Monday, September 5, 2016

Hattara Da Abokan Facebook Da Baka San su Ba


HATTARA DA ABOKAN FACEBOOK DA BAKA SAN SU BA

Wani abu ya faru a wannan Makon da wani matashi a sanadiyar facebook. Yana da kyau mutane su dinga sanin hakikanin da su wa suke mu'amala a facebook kafin sakin jiki da mutum. Domin kuwa halin da ake ciki yanzu rashin aminci yayi yawa tsakanin wannan al'umma. 

Wani matashi mai suna Salman ya hadu da wani a facebook har ta kai su ga yin magana a Inbox. Suna tattaunawa da wannan mutumin mai suna Micheal amma ba ainihin sunansa Micheal din ya rubuta a facebook ba, ya sa wani suna daban. Suna hira har dai shi Micheal yake tambayar Salman cewar me yake yi na neman kudi a matsayinsa na matashi? Salman yace ba abinda yake yi. Anan ne shi Micheal ya yiwa Salman alkawarin samar masa aiki anan Kano.

Bayan haka, shi Micheal yasha daukar hoton office da gida da mota yana turawa shi Salman yana bashi labarin irin rayuwar da yake ciki ta jin dadi. Wannan ta sanya shi Salman nuna zilama da kwadayi akan abinda Micheal ke nuna masa. Anan ne suka sanya lokacin da shi Salman zai zo Kano tunda yana zaune ne a jihar Adamawa. Salman yazo bisa romon bakan da Michel yayi masa cewar zai sama masa aikin yi a kamfanin da yake aiki.

Ranar Juma'a sai Salman yayi niyyar zuwa Kano, dan haka ya kira Micheal ya sanar masa cewar gashi nan zai Taho.  Shi kuma ya amsa masa da cewar ba matsala Allah ya kawo shi lafiya. Da isowar Salman Kano da yamma ana dab da Magriba, sai ya kira Micheal yake gaya masa cewar gashi ya sauka a Kano. Anan ne shi kuma ya shaida masa cewar baya nan yana wajen aiki, amma zai sanya kan in yazo ya taho da shi zuwa masauki.

Salman na tsaye a tasha wajen karfe 7 na Yamma wani yazo ya same shi bayan da suka yi waya yayi masa kwatancen inda yake a tsaye. Yace masa shi kanin Micheal kuma yazo ne ya kaishi masauki, Salman ya bashi suna tafiya har cikin unguwar Sabon gari a Kano. A lokacin da suka shiga wani layi mara kwalta wanda kuma baya bullewa  (close) sai shi Salman ya lura wasu mutum hudu na biye da su a baya, da ya fahimci lallai wadannan matsa bin su suke yi sai ya tsorata. Yayi nufin ya dawo da baya ya gudu, sai sukai masa ishara da cewar zasu yanka shi idan ya gudu.

Suka nuna masa wani gida suka ce ya shiga, suna shiga gida suka nuna masa wani daki suka ce ya shiga. Ya dan tsaya gardama sai daya ya hankadashi cikin dakin. Bayan da suka tura shi ciki sukai masa mugun duka, suka kwace masa wayoyin sa guda uku, suka kwace masa Agogo da Zobe da kuma kudin sa. Sannan suka tambaye shi Katin cire kudi na ATM yace bai zo da shi ba. Suka caje kayan sa basu ga katin cire kudi ba.

Daga nan suka sanya shi ya tube kayan sa tsirara suka dinga daukar hoton sa, sannan suka ce masa, sai ya sayi wannan hoton Video da suka dauke shi ko kuma su yada video din a Whatsapp da Facebook. Suka ce sai ya saya dubu 70000. Ya amince zai basu kudin, a lokacin da yake yana hannunsu duk abinda suka ce masa baya musantawa. Da suka gama haka, wajen 8:30 na dare sai suka rako shi wai ya hau mota ya koma ya kawo musu kudin video din.

Suka fito da shi suka ce masa idan ya kuskura yayi magana ko yayi wani motsi zasu illata shi, haka ya basu hadin kai.  Suna tafiya da shi suna ce masa bi nan bi can, har dai da Salman yaga sun zo inda Jama'ah suke, kawai sai yayi ta maza ya rumbaci daya daga cikin su suka fadi kasa yana ihun Jama'a ku taimake ni b'arawo ne. Ganin haka sauran suka gudu shi kuma yaci Nasarar damke dayan katamau. Nan ne fa jama’a aka taru ana tambayar me ya faru. Da yake mutanan wajen kabilu ne suna magana da shi yaron da Turanci, sai suka nemi su bawa shi Salman rashin gaskiya. 

Nan ne fa, shi Salman yace wallahi ba zai sake shi ba sai an je wajen 'yan sanda. Suka yi juyin duniya ya cika shi, amma Salman yace sai dai a gaban 'yan sanda sannan zai cika shi. Haka kuwa aka yi, aka kira 'yan sanda suka tafi da su. Ana zuwa caji ofis Salman yayi bayanin abinda ya faru, aka ci Nasarar kama dukkan wadannan matasa a daren, aka tsare su. Da yake a lokacin wajen 11:30 sai 'yan sanda suka ce shi Salman yaje ya dawo da safe. Yace shi bai san kowa ba, suka ce masa ba wani wanda ya sani da zai iya zuwa ya tafi da shi.

Nan ne kawai shi Salman ya tuna cewar ya sanni. Kawai sai naji 'yan sanda sun buga min waya, suka bani labarin abinda ya faru dan haka suke rokon nazo na tafi da Salman. To nima a zahiri ban san Salman din ba sani na hakika, domin a facebook kawai muke gaisuwa, kuma ko a facebook maganar mu bata wuce gaisuwa. Amma da yake naje Adamawa da Azumi Salman yazo har inda nake ya gaishe ni. Anan ya karbi lambar wayata. 

Jin haka, na kira abokaina guda uku na basu labari nace su rakani wajen 'yan sandan. Bayan da muka je na gabatar da kaina a wajen 'yan sanda sannan aka sake yi min bayanin ainihin abinda ya faru. Suka ce na tafi da shi Salman na dawo da shi da safe. Na karbi Salman na kaishi ya kwana. Anan ne nake yi masa fad'a, nace wanne irin hauka ne zai sashi haka kurum ya dauki kafa yaje wajen mutanan da bai san su ba.

Sannan shi kuma yake ce min, ai shi yaudarar sa sukai, domin hoton da suke sakawa a facebook ba nasu bane, sannan sunan da suke amfani da shi shima ba ainihin sunansa bane. Sai daga baya ne ya gane wanda suke magana din ashe sunan sa Micheal. Alhamdulillah mun bi dukkan hanyoyin da suka kamata muka nemawa shi Salman hakkinsa. Kuma har ya koma gida. Dan haka, anan nake amfani da wannan damar wajen kira ga mutane lallai suyi taka tsantsan wajen sanin su waye zasu yi mu'amala da su. Ganganci babba baka san mutane ba, kawai su kira ka kuma ka dauki kafa kaje.

Bayan haka, kuma tilas mutane su rage kwadayi da son banza. Domin a garin kwadayin abin da mutum yake tunanin zai samu zai jefa rayuwarsa cikin garari. Don shi Salman wanda suka yi masa wannan abu zasu iya yin Kidnapping dinsa ko ma su kashe shi, ba abinda ba zai faru ba. Dan haka, mutane ayi hattara. 

Yasir Ramadan Gwale 
04-09-2016

Friday, September 2, 2016

Malam Salihu Sagir Takai Na Iya Zama Mafita A Siyasar Kano A 2019


MALAM SALIHU SAGIR TAKAI NA IYA ZAMA MAFITAR SIYASAR KANO 2019

Zaben Malam Salihu Sagir Takai a 2019 ka iya sanya jihar Kano ta kai bantenta. Malam Salihu bayan bukatar a tallata shi a gayawa al'umma waye shi, duk wani dan Siyasa a jihar Kano da me zabe da wanda ake zabe, babu wanda ke bukatar a sanar da shi Nagarta da Ingancin Malam Salihu Sagir Takai. Domin tuni bayanai suka kara be dukkan wani lungu da sako na jihar Kano suna bayyana kyawawan halayensa wanda ake fatan shugabanninmu su kasance. Malam Salihu na daya daga cikin tsirarun 'yan siyasa a jihar Kano da ya samu kyakkyawar shaida daga kusan Galibin b'angarorin siyasar Jihar Kano.

Maganganunsa da irin kalaman da yake furtawa sun nuna hakikanin irin zaton da ake masa na dattako da kamala da sanin ya kamata wajen jagorantar al'amuran al'umma. Tun Malam Salihu Sagir Takai yana Shugaban karamar hukuma ya samu Yabo da Shaida ta Alkhairi daga Jagoran Gwamnatin Lokacin Alh. Rabi'u Musa Kwankwaso. Duk da sun fito a mabambantan jam'iyyu wannan bata hana Kwankwaso yabawa halayen Malam Salihu a harkar Shugabanci da kiyaye dukiyar al'umma.

Wannan gaskiya tasa da ta bayyana ta sanya Gwamnatin mai girma Malam Ibrahim Shekarau tafiya da shi har kusan Shekaru takwas. Bugu da kari har yayi aikin sa ya gama a matsayin Kwamashina ba a same shi da wani abin Allah wadai wanda ya tabbata cewar yayi abubuwa na rashin gaskiya ba. Wannan ta sanya Malam Shekarau sanya shi a gaba domin zama magajinsa, amma bisa kaddarawarsa Subhanahu Wata'ala, bai kaddarawa Malam Salihu Sagir Takai zama Gwamnan Kano a lokacin da aka so ba.

Duk da rashin samun Nasarar da yayi, hakan bata sanya shi zautuwa ba irin ta gafalallaun 'yan siyasa da kan shiga muguwar damuwa idan sun fadi zabe. Dukkan kalaman sa suna cike da nuna mika lamura ga Allah da nuna cewar shi ne mai bayarwa ga wanda yaso a lokacin da ya so. Malam Salihu yaje kotu domin bin hakkin sa da yake ganin anyi ba daidai ba a zaben 2011 hakan bai nuna rashin tawakkalinsa ba, sai dai bisa tsari na rayuwa idan kana ganin an taka hakkin ka karbi kadu, wanda tsarin siyasar wannan lokaci yayi tanadin hakan.

Gwamnonin Kano da suka gabata Malam Ibrahim Shekarau da Alh. Rabi'u Musa Kwankwaso babu wanda bai bayyana kyawawan halayen Malam Salihu Sagir Takai ba. Haka nan,  shima Gwamna mai ci Alh. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana Malam Salihu Sagir Takai a matsayin mutumin kirki da ya dace da samun shugabanci. Ganduje tunda ya hau Gwamnan Kano bai taba yin wasu kalamai na batanci ga Malam Salihu sai dai yaba masa da yakan yi.

A dan haka, bisa wannan kyakkyawar shaida da Malam Salihu Sagir Takai ya samu, daga dukkan b'angarorin siyasar Kano da suka hada da Shekarau, Kwankwaso da kuma Ganduje ba suda wani sabani da Takai, kuma shima ba shida wani sabani da su a siyasance ko a mu'amala ta rayuwa. A sabida irin wannan kyakkyawan tunanin mu akansa muke ganin cewar shi ne mutumin da zai saita siyasar Kano, tare kawo sulhu da fahimtar juna tsakanin tsaffin Gwamnonin Kano. A duk cikinsu babu wanda yake da tunanin cewar Takai zai wulakanta shi ko tozarta shi, a sabida haka, muke fatan jam'iyyar PDP ta sake baiwa Malam Salihu Sagir Takai dama a 2019, sannan al'ummar jihar Kano su zabe shi domin saita jihar Kano da dora ta akan turba ta zaman lafiya da juna da fahimtar juna da kuma karuwar arziki da bunkasa jihar Kano tare da maida hankalin 2 aje ayyukan da zasu maida jihar Kano ta zarce tsara a Nigeria. 

Muna fatan Malam Salihu Sagir Takai a matsayin Gwamnan Kano a 2019. Idan har ka gamsu da wannan ra'ayin nawa ka bayyana goyon bayan ka ga ga Takai, ta hanyar rubuta, #Takai2019. 

Yasir Ramadan Gwale 
02-08-2016