Monday, March 2, 2015

ALJAHI KABIRU SANI KWANGILA: Daya Tamkar Da Dubu


ALHAJI KABIRU SANI KWANGILA: Daya Tamakar Da Dubu

Duk mutumin da yake Kano ko makwabcin Kano, ba zai kasa sanin wannan dan tahaliki ba, Alhaji Kabiru Sani Kwangila a.k.a SKY, mutum ne mai arziki Attajiri mai taimakon bayin Allah da baya kyashin taimakawa a kowanne lokaci. Ya shahara da taimakawa addini a ciki da wajen jihar Kano, ya taimakawa da'awar addini fiye da yadda ake zato, kuma yana kan yin wannan taimako, mutum mai taimakon matasa galihu.

SKY wata rana an gayyace shi taron saukar Al-Qurani da kafa asusun gina wata makaranta. Bai sanni ba, bai taba gani na ba, labarina kawai aka bashi, ya aiko min da kudi wajen Kwata Miliyan, cewa naje wannan makaranta na kaddamar da wannan asusun gina makarantar a madadinsa, ya kuma bude asusun da wannan kudi da ya bayar, tare da alkawarin taimakawa makarantar a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

Hakika wannan al'amari yayi min dadi, sannan kuma naji matukar mamakin yadda wannan bawan Allah ya gasgatani ba tare da yasan ko waye ni ba. Naje makarantar na zauna a katuwar kujerar da aka warewa cif Lanca aka bani abin magana na kaddamar da wannan asusu.

Cikin ikon Allah a jiya na samu lokaci mai tsayi wajen tattaunawa da SKY akan batutuwa da yawa da suka shafi rayuwar Talaka da kuma cigaban Najeriya. SKY ya labarta min irin yadda ya dauki dawainiyar dalibai masu yawa zuwa kasashen duniya daban daban dan yin karatu. Ya tura mutum 60 zuwa Ingila dan yin karatu, mutum 40 zuwa Russia, 6 zuwa Amerika, 80 zuwa Indiya, mutum 200 zuwa Ghana, 38 zuwa Masar  sannan ya tura biyu uku zuwa Ukrain da Malaysia da Singapore da Uganda da da sauran kasashe da yawa.

Haka kuma, SKY ya shaida min cewar a shekarar da ta gabata yayi bajat na kudaden karatun yaran da yake daukar dawainiyarsu sama da Naira Biliyan daya, wannan kusan duk Shekara sai an kashe wannan kudi. Abin farin cikin duk wadannan mutane da yake daukar dawainiyarsu da dukiyarsa gaba dayansu 'ya 'yan Talakawa ne, wadan da bai san su ba. Allahu akbar! Wannan taimako SKY yana yinsa ne kawai fa ta fannin Ilimi banda sauran bangarori daban daban na rayuwar al'umma da ya taba da dukiyarsa. Banda wadan da ya taimakawa da ba wanda ya sani sai shi sai Allah, sai kuma wadan da ya taimakawa.

Ba shakka samun mutum irin wannan a cikin al'umma babbar Ni'ima ce. Domin shi daya ne tamkar da dubu. Allah ya saka masa da mafificin alherinsa, Allah ya yalwata masa dukiyarsa, Allah ya kiyaye shi ya kare shi daga sharrin makiya da mahassada na fili da na boye. Allah ka yawaita mana irinsa a cikin wannan Al'umma tamu. Ya Allah ka sakawa bawanka SKY da alheri, Allah ka sada shi da Manzonka Sallallahu Alaihi Wa Sallam. Allah ka taimaki masu taimako a duk inda suke.

Yasir Ramadan Gwale
02-03-2015

4 comments:

  1. Ya allah ka sakawa alh kabiru sani kwangila da aljannatul firdaus saboda namijin kokari da yake yi na taimako. Ina jin sunan amma ina so na sanshi a zahiri. Daga Mustafa Mohamet Magariya a jamhuriyar Niger

    ReplyDelete
  2. Ameen. Inajin labarinsa da alkairansa amma har yau Allah be nufa mun haduba.

    ReplyDelete
  3. Allah yasaka da Alheri Allah yabiyasa da gidan Aljanna

    ReplyDelete