Tuesday, April 22, 2014

APC: Muhimmin Darasin Siyasa Yarabawa Zasu Koyawa 'Yan Arewa!!!


APC: MUHIMMIN DARASIN SIYASA YARABAWA ZASU KOYAWA 'YAN AREWA!!!

Ba zan taba yarda cewa ba da gayya shugabannin APC na kas suka dinga fusata wasu 'yan Jam'iyyar daga nan Arewa ba, dan a karya kwarin guiwar gamayyar tun kafin al'amura su kankama, dan hanawa wani dan takara mai karfi samun kaiwa gaci daga Arewa ba. A farkon lamarin kafa APC ta shammaci kowa a Nigeria, kuma tunanin mutane da dama ya tafi akan cewa zasu kai labari matukar an dore akan yadda aka taho, amma daga baya duk lamura suka sauya. Abin da yake daure min kai shi ne yadda jam'iyyar da ta ke san kafa gwamnati bata nuna damuwarta akan zogayewar da magoya bayanta suke yi, wasu ma nuna musu ake su kama gabansu idan tsarin bai musu ba, kuma wai masu son karbe gwamnati daga jam'iyya mai mulki.

Wannan ta sanya na fahimci PDP da gaske suke, da suke cewa Mulki zai tabbata a hannunsu har wajen shekaru 60 koma fiye, domin sun iya dinke mafi yawancin barakar da ta taso musu. Shi ya sa basa yin fushi da nasu matukar za'a amfana da shi.

Tarihin siyasar Arewa ya nuna  akwai dadadden tarihin alakar siyasa tsakanin yankin Arewa da yankin Kudu maso Gabas da kudu maso kudu. Awolowo daga yankin Yarbawa yana daya daga cikin 'yan siyasar kudu da ya tsani Arewa matukar tsana, kuma galibin Yarabawa suna da irin wannan ra'ayi. Amma sai muka yi wani mugun kwadon da cinsa da wuyar gaske.

A ganina babban kuskuren da 'yan Arewa suka yi a siyasance da suka dauki Amanar siyasa suka mikawa Yarabawa, mutanan da har gobe basu yarda da mutumin Arewa ba, kuma 'yan Arewa suka nunawa Yarabawan dukkan dogaron cin zaben mutumin Arewa na ya zama shugaban kasa ya rataya akan su Yarabawan, dan haka su ke rawa suke murna tarkonsu ya kama burgu.

'Yan Arewa da ke cikin APC kamar sun kidime, suna ji suna gani suka hakura da yankin Kudu maso kudu da kudu maso Arewa a siyasance, sun nuna ba zasu iya yin wani katabus ba a yankin. Shgaban kasa kuma ya fahimci hakan shi yasa yake rawa namansa na jaka, ai daga lokacin da ake yaki ka fara kare kanka to anci nasara a kanka. Tabbas, Yarabawa zasu koyawa mutanan Arewa da suka basu amannar siyasarsu wani muhimmin darasi. Ga shi dai tun a yanzu, munyi babu tsuntsu babu tarko, jam'iyyun da ake gani na Arewa ne, an tattare su an mikawa Bisi Akande da  Asiwaju Bola Ahmed Tinubu kuma dukkan jaridun kasarnan suna kiran Tinubu da sunan Jagoran APC na kasa.

Duk tarihi da kwarewar siyasa da muke takama da su ba su yi mana amfani ba a ganina. Amma na fahimci da yawa wasu a Arewa idansu ya rufe shugabancin kasar kawai suke so ko ta halin kaka, basa yin lissafin me zai je ya dawo. Shi yasa suma basa nuna damuwarsu akan irin yadda jam'iyyar tasu ta ke zagwanyewa a Arewar. Sun manta cewa jarin dan siyasa shi ne jama'a, da me zabe da wanda ake zaba. Amma dai bad'i war haka tuni mai akuwa ta auku, ana jiran 29 ga mayu dan rantsar da shugaban kasa a karo na goma sha shida (16). Allah ya sa muna raye.

YASIR RAMADAN GWALE 
22-04-2014

Tuesday, April 8, 2014

Shirin Gwamnatin Tarayya Na #YouWin: Anyi Mana Shal

SHIRIN GWAMNATIN TARAYYA NA #YouWin: ANYI MANA SHAL!

A ranar juma'ar da ta gabata ne, hukumar kula da gasar da gwamnatin Tarayya da hadin guiwar wasu kungiyoyi suka kafa dan yaki da talauci da taimakon al'umma dan dogaro da kansu, ta fitar da sakamakon gasar na farkon wannan shekara. Ita dai wannan gasa ana cin kudi kama daga Naira Miliyan Daya har zuwa Naira Miliyan Goma (10M). Abinda kwamatin yake bukata ga duk mai sha'awar shiga gasar shi ne, cikakken bayanin sana'ar da mutum yake son yi idan ya samu Nasarar lashe gasar, wannan a takaice shi ne, abinda kwamatin suke da bukata a karon farko dan samun Nasarar shiga gasar.

Haka kuma, wannan shiri na #YouWin shiri ne da aka yi masa tanadi na musamman, ta yadda babu wanda zai karbi kudin #YouWin ya kwanta akansu, idan kuwa ya yi haka zai iya samun kansa a gidan yari, ya zama dole ga duk wanda ya samu Nasarar lashe gasar ya aiwatar da dukkan abubuwan da ya tsara a takardun shiga gasar da ya gabatarda suka bashi damar lashe gasar.

Ga duk wanda ya kalli sakamakon gasar na ranar Juma'arnan 04-04-2014 da jaridar #DailyTrust ta buga, ya san cewa Mu mutanan Arewa an yi mana kwaf-daya inda aka kwashe mana kafafu, mutanan kudu su ne wadan da suka ci gajiyar wannan shiri inda suka samu Miliyoyin kudi, domin kuwa kaso 80 na wadan da suka samu lashe gasar 'yan Kudu ne kiristoci, a yayin da Mutanan Arewa a cikin gasar ba su wuce kashi 20 ba.

Sakamakon wannan gasar bai zo min da bazata ba, domin kuwa, mutanan Arewa suna da matukar sakaci akan duk wani abun alfanu irin wannan. An jima ana kiran 'yan Boko da suka kammala karatu ba suda aikin yi da su shiga gasar amma da dama suka yi biris, kuma wannan dama ce da babu wadan da zasu shiga gasar sai 'yan boko domin, kowa shi ne zai yi bayanin abinda yake son ya yi, dan masu duba takardun shiga gasar Turawa ne, za su yiwa duk wanda ya gabatar da takardunsa tambayoyi ta yadda indai ba shi ne ya tsara bayanansa ba, to ba zai iya gamsar da su ba. Amma, haka aka yi mana kwaf daya a wannan gasa.

Lallai ya kamata mu farka, mu san inda yake yi mana ciwo, mu kuma sani cewa kanmu muke cuta, muna kara sharewa talauci gindin zama a cikinmu. Babu wani shiri da ake samun makudan kudi kamar wannan shiri na #YouWin amma abin takaici 'yan Bokonmu wadan da ake ganin su ne zasu ci gajiyar shirin amma abin takaici wadan da suka lashe gasar daga cikin kaso 20 da aka bamu raba-dai-dai mukai da 'Yan Kudu mazauna Arewa. Allah ya maganta mana irin wannan rashin kulawa..

YASIR RAMADAN GWALE
08-04-2014

Monday, April 7, 2014

KWANAKI 100: Gwamnatin Kasar Masar Na Tsare Da Ma'aikatan Gidan Talabijin Na Al-Jazeerah

KWANAKI 100: MA'AIKATAN GIDAN TALABIJIN NA ALJAZEERAH NA TSARE A KASAR MASAR

A dan wannan lokacin kasar Masar ta zama wata kasa mafi hadari ga 'yan jaridar kasashen waje. Tun bayan turka-turkar da ta kawo haramtacciyar gwamnatin Adly Mansur karkashin jagorancin Abdel-Fattah Alsisi dan kama karya, kasar Masar ta shiga takun saka da dukkan wasu 'yan jaridu masu tsage gaskiyar abinda yake faruwa a kasar Masar din. Mafiya yawancin 'yan jaridar da suke bayyana ra'ayin talakawan kasar Masar na can kasa akan halin da kasar take ciki, sun fuskanci matsi da kyara da dauri da duka da kisa daga haramtacciyar gwamnatin Masar.

Kusan duk wani dan jarida da zai bayyana gaskiyar abinda ke faruwa, to kai tsaye Gwamnatin Mansur da take samun umarni daga Al-Sisi dan kama karya, zasu kirashi a matsayin mai goyon bayan kungiyar Ikhwanul Muslimin da aka kwace musu Mulki ta karfi da yaji. Gwamnatin Masar ta fara garkame ma'aikatan gidan Talabijin na Al-Jazeerah tun kusan watan Augustan bara inda suka kama Abdallah Al-Shami wanda dan asalin kasar Masar din ne suka daure shi a kurkuku, saboda zarginsa da ake yi da nuna goyon bayan Hambararriyar Gwamnatin Mursi a irin rahotannin da yake aikawa sashin Larabci na AlAl Jazeera Mubasher Misr قناة الجزيرة مباشر مصر, wannan ta sanya gwamnatin ta rufe tashar a kasar, kuma aka hana mata watsa dukkan wasu shirye shirye a kasar.

Bayan dan lokaci kadan, kuma aka sake kame wasu ma'aikatan Al-Jazeerah da suka hada da Peter Greste wanda yake aiko rahoto ga sashin turanci wanda kwararren dan jarida ne tsohon ma'aikacin BBC, daga nan aka kame Bahry Muhammad da Muhammad Fahmy 'yan kasar Masar din masu yiwa sashin Turanci na Al-Jazeerah aikai, har kawo yau din nan da suka cika kwanaki dari suna cigaba da kasncewa garkame a gidan kurkuku. Akan zalinci.

Kamar yadda muka sani ne, gidan Talabijin Na Al-Jazeerah mallakar Gwamnatin kasar Qatar ne, wadda ke zaman Kasa daya tilo a a cikin manyan kasashen larabawa da suka yi na'am da gwamnatin Mursi da kuma kungiyarsa ta Ikhwan duk kuwa da adawar da suke nunawa da wanzuwar Mulkin dimokaradiyya a yankin kasashen Larabawa, to wannan shi ne abinda bai yiwa su Al-Sisi dan kama karya dadi ba, dan haka suka sanya kafar wando da duk wani mai goyon bayan Morsi, dan haka laifin kasar Qatar ya shafi gidan talabijin na AlAl Jazeera English.

Iyaye da dangin 'yan jaridar da ake tsare da su sunyi ta yin kiraye-kiraye akan a sake musu 'yan uwa, amma abin tamkar bara a gidan bebe, gwamnatin kama-karya ta Masar ta yi kememe ta ki sauraronsu, duk kuwa da irin tofin Ala-tsine da aka yi akan keta hakkin 'yan jarida a Warshinton da London da Brusels da New York, amma gwamnatin Masar taki sauraron kowa.

Al-Jazeerah dai na cigaba da kiran a sakar mata ma'aikata ba tare da wani sharadi ba, domin basu aikata wani laifi da ya keta dokar kasar Masar ba, a cewarsu.

YASIR RAMADAN GWALE
07-04-2014

Su Waye Suke Kai Hare-Hare A Zamfara?



SU WAYE SUKE KAI HARE-HARE A ZAMFARA?

Akwai matukar daure kai da damuwa ace har yanzu an kasa gane ko kama wadan da suke yin irin wannan mummunan kisan gillah a jihar Zamfara. Ya faru ba sau daya ba, ba sau biyu ba, an kashe daruruwan jama'a an kone gidaje da dama an kore dubban shanu, amma har yanzu an kasa gane masu yin wannan aikin Ta'addancin, ina hukumomin tsaron kasa da na jihar zamfara suke?

Babban mashawarcin kasa ta fuskar tsaro Kanar Sambo Dasuki dan Sokoto ne mai makwabtaka da Zamfara, sannan babban sufeto janar na rundunar 'yan sandan Najeriya Muhammad Dikko Abubakar dan jihar Zamfara ne duk da ya koma Kano da zama, haka kuma, sabon Ministan tsaron Najeriya wanda duniya gaba daya ta shaida gogewarsa da kwarewarsa ta fuskar tsaro Janar Aliyu Muhammad Gusau (Mutumin Kirki) duk 'yan jihar Zamfara ne, ina gwamnan Zamfara Dakta AbdulAzizi Yari suke? Ta yaya duk wadannan gogaggun mutane masana harkar tsaro ta sirri da ta sarari suke, mahaifarsu na ci da wuta ganga-ganga amma ace an kasa shawo ko magance lamarin. Anya kuwa akwai gaskiya a kasarnan?

A dan karamin sanin da na yiwa Janar Aliyu Gusau na san cewa mutumin kirki ne mai kaunar kasarnan da san cigaba, mutum ne mai kokarin kamanta gaskiya a cikin lamuransa. Ina kyautata masa zaton cewa ba zai taba bari a inda yake da iko a cutar da al'ummar Arewa ba, balle kuma mahaifarsa inda aka yanke masa cibiya ba. Lallai ya kamata a yi wani abu dan kawo karshen wannan lamari. Allah ya jikan wadan da suka rigamu gidan gaskiya. Su kuma masu aikata wannan kisan, muna tuna musu fadin Allah Taala cewar. "Ya zuwa gare shi ne makoma ta ke".

YASIR RAMADAN GWALE
07-04-2014

Sunday, April 6, 2014

RWANDA: Hutu Da Tutsi Bayan Shekaru 20 Da Kisan Kare Dangi

RWANDA: HUTU DA TUSTI BAYAN SHEKARU 20 DA KISAN KARE DANGI

Yau al'ummar kasar Rwanda dake Kudancin Afurka suke bikin tunawa da Shekaru 20 mafiya muni a tarihin kasar da suka shude, haka kuma, ana lissafa wadannan shekaru ashirin a zaman daya daga cikin wani mummunan lokaci da duniya ta yi tozali da shi a wancan lokacin. Wannan lokaci da ya shude, wutar kabilanci da tsananin gaba da kiyayya ita ce ta ruru tamkar wutar daji a zukatan al'ummar kasar Ruwanda inda kabilun Hutu masu rinjaye suka farwa kabilar Tusti mai matsakaicin yawa da kisa babu ji babu gani, kamar an aiko su, bayanai sun nuna cewa wannan yaki ya barke ne a ranar 7 ga watan Afrilun 1994 zuwa tsakiyar watan Yuli, ance fadan an shafe kwanaki 100 cif-cif ana zubar da jini, inda aka yi asarar akalla rayukan mutune Miliyan 2 tare da jikkata sama da mutum dubu dari biyar zuwa Miliyan daya a yayinda da dama suka tsere suka bar kasar zuwa makwabtan kasashe domin samun mafaka.

Kasashen duniya tare da majalisar dinkin duniya a wancan lokaci duk sunyi Wadarai da abinda ya faru a Rwanda, inda suka kira lamarin da cewa Kisan-Kare Dangi ne, ko kuma kisan-kiyashi. A yau da ake bikin tunawa da wannan rana, Shokolo Bangoshiya ta fashe da kuka wurjanjan a yayin da take tuna irin abinda ta gani na kisan rashin Imani a dab da shiga birnin Kigali.

Bayanai sun tabbatar da cewa, duk wannan mummunan kisan gilla da aka yi a cikin kwanaki 100, anyi shi ne da kananan makamai da suka hada da wuka da gatari da lauje da gariyo da barandami da matsefata da tsitaka da fatanya da sauransu. Babu shakka jini ya kwarara a kusan dukkanin kasar ta Rwanda, kabilun Tutsi duk inda suke a kasar sun ga ta kansu, musamman inda 'yan Hutu masu rinjaye suke da yawa, haka kuma, ance suma kabilun Tutsi sun dauki fansa a inda suke da rinjaye a kasar.

Wani abin mamaki da Hutu da Tutsi, shi ne, tamkar Hausa da Fulani suke, domin yare daya suke magana da shi wato KINYARWANDA. A cewar wani masanin tarihi bambancin tsawon mitoci ne kadai tsakaninsu.To, amma, sai turawan mulkin mallaka na Belgium suka kara fito da wasu abubuwa da su ka kara fito da wasu bambance bambance kamar katin shedar zama dan kasa, suka kuma fifita kabilar Tutsi daga bisani kuma suka koma suna fifita Hutu. Farko sai da aka fara yada farfagandar kiyayya kan Tutsi cewa sune matsalar Rwanda akai amfani da kafafen yada labarai, akwai kungiya ta musamman da Hutu suka kafa wadda suka sanya ma suna Akai da yarensu ma'ana "masu kai hari tare" kafin daga karshe da kansu su harbo jirgin Habiyarmana.An tafka rashin imani gaban duniya.a farka cikin mace a fito da dan tayi,a fasa ma shi madiga.sai da kogin Tanganyika ya cika da gawarwaki fal.

Wannan kazamin yakin basasa ya shiga kundin tarihin duniya tun kimanin shekaru 20 da suka gabata, haka kuma, al'ummar duniya ta jima tana yiwa al'ummun Hutu da Tutsawa kallon wasu irin mutane marasa Imani da jin-kai.

A yanzu bayan shekaru 20 da wannan kisan kiyashi dukkan al'ummar kasar Rwanda da suka hada da Hutawa da Tutsawa suna yin nadamar irin rashin Imanin da suka nunawa junansu, tare da bayyana takaicinsu akan abinda ya faru. Babu wani alkhairi a cikin yaki face Nadama!

Muna fatan Allah ya kare Duniya daga shaida irin kisan rashin Imani irin wannan. Allah ya kare kasashenmu daga fuskantar Matsananciyar gaba irin wannan.

Yasir Ramadan Gwale
07-04-2014

Thursday, April 3, 2014

Wa Ye Zai Kashe Malam Yasir Ramadan Gwale?

WA YE ZAI KASHE MALAM YASIR RAMADAN GWALE

Daga Sheriff Ibrahim Muhammad Almuhajir

Abokina Yasir Ramadan Gwale yayi wani rubutu akan hayaniyar da ta auku a Funtua sai wani ya aiko mishi da sakon zai kasheshi. To bari ka ji in kana son ka sheshi yasir dan Gwale ne a Kano. bismillah in ka yanka ka kawo mana kanshi muna jiranka.

KUMA KUJI

Wani corper yayi rubutu da ya ambaci sunan manzo da mahaifiyar shi Amina da cin zarafi, to yaya zaayi idan aka samu wannan labari,

1- Kasheshi za'ayi kai tsaye.
2- Kona chochi coci za'ayi.
3- Kashe Kirista za'ayi a sace dukiyar su.
4- Ko bincike Malamai da masu mulki ke da hakkin yi alamarin ko gama gari mutane.

Tabbas duk mai hankali dalibin ilmi ingantacce ya san amsar wannan tambaya, Allah taala yace
يا أيها الذين آمنوا إن جائكم فاسق بنبإ فتبينوا أن تصيبوا قوما بجهالة فتصبحوا على ما فعلتم نادمين...واعلموا أن فيكم رسول الله.......
Kowa ya san abunda wannan ayah take nufi wajen bincike kafin daukar hukunci sai dai kila anmance da fadin أن فيكم رسول اللهabunda yake nufi shine muddun annnabi na nan to ba mai yanke hukunci sai shi. Yanxu da bayanan wa zaa tuntuba gama garin mutane? To malamai sune magada annabawa su zaa tunyuba da masu mulki kamar yadda ya tabbata a shariah.

LALLAI BA SHAKKA

Idan akayi bincike aka tambayi wannan corper shin kasan waye Muhammad? shin kasan wacece Amina ya amsa cewa ya sansu ya san kimar su awajen Musulmi hukunci zai hau kanshi amma ba na kisa ba har sai an sake tambayershi me yasa ko kuma wanne Muhammad kake nufi idan yayi ikirarin ganganci to na take zaa fille wuyamshi ko da alkali ko babu. Wannan shine hukuncin mai zagin Manzo kuma Allah ya laanceshi ya tsine mishi albarka.

SAKAMAKON HAKA

Abuida mutanen Funtua suka yi na kona chochi da kwashe dukiya da tafa hankalin alummah da sa su guje guje zalunci ne suka yi ba shakka kuma wuce gona da irine. Kuma jahilci ne Allah rabamu da jahilci.

Wannan ba bakon abu ba ne a Funtua saboda ga na garinsu, sun saba su yi kone-kone da zarar Musulmi ya fadi zabe su yi ta sace sacen dukiya. Wannan zai nuna maka cewa akwai bukatar malamai na Funtua su kara himma wajen ilmantar da mutane addini mai zurfi. Kuma su kaucewa sanar da gama garin mutane kalamai na motsa rai akan Mimbari. Mimbari amanar Manzo Allah ce, duk wanda ya hau dole ya isar da ita dai dai ko a sauko da shi.

Kai kuma mai kashe Yasir kar ka fasa. Dan dama mun dade muna son gane hakikanin masu kashe mana malamai da dalibai.

Yasir Ramadan Gwale
03-04-2014

Tuesday, April 1, 2014

Ko Ranar Lahira Sai Anyi Bincike Balle Funtua!!!


KO A RANAR LAHIRA SAI ANYI BINCIKE BALLE KUMA A FUNTUA!!!

Batun da na yi jiya dan gane da abinda ya faru a FUNTUA, ya sanya wasu da dama suka kasa fahimtar abinda na fada, watakila bisa ga Jahilci ko Son Rai. Wasu da dama sunyi maganganu na zagi da cin mutunci da makamantansu wadan da daman na yi tunanin masu fama da tsukakken tunani zasu yi hakan. Laifi na kawai na ce YA KAMATA A YI BINCIKE KAFIN DAUKAR DUKKAN WANI MATAKI. Sau da dama rashin gudanar da bincike na Adalci ya sanya muke yin kwakyariya akan abubuwan da ba haka zahirinsu yake nufi ba, daga baya kuma a ji kunya. Wasu su farma wadan da ba suda laifin fari balle na baki.

Ya na da kyau mutane su sani cewa ko a ranar lahira Allah bazai yiwa kafirai hukunci ba sai ya binciki Annabawa da Manzannin da ya aikowa Bani-Adama ko sun isar da sako, tare da cewa shi Allah shi ne masani abinda yake fake da wanda yake boye, ya san da cewa Annabawa da Manzanni sun isar da sakonSa ga Talikai, amma dan saboda ya kafawa Bani-Adam hujja sai ya bincika ko Annabawa da Manzanni sun isar da sakon da aka turo su da shi Tsarki Ya Tabbata A Gareshi Subhanahu Wata'ala. Shi ya sa ko a Hajjin Bankwana sai da Manzon Allah SAW ya tambayi taron Sahabbai HAL BALLAGHTU? Shin Na Isar Da Sako A Gareku, suka amsa da cewa Ka Isar Ya Manzon Allah, Nan ta ke Manzon Allah SAW ya yi addu'ah ya ce ALLAHUMMA FASH-HAD Ya Allah Ka Shaida, Sahabbai sun yiwa Manzon Allah SAW Shaida cewa ya isar da sakon Ubangiji.

Haka kuma, dukkan sauran Manzanni Allah zai tambayesu shin sun isar da SakonSa ga Talikai, idan sukace sun isar sai Allah ya tambayesu waye shaidar ku, sai suce, shaidarmu shi ne cikamakin Annabawa Muhammad Dan Abdullahi Allah ka yi dadin tsira a gareshi da zurriyarsa da Sahabbansa da wadan da suka bi tafarkinsu da kyautatawa har ya zuwa ranar sakamako Sallallahu Alaihi Wasallam; daga nan sai Allah ya tambayi Manzon Allah shin Annabawa sun isar da sako, sai yace eh! Allah kai da kanka ka bani labari cikin alqur'an kace Manzanni sun isar da sako, sannan sai Allah yayi hukunci ga kafirai. Duk wannan bincike ne Allah da kansa zai yi Ranar Alkiyama domin ya kafa hujja ga kafirai.

Al-Qur'ani tun daga farkonsa har karshensa cike yake da kissoshin Annabawan da suka Gabaci Manzon Allah SAW da bayanin sakon da Allah ya turo su da shi. Dan haka min babi Aula idan har Allah da kansa zai yi bincike dan tabbatar da zahirin abinda ya faru, ace Bil-Adama a Funtua zai dauki hukunci da moolanka ya zartar ba tare da yin wani bincike ba. Allahumma sai dai fa idan bincike ya nuna cewa ga abinda mutum ya aikata kuma aka yi masa hukunci dai-dai da abinda ya aikata, wannan ba'a zalince shi ba.

Dan haka, duk wadan da suke zaton cewa kawai dan wani al'amari ya zo musu zasu dauki hukunci ba tare da yin sahihin bincike ba, su yi duk abinda suka ga zasu iya, to su sani Allah baya zalunci, kuma sai ya sakawa duk wanda aka zalunta ko da kuwa Musulmi ne ya zalunci wanda ba Musulmi ba.

YASIR RAMADAN GWALE
01-04-2014