Saturday, May 9, 2015

Kotu Ta Yanke wa Hosny Mubarack Hukunci


SHARI'A SAI MISRAWA

Kotu yau a Masar ta samu Tsohon hambararren Shugaban Masar Hosny  Mubarack da 'ya 'ya sa biyu Alaa da Gamal da almubazzaranci da kudi kimanin  Dollar Miliyan 18, ta kuma yanke musu hukuncin daurin shekaru uku, ta kuma ce hukuncin zai faro ne tun daga 2011 lokacin da Mubarak ya bar Mulki, dan haka tuni ya gama wa'adinsa na wannan hukunci. A sakamakon haka Kotu ta sallami Mubarack ya koma gida shi da 'ya 'yansa a wannan Shari'ah. Yanzu dai zamu ga yadda Mubarack zai tashi daga kan gado yayi tafiya da kafar sa. 

A hannu guda kuma tsohon zababben  Shugaba MuhammadMursi da aka hambare na can a gidan sarka WAI ana zargin sa da kisan masu zanga zanga guda uku. Ai maka juyin Mulki bisa zalinci sannan a kama ka a daure, a kakaba maka laifin da baka aikata ba. Tab!

 Amma abinda suka manta shi ne, a Lahira ma akwai  wata Shari'ah. Allah ya fada duk wadan da aka zalunta sai ya saka masa, da yawa ba zasu taba fahimtar zancen Allah gaskiya bane, sai ranar da Allah ya kira da kansa Ranar tonan asiri. Ranar da Lauyoyi da Alkalan Bogi su kansu ta kansu suke yi. Allah ya kyauta karshen mu. 

Yasir Ramadan Gwale 
09-05-2015 

No comments:

Post a Comment