Thursday, April 30, 2015

LEGAS: Fiye Da Shanu 6000 Ake Yankawa A Kowacce Rana


LEGAS: KIMANIN SHANU DUBU 6000 AKE YANKAWA A KULLUM 

Fiye da shanu dubu shida ake yanka wa a Birnin iko kowacce rana. Da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, kwamashinan aikin gona na jihar Legas Mista Gbolahan Lawan ne ya bayyana haka. Lawan ya ce a mayankar Oko-oba dake cikin birnin iko kadai ana yanka shanu kimanin dubu biyu (2000) a kowacce safiyar Allah, ya kara da cewar sauran dubu hudu kuma ana yankawa a sauran sassan jihar ta Legas a kananan mayanku. 

Wannan labari jarida Leadership Newspapers ce ta ruwaito shi, kuma ya ja hankali na sosai da gaske. Wannan kuma na kara nuna yadda noma da kiwo ke da matukar muhimmanci a wajen habaka tattalin arzikin Arewa. Misali idan a Legas za'a yanka saniya dubu shida, idan kowacce saniya ana sayanta akan kudi Naira 100,000 kenan kowacce rana ana sayar da shanu na kimanin Naira Miliyan dari shida  (600,000,000), wannan ya nuna a wata daya kadai ana sayar da shanu na kimanin Naira Biliyan Goma sha takwas (18,000,0000,000). Tab!

Wannan fa a Legas ne kadai, ina ga sauran jihohin Nigeria 35 da Abuja, shanu nawa ake yankawa a kowacce rana? Ba shakka wannan babban dalili ne da ke nuna cewar idan mutanan Arewa suka rike harkar noma da kiwo da gaskiya da adalci zamu cigaba da Jan ragamar Najeriya shekaru masu yawa nan gaba. Domin Man fetur din da ake ta yi mana gori da shi dai kullum sabbin kasashen duniya ne ke kara gano shi, sannan darajar sa na dirga kasa sosai.

Sannan kuma,  wannan fa maganar nama kawai ake, ina kuma ga idan an zo batun Madara da sauran amfani da ake samu a jikin shanu? Lallai wannan labari ya tsumani domin nan gaba kadan nima zan zama manomi dan zan fara sayo saniya da dan maraki na turke nima. Sannan zan je wajen Dr. Aliyu U. Tilde in sha Allah har Tilde domin samun horo na musamman akan kiwon shanu a zamanan ce. 

Dr. Aliyu U. Tilde ashe dai kun jima kuna more arziki bamu sani ba. Ba shakka akwai sirri ma yawa na samun arziki a kiwo amma mutane sun tare a birane amma arziki na cikin daji. Lallai masu sana'ar kiwo su mutunta ta sosai dan samun riba mai yawa. Idan ba haka ba suna ji suna gani 'yan Boko zasu yi babakere su tare aikin Gwamnati sannan su diary a noma da kawo a zamanance dan samun arziki mai yawa.

Yasir Ramadan Gwale 
30-04-2015

No comments:

Post a Comment