Thursday, April 9, 2015

Gugawar Sauya Sheka Daga PDP zuwa APC: Koma Baya Ne Ga Demokaradiyyar Najeriya


GUGUWAR SAUYA SHEKA DAGA PDP ZUWA APC:  HADITHUR-ROUH!

Hamayya ko Adawa a siyasance, ita ce ke motsa tafiyar siyasar Demokaradiyya. Yin Hamayya mai ma'ana da nufin zaburar da masu mulki dan aiwatar da kyawawan manufofin da suka yiwa al'umma alkawari  da kuma kalubanatar manufar Gwamnati da ka iya durkusar da kasa, wannan shi ne abinda Demokaradiyya ke bukata a tsarin Hamayya.  Amma a yayin da aka ce Gwamnati bata samun Hamayya mai karfi daga jam'iyyun Adawa, wannan shi ne kansa Shugabanni kanci karensu babu babbaka, daga nan sai Demokaradiyya ta koma kama karya, kamar yadda hakan ke faruwa a Galibin kasashen Afurka  musamman na Arewaci, idan muka dauki Sudan da Masar da Tchadi da Algeria, dukkansu Gwamnatoci ne da suke kiran kansu na Demokaradiyya amma sabida rashin kakkarfar Hamayya dan amfanin siyasa da 'yan kasa sai ka mance ana yin Gwamnatin Demokaradiyya  a wadannan kasashen. 

Kasashen da suke da tsayayya kuma shimfidaddiyar Hamayya sun fi saurin samun cigaba cikin sauri,  domin Gwamnati na da masaniyar al'mma na iya juya mata baya, dan haka irin wadannan Gwamnatoci kan tsaya suyi aiki bilhakki da gaskiya. Hamayya mai ma'ana kan sanya Shugabanni da jam'iyyu shiga taitayinsu da kuma hidimtawa al'ummar su gwargwadan karfin su. Kyakkyawan misali akan haka itace kasar Amurka inda Hamayya ke da karfi, kuma Gwamnati kan shiga taitayinta wajen aiwatar da manufofin gina da kuma cigaban kasa. Anan kusa da mu muna ganin yadda Hamayya ke motsa Gwamnati a jimhuriyyar Nijar da sauran kasashen irinsu Senegal.

Guguwar sauya sheka daga PDP zuwa APC da ta kunno kai tun bayan da jam'iyyar Hamayya ta APC ta samu Nasara a zaben Shugaban kasa da na majalisun dokoki, wannan ba zai haifarwa Demokaradiyya d'a mai ido ba a Najeriya. A baya rashin samun jam'iyyar Adawa mai karfi a Nigeria shi ya sanya Gwamnatin PDP tunanin zata iya shekaru 60  ba tare da an tankwabe mulki daga hannun ta ba. Amma tun bayan da jam'iyyar APC ta kafu, PDP  ta shiga taitayinta ta fahimci yanzu ba da bane.  Misali adawa ta sanya Gwamnati tayi fatali da yin dokar aure jinsi a Najeriya da sauransu da dama.

Haka kuma, Hamayya ta sanya Gwamnatin PDP daukar matakai dan magance tsaro a baya-bayannan. Babu ko shakka, Hamayya ita ce gishirin Demokaradiyya, wannan kuma ke sanya gwamnatoci su himmatu wajen biyan bukatun al'umma. Amma abin da yake faruwa a yanzu na guguwar sauya sheka da wasu 'yan PDP suke zuwa APC wannan ya nuna kwadayi da kulafucin neman mulki irin na 'yan siyasar wannan lokacin, wannan na kara tabbatar da cewar da yawan 'yan siyasar ba hidimtawa kasa ne a ran su ba illa kawai rike madafun Iko dan biyan bukatun kansu. 

Ni sai naga kamar akwai rainin wayo ace mutum yana PDP tsawon Shekaru 16 yana ta yiwa 'yan Hamayya gwalo da fatan tsiya, amma yanzu kawai dan PDP  ta rasa mulki yace ya barta wai babu adalci a cikin ta,  wannan ya zama wasa da hankalin 'yan Najeriya. Idan aka wayi gari duk wani kusa na siyasa a PDP Ya fice ya koma APC  to su wa za'a kalubalanta  dangane da abubuwan da suka faru a baya?

Kamar yadda tsohon Shugaban kasa Obasanjo duk da irin tsayar da ya taka,  da aikata muggan laifuka na magudin zabe, da yunkurin karya tsarin Mulki dan tabbatar da kansa a matsayin Shugaban kasa da kassara kasa, shi kenan sai ya zama mutumin kirki dan ya goyi bayan APC? Idan aka wai gari shima Goodluck Jonathan ya koma  APC  ya kenan, su waye zasu cigaba da amsa gazawar PDP a shekaru 16?

Ya zama tilas talakawa su tashi su farka su sani cewar da yawan 'yan siyasa tara tara sukai mana, ta yadda ake san maida neman Shugabanci ya zama gado ko kuma sai wasu tsirarun mutane da suka taba rikewa a baya, mutane su gama shuka tsiya a PDP  sannan rana tsaka su koma APC  sannan a ce sune mutanan kirki,  su ne zasu sake zama wane da wane? Mutum idan ya rasa mukami anan ya koma can kuma kaga anbashi. Wannan tsiya har ina!

Dan haka dole sabon Shugaban kasa yayi taka tsantsan da baragurbin da ke neman durkusar da Demokaradiyar Najeriya. Buhari shi ne Shugaban da  zai Fi kowanne Shugaba samun kalubale a Najeriya, domin shi ne wanda duk ido ke kansa, kuma ake da yakinin dari bisa dari gyara yazo yi ba neman mulki ko tara abinda duniya ba. Dan haka samun mutane wadan da zasu hidimtawa al'umma shi ne mafita a gareshi.

Yasir Ramadan Gwale 
09-04-2015

No comments:

Post a Comment