyan sabubban da suke haifar da fikrar khawarijanci, domin tana kara k'aimi ga masu wuce gona da iri a addini, su samu abin fakewa da cewa 'yan boko suna 'bata addini da fikrar yahudawa ko yammacin duniya. 

Kai bama batun Musulunci ba, hatta a Demokaradiyya Aminu Gamawa ya tafka babban kuskure, wanda girmansa ya kai ayi Allah wadai ga duk wanda ya furta wannan magana. Domin a tsari na Demokaradiyya, dama ce  da aka baiwa duk wanda ya isa jefa kuri'a, ya zab'i wanda yaga dama ko kuma yafi gamsuwa da manufofinsa domin ya Shugaban ce shi ko ya wakilci shi. Ta ina mutum zai zama Munafuki a Demokaradiyyance idan yace shi ba zai zabi mace ba? Shin akwai wata ayar doka a kundin Demokaradiyya da ta ce duk wanda Ya'ki zab'en mace ya zama Munafuki, kamar yadda Aminu Gamawa ya kawo? Bana zaton ko shi kansa Malam Gamawa zai iya kare kansa da hujja me karfi akan wannan ikirari da yayi na cewa wanda duk Ya'ki zab'ar mace a matsayin Gwamna a jihar sa ya zama Munafuki?

Haka kuma, kalmar MUNAFUKI hukunci/kalma ce da Musulunci yayi bayanin ta filla-filla. Baya ga Ayoyi masu tarin yawa da suka yi bayani akan ta, akwai sanannen Hadisi sukutum da gudu, wanda ga duk wanda ya halarci makarantar Islamiyya ya san shi, wanda nayi Imani a matsayin Aminu Gamawa na tsohon Dalibin Sheikh Ibrahim Gomari ya san wannan hadisi? Shin ya akai Aminu Gamawa ya sauyawa wannan hadisi fassara ko ma'ana kawai dan ta dace da abinda yake son yin suka akai? Ta yaya akan Demokaradiyya zaka kifa Musulmi har abada a cikin wutar Jahannama can kasan ta?  Idan Malam  Aminu Gamawa ya gafala ne to lallai ya sani, abinda kalamin sa ke nufi kenan fa da fassarar da ya kawo kan zaben matar Taraba: wanda Yaki zaben Mace Gwamna a jihar sa ya zama Munafuki kai tsaye ba tare da wani kwane kwane ba, wannan shine zahirin abinda maganar ke nufi.

Lallai ina amfani da wannan damar, in jawo hankalin Malam  Aminu Gamawa da ya janye wannan magana tasa, kuma ya nemi gafarar Allah akan abinda ya aikata na kuskure, Allah mai afuwa ne yana son Afuwa, amma cigaba da tafiya ko kafewa  kan wannan magana/mahangar kuskure ne babba, ba a Musulunci ba kadai, hatta a ita kanta Demokaradiyya din da Malam Aminu Gamawa yayi wannan magana akanta. Domin duk mai zab'e yana da ikon zab'ar abinda yaga dama a Demokaradiyyance bai aikata wani laifi ba, tunda doka ce ta bashi dama. Ya Allah ka nesanta mu daga sharrin kawukanmu, ka yafe mana kurakuranmu wad'anda mukai muna sane da wad'an da mukai bisa ganganci. 

Yasir Ramadan Gwale 
08-11-2015

Thursday, November 5, 2015

Hannunka Mai Sanda Ga Gwamnatin Shugaba Buhari


HANNUNKA MAI SANDA GA GWAMNATIN SHUGABA BUHARI

A kwanakin baya, bayan da sabon shugaban kasa na goma sha shida Muhammadu Buhari​ ya sha rantsuwar kama aiki, nayi wani rubutu tare da bayar da Misali da Shudaddiyar Gwamnatin Mursi ta Masar. Mutane da yawa suka kasa fahimtar abinda nake nufi, masu zafin soyayyar Buhari da makauniyar biyayya suka dinga fadin cewar ina yiwa Gwamnatin ta Buhari mummunan fata da fatan tsiya. Haka naga mutane da yawa suna fadi, amma sam ban damu ba, sabida na san, da yawa tsananin soyayyarsu da Buhari yasa suke ganin komai aka fada a kansa laifi ne, kuma duk abinda ya aikata daidai ne.

Jiya cikin Ikon Allah, sai ga daya daga cikin fitattun Marubuta masani kuma mutafannini Dr. Aliyu U. Tilde​ yayi hannunka mai sanda ga Gwamnatin Ta Buhari da irin kalaman da nayi a baya lokacin da aka kasa fahimta ta. A rubutun da Dakta Tilde yayi jiya mai take "Manufacturing Another Mursi in Nigeria" A takaice a gajarce Dakta Tilde ya bada misalin abinda ya faru ga Gwamnatin Mursi tsakaninsa da masu bore da kuma abinda su Abdulfattah Alsisi suka yi.

Haka kuma, Dakta Tilden yayi tsokaci kan tuntsurarriyar Gwamnatin Buhari ta 1983, ya buga Misali kan abinda ya faru na halin da al'umma take ciki, sannan ya kwatantan da irin halin da aka shiga a wannan sabuwar Gwamnatin ta Buhari a 2015. A karshe Daktan yayiwa Gwamnati hannunka mai sanda akan irin mawuyacin halin ha'u'la'i da al'umma suke ciki.

A dan haka ya zama tilas a yi ta kiraye kirayega wannan Gwamnati ta san irin halin da al'umma suke ciki. Lokaci ya wuce da za ai ta zarge zargen gwamnatocin baya. Domin Obasanjo da ya zo a 1999 ya zargi Gwamnatin Abdulsalam da bar masa "empty treasury" haka nan YarAdua ya zargi Obasanjo da bar masa Gwamnati a murgude, to yanzu ana ta maganar PDP ta ruguza Nigeria. Wannan ba zai zama Uzuri ba a ko da yaushe. Lallai ya kamata Gwamnati ta himmatu wajen samar da canjin da aka zabe ta dominsa.

Yasir Ramadan Gwale
05-11-2015

Sakon Taya Murna Ga Mai Daraja Sardaunan Kano


SAKON TAYA MURNA GA MAI DARAJA SARDAUNA KANO

Ina amfani da wannan dama, a wannan rana, a madadin Ni Yasir Ramadan Gwale da mai daki da dangi baki daya, wajen taya Jagoranmu Mai Daraja Sardaunan Kano Malam (Dr.) Malam Ibrahim Shekarau​ bisa wannan ni'ima da Allah  yayi masa, na cika Shekaru 60 cikin koshin lafiya.

Ba shakka, duk wanda rayuwarsa ta tsawaita zai ga al'amura masu yawa, mabambanta. Da yawa an haifesu kuma sun rayuwa, amma mutuwa ta yanke musu hanzari basu iya kaiwa ko cika shekaru 60 a duniya ba, wasu kuma na nan cikin halin rai kwa-kwai mutu kwa-kwai. Muna yiwa Allah Subhanahu Wata'ala godiya da ya baiwa ubanmu kuma Jagoranmu Malam Ibrahim Shekarau aron lokaci har ya riski wannan muhimmin taqi a rayuwarsa.

Mai Daraja Sardauna Kano, Allah ya bashi dama wajen hidimtawa al'umma a cikin wadannan shekaru, wanda kuma har yanzu akan wannan bigire yake na yin hidima ga wannan al'umma tamu. Allah ya yi masa jagora, ya sanya masa alheri a Shekarunsa da zasu zo nan gaba. Kurakuransa na baya Allah ya yafe masa, muma ya yafe mana namu baki daya.

Yasir Ramadan Gwale
05-10-2015

Friday, October 23, 2015

Ranar Ashoora


RANAR ASHURA: A Galibin kasashen larabawa da gabashin Afurka, watan Zul-Hajj ya kare a 29 ne da ya gabata, inda a lissafi yau Juma'a ta zama 10 ga sabon watan Muharram Hijira 1437 (Ashura). Yayin da a Najeriya watan Zul-Hajj ya cika kwana 30 dan haka yau Juma'a ta zama 9 ga watan Muharram  (Tasu'ah). Malamai da dama sun sha yi mana bayani akan ranar Ashura da falalar azumtarta a addinin Musulunci, a gefe guda kuma, Malamai kan fadakar akan wata gagarumar Bid'ah wanda b'ata ne mabayyani da 'yan Shiah suke yi kuma suke jingina shi ga Musulunci. Dan haka, kamar yadda malamai suka sha fadakar da mu kusan duk Shekara a irin wannan lokaci, duk abinda 'yan Shiah suke yi bata ne kuma kafurci ne, ba Musulunci bane, ba kuma koyarwar addinin Mu lunch bane. Waki'ar da ta faru ga Jikan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam Alhussain Ibn Aliyu Bin Abi-Talib, Malamai sunyi bayani da dama akai, wannan kokarin jingina kansu da Hussain Ibn Ali Allah ya kara yarda da su shi da mahaifinsa, karya Shiah suke ba suda Alaka da su ko ta kusa ko ta nesa, hasalima su Shiah suka kashe jikan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam. Ya Allah ka bamu cikakken Ladan wannan ibada. Ya Allah al'ummar Musulmi na fama da wani mugun ciwo na Shiah Allah ka darkakesu ka wargazasu, Allah ka dammarasu ka hana musu yaduwa, Allah ka kare al'ummar Musulmi daga wannan masifar ta Shiah. Allah ka amshi wannan Ibada da muka yi domin neman yardarka. 

Yasir Ramadan Gwale 
23-10-2015

Wednesday, October 21, 2015

Dr. Goodluck Jonathan: Sabon Malamin Siyasar Kasar Tanzania


Dr. GOODLUCK JONATHAN: SABON MALAMIN SIYASAR KASAR TANZANIA 

Wani hanin ga Allah baiwa ne,  inji 'yan magana. Idan ya karbe ta can sai ya baka ta nan. Yanzu dai ance Mista  Goodluck Jonathan shi ne zai jagoranci wata kakkarfar tawagar kwararru domin sanya ido akan yadda za'a gudanar da zaben Shugaban kasa a Tanzania. Tuni rahotanni suka nuna irin kyakkyawar tarba da maraba lale da akaiwa Mista Jonathan a Arusha, ba da jimawa ba kuma aka ce Jonathan ya shiga aiki ka ' in da na ' in wajen yin kira ga 'yan siyasa da masu takara a Tanzania da su sanya kishin kasarsu akan ra'ayinsu. 

Ba shakka har yanzu ina samun nutsuwa da gamsuwa cewar tsohon Shugaban kasa Dr. Goodluck Jonathan ba yadda da yawa suka dauke shi haka yake ba. Ina ganin mutum ne mai saukin kai da saukin Mu'amala. Ya iya jure yadda da kaddara mai matukar wahala a sahun mutane irinsa. Yayi abinda Shugabanni da yawa a Afrika har da Nigeria basu yi ba, dan haka ne, duniya ta jinjina masa, kuma, aka yaba masa, bisa wannan namijin kokari da yayi na karbar kaddarar faduwa zabe. Har hakan ta kaishi ga samun wannan mukami. Haka zalika, har yanzu sabon Shugaban kasa Muhammadu Buhari bai dena yabawa wannan namijin kokari na Mista Jonathan ba.

Goodluck Jonathan ya nuna misali a Afrika wajen nuna kishin kasarsa da nuna cewar maslahar 'yan Nigeria tafi maslaharsa. Ko da kuwa za a gwale shi ace yaga babu sarki sai Allah shi yasa ya karbi kaddara, hakika yayi abin da ya saya masa mutuncin da kudi ba zasu iya Saye ba. Muna fatan Kullum 'yan Najeriya su kasance abin misali a Afrika wajen nuna kyawawan halaye da mutunta ra'ayin mafiya rinjaye. Ina fatan Allah ya masa jagoranci a wannan aiki yasa 'yan takara a Tanzania suyi koyi da shi (Goodluck Jonathan) wajen karbar dukkan sakamakon da yazo na gaskiya daga hukuma. Allah ya taimaki Najeriya. 

Yasir Ramadan Gwale 
21-10-2015

Thursday, October 15, 2015

Malaman Sunnah Sun Ki Jin Magana ta . . .


MALAMAN SUNNAH SUN KI JIN MAGANA TA . . .

Na karanta bayanin wani dan yaga riga a facebook, yana kalubalantar Malaman Sunnah, akan, dan me, ya jima yana kiransu da su shiga harkokin siyasa, amma sunki, a cewar sa,  ya sha gaya musu, ba sau daya ba, kuma ba sau biyu ba, amma sunki jin kiran sa.  Ya kuma kalubalance su a akan dan me basu taimakawa Shugaban kasa ba a lokacin da yake yakin neman zabe. 

A cewar sa,  ya auna ya gano, sam Malaman basu fadakar da mabiyansu ba a akan su zabi Buhari, yace yayi ta kira amma Malaman sukai shakulatun bangaro da batun sa. Ya cigaba da cewar yana da masaniyar cewa fa 'yan Siyasa suna baiwa Malaman kudi da motoci, kuma yace da idonsa ya hango wasu a Umra, Goodluck Jonathan Mai Nasara,  ya kai su dan suyi wa Najeriya addu'ah. 

A cikin soki burutsun nasa, yace, ku Malamai ku sani fa, dan kafi mutum ilimin addini ba shine yake nuna ka fishi kwakwalwa ba. Sannan ya yabawa Adamu Adamu a kokarin sa na ganin kasar sa ta fita daga halin cin hanci da karbar rashawa da samun mafita a harkar tattalin arziki, ya yabawa Adamu Adamu akan wannan kokari nasa, a daidai lokacin da ya kwarewa Malamansa da yake jingina kansa garesu cewar basu ji irin kiraye kirayen da ya dinga yi musu na su ja hankalin mabiyansu su zabi Buhari ba.

Wannan dan hauragiya yayi ta rambatsu yana aibata Malaman Sunnah da yake jingina kansa garesu, duk kuwa da ta bayyana a fili wasu daga cikinsu da yake muzantawa sun tsunduma kansu cikin siyasa tsundum kuma jam'iyyar da yake wa fatan taci zabe, kuma taci din. Wannan dan harbatamati yayi ta soki burutsu da hayaniya da nuna rashin kunya ga Malaman Sunnah. Kalaman sa na rashin ladabi, ba boyayyu bane musamman ga Babban Malamin Tafsiri na Kaduna Sheikh Dr Ahmad Abubakar Mahmud Gumi da aibata shi da nuna cewa shi yafi Malamin Sanin addini da sanin Sunnah.

Irin wadannan yan jagaliya basa bukatar Nasiha ko Jan hankali,  a biyo masa ta inda ya shigo zai Fi gane wannan yaren. 

Wannan somin tabi ne.

Yasir Ramadan Gwale 
15-10-201

Monday, October 12, 2015

Mugun Nufin 'Yan Shiah Akan Musulmi Da Sunan Aikin Hajji


MUGUN NUFIN 'YAN SHIAH AKAN MUSULMI DA SUNAN AIKIN HAJJI 
 
Su 'yan Shiah ba gaskya bace da su, ba kuma gaskiya suke bi ba, illah kawai makauniyar biyayya da suke yiwa kasar IRAN. Shi yasa sau da yawa zaka samu mabiya Shiah suna b'oye shi'ancinsu, sai fa wadan da asirinsu ya tonu babu yadda zasu yi. Sabinin mu mabiya Sunnah bamu tab'a b'oye Aqidarmu ba, bama shayi ko shakkar wani ko wasu su kiramu da sunan Aqidarmu ko su jinginamu zuwa gareta, ba zaka tab'a ganin wani Ahlussunnah yana kyamar a ce masa 'Dan Izala ko Wahabi ba, domin munyi Imani da Allah kuma mun kyautata masa zaton cewar ba zai tabar da mu ba, dan haka ne muke da yakini cewar ba'a kan hanyar b'ata muke ba.

Ko su kiramu Wahhabiyawa ko 'yan Izala ko duk wani suna da zasu jingina mana, mun yarda kuma mun Amince cewar mu din mabiya Sunnah ne, bama b'oyewa, bama kuma, kin amsawa. Amma har anan Facebook mun sansu da yawa, suna Shiah amma suna b'oyewa, basa son ko kadan a sani. Kaga wannan hujja ce ta cewar sun yi Imani Aqidarsu ba gaskiya bace, kuma b'ata ce, domin indai gaskiya mutum yake bi, baya tab'a shakkar bayyana hakikanin abinda yake bi na Aqidah.

A sabida haka, mabiya Shiah sun san ba gaskiya suke bi ba, kuma ba suda wata manufa, Illa ta kare muradun kasar Iran da yin biyayya ga duk abinda ta zo musu da shi; yasa suka dauka kowa ma haka ne. A dan haka ne, sai suke kokarin Jinginamu ga Sa'udiyya a matsayin masu biyayya a gareta Ido rufe kamar yadda suke yiwa Iran Biyayya Ido rufe.

Amma a zahirin gaskiya mu mabiya gaskiya ne, mabiya Sunnah, ba wai Saudiyya muke wa biyayya Ido rufe ba. Sai dai a bayyane take a zahiri a garemu cewar kasar Sa'udiyya kasa mai tsarki, kasa ce ta Sunnah, kuma tafi kusa da kwatanta gaskiya da bin Sunnah da yada da'awar Sunnah, dan haka muke tare da su a duk wasu abubuwa da basu sabawa Sunnah ba.

Kasancewar Daular Sa'udiyya daula ce ta Sunnah, shi yasa a mafiya yawancin lokaci al'amuransu sukan dace da koyarwar Sunnar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam. Sanin kowa ne, kasar Sa'udiyya bata goyi bayan Gwamnatin Mursi a Masar ba, amma da yawanmu mukai hannun riga da ita akan batun Mursi. kuma kusan kowa yaji matsayarmu ta bakin Sheikh Dr. Sani Umar Rijiyar Lemo dan gane da abinda akaiwa mursi.

Amma duk da haka su 'yan shiah sai basa ganin wannan, suke nunawa duniya cewar mu din ido rufe muke biyayya ga Sa'udiyya kamar yadda ba suda wata manufa sai abinda Iran tace, SUNA MATA BIYAYYA DA DUK ABINDA TA ZO DA SHI. yana daga cikin manufar Iran mayar da Musulunci yayi kamanceceniya da Kiristanci, domin dusashe haskensa, wannan shi ne mugun nufinsu, shi yasa mukaji a wannan lokacin, suka dinga kiran tilas aikin hajji ya koma karkashin kulawar dukkan musulmi ba wata kasa guda daya ba. Duk wanda kaji da wannan furuci, ya sani ko bai sani ba, da yawun Iran yake magana.

Asali su kiristoci mafiya rinjaye suna karkashin Fadar Vatican ne, wadda Paparoma yake jagoranta. Wato Paparoma ba wai kawai shugaban addini bane, domin ita kanta Vatican kasa ce, kuma duk wani Paparoma shi ne shugaban kasar Vatican, a sabida tsarin da suke da shi na yin hadakar kiristoci baki daya wajen tafiyar da duk wani al'amari da ya shafi fadar vatican, shi yasa zaka ji an wayi gari mutumin kasar ARgentina ko Germany ko Poland zai iya zama Paparoma kuma Shugaban kasar vatican.

To misalin irin wannan shi ne manufar Iran akan Musulunci, su mayarda musulunci kamar Kiristanci, ta yadda za'a wayi gari watan wata rana ace mutumin IRAN, HEZBOLA shi ne zai zama shugaba ko sarki da yake kula da biranen Makkah da Madina, shi yasa a wannan lokaci 'yan korensu da 'yan kanzaginsu ke ta yayata cewar tilas shiryawa da gudanar da aikin hajji ya zama mas'uliyya ce ta dukkan musulmi ba Sa'audiyya ita kadai ba. Wannan ita ce manufarsu.

Me kake jin zai faru idan Makkah da Madina suka kasance karkashin jagoranci 'yan Shiah mutanen Iran? Dan haka duk wani me kururwar cewar tilas shirya gudanar da aikin hajji ya zama karkashin kulawar musulmin duniya, to wallahi ya sani ba tunaninsa bane, kuma ba ra'ayinsa bane, wannan shiryayyen al'amari ne da Iran ta shirya, take amfani da 'yan barandanta na sarari da na boye, suke yad'a wannan kururuwar da masu raunin tunani zasu ji kamar akwai gaskiya a cikinta. Babu gaskiya ko ta kwabo illa kokarin sauya tafarkin addinin Allah na gaskiya.

Domin duk lokacin da aka ce ai musulmi ne gaba daya zasu saka hannu akan gudanar da Hajji, to za'a wayi gari kuma, suce ai makkah da madina na musulmi ne duka, dan haka dole musulmi su yi musharaka wajen tafiyar da jagorancin wadannan birane masu tsarki. ya Allah kada ka cika musu wannan buri nasu, ya Allah kada ka basu dukkan wata dama akan al'ummar musulmi. Allah ka taimaki Sunnah da Ahlussunnah ka rusa Shianci da kafurci da duk masu mara musu baya, na sarari da na boye.

Yasir Ramadan Gwale
12-10-2015