Thursday, April 2, 2015

KANO: Tsakanin Mutanan Shekarau Da Na Kwankwasiyya


KANO: DANGANE DA BATUN TAKARAR GWAMNA, TSAKANINMU DA 'YAN KONKOSIA 

Mutane irinsu Jaafar Jaafar​ da Auwal Lawan Aranposu​ da Ibrahim Musa da Fatuhu Mustapha​ da sauransu da dama idan muka yi addu'ah cewa Allah Ya Bawa Takai Nasarar zama Gwamnan Jihar Kano dariya suke yi suna ganin, babu yadda za ai Gwamnatin Kano ta subuce  daga hannun su.  Kamar yadda wasu daga cikin 'yan uwanmu a PDP ke ganin mulki ba zai taba kwace musu ba. Amma mu a ko da yaushe fatan alheri muke yiwa Kano da al'ummarta, akan wanda zai zama Gwamna na gaba bayan Rabi'u Musa Kwankwaso.

Muna tabbatar wa da 'yan uwanmu na Konkosia cewa, Allah ne ya shimfid'a ka'Ida yace ku rokeni zan amsa muku, dan haka ne a kullum muke rokon Allah akan wannan takarar Gwamna. Bamu yi girman kai ko dagawa ko ji da isa ba, Allah muka roka sannan muka roki mutanan Kano da su baiwa Malam Salihu Sagir Takai dama a wannan zaben dan zama sabon Gwamnan Kano.

Muna cike da sanin cewar mulki na Allah ne, yana bayar da shi ga wanda ya so,  a duk lokacin da ya so, kamar yadda tarihi ya nuna a 2003 a Kano, da kuma zaben da ya baiwa Buhari Nasara.  Sau da yawa wasu kan zata cewar idan Allah ya basu mulki su shi kenan, wallahi mulki jarabawa ce mai wahalarci, wasu mulki halaka ne a garesu, wasu kuma Rahama ne, amma sabida yadda Sunnar take dole a samarwa da al'umma jagoranci ta irin wannan hanya shi yasa muma muke neman a zabi Takai.

Har kullum addu'ar mu ita ce, idan Takai shi ne mafi alherin zama Gwamnan Kano a wannan zabe Allah ya bashi, ya yi masa jagoranci, ya bude masa kofofin alheri, idan kuma Gandujiyya ne zai Fi zamarwa Kano alheri shima addu'ar mu Allah ya bashi, yayi masa jagora.  Kuma idan har da gaske 'yan uwanmu na Konkosia Kano ce da al'umma a gaban su suma yiwa Jihar Kano wannan adduar tsakanin Takai da Ganduje. 

Wannan ce ma ta sanya a kullum muke Jan hankalin mutanenmu cewar bamu yarda a muzanta Ganduje dan a tallata Takai ba, Ganduje a matsayin sa na mataimakin Gwamnan Kano shugaba ne, ya cancanci a bashi dukkan girmama a matsayin sa na shugaba. Amma abin mamaki su 'yan uwanmu na Konkosia sun mayar da hanyar muzanta Takai a matsayin hanyar tallata dan takarar su. 

Ya kamata 'yan uwanmu na Konkosia su sani cewar an wuce wannan lokacin na batanci dan tallata kai, ya kamata su shagaltu da bayyanawa al'ummar Kano irin kudurorinsu idan Allah ya basu mulki. Dan haka mu a wajen Allah muke nemawa Malam Salihu Sagir Takai Gwamnan Kano, idan jama'ar Kano sun gamsu da mu sun zabi Takai ina tabbatar musu ba zamu basu kunya ba, idan kuma sun zabi Ganduje In sha Allah zamu yi masa cikakkiyar biyayya a matsayin sa na Shugaba.

Muna kara yin addu'ar da muka saba Ya Allah idan Takai shi ne zai Fi zamarwa Kano alheri a wannan zabe Ya Allah ka tabbatar masa da kujerar Gwamnan Kano, idan kuma Ganduje ne zai Fi zama alheri Allah ka bashi. Duk da haka muke cewa Allah Ka Baiwa Malam Salihu Sagir Takai Gwamnan Kano.

Yasir Ramadan Gwale 
02-04-2015 

No comments:

Post a Comment