Saturday, February 28, 2015

Sakwannin Whatsapp Dubu Talatin


SAKWANNIN WHATSAPP DUBU TALATIN 

Yau sakwannin wayata na Whatsapp sun kai fiye da 30,000. Kusan kullum ina samun sako a Whatsapp sama da 500 da yawansu ban san daga ina suke zuwa ba. Kusan idan zan zauna a kullum sai na share lokaci mai tsayi ina karanta sakwannin Whatsapp, abinda yake bani mamaki shi ne yadda nake samun kaina a cikin wasu groups da ban san dalilin sakani a ciki ba, ba shakka akwai groups din da nake ciki wadan da ina jin dadin su fiye da kima, wasu ina yin matukar farin ciki tare da godiya ga wanda yayi adding dina, amma wasu kam har mamaki nake idan naga an sakani a ciki.

Zan ce na gaskiya bana samun damar duba dukkan sakwannin da nake samu a kullum, nakan karanta wadan da ido na ya kai garesu ne kawai ko kuma wasu mutane da nasan tattaunawa tsakanin a da su tana da muhimmancI. Yana da kyau ga wanda yake da lambata yake san yayi adding dina a wani group ya sanar da ni. Wadannan sakwannin ba su ne suke bani mamaki ba illa idan na duba file dina naita ganin hotuna har da na tashin hankali, shi yasa kullum cikin goge hotuna nake yi. Ya kamata dai Turawan nan su kyalemu mu amfani lokacinmu haka, yanzu dan Allah da wanne zamu ji da E-Mail ko Facebook ko Twitter ko Google Plus ko LinkedIn ko Whatsapp? Gashi kuma shi dan Adam mai buri ne so yake ya zama all round alhali lokaci ba a tsaya yake ba.

Na laura da cewar an fi saurin yada Alkhairi da Sharri a Whatsapp kuma yafi da dama sirri. Wallahi idan naga wani sakon ana yadawa sai nace to wai ina hankali da tunani da Allah ya bambanta Bil-Adama da dabbobi da shi! Wani abin baka bukatar sai an kawo maka aya ko Hadisi ko fatawar magabata zaka san karya ne, yana da kyau mutane su dinga tantance duk wani sako da aka turo musu kafin su yada shi. Akwai mutane kebantattu da nake sanya su a addu'ah sabida kaunarsu da yada Alkhairi a Whatsapp Malam Umar S Zaria da  Ibrahim Nasidi Abu-Ilham​ Mustapha Alfurqan da Ismail Lamido da Mohammed Jungudo​ da sauransu da dama da basa gajiyawa wajen yada Alkhairi, Allah ya saka musu da alheri.

Haka kuma, na laura wasu kan kwaso wasu bayanai a Facebook suyi ta yadawa a Whatsapp ba tare da jingina abin zuwa ga asalin mai shi ba, wanda  wannan tozarta Amana ne, da yawa wasu sukan  dauka haka ba laifi bane, suyi dandatsa ko Plagiarism a social media. Yana da kyau mu kiyaye wa mutane amanarsu, Allah ka sa mu kasance sahun gaba wajen yada Alkhairi tare da kawar da Sharri. Allah ka shiryemu shirin addini ka bamu lafiya da zaman lafiya.

Yasir Ramadan Gwale 
28-02-2015

No comments:

Post a Comment