Wednesday, April 29, 2015

SA'UDIYYA: Sarki Salman Ya Samar Da Canji Mai Ma'ana


SA'UDIYYA: SARKI SALMAN YA SAMAR DA CANJI MAI MA'ANA

Sabon Sarkin Sa'udiyya  Salman Bin Abdulaziz Alsaud an wayi gari da sabon sauyin da ya kawo a majalisar Masarautar kasar da ta kunshi Ministoci da manyan jami'an Gwamnati, wannan shi ne karon Farko da Sarki Salman ya samar da wannan sauyi tun bayan da ya zama sabon sarki a 23 ga watan Janairun wannan shekara bayan rasuwar  King Abdullah bin Abdulaziz Al Saud.

Mutum na karshe da ake sa ran shi ne zai zama Sarki daga cikin 'ya 'yan Abdulaziz Ibn Abdulrahaman Alsaud wanda shi ne ya kafa kasar sa'udiyya, wato Yarima Muqreen, wanda ya zama sabon Yarima mai jiran Gado bayan da Salman ya haye kan karagar mulki. Sai dai kuma a yau an wayi gari inda sabon Sarki Salman ya bayyana sauke Yarima Muqreen aka maye gurbinsa da Mohammad Bin Nayef a matsayin sabon Yarima, rahotanni sun tabbatar da cewYarima Muqreen ya amince zai sauka daga mukaminsa, kamar yadda Mohammad Vall na gidan talabijin na Aljazzerah ya ruwaito daga Sa'udiyya.

Sarki Salman yayi sauyin da ya dace, domin kuwa, Mutumin da aka nada sabon Yarima mai jiran gado Muhammad Bin Nayef ya gaji mahaifinsa ne wanda daya ne daga cikin 'ya 'yan Sarki Abdulaziz, Nayef shi ne Yarima mai jiran gado lokacin marigayi Abdallah na kan sarauta, Allah ya yi masa rasuwa kafin Abdallah. Sauyin da Sarki Salman yayi, ya nuna cewar bayan shudewar 'ya 'yan Sarki Abdulaziz to sarauta zata faro ne daga jikokinsa, daga kuma gidan marigayi Nayef wanda yana daga cikin wanda zai zama Sarki mutuwa ta yi masa yankan hanzari. 

Haka kuma, Sarki Salman ya sauke ministan harkokin wajen Yarima Saud Al-Faisal daga mukaminsa, wanda Jikan Sarki Abdaziz d'a ga Sarki Faisal mutum na farko da ya zama Sarki bayan rasuwar Abdulaziz a Daular Sa'udiyya. Yarima Saud Al-Faisal ance da kansa ya amince ya sauka bayan da ya jima yana fama da rashin lafiya wadda ta kai har baya iya tafiya da kafafunsa sai da sanduna guda biyu, amma yana cigaba da rike da mukamin ministan harkokin waje, mukami mai daraja ta farko bayan Yarima da mataimakinsa. Sabon Ministan Harkokin waje Yarima Muhammad Bin Salman babban dan Sarki Salman ne, masharhanta na ganin nadinsa ya dace kasancewarsa Matashi dan shekaru hamsin a cewar Riyad Khshta wani mai sharhi akan gabas ta tsakiya.

Sannan kuma a karo na farko an nada Adel al-Jubeir Jakadan Sa'udiyya a birnin Warshinton  wani wanda ba dan cikin masarautar ba a matsayin sabon ministan tsaro, mukamin da sabon Yaima Muhammad Bin Nayef yake rike da shi kafin a nada shi wannan sabon mukamin.

Yanzu dai masu sharhi akan kasashen gabas ta tsakiya na ganin Sarautar Saudiyya zata koma hannun matasa kuma wadan da suka yi karatun boko mai zurfi. Inda sabon Yarima MUhammad Bin Nayef dan shekaru 55 yake da kwarewa ta musamman akan harkar tsaro, yayin da mataimakinsa Muhammab Bin Salman matashi dan shekara 50 yake da gogewa wajen muamalar da ta shafi harkokin cikin gida. Allah ya taimaki wadannan shugabanni ya basu ikon sauke nauyin da ke kansu, ya kuma basu ikon yiwa Masallatan Allah masu alfarma hidima.

Yasir Ramadan Gwale 
29-04-2015

No comments:

Post a Comment