Thursday, August 28, 2014

JIGAWA TARIN ALLAH: Fatan ALheri Ga Jigawa A Shekaru 23


JIGAWA TARIN ALLAH: FATAN ALHERI GA JIGAWA A SHEKARU 23

Zanyi amfani da wannan damar wajen taya 'yan uwanmu al'ummar jihar Jigawa murnar cika shekaru 23 da samun jiha. Ba shakka duk wani abin farin ciki da ya samu Jigawa to ya samu Kano, a shekaru 23 da Jigawa ta shafe a matsayin jiha mai cin-gashin kanta, anyi abubuwa masu yawa dan inganta rayuwar al'ummar wannan jihar, haka kuma Gwamnoni da dama sun gabata tun daga na soja har zuwa na farar Hula da suka Shugabanci al'ummar Jihar Jigawa.

Amma a bisa bayanai da abubuwa na zahiri da muka gani, jihar Jigawa bata samu cigaba ba kamar wannan lokacin da Gwamna Sule Lamido ke jan ragamar al'ummar jihar. An samu sauye-sauye masu yawa a Biranen jihar Jigawa da kauyukanta kamar yadda bayanai suke nunawa. 

Kusan tun shekarar 2009 rabona da Dutse babban birnin jihar Jigawa. Ban san yadda Dutse ta zama ba a yanzu, amma a irin bayanan da nake samu shi ne cewar an samu sauye-sauye masu yawa kwarai da gaske a ciki da wajen Dutse, anyi gine-gine na kece raini da gina manya da kananan hanyoyi da kuma gina katafaren filin sauka da tashin Jiragen Sama da sauran ayyukan cigaba.

Bayanai musamman wadan da muke samu daga wajen Malam Mansur Ahmed da kuma irin hotunan da muke gani sun nuna cewar Gwamna Sule Lamido ya ciri tuta wajen sanya Jigawa ta amsa sunanta na sabuwar Duniya. Muna taya al'ummar Jigawa murnar samun wannan cigaba mai ma'ana. 

Haka kuma, a wasu bayanai da muka karanta a kwanakin baya sun nuna cewar Jigawa na daya daga cikin jihar da ta ke da dumbin mutanen da ba su da aikin yi a Arewacin Najeriya, kuma talauci na karuwa sosai a jihar. Anan ne nake son yin Amfani da wannan damar wajen yin kira ga Gwamna Sule Lamido wanda mun san hadimin Talawa ne, ya kara zage dantse wajen taimakawa rayuwar talakawa da kuma inganta ayyukan Noma da kiwo a Jigawa da sauran fannonin da suka shafi rayuwar al'umma kai-tsaye.

Ina kuma kira da babbar Murya ga al'ummar Jihar Jigawa musamman Talakawa su sani cewar Gwamnati ba tada aikin da zata iya baiwa kowa, kuma Gwamnati ba zata iya biyan bukatun kowa ba, a dan haka dole al'umma su tashi tsaye haikan wajen ciyar da kansu gaba da kuma jiharsu. Muna musu fatan alheri, Allah ya taimaki Jihar Jigawa Ameen.

Wani abokina Malam Abdul Ahmad Burra ya fada a cikin rubutunsa cewar babban rashin da mutanan Jigawa zasu yi a 2015 shi ne na Gwamna Sule Lamido Hadimin Talakawa, muna yiwa Gwamna Lamido fatan Allah ya sa ya gama mulkinsa lafiya, kuma Allah ya baiwa 'yan Jigawa wanda yafi Gwamna Sule Lamido a 2015.

Yasir Ramadan Gwale
28-08-2014

No comments:

Post a Comment