Sunday, January 25, 2015

SA'UDIYYA: Najeriya Ta Mika Ta'aziyar Rasuwar Sarki Abdullah


SA'UDIYYA: Najeriya Ta Mika Ta'aziyar Rasuwar Sarki Abdullah

Mataimakin Shugaban Kasa Alh. Muhammad Namadi(na) Sombo jiya a Riyadh a lokacin da yake wakiltar 'yan Nigeria wajen mika ta'aziyar rasuwar Sarki Abdullah Marigayi. Shugabanni kasashen duniya na cigaba da yin turuwa zuwa Sa'udiyya dan yin Ta'aziya da kuma taya sabon Sarki Salman murnar.

Yasir Ramadan Gwale
25-01-2015

"Malam Yasir Wallahi Zan Zabi Malam Takai Saboda Kai"



"MALAM YASIR WALLAHI ZAN ZABI TAKAI SABODA KAI"

Jiya wani dan uwa aboki kuma amini ya shaida min cewa wallahi shi zai zabi Malam Saluhu Sagir Takai ne saboda ni. Ya shaida min cewa shi baya PDP amma albarkacina zai zabi Malam Salihu Takai. Ba shakka wannan magana ta faranta min Rai na kuma ji dadinta matuka. Wannan dan uwa ya nuna min kauna kuma yayi min kara, Allah ya saka masa da alheri ya barzumunci da kauna.

Ya Allah muna rokonka da sunayanka tsarkaka madaukaka. Ya Allah ka baiwa Malam Salihu Sagir Takai Gwamnan Kano. Allah ka sa mulkin ya zamar masa sila ta budewar kofofin alheri a jihar Kano baki daya. Ya Allah mun kyautata zato a gareka, kai mai ji ne mai kuma amsawa ne. Allah kaine kace mu rokeka zaka amsa mana Ya Allah ka baiwa Malam Salihu Sagir Takai Gwamnan kano.

Ya Allah ka sani muna kaunar Takai sakamakon kyawawan halayensa da dabi'unsa na zahiri da suka bayyana a garemu. Allah ka tabbatar da duga dugansa wajen yi maka da'a da biyayya. Allah ka bashi ikon tsare gaskiya da mutuncin al'ummar Jihar Kano.

25-01-2015

Friday, January 23, 2015

SAUDIYYA: Sabon Sarki Salman Ya Karbi Mubayi'ah


SAUDIYYA: SABON SARKI SALMAN YA KARBI MUBAYI'AH

Khadimul Haramain Ash-Sherifain Sarki Salman Bin Abdulaziz Alsaud yayi jawabin karbar mubayi'ah. Sarki Salman ya taya al'ummar Musulmi da al'ummar Sa'udiyya ta'aziyar rasuwar King Abdullah bin Abdulaziz Al Saud, ya yabawa magabancinsa tare da yi masa adduar samun Rahama, ya kuma ci alwashin dorawa daga inda Abdullah ya tsaya. 

Sarkin Ya kuma bayyana Yarima Mukrim Bin Abdulaziz Alsaud a matsayin sabon Yarima Mai Jiran gado (crown Prince) da kuma Muhammad Bin Nayef Bin Abdulaziz amatsayin mataimakin Yarima Mai Jiran gado, Sarkin ya kuma bada sanarwar nada Yarima Muhammad Bin Salman a matsayin ministan tsoro. 

Allah ya yi masa jagoranci ya bashi ikon hidimtawa addini fiye da magabatansa. Allah ya jikan Marigayi Sarki Abdullah ya gafarta masa, ya lullube shi da RahamarSa, Allah ya kyauta namu zuwan ya sa Aljannah ce makomarmu baki daya.

Yasir Ramadan Gwale
23-01-2015

Thursday, January 22, 2015

Sarkin Saudiyya Na Shida (6) Abdullah Ya Kwanta Dama



SARKIN SAUDIYYA NA 6: ABDALLAH YA KWANTA DAMA

Yau juma’a daya daga cikin manyan ranaku a Musulunci, Allah ya karbi rayuwar Sarki Abdullah Ibn AbdulAzizi Al-Saoud na Saudiyya. Allah yayi Sarki Abdullah rasuwa bayan ya sha fama da jinya ba mai tsanani ba, kamar yadda rahotanni suka nuna Sarki Abddullah ya jima yana fama da cutar Numoniya har zuwa lokacin da hukumomi a Riyad suka bayar da labarin kwantar da shi a wani asibii dake Riyar a makwannin da suka wuce. Abdullah Ibn AbdulAzizi ya rasu yana da Shekaru 90 a duniya, ya rasu yabar ‘ya ‘ya da jikoki masu yawa, haka kuma, Sarki Abdullah shi ne Sarki na Shida (6) tun bayan kafa daular Saudiyya a Shekarar 1930.

Marigayi Sarki AbdulAziz Ibn Abdulrahman Ibn Muhammad AlSaud wanda ake yiwa lakabi da Abu-Turki Akhu-Noura, shi ne ya jagoranci Jihadin kafa Daular Sa’udiyya a yankin Hijaz. Bayan rasuwar Sarki AbdulAziz Alsaud a shekarar 1953, yarima mai jiran gado wanda shi ne babban dansa Sa'ud Ibn AbdulAziz ya gajeshi a matsayin Sabon Sarki na biyu bayan kafa Mamlakatul Araabiyat Ass-Sa’udiyya.

Sarki Saud Ibn AbdulAziz ya karbi Sarauta daga mahaifinsa har zuwa shekarar 1964 lokacin da Allah yayi masa rasuwa. Kafin rasuwarsa Saud Ibn AbdulAziz shi ne wanda ya fara samar da majalisar ministoci a masarautar da suka hada da Ilimi, lafiya da kuma kasuwanci. Haka kuma, Sarki Sau’d ya zabi Gwamnan Riyad na lokacin wanda shi ne kaninsa Faisal Ibn AbdulAziz a matsayin Yarima mai jiran gado, inda bayan rasuwarsa Yarima Faisal Ibn AbdulAziz ya zama sabon sarki na uku.

Sarki Faisal shi ne mutumin da ake ganin har yanzu Sa’udiyya bata yi shugaba kamarsa ba, ana ruwaito Sarki Faisal a matsayin wani mutum mai ra’ayin bin addini sau da kafa, mutum ne mai san yin abu da gaggawa, bai cika wasaba, an bayyana shi a matsayin mutumin da bai cika yin dariya a bainar jama’a ba. Kullum maganarsa itace yadda za’a ciyar da addinin Musulunci gaba da kasashen.
A lokacin Sarki Faisal ne Masarautar Sa’udiyya ta fara samar da kamfanoni da kulla alaka da kasashen Gulf dan habaka tattalin arzikin yankin. Sarki Faisal ne ya jagoranci kafa kungiyaar kasashen Musulmi ta OIC, haka kuma, shi ne Sarkin da ya kafa garin Jeddah a matsayin cibiya ta kasuwanci. Sarki Faisal ya damu da harkokin addini ainun a zamanin Mulkinsa.

Sarki Faisal ya rasu a shekarar 1975, inda bayan rasuwarsa ne Yarima na lokacin kuma Gwamnan Riyadh, Khalid Ibn AbdulAziz ya zama sabon Sarki na hudu. Sarki Khalid shi ne Sarki na Farko da ya fara tsallaka Hijaz zuwa kasar Amurka domin yin ziyara da kuma bude ido. Sarki Khalid yayi kokari wajen kulla alakar kasuwanci tsakanin kasashen yankin Gulf inda ya samar da kungiyar GCC da ta hada Qatar, Kuwait, Bahrain, Oman, Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Saudiyya.
Bayan da Allah ya yiwa Sarki Khalid Rasuwa a shekarar 1982 ne Fahad Ibn AbdulAziz ya zama sabon sarki. Sarki Fahad shi ne Sarki mafi dade a kan karagar Mulkin Saudiyya domin ya shafe Shekaru 23 a matsayin Sarki. Sannan kuma, shi ne mutum na farko da aka fara yiwa lakabi da Khadimul Haramain Ash-Sherifain (Custodian of the two holy mosques), Sarki fahad ya kawo sauye sauye masu yawa a kasar Saudiyya ta fuskar lafiya da ilimi da gina kasa da habaka tattalin arziki.

Haka kuma, Sarki Fahad shi ne mutumin da ya tsaya kai da fata wajen ganin an samu ‘yantacciyar kasar Palasdinu, da kuma tsayawa wajen warware mamayar da Iraqi ta yiwa Kuwaiti, haka kuma ya tsaya kai da fata wajen ganin an warware rikicin kasashen Bosnia-Herzegovina, Kosovo, Checniya, Afghanistan, Somaliya da kuma yankin Kahsmir. Bayan haka, a lokacin Sarki Fahad ya maida hankali wajen taimakawa kasashen Musulmi matalauta da suka hada da Somaliya da Bosniya da Afghanistan da sauransu. Allah ya yiwa Sarki Fahad rasuwa a shekarar 2005, inda Yarima mai jiran gado Marigayi Abdullah ya gajeshi, Abdullah shi ne mutumin da yafi kowa daukan lokaci a matsayin Yarima mai jiran gado.

Bayan zamansa Sarki na shida ne Abdullah Bin AbdulAziz ya zabi kaninsa Nayef a matsayin Yarima mai jiran gado, sai dai cikin kaddararSa Subhanahu Wata’ala, Yarima Nayef ya riga Sarki Abdullah rasuwa, inda aka maye gurbinsa da Yarima Salman a matsayin sabon yarima mai jiran gado. Sarki Abdullah za’a jima ba’a manta da shi ba, domin ya cigaba da amsa sunan Khadimul Haramain Ash-Sherifain inda ya kawo sauye sauye masu yawa a Masallacin Makkah da Madina da ba’a taba gani ba a tarihin Saudiyyah. Yayi aiki tukuru wajen ganin ya hidimtawa Masallatan Allah masu alfarma. Ya taimaki addinin Allah gwargwadan iko.

Sarki Abdullah ya samar da manya-manyan jami’o’in kimiyya da fasaha da kere-kere guda biyu da suka hada da Jami’ar King AbdulAzizi da kuma Jami’ai Noura ‘yar uwar mahainsu. Kafin zamansa Sarki Abdullah ya rike mukamai da yawa na Minista inda ya rike ministan tsaro da kasuwanci da cikingida sannan ya zama Gwamnan Riyadh. Sarki Abdullah Bin AbdulAzizi ya rasu yana da Shekaru 90 a duniya a lokacin da Saudiyya ta cika Shekaru 84 da kafuwa. Za a jima ana tunawa da Sarki King Abdullah bin Abdulaziz Al Saud wajen tsayawarsa kai da fata akan kasar Bahrain wajen ganin bata fada hannun 'yan Shiah ba.

Yanzu dai Yarima Salman Ibn AbdulAziz dan shekara 79 shi ne zai zama sabon Sarki na bakwai (7), inda shima ya zabi wani matsahi Yarima Mukrim a matsayin mai jiran gado, kuma shi ne ake zaton mutum na karshe daga ‘ya ‘yan AbdulAziz da zai rike Sarautar Mahaifinsu. Yau in sha Allah bayan kamala Sallar Juma’ah za ayi jana’izar Sarki Abdullah. Muna yi masa adduar Allah ya jikansa ya gafarta masa ya sa Aljannah ce makomarsa, Allah ya biyashi ladan hidimar da yayi dakunanSa masu alfarma a Makkah da Madina, Allah ka yafe masa kurakuransa. Allah ya kyauta bayansa. Allah ka jikan Musulmi.

Yasir Ramadan Gwale
22-01-2015

Sunday, January 18, 2015

Kuskuren Wasu Musulmi Akan Jaridar Kasar Faransa


KUSKUREN WASU MUSULMI AKAN JARIDAR FARANSA

Nakan ga mutane da yawa na yada wasu hotuna na wadan da ba Musulmi ba, da suka yi maganganu na yabawa tare da jinjina ga fiyayyan Halitta Manzon Allah SAW. Ai a matsayinmu na Musulmi tuni Allah ya bamu labarin waye Manzon Allah a cikin alQuraani, yanzu mu da Allah ya bamu labarin ManonSa Sallallahu Alaihi Wasallam, har akwai wani arne da zamu dinga yada maganarsa dan ya yabi Manzon Allah? Duk abin da wani mushuriki daga Mushirikan wannan zamin zai fada na yabawa Manzon Allah, ba zai amfaneshi da komai ba idan bai yi Imani da shi ba, haka kuma, duk wani abu da zai fada bai kai ABU-TALIB ba. Dan haka, idan zamu yada kyawawan Maganganu da aka fada akan Manzon Allah SAW, mu koma cikin al-qurani muji me Allah yace akan ManzonSa Sallallahu AlaihiWasallam.

Haka kuma, yana da kyau mu sani, da yawa masu yada hotunan wannan jarida suna taimakawa gidan jaridar ne wajen yada hotunan. Ba daidai bane, dan mutum zai yada bayanan wannan Jarida sai ya sanya zanen batancin da sukayi akan fiyayyan halitta dan nuna munin aikin da suka yi. Lallai mutane su kaucewa yada hotunan wannan La'anniyar Jarida kuma a yi ta La'antar jaridar.

Sannana kuma, duk wanda zai La'anci wannan Jaridar lallai ne ya halarto da 'yan SHIAH a cikin la'antar tasa. Domin 'yan SHIA sune suka fara zana hoton Manzon Allah suka nuna shi ya daga hannun Sayyadun Aliyu Ibn Abi-talib a matsayin Khalifa. Mabiya Addinin SHIAH sune suka fara yiwa Musulunci zagon kasa kafin wasu arna suyi. Dan haka babban kuskure ne, mutane su dinga La'antar Jaridar kasar Faransa ba tare da sun La'anci 'yan SHIAH masu zana hotan Manzon Allah SAW da Iayalan gidansa ba.

Muna yin Bakarariyar adduar akan duk wanda ya zana hoto yace Manzon Allah ne, ko waye shi Ya Allah ka tsine masa albarka, Allah ka wulakantashi ka La'anceshi, ka kumbura cikinsa, kasa yayi mutuwar wulakanci. Allah ka wargaza shirinsu da sha'aninsu. Allah kar ka basu zaman lafiya da nutsuwa da kwanciyar hankali. Wannan Adduah zamu cigaba da yinta akan wannan La'ananniyar Jarida da kuma 'yan SHIAH masu zana hoton Manzon Allah da iyalan gidansa.

Haka kuma, wannan ba shi ne dalilin da zai sa a farwa wadan da ba Musulmi ba, da basu san hawa ba basu san sauka ba. Arna irinsu Devid David Cameron da suke daurewa wannan cin fuskar addinin gindi suma mu dinga halarto su muna tsine musu. Allah ya taimaki Musulunci da Musulmi ya kaskantar da kafirci da kafirai.

Yasir Ramadan Gwale
18-01-2015

Tuesday, January 13, 2015

NIGER: Ya Zama Dole Shugaba Mouhammadou Isoufou Ya La'anci Jaridar Kasar Faransa


NIJAR: SHUGABA MOUHAMMADOU ISOUFAOU MUNA JIRAN KA KA NUNA FUSHI AKAN BATANCIN DA JARIDAR FARANSA TAI AKAN MANZON ALLAH SAW

Shugaban Jimhouriyar Nijar Mouhammadou Isoufou na daya daga cikin Shugabannin kasashen duniya 50 da suka hadu a birnin Paris a kwanaki biyu da suka wuce, inda suka nuna alhini tare da nuna cikakken goyan baya ga uwargijiyarsu Faransa akan abinda suka kira da "Harin Ta'addanci" da aka kaiwa Jaridar Charlie Hebdo, wacce ta yi batanci ga Manzon Allah, Annabi Muhammadu (SAW). 

Shugaban NIjar Mouhammadou Isoufou ba shi kadai ne shugaban kasar Musulmi da ya halarci wannan gangami ba, akwai shugaban kasar Mali IBK da shugaban Palasdinawa Muhamud Abbas Abu Mazine da Sarkin Jordan. Dukkansu sunyi Allah wadai da abinda akaiwa wannan la'annaniyar Jarida sun kuma tausayawa kasar Faransa da iyalan wadan da aka hallaka. Sai gashi a jiya wannan jarida La'ananniya ta kuma yin zanen batanci ga cikamakin Annabawa Manzon Allah SAW.

Ba shakka, wannan ya zama wajibi ga Shugaba Isoufou da ke zaman kwabci a garemu, muyi kira a gareshi da kakkarfar Murya akan ya fito fili yayi Allah wadai da wannan aikin ta'addanci da wannan Jarida tayi, ko kuma mu lissafashi sahun makiya musulunci, masu yiwa addinin Allah zagon kasa. Wadan da suka fifita martabar Duniya kan ta lahira. Martabar Manzon Allah tafi Martabar kasar Faransa da tarayyar Turai a idan al'ummar Musulmin Kasar NIjar baki daya. Dan haka muna kira ga Shugaba Isoufou da ya fito fili balo-balo yayi Allah wadai da wannan jarida kamar yadda yayi Allah-wadai ga maharan da suka kashe ma'aikatan ta.

Allah ya taimaki Musulunci da Musulmi ya kaskantar da kafirci da kafirai. Allah ka rusa wannan Jarida ka hada su da dukkan dangin bala'in duniya da lahira. Allah ka lalatasu ka wargaza sha'aninsu gaba daya.

YASIR RAMADAN GWALE
13-01-2015

Monday, January 12, 2015

Me Zai Hana A Gano 'Yan Matan Chibok?


IDAN HAR ZA'A IYA GANO JIRGIN AIR ASIA, ME ZAI HANA A GANO 'YAN MATAN CHIBOK?

Hukumomi a Jakarta-Indonesia sun bayar da sanarwa tsamo baraguzan jigin saman kamfanin Air Asia da ya lume a ruwa da kusan mutane 170. Bayan an tsamo gawarwakinsu an kuma tsamo dagargazazzun baraguzan jirgin daga cikin teku, sannan abu mafi muhimmanci, shi ne, an gano jakar da ake kira Bakin Akwatu, dan samun bayanan yadda jirgin ya fadi.

Shi dai wannan Jirgi na Air Asia, an daina jin duriyarsa ne gaba daya bayan da rahotanni suka ce ya tashi daga Surabayo a kasar Indonesia zuwa Singapore. Jirgin ya bace bat, kamar yadda hakan ta faru a makwabciyar Indonesia wato Malaysia a Shekarar da ta gabata. Tun daga nan, aka shiga laluben inda jirgin ya shiga, inda aka bazama nema ta sama ta kasa da ta cikin ruwa. Da taimakon Allah masu linkaya suka fara gano alamun cewa jirgin ya lume ne a ruwa.

Hukumomi a Jakarta sun dukufa haikan, wajen tsananta bincike a ruwa, har Allah yasa aka kai daidai inda jirgin ya fadi kuma aka tsamo garwakin mutane da yawa, sannan dirka-dirkan baraguzan jirgin da suka tarwatse a ruwa suka lume duk aka lalubo kuma aka dauko su zuwa gabar teku. Wannan wata muhimmiyar Nasara ce da Hukumomi suka ci a Jakarta-Indonesia wajen gano wannan jirgi.

A Najeriya shekarar da ta gabata aka bada labarin sace 'yan mata sama da 200 a makarantar Sakandiren Chibok, wanda kafin sace na Chibok sai da aka sace 10,20,30,40 a garuruwan Miri, Mafa, Konguga da sauransu. Sace 'yan matan Chibok ya daurewa mutane kai da dama a duniya, ta yadda d dama suna mamaki yadda  za'a ce an saci wadannan 'yan mata. Kusan da yawa sun karyata labarin faruwar hakan in banda su Boko Haram sun saki wani faifan Video da ya nuna wani sashe na 'yan matan.

Satar wadannan 'yan Mata ta dauki hankalin duniya sosai. Inda har hakan yayi sanadiyar samar da kungiyar #BringBackOurGils wannan ya karade kusan ko ina a duniya, inda aka dinga ganin manyan mutane da Hash Tag na kiran a dawo da 'yan Matan Chibok da suka hada da Matar Obama, McCain da Piraministan Burtaniya Cameron. Na tabbata wannan al'amari da a wata kasa ne ba Najeriya ba ko Afeika da tuni wani batun ake daban.

Lallai inda gaske ne kasashen duniya su taimakawa Najeriya wajen ganin an ceto wadannan mata na Chibok. Ya kamata kamar yadda muka ga an taru a Paris dan taya faransa Makokin mutane 12, to akalla Shugabannin Afurka gaba daya su taru a garin Chibok dan jajantawa iyayan wadannan 'yan mata, tare da matsawa Gwamnatin Najeriya tayi duk abinda ya kamata wajen ganin an kubutar da 'yan matan Chibok.

Gaskiya a shekarar 2014, batun sace 'yan Matan Chibok shi ne abinda yafi bani mamaki matuka da gaske, abin kamar wasan-kwaikwayo amma kuma gaskiya ne, ace an sace Mata sama da 200 kamar Tumaki. Satar wadannan Mata ba ita ce abu mafi ban mamaki ba, illah yadda akayi aka sace su din, domin a Najeriya wannan ba abin mamaki bane sace mutum, dan an taba sace Gwamna Chris Ngige yana matsayin gwamna aka ce an sace shi. Amma yadda aka sace din shi ne zai fi zama abin mamaki.

Watakila nan da wani lokaci Najeriya ta zama kasa mafi abubuwan al'ajabi a duniya, indai ba al'amura ne suka sauya. Domin abinda ake jin ba zai taba faruwa ba a wata kasar to  Najeriya yana faruwa. Allah ya kyauta.

Yasir Ramadan Gwale
12-01-2015

Sunday, January 11, 2015

Shugabannin Duniya 50 Sun Hadu A Faransa, Yaushe Ne Shugabannin Afurka 50 Zasu Hadu A Najeriya Dan Jajantawa Mutanan Borno?


SHUGABANNIN DUNIYA 50 SUN HADU A FARANSA, KO YAUSHE SHUGABANNIN AFURKA 50 ZASU HADU A NAJERIYA DAN JAJANTAWA MUTANAN BORNO?

Yau kamar yadda hankalin dukkan manyan kafafen yada labarai ya karkata, Shugabannin kasashen duniya ance yawansu ya kai 50 sun hadu a Paris dan taya Faransa Makokin mutane 12 da aka kashe a makon jiya. Kisan wadannan mutane ya ja hankalinkasashen duniya sosai, ta yadda wasu kasashen da suka shafe Shekara da Shekarau ana kashe-kashe ba ji ba gani, amma sai gasu suna sahun gaba wajen jajantawa Faransa tare da Allah-Wadai da wadannan maharan da suka kashe mutum 12.

Idan ba'a mantaba wannan gidan Jarida da aka kaiwa wannan hari, ita ce Jaridar da ta dinga zana hotunan batanci ga fiyayyen Halitta Annabi Muhammas Sallallahu Alaihi Wasallam. A lokacin da wannan Jarida take yada wadancan hotuna na batanci tare da bakantawa Musulmi Rai, gani ake 'yancin fadin albarkacin baki ne, da 'yancin bayyana ra'ayi, a lokacin mafiya yawancin Shugabanni sunyi gum da bakinsu, aka bar mutanan da aka kira zauna gari banza sukai ta zanga-zanga suna Allah-wadai. To Allah ba zai taba barin wanda ya taba martabar ManzonSa SAW ya zauna lafiya ba.

Babban abinda ya bani mamaki a wannan gangami na nuna alhini da goyan baya da manyan kasashen duniya sukaiwa Faransa, shi ne haduwar Primamistan Palasdinawa Mahmoud Abbas Abu-Mazin da Piraministan Israeli Benjamin Netanyahu - בנימין נתניהו. Inda dukkansu suka hadu a Paris suna Allah wadai da kisan da akayi. Sun manta da dukkan rayukan da Israeli take kashewa na Palastinawa, wannan ya tabbatar da shi kansa Mahmoud Abbas Abu-Mazine makaryaci ne mara kishi ne kamar yadda aka jima ana masa zargi. Duniya Mai Abin Mamaki!

Tambayar da nayi it ce, mu anan Afrika yaushe ne Shugabannin wannan Nahiya zasu hadu a Abuja dan taya Najeriya zaman makokin hare-haren da ake kaiwa Borno da Yobe da sauran jihohin Arewa babu kakkautawa? Ana kashe al'umma ba kakkautawa amma Shugabannin Afrika basa nuna wata damuwa. Yaushe ne SHugaban Nijar Mouhammadou Isoufou da IBK na Mali da suka ja faransa zaman Makoki zasu maida hankali wajen kula da rayukan al'ummarsu.

Yaushe ne Shugaban kasar Najeriya zai je katse dukkan hidndimun Gwamnati dan taya al'ummar Borno da Yobe alhinin abinda ke faruwa? Allah yana bamu shugabanni daidai da irin halayyarmu, idan mun sauya Allah zai sauyamu, idan bamu sauya ba, zamu jima muna zargin juna akan halin da muke cikin na rashin shugabanci na gari.

YASIR RAMADAN GWALE
11-01-2015

Abinda Soji Sukaiwa 'Yan Agajin Izala


ABINDA SOJI SUKAIWA 'YAN AGAJIN IZALA

Yau mun wayi gari da labari mara dadi daga cikin irin labaran da suke fitowa kowacce safiya daga garuruwanmu, cewa wani Shu'umin soja azzalumi dan ta'adda ya bude wuta ga tawagar 'yan Agajinmu na Izala a lokacin da suke dawowa daga garin Misau a daren jiya bayan kammala wa'azi. Bayanai sun nuna cewa sojojin da ke kan hanya a shingen masu bincike sun tare wannan mota, bayan gamsuwa da bayanai sojojin suka baiwa motar umarni ta shige.

Bayan haka, tashin motar daga shingen jami'an tsaron ke da wuya aka ce wani soja ya budewa motar wuta, wanda hakan yayi sanadiyar jikkatar dan uwa dan agaji. Akan wanne dalili aka budewa wannan mota wuta? Wannan cikaken zalinci ne da sojojin da muke tausayawa a lokacin da aka yankewa wasu daga cikinsu hukuncin kisa bisa abinda ake gani zalinci ne wannan hukunci. Wadannan sojoji su ne mukewa fatan alheri tare da yaba musu akan yadda suka bayar da rayuwarsu dan kare kasarmu, amma abin takaici mu da muke musu fatan alheri mu zasu dinga budewa wuta akan hanya!

Ba shakka munyi Allah-wadai da wannan aikin ta'addancin da soja sukai mana, muna kuma kiran da lallai ayi bincike dan kamo wannan soja da ya aikata wannan aikai-aika dan a hukuntashi bisa tanadin dokar kasa. Adalci shi ne zai zaunar da mu lafiya ba zalinci ba. Babu yadda za ayi ace sojojin da muke tausayawa a lokacin da suke cewa an zalince su kuma ace akanmu zadu dinga huce haushi.

Lallai mun san cewa jami'an tsaronmu suna kokari wajen kare Najeriya daga hare-haren 'yan ta'adda, wannan kuma ba zai taba zama dalilin da zai baiwa Sojoji lasisin aikata mana zalinci ba a lokacin da suke guduwa daga garuruwa suna barin aiki.

Muna fatan Allah ya sanya mana aminci da nutsuwa a kasarmu. Allah ya bamu lafiya da zaman lafiya. Ina kuna amfani da wannan dama wajen mika sakon na na taya jaje ga Shugaban Izala na kasa Sheikh Bala Lau Abdullahi a bisa wannan abu da ya faru Allah ya kiyaye aukuwar haka anan gaba.

Yasir Ramadan Gwale
11-01-2015

Saturday, January 10, 2015

Abinda Sheikh Gumi Ya Tsoratar Da Faruwarsa


ABINDA SHEIKH GUMI YA TSORATAR DA FARUWARSA

Allah ya sakawa Sheikh Dr. Ahmed Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi da alheri, kusan wannan shi ne abinda yayi nuni da faruwarsa a siyasar 2015, dan kaucewa fadawa wannan yanayi SHEIKH GUMI yayi kira ga GEJ da GMB da su hakura da tsayawa wannan zabe, abinda aka kasa fahimtar Malam Gumi. Bankawa motocin shugaban kasa a Jos wuta wannan Sam ba dai dai bane, haka kuma na kara tabbatar da zargin da ake mana na tada hankali.

Alhamdulillah, na ji dadin da Buhari da kansa yayi Allah-wadai da wannan aikin 'yan ta'adda wadanda basarwa nufi Najeriya alheri, ya kuma nesanta kansa da duk wanda yake zaton yayi haka dan nuna goyon baya gareshi, wannan shi ne dattaku abinda GMB yayi. Yana da kyau musani duk abinda bamu tsaya mun sameshi cikin sauki ba tashin hankali ba zai bamu ba. Duk mutumin da kewa GMB fatan yaci zabe ba abinda yake so kamar ayi zabe lafiya. 

Wannan abin a musulunce haramun ne, domin barna ce, lalata dukiya ne, almubazzaranci ne, Allah kuma ya hana almubazzaranci. Haka kuma, indai mun fahimci manufar siyasa shi ne a kyale kowa yayi ra'ayinsa, na meye, wasu zasu hana wasu ra'ayinsu? Kada mu manta GMB yana bukatar goyan baya a kudanci dan cin zabe, kamar yadda yake a Arewa, dan haka bai kamata mu bayar da kofar da za'a ci zarafin magoya bayan GMB a kudu ba. Dan haka mutane suji tsoron Allah su kaucewa tashin hankali cikin wannan zabe. 

Allah ya la'anci masu tada fitina. Allah ya bamu zaman lafiya, ya sa ayi siyasa cikin kwanciya hankali. Ayi zabe lafiya.

YASIR RAMADAN GWALE
10-01-2015

Akwai Alamun Yiwa GMB Yankan Baya A Wannan Zaben


AKWAI WANI ABU DA KE FARUWA A APC

A wannan karon GMB yayi kokari domin ya nuna gogewa a siyasa kwarai da gaske, idan mutum ya kalli sunayan yan kwamatin yakin neman zaben Buhari zai san cewa GMB ya nuna gogewa domin ya nada kansa Shugaban kwamatin Koli na yakin neman zabensa, sannan ya nada gwamna Amaechi a matsayin babban Darakta, bayan nan kuma ya nada Alh. Atiku Abubakar a matsayin babban mataimaki mai kula da yankin Arewa, a hannu guda kuma ya nada Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a matsayin babban Mataimaki mai kula da yankin Kudu.

Siyasar da GMB ya nuna a wannan gabar, ita ce ta dakushe kafafar da shi Bola Tinubu yake yi, idan kullum yake kiran kansa a matsayin JAGORAN APC NA KASA (APC NATIONAL LEADER), anan GMB ya ragewa wancan ikirari na Tinubu karfi, domin shi GMB din ne da kansa ya zama Shugaba, dan haka Tinubu dole yayi biyayya a mtsayin mataimaki babu sauran nuna cewa shi ne APC National Leader a kasa baki daya.

Bayan haka, alamu na nuna cewa akwai wasu al'amura dake faruwa a sha'aninsu Tinubu da suke jin APC tasu ce su yasu, domin, tunda GMB ya kaddamar da yakin neman zabe a Jihar Ribas a kudancin Najeriya, har kawo yanzu da GMB ya halarci jihohi wajen 7, amma ba'a ga keyar Tinubu ba wajen wannan gangamin yakin neman zabe. Dan haka wannan wani siginal ne da yake nuna kodai Tinubu baiji dadin wannan nadin da GMB yayi masa ba, na maida shi mataimaki maimakon kullum ya zama Jagora kamar yadda yake nada kansa, ko kuma akwai wani shiri tsakaninsa da mai-malfa kamar yadda wasu ke dari-dari.

Sannan kuma,  mutane irinsu Gwamna Rochas okorocha da Chris Ngige alamu sun nuna da gaske suke wannan tafiya, domin kuwa tunda aka fara wannan karakaina ta yakin neman zabe dasu ake yi. Bayanai sun nuna cewa, Gwamna Rabiu Musa kwankwaso na Kano da Tsohon Gwamnan Gombe Danjuma Goje da Tsohon Gwamnan Kwara Bukola Saraki da Malam Nasiru el-Rufai duk sunyi kokarin matsawa GMB akan lallai ya dauki Gwaman RIbas Rotimi Fashakin a matsayin mataimakin shugaban kasa, yayinda  shi GMB ya mika wannan dama kacokam ga Tinubu inda ya zabo Osinbajo.

Rashin ganin fuskokin su Kwankwaso, Goje, Bukola, el-Rufai ( duk da cewa el-Rufai shima yana takarar gwamna da take bidar lokacinsa) amma hakan na nuna basu ji dadin rashin daukar Amaechi da ba'ayi ba a matsayin mataimakin Shugaban kasa. Haka kuma, tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar ba'a ga motsinsa ba a wannan gaganiya in banda ta facebook, watakila ko dan yana Arewa ne ba'a zo yankinsa shi yasa bamu ga fuskarsa aba.

Amma lallai akwai tsoron kada ayiwa wannan tafiya ta GMB yankan baya,a wannan zabe. lokaci dai alkali ne.

Yasir Ramadan Gwale
10-01-2015

Friday, January 9, 2015

Da Buhari Dan kano Ne Ba Shakka Takai Zai Zaba


TABBAS DA BUHARI A KANO ZAI YI ZABE TAKAI ZAI ZABA

Ba ko shakka akan cewa idan da GMB dan Kano ne kuma a kano zai yi zabe, to la shakka Malam Salihu Sagir Takai zai zaba a matsayn gwamnan kano na gaba. Mun kwana da sanin cewa GMB mutum ne dan kishin kasa mai kaunar cigaba, da kaunar aiki tsakani da Allah ba cuta ba cutarwa, GMB mutum ne da bai yadda da kashe mu-raba ba, GMB bai yadda da aikin Baba-Rodo ba, dan haka idan GMB zai yi zabe a kano to ba shakka zai bakace tsakanin 'yan takarar Gwamnan Kano guda biyu sannan ya zabi Takai a matsayin gwamnan kano na gaba, domin shi kansa GMB ya san da cewa yanzu lokaci ne da yake bukatar mutane masu gaskiya da zai iya yin aiki da su ko da kuwa bai hada jam'iyya daya da su ba.

Idan ka Dauki Malam Salihu Sagir Takai yayi Shugaban Karamar Hukuma, yayi Kwamashinan kananan hukumomi, sannan yayi kwamashinan ruwa, wanda ya cimma gagarumar nasara a duk inda yayi aiki. Domin yana Shugaban Karamar Hukumar Takai a APP Gwamnatin Kano karkashin PDP ta yaba da dukkan irin ayyukan da yayi, a saboda haka ma gwamnatin ta gayyaci Shugaban Kasa na lokacin Olushegun Obasnjo yaga ayyukan raya kasa a karamar Hukumar Takai a lokacin.

Haka kuma, lokacin da Takai yana Kwamashinan Kananan Hukumomi, duniya ta shaida cewa karkashin kulawarsa ba'a taba yiwa wata karamar hukuma kwangen kasonta na wata-wata ba, hasalima an gudanar da zaben Kananan Hukumomi a Kano inda kowaanne zababben Ciyama yake karbar kudinsa ba tare da anyi musu wani gibi ba. Malam Takai ya tsaya ya kula da aikinsa na Kwamashina tsakani da Allah tare da tabbatar da cewar kowacce karamar hukuma na karbar kasonta cikin lokaci, wadannan bayanan na nan aje a ma'aikatar Kanan hukumomi inda Takai yayi aiki.

Haka zalika, Malam Salihu Sagir Takai yayi Kwamashinan Ruwa na Kano, inda karkashin Jagorancinsa aka samu gagarumar Nasarar gina Matatar Ruwa irinta ta farko a fadin Najeriya. Takai ya tsaya anyi aiki bilhakki da gaskiya a ma'aikatar Ruwa ta kano dan ganin an samar da Ruwan da zai iya kaiwa zuwa bukatunjama'ar Kano. Haka kuma, an gyara tare da inagnta matatun Ruwa na Watari da Guzu-guzu a lokacin. Wannan wata gagarumar Nasara ce da Takai Ya samu a lokacin da ya jagoranci Ma'aikatar Ruwa a matsayin kwamashina.

Idan kuma muka koma bangaren Mataimakin Gwamna na Yanzu Abdullahi Umar Ganduje, wanda shi ne Kwamashina na ma'aikatar Kananan Hukumomi a zamanin da suka yi gwamnati a Zango na farko da wannan Zango na biyu. Gwamantin Kano Karkashin Jagorancin Gwamna Rabiu Musa Kwankwanso tare da dafawar mataimakinsa Abdullahi Umar Ganduje bata yi zaben Kananan Hukumomi ba sai da ta shafe shekaru uku akan karagar Mulkin, Sannan a iya tsawon wadannan Shekaru da Gwamnati tayi babu zababbun Shugabannin Kananan Hukumomi, Gwamnatin Jiha ce ke karbe kudadan Kananan hukumomi da suke zuwa daga Aljihun Gwamnatin Tarayya, Bayanai sun tabbatar da cewar wannan Gwamnati tayi Mursisi akan kudin Kananan Hukumomin Kano da suka kai har Naira Biliyan 255 a tsawon Shekaru uku babu zababbun shugabanni kananan hukumomi.

Haka kuma, Mataimakin Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje yana Kwamashinan Kananan Hukumomi, Gwamnatin Kano tayi alkawarin Gina Tituna masu tsawon Kilomita Biyar a kowacce karamar Hukuma, amma sama da kashi 75 na wannan aiki babu shi babu dalilinsa. Anan Facebook na karanta kamar wattani huddu da suka wuce, Hamza Ibrahim Baba dan asalain Karamar Hukumar Dawakin-Tofa  kuma daya daga cikin masu tallata Ganduje, wadda karamar hukumar Abdullahi Umar Ganduje ce, yana kalubalantar rashin yi musu aikin titin karamar hukumarsu, inda yayi korafin cewar an fara an dakatar da aikin, a daidai wannan lokacin ne Mu'azu Magaji Sarauniya wanda shima dan karamar hukumar Dawakin-Tofa ya mayarwa da Hamza martani da cewar laifin Ma'aikatar kananan Hukumomi ne da shi mataimakin gwamna Abdullahi Umar Ganduje ke jagoranta na rashin cin-nasarar wannan aiki.

Daga nan aka bude sabon babin muhawara inda nan take Hamza Ibrahim Baba ya kare abin da cewar ai aikin gina wadannan hanyoyi yana karkashin ma'aikatar kasa ne (Land), daga nan shi Muaz Magaji ya sake kalubalantar Hamza cewa ai Kwamashinan Kasa na yanzu shi Ganduje ne ya kawo shi akai masa Kwamashina, domin haka kowanne irin kasawa aka samu laifin na ma'aikatar Kananan Hukumomi nekarkashin jagorancin Mataimakin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a cewar Muazu Magaji Sarauniya.

A saboda haka, tayaya GMB zai zabi Abdullahi Umar Ganduje mutumin da ya kasa cimma nasarar gina tituna masu tsawon Kilo Mita Biyar a cikin Shekara Hudu duk kuwa da irin makudan kudaden da aka antayo kananan Hukumomin Jihar Kano daga Gwamnatin Tarayya amma Gwamnatin Jiha karkashin Gwamna da mataimakinsa Abddullahi Umar Ganduje na tare kudin. Dan haka ne, Ya zama wajibi GMB ya zabi cancanta, ya zabi Malam Salihu Sagir Takai mutumin da ya cimma nasarar sama da kashi 90 na aikin gina sabuwar matatar Ruwa ta Tamburawa ta  da babu irinta a Kano, ya tabbatar an baiwa ko wacce karamar Hukuma kasonta ba tare da an rike musu kudade ba. Ba shakka da Buhari dan Kano ne Takai zai Zaba. Dan Haka Al'ummar Jihar Kano Ku Zabi Malam Saluhu Sagir Takai dan Zama Gwamnan Jihar Kano Na gaba.

YASIR RAMADAN GWALE
09-01-2015

Wednesday, January 7, 2015

ZABEN 2015:Babu Sauran Ci-Da-Buguzum


ZABEN 2015 BABU SAURAN CI-DA-BUGUZUM

An dade ana magana akan irin yadda wasu 'yan siyasa ke fakewa da farin jinin wasu mutane dan samun nasarar zabe, kuma su kasa tabuka wani abin kirki bayan sunci zabe, sai dai ga dukkan alamu wannan ci-da-buguzum yazo karshe a wannan zaben. Domin kuwa Idan muka duba batun kaddamar da takarar da GMB yayi a Jihar Ribas, ya isa ya zama ishara ga duk masu jiran ci-a-bagas cewa wannan lokacin na kowa tasa ta fishsheshi ne, dan kuwa shi, GMB ya gabatar da kansa gaban dumbin jama'ar da suka taru ya gaya musu sunansa Muhammadu Buhari yana neman takarar Shugaban kasa, kuma yana rokon su zabe shi, dan kawo sauye-sauye a harkar tafiyar da Gwamnati a najeriya. 

Abinda hakan ya nuna a wannan karon, shi ne cewar Siyasar GMB ta sauya, domin kuwa a Ribas GMB bai daga hannun kowa ba, abinda yake nuna sai dai kowa tasa ta fishsheshi, dan haka wannan babban albishir ne GMB ya yiwa masu jiran ci-a-bagas cewa babu hannun wanda zai daga dan ya rabu da shi yaci zabe, dole kowa tasa ta fishsheshi, wadan da suka kwanta a gida suna jiran GMB yazo jihohinsu ya daga hannunsu dan ci-da-buguzum wannan lokacin ya wuce.

Ina kuma jinjinawa GMB akan wannan mataki da ya dauka, ba shakka wannan abin yabawa ne, kuma wani cigabane a Demokaradiyya. Babu sauran shiga rigar Buhari a ci zabe, mun san GMB na kowa ne, yana da mutane a ko wace Jam'iyya.

Yasir Ramadan Gwale
07-01-2015

Tuesday, January 6, 2015

Duna Wakilin Arna


DUNA WAKILIN ARNA

Sau da yawa nakan ji irin wannan magana ana yinta, kuma kai tsaye a jingina ta ga Malam Ibrahim Shekarau. Kalmomi ne guda uku kalmar DUNA da WAKILI da kuma ARNA, wadannan su ne suka bada jumla mai bada maa'ana. Idan muka dauki kalmar DUNA wannan kalma tana nufin wani LAUNI mai duhu ko kuma ace baki, launi shi ne ko ita ce color da turanci, ya Allah wannan launi na mutum ne, ko dabba, ko wani abu da ababen halitta suka samar. Ana jingina kalar DUNA ga Malam Ibrahim Shekarau saboda yanayin launin jikinsa da yake da duhu!

Allah buwayi gagara misali, shi ne mamallakin mamallaka. Shine ya Halicci Abu Jahal da Abu Lahab daga cikin dangin Bamu Hashim, cikin kabilar Kuraishawa a cikin Larabawa. Idan akayi maganar al'umma aka ce larabawa to su ne karshe, domin Allah buwayi gagara misali ya sanya Manzon Allah SAW cikamakin Annabawa ya zam balarabe kuma cikin kabila mafi buyawa a tsakanin kabilun Larabawa, hakanan ya sanya Manzon Allah ya fito daga tsatso na gidi wato irijinal din, BANU HASHIM, ga kasancewarsu Larabawa ga kyaun suffa, ga shi Annabin da Allah ya ce shi ne cikamakin Annabawa ya fito daga cikin wannan kabila, wannan ya isa abun alfahari, idan ana cikin muhalli na alfahari.

Kasancewar mutum Bahashime Bakuraishe Balarabe, wannan ba zai amfaneshi da komai ba face yayi Imani da Manzon Allah shi ne cikamakin Annabawa, kuma yazo da addinin gaskiya. Wannan shi ne kadai lasisin da zai baiwa mutum saduwa da Allah lami lafiya. Na kawo wannan bayani ne dan na buga mana Misali, domin ga Abu Lahab ya fito daga cikin kabilar Manon Allah SAW amma cikin kaddararwarSa Subhanahu Wata'ala ya sanya shi cikin wadan da basu yi Imani ba, dan haka ne ya zama katafaren Arne makamashin wuta a ranar gobe alkiyama.

Haka kuma, Allah Buwayi gagara Misali, ya sanya Malam Ibrahim Shekarau mai duhun fata ko baki daga kabilar Babur, wanda a jihar Borno bata ita ce Madaukakiyar Kabila ba, Allah ya zabi Malam daga cikinsu ya azurtashi da Ni'ima ta Musulunci. Sannan ya daukaka darajarsa, ya zama Gwamnan katafariyar Jiha a Najeriya Jihar Kano, duk da wasu daga cikin Madaukakiyar Kabila a yankin jihar Borno sunyi masa Hassada da kyashi amma shi Allah babu ruwansa da hassadarsu Subhanahu Wata'ala. Bayan ya zamar da shi Gwamnan Jihar Kano, ya bashi mukamin Ministan Ilimi na tarayyar Najeriya baki daya, wannan wata falalace daga Allah. Watakila Allah ya bashi wannan dan ya jaraba Imaninsa.

Masu yi masa yarfe da cewa shi din DUNA ne, to Allah cikin kaddarawarsa ya sanya shi fitowa daga kabilar Babur kuma mai duhun fatar da wasu ke cewa DUNA. to duk wanda ya kushe Malam Shekarau saboda launin jikinsa ba shakka yana kalubalantar Allaah ne makagin Malam Shekarau ya sani ko bai sani ba, domin ba'a yi shawara da iyayan Malam Shekarau ba kafin sanya dantayinsa a cikin mahaifiyarsa. Allah shi yaga dama ya hallicemu yadda muke, Manzon Allah kuma ya gaya mana cewar wanda yafi wani a wajen Allah, shi ne wanda yafi Imani a cikinmu. Na san kuma a zamantaakewa irin ta rayuwa babu wanda zai yi maka gori a kasar bakaken fata cewa kai baki ne indai ba shi din ubansa ZABIYA bane. Zan cigaba In Sha Allah.

Yasir Ramadan Gwale
06-01-2015

Shiri Na Musamman Kan Gasar #YouWin


SHIRI NA MUSAMMAN KAN GASAR YOUWIN NA GWAMNATIN NAJERIYA

Assalamau Alaikum 'yan uwa masu binmu a wannan gida, kamar yadda na fada a jiya yau In Sha Allah zan kawo shiri na musamman akan gasar YouWin ta gwamnatin Najeriya. Ina fatan 'yan Tandu kuna kusa. Da farko dai zamu yi bayani akan Gasar YouWin. Ita dai YouWIn shiri ne na gwamnatin najeriya da ta kafa wani kakkarfan kwamati da ya hada da turawa jajayen fata da 'yan Najeriya dan tallafawa 'yan najeriya masu bukatar yin sana'o'i.

Wannan shiri na YouWin dai gasa ce, mutum yana iya shiga kuma baici nasara ba, kuma wannan abu ba caca bane. Ya ake shiga gasar YouWin? Wannan wata tambaya ce mai muhimmanci. Abinda kwamatin gasar YouWin yake bukata ga duk mai sha'awar shiga gasar shi ne, cikakken bayanin sana'ar da mutum yake son yi idan ya samu Nasarar lashe gasar, wannan a takaice shi ne, abinda kwamatin suke da bukata a karon farko dan samun Nasarar shiga gasar.

A takaice ina ganin bai kamata mu mutanan Arewa mu dinga kukan talauci ba alhali ga waraka ta zo mana har dakunanmu. Yana da kyau mu sani, a wannan gasa ta YouWin  ana cin kudi kama daga Naira Miliyan Daya har zuwa Naira Miliyan Goma (10M). Wannan kuma ba karya bane, domin wasu sun shiga kuma sun samu kudinsu.

Sannan kuma, wannan shiri na #YouWin shiri ne da aka yi masa tanadi na musamman, ta yadda babu wanda zai karbi kudin #YouWin ya kwanta akansu, idan kuwa ya yi haka zai iya samun kansa a gidan yari, ya zama dole ga duk wanda ya samu Nasarar lashe gasar ya aiwatar da dukkan abubuwan da ya tsara a takardun shiga gasar da ya gabatarda suka bashi damar lashe gasar.

Shawarata garemu ita ce, ga duk wanda yake da wata sana'a da yake san yi, ko kuma yake da Sana'a yake bukatar karin jari ko tallafi, to lallai kayansa ya tsinke a gindin kaba, domin kuwa ga shirin YouWin zai tallafa masa. Ina ganin, abinda ya kamata mutum yayi shi ne, ya idan ya shirya shiga gasar, ya samu wasu mutane na musamman, wadan da aikinsu ne tsarawa duk mai bukata irin abinda yake so na sana'arsa. Akwai Kwanzaltan wanda sun kware wajen tsarawa mutane hanyoyi irin na shiga gasar YouWin. Dan haka sai a samesu a basu dukkan bayanan sana'ar da ake yi ko ake sanyi su kuma zasu baka dukkan tsarin da kake da bukata, ka biyasu. Sai mutum ya gabatar da wannan takardu zuwa zauren gasar YouWin.

Lallai wannan wata dama ce da an jima da yi mana nisa a cikinta. Anan kuma zanyi kira a garemu harda ni mai wannan rubutu da lallai muyi kokarin ganin mun gabatar da bukatar shiga wannan gasa, domin yanzu haka ana karbar Takardun Shiga gasar. Dan haka,'yan uwana Matasa masu karamar sana'a da wadan da basa sana'a ga dama ta samu. Kada mu bari wannan garabasa ta wuce mu.

Muna ji muna ganin idan an tashi bayyana sakamakon wannan gasar sai muga mutanan kudu ne suke amfana, alhali abu ne na kasa baki daya, kuma mune muka jawowa kanmu koma baya ta hanyar kin cin moriyar gasa irin wannan. Ina kira da babbar Murya akanmu da lallai muyi kokarin ganin mun shiga wannan gasa a wannan lokaci. A bara nayi kira da a shiga wannan gasa, amma a iyakar sanina mutum biyu ne kadai suka yi yunkurin shiga gasar. To lallai yanzu ga dama ta samu dan haka kada muyi sake da ita.

Ga duk wanda yake da sha'awar shiga wannan gasa a shirye nake da na taimaka masa akan yadda zai shiga gasar, da kuma yadda zai tsara bayanan sana'ar da yake san yayi. Allah ya yi mana jagoranci. Amma fa nima Kwanzaaalta ne sai an biyani. (DARIYA)! Domin neman karin bayani akan wannan gasa ana iya duba www.youwin.com

Yasir Ramadan Gwale
06-01-2015

Saturday, January 3, 2015

NIGERIA-ISRAELI: Duk Wanda Yaci Ladan Kuturu...


NIGERIA-ISRAELI: DUK WANDA YACI LADAN KUTURU...

A makon da ya gabata ne, Najeriya karkashin Shugabancin Shugaban Kasa Dr. Goodluck Jonathan ta hannun jakaddiyar najeriya a majalisar Dinkin Duniya ta aikata babban abin kunya a majalisar dinkin duniya, inda ta zabi marawa Israeli baya akan goyan bayan samar da 'yan tacciyar kasar Palasdinu a matsayin cikakkiyar kasa kamar kowacce. Kasancewar Najeriya kasa ce mai rinjayen Musulmi duniya tayi zatan cewa Najeriya zata kasance tare da Palasdinu duba da cewa akwai tsohuwar alaka da dangantaka tsakanin Najeriya da Palasdinu, domin kuwa Marigayi Shugaban Palasdinawa Mallam Yassir Arafat ya taba kawo ziyara Najeriya zamanin Gwamnatin marigayi Gen. Sani Abacha.

Najeriya ta lalata waccan tsohuwar dangantaka ne ta hanyar kasancewa tare da Israeli dake zaman haramtacciyar kasa a idon Musulmi da dama. Amma ga dukkan wanda yake bibiyar abubuwan da ke faruwa tsakanin Najeriya da Israeli a 'yan kwanakinnan ba zai yi mamaki wannan mataki da Najeriya ta dauka ba, domin kuwa dangantaka ta kullu tsakanin Shugaba Jonathan na Najeriya da Piraministan Israeli Benjamin Netanyahu - בנימין נתניהו, duba da yadda ake cewa kamfanonin Israeli na samun kwangiloli a Najeriya da kuma irin ziyarar da shugaban Najeriya ke kaiwa Israeli da sunan Ibada.

Shugaban kasa Dr. Goodluck Jonathan yana cikin tsaka mai wuya, ta yadda manyan kasashen duniya da dama irinsu Amerika da kasashen turai basa tare da gwamnatinsa, inda ake masa ganin mugun shugaban kasa wanda ya kasa yin wani katabus dan ceto 'yan matan Chibok, domin kuwa an jiyo Shugaba Obama da mukarrabansa na gwabawa Najeriya a kan batun 'yan matan Chibok, haka manyan sanatoci a majalisar dattawan Amerika irinsu John McCain duk suna yiwa Shugaba Jonathan shagube akan batun matan Chibok da aka sace.

A tunani na wannan ce ta sanya Shugaban kasa Jonathan kasancewa tare da Israeli, domin kuwa muddin Dr. Jonathan yana yana tare da Israli kuma tana agoyon bayansa, to kuwa babu wani dalilaai da zai sanya Amerika da kasashen turai su ki goyawa Mr. Jonathan baya, domin duk wuya duk runtsi mun san Amerika da turai sunaa tare da israeli. Daman duk wanda yaci ladan kyuturu dole ya yi masa saisaye, domin kuwa da jonathan da netanyahu duk sunci ladan juna.

Daga karshe muna barrantar da kanmu daga wannan mara baya da Najeriya ta yiwa Israeli. Na tabbata babu wanda zai ji dadin wannan abin da Najeriya ta yi sai 'yan SHIAH masu bautar son rai. Wa Makaru Wa Makarullah...!

Yasir Ramadan Gwale
03-01-2015

Thursday, January 1, 2015

ADAMAWA 2015; Mallam Nuhu ribadu Ya Zabi Mataimaki


ADAMAWA 2015: NUHU RIBADU YA ZABI MATAIMAKI

Malam Nuhu Ribadu ya bayyana sunan Habila Istifanus tsohon Shugabankaramar hukumar Ganye a matsayin wanda zai dafa masa a kujerar mataimakin Gwamna. Malam Nuhu Ribadu ya bayyana cewa sai da yayi adduah sannan ya tuntubi mutane masu yawa sannan ya yanke hukuncin zaben Mr. Istifanus, wanda ya bayyana shi da cewa mutumin kirki ne mai tsoron Allah da son gaskiya.

Shugabanni Jam'iyyar PDP na jihar Adamawa da kuma shugabannin yakin neman zaben Malam Nuhu Ribadu sun barke da sowwa da murna yayin da Malam Nuhu yake bayyana sunan Habila Istifanus a matsayin mataimakinsa. Mutane da dama sun bayyana wannan zabin a matsayin wanda ya dace, domin an shaidi Mr. Istifanus da cewa mutum ne mai gaskiya da tsoron Allah gashi da son jama'a da san kawo cigaba mai ma'ana.

Haka kuma, Malam Nuhu Ribadu ya bayyana Mr. Habila Istifanus a matsayin masanin siyasa kuma gogaggen mai ilimi, domin kuwa a cewarsa, yayi digirin kwarewa a jami'ar Base dake kasar Burtaniya. daga karshe Malam Nuhu Ribadu da Habila Istifanus sunyi fatan Allah ya dafa musu a wannan takara, ya jama jagoransu. An kuma yi addaur Allah ya baiwa Malam Nuhu Ribadu nasarar wannan zabe.

01-01-2015

Karshen Shekarar Miladiyyar 2014


KARSHEN SHEKARAR MILADIYYAR 2014

Alhamdulillah, kamar yadda Allah ya nuna mana farkon wannan Shekara haka yauma ya sake nuna mana karshenta. Mun shafe kwanaki sama da dari uku (300) muna gaganiya a cikin wannan Shekara. Al'amura masu yawa sun faru a gurare da dama. Kadan ne na farinciki da jin dadi suka faru a wannan shekara. Abubuwa munana sun faru da yawa. Muna fatan kada Allah ya kuma maimaita mana su a wannan sabuwar Shekara da zamu shiga.

Mutane da yawa sun shiga cikin Halin kunci da damuwa da takaici. Mata da yawa sun zama zawarawa, an mayar da 'ya 'ya da yawa marayu, mutane da dama sun bakunci lahira ba tare da sun san laifukan da suka aikata ba. An làlata dukiya ta dumbin miliyoyi hatta shanu da awaki sunga ta kansu a wannan shekarar.

Kusan kullum labarin da muke bude ido da shi ba na alheri bane. An kashe... an kone... an sace... an yanka... da sauran nau'ukan miyagun labarai haka kusan duk hudowar rana da faduwarta ake fama da su.

Ba shaka Allah SWT yace da Manzo SAW yayi bushara ga masu hakuri. Ya Allah ka sanya mu kasance cikin masu hakurin da zamu yi adabo da wannan bushara taka Subhanahu wata'ala.

A karshen Shekara irin wannan lokaci ne da ya kamata muyi bitar irin abubuwan da muka aikata a baya, munana mu nemi Allah ya yafe mana sannan ya karemu daga sake afka musu. Kyawawansu kuma Allah ya cika mana ladan ya tabbatar da dugadugannmu wajen aikatasu.

A irin wannan lokaci ya dace mu koyi yiwa juna afuwa mu yafewa juna irin laifukan da muka aikatawa kawukanmu muna sane ko bama sane. Ba shakka ni Yasir Ramadan Gwale nasan na yiwa abokaina laifuka da daman gaske, da yawa suna jin haushi na ko dai akan ra'ayina musamman na siyasa ko kuma akan abinda na fada wanda bai musu dadi ba. Ina rokon duk wanda na batawa kuma yake jin haushina akan haka ya yafe min. In sha Allah duk wanda ya batamin ko yasa naji haushinsa akan duk abinda hannuna ya rubuta na yafe masa. Allah mai ahuwa ne yana san ahuwa. Allah kai mana ahuwa ka yafe mana ka shiryar da mu hanya madaidaiciya. Ya Allah ka shiga mana gaba kai mana jagora a dukkan lamuranmu na rayuwa. Allah ka bamu lafiya da zama lafiya a Najeriya. Allah ka amintar da mu à garuruwanmu. KULLU AMIN WA ANTUM BI KHAIR.

Yasir Ramadan Gwale
31-12-2014