Wednesday, November 28, 2012

BABBAR FITINA A RAYUWAR MATASA ITA CE SHA'AWA



                             BABBAR FITINA A RAYUWAR MATASA ITA CE SHA'AWA

A wannan zamanin wani muhimmin abu da ya addabi mutane sosai, musamman matasa maza da mata shine SHA'AWA, kusan kullum matasa na fadawa cikin bala’in fasikanci kala-kala a dalilin rashin sanin hanyar kauce wa haka. Idan mutum ya yi duba na tsanaki tare da la’akari da yanayinmu da kuma yanayin zamani zaiga cewar da yawa wasu na fadawa cikin aikata fas
iqanci ba cikin son ran su ba, sai don abin ya fi karfin su. Sau da yawa za ka ga matashi mai hankali mai tarbiyya mai tsoron ALLAH, ya san illar zina, ya san girman zunubin ta, amma saboda fitinar sha’awa ya kasa daurewa ya je ya aikata din. Wani haka zai ta aikatawa ya na tuba, da haka har zina ta zame ma sa jiki ya runka ganin ai yin ta ba komai bane Subhanallah! Haka zaka ga yarinya kamila mai tarbiyya mai hankali, ta san illar zina, ta san girman zunubin ta amma sai fitinar sha’awa ta sa ta afka cikin wannan bala'i. Domin kaucewa fadawa makaranatar shaidan dole ne duk wani matashi da yake fuskantar barazanar Sha'awa ya yi la'akari da wasu dokoki da addini ya shar'anta masa, sannan kuma ya yi amfani da dabaru wanda zasu taimaka masa.

Mu sani cewa fitinar sha’awa halittace kuma a zuciya take, daga cikin ta take bijirowa, don haka mai son ya iya danne fitinar sha’awar sa duk lokacin da ta taso masa, sai ya fara da gyara zuciyarsa tukunna. To ya ake gyara zuciya? Ana gyara ta ne ta hanyar cika ta da kyawawan tunani da shau’uka, da yanke duk wata igiyar mummunan tunani daga cikin ta, da goge mazaunin duk wani mummunan shauqi. Daga nan sai kyautata dabi’u halaye da ayyuka, duk wata dabi’a, wani hali ko wani aiki da mutum ke yi indai ba mai kyau ba ne, to yin watsi da shi zai kara haskaka masa zuciyarsa. kyawawan dabi’u sun hada da yawan murmushi, taimakawa ‘yan uwa, makwabta da abokai, gaskiya da rikon amana, da sauransu. kyawawan ayyuka su hada da taka tsan-tsan wajen tsaida addini, duk abin da akan sa ba dai-dai ba ne a addinance sai ayi kokari a bar shi komin dadin sa ko ribar sa. Yawan sanya ALLAH a zuciya da yin zikiri. ALLAH madaukakin sarki, Ya fada cikin Alqur’ani mai girma cewa: “Lallai da ambaton ALLAH ne zukata kan sami natsuwa.” Shedan ba ya iya zama cikin zuciyar da ke ambaton ALLAH balle har ya gudana cikin hanyoyin jinin ta, to ta yaya kuwa har zai tafarfasar da fitinar sha’awar wannan zuciya?

Kiyaye ibada yana daga cikin maganin da yakewa mutum kandagarki daga fitinar sha’awa. Lallai ne 'yan uwa su kula da kiyaye sallolin farilla da na nafila da yawaita karatun al-qur'ani da sauran azkar da suka tabbata daga manzon ALLAH sallalahu Alaiihi Wasallam. Sannan dole mu kiyaye maganar Manzon ALLAH SAW, inda yake cewa yaku matasa duk wanda ya ke da hali ko iko to ya gaggauta yin aure, wanda kuma ba shida halin yin aure to ya yi azumi domin wannan ya na dakushe kaifin fitinar sha’awa.

Sannan dole su kansu Iyaye su kula da rayuwar 'ya 'yansu matasa maza da mata, domin kare su daga wannan bala'i. Wani matashi ya taba tambayar wani malami cewa shi wallahi yana Azumi yana karatun Al-qur'ani Amma wallahi Sha'awarsa kullum karuwa take yi, malam ya bashi amsa da cewa to lallai ya dage ya yi aure. Kusan babban dalilin da yakan hana matasa aure shine rashin tsayayya ko kwakwkwarar sana'ar da mutum zai iya rike kansa da kuma Iyalinsa, wannan kam babban al'amari ne, domin babu yadda za'aji dadin aure idan babu wata hanya da mutum zai iya daukan dawainiyar iyalinsa, dan haka dile a dage a koyi sana'a domin a dogara da kai. Ya ALLAH ka baiwa dumbin matasanmu dama da ikon yin aure.

Julius Kambarage Nyerere: Shugaba Mafi Kima A Afurka



                             Julius Kambarage Nyerere: Shugaba Mafi Kima A Afurka


Julius Nyerere kamar yadda aka fi saninsa shine shugaban kasar Tanzaniya na farko, ya zama shugaban kasa tun kasar tana amsa tsohon sunanta na Tanganyika. An haifi Nyerere a ranar 13 ga watan Afrilu a shekarar 1922 a kauyan Butaima, mahaifinsa cif Zanaki mutumin kirki ne da ake girmamawa, Nyerere ya fi shahara da sunan “Mwalimu” wanda a yaren Suwahila yake nufin “Malami”. Bayan da ya yi karatu a jami’ar Makere da ke kampala a kasar Uganda ya wuce jami’ar Edingbugh a kasar Burtaniya, daga nan ya dawo gida ya zama malamin makaranta.

Kasancewar Nyerere mutum mai kima a idanun jama’a wannan ya bashi damar sanin jama’a sosai da kuma zama tare da tattaunawa da mutanansa domin basu shawarwarin yadda zasu warware matsalolinsu na rayuwa. A shekarar 1954 ya jagoranci kafa wata jam’iyyar siyasa mai suna Tanganyika African National Union, an zabe shi a matsayin Prime Minista a shekarar 1961 a wannan lokacin ya kasance shugaban kasar tanganyika na farko. A shekarar 1964 ya ci nasarar hade kan tsiburin Zanzibar da Tanganyika inda suka zama kasa daya wadda aka radawa suna TANZANIYA, haka kuma a shekarar 1967 ya kaddamar da shirin nan na Tanzaniya ta dogara da kanta wanda aka fi sani da Arusha Declaration.

Nyerere ana kwatantashi da mutum mai tsananin kishin al’ummarsa da kuma Nahiyar Afurka. Yayi matsakaiciyar rayuwa a lokacin da yake shugaban kasa. Shuagab Nyerere dai bai zakewa turawa ba kamar sauran shugabannin Afurka, a mafiya yawancin lokuta baya boye akidarsa dangane da yadda turawa suka yi kaka-gida a nahiyar Afurka, sannan ya kalubalanci prime ministan Burtaniya Harold Wilson da Ian Smith akan 'yancin kasar Rhodesiya wadda ake kira Zimbabwe a yanzu, a saboda haka ne yafi kusanci da kasar chana sama da sauran kasashen yamma, amma sunyi zaman lafiya da tsohuwar rusashshiyar Tarayyar Sobiya da sauran kasashen duniya, musamman masu adawa da mulkin danniya na turawan mulkin mallaka. Haka kuma, yana daya daga cikin mutanan da suka jagoranci samun 'yancin kasashen Zambiya da Botsuwana da Muzambique da Angola da kuma Rhodesiya ko Zimbabwe. Nyerere ya taba zuwa Najeriya har fadar mai martaba sarkin Kano a zamanin mulkinsa.

Shugaba Nyerere ya sauka daga shugabanci bisa radin kansa a shekarar 1985 domin ya koma ci-gaba da matsakaiciyar rayuwarsa. Ana bayyanashi a matsayin wani mutum mai kaifin Harshe da iya magana, shugaba Nyerere yana da kima sosai a idon takwarororinsa Shugabannin Afurka, ya rasu a shekarar 1999 ba tare da ya mallaki ko da filin da zai gina gida ba. Turawa suna yi masa kirari da mutum mai gaskiya da rikon amana a lamuransa. Nyerere yana daga cikin shugabannin Afurka da suke da kima ainun.

Yasir Ramadan Gwale.

Tuesday, November 27, 2012

Mobutu Sese Seko Ngbengdu Wa Za Banga


                  Mobutu Sese Seko Ngbengdu Wa Za Banga



Sunan da ya fi shahara da dai shi, shine Mobutu Sese Seko, shine Shugaban kasar Jamhuriyyar Demokaradiyyar Kwango mafi dadewa. Ya dare kan madafun iko kusan tun shekarar 1965 har zuwa 1997. Mobutu dai shine mutumin da ya sauyawa kasar suna zuwa sabon sunanta Zaire. Shugaba Mabutu yana daya daga cikin shugabannin Afurka da tarihi ba zai taba mantawa da su ba, tarihi zai ci-gaba da tunawa da Mobutu ba dan yayi wani abin kwarai ba, sai dan yana daya daga cikin shugabannin da akayi a Afurka Almubazzarai mabarnata masu dan-karan ta'adi.

Shugaba Mobuto mutum ne mai shegen girman kai da nuna isa da kama karya. Ya jefa kasarsa cikin mawuyacin halin fatara da matsanancin talauci da karyewar tattalin arziki a zamanin mulkinsa, domin shi kadaine a Afurka wanda matarsa take zuwa Amerika gyaran gashi a duk lokacin da ta bushi iska, ko kuma ta tafi kasar faransa domin sayan manshafawa da turare a zamanin mulkinsa.

Mobutu shine da na farko na wata mata mai aikin hotel da ake kira Marie Medeliene Yemo. A rayuwarsa ta kuriciya ance mutumne da baya jin magana kuma sannan mai kiriniya, abokanansa da suka yi makaranta tare da shi sunce yana da kaifin kwakwalwa da hazaka sosai, amma kuma mutum ne mai wasa da yawa, wannan yasa kuma bai cika maida hankali a karatu ba, daga mahaifiyarsa ta maida shi garin Coquilhatville dan ya ci gaba da karatu, anan aka ringa zaneshi saboda yiwa turawa rashin kunya, domin ansha kama shi yana yiwa turawa gwalo da dakuwa a cikin aji.

Saboda irin yadda Mobutu ya zama dan kama karya da rashin alkibla ya sa Laurent Kabila ya yi masa juyin mulki a shekarar 1997, inda ya gudu ya koma kasar Morocco dan neman mafakar siyasa. Ya karasa sauran rayuwarsa a can kasar ta Magrib, rahotanni sun tabbatar da cewa ya mutu ne sakamakon bugun zuciya sakamakon damuwar da ya shiga tun bayan hambarar da shi daga kan mulki.

Mobutu dai ana kirga shi a zaman wani irin mutum mai al-mubazzarancin gaske, domin ansha ganin hotunansa ana zuba masa kudi ko fulawa a kasa yana takawa.

Shugaba Obama Zai Gudanar Da Garambawul A Fadar White House



Shugaba Obama Zai Gudanar Da Garambawul A Fadar White House



Shekarunki 8 kina first lady, sannan kin kara wasu shekaru takwas a majalisar dattabai haka kuma, kin samu shekaru hudu kin matsayin sakatariyar harkokin wajen Amerika; dan haka yanzu lokaci ya yi da zaki koma gida ki ci gaba da dafawa mijinki abinci. Ana sa ran nan bada jimawa ba shugaban Obama na Amrika zai yi wani garambawul mai girma a cikin gwamnatinsa dan sake shimfida mulki a karo na biyu, wannan garambawul zai yi awon gaba da Madam Hillary Rodham Clinton inda ake sa ran jakadiyar Amerika a majalisar dinkin duniya Dr Susan Rice zata maye gurbin Hillary a fadar white house, wata majiya kuma na hasashen tsohon dan takarar shugaban kasa Sanata John F Kerry zai maye gurbin Hillary. 

Sannan Babban sakataren baitul malin Amerika Mista Tim Gierthner shima wannan sauyi zai yi awon gaba da shi, inda ake sa ran shugaban ma'aikatan fadar white house Dr. jack Lew zai maye gurbinsa. Sannan shima babban sakataren tsaron Amerika Mista Leon Panetta da babban mashawarcin tsaro Tom Danilon da mataimakinsa Denis McDonough  duk suma wannan sauyi zai yi awon gaba da su. Kusan wadannan sune manyan jami'an gwamnatin Obama a shekaru hudu da suka gabata.

Monday, November 26, 2012

ZA'A TONO GAWAR MALAM YASSIR ARAFAT DAN BINCIKE



 ZA'A TONO GAWAR MALAM YASSIR ARAFAT DAN BINCIKE

Marigayi shugaban Palasdinawa Malam Yassir Araft an haifeshi ne ranar 24 ga watan agusta a shekarar 1929 a birnin al-kahira na kasar masar. Ya taso cikin matsakaiciyar rayuwa ta babu yabo 
 babu fallasa, ya yi karatu cikin kalubalen rayuwa, a shekarar 1958 shi da abokinsa suka ci nasarar kafa kungiyar gwagwarmayar 'yanto kasar Palasdinu daga mamayar Israela wadda aka fi sani da Al-FATAH sunyi ta kokarin yin managartan tsare-tsare domin yin gwagwarmaya cikin sirri, a shekarar 1959 suka fara buga wata mujallah da take kiran matasa da su fito domin gwagwarmayar kare palasdinu daga mamayar Israela, a karshen shekarar 1964 Malam Arafat ya zama Babban jagoran 'yan gwagwarmayar cetar da Palasdinu. 

Malam Arafat ya fafata da Israela ta sunkuru, sannan ya jagoranci wata kafsawa da kasar Urdun da aka fi sani da Jordan bayan da ya zama Sabon shugaban kungiyar Palasdinawa ta PLO a shekarun 1960 zuwa 1970. Malam Yassir Arafat ya halarci manyan tarukan tattaunawa na shan-shayi da kasar Israela domin neman mafita wanda ya hada da Yarjejeniyar da aka kulla a Birnin Madrid a shekarar 1991, haka kuma, ya halarci Ittifaqiyar da kayai a birinin Oslo a 1998 da kuma Ganawa da sukayi ta karshe da Shugaban Israela Areil Sharon karkashin jagorancin tsohon shugaban kasar Amerika Bill Clinton wadda akafi sani da yarjejeniyar Camp David.

Malam Yassir dai ana yi masa kallon wani mutum dan-gwagwarmaya amma ta neman sulhu wadda za'a zauna akan kujera. Karkashin shugabancinsa ya Amince da kafa kungiyoyin Hamas da Jahadil Islami a matsayin kungiyoyin gwagwarmayar a yankin Gaza da palasdinu baki daya, ana yiwa kungiyoyin biyu dai kallon wasu masu kishin addini sosai, sama da ita Fatah da ta hada da kiristoci a ciki da kuma suke san tattaunawa akan tebur.

Arafat dai ana ruwaito shi a masayin wani mutum mai kishin Palasdinu domin yana yawan maimaita kalaman "kada ku mance da palasdinu" ance kusan duk wani taro da ya halarta sai ya maimaita wannan magana. A ranar 29 ga watan maris na 2002 ya yi wata magana da kusan ta mamaye galibin jaridun kasashen larabawa inda aka ruwaito shi yana cewa "suna san kama ni a matsayin wani fursuna, ni kuma ina ce musu mutuwa cikin shahada nake fata" da kuma wata magana da ya taba fada a Camp david cewa "shugabannin larabawa basu taba mafarkin barin Jerusalem a hannun Yahudawa ba".

Malam Yassir Arafat dai ya rasu yana da shekaru 75 a wani asibiti a kasar faransa bayan ya shafe wani lokaci yana jinya. Sai dai bayan shekaru 8 da mutuwarsa aka fara wani bincike kan musabbabin mutuwarsa, shin mutuwa ce ta ALLAH da ANNABI ko kuwa guba aka sanya masa, inda ya zuwa yanzu bayan wani bincike na sirri da gidan talabijin na Al-Jazeera ya gudanar ya tabbatar da cewar Kashe Malam Yassir Arafat akayi, inda wannan batu ya tayar da kura. yanzu haka dai yau za'a tono gawarsa domin yin bincike na karshe. ALLAH ya jikan Malam Yassir Arafat, ALLAH ya taimaki Palasdinawa ya kawo karshen wannan zama na tashin hankali da aka kwashe sama da shekaru 60 ana yi.

Yasir Ramadan Gwale.

Sunday, November 25, 2012

PDP DA ZABEN 2015


PDP DA ZABEN 2015

Buba wata hadaka da 'yan Hamayya zasu iya yi da zata kawar da PDP a matakin zaben Shugaban kasa. Ya kamata 'yan Najeriya mu gayawa kanmu gaskiya, Bahaushe ya ce shirin zaune yafi na tsaye, tabbas PDP suna da cikakken shiri da tsari na cigaba da mallakar kujerar shugaban kasa a Najeriya ko talakawa sunso ko basu so ba. 'Yan Hamayya kullum labari suke bayarwa cewa zasu yi hadakar da zata kawo karshen PDP, wanda wannan abu shafu labari ne. A Najeriya talauci ba karya bane, Talauci gaskiya ne, jama'a na fama da talauci a birane da kauyuka, PDP suna da kudin da zasu sayi kuri'u dan samun zabe kuma za'a sayar musu, duk mutumin da zai je masallaci ya saci takalmi ko Agogo, ko matar da zata je gidan biki ta zari takalman mutane bana jin za'a sayi kuri'unsu lokacin zabe suki sayarwa. Sannan ga jama'a da suke fama da kuncin tunani a birane da kauyuka sannan ga talauci ya yi musu daurin butar malama.

Tabbas Zabe ba shine zai kawo karshen Mulkin PDP a Najeriya ba. Idan da gaske muke son gyara ko dai 'yan Najeriya su dunguma su koma PDP, Bahaushe ya ce Sarkin Yawa yafi sarki karfi Alabashshi su samar da wanda suke so ya zama shugaban kasa ta karfi da yaji, ko kuma 'yan Najeriya su yi bore irin wanda ya kawar da Hosny Mubarak a Masar, ko kuma su cigaba da hakuri cikin Mulkin PDP. Amma indai zabe ake nufin zai kada PDP to lashakka za'a jima zaben bai kada PDPunba.

A kwanakin baya anyi zaben gwamna a Ondo wanda jam'iyyar Labour ta lashe wanda daman ita ke jan ragamar mulkin jihar. Kowa yasan cewa PDP ta tsayar da dan takarara kuma ya sha kaye a hannun gwamna me ci Mimiko, wannan ko shakkau ba ba wani abun mamaki bane, domin sanin kowa ne a zaben shugaban kasa da ya gabata Jami'yyar Labour ta fito fili balo-balo ta nuna goyon bayanta a zaben shugaban kasa da cewa su PDP suke yi, dan haka abun da ya faru a Ondo ramawa kura aniyar ta ne, PDP basu ki su fadi zabe a kowacce jiha ba, matukar sune suke da kujerar Shugaban kasa.

A 'yan kwanakin da suka gabata Majalisa ta zauna a kowacce mazabu a Najeriya domin jin ra'ayoyin 'yan Najeriya dangane da kundin tsarin mulki da za'ayiwa kwaskwarima. Wannan jin ra'ayi ya sake tabbatar da cewar 'yan Najeriya ba a shirye suke domin samun gyara ba. Idan muka buga misali da kanmu a Arewa su waye suka zauna suka shirya wani kuduri kwakkwara da da sunan Arewa wanda zai lalubo hanyoyin da zamu fita daga halin da muke ciki na kaka naka yi? Amsar ita ce babu, Ina malamai? Ina 'yan Boko? Ina tsaffin shugabanni? Duk kowa ya kame hannunsa sai aka bar 'yan Siyasa zallah da matasan da basu san inda Najeriya ta sanya a gaba ba, wai ra'ayinsu za'ayi amfani da shi a gyaran rayuwarmu ta nan gaba. Kaico!

Rahotannin da suka biyo bayan wannan jin ra'ayin sun nuna, babu wani guri da aka samar da wata kyakykyawar natija da sunan Arewa, 'yan daba da 'yan shaye-shaye kusan sunci kasuwarsu yadda suke so! Magana fa ake ta rayuwamaru gaba daya. idan har da gaske muke me yasa bamu yiwa wannan jin ra'ayi cikakken shiri ba, me ya sa bamu rufe kasuwanni da makarantu ba, limamai da ladanai da masu unguwanni da hakimai da dagatai da shugabannin kananan hukumomi da kansiloli da sauran al'umma su fito kwansu da kwarkwatarsu ba? Muna tsammanin kowa yana can yana harkokinsa gyara zai zo? Duk wanda ya zaci haka to ya fahimci kuskure. A masar mata da maza suka bar gidajansu da kantunansu da makarantansu da guraran ayyukansu, suka zo filin ALLAH suna kiran sai shugaba Mubarak ya tafi, Bahaushe ya ce komai girman doka taron jama'a ya fita, babu girma babu arziki Mubarack ya kama gabansa.

Mu sani mu kara sakankancewa babu wani gyara da zai zo, alhali kowa ya kama gabansa. Dole sai mun fito mu duka mun taru munce ga abinda muke so sannan zamu samu. Amma abin haushi da takaici a wasu guraran wannan jin ra'ayi bai yuwuba, saboda 'yan jagaliya sun hana kuma ya hanu, amma da yau liman ya fito mai unguwa da sauran jagororin al'umma sun fito, shin kana jin akwai wani marar kunya da zai kawo wargi a wajen? Wallahi gyara bai taba zuwa cikin lalaci da san jiki da jin dadi ba. Mahtuma ghandi sai da yayi tafiya a kasa ta sama da mul 250 domin neman 'yanci, har hakarsu ta cimma ruwa.

Sannan kuma, Sakamakon zaben da akayi a jihohin Kebbi da Adamawa ya kara tabbatar da cewar duk balakoko da hayagaga da 'yan Arewa suke akan neman canji zance ne kawai. Domin babu wani abu da ya sauya, kuma haka za'ayi ta tafiya har zuwa 2015. Dama daya 'yan Arewa suke da ita ya zuwa yanzu, shine takawa Shugaban kasa Goodlock Burki daga tsayawa takara a zabe mai zuwa, sannan su samar da dan Arewa wanda zai tsayawa PDP takara. Amma matukar muka ce zamu kada PDP da Jam'iyyar Hamayya to wallahi wannan tatsuniya muke yi, zaben shugaban kasa jam'iyyun Hamayya ba da gaske suke ba, dan babu wani abu da ya nuna cewa da gaske akeyi. Kuma mu 'yan Arewa dole mu sani cewa zaben shugaban kasa ba zai taba cuwuwa a Arewa ba, idan ana cin zaben kenan. Idan kuma ana maganar satar zabe to PDP sunyi shal ALLAH ya kiyaye.

Yasir Ramadan Gwale

Friday, November 23, 2012

RANAR GODIYAR ALLAH A AMERIKA



RANAR GODIYAR ALLAH A AMERIKA


A ranar kowacce Alhamis ta karshen watan Nuwamba ita ce rana mafi muhimmanci a wajen Amerikawa sama da duk wasu ranaku na ibada ko na bukukuwa. Amerikawa sun dauki wannan rana da kima da kuma muhimmanci kwarai da gaske, domin acewarsu rana ce da suke nuna godiya ga ALLAH bisa baiwa da ni’imar da ya yi musu, miliyoyin Amerikawa na yin doguwar tafiya domin saduwa da Iyali da ‘yan uwa da abokai, domin wannan rana, haka kuma, gwamnati kan bayar da hutun da ya kai kwanaki hudu, domin mutane su sami zarafin tafiya su sadu da ‘yan uwansu da suka jima basu ga juna ba.

Ita dai wannan rana ta samo asali ne tun kusan shekarar 1598 a jihar Texas inda Asalin Amerikawa wato Indiyawan daji kan hadu domin yin murnar kammala aikin gona lafiya tare da nuna godiya ga Ubangiji cewa anyi noma lafiya kuma angama lafiya. Kusan bayanai sun tabbatar da cewa daga shekarar 1863 ta zama cewa duk shekara sai wadannan Indiyawan daji sunyi maci tare da yin gangami domin bikin wannan rana, wanda wannan yayi kama da bikin kalankuwa a al’adar Hausawa ta dauri.

Kusan tun zamanin shugaban Amerika na farko George Warshington ake yin wannan biki a hukumance, inda wasu kan shirya gangami tare da fadakarwa da wayar da kan jama’a, wasu kuma kan zagaya domin barka da wannan rana, wasu kuma kan zauna a gida su dagargaji naman talo-talo da sauransu. A mafiya yawancin jihohin Amerika ana yin wannan biki, sai dai yakan sha-bamban daga wannan waje zuwa wannan waje.

Amerikawa suna taran wannan rana ne da wasu muhimman abubuwa, misali wasu kan canza sabuwar mota a wannan rana, wasu kuma kanyiwa gidajensu sabon fenti, ko dasa sabbin furanni, wasu kuma kancanza ilahirin abubuwan da suka mallaka, da suka hada da kayan sawa, gadaje da kujeru, talabijin, kwamfuta da sauransu. Haka kuma, akan yiwa gidaje da wuraren shakatawa ado da furannin roba masu kawa da kuma abun falfali da sauran kayan zayyana masu daukar ido.

Shaguna da kantuna da kasuwanni da guraren hada-hadar yau da kullum sukan kasance a garkame a wannan rana. Da yawan ‘ya ‘yan da suka jima a wajen cirani sukan zo su gaida iyayansu suyi hira da su, su tattauna labarun bayan rabuwa, haka kuma, sukan raba kyaututtuka ga junansu da suka hada da kwamfutar tafi da gidanka, wayar hannu, na’urar sauraron kade-kade da sauran dangin kayan latironi, har ila yau kuma, sukan yi musayar kayan tande-tande wadan da ake nannadewa a cikin wata irin leda ta musamman a saka acikin kwali.

Akanyi dafe-dafe da ciye-ciye sosai a wannan rana. Babban abinda aka fi ci domin bikin wannan rana shine tsun-tsayen Talo-talo, a kafatanin kasar Amerika akan yanka talo-talo sama da miliyan biyar domin yin ragadada aci tare da ‘yan uwa da iyalai da kuma abokanai sannan kuma akanci kayayyakin itatuwa da suka hada da ayaba da mangwaro da kuma matsatststun kayan marmari.

Amerikawa sun dauki wannan rana a matsayin ta hutu, dan haka basu zuwa guraran ibada ko wajen fastoci. Sabanin sauran kasashen da suka kwai-kwayi wannan al-adar ta gargajiyar Amerika, inda ake dunguma zuwa majami’u da ikilishiyoyi domin yin ibada.

Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com






Thursday, November 22, 2012

AL-SA'UD


                                             AL-SA'UD

Abdulaziz Ibn Abdulrahman ibn Faisal ibn Turki Al-sa'ud, an haifeshi a birnin Riyad a shekarar 1879, sunan da ya fi shahara da shi shine Abu-Turki Akhu-Nura (wato baban Turki dan uwan Nura, wadda Nura kanwarsa ce). Ya taso cikin rayuwar kuruciya mai ban sha'awa, ya yi karatun addini a wajen mafaifinsa Imam Abdurrahman, ya nuna kwazo matuka lokacin da yake karami.

Bayan da ya girma ya zama saurayi sunyi wata tafiya da mahaifinsa Imam Abdurrahman Ibn Faisal Ibn Turki zuwa kuwait ya nuna cewa shi namiji ne, kuma jarumi, bayan dawowarsu daga wannan tafiya ne, ya hada wata runduna ta mutum 60 domin jihadin daukaka addinin ALLAH tare da tsayar da sunnah da Shari'ah a yankin Khalij. A ranar 5 ga watan Shawwal 1319 suka yi jihadin da ya tabbatar da kasar Saudiyya mai bin tafarkin sunnah.



Wednesday, November 21, 2012

GA ABINDA ABBAS FAGGO YA FADA WANDA YA JA MASA FUSHIN GOV ISA YUGUDA



GA ABINDA ABBAS FAGGO YA FADA WANDA YA JA MASA FUSHIN GOV ISA YUGUDA

'Yan uwanmu da suke Abuja zasu shaida wani gagarumin biki da za'ayi, ba bikin kowa bane ba kuwa Illa bikin dan gidan maigirma gwamnan Bauchi inda zai angwance da Amaryars
a 'yar gidan wani hamshakin mutum wanda ya taba yin takarar Shugabancin jam'iyyar PDP ta kasa. Rahotanni dai sun tabbatar da cewa tuni Ma'aikatar kananan Hukumomi ta jihar Bauchi ta umarci kowace karamar Hukuma da ta bayar da gudunmawa ta Naira Miliyan Biyu (2m) Domin wannan shagali na bikin dan maigirma Gwamna. Tuni Iyalin maigirma gwamna suka bayar da kwangilar Buga kalanda da wasu takardu da za'a raba yayin wannan biki ga wata madaba'a a birnin tarayya Abuja, Sannan kuma anbayar da kwangilar Buga wasu karin kayan tsara da suka hada da Jakunkuna da kofunan shayi na kawa da sauran kayayyaki ga wata mata dake Legas, duk wadannan abubuwa dai za'a rabar da su a yayin wannan biki, kuma za su kasance dauke da hoton Ango ne da Amarya.

Tuni kuma aka baiwa Ango kyautar wata dirkekiyar Mota SUV JEEF a matsayin kyauta ta musamman. Sannan kuma kowanne Shugaban karamar Hukuma daga cikin kananan Hukumomi 20 zasu tura matansu Abuja domin shaida wannan biki na kasaita da za'ayi, tun daman Maigirma Gwamna tuni ya zama dan Abuja.

Labarin wannan biki dai ya karade dukkan jihar Bauchi. Sannan kuma Gwamnatin Jihar Bauchi ta hannun Sakataren Gwamnati ta turawa Ango da kudi wuri na gugar wuri har Dalar Amurka 80,000 domin bikin da zaiyi a Ingila na murnar kammala karatunsa na Jami'ah, wannan kudi dai maigirma gwamna ya bada umarni a aikawa da dansa saboda yana bukatarsu cikin gaggawa, dan yana san sayan wata dirkekiyar marsandi wadda zai hau yayin wannan biki.

Haka kuma, a watan Nuwambar 2009 mai dakin mai girma gwamna ta bukaci a aikawa da danta wanda yake a birnin Washington na kasar Amurka da kudi Fan na Ingila 150,000, wanda wannan kudi tuni aka tura su ta hannun tsohon akawun jihar Bauchi.

Wani abin mamaki dangane da haka shine, maigirma gwamna yana da mata uku (3) da 'ya 'ya ashirin da daya (21) dukkansu anhaifesu a Najeriya amma kuma wasu daga cikinsu suna waje ana yi musu hidima da kudin al'ummar Jihar Bauchi, sannan kuma maigirma gwamna yana yin amfanin da kudin jihar Bauchi wajen nemawa 'ya 'yansa biyu da aka haifa a Amerika izinin zama 'yan Amerika! Tuni maigirma Gwamna ya mallaki wani katafaren gida a birnin Maryland dake kasar ta Amerika. Duk wannan facaka da kudin al'ummar Bauchi tana faruwa ne a yayin da ma'aikata suke tagayyara wajen karbar hakkinsu a matsayinsu na ma'aikata. ALLAH ya ceci jihar BAUCHI.

Ya Mai karatu wannan fa shine abinda ABBAS FAGGO ya fada a shafinsa na facebook wanda ya bakantawa Gwamna Isa Yuguda Rai, har ta kai ya sanya aka kama shi aka daure shi. Yanzu zance da muke Ankori ABBAS FAGGO daga aikin da yake a matsayinsa na dan jihar Bauchi, laifinsa kawai shine yayi magana akan Amfani da maigirma Gwamna ya yi da dukiyar al'umma wajen hidimtawa Iyalansa. ALLAH ya sawwake Najeriya Ina muka dosa?

Tuesday, November 20, 2012

ANKASHE MALAMI, ANKASHE SOJA, ANKASHE DANSIYASA




ANKASHE MALAMI, ANKASHE SOJA, ANKASHE DANSIYASA

Sheikh Jafar Adam yana Sallah a Masallaci, yana karanta al-qur'ani aka bishi har cikin masallaci aka kashe shi (wajen Ibada), har yanzu babu wani abu da aka yi, walau angano wadan da suka kashe an hukuntasu, walau anbiya Iyalansa diyyar jinisa, babu ko daya da ya faru.

Madu Fannami Gubio Dan takarar Gwamna ne a Borno, ranar Juma'a yana dawowa daga Sallar Juma'a aka kasheshi, har ya zuwa yanzu sai dai labari, babu wani mataki da aka dauka, dan sake aukuwar hakan a gaba.

Gen. Mamman Shuwa Soja ne, wanda ya yi yaki domin tabbatar da Najeriya bata balle ba. Amma wasu suka shiga har cikin gidansa suka kasheshi, har yanzu ko ta'aziya gwamnati bata yiwa Iyalansa ba, WAI wannan wanda ya karar da rayuwarsa ta samartaka gaba daya dan bautawa Najeriya kenan.

Hon Abubakar Abba Garko dan majalisa ne a kano, anbishi har inda yake zama ankashe shi. Wannan fa sune Masu yin doka dan al'umma. Wanda shima babu wani abu da za'ayi, haka nan abin zai wuce.

Ankashe Malami, Ankashe soja, Ankashe Dansiyasa Talaka kuwa wannan ko labarin kisansa baka gani a jarida ballantana ka sani, sai dai kaji kudin goro ankashe mutane kaza... Yanzu wa ya yi Saura kenan? Kamar Yadda muke karantawa ankashe wane To Wallahi haka wata rana za'a wayi gari ace ankashini ko ankashe ka, kuma babu wani mataki da za'a dauka. 

Dan haka duk wanda ya dauka Gwamnati zata bashi kariya to yana batawa kansa lokaci ne. Wallahi kodai mu tashi domin kawo karshen wannan zaman zullumi da tsadar rayuwa ko kuma muna ji muna gani kaskanci da wulakanci suyi ta faruwa akanmu, babu kuma yadda muka iya. A garinku kana kallo sojojin JTF zasu zo su kashe wanda suka ga dama su tafi kuma sun kashe . . . (banza anan Duniya) ALLAH ya sawwake! Wadanda aka kashe ba tare da hakkinsu ba, ALLAH shaheed ne, zai yiwa kowa sakayya. ALLAH ka gafartawa wadan da suka mutu da Imani.

Wednesday, November 14, 2012

‘Yan Najeriya Na Wancakalar Da Babbar Dama



‘Yan Najeriya Na Wancakalar Da Babbar Dama

Sau da dama nakan yi mamaki yadda mu ‘yan Najeriya muka cika yawan korafi akan rashin tabuka wani abun kuzo mugani da masu muki suke yi. Kullum muna ta yamadidi da cewa masu mulki idan anzabesu suna komawa su zama ‘yan dumama kujera da amshin shata ga iyayan gidansu wadan da suke zama tsani na hayewarsu kan Dukkan wasu madafun iko.

Siyasa na da muhimmanci ga kowace kasa da take bin tafarkin mulkin dimokaradiyya, dalili akan haka kuwa shine tsarin siyasar demokaradiyya na Baiwa al’umma kasa damar zaben shugabannin ko wakilai da zasu jagoranci al’umma ta Dukkan bangarori na gwamnati, wannan tsari na demokaradiyya ya Baiwa al’ummar kasa damar zaben mutanan da suke ganin sun cancanta da su share musu hawaye domin fitar da su daga halin kunci da masti na rayuwa.

Al’ummar kasa suna bayar da goyon baya ainun wajen ganin sun marawa mutumin da suke da yakin zai share musu hawaye, ya samu kaiwa ga gaci domin yi musu shugabanci ko wakilci nagari. To amma babban kuskuren da al’umma suke tafkawa wajen zaben shugabannin da wakilai shi ne shin sanin tayaya talakawa zasu san mutumin da ya dace su zaba ya shuagabancesu ko ya wakilce su? A lokuta da dama talakawa na korafin cewar sunyi zaben tumun-dare musamman ga wakilai wadanda suke tafiya majalisar kasa su zama ‘ya Aye da Nay.

Talakawa ko masu zabe suna da babbar dama da kusan tun da Najeriya ta komo mulki irin na tsarin demokaradiyya ake ta wanacakali da wannan muhimmiyar damar. Domin tsarin mulkin da yanzu ake neman yiwa kwaskwarima ya yi tanadin cewa duk mutumin da baya yiwa al’umma wakilci na gari suna iya yi masa kiranye ya dawo gida a sake zabe a tura sabon wakili, amma wannan damar muna ji muna kallo ta saraya a garemu, duk kuwa da masu ilimi da muke da su da suka san da zaman wannan ayar doka. Duk mutumin da muka zaba muna ji muna kallo sai ya tafka tsiyarsa har ta tsawon shekaru hudu, ya kudance ya zama hamshakin attajiri cikin ‘yan shekarun da basu kai cikin ‘yan yatsunsa ba.

Mafiya yawan wadan da suke yin korafin cewar sun zabi wakili ko shugaba yaje yana dumama kujera sune matasa. Wanda a hakikanin gaskiya matasa a tsarin demokaradiyya sune gishirin tafiya, sau da yawa ‘yan siyasa na amfani da matasa wajen cimma kaiwa zuwa ga wasu madafun iko, ba laifi bane a yi amfani da matasa wajen tallata manufofi a tsarin demokaradiyya, kamar yadda a baya bayannan ya nuna cewa a zaben da ya gabata na Amerika matasa sun taka muhimmiyar rawa wajen samun nasarar shugaban Obama, wannan ta sanya Obaman fashewa da kuka a gaban matasan lokacin da yake yi musu jawabin godiyar sadaukar da kansu da sukayi.

Abinda yake laifi a tsarin siaysar demokaradiyya shine ayi amfani da matasa wajen bangar siyasa domin samun nasara ko ta halin kaka. A mafiya yawancin lokuta ana amfani da matasan ne domin razana abokan hamayya da miyagun makamai, bayan anbasu kwayoyi da wiwi sunsha sun cake. Abinda yafi zama abin mamaki shine su wadannan matasa ‘yan uwanmu suna da masaniyar cewa shi wannan dan siyasa da ya basu kudi suka masa abinda suk yi, ba tasu yake yi ba, sun san da cewar idan fa yaci zabe, basu isa su je wajen da yake ba. Abinda yake zama abin mamaki shine shin matasan nan da suke bari ana amfani da su dan cimma manufar zabe, duk da cewar sun san ‘yan siyasa zasu yi watsi da su da zarar sun ci nasarar samun zabe, sun san ciwon kansu kuwa?  Suna da masaniyar cewa wadannan ‘yan siyasa basu damu da su ba illa kawai sun maida su wata matattakala ta kaiwa zuwa ga samun nasarar zabe? Amsar da muke san mu sani it ace yaushe ne matasanmu zasu ki yarda ana amfani da su a matsayin ‘yan bangar siyasa a bisa kudi kalilan?

Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com

Yuwuwar Juyin Juya Hali A Najeriya



Yuwuwar Juyin Juya Hali A Najeriya

Najeriya kusan ita ce kasar da muka fi kowace sanin halin da take ciki, amma ban taba jin labarin wata kasa da ake irin abinda ake yi a Najeriya ba. Hakika abin na Najeriya ya wuce munshairin, shugabannin suna mahaukaciyar sata da ta shallake hankali da tunanin dan adam mai lafiyayyan hankali, ga kazamin cin-hanci da rashawa da ya dabaibaiye kusan Dukkan wasu harkoki a Najeriya, babu maganar bangaren gwamnati da bangaren ‘yan kasuwa duk inda ka latsa abin daya ne, kawai sai dai wani yafi wani muni, ko kuma gwargwadon yadda kudi ke zirga-zirga.

A Najeriya ne kadai inda ake irin wannan mahaukaciyar satar kuma a ringa yabawa barayin da suka dibga irin wannan sata. Misali tsohon shugaban hukumar kula da tashashin jiragen ruwa ta Najeriya Olabode George da manajan darakta Aminu Dabo da mukarrabansu sun tafka wawar gararuma da dukiyar kasa da ta kai kusa Naira Biliyan 85, amma da aka tabbatar da laifinsu kuma kotu ta dauresu shekaru biyu kacal, wai lokacin da zasu fito daga kaso, sai ga jama’a sunyi tururwa wajen taryansu daga gidan sarka, wannan babban abin takaici ne da rashin sanin ‘yancin kai da wawanci, idan ba haka ba, tayaya mutanan da kowa yasan laifinsu shine sun yiwa kasa sata aka daure su amma jama’a na tururwa wajen yi musu san barka, sai ka kasa fahimta shin muran ake taya su sunyi sata ko kuwa me?

Haka kuma, kamar yadda rohoto na baya bayan nan wanda kwamatin da gwamnati ta kafa karkashin tsohon shugaban hukumar yaki da yiwa tattalin kasa ta’annati EFCC Malam Nuhu Robadu akan ya binciko badakalar da ake yi da kudadan man-fetur, kuma sunyi bankada mai girman gaske, wanda kuma alamu suka nuna ana neman yiwa wannan rahoton bita da kulli. Shi dai rahoton na Malam Nuhu Ribadu ya ce antafka kazamar sata a harkar man-fetur inda ya ce ansace kudi sama da Naira Tiriliyan 2.8 Hasbinallahu wani’imal Wakeel! Sai gashi tun lokacin da shugaban yake gabatar da rahoton binciken nasa aka nemi a yiwa abin kafar ungulu, domin daga cikin ‘yan kwamatin wanda alamu suka tabbatar da cewar daman an saka su ne domin su yiwa rahoton yankan baya, sai mataimakin shugaban kwamatin wanda bayanai suka tabbatar da cewar ko sau daya bai-taba halartar zaman kwamatin ba sai daga karshe yazo yana cewa wai rahoton yayi tsauri! Saboda kawai kwamatin ya zargi iyayan gidansa da rubdaciki da dukiyar kasa.

Wannan aiki na bankada da kwamatin Malam Nuhu Ribadu ya yi wani muhimmin al’amari ne. Domin da farko lokacin da aka bayar da sanarwar kafa wannan kwamiti karkashin Jagorancin Ribadu, ‘yan Najeriya da yawa sunga wallensa cewa daman amfani gwamnati ta yi da shi a zaben da ya gabata. Duk da cewar Ribadun ya sha nanata cewa wannan batu karya ne, jama’a basu yarda da shi ba, sai yanzu da ya yi wannan bankada mai girman gaske a harkar man-fetur jama’a ke yaba masa tare da nuna cewa ya yi kokari wajen wannan aiki.

Tabbas a Najeriya barayi bazasu daina sata ba. Domin matukar akwai dumbin arzikin mai a Najeriya to kuwa suma barayin suna nan sun bude bakin jakunkunansu domin jidar dukiyar kasa suje su boye a kasashen waje. Bangaren da yafi kowa ne bangare muhimmanci a Najeriya shine bangaren Shir’ah amma harkar rashawa da cin-hanci tayi masa daurin gwarmai. Sai kayi mamakin harkar shar’ah a Najeriya inda ta dosa, a Najeriya ne kotu mai alkalai ta wanke tsohon gwamnan jihar delta James Ibori cewa mai gaskiya ne, tsarkakakke ne daga Dukkan zargin cin-hanci da halarta dukiyar haram, amma abin mamaki kuma sai gashi kotu a kasar Burtaniya ta kamashi da laifi kuma ya amsa laifinsa. Anan ne mutum zaiyi tambaya anya kuwa a Najeriya kotuna shari’un da suke yi na gaskiya ne kuwa? Domin mutumin da kotu ta tsarkake shi daga zargin halatta kudin haram, sai gashi kuma kotu a wajen Najeriya ta ce yana da laifin halatta dukiyar haram kuma ya amsa da bakinsa cewa haka ne! Wannan yake kara nuna babban abin tsoro dangane da harkar shari’ah a Najeriya.

Dan haka lokaci yayi da ‘yan Najeriya zasu fito su yaki wannan mummunan cin hanci da rashawa da ci da gumin talakawa. Sanin duk dan Najeiya ne cewa halin da ake ciki na matsin rayuwa da kamfar kudi a hannun talakawa ya kai magaryar tukewa, su kuma wadannan miyagu azzalumai da sunan masu rike da madafun iko basu da wata niyya ta daina wannan satar, bil-hasali ma har gasar sayan jirage suke yi da kudin da suka sata, to dan haka ya zama dole al’ummar kasa su yi fito-na-fito da miyagun masu mulki.

Kamar yadda muka samu labari halin matsi da kuncin rayuwa ya sanya bore wa shugabannin kasashen larabawa wanda ya yi awan gaba da shugabannin ‘yan kama karya irinsu Hosny Mubarack a Masar da Zainul Abiden Ben Ali a Tunisiya da Ghaddafi a Libya da kuma irinsu Ali Abdallah Saleh a Yeman. Lalli duk wani hali na matsi da al’ummar wadan-can kasashe na larabawa suka shiga nafila ne akan abinda yake faruwa a Najeriya, dan haka mune a hakku mu fito muyi Allah-wadarai da wadannan gungu na azzaluman masu mulki.

Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com

Tuesday, November 6, 2012

Shiri Na Musamman Dangane Zaben Amurka



Shiri Na Musamman Dangane Zaben Amurka

Ita dai kasar Amurka kasa ce da ta samu daukaka a wannan karni inda a halin yanzu ita kadai ce tilo a cikin kasashe da ke da matsayin mai karfi sai Allah ya isa. Duniya, baki daya, na zura ido ne ga abubuwan da ke gudana a kasar Amurka domin kwaikwayo ko kuma tsara yadda makomar sauran kashen duniya zata kasance.

Wannan matsayi da ta samu kuwa ya samo asali ne daga irin gwagwarmaya da wahalhalu da ta sha a hannun Birtaniya a lokacin da ta yi mata mulkin mallaka.

Lokacin da tayi kokarin kubucewa daga hannun Birtaniya an kai ruwa rana wanda daga karshe suka samu nasarar samun yanci. Wannan yanci da Amurkawa suka samu sai suka yi amfani da shi wajen tsarin da zai raba su daga komawa irin kangin da suka fito. Babban abinda suka dabbaka shi ne yancin dan adam ta wajen magana da harkokin rayuwa. Sun kuma bawa kokarin daidaita mutane mahimmanci. Kai a saboda wannan ne lokacin da aka yi kokarin kawar da bauta kasar ta shiga yakin basasa.

Wannan yanci dai shi ne abinda bakaken fata suka yi amfani da shi a cikin shekarun alif dari tara sittin wajen samar musu matsayi daidai da duk wani dan adam a kasar Amurka.

A kunshe a cikin dimokradiyyar Amurka akwai wannan tsari na yanci. A Amurka matukar ba wata ta'asa ko aikin assha, bayyananne, mutum ya aikata ba yana da damar ya fito yayi takara kuma a zabe shi, in har mutane sun gamsu da nagartarsa da kuma manufofinsa.

Wanna salo ya karawa kasar Amurka tagomashi a duniya da kuma sauran tsare-tsare masu inganci da suka maida ita farin wata a cikin kasashen duniya.

Zaben bana dai za'a kara ne tsakanin Shugaba mai ci a yanzu, Barack Hussein Obama II da  Willard Mitt Romney. Shugaba Obama na takara ne a karkashin jam'iyyar Demokrat a inda shi Romney yake takara a karkashin jam'iyyar Rifublikan.

Tarihin jam'iyyar Demokrat ya samo asali daga shekarar alif dari bakwai da casa'in da biyu (1792) inda ta ware daga wata jami'iyya mai rajin juyawa tsarin tarayya baya da ake kira Anti Federalist. A shekarar alif dari takwas da ashirin da takwas ne jam'iyyar ta zama jam'iyyar Demokrat bayan zaman gamin gambizar da suka yi da yan Refublikan ya watse.

Manyan manufofin ita wannan jam'iyya ba su wuce tabbatar da yanci ba da kuma samarwa mutane sake da walwala.

Ita kuwa jam'iyyar Refublikan ta kafu ne a shekarar alif dari takwas da hamsin da hudu a saboda manufar ruguje cinikin bayi da bauta da suka tsaya a kai. Wannan ya sa ta samu karbuwa sosai a arewacin Amurka da kuma rashin tagomashi a kudancin Amurka.

Babbar manufar jam'iyyar Refublikan (wacce ake kuma kira da GOP ko Grand Old Party) shi ne kare masu hannu da shuni domin su tara dukiya mai yawa. Haka kuma suna da hali irin na yan mazan jiya.

To shi dai Barack Hussein Obama shi ne shugaban Amurka na arba'in da hudu kuma na farko da ke da jinin bakar fata. Shi dai an haife shi a Honalulu a jihar Haway (Hawaii). Baban sa baki ne dan kasar Kenya wanda ya je kasar Amurka karatu inda ya hadu da mahaifiyarsa, wacce take farar fata ce yar Amurka.

Shi dai lauya ne da yayi aiki a matsayin lauyan masu neman kwatar yanci a jihar Chikago ya kuma koyar da ilimin shari'ar tsarin mulki a makarantar koyon aikin lauya ta jami'ar Chikago.

Ya zama dan majalisar dattijan jihar Chikago har karo uku kafin ya zama dan majalisar dattijai ta kasa daga jihar Chikago a shekarar 2004 bayan sha kaye a kokarinsa na samun zuwa majalisa wakilai a shekarar 2000.

Obama shi ne bakar fata na farko da ya zama shugaban mujallar Haward Law Review, wacce mujalla ce mai kima a harkar shari'a a Amurka.

Williard Mitt Romney hamshakin dan kasuwa ne kuma tsohon gwamnan jihar Massachusetts. An haife shi a garin Ditroit da ke jihar Michigan. Mahaifinsa wani babba ne a harkar kere-keren motoci.

Karatun Romney dai tsince-tsince ne. Ya shiga jami'ar Stanford amma ba'a je ko'ina ba ya tsallake ya barta. Daga baya ya sake shiga wani kwas da makarantar shari'a ta Havard ta ke yi tare da hadin gwiwar makarantar kasuwanci ta Havard. Ya gama wannan karatu a 1975.

Hasashen masana ya fi bada karfi ga samun nasarar Shugaba Obama duk da cewa kuri'ar jin ra'ayin jama'a na nuni da cewa har yanzu ba wanda ya bawa wata rata ta azo a gani.

Babban abinda Amurkawa ke dubawa wajen wa zasu zaba a wannan zabe bai wuce wanda zai taimaka wajen fitar da su daga kangin talauci da suka samu kansu a ciki ba.

Obama yayi kokari mutuka wajen ganin Amurkawa sun koma aiki kuma tattalin arzikinsu ya karu. Duk da an samu cigaba kadan ta wannan fanni wasu na ganin kokarin da akayi ya gaza fatansu.

Obama yayi kamfe a shekarar 2008 a bisa doron tsamar da kasar Amurka daga yakin Iraki da Afghanistan da kuma rufe kurkukun Guantanamo. Haka kuma yayi alkawarin inganta rayuwar Amurkawa.

Wani babban abu da Shugaba Obama ya ba muhimmanci shi ne inshorar lafiya ga Amurkawa.

Amurkawa da yawa na ganin cewa Obama ya taka rawar gani wajen fannoni da dama na al'amuran kasar Amurka amma babba abin damuwarsu shi ne, duk da cewa an samu cigaba, kason marasa ayyukan yi a kasar har yanzu ya da dan yawa. Kusan kashi bakwai da digo tara cikin dari ne ke gararamba ba aikin yi.

Kamfe din Obama a wannan karon an yi masa lakabi ne da (ci) gaba (forward).

Romney da yan kamfe dinsa sun maida hankali ne wajen kushe manufofin gwamnatin Obama tare da yin amfani halin matsi da Amurkawa ke fama da shi wajen nuna cewa Obama bai taka rawar gani ba saboda haka ba dalilin barinsa yayi tazarce. Suna caccakar tsarin inshorar lafiyar da ya fito da shi.

Idan aka yi la'akari da abubuwan da ka je su zo da wuya Romney ya kada Obama. Na farko dai Romney yana fama da matsalar addininsa. Ma fi yawancin Amurkawa na kallon yan darikar Mormon a mazaunin yan kungiyar asiri ba kiristocin kirki ba.

Na biyu akwai matsalar wani bangare na jam'iyyarsu masu akida yan mazan jiya da ake kira yan Tea Party. Shi dai Romney ba shi da akidar yan mazan jiya wanda haka ne ma ya sa shi dauko Paul Ryan a mazaunin mataimaki don ya samu karbuwa a wajen yan tea party.

Amurkawa da yawa na da amannar cewa duk da rashin samun sa'ar fitar da su daga kangin talauci gaba daya, Obama ya fi Romney alamun fahimtar halin da mutane ke ciki da kuma sanin hanyar da zai fito da su. Kai hasalima mutane, musamman masu shirye-shiryen barkwanci a talabijin, na caccakar Romney a kan cewa shi hamshakin mai kudi ne wanda bai san wahala ba tun tashinsa. Haka kuma kamfuna da dama sun mutu a hannunsa. Ga maganar haraji da ake ganin yana kwange wajen biyan abinda ya kamata.

Duk da cewa Romney ya samu dan tagomashi bayan muhawarar da suka yi ta farko da Obama da kuma tabukawar da ake ganin yayi a sauran biyun, duk da cewa Obama ya fi shi kokari, ra'ayuyyka sun fi karkata ga cewa Obama ne zai lashe zaben talata amma da tazara da bata taka kara ta karya ba.

Wani abu da ya karawa  bada karfin gwiwar cewa Obama zai samu nasara shi ne iska mai tafe da ruwa da aka yiwa lakabi da Sany. Obama ya yi amfani da wannan damar wajen shiga cikin talakawa da wadanda masifar ta same su tare da nuna alhininsa. Kai har wani gwamna dan Rifublikan na New Jersey ya jinjinawa Obama a kan irin rawar da ya taka a lokacin wannan masifa.

Zaben kasar Amurka an la'akari da yawan masu kada zabe da kowacce jiha ke da shi ba wai yawan kuri'un da jama'a suka kada ba. Wannan tsari dai ana kiransa da electoral college.

A halin yanzu Obama yana da tabbacin 186 daga cikin 270 da ake bukata kafin mutum ya samu darewa kan kujerar mulki. Haka kuma akwai 57 da bakwai da ake ganin zasu tafi ne ga Obama. Romney na da tabbacin 170 akwai kuma 36 da ake ganin sun karkata ne zuwa gare shi.

Wannan zabe dai ana ganin nasararsa tana hannun wanda ya samu rinjayen wadanda basu gama zartar da wa zasu zaba ba.

Ko ma dai ya faru gobe, ko ma wanene ya ci zaben maufofin Amurka ba zasu taba canjawa ba. Saboda haka ga mu sauran kasashen duniya duk kanwar ja ce.