Monday, February 16, 2015

ZABEN 2015: Tsakanin GMB Da GEJ Ido Ba Mudu Ba . . .


ZABEN 2015: TSAKANIN GMB DA GEJ, IDO BA MUDU BA . . .

Da an gudanar da wannan zabe kamar yadda aka tsara a ranar 14 ga wannan wata da ya gabata, da yanzu haka watakila sakamako ya gama fitowa, al'umma ciki da wajen Najeriya sun san inda alkiblar kasarnan ta dosa. Allah bai nufa za'a gabatar a ranar da 'yan Najeriya suka hakkake ita ce ranar zabe ba, amma duk da haka al'umma suka sake mika wuya ga sabuwar ranar da aka tsara dan aiwatar da wannan muhimmin zabe da zai tabbatar da Najeriya a matsayin jim'huriya ta shida.

Shugaban Kasa Dr. Goodluck Jonathan shi ne mutumin da Najeriya bata tab'a samun shugaba kamarsa ba, nayi tsammanin Gwamnatin Mr. Jonathan tafi kowacce Gwamnati a Najeriya kafa tarihi wajen ciyar da Najeriya gaba da kaso mai yawa, kasancewar shi ne mutum kwaya daya tak da kafin ya zama Shugaban kasa sai da ya zama Mataimakin Gwamna, ya zama Gwamna, ya zama Mataimakin Shugaban Kasa, sannan ya zama Shugaban Kasa. A tarihi ba'a taba samun Shugaban Najeriya da ya ratso wannan rintsi ba. Bisa la'akari da irin wadannan matakai da Mista Jonathan ya ratso ya kamata ace yafi kowanne Shugaba da aka taba yi a Najeriya gogewa da sanin makamar aiki, amma sai dai kash!

Tun bayan da ya kama aiki a matsayin cikakken Shugaban kasa a ranar 5 ga watan Yunin 2010, Mr. Jonathan yayi ta yin tufka da warwara a sha'anin tafiyar da gwamnati, Mr. Jonathan ya aikata sakaci mai yawa a Gwamnatinsa ta yadda ya dabaibaye kansa da mutanan da duniya ta shaida cewa marasa gaskiya ne. Bashakka a Shekarun da Mr. Jontahan ya shafe a matsayin Shugaban Najeriya tun daga 2010 har zuwa yau, ya tabbatarwa da 'yan Najeriya gazawarsa ta fannoni da yawa a al'amuran da suka shafi sha'anin tafiyar da Gwamnati.

Mr. Jonathan bai yi sa'ar samun mutane nagari wadan da zasu bashi shawarar tafiyar da Mulki cikin gaskiya da adalci ba, har ya zamo mutumin da za'a dinga buga misali da shi kamar yadda ake kiran sunan Jerry Rolins a Ghana da Sam Nyioma a Namibia da irinsu Julius Nyarere a Tanzaniya. Shugaban kasa yayi bankaura da hauragiya mai yawa, wadda a matsayin kasa irin Najeriya da take da karfin fada aji a duniya kuma take da buwaya a tsakanin kasashen Afurka ace Shugabanta ya kasance haka ba.

Naji matukar takaici lokacin da naji mutum d'an daba irin Julius Malema tsohon shugaban Matasan jam'iyyar ANC a Afrika ta kudu ya kalli Najeriya ya dinga zagin shugabanta! Amma kuma a gefe guda, Shugabanmu na Najeriya da laifinsa a dukkan irin cin-kashi da wasu daga waje sukaiwa Najeriya, domin ya nuna rashin kwarewa da iya tafiyar da mulki. Zaka yi mamaki a ce General Gowon a Shekaru 31-2 ya iya saita Najeriya tare da kawo karshen yakin basasa.

Duk da wannan kasawa da gazawa ta Shugaban kasa da ta bayyana, ba ga 'yan Najeriya kadai ba; har da sauran kasashen duniya, wannan ba dalili bane da zai sanya al'umma su tozarta Shugaban Najeriya ta hanyar jifansa da yi masa ihu ko kona motocinsa a lokacin da yake yawan kamfe. ko kusa wannan ba daidai bane, a matsayinsa na dan Najeriya doka ta bashi damar ya nemi 'yan Najeriya su zabe shi idan sunga dacewar hakan dan yacigaba da shugabanci. 

Abu mafi muhimmanci da zamu yi amfani da shi dan nunawa Shugaban kasa rashin gamsuwarmu da shi shi ne mu kauracewa zabarsa a wannan zabe, amma tozartashi dan kawai muna adawa da ko dan kasancewarsa ba Musulmi ba, wannan ba daidai bane a matsayinsa na Shugaban kasa.

Haka kuma, GMB da yake zaman dan takarar jam'iyyar hamayya, ba shakka duk mai lafiyayyan hankali da yasan me yake, yasan abin nan da Bahaushe ke cewa ido ba mudu ba amma yasan k'ima. Ko shakka babu idan ka hada GMB da GEJ to shakka babu GMB yafi GEJ cancantar ya zama Shugaban Najeriya nesa ba kusa ba, domin  'yan Najeriya kudu da Arewa sun kyautatawa GMB zaton cewa zai yi fiye da abinda babu wani Shugaba da bai yi ba a baya, al'ummar Najeriya sun gamsu da cewa GMB yana da kishin Najeriya matukar kishi dan haka suke masa fatan zai iya fito da Najeriya daga halin ni 'yasu da take ciki.

A duk da haka wasu na tafka babban kuskure cikin tsukakken tunanin da tsukakkiyar fahimtar cewar GMB ne kadai zai iya ceto Najeriya daga halin da take ciki, duk wanda tunaninsa ya kasance irin wannan to ba shakka ya munanawa Allah zato, sannan ya takaice ni'imar Allah. Akwai dumbin mutane da suke da kishin kasa da watakila zasu iya yin abubuwan da ba'a taba zato ba idan an basu dama.

'Yan Siyasa da suke dauke da katin wata jam'iyya ko sun fada ko basu fada ba, suna fatan jam'iyyarsu ta kafa Shugabanci a kowane irin mataki, abinda ake cewa daga sama har kasa. Sauran al'umma da basa dauke da katin kowacce jam'iyya sune ke bakacewa su fitar da mutanan kirki a kowacce jam'iyya suke domin zabarsu. Abu mafi muhimmanci anan shi ne, shin mun yarda cewar SIYASAR DEMOKARADIYYA HALAL CE? Idan har mun yarda da cewar Demokaradiyya Halal ce a Musulunci, kuma Shiga jam'iyyar Siyasa Halal ne, to babu wani dalili da wasu sabida zafin kai zasu kafirta wani dan ya goyi bayan jam'iyyarsa a kowane irin mataki.

A ganina a siyasance idan d'an siyasa yace yana goyan bayan jam'iyyarsa to yana goyan bayan dukkan 'yan takararta ko da kuwa bai furta hakan ba, indai ya d'auki kansa a matsayin halastaccen d'an wannan jam'iyya. Kuma ko da ya goyi bayan wani dan takarar na jam'iyyarsa da ba Musulmi ba, bana zaton yayi hakan da nufin tarayya da shi a cikin abinda ya shafi Imani na Aqidah ta addini illaiyaka batu na siyasa. Domin kuwa siyasa gaba dayanta Maslaha ce, kowanne d'an siyasa yana duba a ina ne maslaharsa da ta mutanansa zata iya biya cikin sauki sai ya shiga.

Misali akan haka, a baya GMB ya fahimci ba lallai ayi masa adalcin da yake so ba, kuma ya fahimci maslaharsa ba zata iya biya a ANPP ba dan haka ya fice ya koma CPC, haka tsohon Gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau da aka haifi APC da shi, da ya fahimci ba za ai masa adalci ba kuma maslaharsa da ta mutanansa ba zasu biya ba a APC dan haka ya fita ya koma PDP, haka Gwamnonin PDP biyar da suka fice, suma sunga cewar Maslaharsu ba zata iya biya a jam'iyyar ba dan haka suka fice suka koma APC! To wannan yake bamu hotan cewa ita siyasar Demokaradiyya gaba dayanta Maslaha ce, inda mutum yaga zai samu maslaha kuma za ai musu adalci shi da mutanansa, nan zasu share wuri su zauna.

Dan haka duk wanda yayi amfani da addini ya halattawa wasu siyasa, sannan kuma ya haramtawa wasu siyasa to wannan babban Azzalumi ne. Bana zaton kirista da yake goyon bayan APC dan yayi tarayya da Musulmi a aqidah ta Musulunci bane ya sanya shi yin jam'iyyar, haka nan shima Musulmi wanda yake yin PDP bana zaton dan ya yarda da Aqida ta kafurci zai bi abinda ya zaba.

A tunani na duk wani Malami da zai yi maganar halaccin a zabi wata jam'iyya shi ne ya dace da addini, to abinda ya kamata ya fara duba halaccinsa shi ne tushe ko ginshiki wato DEMOKARADIYYA, babu yadda wani zai gamsu cewar tsarin Demokaradiyya ya halatta amma kuma wasu jam'iyyu su Haramta ga wasu mutane, wannan kam ko waye ya fadi haka bai yi Adalci ba.

Nakan yi mamaki matuka, idan naga yadda mutane ke mayar da martani a fusace, kaga sabida siyasa Musulmi na yiwa Musulmi mummunar adduah. Wani Allah ya tashi wane tare da wane, ai na zata a lahira za aiwa kowannemu Hisabi ne gwargwadon aikin da ya aikata ko da kuwa kusa da wa ya tashi, Manzon Allah SAW ya gaya mana cewar babu wani daga cikinmu da ayyukansa zasu iya tsallakar da shi face Rahamar Allah. Ba Shakka Allah Mai Gamammiyar Rahama ne kuma mai jin kai, Rahamar Allah bata takaitu ga wasu kebantattun mutane ba, rahamar Allah ta yalwaci kowa. Ya Allah ka lullubemu da rahamarka, ka siturtamu, ka yafe mana kura kuranmu.

Fatana shi ne Allah ya dubemu ya dubi halin da muke ciki na kaskanci da wulakancci ta yadda a kasarmu wasu suka zama 'yan gudun hijira. Allah ya fitar da mu daga cikin wannan hali, Allah ka azurtamu da samun Shugabanni na gari Adalai wadan da zasu tausaya mana su ji kanmu. Allah kasa ayi wannan zabe lafiya a gama lafiya.

Yasir Ramadan Gwale
16-02-2015

No comments:

Post a Comment