Tuesday, January 31, 2012

Karya da Gaskiya a Tsakanin ‘Yan Najeriya

Karya wani mummunan laifi ne da yake maida mutum mai kima ya zama maras kima, haka kuma karya na maida babba ya koma karami. Ma’ana babu abin da zai zubar maka da kima cikin kankanin lokaci kamar karya ita ke bata tarihi da zuriyya, wannan cema ta sanya koda lokacin jahiliyya mutane kan kyamaci yin karya, da yawan mushurukai suna kyamatar karya a wancan lokacin saboda irin illar ta da suka sani ta zubar da kima da daraja da bata tarihi. Bayan da addinin musulunci ya zo ya sake tabbatar da haramcin karya ga wanda ya yi imani. Karya tana kai mai yinta zuwaga munafurci kamar yadda hadisi ya zo cewa alamar munafuki guda uku ce kuma karya ita aka fara ambata. Kaga wannan ya sake bayyana munin karya.

Menene ma’anar karya: karya dai ita ce bayyana abu sabanin yadda yake wato akasin abin da yake gaskiya ne, ko kuma mutum ya kudure wani abu a zuciyarsa na gaskiya amma ya bayyana sabaninsa. Ana iya yin karya ta hanyar Magana wato mutum ya fadi abin da yake ba haka ne zahirinsa ba. sannan kuma akanyi karya ta hanyar nune, hakana kuma kanyi karya ta hanyar sanya sutura da cin abinci da dukkan sauran fannonin rayuwa ana iya yin karya akansu. Zakaga wasu mutane sun yarda da tafiyar da rayuwarsu bisa karya komai nasu idan ka gani karyane daga maganarsu zuwa tafiyarsu kai hattana sutura da abin hawa da gidan zama wasu duk karya ne a rayuwarsu.

Domin zakaga a Najeriya talaka yana karyar talauci haka kuma mai kudi yana karyar arziki. Talaka bai yarda da talaucinsa ba haka shima mai kudi bai yarda da arzikinsa ba, zakaga mutum talaka mai iyali yana ta tunanin canza sabuwar wayar salula, kaga duk ya tada hankalinsa sai ya mallaki wayar Blackberry bayan ba wannan ne abin da ya dameshi ba, shi kuma mai kudi kaga yana ta hakilon canza mota sabuwar yayi al’hali shima ba wannan ne abinda ya kamaceshi ba. Na taba ganin wani talaka da yake rayuwa da kyar da wahala amma kuma tunaninsa shi ne ya samu kudi ya sayi talabijin samfurin Plasma kaga ko shakka babu wannan ya so yiwa kansa karya.

Karya a tsakanin al’umma: kusan yanzu karya ta zama ruwan dare musamman a tsakanin al’ummar Najeriya idan nima banyi karya ba ina iya cewa karya kusan ta rinjayi gaskiya a dukkan al’amuranmu na yau da kullum, domin idan ka dauki dukkan fannoninmu cike suke da karairayi da zancen banza, zakaga wasu sunfi gamsuwa kayi musu karya sama da kafadi gaskiya, don su zasu haska maka yadda zakayi musu karya. Kuma ita karya kusan zakace ana koyarta ne tun a gida, wato mahaifiya kan yiwa danta karya miji kanyiwa matarsa karya haka itama tana yi masa karya don haka a wannan yanayi sai ka samu yaro ya tashi ya koyi karya tun yana cikin gida. Musamman yanzu da mafi yawancin mutane suka mallaki wayar salula zaka ka samu tana daga cikin abin da ya sake mai da mutane makaryata, kusan kididdiga ta nuna cewa akwai layukan wayar salula miliyan 90 a Najeriya nasan a dukkan wadan da suka mallaki wadan nan layuka da wahala ka samu wanda baitaba yin karya ta hanyar wayar salularsa ba, mutum baya jin wata damuwa yana cikin daki a zaune ga matarsa ga dansa za’a doka masa kira amma sai kaji yace yana kasuwa ko yana kan hanya alhali kuma gashinan tare da iyalansa. Kaga kenan karara yana bada sako ga iyalansa cewa shidin makaryaci ne. gwari-gwari zaka iya cewa akwai makaryata miliyan 90 a Najeriya Allah masani. Kusan yanzu karya babu babba babu yaro wala mace wala namiji, ba malami ba jahili. Kusan kowa na sharata iyakar iyawarsa.

Bari mu dauki wani bangare mu buga misali da shi wato siyasa. Kusan a bayyane ta ke cewa duk ‘yan siyasarmu makaryata ne, domin da wanda yake tallar kansa da wanda yake tallata shi duk makaryata ne. Abin mamaki shi ne zakaji ana tallar mutum a kafafen watsa labarai ana baiyana wasu abubuwa wadan da duk mai hankali yasan karya ne hattana shi mai karantawar yasan karya yake fada amma kuma a haka ake rayuwa. Sannan wani Karin abin mamaki dan siyasa zai zo yana fadawa mutane karya shi yasan karya yake kuma suma jama’a sun san karya yake amma kuma a haka yake Magana har ake tafa masa, sai karasa gane shin wace irin al’umma cemu! Kusan duk dan siyasar da zai zo ya bayyana hakikanin manufarsa ta gaskiya da wahala kaga anyarda dashi amma idan ya yi karya sai kaji ana tafi harda fito. Duk da ban taba ji da kunnena ba amma naji jama’a na fada cewa a Najeriya akwai ‘yan siyasar da sukayiwa al’umma alkawarin famfon fura da nono, kaga da zaka ga wannan dan siyasar da sai ka bashi sunan shugaban makaryata ‘yan siyasa.

Idan muka kalli al’amari na baya bayan nan abin da shugaban kasa ya yi na janye tallafin man fetur na tabbatar da ya furta wannan a lokacin da yake yakin neman zabe da babu wani dan Najeriya da zai saurareshi, amma saboda munfi son a fada mana karya shima yazo ya shara irin tasa kuma ya zauna lafiya. A lokacin jam’huriya ta biyu Awolowo yana yakin neman zabe da yaje jihar Abiya inda a lokacin babu abin da yake tafiya a kasuwanninsu kamar gwanjo yace idan yaci zabe zai hana shigo da gwanjo Najeriya, wasu ‘yan siyasa suka ja hankalinsa me yasa zai furta wannan maganar bazai bari ba kawai sai yaci zabe sannan ya aiwatar da nufinsa; ya kada baki yace shikam Allah ya sawwake ya yiwa talaka karya don ya bashi kuri’a! kaji ‘yan siyasa masu gaskiya.

Haka kuma idan ka dauki fannin saye da sayarwa kusan zakace nanne babbar hedikwatar karya domin da mai saye da mai sayarwa duk sunyi tarayya wajen karya, kana da gaskiyarka kana saida abu mai saye zaisa kayi masa karya, misali ya tambayeka nawa ne farashin abu kaza tsakani da Allah ka gaya masa amma sai kaji ya nemi ragi kuma kayi masa kaga kenan duk sunyi musharaka cikin wannan karyar, kaji mutum yana ihu yana tallar hajarsa amman da ka bincikashi sai kasamu cikakken makaryaci yake. Ga al’gus ko tsoron Allah basaji.

Wannan ce ma ta sanya na tuna da wani labarin uba da dansa akan karya. Wani uba ne ya kira yaronsa cewa yazo ya tukashi a mota ya kaishi cikin gari domin yanada wani taro da zai halarta, bayan da suka iso cikin gari sai yace da dansa kaje ka kai wannan motar wajen gyara ya yi masa kwatance daman ya saba kai gyaran wajen yace masa ka dawo da wuri domin karfe 5 na yamma zamu koma gida, bayanda yaro yaje aka kammala gyara kawai sai ya nufi sinima inda ya shantake yana kallon kwallo bai tashi duba lokaciba sai da karfe 6 na yamma tayi nan da nan hankalinsa ya tashi ya garzaya inda ya tarar mahaifinsa yana jiransa ya tambayeshi a ina katsaya sai yace masa ba’a gama gyaran da wuriba sai yanzu, bai san cewa tuni mahaifin ya buga waya yaji ko angama gyaran aka shaida masa cewa tun karfe 3 na rana aka kammala gyaran, yace da yaron naji takaicin da ka kasa jure gayamin gaskiyar inda kaje amma wannan ba laifinka bane domin a matsayina na mahaifinka nine ban baka tarbiyyar da zaka iya jure gayamin gaskiyaba. A saboda haka zan ladabtar da kaina da komawa gida a kafa, saboda wannan kuskuren da nayi na kin koyarda dan da na Haifa yadda zai jure gayamin gaskiya.

Ya mai karatu ka kalli wannan labarin da kyau kaga cewa uba ya ladabtar da kansa a saboda laifin da dansa ya aikata, inda ya gano ashe tun asali shine bai koyarda dansa yadda zai gaya masa gaskiya ba, lallai akwai darasi acikin wannan labarin. To haka karya take maida mutum mai kima ya koma maras kima, sannan mutum mai mutunci ya koma marashi. Na tuna badakalar karyar da tsohon shugaban kasar Amurka Bill Williams Clinton ya yi lokacin yana shugaban kasa na gaskiyar alakarsa da Monica Lewinsky kusan wannan ce ta sanya Mr Clinton furfura a wancan lokaci. Ka duba yadda gaskiya take da kima a wajensu.

Babban abin da zai baka haushi da mamaki shi ne manyan mutane da malamai suna shara karya. Wani abu da zai tabbatar maka da wannan ka duba dukkan wasu taruka da ake shiryawa a Najeriya idan kaga anbuga takarda za’a fara taro 10 na safe insha Allahu sai karfe 11 ko 12 zakaji anfara alhali kuma ga jadawali anbuga kamar gaske, kaga wannan shi ne zai nuna maka isa matuka da mukayi wajen shirya karya hattana a takarda. Idan shugaban ya yi karyar fara taro akan lokaci inaga sauran al’umma? Ya dan uwana ka tsaya ka kalli kanka tsakaninka da Allah sau nawa kake yin karya a kullum wannan shi ne zai tabbatar maka da waye kai?

Gaskiya tayi karanci: malamai suka gaya mana cewa lokaci zaizo da sai anyi doguwar tafiya kafin a samu mutum mai gaskiya. Gashi dai tana da saukin fada a baki kusan kowa zai iya fada amma ba kowa zai iya aikata ta ba, mutane suna son gaskiya amma basa son ace kodai sufara ko kuma ta fada a kansu. Misali jama’a da dama suka bukaci gwamnati ta aiwatar da shari’ar Musulunci amma a kano a shekarar 2008 da hukumar Hizba tace ta hana mata hawa baburdin acaba jama’a suka ringa ihu akan basaso suna munanan kalamai akan hakan, ka duba babur fa kawai inaga sauran al’amuran rayuwa na yau da kullum, ina zaton da za’a sami wata gwamnati tace dole kowane mai awo ya cika mudu kamar yadda shari’ah tace da sai kaji jama’a na korafin cewa ai ba su kadai bane macuta! Matsalarmu itace idan kace mutum ya yi gaskiya sai ya kafa maka hujjar ai ba shi kadai bane yake aikata badai-dai ba su wane da suwane duk suna aikatawa.

Ya dan uwa gaskiya itace ke maida yaro ya zama dattijo, ita ke sanya soyayya ta gaskiya a zukatan al’umma ga mai yinta. Wannan ce ma ta sanya ko a maganarmu ta yau da kullum baka tabajin ance wane gaskiyarsa ta kare ba, kullum sai dai kaji cewa wane karyarsa ta kare, Allah ka arzurtamu da fadar gaskiya da kuma aiki da gaskiya. Ka kalli yanayinmu komai da ka sani babu gaskiya acikinsa domin mai faskare zai yi maka karya mai nika hatsi zaiyi karya, abin tambaya shin wane mai gaskiya acikinmu? Kullum muna addu’ar Allah ya kawo mana masu gaskiya amma muda kanmu muke tona musu asiri kuma muke basu hanyar da zasu yi mana karya, sai kaga wasu suna yimaka mu’amalar da zasu kureka kawai su sanya kayi karya, ko kuma yawan tambaya marar amfani wanda da yawa wasu kanyi karya don su kare kansu.

Daga karshe ina addu’a ga kaina da sauran al’umma Allah ya bamu ikon fadar gaskiya da kuma karbar gaskiya komai dacinta, Allah ka sanya gaskiyarmu ta rinjayi karyarmu, Allah ka karemu daga sharrin da yake tattare da karya. Ina rokon Allah abin da na fada ya zama dai-dai wannan daga gareshi ne abinda kuma nayi kuskure ko tuntuben al’kalami ko kuskuren fahimta wannan daga gareni ne Allah ya yafemin.

Yasir Ramadan Gwale

yasirramadangwale@hotmail.com

http://yasirramadangwale.blogspot.com

Saturday, January 21, 2012

Shin Idan Nayi Zina Laifin Nawa ne ko na Mahaifina?

Yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah ubangijin talikai, tsiransa da amincinsa su kara tabbata ga fiyayyan halitta babban Fatima cikamakin annabawa Annabi Muhammad salallahu alaihiwasallam da alayansa da sahabbansa da wadand sukabi tafarkinsu har ya zuwa ranar sakamako. Ina shaidawa babu abin bauta bisa cancanta sai Allah kuma annabi Muhammad bawansa ne manzonsa ne. dukkan wanda Allah ya shiryar shi ne hakikanin shiryayye, haka kuma dukkan wanda Allah ya batar babu mai iya shiryar da shi.

Hakika yanzu muna cikin wani yanayi mai cike da tashin hankali da firgici da ban tsoro. Zaka yarda dani ya dan uwa mai karatu cewa wannan lokacin yana cike da kalubale mai yawan gaske, kalubale ta kowane fanni na rayuwa. Kayiwa Allah godiya idan ka samu kanka cikin masu aikata alkhairi da kuma kokarin kaucewa munanan ayyuka wadan da suke kaiwa izuwa ga fushin ubangiji, kamar zina da dangoginta. Ya mai karatu ina fatan zaka bani aron lokacinka tare kuma da fahimtata dan gane da wannan maudu’I, babu wani abu mai ban mamaki dangane da taken wannan mukala.

Ko shakka babu, yana daya daga cikin kalubalen wannan zamani shi ne kowane uba yana son yaga dansa ko ‘yarsa ya/ta samu ilimi ingatacce. Wanda wannan ilimi shine silar ginuwar rayuwar kowane mutum a wannan lokaci. Wannan ce ta sanya iyaye kan baiwa ilimin ‘ya ‘yansu kulawa ta musamman da kuma fatan watakila zasu zama wasu a nan gaba. Tabbas kusan duk wanda kaga ya zama wani abu to tabbas karatu yana daga cikin sila, Domin da karatu ne dan adam kan kai kololuwarsa ta kamala.

Irin wannan kalubale ne yakansa duk da soyayyar da iyaye ke yiwa ‘ya ‘yansu su daukesu su kaisu garuruwa masu nisa domin samun ilimin da zai yi musu linzami a rayuwa da samun kyakkyawan yanayi. Shakka babu iyaye na da gudunmawa me yawa da zasu baiwa ‘ya ‘yansu wajen ganin sun zama mutane na gari, domin sudin makiyayane akan abin da damansu ya mallaka.

Ya dan uwa shin ko kana da labarin rayuwar da akeyi a makarantun gaba da sakandare ko jami’a. hakika rayuwar jami’a wata irin rayuwa ce mara misaltuwa cikin dan gajeren lokaci. Da yawan iyaye kan so ‘ya ‘yansu su je jami’a domin karatu, amma kuma da yawa basu cika bibiyar wace irin rayuwa ‘ya ‘yansu sukeyi acikin jami’a ba. Hakika rayuwar ‘ya ‘yanka tana cikin hadari musamman mata, Ina fatar zaka yarda dani, domin yanzu rayuwar mata a jami’a ta zama abin tausayi matuka. Mafiya yawan ‘yan mata kanso suyi aure bayan kamala jami’a a yayin da suke dokin shiga jami’a amma ba’anan gizo yake sakarba sai bayan sun kamala suke gane ashe sunyi kuskure!

Yanzu makarantun jami’a sun zama wani abin tsoro ga dukkan wani uba mai kishi. Domin bawai kawai karatun da kasani ba dalibai suke koya harda wasu munanan halaye wadan de ke cigaba koda bayan sun gama makaranta. ‘Yanmata da yawa na fadawa cikin wani mawuyacin hali na bala’in zina da dangoginta a jami’a, yanzu ansamu wasu muggan kungiyoyi acikin jami’o’I wadan da ke kokarin kauda budurcin ‘ya ‘ya mata ta kowane irin hali, wannan ta sanya akan hada baki da wasu muggan malamai wadan da ke kada dalibai mata jarabawa ba dan sun cancanci su fadi ba kawai sai domin neman wata dama da za’a nemi daliba ta bada kanta domin bata mata rayuwa.

Wannan ta faru a kusan dukkan jami’o’inmu ba sau dayaba ba sau biyu ba. Idan zaka ga wani abin bakin cikinma harda matan aure ake kokarin jefawa cikin irin wannan mummunan tarko. Yanzu makarantun jami’o’I sun zama wata kafa ta yada muggan dabi’un nan na mata masu neman junansu ta kowane hali, kusan mafiyawa daga cikin daliban jami’a suna da masaniya akan wannan batu.

Hankalina ya jawu kan rubuta wannan mukalane sakamakon wani kaset na wa’azi da marigayi shekh Jafar Adam kano ya yi a Maiduguri ta jihar Borno, wato karatun tafsiri da yake gabatarwa dukkan watan azumi. A lokacin da mallam ke karatu cikin suratu Tauba wata daliba ta rubuto masa wasika daga jami’a akan wani mawuyacin hali da ta shiga, sakamakon iyayanta sunce sai tayi karatun jami’a sannan tayi aure ita kuma tanada burin tayi aure kafin ta shiga jami’a amma iyayanta suka kekasa kasa suke ce ba haka ba. Wannan ce ma ta sanya na ari kalmominta wajen gina kanun wannan muqala. Kamar yadda ta rubuta a karshen takardar da marigayi shekh Jafar Adam ya dauki lokaci maitsowo yana karantawa. A cikin wasikar da ta rubuta tayi bayanai masu cike da tashin hankali wanda duk wanda ke da ‘ya da take a jami’a dole hankalinsa ya tashi, domin tace akan yi kokarin yaudarar yarinya da kudi da wasu kyale-kyale a karon farko idan kuma ta kiya akan tursasata ko ayi amfani da karfi ko kuma ta hanyar kayarda ita jarabawa da nufin samo kanta, ta kara da cewa akwai kulab na dalibai wanda suke hada baki da miyagun malamai da kuma manyan gari domin lalata rayuwar ‘ya ‘ya mata, wannan babban abin tashin hankali ne kwarai da gaske. Alokacin da nake sauraren wannan wasika wallahi saida na zubar da hawaye domin ganin irin halin da ‘yan uwanmu suke ciki a jami’o’i.

Akan wannan batu, ni ganau ne, domin naji labarin irin yadda ake dabdala acikin jami’o’I kuma na gani musamman da daddare. Abinciken da nayi na tabbatar da haka don Alhazan birni kanshiga jami’o’I da daddare su debo dalibai mata su je suyi fasikanci da su sannan su dawo da su kai wani abin tashin hankalima wasuma acikin mota suke aikata irin wannan ta’annati acikin jami’a kawai sai dai suyi nesa da idan jama’a wannan ba boyayyan abu bane a jami’a.

Idan muka koma kuma batun waccan wasika da wannan daliba ta aikowa da mallam, acikin wasikar tayi bayanin cewa tanada wanda take so kuma yana da sana’arsa dai-dai gwargwado tace taji ta gani ko agidan kara zai zauna da ita amma iyayanta suka ce sai ta gama jami’a sannan tayi “tsada” kamar yadda tace. Wannan babban kalubalene ga iyaye domin a kokarin da suke na ganin ‘ya ‘yansu sunyi karatu sun zama wasu kuma sun taimakawa rayuwarsu wajen fadawa cikin halaka. Domin babu wanda yake da garantin cewa ‘yarsa zata kamala jami’a bata fada cikin irin wancan tarkon ba. Tabbas rayuwar ‘yarka abin tambayace a gareka ranar gobe kiyama.

Kamar yadda na fada a baya da yawa dalibai kanyi dokin jami’a afarkon shiga kuma da tunanin cewa sai sun gama sun fara aiki sannan zasuyi aure, wannan takan sanya da yawa fadawa cikin hadari domin da yawa basa gane kuskurensu sai lokacin da suka gama jami’a suke naman mazajen aure kaga da yawan mutane na gudun wacce ta kamala jami’a kodai tsoron irin abin da waccan yarinya da ta fada cewa ya fada akanta ko kuma wani abin da ya ke ba wannan ba.

Kamar yadda ya rinyar ta nema da cewa don Allah malam acikin irin wannan mawuyacin hali da ta sami kanta, a irin wannan hali na fadawa tarkon shedan cewa shin idan tayi zina shin laifin nata ne ko na mahaifinta, a lokacin da mallam yazo wannan gabar sai da yayi ajiyar zuciya. Tayi maganganu masu daukar hankali tace ya kamata iya ye su tuna shin su a yadda suke ya sukeji a lokacin da sha’awa ta motsa musu, ballantana kuma ga ‘yan mata suna cikin shekaru kanana ga kuma motsuwar sha’awa a kowane lokaci kasan cewar suna cakuduwa da maza a koda yaushe, akwai abin tsoro ainun acikin wannan yanayi.

Anan nima zanyi amfani da wannan dama nayi kira ga iyaye cewa. Wallahi kowannenmu zai bada bayanin yadda ya gudanar da rauywarsa da kuma rayuwar wadan da take ta’allake da tasa wato ‘ya ‘yansa yana da kyau iyaye su sake tunani akan ‘ya ‘yansu musamman mata, da yawan basu cika neman shawarar ‘ya ‘yansu mata ba akan halinda suke ciki da kuma irin abin da suke bukata. Yana da kyau ka sami lokaci ka rika tattaunawa da ‘yarka kanajin shawararta akan halin da ta ke ciki tare kuma da jin me ta ke da bukata, domin mata kamar tangaran suke dole sai ana kulawa dasu lokaci zuwa lokaci, da yawa idan ka tuntubi iya ye mata da maza basu san ya rayuwar ‘ya ‘yansu ta ke ba musamman yadda suke gudanar da al’amura da suka hada da kuma halinda suke ciki dangane da karatunsu.

Akwai wani uba da na sani ‘yarsa tana jami’a amma baisan me ta ke karantawa ba kawai tsakaninsa da ita ya bata kudin makaranta wane hali take ciki babu abinda ya dameshi. Haka kuma ba kowane uba ne yake bibiyar cewa ya karatun ‘yarsa yake a semester kaza ba yarinya tayita samun carryover a karshe har ace sai ta maimaita shekarar amma agidansu babu wanda ya sani, ambarta ita zata yiwa kanta tunani kuma ita zata yankewa kanta hukuncin halinda da ta ke ciki.

Yana da kyau iyaye su dawo daga rakiyar wannan al’ada da take zagwanyar da tarbiyyar da aka dade ana tsuwurwurinta wajen ganin yara sun kasance na gari. Hakkin ka ne ka janyo ‘yarka ajiki kaji kokenta domin ganin yadda zaka maganta mata. Malamai suka gaya mana cewa “manzon Allah yakan zauna da diyarsa Fatima yaji halinda take ciki, haka kuma yakan je har gidanta ya zauna a tare da ita yana jin irin halin d suke ciki ita da mijinta” wannan babban abin koyi ne da iyaye zasu koya daga baban Fatima kakan Hassan da Hussaini salallahu alaihi wasallam. Allah ya shiryemu ya shiryi zurriyarmu.

Yasir Ramadan Gwale

yasirramadangwale@yahoo.com

http://yasirramadangwale.blogspot.com

Monday, January 9, 2012

Cire Tallafin Mai Fitana Ce Cikin Tattalin Arzikin Kasa

Cire Tallafin Mai Fitana Ce Cikin Tattalin Arzikin Kasa

Yanzu dai kusan za a ce ta faru ta kare dan gane da batun da akayi ta dogon turanci akansa wato batun nan na Fuel Subsidy Removal a turance ko kuma janye tallafin albarkatun mai. Kusan wannan batu shi ne goron sabuwar shekarar da gwamnatin tarayyar Najeriya ta baiwa ‘yan kasa na sabuwar shekarar 2012. Tun da gwamnati ta baiyana wannan aniya tata ta janye tallafin man fetur jama’a da kungiyoyi da masana da talakawa sukayi ta jan hankalin gwamnati akan wannan batu cewa ta janye wannan aniya tata, domin kuwa wannan abu zai jefa talakan kasarnan cikin halin kaka nakayi da kazamin talauci. Tun a wancan lokaci gwamnati tayi hasashen cewa idan aka cire wannan tallafi litar mai zata koma N150 daga tsohon farashi na N65.

Bada wannan sanarwa ke da wuya sai al’amura suka sauya. Inda akayi ta ganin dogayan layuka a gidajen mai nan da nan lita ta d’aga daga N65 har zuwa N200 a wasu guraran. sannan kayan masarufi suka yi tashin gwauron zabi haka ma harkokin sufuri suma duk suka sauya daga tsohon farashi, kai kace dama duk jama’a jira suke gwamnati ta janye wannan tallafi su kwashi garabasa. Kusan wani abun ban haushi da kasarmu shi ne duk lokacin da farashi ya tashi kamar shekarun mutum haka yake ma’ana baya sauka. A tarhin Najeriya saudaya farashin fetur ya taba dawowa baya lokacin marigayi tsohon shugaban kasa Mallam Umaru Musa YarAdua inda daga N70 ya koma N65, wanda wannan shi ne irinsa na farko a tarihin farashin man fetur a Najeriya amma duk da haka kayan masarufi basu dawo daga hawan da sukayi ba.

Da yawan ‘yan Najeriya basu san ma wani abu Tallafin man fetur ba sai da wannan batu na janyewa ya taso. Abin tambaya shin menene wannan tallafin da ake bukata wanda aka ce ana baiwa albarkatun man fetur. Wato tunda kungiyar kwadago ta tursasa gwamnati na biyan sabon tsarin albashi na mafi karanci na N18,000 gwamnati ta ke ta neman hanyoyin da zata samar da wancan kudi domin cika wannan alkawari da ta dauka, don haka ne ta fito da wannan batu na cire tallafi, inda za a samu kudin da zata raba tsakaninta da gwamnoni wanda zasu iya biyan wannan sabon tsarin albashi. Ma’aikatan da basu wuce kashi 5 cikin dari na al’ummar Najeriya ba.

Abin tambaya lokacin da ake baiwa albarkatun man fetur wannan tallafi da ake Magana shin amfitar da talaka daga cikin halin kaka nakayi an maganace al’amuran tsaro da ya damu al’ummar kasarnan an samar da wutar lantarki da ruwan sha mai inganci? yanzu waye zai bugi kirji ya gasgata gwamnati cewa da gaske suke bayan cire wannan tallafi za a inganta rayuwar talaka. Wadan nan mutanan da suke rike da madafun iko kafin cire wannan tallafi sune dai haryanzu don haka wannan wani wasan kwaikwayo ne kawai, cewa za a inganta rayuwar talaka bayan cire wannan tallafi babu wani abu da zai canza, tunda shekara 13 da PDP tayi akan mulki bata iya samarwa da ‘yan Najeriya tsayayyar wutar lantarki ba duk da karairay da kumfar baka da akayi ta mana, da kuam irin dimbin dukiyar da aka ce an kashe.

Abin tambaya wai shin gaba daya adadin lita nawa ne ake bukata na al’barkatun mai domin ‘yan Najeriya suyi amfani dashi na fetur da kananzir da man dizal da dangoginsu? Sannan akwai abin da ake cewa “domestic allocation” wato wani abu da ake bayarwa na gurbataccen man fetur din da aka hako shin menene adadin da ake bayarwa saboda wannan? Sannan kuma har ila yau acikin adadin matatun man fetur din da muke da su guda 4 wanne adadi suke bukata na shi wannan allocation domin suyi amfani dashi su tace manfetur da dangoginsa? Shin suna tacewa ko yana saura, kuma idan ya yi saura me ake yi da ragowar? Sannan kuma idan za a shigo da man fetur daga waje a nawa ne ake kashewa kafin da bayan zuwansa kasar nan?

Har wa yau kuma menene rarar da ke tsakanin abinda Najeriya ta ke sayarwa domin ‘yan kasa da kuma abin da ake kawowa daga waje? A ganina sai anyi wannan kididdiga ne sannan zamu gane abu kaza ne muke bukata na shi wannan tallafi, ba wai kawai ayi ta mana dodorido da sunan tallafi ko janye tallafi ba. Kuma wannan abin shi ne yake nuna cewa akwai badakala mai yawa a harkar da ta shafi NNPC domin idan zamu iya tunawa a lokacin gwamnatin Olushegun Obasanjo karkashin mai bashi shawara a harkar manfetur Alh. Lurwanu Lukman ance ambada lasisin kafa sabbin matatu guda 18 ina batun ya kwana?

Sannan wannan batu babu abinda zai kawo sai fitina cikin sha’anin tattalin arzikin kasa, domin indai gwamnati akeyi ta Demokaradiyya ‘yan Najeriya sunce basu yarda ba da wannan aniya ta gwamnati ta janye tallafi. Kuma ita gwamnati bata yiwa al’umma bayani na gaskiya ba akan wannan batu sai kawai gwamnan babban Banki da minister kudi ne suke ta lankwasa harshe akan wannan batu da ‘yan Najeriya sun kasa fahimtar shin wannan tallafi akwaishi ko babu shi, domin wannan abun yana da sarkakiyar gaske, ita kuma gwamnati tana ta yiwa ‘yan kasa kafar angulu.

Kuma idan har da gaske wasu ‘yan tsiraru ne suke amfanar wannan tallafi shin su wane su harda gwamnati ta kasa daukar mataki akansu. Naji mamaki kwarai da gaske lokacin da gwamnan babban Banki yake bayanin cewa manyan mutanenen suke amfanar wannan batu me gwamnati ta keyi da bazata iya fitowa ta kalubalanci wadan nan mutane ba da suke ci da gumin talaka.

Kuma kamar yadda mukaji masana na sharhi akan wannan al’amari taya za a dauki kudinka ayi maka bukata sannan kuma ace wai ambaka wani abu wai shi tallafi ta ina. Bayan dukiyar kasa ce kuma ta al’ummar kasa ce. Kuma idan da gaske gwamnati ta ke mutanan da suka mallaki rijiyoyin man fetur a ina suka samu uban wa ya basu a ina suka gada? Ta kwace su ta dawowa da talakawa hakkinsu mana idan da gaske suke, sannan bayan haka muna sane da yadda akace duk gangar danyan man da aka hako wadan can miyagu azzalumai suna da wani kamasho aciki.

Kasan cewar babu wani yare da gwamnati take saurin fahimtarsa kamar zanga-zanga wannan tasa kungiyoyi sukayi amfani da wannan dama domin shirya gangami na lumana don nuna bacin ransu akan wannan batu. Kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada Kuma Alhamdulillah kusan tun farkon wannan zanga-zanga da aka fara daga Ilori har zuwa kano, kaduna, Abuja, legas, Ibadan, sokoto da sauransu duk babu inda aka samu rahoton ‘yan zanga-zanga sun tayar da hankali hasalima sai dai amfani da jami’an tsaro da gwamnati tayi don muzguna musu musamman a Ilori da Kano inda rahotanni suka ce an kashe mutum biyu tare da raunata daruruwa, da lalata ababen hawa na dalibai da kungiyoyi.

Hakika ansha ankarar da gwamnati cewa irin abin da yake faruwa a kasashen larabawa da akwai yiwuwar zai faru a Najeriya. Allah ya jikan sheikh Ahmad Lemu badan ya mutu ba sai da ya ankarar da gwamnati acikin rahoton da ya mika na musabbabin rikicin bayan zabe. Kuma da alamar abinda ya yi awon gaba da Husni Mubarack a Egypt da Zainul Abiden Ben Ali a Tunisiya da kuma wanda ya yi sanadiyar mutuwar Kanal Gaddafi shi ne zai faru a Najeriya. Hausawa dai sunce a juri bara wai albasa far ace.

Yasir Ramadan Gwale

Yasirramadangwale@hotmail.com

http://yasirramadangwale.blogspot.com