Sunday, August 17, 2014

Malam Nuhu Ribadu!

Nuhu Ribadu yana gaisawa da Atiku Abubakar
MALAM NUHU RIBADU: Sunan Malam Nuhu Ribadu ya fara bayyana ne ga mafiya yawancin al'ummar Najeriya a lokacin da ya jagoranci hukumar EFCC mai yaki da zamba da almundahana ga dukiyar kasa. Malam Nuhu Ribadu yayi aiki bil-hakki da gaskiya wajen dawo da martabar sunan Najeriya da ya zube a idon duniya, wajen ganin ba'a cigaba da kwasar dukiyar talakawa ba. Ribadu yayi aikin da babu wani mahaluki da yayi a lokacinsa, ya kama tare da tuhumar mutanan da ake zarginsu da azurta kansu da dukiyar Haram, ya dawowa da gwamnati da dumbin dukiyar da aka diba ba bisa ka'ida ba.

A saboda aiki tsakani da Allah babu sani babu sabo da Malam Nuhu Ribadu yayi a lokacin da yake shugabantar EFCC ya sanya Transparency International suka fara mutunta sunan Najeriya a fannin yaki da cin-hanci da rashawa. Mutane a ciki da wajen Najeriya sun yabawa Malam Nuhu Ribadu a bisa irin yadda ya rike gaskiya a aikinsa duk da barazanar da aka dinga yi masa da bashi toshiyar baki amma ya kekasa kasa.

A dalilin kwazonsa da jajircewarsa ta sanya Majalisar dinkin duniya ta daukeshi aikin binciken badakalar rubda-ciki da dukiyar al'umma dake zargi a kasar Afghanistan, ya kuma nuna hazaka a lokacin da yayi aikin. Daga nan likkafar Malam Riabdu ta dinga cigaba, har ta kai ga rusashshiyar jam'iyyar ACN ta Yarabawa suka nemeshi da ya zo yayi takarar Shugaban kasa a karkashin jam'iyyar dan samar da sabuwar Najeriya.
Duba da kwarewa da gogewa irin ta Malam Nuhu Ribadu ya sanya gwamnatin Shugaban kasa Goodluck Jonathan ta nada shi a matsayin wanda zai shugabanci kwamitin Petroleum Revenue Special Task Force dan sanya ido da bayar da shaida akan kudin rarar Man-fetur, ya kuma kammala aikinsa cikin nasara, yayin da al'ummar kasarnan suka yabawa Rahaton Kwamitinsa.

A 'yan makwannin da suka wuce, Malam Nuhu Ribadu ya samu kansa a cikin wani yanayi da za'a iya cewa Allah ne ya nunawa al'umma gaskiyarsa, inda jam'iyyun APC da PDP suka dinga zawarcinsa akan yayiwa Allah ya yi musu takarar Gwamnan jihar Adamawa a zaben cike gurbin da za'ayi nan gaba a Oktoba mai zuwa. Kungiyoyin matasa da yawa daga jihar Adamawa suka dinga kira ga Malam Nuhu Ribadu da ya yi musu takarar Gwamnan jihar karkashin jam'iyyar PDP duk kuwa da cewar shi yana jam'iyyar APC mai hamayya.

A dalilin wannan kiraye-kiraye ne Malam Nuhu Ribadu a jiya ya yanke hukunci na karshe, inda ya amince da shiga jam'iyyar PDP domin bayar da tasa gudunmawar kamar yadda ya saba dan samar da sabuwar Najeriya mai mutunci da kima. Ana sa ran cewa Malam Nuhu Ribadu zai zama dan-takarar Gwamna na PDP a Adamawa. Na yi imanin cewar Malam Nuhu Ribadu zai iya yin dukkan aikin da aka bashi dan hidimtawa al'umma tsakaninsa da Allah. Kamar yadda ya sha nanatawa cewar a shirye yake ya taimakawa kasarsa a kowanne irin mataki idan ambukace shi.

Muna yi masa fatan alheri. Ina kuma amfani da wannan damar na yi kira a gareshi da ya kasance mutum mai gaskiya da rikon Amana kamar yadda aka sanshi, kuma yaji tsoron Allah wajen alkinta dukiyar al'umma a duk inda ya samu aikin hidimtawa al'umma. Allah ya taimaki Najeriya ya bamu Shugabanni na gari Adalai masu rikon Amana. 

Yasir Ramadan Gwale
17-08-2014

No comments:

Post a Comment