Saturday, August 9, 2014

Ebola


EBOLA: Ance sunan Ebola asali ya samo wannan sunan ne daga wani kududdufi mai dauda cike da dagwalo a kasar kwango. Wannan cuta da bincike ya tabbatar da cewa mutanen farko da suka kamu da ita, sun sameta ne sakamakon cin naman dajin da akayi farautarsa irin su Beran dinka da Damo da gafiyoyi da jemage da sauran dangin haiwanat irin wadannan. Haka kuma likitoci sun tabbatar da cewa wanna cuta na da saurin yaduwa da kuma halaka jama'a nan take.

Wannan cuta ta bulla ne a karon farko a shekarar 1976 a kasar Sudan ta kaudu ta yanzu, a wancan lokacin kusan mutum 284 suka rasu sakamakon kamuwa da wannan cuta. Sannan a karo na biyu wannan cuta ta kuma bulla a kauyen Yambuku a Zaire kasar Kwango inda mutane kusan 318 suka harbu da ita, da damansu suka margaya sakamakon wanan cuta.

Karona hudu da wannan cuta ta bulla, ita ce a jihar Virginia ta kasar Amurka, wanda bayanai suka nuna cewa ta bulla ne a sakamakon cin namu wasu birre da aka shiga da su garin daga yankin nan mai fama da yamutsi na Mindanao a kasar Filifins a cikin shekarar 1989. Wanda mutane kalilan ne suka harbu da wannan cuta.

Haka kuma, karo na karshe da aka ji labarin bullar wannan cuta shi ne lokacin da wata Likitiya a kasar Kwadebuwa take duba lafiyar wani biri, bayanai sun tabbatar da cewar birin da Likitiyar ta duba yana dauke da cutar, nan ta ke kuma matar ta harbu da cutar a cikin shekarar 1994.

Daga nan kuma sai a ranar 6 ga watan Augutan wannan shekarar aka samu labarin bullar wannan cuta a kasashen Gini da Laberiya da Saliyo, ance cutar ta sake bulla ne sakamakon cin naman dabbobin da aka yi farautarsu a wadannan kasashe. Tuni dai wannan cuta ta aika da sama da mutu 700 lahira a dalilin harbuwa da suka yi da ita.

Bayanai na likitoci sun tabbatar da cewa wannan cuta na da saurin yaduwa da kuma saurin halaka mutane kamar yadda kullum ake bayani a Talabijin da Radiyo da jaridu. Haka kuma, wasu bayanai sun nuna cewar bayaga cin naman dabbobin da aka ambata ko yin cudanya da mai cutar, ana kuma iya harbuwa da ita ta sanadiyar cin 'ya 'yan itatuwan da Birbiri ya fara gatsa su a bishiyarsu.

Kamar yadda dukkanmu muka sani, tuni wannan cuta ta bulla a Najeriya, kuma ana ta daukan matakan kariya tare da kira ga jama'a da su tabbatar da tsaftar abincinsu da abin shansu da kuma gurin kwanansu. Haka kuma bin ka'idojin da hukumomin lafiya suka gindaya zasu zama garkuwa ga wannan annoba. Wadan da suka kamu da wannan cuta Allah ya basu lafiya, wadan da kuma suka mutu Allah ya jikansu, mu kuma Allah ya karemu da karewarsa.

DISCLAIMER: A cikin hadisi na 625 a cikin Sahihul Bukhari, Manzon Allah SAW ya ce idan annoba ta barke, kada wani da yake dauke da wannan cuta ya fita zuwa garin da basu da ita, kada kuma wanda yake zaune a inda annobar ta barke ya fita daga inda yake dan gudun kamuwa da ita. Riko tare dayin amfani da bayanan kariya da likitoci suka bayar zasu tairigakafin wannan cuta. Kuma jama'a su yawaita rokon Allah akan neman tsari daga wannan annoba.

YASIR RAMADAN GWALE
09-08-2014

No comments:

Post a Comment