Thursday, September 25, 2014

Shekau Mai Rayuka Da Yawa


SHEKAU MAI RAYUKA DA YAWA

Shugabannin hukumomin tsaro a Najeriya sunyi ikirarin kashe Shekau a wannan karon, bayan a baya ansha cewa an kashe shi amma a bada labarin ya sake b'ulla. A yadda naga Olukolade na bada sanarwa da kwarin guiwar cewar sunfa kashe Shekau, ina zaton da gasken ne, idan har haka ne batun munyi murna, muna kuma fatan Allah ya sa ba za ayi baya babu zani ba, muna kuma yabawa sojojin da suka sadaukar da rayuwarsu dan kare kasarmu Najeriya daga hare-haren miyagun 'yan ta'adda.

Amma ni abinda ya tsaya min a rai game da wannan batu shi ne, me yasa sai yanzu da aka bayar da rahoton kama jirgin shugaban CAN da yunkurin safarar makamai, akai irin wannan maza-maza haka? Bana shakkar cewar anyi kokari wajen aika Shekau Barzahu, nayi murna da hakan.

Ina fatan Allah ya sa wannan karan anyiwa Shekau din kisan karshe, daga nan muji THE END akan al'amarin Boko Haram. Suma wadan da aka ce sunyi saranda sun mika kansu ga hukuma, ina fatan Allah ya sa sunyi tuba taubatan-Nasuha. Amma duk da haka ina tambayar ina makomar rayukan mutanan da wadannan sarandaddu suka kashe ba bisa hakki ba? Shin sunci banza kenan? Duk wata kungiya da taga dama ta dauki makamai da sunan ko ma meye su kashe wadan da suka ga dama, Alabashshi daga baya bayan anci galabarsu su ce sunyi saranda, hakan ya dace?

Lallai wadan da aka kashe ba bisa hakki ba, suna da hakkin a bi kadun jininsu. Masu kulle-kulle daga nesa ko daga kusa Allah ya sansu ya san duk abinda suke aikatawa, kuma yasan duk inda suke, Allah ya tona musu asiri. Allah ya bamu lafiya da zaman lafiya mai dorewa. Allah ka sa wannan shi ne karshe Boko Haram.

Yasir Ramadan Gwale
25-09-2014

Saturday, September 20, 2014

Muntaka Abdul-Hadi Dabo


MUNTAKA ABDULHADI DABO: A wannan yammaci na Asabar, a madadin Ni da Zainab muke bin sahun dimbin 'yan uwa da abokan arziki na abokina Malam Muntaka Abdul-Hadi Dabo dan taya shi murnar shiga wata sabuwar rayuwa da baya bai taba yin kamarta ba. Ba shakka daga yanzu har zuwa karshen rayuwar Malam muntaka zai samu sauyi gagarumi a rayuwarsa, domin ya matsa daga inda ya tashi ya tsinci kansa tun kuruciya da samartaka zuwa Magidanci. Ba ko tantama wannan wani sauyi ne mai girma a rayuwa kuma mai ma'ana.

Muna taya su murna da farin ciki da fatan alheri a iya tsahon rayuwar aurensu. Lallai daya daga cikin ginshikin burin rayuwar Malam Muntaka ya cika, fatanmu Allah ya tabbatar da su har karshen rayuwarsu, Allah ya basu hakuri da juriyar zama da juna.
Haka kuma, ina amfani da wannan damar nayi kira ga abokina kuma ango da yaji tsoron Allah ya rike diyar mutane tsakani da Allah gwargwadan iyawarsa, ya sani nauyi ne aka dora masa na kula da kansa da kuma abinda ya mallaka na iyalinsa, shi din zai kasance abin tambaya dangane da nauyin da yake kansa a matsayin magidanci. Ina kira a gareka ka zama mai adalci ga iyalinka a koda yaushe.

Ni da Zainab muna yin addu'ah ta musamman a gareka kai da iyalinka Allah ya sanya alheri ya bada zaman lafiya. Allah ya bada zurriyar dayyiba.
YASIR RAMADAN GWALE
20-09-2014

Wednesday, September 17, 2014

Artabun Malam Nuhu Ribadu Da 'Yan Fashi


ARTABUN MALAM NUHU RIBADU DA 'YAN FASHi

Malam  Nasir El-Rufai ya bayyana a cikin littafinsa The Accidental Public Servant cewa Malam Nuhu Ribadu ya taba fellawa dan fashi mari. A cikin babi na 7 shafi na 158 Malam Nuhu Ribadu ya fada cewar a lokacin da ya fara jin sunan Nuhu Ribadu a jami'ar Ahmadu Bello dake Zariya shi ne lokacin da labari ya cika jami'ar cewa Ribadu ya fellawa wani dan fashi mari.

Yadda abin ya faru shi ne, Nuhu Ribadu suna tafiya da abokinsa a cikin mota, kuma shi Ribadun ke tuka motar, babu zato babu tsammani suka yi arba da 'yan fashi, nan take 'yan fashin suka taresu, inda suka nemi Nuhu Ribadu da ke tuka motar ya basu mukillinta abinda ke nuna sun kwace motar, babu musu Malam Nuhu Ribadu ya fito ya mikawa 'yan fashi mukullin motar.

Bayan da dan fashin ya karbi mukullin motar daga hannun Nuhu Ribadu ne kuma, ya sa hannu ya tsinke Ribadu da mari, nan take Ribadu shima ya sa hannu ya faskawa dan fashin mari tasss yace yaya zaka nemi na baka mukullin mota kuma na baka duk da haka ka mareni! Daga nan shugaban 'yan fashin ya ja 'yan fashin dan su gudu.

Mutum mara tsoro irin wannan da har ya iya yin ta maza ya gaurawa dan fashi mari, bana jin idan ya samu wata dama a Gwamnati akwai wanda zai iya bashi tsoro wajen aiwatar da aikinsa. Bugu da kari, aikin da Nuhu Ribadu yayi na shugaban hukumar EFCC kadai ya isa ya nunawa duniya cewar waye shi.

Ya kama tare da gurfanar da wadanda ake ganin ba zasu iya tabuwa ba, ya tonawa barayin dukiyar kasa asiri. Dalilin aikinsa kima da martabar sunan Najeriya ya fara dawowa a idan duniya. Ba shakka wannan dan tahaliki duk inda ya samu dama zai baiwa mara d'a kunya.

Mlam Nuhu Ribadu ba gwamnan Adamawa kadai ba, har Shugaban Najeriya zai iya rikewa cikin adalci da daidaito. Mutanan Adamawa lallai duk wanda zai sha inuwar gemu a bayan mokogoro yake, ku amincewa Nuhu Ribadu a 2015 dan zama Gwamna.

Yasir Ramadan Gwale
17-09-2014

Sunday, September 14, 2014

Hassada Na Iya Kai Mai Yinta Wuta ko Aljannah- Sheikh Abdulwahab Abdallah

HASSADA NA IYA KAI MAI YINTA WUTA KO AL-JANNAH - Sheikh Abdulwahab Abdallah

Wata rana an tambayi Sheikh Abdulwahab Abdallah dangane da HASSADA. Sai Malam ya yi bayani kamar haka: Ita Hassada wani ciwo ne, wanda dukkan 'ya 'yan Adam da Hauwa suna dauke da ita.

Malam ya yi bayanin cewar, akwai Hassadar da zata iya kai mai yinta zuwa Al-Jannah, ya buga misali da Abubakar Ibnu Abi-Kuhafa RA da Umar Bin Khattab RA, ya ce sun kasance suna yin rige rige wajen aikata ayyukan alkhairi, domin faranta ran Manzon Allah SAW da kuma neman yardar Allah, haka suka dinga rigegeniya wajen ciyar da dukiyarsu.

Malam ya kara da ce, akwai daya bangaren Hassada wanda yana kai mai aiktawa zuwa ga Halaka da tabewa da tashin hankali a ranar kiyama, Malam ya cigaba da cewa, daya bangaren Hassada shi ne, mummunar Hassada, wadda ta ke dauke da kyashi da bakinciki da kiyayya da gaba da mummunar niyya, ya ce, mummunar Hassada kusan a yanzu ita tafi damun wannan al'ummar tamu, ta yadda Malamai da Sarakuna da 'yan Siyasa da Masu kudi da Dalibai da Masu yin Facebook da sauransu da dama kanci duniduniyar juna dan ganin bayan juna wajen aikata alkhairi saboda Hassada.

Malam ya cigaba da cewa, hanyar da Mutum zai rage radadi da kafin Hassada a tare da shi shi ne ya dinga kokarin tunawa zuciyarsa Allah da shagaltar da ita (zuciyar) da zikiri da karatun al-kur'ani da tadabburi da shi.

Daga karshe Malam ya kara Jaddada cewar dukkanmu muna da dauke da Hassada a zukatanmu sai dai wani yana iya danne zuciyarsa a duk lokacin da Hassadarsa ta motsa, wani kuwa baya iya jurewa har sai ya bayyana Hassadarsa a Fili, ta yadda Jama'a zasu dinga cewar wane kaza yana da Hassada. Allah ka bamu ikon danne zukatanmu.

Yasir Ramadan Gwale
14-09-2014

Wednesday, September 10, 2014

Risala Daga Yasir R. Gwale Zuwa Ga Muhammad Sulaiman

RISALA DAGA YASIR R. GWALE ZUWA GA MUHAMMAD SULAIMAN

Sakon fatan alheri gareka dan uwa Malam Muhammad Sulaiman tare da iyalanka da fatan alheri a gareku: Naga sakon ka kuma kalmomin da kayi amfani dasu gareni sun yi min dadi a zuciyata, dan yadda ka lausasa ra'ayi cikin hikima da basira, ina nufin ka yi min kalubale mai ratsa zuciya cikin sauki. Ni da kai ina mana addu'ar Allah yasa mu dace da daidai ya kuma tabbatar da mu akan daidai a cikin dukkan lamuranmu na rayuwa. 

A tawa gajeriya kuma rarraunar fahimtar kira kake yi a gareni akan na juyo daga tawa fahimtar, ko na dawo daga rakiyar gwanaye na a siyasa Malam Ibrahim Shekarau da Malam Nuhu Ribadu na dawo zuwa ga wadansu wadan da watakila nan gaba zaka ambata min su. Duk da cewa siyasa ra'ayi ce, kuma masu magana suka ce kamar riga ce, amma ni da kai muna da manufa iri daya ta duba cancantar mutum mai nagarta a addini da rayuwa. 

To anan ina so mu dubi wadannan bayin Allah da ka ambata acikin rubutunka wato gwanaye na, a zahirin abinda ya bayyana game da halayen su cikin siyasa da sauran mu'amalolin su, musamman irin jagoran cin da sukayi, ya bayyana a gareni a zahiri cewa mutanan kirki ne, na kuma kyautata zato a garesu a siyasa da cigaban kasa, watakila ra'ayina ko fahimtata a garesu kuskure ce, amma Allah shi ne mafi sanin abinda ya boyu a garemu. Ni a tawa fahimtar na nisantar dasu daga abubuwan da wassu irin su keyi na rashin gaskiya da cin-amanar kasa, watakila akwai wani abu game da halayensu da ya boyu a gareni, amma nayi Imani cewa Allah ba zai kamani akan rashin sani ba. 

A iya dan abinda naji ko na karanta, kuma zuciya da tunani da hankali irin nawa masu rauni sun nuna min cewa wadannan mutane sunyi aikin da aka yaba musu ana ganin girmansu da dattakon su. Amma wannan ba yana nuna cewa su tsarkakakku bane, a matsayinsu na mutane kamar ni, za'a iya samunsu da tarin kurakurai da laifuka irin na Bani-Adam, Allah shi ne masanin abinda kowa daga cikinmu yake aikatawa. Haka kuma, sam ban manta da abinda ka ambata na zakewar wadansunmu ba na tilastawa kowa ra'ayinsu na siyasa ba, wato kace kowa ga jam'iyyar da zaiyi, idan yaki yi ya zama abin aibatawa, ko kuma wane na iya canza jam'iyya amma wane ba shi da 'yancin abinda ya fahimta shi ne daidai a ra'ayi irin na siyasa. 

Ina so ni da kai mu kalli siyasa hagu da dama duk lokacin da bana jam'iyya kalmomin sukarta na iya fitowa daga bakina, kuma hakan ba zai hana in yaba mata ba ko in dawo cikin ta ba, kamar yadda ake cewa jam'iyyar siyasa ba ta da halastaccen makiyi kuma abinda ya bayyana na zahiri a siyasar Najeriya ya karfafa wannan magana, a tunani na a nan babu tubka da warwara a'a, kowa na tallata jam'iyyarsa ne a salon siyasar zamani. Kuma akwai misalai da yawa na manyan 'yan siyasa a Najeriya idan ka duba tun daga kan tsohon mataimakin shugaban kasa, gwamnoni, sanatoci da sauran su nawa suka fita daga wata jam'iyya suka koma wata? 

Nasan girmamawa da zaton alheri yasa kai da masu ra'ayi irin naka ke ganin laifin Sardaunan Kano Malam Ibrahim Shekarau da Malam Nuhu Ribado da kuma mutane irina da suka zabi wadannan mutane a matsayin jagorori na siyasa, don ba su kadai suka canza jam'iyya ba, amma nagartar su yasa ake jin zafin sauyin da suka yi. Kamar yadda dan uwa kuma yayana Bello Muhammad Sharada ya fada cewa Jam'iyyar Siyasa wani dandamali ne da ake takawa dan kaiwa zuwa ga madafun iko a bisa tanadi na kundin tsarin mulkin Najeriya, haka kuma, ga wadansu daga cikinmu nada mugun taqalidancin dole a bar jam'iyyar PDP a komawa wata, wanda a ganina wannan dagewa da tilastawar kuskure ne. Zamanin mu na bukatar a duba na kwarai ne wanda ya cancanta ba jam'iyya ba, wanda idan mutum ya dage akan jam'iyya ina ganin watakila iyakar fahimtarsa kenan.

Naji dadi da irinka masu ilimi, fasahar zance da hangen nesa kuke leka irin sakonnin mutane irina, kuma ina maka zaton alheri da godiya cewa ni da Sardaunan Kano da Ribado duk kana son mu ne, kuma kana ganin nagartar mu yasa kake fatan mu nisanci PDP mu dawo zuwa wadda ba'a sukar mutum komai muninsa in yana yi. To anan fata na irinka mutanen kirki masu dauke da alheri su daina rufe ido suna tilastawa kowa wata jam'iyya, sannan su kasance masu sanya hanci wajen sansano kowa ko da yana jam'iyyar su, kuma su kasance masu adalci ga mutum ko da ya bar jam'yyar su. 

Haka nan kuma, su kasance masu waiwaye da kokarin hasashen gaba a siyasance, cikin kyautata zaton alheri ga mutum. Ra'ayi na kan shugaban kasa Goodluck Jonathan a bayyane yake, illa iyaka kawai ina ganin yanzu mutane kan kalle ni ne ba abinda na fada ba, dan haka ba zaka iya sanya kowa ya fahimceka yadda kake so ba, kowa na da ikon tunani da fahimtarsa, abin lura shi ne wai nasarar wata jam'iyya muke so a kasar nan ko nasarar mutanen kirki? Kuma canji dole muke so, ko canji mafi alheri? So ake mu rufe ido, mu toshe kunne don tsoron maganar mutane, da gudun a zage mu idan mun yabi wadan da mu ke ga ya dace a yabesu ko da yana wata jam'iyyar da ta saba da tamu?

Wannan sako naka ya min dadi kwarai da gaske, domin ya kara min karfin guiwa, kuma ka taimaka min wajen kara fito da manufata fili, sannan na samu amsa tambayoyin da ake ta aiko mini wadan da a baya nayi shiru ban ce komai ba. Ni dai ina nan daram kan yabawa tafiya da tsarin Sardaunan Kano Malam Dakta Ibrahim Shekarau da Malam Nuhu Ribadu kuma na aminta da su a matsayin jagorori. Wannan kam ko shakka babu ra'ayi na ne, da babu wanda na tilastawa akansa, haka kuma, ina ganin a matsayina na dan kasa ina da cikakken 'yancinyin ra'ayin siyasa da sanya wasu a matsayin jagori na ko da kuwa nayi kuskuren zabar mutanan da na zaba. Amma na kyautatawa Allah zato cewar ba zai tabar da ba, domin kullum ina fada a cikin suratul Fatiha cewa Allah ya shiryar da ni hanya madaidaiciya. Ina rufewa da kara gode maka da yi maka addu'ar fatan alheri.

Ina kuma addu'ar Allah ya azurtamu da samun shugabanni nagari adalai da zasu ji tausayinmu, su tsaya kai da fata wajen kare muradunmu ko da kuwa hakan zai yi sanadiyar rayuwarsu. Allah ya bamu lafiya da zaman lafiya. Na gode.

YASIR RAMADAN GWALE
10-09-2014

Tuesday, September 9, 2014

Munir Muhammad Usman


Munir Muhammad Usman: Kani na ne, kuma abokina mun tashi tun muna yara, kwanakin baya ya gamu da jarabawar rayuwa, yayi hadari a bisa abin hawa, har ta kai kuma yau dinnan za'a yi masa aikin tiyata, muna yi masa addu'ar fatan alheri da fatan samun lafiya, Allah ya sa abinda ya sameshi ya zama kaffara a gareshi, Allah kuma ya sa a yi masa fida cikin Nasara. Allah ya baka lafiya Muniru, muna rokon 'yan uwa da su sanya shi a cikin addu'o'insu da bakunansu masu albarka.

YASIR RAMADAN GWALE
09-09-2014

Saturday, September 6, 2014

Makarantar Malam Bambadiya


MAKARANTAR MALAM BAMBADIYA: Ustaz Lawal Adam Gangara kenan yake karbar kyauta daga hannun Farfesa Malumfashi Ibrahim a madadin Yasir Ramadan Gwale dazu a Kaduna, wajen bayar da kyautukan gasar kagaggun Labarai da Makarantar ta shirya. Ina godiya da farin ciki da wannan kyauta, ina kuma fatan alheri ga sauran abokan takara da 'yan makaranta.

YASIR RAMADAN GWALE
06-08-2014

Boko Haram


Manzon Allah SAW yace, a karshen duniya kisa zai yawaita, wanda yake kisa da wanda ake kashewa babu wanda ya san dalilin kisan. Da yawan mutanan da 'yan Boko Haram suke kashewa basu san me suka yi musu ba aka kashe su, watkila idan da za'a tambayi wani dan Boko Haram din sai yace shima bai san dalilin kisan da yayi ba domin shima sashi aka yi (ba-mamaki). Duk wanda yake zaton duniya zata zauna lami-lafiya to ya sauya tunani, domin acikin al'umma akwai waliyyan Allah mutanan kirki wadan da suke umarni da kyakkyawa kuma su yi hani ga mummuna, kuma akwai waliyyan Shaidan, shi Iblis a koda yaushe waliyyansa yana yi musu mummunar huduba ne, yana kawata musu mummunan aiki har su dinga jin babu komai idan sunyi ko da kuwa sun san cewa abinda suka aikata haramun ne, wannan matakin shi ne na kekashewar zuciya Allah ya karemu. Shi yasa da yawa wasu suna yin zina da luwadi da sata, sun san laifi ne, amma suna ganin kamar ba komai, sun gafala cewa direban da yake jan su Iblis ne. Allah kuma labari ya bamu cewa, yana nan yana jiran kowannemu. Allah ka shiryemu shiriya ta gaskiya.

Yasir Ramadan Gwale
06-08-2014

Masu Jihadin Karya


Kungiyoyin Musulunci na 'yan Ta'adda suna fakewa da Musulunci wajen aikata Ta'addanci da cin zarafin Musulmi. Kasashen Yamma na fakewa da kungiyoyin 'yan Ta'adda dan yaki da Musulunci. Shi yasa duk abinda Israela ta ke yi a Ghazza sunansa kare kai a wajensu, Israela kuma na cewa 'yan Hamas ta ke yaka, a yayin da take jefa boma-bamai kan gidajen jama'a. Musulmi da dama an rude su da kafafen yada-labarai na kasashen Turai, da dama suna zaton duk abinda suka ji gaskiya ne.

Yasir Ramadan Gwale
06-08-2014

Tuesday, September 2, 2014

Idan An Bi Ta Barawo . . .


IDAN AN BI TA BARAWO . . .

Jiya an ruwaito cewar Shugaban Kasa Dr. Goodluck Jonathan ya manta inda garin Gwoza ya ke, a Borno ne ko a Adamawa abin ya shige masa duhu. Da naji wannan magana sai nace alamu na nuna cewar masu baiwa Shugaban kasa bayanan harkar tsaro a Arewa Maso Gabas basa gaya masa gaskiyar abinda ke faruwa kenan. Ina Gwamnan Borno Kashem Shettima, Ina Sambo Dasuki mai baiwa Shugaban kasa shawara a harkar tsaron kasa, ina Alhaji Aliyu Gusau Ministan tsaron Kasa, ina sabon sufeton 'yan sanda na kasa? Suna ina har Shugaban kasa ya manta inda Gwoza ta ke?

Lallai dole Gwamnati da hukumomin tsaro su tashi tsaye tare da matsa kaimi wajen yaki da 'yan ta'adda. Abin akwai tashin hankali ace mutane na guduwa suna barin garuruwansu a Bama da Gwoza saboda ceton rayukansu, tilas ne masu mulki su kiyaye amanar da ke hannunsu.

Ya Allah ka fitar da jihar Borno daga cikin wannan kangi da tashin hankali da ta ke fama da shi. Allah ka dawo da zaman lafiya dawwamamme a wannan yanki na Arewa maso gabas. Yana da kyau mu yawaita addu'o'in samun zaman lafiya a Najeriya mu kuma yi riko da sabubban karbar addu'ah mu kyautata tsakaninmu da Allah. Allahumma Sallim Sallim!!!

Yasir Ramadan Gwale
02-09-2014

Monday, September 1, 2014

Ta'aziya Ga Shahrazad Bibi Farouk


TA'AZIYA GA SHAHRAZAD BIBI FAROUK

Dazu muka samu labarin Allah ya yiwa mahaifin 'yar uwa Shahrazad Ibrahim Faruq rasuwa, Alhaji Farouk Bibi Farouk wanda tsohon mataimakin Gwamnan Kano ne a jamhuriya ta biyu. A madadina ni da Zainab muna mika sakon ta'aziyarmu ga Malama Shahrazad da Rihab bisa rasuwar mahaifinsu. Allah ya jikansa ya gafarta masa, ya sa Al-jannah ce makomarsa. Allah ya basu hakurin jure wannan rashi.

Wa'azi A Kano


WA'AZI A KANO: A 'yan kwanakinnan naga mutane na ta yin rubutu cewar Gwamnantin Kano zata takaita mana yin wa'azi a Kano. Ni kam ban fahimci wannan magana ba, ban kuma ji sahihancin maganar ba. Da farko dai tambaya ta ita ce, shin da gaske ne akwai wannan yunkuri? Sannan ya abin zai kasance (ma'ana hanawar, shin harda shafuka irinsu Facebook, ko kuwa wa'azozi na cikin unguwanni?) Shin wane irin Wa'azi ake nufi, karatuttukan Tafseer da na Hadisai da ake gabatarwa a Masallatai da Majalisai daban-daban a fadin Kano ake nufi, ko kuwa Muhadarori (Lacca) da akan shirya dan zaburar da al'umma idan hali ya samu? Irin Wa'azin Kasa da kungiyar Izala ta ke Shiryawa da Maukibin Qadiriyya da Sheikh Qaribullah Nasiru Kabara ke jagoranta da kuma taron Adduah da ake yi a fadar Maimartaba Sarkin Kano wanda Khalifa Sheikh Isyaka Rabiu yake jagoranta duk suma suna cikin abubuwan da za'a hana? Ina matsayin mutanan nan masu yin maci dauke da tutoci sanye da bakaken kaya suna tottoshe hanyoyi suna damun mutane da mugun wari da zarni, suna bata gari da tarin shara duk suma suna cikin wannan doka? Ban sani ba ko Kiristoci suma suna yin Wa'azin kasa da sai na tambaya har da kiristoci wannan abin zai shafa? Sannan wannan doka ce da gwamnati ke son Majalisar Dokoki ta jihar Kano tayi, ko kuwa wani kundin Daftari ne ya baiwa Gwamnati damar sanya wannan doka? Ko kuwa Dikiri (Decree) ne irin na soja mazan fama, dan nasan gwamnan Kano ya taba zama mininstan tsaro ban sani ba ko tsohuwar allura ce ta motsa? Ko ma dai meye Ini da ire-irena muna neman karin bayani akan wannan batu. Duk da na karanta mabanbantan ra'ayoyin abokaina irinsu Danladi Haruna da El-Ameen Daurawa da sauransu da dama da naga sun yi magana akai. Allah ya sa mu samu cikakken bayani.