Tuesday, March 31, 2015

Shugaban Kasa Goodluck Jonathan Ya Cancanci Yabo


SHUGABAN KASA GOODLUCK JONATHAN YA CANCANCI YABO

Ba shakka mutum na biyu da za a yiwa godiya bayan an gode wa Allah a wannan zaben shi ne Shugaban Nigeria Dr. Goodluck Jonathan​ bisa irin yadda ya nuna dattako da kishin kasa ta hanyargirmama abinda 'yan Nigeria suka zaba, tarihi zai jima yana tuna Shugaba Jonathan bisa wannan namijin kokari da yayi na karbar sakamakon zaben da 'yan Nigeria suka yi, duk da cewa hukumar zabe bata kai ga bayyana sakamako na karshe ba, Shugaban kasa ya yiwa kowa yankan hanzari.  

Shugaban kasa, ya kawo karshen dukkan wani zullumin barkewar rikicin da aka dinga yi yayin fadin wannan sakamako. Manyan kasashen duniya da kungiyoyi da dama ciki da wajen Nigeria suka ta Kiran da a zauna lafiya a yin wannan zabe.

Shugaba Goodluck Jonathan ya cika alkawarin da yayi na cewa za'a yi zabe na gaskiya a wannan zabe. A sakon sa ga al'Umar Nigeria shi kansa GMB ya jinjinawa shugaban kasa Jonathan,  muna fatan wannan ya Bude sabon babi dan samar da sabuwar Nigeria. 

Wannan alamu ne da ke nuna al'amura zasu sauya a Nigeria In Sha Allah. Ina kara taya sabon Shugaban kasa Muhammadu Buhari​ murna da kuma fatan Allah ya shige masa gaba yayi masa jagora a wannan babban nauyi da yake kansa,  domin idan duniya baki daya na kan GMB wajen ganin yadda zai yi Gwamnatin da babu kamarta a tarihin Nigeria, wajen tsare gaskiya da adalci. Allah ka bamu lafiya da kwanciyar hankali da karuwar arziki a kasarmu. Fatan alheri ga Nigeria.

YASIR RAMADAN GWALE​
31-03-2015

No comments:

Post a Comment