Monday, December 23, 2013

Wane Darasi 'Yan Arewacin Najeriya Zasu Dauka Daga Sudan Ta Kudu?

WANE DARASI 'YAN AREWACIN NAJERIYA ZASU DAUKA DAGA SUDAN TA KUDU?

Abin da ya faru a makon da ya wuce na barkewar rikici a tsakanin jaririyar kasar Sudan ta kudu ya zowa da mutane da dama da bazata. Kamar yadda galibin al'ummar kudancin Sudan suka dinga korafin cewar Larabawan da suke Mulki a dunkulalliyar kasar Sudan sun ware su, kuma an hana musu dama ta yin rawar gaban hantsi, irin wannan zance da sauran zuga da dama ta sanya al'ummar dake zaune a Sudan ta Kudu suka jefa kuri'ah da gagarumin rinjayen ballewa daga kasar Sudan, bayan da Shugaba Omar Hasan Albashir ya basu damar kasancewa a dunkulalliyar Sudan ko kuma ballewa, wannan ta sanya galibin kabilun wannan yanki suka zabi ballewa daga Sudan. Wannan ballewar tasu ta zama tofin Allah-tsine ga tsohon jagoransu John Garang wanda ya tsaya kai da fata wajen ganin al'ummarsa basu balle daga Sudan ba duk kuwa da zuga da matsin lamba da yake sha daga kasashen waje akan yin hakan.

Bayan mutuwar Garang a wani yanayi mai cike da ayar tambaya, wanda dan kabilar Dinka ne masu rinjaye, aka nada Silva Kiir a matsayin sabon magajinsa, kuma shugaban al'ummar kudancin Sudan a gwamnatin Bashir dake Khartoum. Kiir shima dan kabilar Dinka ne, wannan kabila sune mafiya rinjaye a cikin dukkan kabilun da suke zaune a wannan yanki na kudancin Sudan, sun linka kabilun Nuer da Meseriya da sauransu yawa nesa ba kusa ba. Kabilar Nuer su ne suke biyewa Dinka wajen yawan jama'a a kudancin Sudan. Amma wani abin Sha'awa shi ne, su kabilar Nuer duk da rashin rinjayensu a kasar amma su ne suke da rinjayen wadan da suka yi karatun Boko, wannan ta sanya suka fi dukkan kabilun yankin wayewa da saukin lamari.

Shi wannan shugaba Silva Kiir, mutum ne da ya taso a gaba dayan rayuwarsa bai san komai ba sai yaki, da zaman kadaici a cikin daji irin na sojoji, dan haka ko makaranta bai yi ba da zata bashi damar gogewa da kuma gogayya. A saboda haka ne, a lokacin da suka samun 'yancinsu daga Sudan, kuma ga arzikin manfetur Allah ya huwace musu, akai ta fadin tashin kafa gwamnatin hadin kan-kasa, a Naivasha ta kasar Kenya suka cimma yarjejeniya da kabilar Nuer wajen tafiya tare, dan gina sabuwar kasar tasu mai cike da kalubale. Tun farkon kamun ludayin Gwamnatin Kiir masu sharhi suka fahimci cewar lallai ba zai jima ba za'a samu gagarumar baraka a cikin gwamnatinsa, don na farko kamar yadda na fada, bai yi karatu ba, kuma ba shida wata wayewa ko gogewa da zata bashi damar hada kan al'ummar kasar. Dan haka ne ba shida wani aiki face daukar zuga ko abinda aka sanya shi yi daga kasashen da suke hankoron Man-fetur din kasar ta ke da shi.

Yana daga cikin dalilin da ya sanya a karon farko ya samu sabani da 'yan kabilar Nuer din da dake cikin gwamnatinsa. Don sum fahimci babu inda shugaban ya sa gaba, face tara dukiyar haramun da kuma jiran umarni daga kasashen waje, matsin lamba da caccakar da 'yan Kabilar Nuer dake cikin gwamnatinsa ta sanya, rana a tsaka ya bayar da sanarwar korar jami'an gwamnatinsa gaba daya! Abin da ba'a taba yi ba a duniya, wannan al'amari ya harzuka 'yan Kabilar Nuer bisa jagorancin mutumin da shi ne mataimakin shugaban kasa Reak Machar. Shi Reak mutum ne dan boko wanda yayi ilimi zamani mai zurfi kuma gogagge ta fuskar mu'amala.

Zan cigaba In Sha Allah.

Yasir Ramadan Gwale
23-12-13

No comments:

Post a Comment