Thursday, April 30, 2015

LEGAS: Fiye Da Shanu 6000 Ake Yankawa A Kowacce Rana


LEGAS: KIMANIN SHANU DUBU 6000 AKE YANKAWA A KULLUM 

Fiye da shanu dubu shida ake yanka wa a Birnin iko kowacce rana. Da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, kwamashinan aikin gona na jihar Legas Mista Gbolahan Lawan ne ya bayyana haka. Lawan ya ce a mayankar Oko-oba dake cikin birnin iko kadai ana yanka shanu kimanin dubu biyu (2000) a kowacce safiyar Allah, ya kara da cewar sauran dubu hudu kuma ana yankawa a sauran sassan jihar ta Legas a kananan mayanku. 

Wannan labari jarida Leadership Newspapers ce ta ruwaito shi, kuma ya ja hankali na sosai da gaske. Wannan kuma na kara nuna yadda noma da kiwo ke da matukar muhimmanci a wajen habaka tattalin arzikin Arewa. Misali idan a Legas za'a yanka saniya dubu shida, idan kowacce saniya ana sayanta akan kudi Naira 100,000 kenan kowacce rana ana sayar da shanu na kimanin Naira Miliyan dari shida  (600,000,000), wannan ya nuna a wata daya kadai ana sayar da shanu na kimanin Naira Biliyan Goma sha takwas (18,000,0000,000). Tab!

Wannan fa a Legas ne kadai, ina ga sauran jihohin Nigeria 35 da Abuja, shanu nawa ake yankawa a kowacce rana? Ba shakka wannan babban dalili ne da ke nuna cewar idan mutanan Arewa suka rike harkar noma da kiwo da gaskiya da adalci zamu cigaba da Jan ragamar Najeriya shekaru masu yawa nan gaba. Domin Man fetur din da ake ta yi mana gori da shi dai kullum sabbin kasashen duniya ne ke kara gano shi, sannan darajar sa na dirga kasa sosai.

Sannan kuma,  wannan fa maganar nama kawai ake, ina kuma ga idan an zo batun Madara da sauran amfani da ake samu a jikin shanu? Lallai wannan labari ya tsumani domin nan gaba kadan nima zan zama manomi dan zan fara sayo saniya da dan maraki na turke nima. Sannan zan je wajen Dr. Aliyu U. Tilde in sha Allah har Tilde domin samun horo na musamman akan kiwon shanu a zamanan ce. 

Dr. Aliyu U. Tilde ashe dai kun jima kuna more arziki bamu sani ba. Ba shakka akwai sirri ma yawa na samun arziki a kiwo amma mutane sun tare a birane amma arziki na cikin daji. Lallai masu sana'ar kiwo su mutunta ta sosai dan samun riba mai yawa. Idan ba haka ba suna ji suna gani 'yan Boko zasu yi babakere su tare aikin Gwamnati sannan su diary a noma da kawo a zamanance dan samun arziki mai yawa.

Yasir Ramadan Gwale 
30-04-2015

Wednesday, April 29, 2015

SA'UDIYYA: Sarki Salman Ya Samar Da Canji Mai Ma'ana


SA'UDIYYA: SARKI SALMAN YA SAMAR DA CANJI MAI MA'ANA

Sabon Sarkin Sa'udiyya  Salman Bin Abdulaziz Alsaud an wayi gari da sabon sauyin da ya kawo a majalisar Masarautar kasar da ta kunshi Ministoci da manyan jami'an Gwamnati, wannan shi ne karon Farko da Sarki Salman ya samar da wannan sauyi tun bayan da ya zama sabon sarki a 23 ga watan Janairun wannan shekara bayan rasuwar  King Abdullah bin Abdulaziz Al Saud.

Mutum na karshe da ake sa ran shi ne zai zama Sarki daga cikin 'ya 'yan Abdulaziz Ibn Abdulrahaman Alsaud wanda shi ne ya kafa kasar sa'udiyya, wato Yarima Muqreen, wanda ya zama sabon Yarima mai jiran Gado bayan da Salman ya haye kan karagar mulki. Sai dai kuma a yau an wayi gari inda sabon Sarki Salman ya bayyana sauke Yarima Muqreen aka maye gurbinsa da Mohammad Bin Nayef a matsayin sabon Yarima, rahotanni sun tabbatar da cewYarima Muqreen ya amince zai sauka daga mukaminsa, kamar yadda Mohammad Vall na gidan talabijin na Aljazzerah ya ruwaito daga Sa'udiyya.

Sarki Salman yayi sauyin da ya dace, domin kuwa, Mutumin da aka nada sabon Yarima mai jiran gado Muhammad Bin Nayef ya gaji mahaifinsa ne wanda daya ne daga cikin 'ya 'yan Sarki Abdulaziz, Nayef shi ne Yarima mai jiran gado lokacin marigayi Abdallah na kan sarauta, Allah ya yi masa rasuwa kafin Abdallah. Sauyin da Sarki Salman yayi, ya nuna cewar bayan shudewar 'ya 'yan Sarki Abdulaziz to sarauta zata faro ne daga jikokinsa, daga kuma gidan marigayi Nayef wanda yana daga cikin wanda zai zama Sarki mutuwa ta yi masa yankan hanzari. 

Haka kuma, Sarki Salman ya sauke ministan harkokin wajen Yarima Saud Al-Faisal daga mukaminsa, wanda Jikan Sarki Abdaziz d'a ga Sarki Faisal mutum na farko da ya zama Sarki bayan rasuwar Abdulaziz a Daular Sa'udiyya. Yarima Saud Al-Faisal ance da kansa ya amince ya sauka bayan da ya jima yana fama da rashin lafiya wadda ta kai har baya iya tafiya da kafafunsa sai da sanduna guda biyu, amma yana cigaba da rike da mukamin ministan harkokin waje, mukami mai daraja ta farko bayan Yarima da mataimakinsa. Sabon Ministan Harkokin waje Yarima Muhammad Bin Salman babban dan Sarki Salman ne, masharhanta na ganin nadinsa ya dace kasancewarsa Matashi dan shekaru hamsin a cewar Riyad Khshta wani mai sharhi akan gabas ta tsakiya.

Sannan kuma a karo na farko an nada Adel al-Jubeir Jakadan Sa'udiyya a birnin Warshinton  wani wanda ba dan cikin masarautar ba a matsayin sabon ministan tsaro, mukamin da sabon Yaima Muhammad Bin Nayef yake rike da shi kafin a nada shi wannan sabon mukamin.

Yanzu dai masu sharhi akan kasashen gabas ta tsakiya na ganin Sarautar Saudiyya zata koma hannun matasa kuma wadan da suka yi karatun boko mai zurfi. Inda sabon Yarima MUhammad Bin Nayef dan shekaru 55 yake da kwarewa ta musamman akan harkar tsaro, yayin da mataimakinsa Muhammab Bin Salman matashi dan shekara 50 yake da gogewa wajen muamalar da ta shafi harkokin cikin gida. Allah ya taimaki wadannan shugabanni ya basu ikon sauke nauyin da ke kansu, ya kuma basu ikon yiwa Masallatan Allah masu alfarma hidima.

Yasir Ramadan Gwale 
29-04-2015

Tuesday, April 28, 2015

Kwankwaso Na Yiwa 2019 Tanadi Na Musamman


KWANKWASO NA YIWA 2019 TANADI NA MUSAMMAN 

Muhammadu Buhari, Ibrahim Badamasi Babangida​, Abdul salami Abubakar,  Yakubu Gawon, Olushegun Obasanjo, Ernest Shonekan, TY Danjuma, Justice Dahiru Musdapha, Jibril Aminu, Tony Momoh da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu​ duk Gwamnan Kano Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso​ ya gayyato su Kano dan bude ayyukan da Gwamnatin sa ta yi a wannan lokaci. Duk me nazari da tsinkaye ya san cewar wannan ba komai bane illa wani shiri mai karfi da Kwankwaso yake yi dan tunkarar takarar Shugaban kasa a 2019.

Bahaushe yace mai kwarmin ido da wuri yake fara hawaye, Gwamna Kwankwaso dan siyasa ne, yasanta kuma ya san lagonta dan haka yake kafa wa siyasar 2019 wani ginshiki mai karfin gaske, ta hanyar katange kansa da manyan duwatsu, wadan nan sune who is who a siyasar Najeriya. Idan Kwankwaso yayi sa'ar samun cikakken loyalty nasu to zai yi barazana ga duk wani dan siyasa a 2019.

Zaben fidda gwani na APC da akai Kwankwaso yazo na biyu, wannan ya kara masa kwarin guiwar cewar, lallai zai bada ruwa anan gaba, domin 'old tamers' irinsu Atiku Abubakar tuni Kwankwaso yaga tsiraicin siyasarsu ta hanyar rashin wata structure me karfi ta samun Nasarar zabe.

Bugu da kari, Kwankwaso ya fahimci mafi yawancin 'yan Najeriya  mutane ne da ake iya cinsu da buguzum, wannan ta sanya shi cikin lokaci kankani ya samar da makaranta domin 'yan gudun hijira na Borno a Kano, wanda wannan aiki tsagwaron siyasa ne, domin Miliyoyin 'ya 'yan talakawa suna nan a Kano basu ci wannan gajiya ba.

A ganina a 2019 idan Allah ya kaimu, ya kamata a ce dan takarar Shugaban kasa a dukkan jam'iyyun APC da PDP ya kamata ya fito daga shiyyar Arewa Maso Gabas, domin hakan shi ne zai nuna Adalci, kuma wannan zai nuna cewar mu mutanan Arewa Maso Yamma ba mu yi babakere a shugabancin Najeriya ba, domin wannan yanki namu ya samar da Murtala Mohammed, Shehu Shagari, Muhammadu Buhari​, Sani Abacha, Umaru YarAdua da kuma Muhammadu Buhari​ a karo na biyu a matsayin Shugabanin kasa; su kuma Arewa Ta Tsakiya suka samar da Yakubu Gawon, IBB da kuma Abdul Salami Abubakar; A yayin da Arewa Maso Gabas basu da kowa in banda Sir Abubakar Tafawa Balewa​.

Ina gani indai ana son Arewa ta zama curarriya kwaya daya, to ya kamata shiyyar Arewa Maso Gabas a taimaka musu wajen samar da Shugaban Najeriya bayan shudewar Gwamnati Muhammadu Buhari, hakan shi ne zai zaunar da mu lafiya ba tare da wasu na ganin an kwaresu ba, mu kuma ba'a kallemu amatsayin masu babakere da nuna mu kadai ne Arewa ba. Wannan zai bayu ne kadai, idan mutanan Arewa Maso Gabas sun yunkura wajen ganin suma an dama da su a tsarin siyasar Najeriya.

Amma idan ba haka ba, sai an kwashe fiye da Shekaru 20 mutanan Arewa Maso Gabas basu d'ana Shugabancin Najeriya ba. Domin bayan Buhari ya kammala wa'adin Shekaru hudu kamar yadda ake zato, to Kwankwaso zai zo yayi Shekaru takwas sannan ya mika wa Yarbawa suma su shekara takwas sannan ne watakila mulki zai juyo Arewa kana kuma ayi tunanin Arewa Maso Gabas watakila. Amma duk da haka da arziki a garin wasu gwara a naku inji masu iya magana.

Yasir Ramadan Gwale 
28-04-2015

KANO: Rugujewa Tskanin Gada Mai Doron Zabuwa Da Mai Ramin Kurege


KANO: RUGUJEWA TSAKANIN GADA MAI DORON ZABUWA DA MAI RAMIN KUREGE

A ranar 23 ga watan Maris din da ya gabata, sa'o'i saba'in da biyu, bayan da Shugaban kasa Dr. Goodluck Jonathan ya kaddamar da bude sabuwar Gadar da Sanatan Kano ta Tsakiya Bashir Garba Lado ya samar a cikin birnin Kano da aka sanyawa sunan Sarkin Kano mai rasuwa Alhaji Ado Bayero, aka samu labaran da suke nuna cewar anga wata tsaga a kan gadar. Wannan ya haifar da tururwar jama'a domin ganewa idonsu wannan lamari. Cike da murna da jin dadi masu hamayya da Takarar Sanatan Lado suka dinga yada hotunan wannan gada, ana yarfa masa magana; Ciki kuwa harda Shugaban Gwamnatin Kano, ance ya nuna murnarsa akan abinda ya samu gadar.

Daga bisani, bayanai suka tabbatar da cewar wannan tsaga ta kan gadar, ba ta rashin lafiya bace, ko samun matsala, illah kamfanin da yayi aikin ya tsara wannan tsaga dan sanya wasu alamau. Allah masani. Abinda ya tabbatar da cewar Gadar da masu hamayya da Lado ke kira da Mai Doron Zabuwa ba tsagewa tayi ba, shi ne cigaba da amfani da ita da aka dinga yi har kawo yau, wannan ya kara tabbatar da cewar gadar lafiya lau take.

Sai gashi kimanin wata guda bayan wancan yarfe da akaiwa Gadar Mai Martaba Sarki mai rasuwa, wata gada da aka samar a unguwar Dorayi cikin karamar hukumar Gwale mai kama da Ramin Kurege, ta rufto akan motar wani dan kabu-kabu da akai imani yana dauke da mutum hudu har da shi na biyar. Dukkan mutanan da ke cikin motar Allah ya yi masu rasuwa. Muna adduar Allah ya jikansu ya gafarta musu ya kyauta bayansu. Allah kuma ya kare aukuwar hakan anan gaba.



Har ila yau, kasa da awanni 24 bayan wannan hadari, gadar dake dorayin ta kuma subucewa ta zaftaro kasa, wannan karo Allah ya takaita domin akan Adaidaita Sahu ta fado, babu rahotannin asarar Rai. Allah ya kare mu daga sake samun aukuwar irin wannan hadari a nan gaba.

Ba shakka, a baya, abinda Gwamnan Kano da masu goyon bayansa sukai na terere da gadar lado da nuna farin ciki akan samun matsalar da gadar tayi a cewarsu, basu kyauta ba. Domin kuwa wannan gada anyi ta ne domin amfanin al'umma, watakila Lado sai ya shekara bai bi ta kan gadar ba, amma al'umma na amfani da ita kullum ranar Allah. Lallai jama'a suji tsoron Allah, su sani ba muda wani gari ko jiha da ta wuce Kano, duk wani abu na cigaba domin amfanin al'umma bai kamata ya zama an siyasantar da shi har ya zama abin zolaya ba.

Wannan hadari kuma da ya faru akan gadar dorayi, muna kira da babbar murya ga Gwamnatin Kano, bayan an biya diyyar wadan da suka rasu kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar, kuma lallai ne a yi bincike na gaskiya domin gano musabbabin wannan hadari, domin kaucewa fadawa irinsa anan gaba. Sannan duk wadan da suke da sakaci a wajen wannan rugujewar matukar akwai sakacin to a hukuntasu daidai da abinda suka aikata.

A koda yaushe ana son Musulmi ya kasance mu yawaita fatan alheri garemu ga al'ummarmu da kasarmu. Ba daidai bane, dan wata masifa karama ko babba ta samu wasu abin ya zama abin dariya ko zunde ko zolaya ko a maida abin siyasa ba. Allah ya kara kiyayewa.

Yasir Ramadan Gwale
27-10-2015

Saturday, April 18, 2015

Abin Da Ke Faruwa A Sawuz Afurka: Kalubalen Gwamnatin Najeriya


ABINDA KE FARUWA A SAWUZ AFURKA: KALUBALEN GWAMNATIN NAJERIYA 

Ba shakka wannan lamari yayi muni matuka, abu ne mai karkada zukata idan mutum ya kalli hotunan yadda ake Bankawa mutane wuta da ransu a sawuz Afurka. Ni kam, nace Allah ya isa, ga duk wadan da ke aikata wannan ta'addanci,  ba maka wa masu aikata irin wannan kisa na al'ummar da basu jiba basu gani ba zasu gamu da fushin Allah.

Abin akwai daure kai yadda ake ta yayata wannan batu a duniya, amma har yanzu babu wani kwakkwaran mataki da Gwamnati a Johannesburg ta dauka dan magance cigaban wannan ta'addanci, sannan tarayyar Afurka bata yi wata suka da kakkausar murya akan Gwamnatin Shugaba Zuma ba. Allah ya isa akan wannan ta'addanci.

Lallai ya dace Gwamnatin Najeriya ta dauki mataki na gaggawa domin kubutar da rayukan 'yan Najeriya da ke can. Akwai abin takaici da rashin tunani, a lokacin da kasashen turai ke mancewa da bambance bambancensu suna dunkulewa su zama al'umma daya, suna rayuwa ta bai daya, sannan ace mu mutanan Afurka jahilci da dabbanci yana kara bayyana a tare da mu.

Mu 'yan Afurka Turai suka hada baki suka bautar da mu, suka kakaba mana wasu abubuwa da basu dace da al'adunmu ko addinin mu ba, a lokacin da ya kamata ace mun hadu mun kalubalanci bautar da mu da akai, mu jingine duk wani kaya na Bature mu dauki namu da suka dace da yanayi da al'adunmu amma sannan ne zamu maida kanmu baya.

Wannan abin da yake faruwa a Afurka ta kudu, nayi Imani ba wai kawai akan bakaken mutane ake huce haushi ba, akan 'yan Najeriya ne, kuma wannan batu ba wai kawai a SA ba, har da sauran kasashen Afurka suna da irin wannan mugun nufi da tunanin 'yan Najeriya sun zo musu kasashe suna cine musu arziki.

Kuma wannan al'amari idan ba Gwamnatin Najeriya ta dauki Matakin da ya dace ba, 'yan Najeriya zasu fuskanci kalubale da yawa a kasashen Afrika da na larabawa.  Lallai tilas Gwamnati ta dauki Matakin da ya dace, dan magance faruwar wannan dabbanci da jahilci da ke tsiraita dan Adam.

Haka kuma, dole 'yan Najeriya a duk inda suke su hada kansu, sannan su zama jakadu na gari ga kasarsu. Sau da yawa mu muke bayar da dama a duk wani cin fuskar da ake mana, daya daga cikin kasashen larabawa wani yace idan kaji an kama masu laifi goma zaka samu 4 ko 5 'yan Najeriya ne. Kullum mune sata, fashi, Damfara,  almundahana, zamba-cikin-aminci, yankan-baya, kwace, zina,  caca,  shan-giya da sauran nau'ikan laifuka duk mune. Ya zama dole mu sauya halayen mu,  mu mutunta kanmu, mu girmama kanmu, sannan duniya zata ga mutunci da darajar mu. 

Yasir Ramadan Gwale 
18-04-2015

Thursday, April 16, 2015

Bazuwar Labarin Kanzon Kurege A Facebook


BAZUWAR LABARUN KARYA A FACEBOOK 

A 'yan kwanakin nan, ana ta baza ko yaya ta labaran kanzon kurege wadan da ba su da tushe balle maka anan facebook. Babban abinda yake bani mamaki shi ne yadda wasu kan dauka duk labarin da suka gani a facebook gaskiya ne, ba tare da bincike ko tabbatar da sahihancin da kafar da labaran ya fito ba sai kawai mutane su hau yadawa. Ya isa a kira mutum makaryaci idan duk labarin da yaji zai yada.

Tun bayan da aka kammala zaben Shugaban kasa wasu shafuka a Internet da facebook suke ta yada jita jita mara kan gado. Misali a kwanakin nan an ta baza wasu labarai na karya wai sabon zababben Shugaban kasa Yaki ganawa da Abdullahi Inde Dikko babban Shugaban hukumar kwastam  ta kasa,  wanda ko kusa wannan bai yi kama da gaskiya ba, sananne ne cewar tunda Buhari yaci zabe gidan sa a Bude yake ga duk masu zuwa taya shi murna, hatta masu wasan kwaikwayo sun je sun taya shi murna balle kuma ace Shugaban hukumar kwastan, wanda jiharsu daya da Buhari. Wannan labari na karya babu wata sahihiyar kafa da ta ruwaito shi sai dai wasu shafaka na makaryata.

Haka nan, aka dinga yaya ta cewar wai tsohon Shugaban kasa Olushegun Obasanjo wai ya maida kudi kimanin  $200 Miliyan zuwa asusun Gwamnati kuma wai yayi alkawarin tonawa wasu asiri matukar basu dawo da abinda suka dauka ba, kaga wannan labari duk mai hankali da sanin meye Gwamnati ya san ko kadan ba gaskiya bane. Haka nan fa, aka dinga yada cewar wai kudin nan $20Bilian da tsohon Gwamnan babban bankin kasa Sanusi Lamido yace ba'a shigar da su Bankin ba wai anga kudin a Bankin Zenith.

Sannan kuma a wannan Makon aka kawo labarin cewar wai Bankin Duniya ya fitar da sunayan manyan Barayin Najeriya, inda aka dinga bada sunayan wasu fitattun mutane wai sune manyan barayi, kaga dai duk mutum mai tunanin ya san duk wadannan labaru basu yi kama da gaskiya ba. Ko kuma mutane su dauki hoton wani mutum ko wani shugaba a wata munasaba da ta faru a baya, su jingina da wani abu da ya faru a yanzu, su kuma mutane babu bincike kawai sai su yada. Yana da kyau mutane suji tsoron Allah wajen yada labarin karya.

Shafaka da dama irinsu Hope for Nigeria, Scannews, report247, Naijagossip, Hausa24​ da sauransu da dama duk sun shahara  wajen yada jita jita da labarin karya a facebook. Hatta gidan jarida irin Rariya​ su kansu sukan tsinci irin wadannan labarai a facebook su yi musu kwaskwarima  su yada ba tare da tantance wa ba. Wannan basu san cewar rage musu kima da daraja yake yi ba. Kafafan yada labarai irinsu Premium Times​ da Leadership Newspapers​ da Daily Trust​ da BBC Hausa​ da VOA Hausa Service​ labaransu yafi kusa da gaskiya, duk da cewar ba zaka ce dari bisa dari duk abinda suka fada gaskiya bane, amma basu cika yada jita jitar wani abu da bai faru ba, musamman a siyasar Najeriya. 

Haka wata rana, wani Malami, daga ganin irin wadannan labarai a facebook  kawai ranar juma'a yana huduba ya dinga kafa hujja da irin wadannan labarai na karya, sai da aka idar da Sallah wani ya same shi yake tambayar sa gaskiyar abinda ya fada, Malamin budar bakin sa sai cewa yayi ga abu nan duk ya cika internet da social media,  mutumin ya cewa Malamin shin yanzu duk abinda ka gani a littafi gaskiya ne? Abu ne mai cike da takaici da damuwa kaga mutane masu kima suna yada irin wadannan labaru marasa tushenmu balle makama. 

Lallai yana da kyau, mutane su kiyaye wajen gaggawar yada irin wadannan labaru na kanzon kurege. Godiya ta musamman ga  Doc. Ibrahim Musa da Jaafar Jaafar​ da suka ja hankalinmu akan yada jita jita da ake ta faman yi a yanzu.

Yasir Ramadan Gwale 
16-04-2015

Wednesday, April 15, 2015

Yasir Ya Taya Takai, Ribadu, el-Rufai Dankwambo Murnar Zabe


YASIR YA TAYA TAKAI, RIBADU, EL-RUFAI, DANKWAMBO MURNAR ZABE 

Dazu muka yi waya da Malam Muhammad Salihu Sagir Takai dan takarar Gwamnan mu na PDP a Kano. Na taya shi murnar wannan zabe tare da yi masa godiya bisa kyawawan halayen da ya nuna a yayin wannan zabe. Na shaida wa Malam Salihu cewar mu da muka ce mun ji mun gani akan wannan al'amari na sa, hakika munyi Nasara a wannan zabe, domin mun ji kuma mun gani yadda al'mma ta nuna kauna da soyayya dan Allah ga wannan tafiya, kuma ko kadan bama yin nadama ko da-nasani akan abinda muka kudurce muna yi da gaske, domin cigaban al'umma da addini a jihar Kano ba. 

Malam Salihu cikin farin ciki da annashuwa ya shaida min cewa wallahi yana gani kuma yana jin labarin dukkan irin kokarin da muke, ya kuma kara da cewa, shi al'amarin nema irin wannan daman dole daya ne zai samu a cikin masu nema, sannan yace, a duk abinda Allah ya hukunta babu kuskure a ciki. Daga karshe na sake tabbatar masa cewa wannan Nasara domin bamu dauke ta faduwa ba, babu abinda zata sanya mana sai karin tabbata akan manufa tare da kyautatawa Allah zato! 

Sannan kuma, ina taya Malam Nuhu Ribadu murnar Nasarar wannan zabe. Hakikanin gaskiya, tunda Ribadu ya shiga wannan takara ban taba jin an zarge shi da  rashin cancanta ko dacewa da zama Gwamna ba, illa kawai abinda wasu ke ganin Malam Nuhu Ribadu ya fito a jam'iyyar PDP shi ne dalilin faduwarsa,  wanda wannan tunanin kuskure ne, Mulki Allah ke bayar wa,  kuma shi ke hukunta wanda ya so dan ya zama Shugaba a lokacin da ya so. 

Hakan nan a Jigawa, ina taya Malam Aminu Ibrahim Ringim murnar Nasarar wannan zabe. Na so ace Malam Aminu ya Dora daga inda Gwamna Sule Lamido zai tsaya, amma Allah bai hukunta  hakan ba. Ina masa fatan alheri. 

A wannan zabe ina mai cike da farin cikin Nasarar da Malam Nasiru el-Rufai ya samu a Kaduna, ina fatan Malam Nasiru zai baiwa al'umma mamaki wajen kawo ayyuka na cigaba wadan ba Kaduna kadai zasu amfana ba har da Arewacin Najeriya. 

Haka nan, ina jinjinawa mutanan Gombe, da suka fito suka tsaya wajen tabbatar da zab'in da suke ganin shi ne daidai domin cigaban jiharsu, duk da jafa'I da mugun baki da su Danjima Goje sukaiwa PDP wannan bai hana ta cin zabe a Gombe ba, wannan kuma na kara tabbatar mana da yadda al'umma suka duba cancanta ba inna rududu ba.

Ina fatan alheri ga duk wadan da suka ci zabe ko aka ce sunci zabe, ina fatan alheri ga Gwamnan Kano Gonduje, ina fatan Allah ya basu ikon sauke nauyin alkawarin da aka daukarwa al'umma. Ko da Alkawari ko babu Mulki / Shugabanci amana ne akan duk wanda yake kansa. Idan yayi gaskiya zai tsira kuma zai rabauta har a wajen Allah, wanda duk ya kaucewa gaskiya yabi san zuciya, yabi hanyar zalince to ba shakka shi ne wanda zai Fi kowa takaici a ranar da mulki ba zai amfana masa da komai ba sai nadama mara amfani. 

Allah ka bamu alherin da ke cikin wadannan Shekaru hudu da zamu shiga na mulkin Demokaradiyya, ka kare mu daga dukkan wani sharri, musamman na asarar rayuka da dukiya. Allah karaba mu da Boko Haram ka raba mu da barayi, ka raba mu da masu magudin zabe. Allah ka taimaki Najeriya. 

Yasir Ramadan Gwale 
15-04-2015 

Saturday, April 11, 2015

Rahoto Daga Kano Dangane Da Zaben Gwamna


RAHOTO DAGA KANO

Da yawa mutanen da suke wajen Kano gani suke kamar mafarki idan ance musu Allah ya bawa Takai Gwamna har ka ji wasu suna izgili ko wani abu makamancin haka.

Inama ace wanda suke wannan tada jijiyar wuyar 'yan Kano ne, da a yau sun ganewa idonsu cewa Kano ta Takai ce da ikon Allah. Akasarin mutanen da suka fito zabe yau idan ka ga mutum goma to bakwai ko takwas za ka ji suna fadin Takai za mu zaba ko ba a bamu ko sisi ba.
Wannan ya canja min tunani na cewa wai kalmar SAK za ta yi aiki a Jihar Kano, sai yau na tabbatar ba dai a garin Kano ba sai dai ko a wata Jihar.

Duk da wannan albishir da muke gani kuma muke ji, wannan bai isa ya sa muke cika baki da kambami ba, illa kawai mu godewa Allah kuma mu kara risunawa gare shi kan ya taimake mu ya bawa Malam Salihu Sagir Takai Gwamnan Kano a wannan zabe da yake gudana yanzu.

Wakilinmu ya sanar da mu halin da ake ciki. Dan haka muna kara kira ga magoya da magoya bayan Malam Salihu Sagir Takai  da su fito domin wannan zabe. Allah ya bamu Nasara,  ya baiwa Malam Salihu Sagir TAKAI Nasara akan abokan karawarsa. Barayin kuri'u kuma Allah ya shirye su, ya hana musu sa'a.

Yasir Ramadan Gwale 
11-04-2015 

Kuri'ar Jin Ra'ayin Jama’a A Kano Ta Nuna Cewar Takai Ne A Gaba


KURI'AR JIN RA'AYIN JAMA'A A KANO TA NUNA TAKAI NE A GABA

A sakamakon farko na kuri'ar jin ra'ayin jama’a da Shafin Taskira suka fitar ya nuna cewar dan takararmu Malam Salihu Sagir Takai na jam'iyyar PDP shi ne a gaba da kaso 58 a yayin da Umar Abdullahi Gondoji na jam'iyyar APC yake biye da shi da kashi 30. Babu shakka wannan sakamako mai faran ta rai ne a wajenmu. In sha Allah irin wannan sakamako zamu samu bayan kammala zabe a gobe In Sha Allah. Allah ya bamu Nasara. Kano Sai Takai.

Yasir Ramadan Gwale 
10-04-2015

Lamurje Dan Zaben Gwamnan Na Kano


LAMURJE DAN ZABEN GOBE

Alhamdulillah yanzu na dawo daga kasuwa wajen neman Zoborodo, kuma na samu har na jika Lamurje abin sha na Musamman domin zaben gobe. Idan Allah ya kaimu gobe Asabar ina kara yin kira ga al'ummar jihar Kano da su fito fitar farin d'ango dan kad'awa Malam Salihu Sagir Takai kuri'u masu train yawa. In Sha Allah ba zamu baiwa al'umma kunya ba idan Allah ya bamu wannan Nasara. Allah ya bamu Nasara kuma yayi mana jagora. Ya Allah a wajenka muke nema kaine mamallakin mulki kai ke bada shi ga wanda kaso, Ya Allah mun kyautata zato a gareka zaka bamu Nasara a wannan zabe. Allah ka amincewa Takai ya zama Gwamnan Jihar Kano a wannan zabe da za'a gudanar a gobe. Kano Sai Takai.

Yasir Ramadan Gwale 
10-04-2015

Thursday, April 9, 2015

In Sha Allah Idan Mun Ci Zabe Zamu Sha Lamurje


IN SHA ALLAH IDAN MUNCI ZABE ZAMU SHA LAMURJE 

Ina amfani da wannan damar nayi kira ga dukkan abokina da 'yan uwana na kusa da na nesa da dangi dake Kano da su fito ranar Asabar su zabi Malam Salihu Sagir Takai​ a matsayin Gwamnan Kano na gaba. Alamar jam'iyyar mu ita ce Lema, a duba daidai wajen da aka rubuta PDP a dangwala a inda aka ware dan yin hakan. Munyi muku alkawarin In Sha Allah ba zamu baku kunya ba, zamu yi Gwamnatin al'umma domin hidimtawa al'ummar jihar Kano. 

Dan takarar mu Malam Salihu Sagir Takai yayi Shugaban karamar hukuma yayi kwamashinan kananan hukumomi da na Ruwa amma ba a sameshi da cin dukiyar al'umma ba bisa ka'Ida ba. Ya fada da bakin sa cewar duk wanda ya gani ko ya sani ko ya tabatar shi Malam Salihu Sagir Takai yaci dukiyar Gwamnati ba bisa doka ba, yace idan ya rufa masa asiri ya cuci al'umma, Alhamdulillah har yau babu inda aka samu Malam Salihu da diban dukiyar al'umma ba bisa doka ba. 

Dan haka muna tabbatar wa da al'ummar Kano inganci da nagarta  da amana na dan takarar mu Malam Salihu Sagir Takai, yayi shugabanci abin misali, dan haka mun tabbatar zai iya wannan aiki na Gwamnan Kano. Jama'a a fito ranar zabe a zabi Malam Salihu Sagir Takai na jam'iyyar PDP domin cigaban Jihar Kano.

Haka nan kuma, muna kiran al'umma musamman magoya baya da su fita kasuwa a gobe su sayo Zoborodo  da citta da kanam-fari da masoro  a jika a cikin kyakkyawaan  mazubi a sanya sukari da kankara domin yin murna da nuna godiya ga Allah a yayin  da aka fadi sakamakon zabe.

Zamu sha lamurje ne sabida yafi kara lafiya da kuzari,  sannan hakan zai taimaka wajen habaka tattalin arzikin 'yan kasuwar mu na kurmi dake kasuwancin  citta da kanam-fari da masoro.  Sannan ga wadan da suke da hali suma su tanadi tinkiya b'atala mara kitse dan shan shagali. Dan uwa uwa Malaminmu Dakta Jamilu Zarewa​ yayi fatawa akan halarci a nuna murna ta irin wannan siga aci asha a gode wa Allah.

Allah ya bamu Nasara, ya tabbatar mana da alheri a jihar mu da kasarmu baki daya. Allah yasa ayi zabe lafiya a gama lafiya, Allah ya bamu Nasara akan abokan takarar mu.  Dan takararmu Ya Allah idan ka bashi Nasara kayi riko  da hannunsa  kayi masa jagora, Ya Allah Kada ka barshi da iyawarsa. Kano Sai Takai In Sha Allah.

Yasir Ramadan Gwale
09-04-2015 

Gugawar Sauya Sheka Daga PDP zuwa APC: Koma Baya Ne Ga Demokaradiyyar Najeriya


GUGUWAR SAUYA SHEKA DAGA PDP ZUWA APC:  HADITHUR-ROUH!

Hamayya ko Adawa a siyasance, ita ce ke motsa tafiyar siyasar Demokaradiyya. Yin Hamayya mai ma'ana da nufin zaburar da masu mulki dan aiwatar da kyawawan manufofin da suka yiwa al'umma alkawari  da kuma kalubanatar manufar Gwamnati da ka iya durkusar da kasa, wannan shi ne abinda Demokaradiyya ke bukata a tsarin Hamayya.  Amma a yayin da aka ce Gwamnati bata samun Hamayya mai karfi daga jam'iyyun Adawa, wannan shi ne kansa Shugabanni kanci karensu babu babbaka, daga nan sai Demokaradiyya ta koma kama karya, kamar yadda hakan ke faruwa a Galibin kasashen Afurka  musamman na Arewaci, idan muka dauki Sudan da Masar da Tchadi da Algeria, dukkansu Gwamnatoci ne da suke kiran kansu na Demokaradiyya amma sabida rashin kakkarfar Hamayya dan amfanin siyasa da 'yan kasa sai ka mance ana yin Gwamnatin Demokaradiyya  a wadannan kasashen. 

Kasashen da suke da tsayayya kuma shimfidaddiyar Hamayya sun fi saurin samun cigaba cikin sauri,  domin Gwamnati na da masaniyar al'mma na iya juya mata baya, dan haka irin wadannan Gwamnatoci kan tsaya suyi aiki bilhakki da gaskiya. Hamayya mai ma'ana kan sanya Shugabanni da jam'iyyu shiga taitayinsu da kuma hidimtawa al'ummar su gwargwadan karfin su. Kyakkyawan misali akan haka itace kasar Amurka inda Hamayya ke da karfi, kuma Gwamnati kan shiga taitayinta wajen aiwatar da manufofin gina da kuma cigaban kasa. Anan kusa da mu muna ganin yadda Hamayya ke motsa Gwamnati a jimhuriyyar Nijar da sauran kasashen irinsu Senegal.

Guguwar sauya sheka daga PDP zuwa APC da ta kunno kai tun bayan da jam'iyyar Hamayya ta APC ta samu Nasara a zaben Shugaban kasa da na majalisun dokoki, wannan ba zai haifarwa Demokaradiyya d'a mai ido ba a Najeriya. A baya rashin samun jam'iyyar Adawa mai karfi a Nigeria shi ya sanya Gwamnatin PDP tunanin zata iya shekaru 60  ba tare da an tankwabe mulki daga hannun ta ba. Amma tun bayan da jam'iyyar APC ta kafu, PDP  ta shiga taitayinta ta fahimci yanzu ba da bane.  Misali adawa ta sanya Gwamnati tayi fatali da yin dokar aure jinsi a Najeriya da sauransu da dama.

Haka kuma, Hamayya ta sanya Gwamnatin PDP daukar matakai dan magance tsaro a baya-bayannan. Babu ko shakka, Hamayya ita ce gishirin Demokaradiyya, wannan kuma ke sanya gwamnatoci su himmatu wajen biyan bukatun al'umma. Amma abin da yake faruwa a yanzu na guguwar sauya sheka da wasu 'yan PDP suke zuwa APC wannan ya nuna kwadayi da kulafucin neman mulki irin na 'yan siyasar wannan lokacin, wannan na kara tabbatar da cewar da yawan 'yan siyasar ba hidimtawa kasa ne a ran su ba illa kawai rike madafun Iko dan biyan bukatun kansu. 

Ni sai naga kamar akwai rainin wayo ace mutum yana PDP tsawon Shekaru 16 yana ta yiwa 'yan Hamayya gwalo da fatan tsiya, amma yanzu kawai dan PDP  ta rasa mulki yace ya barta wai babu adalci a cikin ta,  wannan ya zama wasa da hankalin 'yan Najeriya. Idan aka wayi gari duk wani kusa na siyasa a PDP Ya fice ya koma APC  to su wa za'a kalubalanta  dangane da abubuwan da suka faru a baya?

Kamar yadda tsohon Shugaban kasa Obasanjo duk da irin tsayar da ya taka,  da aikata muggan laifuka na magudin zabe, da yunkurin karya tsarin Mulki dan tabbatar da kansa a matsayin Shugaban kasa da kassara kasa, shi kenan sai ya zama mutumin kirki dan ya goyi bayan APC? Idan aka wai gari shima Goodluck Jonathan ya koma  APC  ya kenan, su waye zasu cigaba da amsa gazawar PDP a shekaru 16?

Ya zama tilas talakawa su tashi su farka su sani cewar da yawan 'yan siyasa tara tara sukai mana, ta yadda ake san maida neman Shugabanci ya zama gado ko kuma sai wasu tsirarun mutane da suka taba rikewa a baya, mutane su gama shuka tsiya a PDP  sannan rana tsaka su koma APC  sannan a ce sune mutanan kirki,  su ne zasu sake zama wane da wane? Mutum idan ya rasa mukami anan ya koma can kuma kaga anbashi. Wannan tsiya har ina!

Dan haka dole sabon Shugaban kasa yayi taka tsantsan da baragurbin da ke neman durkusar da Demokaradiyar Najeriya. Buhari shi ne Shugaban da  zai Fi kowanne Shugaba samun kalubale a Najeriya, domin shi ne wanda duk ido ke kansa, kuma ake da yakinin dari bisa dari gyara yazo yi ba neman mulki ko tara abinda duniya ba. Dan haka samun mutane wadan da zasu hidimtawa al'umma shi ne mafita a gareshi.

Yasir Ramadan Gwale 
09-04-2015

Sunday, April 5, 2015

Ba Shakka Mutane Da Yawa Sun Jahilci Maganar Sheikh Gumi


BA SHAKKA JAMA'A DA YAWA SUN JAHILCI MAGANAR SHEIKH GUMI

Mutane da yawa suka dinga suka da zagi da cin zarafin Sheikh  Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi​, akan maganar da yayi kan tambayar da akai masa bayan samun Nasarar sabon Shugaban kasa Muhammadu Buhari​Hakika, da yawan mutane sun zagin Sheikh Gumi akan abinda suka dinga yadawa akansa, alhali ba gaskiya bane, mafiya yawancin masu zagin Sheikh Gumi ko dai basu karanta abinda ya fada sun fahimta ba, ko kuma basu saurari ainihin hirar da akai da shi a  VOA Hausa Service​ ba, domin a zahirinmu gaskiya bayanan da yayi kwata kwata basu yi kama da abubuwan da aka dinga yadawa cewa shi ya fade su ba.

Ya kamata mutane suji tsoron Allah, su dinga sauraron mutane da kunnen basira  kafin yanke musu hukunci. Wannan zalince ne a dinga jinginawa MALAMAI abinda basu ce ba, kawai dan bayar da dama ga magauta su Zage su.  Da yawan 'yan Shia da masu bakar adawa da nuna kiyayya ga Sunnah sukai amfani da wannan karairayi da aka yada akan Sheikh Gumi suka ci zarafin sa.  

Daga cikin masu adawa da Sheikh Gumi har da wasu gurbatattun Ahlussunnah da santsi ya kwashesu suke nema su kore shi Malamin daga Sunnah, wal'I ya zu bill!  Wace riba zaka samu a matsayin ka na Ahlussunnah a kokarin da kake ta yi na nunawa mutane Sheikh Gumi ya sabawa Sunnah tun fil azal  ko kuma ba Sunnah yake kira akai ba. Bana jin akwai wata burgewa akan haka, in ba neman suna a wajen wadan da basa ganin kamar duk wani Ahlussunnah ba.

Allah ya sakawa Sheikh Gumi da alheri ya kyauta bayansa. ina rokon sa akan ya yafewa duk wadan da suka zargeshi ko suka ci zarafin sa bisa jahiltar abinda ya fada. Allah mai afuwa ne yana son Afuwa. Amma lallai mutane suji tsoron Allah akan irin wadan nan maganganu da basu da ainihin masaniyar abinda aka ce. Ya kamata kafin mutum yayi zargi ya tabbatar da sahihancin batun da yake san yayi kalubale akansa.

Ga ainihin hirar da aka yi da Malam wanda wasu marasa tsoron Allah suka fassara à gurbace  dan bayar da dama a ci zarafin Malamin.  Ga abinda Malam yace: Saukar da wannan tattaunawa kuma ka saurareta da kunnen sauraro cikin natsuwa kafin ka yanke wa kanka hukunci http://www.dandalinsunnah.com/mul…/AhmadGumi/drbayanzabe.mp3

Yasir Ramadan Gwale
05-04-2015

Friday, April 3, 2015

Darasin Da Buhari Zai Dauka Daga Rusasshiyar Gwamnatin Mursi Ta Masar

WANE DARASI BUHARI ZAI DAUKA DAGA RUSASSHIYAR GWAMNATIN MURSI TA MASAR? 

A lokacin da ake ganin wata gugawar sauyi ta fara kadawa a kasashen Arewacin Afurka da ta faro daga Tunisiya, masana da masharhanta sunyi fashin baki sosai akan yadda wannan guguwa zatai awon gaba da shugabanni da dama musamman masu kama karya da sunan Demokaradiyya. Wannan guguwa bayan da tayi gaba da Zain el-Abideen Ben Ali babu zato ba tsammani, ta cigaba da bugawa nan da can a kasashen larabawa. 

Dubu dubatar Misrawa ne suka fito kan tituna suna rera wakokin canji tare da Allah wadai da shekaru 30 na Gwamnatin kama-karya ta Muhammad Hosny Mubarack. Mista Mubarack yaga ta kansa lokacin da al'umma ta hadu a dandalin 'yanci na Tahrir dan kira a gareshi ya san inda dare yayi masa. Ba shiri Mubarack yayi sallama da kujerar da ya shafe sama da shekaru 28 yana rike da ita a matsayin Shugaban kasa.

Bayan da Mubarack ya tafi ne, aka shiga fafutukar ganin wanda zai gaji Gwamnati, inda Ikhwanul Muslimin​ sukai tasiri kwarai da gaske a yayin wannan guguwa ta sauyi. Lokacin da zabe yazo gab ne, ba zato Allah ya kutso da Muhammad Mursi, inda Miliyoyin al'ummar Misrawa suka hadu akan Allah ya baiwa Mursi Shugabancin kasar. Duk da irin mahaukatan kudade da su Ahmed Shafeeq wadan da gyauron Gwamnatin  Mubarack ne sukai amfani da su a wannan zabe, amma sai da guguwar sauyi ta tabbatar da Mursi a matsayin sabon zababben Shugaban kasa na farar hula a karon farko a tarihin Demokaradiyyar Masar.

Bayan da Mursi ya zama sabon zababben Shugaban kasa, duniya baki daya ta zura masa ido taga wacce irin Gwamnati Muhammad Mursi da kungiyar Muslim Brotherhood zasu yi. Misrawa sun zabi Mursi tare da kyakkyawar fatan cewar zai fitar da su daga halin kangi da danniya da babakere da ake ganin anyiwa Masar tun zamanin Gamal Abdel-Nassir.  A gefe guda gyauron Gwamnatin Mubarack  basu yi kasa a guiwa ba wajen ganin Gwamnatin Ikhwan karkashin Mursi bata ci Nasara ba, sannan a daya gefen ga Misrawa na ci-da-zuci da fatan ganin sha-yanzu magani-yanzu.

Misrawa sunyi gajen hakuri tare da gaggawa gami da gandokin ganin Gwamnatin Mursi ta gyatta Barnar da Mubarack yayi cikin kusan Shekaru 30 a cikin kankanin lokaci. Ba shakka Mursi an kyautata masa zaton cin Nasara da kaso mafi rinjaye a Gwamnatin sa. Sai dai tafiya ba tayi Nisa ba Misrawa suka fara zargin Mursi da fifita wani sashe a matsayin sune kadai wadan da zasu baiwa Gwamnatin sa shawarar yadda za'a aiwatar da al'amuran Gwamnati, da kuma yunkurin da Mursi yayi na baiwa kansa iko da karfi karkashin tsarin Demokaradiyya.

Sannan kuma, Gwamnatin Mursi ta shagaltu da yin Shari'ah ga hambararren Shugaba Mubarack  wanda duk da wannan guguwa da tayi awon gaba da Mubarck yana da dumbin magoya baya masu yawan gaske. Ba'a je ko ina ba, aka sabauta Gwamnatin Mursi ta yadda gyauron Gwamnatin Mubarack suka dinga yiwa Gwamnati adawa mai karfin gaske, a gefe guda kuma ana zuga al'umma akan cewa Gwamnati na tafiyar hawainiya, wannan ta sanya Misrawa suka kasa baiwa Gwamnatin Ikhwan karkashin Jagoranci Mursi uzuri. Inda cikin shekara guda tal al'umma suka koka da Shugabancin Mursi. Kai ka ce ba sune sukai fitar farin dango wajen nuna soyayya da kauna gareshi ba.

Galibin mutanan da suke wajen kasar Masar wannan al'amari yazo musu da bazata, domin shekara daya tak bata kai ace sabon Shugaban kasa har ya fahimci yadda zai tafiyar da Gwamnatin sa ba ya aiwatar da sauyi sauye. Al'Amura da yawa sun faru, inda Misrawa sukai gajen hakuri suka kasa jurewa abinda suka jima suna mafarki na samun canji, suka sake fitowa kwai da kwarkwata suna Allah-wadai da Mursi da Kiran ya sauka ya basu waje. Yanzu dai ga yadda Mursi ya kare daga mutumin da ake tsananin kauna zuwa fursuna, sannan kuma Gwamnati ta koma hannun da ta baro. Allah mai iko!

Ba shakka akwai darussa masu dumbin yawa da sabon zababben Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari​ zai dauka daga Rusasshiyar Gwamnatin Mursi ta Masar, sannan suma al'ummar Najeriya dole su dauki darasi daga al'ummar kasar Masar na yin hakuri da juriya da kuma yiwa sabon Shugaban kasa fatan alheri da fatan kawo sauyi mai ma'ana a sha'anin tafiyar da Gwamnatin Tarayyar Najeriya. Duk da cewa Buhari yana da gogewa ta Mulki yayi Shugaban kasa yayi Gwamna yayi Minista sannan kuma ya shiga takara ba sau daya ba dan haka ne ake sa masa ran cewa zai kawo sauyi cikin kankanin lokaci. Amma dai ba shakka 'yan Najeriya da Sabon Zababben Shugaban kasa zasu dauki darussa daga Rusasshiyar Gwamnatin Mursi. 

Yasir Ramadan Gwale
 03-04-2015

Thursday, April 2, 2015

KANO: Tsakanin Mutanan Shekarau Da Na Kwankwasiyya


KANO: DANGANE DA BATUN TAKARAR GWAMNA, TSAKANINMU DA 'YAN KONKOSIA 

Mutane irinsu Jaafar Jaafar​ da Auwal Lawan Aranposu​ da Ibrahim Musa da Fatuhu Mustapha​ da sauransu da dama idan muka yi addu'ah cewa Allah Ya Bawa Takai Nasarar zama Gwamnan Jihar Kano dariya suke yi suna ganin, babu yadda za ai Gwamnatin Kano ta subuce  daga hannun su.  Kamar yadda wasu daga cikin 'yan uwanmu a PDP ke ganin mulki ba zai taba kwace musu ba. Amma mu a ko da yaushe fatan alheri muke yiwa Kano da al'ummarta, akan wanda zai zama Gwamna na gaba bayan Rabi'u Musa Kwankwaso.

Muna tabbatar wa da 'yan uwanmu na Konkosia cewa, Allah ne ya shimfid'a ka'Ida yace ku rokeni zan amsa muku, dan haka ne a kullum muke rokon Allah akan wannan takarar Gwamna. Bamu yi girman kai ko dagawa ko ji da isa ba, Allah muka roka sannan muka roki mutanan Kano da su baiwa Malam Salihu Sagir Takai dama a wannan zaben dan zama sabon Gwamnan Kano.

Muna cike da sanin cewar mulki na Allah ne, yana bayar da shi ga wanda ya so,  a duk lokacin da ya so, kamar yadda tarihi ya nuna a 2003 a Kano, da kuma zaben da ya baiwa Buhari Nasara.  Sau da yawa wasu kan zata cewar idan Allah ya basu mulki su shi kenan, wallahi mulki jarabawa ce mai wahalarci, wasu mulki halaka ne a garesu, wasu kuma Rahama ne, amma sabida yadda Sunnar take dole a samarwa da al'umma jagoranci ta irin wannan hanya shi yasa muma muke neman a zabi Takai.

Har kullum addu'ar mu ita ce, idan Takai shi ne mafi alherin zama Gwamnan Kano a wannan zabe Allah ya bashi, ya yi masa jagoranci, ya bude masa kofofin alheri, idan kuma Gandujiyya ne zai Fi zamarwa Kano alheri shima addu'ar mu Allah ya bashi, yayi masa jagora.  Kuma idan har da gaske 'yan uwanmu na Konkosia Kano ce da al'umma a gaban su suma yiwa Jihar Kano wannan adduar tsakanin Takai da Ganduje. 

Wannan ce ma ta sanya a kullum muke Jan hankalin mutanenmu cewar bamu yarda a muzanta Ganduje dan a tallata Takai ba, Ganduje a matsayin sa na mataimakin Gwamnan Kano shugaba ne, ya cancanci a bashi dukkan girmama a matsayin sa na shugaba. Amma abin mamaki su 'yan uwanmu na Konkosia sun mayar da hanyar muzanta Takai a matsayin hanyar tallata dan takarar su. 

Ya kamata 'yan uwanmu na Konkosia su sani cewar an wuce wannan lokacin na batanci dan tallata kai, ya kamata su shagaltu da bayyanawa al'ummar Kano irin kudurorinsu idan Allah ya basu mulki. Dan haka mu a wajen Allah muke nemawa Malam Salihu Sagir Takai Gwamnan Kano, idan jama'ar Kano sun gamsu da mu sun zabi Takai ina tabbatar musu ba zamu basu kunya ba, idan kuma sun zabi Ganduje In sha Allah zamu yi masa cikakkiyar biyayya a matsayin sa na Shugaba.

Muna kara yin addu'ar da muka saba Ya Allah idan Takai shi ne zai Fi zamarwa Kano alheri a wannan zabe Ya Allah ka tabbatar masa da kujerar Gwamnan Kano, idan kuma Ganduje ne zai Fi zama alheri Allah ka bashi. Duk da haka muke cewa Allah Ka Baiwa Malam Salihu Sagir Takai Gwamnan Kano.

Yasir Ramadan Gwale 
02-04-2015 

Wednesday, April 1, 2015

Har Yanzu Washington Da London Basu Taya Buhari Murna Ba



HAR YANZU WASHINGTON DA LONDON BASU TAYA BUHARI MURNA BA

Kamar yadda suka sha nanatawa fadar Gwamnatin Amurka dake Washington cewa suna bibiyar halin da Najeriya take ciki, a sakamakon wannan zabe na 2015. Da kansa Shugaba Barack Obama​ ya fitar da sanarwa ta musamman ga al'Umar Najeriya akan su tsaya suyi zabe tsakanin da Allah ba tare da tashin hankali ba. Alhamdulillah 'yan Najeriya sun ji wannan kira sunyi zabe cikin tsanaki, amma har yanzu Washington tayi gum game da Nasarar da Muhammadu Buhari​ ya samu.

Haka nan itama fadar Prime Ministan Burtaniya David Cameron​ dake Lamba 10 Dorning Street tayi shiru, duk da Kiran da Mista Cameron yayi na ayi zabe na gaskiya da adalci, dan tabbatar da Najeriya a matsayin dunkulalliyar  kasa.

Wannan dai zabe ne mai cike da adalci a tarihin Demokaradiyyar Najeriya. Muna cike da masaniyar irin Demokaradiyar da Amurka da Burtaniya suka aiwatar a Algeri da ta kawo Abdulaziz Boutoufiqa. Allah ya kiyaye sabon Shugaban Najeriya daga dukkan masu sharri na gida da na waje.

Idan bamu manta ba Muhammadu Buhari​ yayi alkawarin daga darajar Naira zuwa matsayin damar Amurka,  kamar yadda wasu jaridu suka ruwaito. Allah ya shiga tsakanin Nagari da mugu.

Yasir Ramadan Gwale​
01-04-2015 

Fatan Alheri Ga Zaratan Canji Na Hakika


ZARATAN CANJI NA HAKIKA 

Zanyi amfani da wannan dama wajen kara mika sakon taya murnar Nasarar Gen. Muhammadu Buhari​ ga mutanan da na kira zaratan canji na hakika, wadan da tun da aka faro wannan tafiya sun tabbata akan manufar su basu yi rani ba kullum kara samun yakini suke akan abinda sukai Imani zai faru. Ba shakka wannan Gwagwarmaya da mu aka farota tun a Shekarar 2003 munyi kuka mun zubar da hawaye a baya sabida rashin Nasara, ashe bamu sani ba hawayen da muka zubar na farin ciki ne, jiya Allah ya tabbatar mana da cewa Mulki da iko nasa ne.

Haka kuma, jiya Allah ya nuna mana cewar komaI na da lokaci, babu wani abu da yake zuwa lokacin sa bai yi ba, wannan tafiya an farota tare da 'yan uwa da yawa, wasu sun sare, wasu sun gajiya, wasu sun fidda tsammani, wasu sun saduda, wasu sun mika wuya, amma zaratan canji sun tabbata akan manufa tare da kyautatawa Allah zato! Alhamdulillah.

Sakon fatan alheri ga zaratan canji irinsu Malam Ibrahim Sanyi-Sanyi​ da Kwamared Baban Shareek Gumel​ da Affan Buba Abuya​ da Garba Tela Hadejia​ da Sagir Musbahu Daura Dole​ da Hamza Ibrahim Baba​ da Yakubu Muhammad Rigasa​ da Hamisu Gumel​ da Hisham Habib​ da sauransu da dama da suka tabbata akan manufa tare da  yakinin cewar hakarsu zata cimma ruwa, Alhamdulillah! 

 Mutanan da sukai rawa ko suka sare da wadan da sukai ungulu da kan kaza irinsu Jaafar Jaafar​ da Ibrahim Musa​ da Fatuhu Mustapha​ da kuma abokina Sheriff Muhammad Ibrahim Almuhajir​ wanda kusan kullum ina cike da takaicin sa baya mana kara baya daga kafa amma daga jiya duk na huce. Yayyanmu irinsu Aunty Saratu G. Abdul​ duk da irin cakulkuli da ake mana amma ya zuwa yanzu munyi tarayya wajen nuna farin ciki da murnar mu. 

Abokai da 'yan uwa da muke wannan tafiya tare suma ina taya su murna, Ahmad Abubakar-Dr​, Shamsu Abbaty​, haka nan irinsu Mansur Manu Soro​ da Abdulrashid Ahmad​ da Baba Bala Katsina​ da Muhammad Aliyu Dutsin-Ma​ da kullum ake mana gatsune da cakulkuli duk mun taya juna murna da fatan alheri. Ba  zan manta da abokan Gwagwarmaya  guda biyu da suka riga mu gidan gaskiya ba akan wannan tafiya kamar Dalhatu Mai Chemist Makarfi da  Bilyaminu Adanji Abdullahi​ Allah ya kai Rahama garesu, ina musu bushara da samun sauyin da sukai ta fatan ganin faruwarsa suna raye,  cikin Kaddarawarsa Subhanahu Wata'ala ya tabbatar mana bayan sun rigayemu. 

Haka nan ina kira ga sabon Shugaban kasa Muhammadu Buhari​ da ya rungumi kowa a tafi tare dan samun Nasarar da aka jima ana tsammani da wadan da suka ji haushi suka daina da wadan da suka fusata suka bar tafiyar da wadan da aka fusata da gangan  a yafi kowa a tafi tare dan samar da sabuwar  Nigeria.  Allah ya yiwa sabon Shugaban kasa jagoranci yayi riko da hannunsa wajen aikata dai dai. 

Yasir Ramadan Gwale​
01-04-2015