Tuesday, April 28, 2015

Kwankwaso Na Yiwa 2019 Tanadi Na Musamman


KWANKWASO NA YIWA 2019 TANADI NA MUSAMMAN 

Muhammadu Buhari, Ibrahim Badamasi Babangida​, Abdul salami Abubakar,  Yakubu Gawon, Olushegun Obasanjo, Ernest Shonekan, TY Danjuma, Justice Dahiru Musdapha, Jibril Aminu, Tony Momoh da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu​ duk Gwamnan Kano Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso​ ya gayyato su Kano dan bude ayyukan da Gwamnatin sa ta yi a wannan lokaci. Duk me nazari da tsinkaye ya san cewar wannan ba komai bane illa wani shiri mai karfi da Kwankwaso yake yi dan tunkarar takarar Shugaban kasa a 2019.

Bahaushe yace mai kwarmin ido da wuri yake fara hawaye, Gwamna Kwankwaso dan siyasa ne, yasanta kuma ya san lagonta dan haka yake kafa wa siyasar 2019 wani ginshiki mai karfin gaske, ta hanyar katange kansa da manyan duwatsu, wadan nan sune who is who a siyasar Najeriya. Idan Kwankwaso yayi sa'ar samun cikakken loyalty nasu to zai yi barazana ga duk wani dan siyasa a 2019.

Zaben fidda gwani na APC da akai Kwankwaso yazo na biyu, wannan ya kara masa kwarin guiwar cewar, lallai zai bada ruwa anan gaba, domin 'old tamers' irinsu Atiku Abubakar tuni Kwankwaso yaga tsiraicin siyasarsu ta hanyar rashin wata structure me karfi ta samun Nasarar zabe.

Bugu da kari, Kwankwaso ya fahimci mafi yawancin 'yan Najeriya  mutane ne da ake iya cinsu da buguzum, wannan ta sanya shi cikin lokaci kankani ya samar da makaranta domin 'yan gudun hijira na Borno a Kano, wanda wannan aiki tsagwaron siyasa ne, domin Miliyoyin 'ya 'yan talakawa suna nan a Kano basu ci wannan gajiya ba.

A ganina a 2019 idan Allah ya kaimu, ya kamata a ce dan takarar Shugaban kasa a dukkan jam'iyyun APC da PDP ya kamata ya fito daga shiyyar Arewa Maso Gabas, domin hakan shi ne zai nuna Adalci, kuma wannan zai nuna cewar mu mutanan Arewa Maso Yamma ba mu yi babakere a shugabancin Najeriya ba, domin wannan yanki namu ya samar da Murtala Mohammed, Shehu Shagari, Muhammadu Buhari​, Sani Abacha, Umaru YarAdua da kuma Muhammadu Buhari​ a karo na biyu a matsayin Shugabanin kasa; su kuma Arewa Ta Tsakiya suka samar da Yakubu Gawon, IBB da kuma Abdul Salami Abubakar; A yayin da Arewa Maso Gabas basu da kowa in banda Sir Abubakar Tafawa Balewa​.

Ina gani indai ana son Arewa ta zama curarriya kwaya daya, to ya kamata shiyyar Arewa Maso Gabas a taimaka musu wajen samar da Shugaban Najeriya bayan shudewar Gwamnati Muhammadu Buhari, hakan shi ne zai zaunar da mu lafiya ba tare da wasu na ganin an kwaresu ba, mu kuma ba'a kallemu amatsayin masu babakere da nuna mu kadai ne Arewa ba. Wannan zai bayu ne kadai, idan mutanan Arewa Maso Gabas sun yunkura wajen ganin suma an dama da su a tsarin siyasar Najeriya.

Amma idan ba haka ba, sai an kwashe fiye da Shekaru 20 mutanan Arewa Maso Gabas basu d'ana Shugabancin Najeriya ba. Domin bayan Buhari ya kammala wa'adin Shekaru hudu kamar yadda ake zato, to Kwankwaso zai zo yayi Shekaru takwas sannan ya mika wa Yarbawa suma su shekara takwas sannan ne watakila mulki zai juyo Arewa kana kuma ayi tunanin Arewa Maso Gabas watakila. Amma duk da haka da arziki a garin wasu gwara a naku inji masu iya magana.

Yasir Ramadan Gwale 
28-04-2015

No comments:

Post a Comment