Tuesday, April 28, 2015

KANO: Rugujewa Tskanin Gada Mai Doron Zabuwa Da Mai Ramin Kurege


KANO: RUGUJEWA TSAKANIN GADA MAI DORON ZABUWA DA MAI RAMIN KUREGE

A ranar 23 ga watan Maris din da ya gabata, sa'o'i saba'in da biyu, bayan da Shugaban kasa Dr. Goodluck Jonathan ya kaddamar da bude sabuwar Gadar da Sanatan Kano ta Tsakiya Bashir Garba Lado ya samar a cikin birnin Kano da aka sanyawa sunan Sarkin Kano mai rasuwa Alhaji Ado Bayero, aka samu labaran da suke nuna cewar anga wata tsaga a kan gadar. Wannan ya haifar da tururwar jama'a domin ganewa idonsu wannan lamari. Cike da murna da jin dadi masu hamayya da Takarar Sanatan Lado suka dinga yada hotunan wannan gada, ana yarfa masa magana; Ciki kuwa harda Shugaban Gwamnatin Kano, ance ya nuna murnarsa akan abinda ya samu gadar.

Daga bisani, bayanai suka tabbatar da cewar wannan tsaga ta kan gadar, ba ta rashin lafiya bace, ko samun matsala, illah kamfanin da yayi aikin ya tsara wannan tsaga dan sanya wasu alamau. Allah masani. Abinda ya tabbatar da cewar Gadar da masu hamayya da Lado ke kira da Mai Doron Zabuwa ba tsagewa tayi ba, shi ne cigaba da amfani da ita da aka dinga yi har kawo yau, wannan ya kara tabbatar da cewar gadar lafiya lau take.

Sai gashi kimanin wata guda bayan wancan yarfe da akaiwa Gadar Mai Martaba Sarki mai rasuwa, wata gada da aka samar a unguwar Dorayi cikin karamar hukumar Gwale mai kama da Ramin Kurege, ta rufto akan motar wani dan kabu-kabu da akai imani yana dauke da mutum hudu har da shi na biyar. Dukkan mutanan da ke cikin motar Allah ya yi masu rasuwa. Muna adduar Allah ya jikansu ya gafarta musu ya kyauta bayansu. Allah kuma ya kare aukuwar hakan anan gaba.



Har ila yau, kasa da awanni 24 bayan wannan hadari, gadar dake dorayin ta kuma subucewa ta zaftaro kasa, wannan karo Allah ya takaita domin akan Adaidaita Sahu ta fado, babu rahotannin asarar Rai. Allah ya kare mu daga sake samun aukuwar irin wannan hadari a nan gaba.

Ba shakka, a baya, abinda Gwamnan Kano da masu goyon bayansa sukai na terere da gadar lado da nuna farin ciki akan samun matsalar da gadar tayi a cewarsu, basu kyauta ba. Domin kuwa wannan gada anyi ta ne domin amfanin al'umma, watakila Lado sai ya shekara bai bi ta kan gadar ba, amma al'umma na amfani da ita kullum ranar Allah. Lallai jama'a suji tsoron Allah, su sani ba muda wani gari ko jiha da ta wuce Kano, duk wani abu na cigaba domin amfanin al'umma bai kamata ya zama an siyasantar da shi har ya zama abin zolaya ba.

Wannan hadari kuma da ya faru akan gadar dorayi, muna kira da babbar murya ga Gwamnatin Kano, bayan an biya diyyar wadan da suka rasu kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar, kuma lallai ne a yi bincike na gaskiya domin gano musabbabin wannan hadari, domin kaucewa fadawa irinsa anan gaba. Sannan duk wadan da suke da sakaci a wajen wannan rugujewar matukar akwai sakacin to a hukuntasu daidai da abinda suka aikata.

A koda yaushe ana son Musulmi ya kasance mu yawaita fatan alheri garemu ga al'ummarmu da kasarmu. Ba daidai bane, dan wata masifa karama ko babba ta samu wasu abin ya zama abin dariya ko zunde ko zolaya ko a maida abin siyasa ba. Allah ya kara kiyayewa.

Yasir Ramadan Gwale
27-10-2015

No comments:

Post a Comment