Wednesday, September 17, 2014

Artabun Malam Nuhu Ribadu Da 'Yan Fashi


ARTABUN MALAM NUHU RIBADU DA 'YAN FASHi

Malam  Nasir El-Rufai ya bayyana a cikin littafinsa The Accidental Public Servant cewa Malam Nuhu Ribadu ya taba fellawa dan fashi mari. A cikin babi na 7 shafi na 158 Malam Nuhu Ribadu ya fada cewar a lokacin da ya fara jin sunan Nuhu Ribadu a jami'ar Ahmadu Bello dake Zariya shi ne lokacin da labari ya cika jami'ar cewa Ribadu ya fellawa wani dan fashi mari.

Yadda abin ya faru shi ne, Nuhu Ribadu suna tafiya da abokinsa a cikin mota, kuma shi Ribadun ke tuka motar, babu zato babu tsammani suka yi arba da 'yan fashi, nan take 'yan fashin suka taresu, inda suka nemi Nuhu Ribadu da ke tuka motar ya basu mukillinta abinda ke nuna sun kwace motar, babu musu Malam Nuhu Ribadu ya fito ya mikawa 'yan fashi mukullin motar.

Bayan da dan fashin ya karbi mukullin motar daga hannun Nuhu Ribadu ne kuma, ya sa hannu ya tsinke Ribadu da mari, nan take Ribadu shima ya sa hannu ya faskawa dan fashin mari tasss yace yaya zaka nemi na baka mukullin mota kuma na baka duk da haka ka mareni! Daga nan shugaban 'yan fashin ya ja 'yan fashin dan su gudu.

Mutum mara tsoro irin wannan da har ya iya yin ta maza ya gaurawa dan fashi mari, bana jin idan ya samu wata dama a Gwamnati akwai wanda zai iya bashi tsoro wajen aiwatar da aikinsa. Bugu da kari, aikin da Nuhu Ribadu yayi na shugaban hukumar EFCC kadai ya isa ya nunawa duniya cewar waye shi.

Ya kama tare da gurfanar da wadanda ake ganin ba zasu iya tabuwa ba, ya tonawa barayin dukiyar kasa asiri. Dalilin aikinsa kima da martabar sunan Najeriya ya fara dawowa a idan duniya. Ba shakka wannan dan tahaliki duk inda ya samu dama zai baiwa mara d'a kunya.

Mlam Nuhu Ribadu ba gwamnan Adamawa kadai ba, har Shugaban Najeriya zai iya rikewa cikin adalci da daidaito. Mutanan Adamawa lallai duk wanda zai sha inuwar gemu a bayan mokogoro yake, ku amincewa Nuhu Ribadu a 2015 dan zama Gwamna.

Yasir Ramadan Gwale
17-09-2014

No comments:

Post a Comment