Tuesday, December 31, 2013

Gwaro Na A Shekarar 2013, A Facebook!!!

GWARZO NA A SHEKARAR 2013, A FACEBOOK!!!

A wannan shekara da muke yin bankwana da ita a yau, na zabi Malam Najib Aliyu Harazimi a matsayin Gwarona na wannan shekara. Ba shakka, na jima ina bibiyar dukkan irin sakonnin da Najib yake yadawa a facebook, mutum ne mai son yada alkhairi da kokarin shiryar da mutane zuwa ga hanya ta gaskiya. Hakika, irin sakonnin da yake sakowa a koda yaushe sukan yi tasiri a gareni ainun, sau da dama idan naga ya yi wani tsokaci nakan zata kai tsaye da ni yake. Haka kuma, idan naga yayi wata addu'ah sai na dauka kamar ya san irin hali ko yana yin da nake ciki, ba shakka, Najib yana daga cikin mutanan da nake karuwa da su sosan-gaske a facebook da ire-irensa da dama.

Najib, na zabeka a matsayin gwarzo na, na wannan shekarar, dan ka dace ka kuma cancanta da na zabeka. Kuma na zabeka ne dan nuna godiya da yabawa da irin sakonnin da kake yi na fadakarwa a ko da yaushe, ina kira a gareka, kada ka ja da baya akan wannan aikin alkhairi da kake yi. Ina kuma kira a gareka, da ka jajirce wajen cigaba da neman ilimi da yadashi. Kuma ka kasance, kana aiwatar da abinda kake shiryar da mutane izuwa gareshi, kada ka zama irin wadan da suke shiryar da mutane zuwa ga aikin alkhairi amma su basa yi. Ina yi maka fatan alheri da fatan samun kyakykyawan sakamako a wannan aikin alkhairi da kake yi. Na gode.

Yasir Ramadan Gwale
31-12-2013

Monday, December 30, 2013

Iran


IRAN: Duk wani yunkuri na dakushe tare da rage karfi da tasirin Kasar Iran a yankin gabas ta tsakiya, musamman a kasashen Lubnan da Suriya da Iraqi abu ne da ya kamata ya samu goyon baya daga dukkanninmu. Muna maraba da dukkan wani yunkuri akan haka. Iran ta zama iblishiya a tsakanin kasashen Gabas ta tsakiya, ta hada-kai da Israela ana ta wasa da hankulan mutane dangane da makamin Nukiliya. Suna karfafa Hiz-bola tana kashe mutane a Lubnan, sun kashe Rafeeq Alhariri Rahimahullah, sun kuma kashe Mumammad Shattah. Suna kuma taimakon Bashar Asad dan Ta'adda yana kashe talakawa bayin Allah a suriya. Sannan kuma, sun mayar da Iraqi tamkar wata jiha ce a cikin Farisa ta hanyar bayar da umarni ga karen farautarsu Nuri Maliki dan ta'adda. Muna nuna cikakken goyon bayanmu akan dankwafar da Iran. Ina kuma da yakinin za'a cimma Nasara, dan Allah yana taimakon duk inda gaskiya take komai karancin masu yi mata biyayya. Allah ka rusa duk wasu masu yiwa Addini zagon kasa suna basaja a cikin musulmi.

YASIR RAMADAN GWALE
29-12-2013

Saturday, December 28, 2013

Bayan Tattaki Kuma Sai Me?

BAYAN TATTAKI KUMA SAI ME?

Yanzu dai angama Ibadar da 'yan Shia'h suka yi a Husainiyya dake Zariya da sukawo Tattaki daga gurare masu nisa. Wanda a ranar wannan taro nasu muka jiyo Nuri Maliki Mai Gasa-Burodi a Bagadaza wanda yanzu prime Minister ne na Iraqi Bayan Shahadar Marigayi Saddam Hussein Rahimahullah yana cewa Musulmi su mayar da Alkibla zuwa KARBALA domin anan ne Kabarin Sayyaidina Husain Ibn Ali Ibn Abi-Talib (Radiyallahu Anhu) yake. Shin ko Maliki ya mance da cew
ar Kabarin kakan Husain baban mahaifiyar Husain Annabi Muhammadu Dan-Abdullahi cikamakin Annabawa yana garin Madina Al-munawwarah ne, watakila ko bai sani ba ne. To amma su Masu bakaken kaya na Najeriya da basa iya zuwa Karbala a irin wannan ranar har suma zasu dinga kallon Karbala ne ko kuwa su GYALLESU zasu dinga Kallo yayin da zasu yi tasu ibadar? Dan Allah ku bani labari shin Masu Tattakin nan a kafa suka juyo zuwa mazaunansu ko kuwa ladan zuwa (safa) ya ishesu, ba sai sunyi (marwa) ba suka hawo ababen hawa dan komawa gida? Sannan kuma, bayan da a yanzu suka yi Idin-Ghadir da Idin Ashura sai kuma meye ya rage? Sai naji daga gareku.

Yasir Ramadan Gwale
28-12-13

Tuesday, December 24, 2013

Wane Darasi 'Yan Arewacin Najeriya Zasu Dauka Daga Sudan Ta Kudu 2


WANE DARASI 'YAN AREWACIN NAJERIYA ZASU DAUKA DAGA SUDAN TA KUDU? [2]

A lokacin da gwamnatin Sudan dake Khartoum ta ci garin Abye mai arzikin manfetur a shekarar bara waccan inda suka fatattaki sojojin Sudan ta Kudu daga yankin, shugaba Omar Albashir yayi wani abu na ba sabamba, inda ya sanya khakin soja ya yi wata Khuduba a ranar juma'ar da suka samu wannan nasara ya sanyawa Hudubar suna "Juwwa Juba" wato sai sun shiga har juba sun cita da yaki. Watakila irin wannan abin da shugaba Bashir yayi shi ne ya burge Shugaban Sudan ta kudu Silva Mayardit Kiir Mai Malafa, a talatar makon da ta gabata aka wayi gari da harbe-harbe a cikin Birnin Juba kawai shima sai aka ga Shugaba Kiir cikin Khakin Soja yayin taron manema labarai, a inda akai ta mamaki kuma abin ya zama abin zolaya ga shugaba Kiir a tsakanin Jaridun Khartoum.

Mutanan Sudan ta kudu suna zaton idan suka balle daga Sudan shi kenan rayuwa zata zamar musu sabuwa su yi ware-wake, su yi duk irin yadda suke so. Amma ina abin ba haka bane, domin Tun bayan ballewarsu, suka yi ta samun kalubale masu yawa da suka hada da rikicin yankin Abye mai arzukin mai, da hadin-kan-kasa da kuma tsaffin 'yan tawayen SPLM da suka jima da makamai a hannunsu suna yawo, da kuma batun gina kasa da Ilimi da kiwon lafiya da noma da sauransu. Duk da irin wannan kalubale dake gaban Gwamnatin Silva Mayardit Kiir Mai Malafa, maimakon ya hada kan al'ummomin kasar wajen ciyar da kasar gaba, sai ya dabarbarce yayi ta jidar dukiyar kasar yana tarawa a cewar masu hamayya da gwamnatinsa karkashin jagorancin Reak Machar.

Yana da kyau mu sani cewar Mutanan Kudancin Sudan kusan mafiya yawansu sun saba da yaki, kuma sun saba da gudun hijira, dan gabaki dayan rayuwarsu a haka ta taso. Dan haka ne da aka wayi gari da wannan harbe-harbe a Juba tsakanin Dakarun Reak Machar da na Gwamnatin Kiir Mai Malafa, jama'a da dama suka dinga diban tsummokaransu da katifu suna zuwa ofisoshin majalisar dinkin duniya dan samun mafaka. A lokacin da Shugaba Kiir ya tashi yin taron manema labarai ya ambaci sunan tsohon mataimakinsa Reak Machar da cewa shi ne ya haddasa wannan tashin tashi-na, abinda wasu manzarta suke ganin Kiir yayi azarbabin kama sunan Machar, mutumin da a yanzu yake neman goyon bayansa dan dawo da doka da oda. Haka kuma, wani dalili da zai nuna gazawar Gwamnatin kiir shi ne yadda cikin kankanin lokaci aka karbe ikon Jihar Unity da Upper Nile daga hannun gwamnati abinda ya nuna daman can gwamnati ba tada wani tanadi ingantacce na tsaron kasa.

Darasin da masu fatan ganin Arewa ta zama kasa mai cin gashin kanta bayan ta yanke daga Najeriya shi ne, za'a samu tsananin gaba da kiyayya tsakanin Musulmi da Kiristoci a Arewa. A sudan ta Kudu matsalarsu kabila ce kawai, dan haka, lamari ne da ake iya warware shi akan tebur, amma dangane da Arewacin Najeriya batu ne za'ai na addini tsakanin Hausa/Fulani-Musulmi da sauran Kabilun Idoma/Berom/Tarok-Kiristoci da sauran kananan kabilun da suke Arewa. Wannan shi ne abinda zai sabbaba rashin jituwa mai tsananin gaske, abida ka iya kaiwa zuwa ga gwabza yaki, da dama suna ganin Idan mu Arewa muka balle shi kenan zamu tafiyar da rayuwarmu yadda muka ga dama. Sabanin yadda muke a dunkulalliyar Najeriya inda ake kudu da Arewa. Ba shakka sharrin da zai biyo bayan darewar najeriya sai an gwammace inama dai ba'a rabu ba! Akwai illoli masu yawa wadan da darewar Najeriya zata haifar. Dan haka wannan turka-turka ta kasar Sudan Ta kudu take zaman babban Darasi ga 'yan Najeriya musamman mu 'yan Arewa.

Yasir Ramadan Gwale
24-12-13

Monday, December 23, 2013

Wane Darasi 'Yan Arewacin Najeriya Zasu Dauka Daga Sudan Ta Kudu?

WANE DARASI 'YAN AREWACIN NAJERIYA ZASU DAUKA DAGA SUDAN TA KUDU?

Abin da ya faru a makon da ya wuce na barkewar rikici a tsakanin jaririyar kasar Sudan ta kudu ya zowa da mutane da dama da bazata. Kamar yadda galibin al'ummar kudancin Sudan suka dinga korafin cewar Larabawan da suke Mulki a dunkulalliyar kasar Sudan sun ware su, kuma an hana musu dama ta yin rawar gaban hantsi, irin wannan zance da sauran zuga da dama ta sanya al'ummar dake zaune a Sudan ta Kudu suka jefa kuri'ah da gagarumin rinjayen ballewa daga kasar Sudan, bayan da Shugaba Omar Hasan Albashir ya basu damar kasancewa a dunkulalliyar Sudan ko kuma ballewa, wannan ta sanya galibin kabilun wannan yanki suka zabi ballewa daga Sudan. Wannan ballewar tasu ta zama tofin Allah-tsine ga tsohon jagoransu John Garang wanda ya tsaya kai da fata wajen ganin al'ummarsa basu balle daga Sudan ba duk kuwa da zuga da matsin lamba da yake sha daga kasashen waje akan yin hakan.

Bayan mutuwar Garang a wani yanayi mai cike da ayar tambaya, wanda dan kabilar Dinka ne masu rinjaye, aka nada Silva Kiir a matsayin sabon magajinsa, kuma shugaban al'ummar kudancin Sudan a gwamnatin Bashir dake Khartoum. Kiir shima dan kabilar Dinka ne, wannan kabila sune mafiya rinjaye a cikin dukkan kabilun da suke zaune a wannan yanki na kudancin Sudan, sun linka kabilun Nuer da Meseriya da sauransu yawa nesa ba kusa ba. Kabilar Nuer su ne suke biyewa Dinka wajen yawan jama'a a kudancin Sudan. Amma wani abin Sha'awa shi ne, su kabilar Nuer duk da rashin rinjayensu a kasar amma su ne suke da rinjayen wadan da suka yi karatun Boko, wannan ta sanya suka fi dukkan kabilun yankin wayewa da saukin lamari.

Shi wannan shugaba Silva Kiir, mutum ne da ya taso a gaba dayan rayuwarsa bai san komai ba sai yaki, da zaman kadaici a cikin daji irin na sojoji, dan haka ko makaranta bai yi ba da zata bashi damar gogewa da kuma gogayya. A saboda haka ne, a lokacin da suka samun 'yancinsu daga Sudan, kuma ga arzikin manfetur Allah ya huwace musu, akai ta fadin tashin kafa gwamnatin hadin kan-kasa, a Naivasha ta kasar Kenya suka cimma yarjejeniya da kabilar Nuer wajen tafiya tare, dan gina sabuwar kasar tasu mai cike da kalubale. Tun farkon kamun ludayin Gwamnatin Kiir masu sharhi suka fahimci cewar lallai ba zai jima ba za'a samu gagarumar baraka a cikin gwamnatinsa, don na farko kamar yadda na fada, bai yi karatu ba, kuma ba shida wata wayewa ko gogewa da zata bashi damar hada kan al'ummar kasar. Dan haka ne ba shida wani aiki face daukar zuga ko abinda aka sanya shi yi daga kasashen da suke hankoron Man-fetur din kasar ta ke da shi.

Yana daga cikin dalilin da ya sanya a karon farko ya samu sabani da 'yan kabilar Nuer din da dake cikin gwamnatinsa. Don sum fahimci babu inda shugaban ya sa gaba, face tara dukiyar haramun da kuma jiran umarni daga kasashen waje, matsin lamba da caccakar da 'yan Kabilar Nuer dake cikin gwamnatinsa ta sanya, rana a tsaka ya bayar da sanarwar korar jami'an gwamnatinsa gaba daya! Abin da ba'a taba yi ba a duniya, wannan al'amari ya harzuka 'yan Kabilar Nuer bisa jagorancin mutumin da shi ne mataimakin shugaban kasa Reak Machar. Shi Reak mutum ne dan boko wanda yayi ilimi zamani mai zurfi kuma gogagge ta fuskar mu'amala.

Zan cigaba In Sha Allah.

Yasir Ramadan Gwale
23-12-13

Saturday, December 21, 2013

Obasanjo Ne Fa . . . Gwanki Mai Rangwangwan!!!


OBASANJO NE FA . . . GWANKI MAI RANGWANGWAN!!!

Wasikar da aka ruwaito tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya rubutawa Shugaban kasa Goodluck Jonathan ta janyo masa farin jini da yawa a wajen mutane masu saurin manta abinda ya faru a baya. Ba shakka yana da kyau mu tunawa kanmu waye Obasanjo a wajenmu ('Yan Arewa), sannan kuma mu tambayi kanmu, Shin Allah ne ya shiryi Obasanjo? Sannan kuma, halin da muke ciki mawuyaci na koma baya ta fuskar tattalin arziki, da lalacewar harkar ilimi, da koma baya ta fuskar Noma da kiwo, da lalacewar harkokin tsaro da fatara da yunwa da cututtuka da sauransu, wadannan wasu lamura ne da mu mutanan Arewa bama bukatar Obasanjo ya sanar da mu wadannan lamura. Dukkan irin lalacewa da wannan gwamnati ta mai malafa ta yi da kuma gasa mana aya a hannu da ta yi, Obasanjo yana da kamasho a ciki ko mun yaba masa ko bamu yaba masa ba, domin shi ne silar samuwarta.

Kada mutanan Arewa mu yi saurin manta irin kitififi da kitumurmura da makircin da Obasanjo ya shirya mana a baya. Mutumin nan, shi ne fa ya yi dukkan mai yuwuwa wajen mayar da yankin Arewa baya ta fuskar tattalin arziki da karfin soja da ilimin boko da sauransu. Manyan sojojin Najeriya 'yan Arewa masu mukamin General da Brigadier da Major nawa ne suka rasa rayukansu a cikin wani yanayi mai cike da tuhuma a zamanin Obasanjo? 'Yan kasuwa nawa aka gurgunta bayan an kakkarya wasu a Arewa? Ina bankin da Arewa take takama da shi na Bank Of The North? Shin ba Obasanjo ne ya rusa shi ba, dan murkushe tattalin arzikinmu! Shin ba Obasanjo ne ya yi amfani da Kwanturola na Kwastam Jacob Gyang Buba ba wajen durkusar da kasuwannin jihar kano da na Arewacin Najeriya ba, ta hanyar bin mutane har cikin shagunansu ana kwashe musu kaya ana konewa dan tsabar zalunci da keta da mugunta? Shin yanzu har munyi saurin manta irin wannan manakisar da Oban-shegu ya yi mana?

Dukkan zaben da aka yi a baya tun daga 2003 har zuwa 2011 shin ba Obasanjo ne ya yi amfani da karfinsa ba wajen yin kaci-baka-ci ba, baka-ci-ba-kaci! Duk irin wannan shegantaka da tsiyataku da Obasanjo ya yi mana har muna da bakin da zamu yaba masa akan ya rubutawa Shugaban kasa Goodluck wata wasika da babu abin da zata rage na daga irin mawuyacin halin da muke ciki ba. Shin Obasanjo yanzu yana son nuna mana cewa a yanzu shi masoyin 'yan Arewa ne, yana gaya mana manakisar da wannan gwamnati ta shirya dan kashe wasu muhimman mutane? Mutum nawa aka kashe a Arewa da Najeriya baki daya wanda Obasajo ya kamata ya yi bayanin yadda aka yi kisan kuma aka kasa gano wadan da suka yi kisan!

Obasanjo yana shugabancin Kwamitin Amintattu na Jam'iyyar PDP, tsohon mashawarcin kasa ta fuskar tsaro Marigayi Andrew Azazi ya yi bayanin cewar PDP su ne BOKO HARAM, Shin ina Obasanjo yake a lokacin? Ko Azazi yace banda Obasanjo ne? A saboda a wautar da hankalin mutane sai aka ce wai Obasanjo zai je Maiduguri domin sasanta Gwamnatin Borno da 'Yan Boko Haram, a yi wasa da hankulanmu, shin zamu iya gamsuwa cewa babu hannun Obasanjo a cikin duk wannan sabatta juyatta da ake yi ta fuskar tsaro ne? Ba obasanjo ne ya yi uwa yayi makarbiya ba wajen ganin ya daurewa wannan shugaban mai malafa gindi ya tsula dukkan irin tsiyar da yaga dama ba? Bai kamata mu yi saurin mancewa da abin da Obasanjo ya aikata mana ba, har mu dinga yekuwa da sunan cewa OBJ yayi abin kai fitsari da kumfa! Kamar yadda na fada, shin muna bukatar Obasanjo ya fada mana halin da muke ciki, ko ya ce mana za'a kashe mu? Ina kisan da ya yi mana a baya? Shedan ya fadi magana Manzon Allah SAW ya ce abinda ya fada gaskiya ne, amma shi din makaryaci ne, dan haka gaskiyar da ya fada bata tsarkakeshi daga kan batan da yake kai ba; to haka shima Obasanjo.

Obasanjo ya fahimci 'yan Arewa sarai dan haka ya gama rainamu ya yi dukkan irin wasan da yaga dama da hankulanmu. Domin ya fahimci yanzu duk wani wanda zai samu farin jini da karbuwa musamman a wajen 'yan Arewa to ya kalubalanci gwamnatin mai malafa, dan haka ya fito da wannan sigar dan ya mantar da mu abin da ya faru a baya na badakalar da ya tafka a Kwangilar Wutar Lantarki ta Dala Biliyan Goma sha shida ($16B) ya mantar da mu badakalar da su Cif Tony Anineh da su Bode George suka tafka a karkashin gwamnatinsa.

Ni a ganina, wannan wasika ta Obasanjo tana da fuskar silai (mutum ko Doki), Abu na farko shi ne, ficewar Gwamnonin PDP guda biyar babu shakka sun batawa Obasanjo rai, dan bai so haka ba, dan haka bari yayi amfani da wannan dama ya caccaki mutumin da 'yan Arewa suke tsananin kyamata da nunawa gaba, ta hanyar nuna mana cewar yanzu Mulki rabon 'yan Arewa ne, bayan mun san da cewar yayi dukkan abin da zai iya wajen murdewa kundin tsarin mulkin Najeriya wuya dan ya zarce a karo na uku Allah bai nufa ba, ko waccan Tazarce ba 'yan Arewa ya so ya yiwa sata ba? Duk da mun hana shi wucewa ba dan yana so ba, muka zuba masa ido ya zabo mana wanda yaga dama a matsayin wanda zai gajeshi, kuma, muka ce masa "sami'ina wa'ada'na". Dan haka, duk wani sabani da za'a samu tsakanin Obasanjo da Goodluck ko da kuwa OBJ zai halaka mahaifiyar Shugaban kasa ba shakka zasu gyarota a tsakaninsu.

Abu na biyu, Obasanjo ya hango hadarin da yake tunkaro PDP ba mai ruwa bane, hadari ne mai tafe da kura da guguwa da zata yi awon gaba da duk abinda ta samu, dan haka bari ya yi riga malam Masallaci; tunda ya fahimci cewar duk wanda zai yi farin jini a idan APC to ya caccaki shugaban kasa Jonathan, komai lalacewarsa hakan zata bashi kima a wajen APC tunda anyi walkiya yaga wallensu. Ni a ganina wadannan dalilai guda biyu suka sanya Obasanjo rubuta wannan wasika, idan tayi ruwa rijiya, idan kuma tayi fako shadda ce, yasan indai APC ta kafa gwamnati a kalla ya wanke kansa ta hanyar caccakar gwamnatin GEJ da tsinken-tsire, idan kuma abin Allah ya kiyaye GEJ ya kai labari, to babu shakka zai gyarota tsakaninsa da Shugaban kasa, kamar yadda muka hangosu a Nairobi da Soweto suna musabiha cikin annashuwa bayan aikewa da wannan wasikar. Hausawa sun ce a Juri 'Bara Albasa Fara Ce.

Yasir Ramadan Gwale
21-12-2013

Thursday, December 12, 2013

Obasanjo Ya Fadi Gaskiya, Amma Mai Zunubi Ne

OBASANJO YA FADI GASKIYA, AMMA MAI ZUNUBI NE

Ba shakka wasikar da tsohon shugaban kasa Obasanjo ya aikewa Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yi bayanai na gaskiya da dattako. Obasanjo saninmu ne ba wani mutum bane mai gaskiya, yana daga cikin ummul haba'isin duk halin da muke ciki na kaskanci da koma baya a kasarnan Musamman yankin Arewa, bamu manta da yadda ya lalata mana tattalin arziki ba ta hanyar amfani da karnukan farautarsa, ya nakastamu ta fannin karfin soja. Ya mayar da mu baya a harkar noma da kiwo da muke tunkaho da shi, a gefe guda kuma ya daga darajar noma da kiwo a yankin kudancin Najeriya. Bamu manta da irin yadda ya yi amfani da murar suntsaye ba ya nakasta da dama daga cikin manyan manoman arewa ba.

Hakika laifukan da Obasanjo ya tafka a wannan kasa ba zasu lissafu ba cikin kankanin lokaci. Anyi kwangiloli na rainin wayo da raina 'yan Najeriya, bamu manta da kwangilar Naira Biliyan 200 da aka sanya Cif Tony Anineh ba, akan gyaran manyan hanyoyin gwamnain tarayya ba, wanda babu kudin babu dalilinsu, kuma babu aikin, bamu manta da badakalar kudin wutar lantarki ba. Da dumbin laifuka da zunubbai da ya aikatawa al'ummar Najeriya duk suna nan rubuce a cikin daftarinmu.

Babban laifinsa mafi muni, shi ne yadda yayi uwa yayi makarbiya wajen shigowa da 'yan Najeriya da haramtacciyar Gwamnati a 2007. Saninmu ne shi ne ya daurewa Marigayi Malam Umaru Musa YarAdua (Allah ya jikansa da rahama) gindi wajen yakai labari ko ta halin-kaka. Shi ne kuma ya daurewa Wannan mugun shugaban kasar gindi wajen dawowa a matsayin magajin Umaru YarAdua. Har yanzu wannan ciwo da miki da Obasanjo ya aikata mana bai warke ba a zukatanmu.

Ba haushe ya yi gaskiya, yace gaskiya ko ta karece a bashi abarsa! Kuma haka addinin Musulunci ya horemu. Ba shakka Duk da waccan balbalcewa da lalacewa ta Obasanjo yayi gaskiya akan abinda ya fada game da yadda Shugaban kasa Goodluck yake tafiyar da harkokin wannan kasa. Masana sun jima da fadin cewa, a tarihi ba'a taba samun shugaban kasar da bai san me yake yi ba, irin wannan mugun mayaudarin shugaban kasar, Azzalumi maketaci, mayaudari wanda baya son al'ummar Najeriya da alheri ko na sisin kwabo. Ya mayar da kasarnan baya ta ko ina, ya lalata komai. Ya daurewa cin hanci da rashawa gindi, ya mayar da aikata zunubbai tamkar Ibada.

Anyi hasarar dumbin rayukan talakawa bayin Allah da basu san hawa ba balle sauka a wannan muguwa Azzalumar gwamnti. Mutane da yawa sun talauce a sanadiyar kona musu dukiyoyinsu a jihohi da dama a Arewa. Barna da ta'adi da wawaso da facaka sun zama sune abinda kowa ke alakanta wannan gwamnati da shi ciki da wajen Najeriya. Ya sace dukiyar kasa shi da wasu tsirarun 'yan iska maciya amanar kasarsu, marasa kishi, sun zamar mana Alaka-kai. Babu shakka dukkan dangin wani kasawa ya tabbata akan wannan shugaban kasa, mugu ne, maketaci ne, Azzalumi ne, 'yan Najeriya birni da kauye sun gaji da wannan gwamnati. Dan haka dole mu yabawa Obasanjo akan abinda ya fada dan gane da wannan shugaban kasa da Azzalumar Gwamnatinsa. Allah ya yi mana canji mai amfani a 2015.

Yasir Ramadan Gwale
12-12-13

Sheikh Aliyu Harazumi Hausawa


SHEIKH ALIYU HARAZUMI: Ina mai bin sahun dimbin al'ummar Musulmi musamman na jihar Kano da karamar hukumar Gwale wajen nuna alhininmu bisa rashi na Shehun Malami Sheikh Aliyu Harazumi, hakika dukkan mai rai mamaci ne, kasancewarmu a raye babban dalili ne da yake tabbatar mana da cewa Mutuwa na nan tana jiranmu komai tsawon lokacin da muka diba a rayuwa. Mutuwa ita ce mai yanke dukkan hanzarin abin halitta da yake motsi a ban kasa, dole zuciya ta kadu idanu su raurawa hankali ya dugunzuma, a yayin da mutum yayi rashin wani nasa musamman mutum irin Sheikh Harazumi da yayi tasiri a zukatan mutane da yawa. Muna baiwa juna hakuri a bisa wannan rashi, muna kuma tunasar da juna cewa wannan sunnar Allah ce, kamar yadda ya fada a cikin littafinsa mai tsarki cewa dukkan mai rai sai ya dandana radadin mutuwa. Haka nan kowannemu zai riski wa'adinsa, babu tsumi babu dabara a lokacin da wa'adi yayi. Ba shakka a wannan lokacin anyi rashe-rashe na Malamai irin s Sheikhu Na'ibi Sulaiman Wali da Sheikh Isah Waziri da kuma wannan ta sheikh Aliyu Harazumi.

Ya 'yan uwa na masu girma, hakika a rayuwa babu wani wa'azi da yakai mutuwa. Ba shakka mutuwa ita ce Muntaha a rayuwar dan adam, lallai mu nustu, mu fadaka, mu sani, mu ba mazauna bane, yadda muke fadan cewa wane da wane sun rigamu gidan gaskiya, haka muma wataran za'a bayar da labarin tafiyarmu inda babu dawowa, dan haka nake jan hankalinmu da mu jajirce wajen yiwa wannan tafiya Guzuri na tsoron Allah da Imani da kadaita Allah da bauta, tare da yawan Istigfari da Hailala da karatun Al-Qur'ani. Allah ya bamu ikon tafiya, Allah ya rinjayar da kyawawan ayyukanmu akan sikelin ranar Alkiyama. Ranar da Allah ya kirata da sunaye da yawa dan jan hankin bayi na gari masu kadaitashi da bauta. Allah ka jikan mamatanmu, da 'yan uwanmu da malamanmu da dukkan al'ummar Musulmi a duk inda suke a duniya.

YASIR RAMADAN GWALE
12-12-13

Monday, December 2, 2013

Kamun Da SSS Sukaiwa Sheikh Nazifi Yunus Jos: An Fake Da Guzuma . . .

KAMUN DA SSS SUKAIWA  SHEIKH NAZIFI YUNUS JOS: AN FAKE DA GUZUMA . . .

Ba shakka kamun da hukumar SSS ta yiwa Dr. Yunus Jos dangane da zarginsa da ake yi da alaka da Boko Haram, ko kasancewa dan Boko Haram wani al'amari mai daure kai. An je har gidansa cikin tsakar dare aka kama shi a lokacin da yake tare da iyalinsa, aka keta masa haddi, aka ci zarafinsa, aka kuma yi masa dai-dai da kayan gidansa da nufin bincike dan samun wasu abubuwa da ake zargin 'yan BH na amfani da su wajen tayar da hanali, sai dai cikin ikon Allah haka aka fita ba tare da an samu ko da matsefata da sunan an ajiye dan tayar da hankali ba a gidansa.

Shugabar hukumar SSS Maryellen Ogar ta sha sharara karya akan zargin mutane da Boko Haram. Kamar yadda kowa ya sani ne, haka suka kashe matasa basu san hawa ba, basu san sauka ba a Apo a Abuja a kwanakin baya, da nufin zargin matasan da kasancewa 'yan BH. Abin tambaya, daman doka ta bayar da iznin kashe mutumin da ake zargi mai lafi ne? Na zata cewar ko mutum aka kama dumu-dumu yana aikata laifi sai an gabatar da shi gaban Shar'ah daga bisani kotu ta yi masa hukunci. Amma kiri-kiri ake keta haddin Mutane a Najeriya dan kawai su Musulmi ne, a kashe su ba da hakki ba, laifinsu kawai sunyi Imani da Allah da Manzon Allah. Muna fahimtar irin wannan sunkuru da hukumar SSS take yi karkashin wannan arniyar kokari ne na dakushe Musulunci da kuma fada da Musulmi a kai-kaice. Kawai an fake da BH ne dan a cuzgunawa Musulmi.

Duk wani Musulmi na gari a Najeriya yana yin Allah-wadai da dukkan wani Nau'i na tayar da hankali, kamar yadda addinin Musulunci yayi haramcin tayar da hankalin Mutanan da basu san hawa ba balle sauka, balle kuma har ta kai ga daukar makamai a dumfari mutane haka kurum a kawo karshen rayuwarsu ba tare da sun aikata wani laifi da suka cancanci hakan ba. Mun yi tir da dukkan wani dangi na zubar da jinin bayanin Allah, kuma ko waye ya aikata hakan muna kiran doka ta yi aiki akansa matukar an kama shi da laifi ko musulmi ne ko ba musulmi bane. Amma abin ya zama rainin wayo da rainin hankali, domin Kiristoci nawa aka kama dauke da makamai a Arewacin Najeriya zasu tayar da hankali, har Kwanturola na Kwastan aka kama da safarar makamai ta barauniyar hanya, amma me aka yi musu? Saboda kawai su Kiristoci ne suna da uwa a gindin murhu! Adalci shi ne a yiwa duk wanda aka kama da laifi hukunci dai-dai da abinda ya aikata ko daga wane yanki yake ko meye addininsa, babu yadda za'a maida wasu 'yan mowa wasu 'yan bora sannan a yi zatan dorewar zaman lafiya a tsakanin ko wacce irin al'umma; Mutum ko a tsakanin 'ya 'yansa ya fifita wani sai an samu rigima da rashin jituwa a tsakanin 'ya 'yan ballantana kuma al'ummar Najeriya da ake zaman doya da manja.

Bamu taba baiwa wani wanda ya aikata lafi kariya ba, ba kuma zamu taba zama inuwa daya da masu aikata laifuka dan basu kariya ba. Amma ya zama tilas a baiwa kowane dan kasa 'yancin walwala da yin addininsa kamar yadda kundin tsarin Muki ya bayar da dama, Kai ko tsarin Mulki bai bamu dama ba sai munyi Addinin Musulunci.  Lallai sai an baiwa kowa 'yancinsa, domin babu yadda za'a dinga bin malamai na Musulunci ana yi musu dauki dai-dai sannan a ce mana ana son zaman lafiya, alhali ga kiristoci can anyi shakulatun bangaro da batunsu. Ina hukumar SSS take lokacin da Dokubo Asari ya yi barzanar kashemu idan bamu zabi Jonathan ba a 2015? Suna ina shugaban kiristocin Najeriya Oritsejafor yake kalamai na ganganci da gatsali ga Musulmi? Me suka yi ko kuwa dan an raina mu. Ba shakka Allah yana tare da wadan da suka yi Imani suka bada gaskiya.

Yasir Ramadan Gwale
02-12-2013

Sunday, December 1, 2013

PDP: Tsakanin Fadar Shugaban Kasa Da G-7!!!

PDP: TSAKANIN FADAR SHUGABAN KASA DA G-7!!!

Tuni sanarwa ta gama karade ko ina cewar tsagin gwamnonin PDP guda bakwai da suka darewa uwar jam'iyyar PDP zasu gana da Shugaban kasa a yau. Kafin wannan ganawa dai an jima ana kai ruwa rana tsakanin wadannan Gwamnoni da fadar Shugaban kasa, har ta kai a ranar talatar da ta gabata, shugaban tsagin nPDP Alhaji Kawu Baraje ya bada wata sanarwa a dukunkune cewar sun hade tsakanin nPDP da kuma babbar jim'iyyar Hamayya ta APC. Tambayar da zamu yi anan ita ce, Shin Shugaban kasa zai gana da wadannan gwamnoni a matsayinsu na nPDP ne ko kuwa a matsayin sabbin Gwamnonin APC, ko kuma 'yan kan-katanga? Duk da cewar Gwamnan Jigawa da na Neja sun bayyana matsayarsu akan waccan sanarwa da Baraje ya bayar.

A ranar juma'ar da ta gabata, a cikin shirin BBCHausa na Ra'ayi Riga, sun tattauna wannan al'amari na turkaturkar PDP. A cikin wannan tattaunawa, sakataren tsare-tsare na PDP bangaren Bamanga Tukur Abdullahi Ibrahim Jalo ya yi wata tambaya mai muhimmanci, amma aka kewaye ba'a bashi amsar tambayar ba. Ya yi tambaya kamar haka, "Shin su wadannan Gwamnoni sun shiga APC ne a matsayin sauya sheka daga PDP zuwa APC, ko kuwa hadewa ce irin wadda ANPP da ACN da CPC suka yi" wannan tambaya tana da muhimmanci a yi bayaninta, amma cikin shirin aka kewaye mata. Domin bayan da Baraje ya bayar da wannan sanarwa, Gwamnan Jihar Kano Alh. Rabiu Kwankwaso ya yi wani bayani a BBC mai rudarwa kan cewa zasu koma su tattauna da jama'arsu sannan su yanke matsaya; wannan ya nuna cewar kamar ba su shiga APC din ba kenan.

Dangane da ita waccan tambaya da Jalo ya yi, yana da kyau suma APC su yi mana warwarar wannan al'amari, domin dai mun san cewar tsakanin ANPP da ACN da CPC da suka yi hadaka ba da baki suka yi ba, sai da kowacce ta mayar da satifiket dinta ga hukumar zabe sannan wannan hadewa ta tabbata, dan haka, su wadannan gwamnoni na nPDP sun dawo da nasu satifiket din ne ko anyafe musu, ko kuwa sauyin sheka suka yi? Wannan al'amari yana da kyau kada a dinga tafiya da 'yan Najeriya a dukunkune.

A dangane da Gwamnonin G-7, shin Me zai faru idan suka tabbatarwa da Shugaban kasa cewar suna nan daram dam dam a PDP? Bukatunsu a bayyane suke ga al'ummar Najeriya, manyan bukatunsu guda biyu dai sune na cewar (a) Dole Shugaban kasa ya ajiye batun tsayawa takara a 2015. (b) Dole a kori Bamanga Tukur. Anan ma zamu iya yin tambaya, shin wadannan Gwamnoni sun gamsu da yadda gwamnatin Jonathan ke tafiya ko kuwa kawai bukatarsu kada shugaban kasa ya tsaya zabe a 2015? Me ya sanya ba zasu tsaya kai da fata wajen ganin shugaban kasa da Gwamnatin Tarayya sun yiwa al'ummar Najeriya ko Arewa Adalci ba? Sanin kowa ne Shugaban kasa yana nuna bambanci da zalunci tsakanin bangarorin kasarnan a bayyane, babu wanda ya yi haka, idan banda gwamnan Kano da na Kwara da suka yi batun rashin adalci a tsarin rabon arzikin kasa na Man da ake tonowa a cikin Ruwa da kuma wanda ake tonowa a kan tsandaurin yankunan da suke da man (Off-shore da On-Shore) Wannan korafin wadannan gwamnoni sun yi ne a kashin kansu tun kafin haifar da G-7.

Ko shakka babu irin wadancan bukatu su ne suka damu al'ummar Najeriya. Dole a yiwa kowa adalci a baiwa ko wanne mai hakki hakkinsa, amma gabaki daya al'amarin PDP babu gaskiya a cikinta, da wanda yake zagin PDP da me yabonta duk ba masu gaskiya bane, illa nadiran indai 'yan PDP ne. Domin Atiku Abubakar da Abubakar Rimi babu irin abinda basu kira PDP ba, amma kuma suka yi mata kome daga baya. Yana da kyau al'ummar Najeriya su fadaka cewa, PDP wani gungu ne na 'yan MAFIA babu wani wanda ya isa ya kauce daga tsarin da aka gindaya, dole dan PDP ya yi mata aiki yana so ko baya so, ya yarda ko bai yarda ba, duk wanda yaci ladan kuturu dole ya mar aski. Yana da kyau mu sani su PDP wadannan gwamnoni basa tayar musu da hankali illa kawai tashin hankalinsu shi ne kada darewar wadannan Gwamnoni ta haifar da barakar da PDP zata rasa rinjaye a majalisar wakilai ta tarayya, amma indai tafiya zasu yi daga PDP ana iya hada musu da gyaran Gwamnonin Kebbi da Katsina da Bauchi. Kayar da PDP ba abu bane mai sauki, domin rijiyar da ta cika da datti da dagwalo baza a taba iya yasheta daga waje ba, ya zama dole a shiga ciki a kwarfe ruwan da yake ciki sannan a samu ruwa mai kyau, ko kuma a cike ta a sake tona wata. Dan haka, Gasa Rago A Murhun Alade Bai Zai Taba Haramta Naman Rago Ba.

YASIR RAMADAN GWALE
01-12-2013