Saturday, August 16, 2014

Shari'ar Musulunci A Hannun 'Yan Daba

SHARI'AR MUSULUNCI A HANNUN 'YAN DABA (K'AURAYE)!

Kusan yanzu Allah ya kawo mu wani lokaci da 'yan daba (Kauraye) 'yan ta'adda suke daukan makamai suna Allahu Akbar wai su zasu kafa Shari'ar Musulunci. Wannan al'amari haka yake faruwa a Iraqi da Nigeria da Mali da Somaliya da Yaman da sauran kasashe da dama, wasu tunzurarrun matasa suna dauke da muggan makamai akan motoci wani zubin suna busa taba sigari wai su ne zasu kafa kasar Musulunci su yi Shari'ah.

Sai kayi ta mamaki idan kaga fuskokin mutanen da ke ikirarin su ne zasu kafa Shari'ah a Iraqi ko Najeriya ko Mali, ba su da wata kamala da ta ke nuna su din suna da ilimin addinin da zasu jagoranci al'ummah har su tsaida musu da Shari'ah. Ta inda zaka fahimci dukkan wadannan masu wannan ikirari tantagaryar makaryata ne, shi ne wane Musulunci suke bi da ya yi umarni da kisan mutanan da basusan hawa ba balle sauka? mutane suna zaman zamansu azo a tayar musu da abubuwan fashewa wasu su mutu wasu namansu yai daidai, wasu su karairaye haka kurum, kuma wadannan tsagerun su dinga ikirarin wai Shari'ar Musulunci suke son tabbatarwa!

Ya zama wajibi jama'a su fadaka su san cewar, wadannan mutane da suke dauke da bakaken tutoci da rubutun La Ila Ha Ilallah, karya suke yi ba Musulunci suke ba, kuma babu abinda ya hada su da kafa Shari'ar Islama. Sau da dama ana yaudarar mutane musamman masu kishin addini har su dinga kallon irin wadannan matasa amatsayin masu kishin addini ko Jihadi, wanda a zahiri manufofinsu sunci karo da na Musulunci.

Tayaya mutanan da basu da wani Ilimin Addini basu ma san addinin ba, basu da wani iko na shugabanci, ba malamai ba, tantagaryar jahilai su dauki makamai suna Allahu Akbar wai zasu yi Shari'ah har mutane su dinga ganinsu a matsayin masu kare addini, a fahimtata dukkansu ba gaskiya ba ne a cikin al'amarinsu, kungiyoyi irinsu Al-Qa'ida da Al-Shabab da Tuareg da ISIS da Boko Haram da sauran irinsu, dukkansu babu wani alkhairi da sukajawowa Musulunci illa bakin suna a wajen wadan da ba Musulmi ba. Hanyarsu daban, ta Musulunci daban, domin dukkansu sunfi kama da 'yan daba ko kauraye akan ka kirasu da masu Jihadi ko kishin Musulunci, siffofinsu da ayyukansu sunfi kama da na Khawarij. 

Babu shakka batattu ne, suna kan bata da tabewa mai girma, idan har da gaske Musulunci suke kishi dole su koma makaranta su koyi ilimin addinin su sanshi a wajen Malamai na gari masu tsoron Allah. Addinin Musulunci ba addini ba ne na tashin hankali ko jefa rayuwar mutane cikin garari. Kuma ta ina mutumin da ba shugaba ba zai tsayar da Shari'ah akan mutane?

Inda zaka fahimci wadannan 'yan daba bakinsu daya duk inda suke, shi ne ka duba irin Tutar Al-Qa'ida ita Boko Haram a Najeriya da ISIS a Iraqi da Alshabab a Somaliya da mutanen Mali suke amfani da ita. Ko kusa wadannan mutane ba suda alaka da Musulunci ko ta kusa ko ta nesa da irin abinda suke yi na kisan gilla ga al'umma. Ta yaya zasu dinga kashe mutanan da suke son tabbatarwa da Shari'ah, misalia Najeriya Boko Haram na ikirarin aiwatar da Shari'ar Musulunci amma kuma zasu dinga kashe Musulmai? Shin haka Musulunci ya fada daman ko kuwa nasu addinin ne ya yiumarni da zubarda jinin bayin Allah? 

Wadannan mutane Allah ya sansu kuma yasan nufinsu ba na alheri ba ne, Ya Allah ka tsaremu daga sharrin wadannan 'yan daba 'yan ta'adda marasa tsoron azabarka. Allah ka taimaki Musulmi na hakika ba masu batasunan Musulunci ba.

YASIR RAMADAN GWALE
15-08-2014

No comments:

Post a Comment