Saturday, April 18, 2015

Abin Da Ke Faruwa A Sawuz Afurka: Kalubalen Gwamnatin Najeriya


ABINDA KE FARUWA A SAWUZ AFURKA: KALUBALEN GWAMNATIN NAJERIYA 

Ba shakka wannan lamari yayi muni matuka, abu ne mai karkada zukata idan mutum ya kalli hotunan yadda ake Bankawa mutane wuta da ransu a sawuz Afurka. Ni kam, nace Allah ya isa, ga duk wadan da ke aikata wannan ta'addanci,  ba maka wa masu aikata irin wannan kisa na al'ummar da basu jiba basu gani ba zasu gamu da fushin Allah.

Abin akwai daure kai yadda ake ta yayata wannan batu a duniya, amma har yanzu babu wani kwakkwaran mataki da Gwamnati a Johannesburg ta dauka dan magance cigaban wannan ta'addanci, sannan tarayyar Afurka bata yi wata suka da kakkausar murya akan Gwamnatin Shugaba Zuma ba. Allah ya isa akan wannan ta'addanci.

Lallai ya dace Gwamnatin Najeriya ta dauki mataki na gaggawa domin kubutar da rayukan 'yan Najeriya da ke can. Akwai abin takaici da rashin tunani, a lokacin da kasashen turai ke mancewa da bambance bambancensu suna dunkulewa su zama al'umma daya, suna rayuwa ta bai daya, sannan ace mu mutanan Afurka jahilci da dabbanci yana kara bayyana a tare da mu.

Mu 'yan Afurka Turai suka hada baki suka bautar da mu, suka kakaba mana wasu abubuwa da basu dace da al'adunmu ko addinin mu ba, a lokacin da ya kamata ace mun hadu mun kalubalanci bautar da mu da akai, mu jingine duk wani kaya na Bature mu dauki namu da suka dace da yanayi da al'adunmu amma sannan ne zamu maida kanmu baya.

Wannan abin da yake faruwa a Afurka ta kudu, nayi Imani ba wai kawai akan bakaken mutane ake huce haushi ba, akan 'yan Najeriya ne, kuma wannan batu ba wai kawai a SA ba, har da sauran kasashen Afurka suna da irin wannan mugun nufi da tunanin 'yan Najeriya sun zo musu kasashe suna cine musu arziki.

Kuma wannan al'amari idan ba Gwamnatin Najeriya ta dauki Matakin da ya dace ba, 'yan Najeriya zasu fuskanci kalubale da yawa a kasashen Afrika da na larabawa.  Lallai tilas Gwamnati ta dauki Matakin da ya dace, dan magance faruwar wannan dabbanci da jahilci da ke tsiraita dan Adam.

Haka kuma, dole 'yan Najeriya a duk inda suke su hada kansu, sannan su zama jakadu na gari ga kasarsu. Sau da yawa mu muke bayar da dama a duk wani cin fuskar da ake mana, daya daga cikin kasashen larabawa wani yace idan kaji an kama masu laifi goma zaka samu 4 ko 5 'yan Najeriya ne. Kullum mune sata, fashi, Damfara,  almundahana, zamba-cikin-aminci, yankan-baya, kwace, zina,  caca,  shan-giya da sauran nau'ikan laifuka duk mune. Ya zama dole mu sauya halayen mu,  mu mutunta kanmu, mu girmama kanmu, sannan duniya zata ga mutunci da darajar mu. 

Yasir Ramadan Gwale 
18-04-2015

No comments:

Post a Comment