Friday, April 3, 2015

Darasin Da Buhari Zai Dauka Daga Rusasshiyar Gwamnatin Mursi Ta Masar

WANE DARASI BUHARI ZAI DAUKA DAGA RUSASSHIYAR GWAMNATIN MURSI TA MASAR? 

A lokacin da ake ganin wata gugawar sauyi ta fara kadawa a kasashen Arewacin Afurka da ta faro daga Tunisiya, masana da masharhanta sunyi fashin baki sosai akan yadda wannan guguwa zatai awon gaba da shugabanni da dama musamman masu kama karya da sunan Demokaradiyya. Wannan guguwa bayan da tayi gaba da Zain el-Abideen Ben Ali babu zato ba tsammani, ta cigaba da bugawa nan da can a kasashen larabawa. 

Dubu dubatar Misrawa ne suka fito kan tituna suna rera wakokin canji tare da Allah wadai da shekaru 30 na Gwamnatin kama-karya ta Muhammad Hosny Mubarack. Mista Mubarack yaga ta kansa lokacin da al'umma ta hadu a dandalin 'yanci na Tahrir dan kira a gareshi ya san inda dare yayi masa. Ba shiri Mubarack yayi sallama da kujerar da ya shafe sama da shekaru 28 yana rike da ita a matsayin Shugaban kasa.

Bayan da Mubarack ya tafi ne, aka shiga fafutukar ganin wanda zai gaji Gwamnati, inda Ikhwanul Muslimin​ sukai tasiri kwarai da gaske a yayin wannan guguwa ta sauyi. Lokacin da zabe yazo gab ne, ba zato Allah ya kutso da Muhammad Mursi, inda Miliyoyin al'ummar Misrawa suka hadu akan Allah ya baiwa Mursi Shugabancin kasar. Duk da irin mahaukatan kudade da su Ahmed Shafeeq wadan da gyauron Gwamnatin  Mubarack ne sukai amfani da su a wannan zabe, amma sai da guguwar sauyi ta tabbatar da Mursi a matsayin sabon zababben Shugaban kasa na farar hula a karon farko a tarihin Demokaradiyyar Masar.

Bayan da Mursi ya zama sabon zababben Shugaban kasa, duniya baki daya ta zura masa ido taga wacce irin Gwamnati Muhammad Mursi da kungiyar Muslim Brotherhood zasu yi. Misrawa sun zabi Mursi tare da kyakkyawar fatan cewar zai fitar da su daga halin kangi da danniya da babakere da ake ganin anyiwa Masar tun zamanin Gamal Abdel-Nassir.  A gefe guda gyauron Gwamnatin Mubarack  basu yi kasa a guiwa ba wajen ganin Gwamnatin Ikhwan karkashin Mursi bata ci Nasara ba, sannan a daya gefen ga Misrawa na ci-da-zuci da fatan ganin sha-yanzu magani-yanzu.

Misrawa sunyi gajen hakuri tare da gaggawa gami da gandokin ganin Gwamnatin Mursi ta gyatta Barnar da Mubarack yayi cikin kusan Shekaru 30 a cikin kankanin lokaci. Ba shakka Mursi an kyautata masa zaton cin Nasara da kaso mafi rinjaye a Gwamnatin sa. Sai dai tafiya ba tayi Nisa ba Misrawa suka fara zargin Mursi da fifita wani sashe a matsayin sune kadai wadan da zasu baiwa Gwamnatin sa shawarar yadda za'a aiwatar da al'amuran Gwamnati, da kuma yunkurin da Mursi yayi na baiwa kansa iko da karfi karkashin tsarin Demokaradiyya.

Sannan kuma, Gwamnatin Mursi ta shagaltu da yin Shari'ah ga hambararren Shugaba Mubarack  wanda duk da wannan guguwa da tayi awon gaba da Mubarck yana da dumbin magoya baya masu yawan gaske. Ba'a je ko ina ba, aka sabauta Gwamnatin Mursi ta yadda gyauron Gwamnatin Mubarack suka dinga yiwa Gwamnati adawa mai karfin gaske, a gefe guda kuma ana zuga al'umma akan cewa Gwamnati na tafiyar hawainiya, wannan ta sanya Misrawa suka kasa baiwa Gwamnatin Ikhwan karkashin Jagoranci Mursi uzuri. Inda cikin shekara guda tal al'umma suka koka da Shugabancin Mursi. Kai ka ce ba sune sukai fitar farin dango wajen nuna soyayya da kauna gareshi ba.

Galibin mutanan da suke wajen kasar Masar wannan al'amari yazo musu da bazata, domin shekara daya tak bata kai ace sabon Shugaban kasa har ya fahimci yadda zai tafiyar da Gwamnatin sa ba ya aiwatar da sauyi sauye. Al'Amura da yawa sun faru, inda Misrawa sukai gajen hakuri suka kasa jurewa abinda suka jima suna mafarki na samun canji, suka sake fitowa kwai da kwarkwata suna Allah-wadai da Mursi da Kiran ya sauka ya basu waje. Yanzu dai ga yadda Mursi ya kare daga mutumin da ake tsananin kauna zuwa fursuna, sannan kuma Gwamnati ta koma hannun da ta baro. Allah mai iko!

Ba shakka akwai darussa masu dumbin yawa da sabon zababben Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari​ zai dauka daga Rusasshiyar Gwamnatin Mursi ta Masar, sannan suma al'ummar Najeriya dole su dauki darasi daga al'ummar kasar Masar na yin hakuri da juriya da kuma yiwa sabon Shugaban kasa fatan alheri da fatan kawo sauyi mai ma'ana a sha'anin tafiyar da Gwamnatin Tarayyar Najeriya. Duk da cewa Buhari yana da gogewa ta Mulki yayi Shugaban kasa yayi Gwamna yayi Minista sannan kuma ya shiga takara ba sau daya ba dan haka ne ake sa masa ran cewa zai kawo sauyi cikin kankanin lokaci. Amma dai ba shakka 'yan Najeriya da Sabon Zababben Shugaban kasa zasu dauki darussa daga Rusasshiyar Gwamnatin Mursi. 

Yasir Ramadan Gwale
 03-04-2015

No comments:

Post a Comment