Friday, May 1, 2015

Takaitaccen Tarihin Imam Abu Hanifa Rahimahullah


IMAM ABU HANIFA

Imam Abu Hanifa asalin sunan sa shi ne: An-Nu’uman bin Thabit, At-Taimi, Al-Kufi, an haife shi a shekara ta (80A.H) a birnin kufa na kasar Iraqi ya hadu da wasu daga cikin sahabbai kamar Anas bin Malik, amma ana cewa ba shi da riwaya ko daya daga sahabi. 

Imam Abu Hanifa daya ne daga cikin manya-manyan Malaman Muslinci, wanda sukaiwa addini Allan hidama, kuma al'muma ta amfana da tarin ilimi sa,  Allah ya ba shi tarin ilimi da yawan ibada, ana cewa yana saukar kur’ani duk dare. 

Abu Hanifa yana cewa: wata rana na yi mafarki wanda ya razana ni, na yi mafarki kamar gani ina tono kabarin Annabi (SAW) sai na tafi Basra na sa wani mutum ya tambayar min Ibn Sirin ma’anar wannan mafarki, sai Ibn Sirin ya ce: wannan mutumin zai dinga tono hadisan Annabi (SAW). 

Yahya bin Ma’in yana cewa: Imam Abu Hanifa thiqa ne, ba ya rawaito hadisi sai wanda ya haddace, ba ya rawaito hadisin da be haddace ba. Imam Abu Hanifa ya rasu a shekarata (150A.H). 

Yasir Ramadan Gwale 
01-05-2015

No comments:

Post a Comment