Thursday, December 17, 2015

SHIAH: Nasiha Daga Bakin Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi Na Biyu


SHIAH: NASIHA DAGA BAKIN MAI MARTABA SARKIN KANO MUHAMMADU SUNUSI NA BIYU

A dangane da abinda ya faru a Zaria, Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi Na Biyu yayi Nasiha mai ratsa zukata akan wannan batu. Ya kuma yi kira mai matukar muhimmanci.  Na san da yawan mutanan Kano sun saurara jiya a Freedom Radio. Tun lokacin da akai wannan batarna'ka tsakanin yaran Sayyid Zakzaky da Sojoji na zabi kame baki na kan wannan lamari, domin abu ne da nake gani tsakanin sojoji da masu kunnen k'ashi. Cikin ikon Allah, daya daga cikin abinda yake damuna a Rai sosai game da Shiah da Zakzaky, mai martaba Sarkin Kano ya wanke mun shi.

Ta bakin Sarkin Kano,  Kasar Najeriya an gina Musulunci ne a bisa doron Ahlussunnah Wal Jama'ah. Dan haka duk wanda ya zo da batun darikun sufaye da sauran su, to daga baya ya zo da shi. Haka kuma, kamar yadda Sarkin ya fada, tun farko anyi sakaci, domin, an san Da'awar Zakzaky karya ce ba Musulunci bane, akai shiru aka barshi ya shiga kauyuka ya tara jahilai a matsayin mabiya, har yake neman zamarwa al'umma barazana shi da mabiyansa na kin mutunta dan Adam da kuma dokokinsa hukuma. 

Tabbas akwai laifin Sarakuna wajen yaduwar Shiah a Najeriya, domin sun san tushen Musulunci babu aqidar Zagin sahabbai ko Matan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam, amma sabida ana ganin Ahlussunnah ne ke adawa da abin da kuma kausasa harshe akan koyarwar Shiah, sai ake ganin kamar matsala ce da ta shafi Ahlusunnah ko 'yan Izala Sarakuna sukai kurum Zakzaky na halaka musu al'umma, alhali an san karya yake yi ba Musulunci yake ba.

Alhamdulillah, ya zuwa yanzu Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi ya farga, kuma ya ankarar da 'yan uwansa Sarakuna da Sauran al'umma cewar,  Musulunci a Najeriya an gina shi ne akan koyarwar Ahlussunnah Wal Jama'ah, dan haka an gina mu akan mutunta dangi da iyalan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam da suka hada da Ahlulbaity da Sahabbai da Matansa Sallallahu Alaihi Wa Sallam. Allah ya sakawa Mai Martaba sarki da wannan nasiha mai matukar muhimmanci. 

Kuma wani abin Albashir ga al'ummar Musulmi a Najeriya, shi ne, Wannan Waki'a ta Zaria da ta auku tsakanin Soji da Yaran Zakzaky, tayi Sanadiyar Kawo karshen yadawar  Shiah a Najeriya In sha Allah. Domin filin Husainiya da ake yin kafurci da zagin Sahabbai a cikinsa, asalin sa filin Deport ne na NA wato Chidit Barrack, shi ne Sardauna Sokoto Firimiyan Jihar Arewa Sir Ahamadu Bello ya nemi Turawa su bashi filin dan yana gina filin Polo, kuma a yarjejeniyar da akai da Soji wannan fili ba na sayarwa bane, amma aka samu wata Gwamnati a Kaduna ta maida filin Mallakarta kuma ta baiwa Zakzaky. To Alhamdulillah yanzu haka Buratai ya ce filin Husainiya ya dawo gayaunar sojoji.

Bayan haka kuma, gidan Zakzaky da ke Gyallesu asalinsa shima Gwamnatin Abdussalam Abubakar ce ta gina masa, ta bashi kyauta a matsayin Diyyar abinda Marigayi Gen. Sani Abacha yayi masa, to al'umma dake zaune a Gyallesu sun rubuta dubban sakonnin koke koke akan irin cuzguna musu da Zakzaky da yaransa suke yi, dan haka shima wannan gida Zakzaky ya karya dokar bashi gidan, dan haka sojoji sun kwace shi. A yanzu dai zamu iya cewa Buratai yayi Jana'izar Shiah a duk fadin Najeriya.

Saura da me? Ya kamata al'umma su sani, kuma su fadaka, babu wata akida ta zagin Sahabbai da Iyalan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam a cikin addinin Musulunci. Dan haka kamar yadda mai martaba Sarkin Kano yayi kira dole Sarakuna su tashi tsaye wajen Yaki da duk wanda ya zo dan gurbata addinin Musulunci da aka gina shi akan koyarwar Ahlussunnah Wal Jama'ah a wannan kasa tamu mai Albarka. Ya Allah kasa  wannan shi ne karshen Shiah a Nijeriya. Allah ka taimaki Musulunci da Musulmi ka kaskantar  da Shiah da duk masu goya musu baya na saurari da na b'oye munafukai masu takiyya. 

Yasir Ramadan Gwale 
17-12-2015

1 comment:

  1. To kaddara ce idan tafadawa mutum babu yanda ya iya kokuwa nace sakamako ne Allah yafara nunawa akan masu zagin sahabban manzon sa

    ReplyDelete