Thursday, April 9, 2015

In Sha Allah Idan Mun Ci Zabe Zamu Sha Lamurje


IN SHA ALLAH IDAN MUNCI ZABE ZAMU SHA LAMURJE 

Ina amfani da wannan damar nayi kira ga dukkan abokina da 'yan uwana na kusa da na nesa da dangi dake Kano da su fito ranar Asabar su zabi Malam Salihu Sagir Takai​ a matsayin Gwamnan Kano na gaba. Alamar jam'iyyar mu ita ce Lema, a duba daidai wajen da aka rubuta PDP a dangwala a inda aka ware dan yin hakan. Munyi muku alkawarin In Sha Allah ba zamu baku kunya ba, zamu yi Gwamnatin al'umma domin hidimtawa al'ummar jihar Kano. 

Dan takarar mu Malam Salihu Sagir Takai yayi Shugaban karamar hukuma yayi kwamashinan kananan hukumomi da na Ruwa amma ba a sameshi da cin dukiyar al'umma ba bisa ka'Ida ba. Ya fada da bakin sa cewar duk wanda ya gani ko ya sani ko ya tabatar shi Malam Salihu Sagir Takai yaci dukiyar Gwamnati ba bisa doka ba, yace idan ya rufa masa asiri ya cuci al'umma, Alhamdulillah har yau babu inda aka samu Malam Salihu da diban dukiyar al'umma ba bisa doka ba. 

Dan haka muna tabbatar wa da al'ummar Kano inganci da nagarta  da amana na dan takarar mu Malam Salihu Sagir Takai, yayi shugabanci abin misali, dan haka mun tabbatar zai iya wannan aiki na Gwamnan Kano. Jama'a a fito ranar zabe a zabi Malam Salihu Sagir Takai na jam'iyyar PDP domin cigaban Jihar Kano.

Haka nan kuma, muna kiran al'umma musamman magoya baya da su fita kasuwa a gobe su sayo Zoborodo  da citta da kanam-fari da masoro  a jika a cikin kyakkyawaan  mazubi a sanya sukari da kankara domin yin murna da nuna godiya ga Allah a yayin  da aka fadi sakamakon zabe.

Zamu sha lamurje ne sabida yafi kara lafiya da kuzari,  sannan hakan zai taimaka wajen habaka tattalin arzikin 'yan kasuwar mu na kurmi dake kasuwancin  citta da kanam-fari da masoro.  Sannan ga wadan da suke da hali suma su tanadi tinkiya b'atala mara kitse dan shan shagali. Dan uwa uwa Malaminmu Dakta Jamilu Zarewa​ yayi fatawa akan halarci a nuna murna ta irin wannan siga aci asha a gode wa Allah.

Allah ya bamu Nasara, ya tabbatar mana da alheri a jihar mu da kasarmu baki daya. Allah yasa ayi zabe lafiya a gama lafiya, Allah ya bamu Nasara akan abokan takarar mu.  Dan takararmu Ya Allah idan ka bashi Nasara kayi riko  da hannunsa  kayi masa jagora, Ya Allah Kada ka barshi da iyawarsa. Kano Sai Takai In Sha Allah.

Yasir Ramadan Gwale
09-04-2015 

No comments:

Post a Comment