Thursday, April 16, 2015

Bazuwar Labarin Kanzon Kurege A Facebook


BAZUWAR LABARUN KARYA A FACEBOOK 

A 'yan kwanakin nan, ana ta baza ko yaya ta labaran kanzon kurege wadan da ba su da tushe balle maka anan facebook. Babban abinda yake bani mamaki shi ne yadda wasu kan dauka duk labarin da suka gani a facebook gaskiya ne, ba tare da bincike ko tabbatar da sahihancin da kafar da labaran ya fito ba sai kawai mutane su hau yadawa. Ya isa a kira mutum makaryaci idan duk labarin da yaji zai yada.

Tun bayan da aka kammala zaben Shugaban kasa wasu shafuka a Internet da facebook suke ta yada jita jita mara kan gado. Misali a kwanakin nan an ta baza wasu labarai na karya wai sabon zababben Shugaban kasa Yaki ganawa da Abdullahi Inde Dikko babban Shugaban hukumar kwastam  ta kasa,  wanda ko kusa wannan bai yi kama da gaskiya ba, sananne ne cewar tunda Buhari yaci zabe gidan sa a Bude yake ga duk masu zuwa taya shi murna, hatta masu wasan kwaikwayo sun je sun taya shi murna balle kuma ace Shugaban hukumar kwastan, wanda jiharsu daya da Buhari. Wannan labari na karya babu wata sahihiyar kafa da ta ruwaito shi sai dai wasu shafaka na makaryata.

Haka nan, aka dinga yaya ta cewar wai tsohon Shugaban kasa Olushegun Obasanjo wai ya maida kudi kimanin  $200 Miliyan zuwa asusun Gwamnati kuma wai yayi alkawarin tonawa wasu asiri matukar basu dawo da abinda suka dauka ba, kaga wannan labari duk mai hankali da sanin meye Gwamnati ya san ko kadan ba gaskiya bane. Haka nan fa, aka dinga yada cewar wai kudin nan $20Bilian da tsohon Gwamnan babban bankin kasa Sanusi Lamido yace ba'a shigar da su Bankin ba wai anga kudin a Bankin Zenith.

Sannan kuma a wannan Makon aka kawo labarin cewar wai Bankin Duniya ya fitar da sunayan manyan Barayin Najeriya, inda aka dinga bada sunayan wasu fitattun mutane wai sune manyan barayi, kaga dai duk mutum mai tunanin ya san duk wadannan labaru basu yi kama da gaskiya ba. Ko kuma mutane su dauki hoton wani mutum ko wani shugaba a wata munasaba da ta faru a baya, su jingina da wani abu da ya faru a yanzu, su kuma mutane babu bincike kawai sai su yada. Yana da kyau mutane suji tsoron Allah wajen yada labarin karya.

Shafaka da dama irinsu Hope for Nigeria, Scannews, report247, Naijagossip, Hausa24​ da sauransu da dama duk sun shahara  wajen yada jita jita da labarin karya a facebook. Hatta gidan jarida irin Rariya​ su kansu sukan tsinci irin wadannan labarai a facebook su yi musu kwaskwarima  su yada ba tare da tantance wa ba. Wannan basu san cewar rage musu kima da daraja yake yi ba. Kafafan yada labarai irinsu Premium Times​ da Leadership Newspapers​ da Daily Trust​ da BBC Hausa​ da VOA Hausa Service​ labaransu yafi kusa da gaskiya, duk da cewar ba zaka ce dari bisa dari duk abinda suka fada gaskiya bane, amma basu cika yada jita jitar wani abu da bai faru ba, musamman a siyasar Najeriya. 

Haka wata rana, wani Malami, daga ganin irin wadannan labarai a facebook  kawai ranar juma'a yana huduba ya dinga kafa hujja da irin wadannan labarai na karya, sai da aka idar da Sallah wani ya same shi yake tambayar sa gaskiyar abinda ya fada, Malamin budar bakin sa sai cewa yayi ga abu nan duk ya cika internet da social media,  mutumin ya cewa Malamin shin yanzu duk abinda ka gani a littafi gaskiya ne? Abu ne mai cike da takaici da damuwa kaga mutane masu kima suna yada irin wadannan labaru marasa tushenmu balle makama. 

Lallai yana da kyau, mutane su kiyaye wajen gaggawar yada irin wadannan labaru na kanzon kurege. Godiya ta musamman ga  Doc. Ibrahim Musa da Jaafar Jaafar​ da suka ja hankalinmu akan yada jita jita da ake ta faman yi a yanzu.

Yasir Ramadan Gwale 
16-04-2015

No comments:

Post a Comment