Tuesday, August 5, 2014

ADAMAWA: Mallam Nuhu Ribadu Ne Zai Zama Dan Takarar Gwamnan PDP


ADAMAWA: MALAM NUHU RIBADU ZAI ZAMA DAN TAKARAR GWAMNAN PDP

Jaridar TheCable ta jiya Asabar ta ruwaito wani labari da yake cewa tsohon shugaban hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa Mallam Nuhu Ribadu na samun matsin lamba akan ya tsaya takarar zaben Gwamnan jihar Adamawa da za'a yi mai zuwa. Majiyar jaridar ta ce, Ribadun na samun kiraye-kirayen tsayawa takarar, tuni kuma jam'iyar PDP ta kuduri aniyar baiwa Malam Nuhu Ribadu tikitin tsayawa takara a doran jam'iyyar.

Haka kuma, wata majiya a cikin jam'iyyar PDP ta tabbatar da cewar, tana da kwarin guiwar cewa Malam Nuhu Ribadu zai amsa wannan kira na tsallakawa PDP daga APC dan ya cike gurbin kujerar Gwamnan jihar da aka tsige Murtala Nyako, zaben dai ana sa ran guddanar da shi a watan Oktoba mai zuwa nan gaba a wannan shekarar. Haka suma a nasu bangaren wata kungiya da ake kira Adamawa Concerned Youths for Good Governance suna ta jaddada kira ga Malam Nuhu Ribadu da ya amsa wannan kiran.

Wasu masharhanta na ganin idan Malam Nuhu Ribadu ya tsallaka zuwa PDP kuma ya zama dan takarar Gwamna a jihar Adamawa babu shakka zai doke dukkan wanda APC zata tsayar duba da gaskiya da rikon Amana ina na Ribadun. Haka kuma, da dama na ganin fitar Malam Nuhu Ribadu daga APC zai zama wani babban koma baya ga jam'iyyar.

Sai dai a nasa bangaren Malam Nuhu Ribadu har ya zuwa yanzu bai ce komai ba dangane da wadannan kiraye-kirayen da ake yi masa na tsayawa takara, da kuma damar da PDP zata bashi idan ya shigo Jam'iyyar.

Yasir Ramadan Gwale
03-08-2014

No comments:

Post a Comment