Wednesday, September 10, 2014

Risala Daga Yasir R. Gwale Zuwa Ga Muhammad Sulaiman

RISALA DAGA YASIR R. GWALE ZUWA GA MUHAMMAD SULAIMAN

Sakon fatan alheri gareka dan uwa Malam Muhammad Sulaiman tare da iyalanka da fatan alheri a gareku: Naga sakon ka kuma kalmomin da kayi amfani dasu gareni sun yi min dadi a zuciyata, dan yadda ka lausasa ra'ayi cikin hikima da basira, ina nufin ka yi min kalubale mai ratsa zuciya cikin sauki. Ni da kai ina mana addu'ar Allah yasa mu dace da daidai ya kuma tabbatar da mu akan daidai a cikin dukkan lamuranmu na rayuwa. 

A tawa gajeriya kuma rarraunar fahimtar kira kake yi a gareni akan na juyo daga tawa fahimtar, ko na dawo daga rakiyar gwanaye na a siyasa Malam Ibrahim Shekarau da Malam Nuhu Ribadu na dawo zuwa ga wadansu wadan da watakila nan gaba zaka ambata min su. Duk da cewa siyasa ra'ayi ce, kuma masu magana suka ce kamar riga ce, amma ni da kai muna da manufa iri daya ta duba cancantar mutum mai nagarta a addini da rayuwa. 

To anan ina so mu dubi wadannan bayin Allah da ka ambata acikin rubutunka wato gwanaye na, a zahirin abinda ya bayyana game da halayen su cikin siyasa da sauran mu'amalolin su, musamman irin jagoran cin da sukayi, ya bayyana a gareni a zahiri cewa mutanan kirki ne, na kuma kyautata zato a garesu a siyasa da cigaban kasa, watakila ra'ayina ko fahimtata a garesu kuskure ce, amma Allah shi ne mafi sanin abinda ya boyu a garemu. Ni a tawa fahimtar na nisantar dasu daga abubuwan da wassu irin su keyi na rashin gaskiya da cin-amanar kasa, watakila akwai wani abu game da halayensu da ya boyu a gareni, amma nayi Imani cewa Allah ba zai kamani akan rashin sani ba. 

A iya dan abinda naji ko na karanta, kuma zuciya da tunani da hankali irin nawa masu rauni sun nuna min cewa wadannan mutane sunyi aikin da aka yaba musu ana ganin girmansu da dattakon su. Amma wannan ba yana nuna cewa su tsarkakakku bane, a matsayinsu na mutane kamar ni, za'a iya samunsu da tarin kurakurai da laifuka irin na Bani-Adam, Allah shi ne masanin abinda kowa daga cikinmu yake aikatawa. Haka kuma, sam ban manta da abinda ka ambata na zakewar wadansunmu ba na tilastawa kowa ra'ayinsu na siyasa ba, wato kace kowa ga jam'iyyar da zaiyi, idan yaki yi ya zama abin aibatawa, ko kuma wane na iya canza jam'iyya amma wane ba shi da 'yancin abinda ya fahimta shi ne daidai a ra'ayi irin na siyasa. 

Ina so ni da kai mu kalli siyasa hagu da dama duk lokacin da bana jam'iyya kalmomin sukarta na iya fitowa daga bakina, kuma hakan ba zai hana in yaba mata ba ko in dawo cikin ta ba, kamar yadda ake cewa jam'iyyar siyasa ba ta da halastaccen makiyi kuma abinda ya bayyana na zahiri a siyasar Najeriya ya karfafa wannan magana, a tunani na a nan babu tubka da warwara a'a, kowa na tallata jam'iyyarsa ne a salon siyasar zamani. Kuma akwai misalai da yawa na manyan 'yan siyasa a Najeriya idan ka duba tun daga kan tsohon mataimakin shugaban kasa, gwamnoni, sanatoci da sauran su nawa suka fita daga wata jam'iyya suka koma wata? 

Nasan girmamawa da zaton alheri yasa kai da masu ra'ayi irin naka ke ganin laifin Sardaunan Kano Malam Ibrahim Shekarau da Malam Nuhu Ribado da kuma mutane irina da suka zabi wadannan mutane a matsayin jagorori na siyasa, don ba su kadai suka canza jam'iyya ba, amma nagartar su yasa ake jin zafin sauyin da suka yi. Kamar yadda dan uwa kuma yayana Bello Muhammad Sharada ya fada cewa Jam'iyyar Siyasa wani dandamali ne da ake takawa dan kaiwa zuwa ga madafun iko a bisa tanadi na kundin tsarin mulkin Najeriya, haka kuma, ga wadansu daga cikinmu nada mugun taqalidancin dole a bar jam'iyyar PDP a komawa wata, wanda a ganina wannan dagewa da tilastawar kuskure ne. Zamanin mu na bukatar a duba na kwarai ne wanda ya cancanta ba jam'iyya ba, wanda idan mutum ya dage akan jam'iyya ina ganin watakila iyakar fahimtarsa kenan.

Naji dadi da irinka masu ilimi, fasahar zance da hangen nesa kuke leka irin sakonnin mutane irina, kuma ina maka zaton alheri da godiya cewa ni da Sardaunan Kano da Ribado duk kana son mu ne, kuma kana ganin nagartar mu yasa kake fatan mu nisanci PDP mu dawo zuwa wadda ba'a sukar mutum komai muninsa in yana yi. To anan fata na irinka mutanen kirki masu dauke da alheri su daina rufe ido suna tilastawa kowa wata jam'iyya, sannan su kasance masu sanya hanci wajen sansano kowa ko da yana jam'iyyar su, kuma su kasance masu adalci ga mutum ko da ya bar jam'yyar su. 

Haka nan kuma, su kasance masu waiwaye da kokarin hasashen gaba a siyasance, cikin kyautata zaton alheri ga mutum. Ra'ayi na kan shugaban kasa Goodluck Jonathan a bayyane yake, illa iyaka kawai ina ganin yanzu mutane kan kalle ni ne ba abinda na fada ba, dan haka ba zaka iya sanya kowa ya fahimceka yadda kake so ba, kowa na da ikon tunani da fahimtarsa, abin lura shi ne wai nasarar wata jam'iyya muke so a kasar nan ko nasarar mutanen kirki? Kuma canji dole muke so, ko canji mafi alheri? So ake mu rufe ido, mu toshe kunne don tsoron maganar mutane, da gudun a zage mu idan mun yabi wadan da mu ke ga ya dace a yabesu ko da yana wata jam'iyyar da ta saba da tamu?

Wannan sako naka ya min dadi kwarai da gaske, domin ya kara min karfin guiwa, kuma ka taimaka min wajen kara fito da manufata fili, sannan na samu amsa tambayoyin da ake ta aiko mini wadan da a baya nayi shiru ban ce komai ba. Ni dai ina nan daram kan yabawa tafiya da tsarin Sardaunan Kano Malam Dakta Ibrahim Shekarau da Malam Nuhu Ribadu kuma na aminta da su a matsayin jagorori. Wannan kam ko shakka babu ra'ayi na ne, da babu wanda na tilastawa akansa, haka kuma, ina ganin a matsayina na dan kasa ina da cikakken 'yancinyin ra'ayin siyasa da sanya wasu a matsayin jagori na ko da kuwa nayi kuskuren zabar mutanan da na zaba. Amma na kyautatawa Allah zato cewar ba zai tabar da ba, domin kullum ina fada a cikin suratul Fatiha cewa Allah ya shiryar da ni hanya madaidaiciya. Ina rufewa da kara gode maka da yi maka addu'ar fatan alheri.

Ina kuma addu'ar Allah ya azurtamu da samun shugabanni nagari adalai da zasu ji tausayinmu, su tsaya kai da fata wajen kare muradunmu ko da kuwa hakan zai yi sanadiyar rayuwarsu. Allah ya bamu lafiya da zaman lafiya. Na gode.

YASIR RAMADAN GWALE
10-09-2014

No comments:

Post a Comment